Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nesa Abbu ya hango Abba ya zube ƙasa da sauri ya ƙarasa gurinda yake cikin ruɗewa yace Muhammad Muhammad Innalillahi wa'inna Ilaihi Raju'un me ya samekane halan?

Ruwa ya zuba masa tare da Fara karanta duk wata addu'a da tazo bakinsa Yana tofa masa, a hankali yafara motsawa can kuma ya tashi zaune yana Kalle Kalle, "Sannu Muhammad" Abu ya faɗa yana riƙe masa kafaɗa. Kallon Abbu yayi yace "me yafaru dani Yaya?" "Ba Abunda yasameka ka kwantar da hankalika Kaji"
Yaya haka Kawai Naji wani yanayi da ban taɓa jin irinsa ba, Yaya naji duk jikina yayi weak dan Allah Kamin addu'a Yaya ya faɗa hawaye na bin kumatun sa.

Da sauri Abbu ya rungume Shi ajikinsa
Shima hawaye fall Idanunsa Yana Jin wata ƙuna Aransa wacce tun rasuwar mahaifiyarsu Rabon da yaji irinta, cikin rawar murya Abbu yace "kadaina Kuka Muhammad Idan Naga kana hawaye nakanji cewa nakasa riƙe Amanar mahaifiyarmu ne, kai Amanata ne Bana son duk wani abunda Zai taɓaka ko Yaya ne" Abba yanajin kalaman Yayan nasa ya ƙara rungumeshi sosai Yana ci gada da sauke wata ajiyar zuciya.

Kamar Wanda aka mutsukka ya janye jikinsa daga na Abbu yace "Yaya Ina Ahanaf inaji ajikina Kamar najima ban saks Shi a idanuna ba" cike da mamaki Abbu ya ƙurawa Abba Ido Aransa Kuma Yana Nazarin tabbas abinda Haj Mama ta faɗa gaskiya ne Kenan?
"Yaya Ina Ahanaf" Abba yaƙara maimaita tambayar Abbu.
Numfashi Abbu ya sauke tare da cewa "Ahanaf yana lafiya saidai baya Nan yayi tafiya" Tafiya kuma Yaya? Ina Ahanaf yaje batare da ya sanar dani ba?

Abba yace "Yaya Dan Allah kafaɗamin me yasameshi inaji ajikina ba lafiya yake ba, Yaya nasan waye Ahanaf ba gurinda zaije Batare da ya sanar min ba.

Abbu yace "Kanutsu Muhammad insha Allah Ahanaf yana cikin ƙoshin lafiya"








______________ Fitowa tayi daga ɗakinta hankali tashe a parlour taci Karo da ƙaseem Shima ya fito daga ɗakin nasa cikin tashin hankali. Kallon Norr yayi cikin mamaki yace "Norr lafiya me kikeyi anan?............✍️✍️✍️








Nabeela Binji ce💃💃💃







More comment
More taping 😉😉


♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM


PAGE

2️⃣ 8️⃣










______________ Norr tace "Kaine ya kamata na yiwa wannan tambayar ƙaseem Ina Ya Shadow?" Kan ƙaseem ya ɗaure sosai wannan wane irin lamari ne haka.

Kallon Norr yayi Amma kuma ya kasa yayi Magana juyawa kawai yayi yafita harabar gidan, anan ma Kansa ne yaƙara ƙullewa saboda shidai a iya saninsa wannan gidan Yayansa ne Shadow. Tohm meya kawo Shi nan yaushe yazo gidan? Tambayar da ba shida mai amsa masa ita Kenan, Akan wasu fararen kujeru ya zauna tare da dafe kansa da yake masifar yi masa ciwo, lumshe Idanunsa yayi yana tunani, tiryan tiryan abunda ya faru yafara dawo masa tun lokacin da aka ɗaura Aurensa da Norr saɓanin Yayansa Shadow har izuwa lokacin da bacci yayi awon gaba dashi daga nan ba abunda ya ƙara tunawa kuma.

Da sauri ya buɗe idanunsa waƴanda yanzu har sun sauya Kala tsabar shiga ruɗani. Innalilla wa'inna Ilaihi Raju'un me yake faruwa dani ne Kodai mafarki nayi ne?

Yana cikin wannan halin ne ya hango Norr Tana dun Faro gurinda yake, nan take bugun zuciyar sa ya ƙaru. Addu'o'i Kawai yake nanatawa a bakinsa har ta ƙaraso gurinda yake.
Tana zuwa gurinsa tsaya tare da cewa "wai mai yake faruwa ne ƙaseem?" Ni wasu abubuwa nake gani kamar a mafarki ta faɗa hawaye nabin kumatun ta.

Runtse Idanunsa yayi shima sannan yace "Nima haka nakeji Norr nakasa gane a wace duniyar nake."

Kanta ta ɗauke daga kan fuskarsa tace "Dan Allah muje ka kaini gida Ina So Naji gaskiyar Abunda yake faruwa" saidai driver ya kaiki nima namu gidan nake son zuwa yanzu.

Bata ƙara ce masa ƙala ba ta nufi hanyar fita faga gidan, Saida tayi Tafiya mai Nisa sannan ta haɗu da mai napep misalin gurinda zai kaita tayi masa sannan ta shiga suka Fara Tafiya.

Tunani Kala Kala ne a zuciyar ta.
Taya akayi taga kanta gida ɗaya da ƙaseem ba Ahanaf ɗinta ba?
Me ya faru da ita tun Bayan ɗaura wannan rikitaccen Auren?

Gabaki ɗaya kwakwalwarta ta cunkushe jima take kamar idan taci gaba da tunani brain ɗinta zata iya tarwatsewa.

Mai napep yana Isa ƙofar gidan su ta hango Yassar zai shiga gidan da sauri ta kwala masa kira.
Tahowa yayi dan ganin mai kiransa.
Norr ya faɗa cikin mamaki.
Tace "dan Allah Yassar Idan Akwai kuɗi a hannunka ka bawa mai napep ɗin nan" Kuɗin ya bashi.

Zasu Shiga cikin gida Yassar ya Kalle ta yace "kinzo Duba jikin Dady ne?" Da sauri ta Kalli Yassar tace "Mai ya sameshi, Dama bashida lafiya ne? Shine bansani ba sai yanzu da nazo?

Yassar yace "a'a Norr ba haka bane Yau fa lafiya Lau Dady ya fita gurin aiki ba Abunda yake damunsa" Nima ina zaune aka Kirani a waya wai nazo Dadyn mu ya Suma.
Koda naje natar da ya farfaɗo.
Naso na wuce dashi asibiti sai yace a'a Kawai dai na kawoshi gida. Yanzu haka ma yana part ɗinsa.

Kan Norr ya ƙara ƙullewa sosai wannan wace kalar Rana ce da tazo mata ba fasali?






_____________ wayar Abbu ce ta Fara ringing ɗauka yayi ya ƙara a kunnensa tare dayin sallama, murmushi Abbu yayi yace "Toh Angode Allah za'a ce Haidar Ina Kamalu?" Gashi Abbu Haidar ya faɗa Yana bawa Kamal wayar Bayan sun gaisane Kamal yasaka wayar a speaker. Suka tambayi labarin Ahanaf kamar yadda suka Saba Idan sunyi waya.
Gyara zama Abbu yayi tare da furzar da iska Mai zafi yace "labarin Ahanaf dai Kam Shiru har yanzu bamuji komai ba Amma kuma har yanzu bamu sare ba D.p.o Abdul Naseer Yana Kan aikin sa na bin cike.
Mu kuma muna kan miƙa buƙatanmu gurin ubangiji"
Ajiyar zuciya Haidar yayi sannan yace "Muma nan bamu sare ba Abbu Muna iya bakin ƙoƙarin mu gurin addu'a dafatan Allah ya nuna Mana Shi cikin ƙoshin lafiya" Allah ya saka muku da mafificin Alkhairi
"Ameen ameen Abbu"


Abbu yace "yawwa kuna Jina?"

"Eh" munajinka Abbu

Abbanku ya dawo cikin hankalinsa ɗazun nan Bada jimawa ba, kuma ba Wanda ya Fara tambaya Sai Ahanaf.


"Da gaske Abbu? Dama na faɗa maka abunda Haj Mama ta faɗa Zai iya Zama gaskiya" Amma kuwa Lallaima waƴan nan Mutanen sun cika marasa Imani" Kamal ya gaɗa cikin tsantsar mamaki.

Abbu yace "a'a Kamal har yanzu bazamu yanke hukunci Akan zargin mu ba sai mun Samu cikakkiyar hujja. Idan muka samu hujja Mai ƙarfi anan zamu kama su dumu dumu kuma ko basuyiwa Allah sai sun nuna mana gurinda suka Kai Ahanaf, saboda Shakka Babu Idan dai sune masu laifin to tabbas sune suka ɓatar da Ahanaf" Dady Yace Ko ya kuka Gani?" Haidar yace nima tunanina Kenan Abbu yakamata mu bi Kumi a hankali Saboda dama Idan baka iya Kama ɓarawo ba sai shi ɓarawon ya Kama ka. KAMATA YAYI TUNANIN MAI BINCIKE YA ZARTA Na MAI LAIFI. Kuma yanzu dole musake sabon Salo Abbu.
Saboda wannan gaɓar tafi kowace haɗari zasu iya Komi Dan gudun tonuwar asirin su. A yanzu yazama dole Abba yasan halinda Ake ciki saboda banga an fanin ɓoye Masa Komai ba" Abbu ya gamsu sosai da shawarar Haidar yace "Nima kaina nayi wannan tunanin namesake kuma Insha Allah Komai zai tafi cikin tsari" sallama sukayiwa Abbu da Al ƙwarin zasuzo Sokoto cikin kwanakin nan da yarda Allah.
Abbu yaji daɗi sosai tare da yi musu fatan Alkhairi ya katse Kiran.


Parlour ya Koma, agurinda ya bar Abba anan ya Tarar da Shi, zama yayi kusa dashi tare da dafa kafaɗar sa yace "ya akayi Muhammad tunanin me kake?" Numfashi Abba ya furzar tare da latsa wayar hannunsa yace "tun ɗazu nake Kiran Number Ahanaf Amma Bata Shiga, hankalina ya Tashi Yaya Ina son Naji Koda muryar sane kamfin na ganshi Dan Allah" ya faɗa Yana marairaice fuska.
Ajiyar zuciya Abbu yayi sannan yace "zakasan halinda Ahanaf yake ciki, yanzu dai abinda nake so dakai Shine ka Kira abokin ka Alh Mukhtar Salah kace dashi yazo nan gidan shida iyalansa" da kallon mamaki Abba yabi Yayansa.
"Bazaka Kira Shin bane?" Abbu ya tambayi Abba.

Waya ya ɗauka tare da Danna Kiran Number Alh Mukhtar.

Ɗagawa yayi tare dayin sallama, bayan sun ɗan gaisa Abba yace "Dan Allah Idan da hali kazo gidana Yaya Na nemanka kaida iyalinka" Ajiyar zuciya Alh Mukhtar yayi sannan yace "Dama koda baka kirani ba ina da niyar zuwa gidanka dumin warware wata sarƙaƙiyar saƙa, da yayewar DUHUN DA YA BAIBAYEMU YAYI MUNA BAƘAR INUWA" Kalaman Alh Mukhtar sun saka Abba a cikin ruɗu sosai. Kallon fuskar Yayansa yayi Amma ga mamakin sa Sai yaga yana murmushi. Kuma da alama yaji kalaman Alh Mukhtar Duk da wayar ba'a speaker take ba Amma ana Ji.


Shikuma Abbu lumshe Idanunsa yayi Yana tunanin tattaunawar sa da Ƙaseem.
Saboda ƙaseem Yana shigowa gidan da Abbu ya Fara cin Karo Kuma yayi masa duk wasu tambayoyi yasamu wasu bayanai da yake son ji daga bakinsa.








_____________ Zaune suke a Babban parlourn gidan Suna Hira. Ammi zaune Kan doguwar kujera Shabana ta kwanta ta ɗaura Kanta a Kan ƙafafun Ammi.

Hidayat da Hafeeza Sai faman tsokanar ta suke wai ƙatuwa da ita tazo ta haye ƙafafun tsohuwa. Shabana Bata ce Musu ƙala ba saboda bugun zuciyar ta da taji yana ƙaruwa kamar zuciyar zata faɗo ƙasa.

Ammi tace "ba ruwanku Sa'idinawa ku rabar min da Auta ta, Idan bata kwanta Akan ƙafar ba wazai Kwanta?

Haka Dai sukayi ta tsokanar Shabana Ammi tana kare mata.

Suna a haka sukaji shigowar Mota gidan da sauri Shabana ta rungume Ammi tare da Tura kanta cikin jikinta kamar mai tsoron ganin wani Abu. Kallonta Ammi tayi cikin tausayawa. Tafara Shafa mata Kanta a hankali.


Sallama sukayi tare da shigowa parlourn Kai tsaye.
Ya Suhail da ya Maleek ne a gaba Sai Dady da Shadow a Baya. Gabaki ɗayansu Ido suka zubawa Shadow Suna kallonsa.
Banda Shabana da har yanzu bata ɗago ba Saima ƙara Shiga jikin Ammin take Kamar zata koma ciki.

Zama sukayi akan kujera.
Shikuma Shadow tsaye yayi yana binsu da Ido. Dady yace "zo nan ka zauna Ahanaf" ya faɗa Yana nuna masa kusa dashi. Ba musu yaje Amma Maimakon yazauna Kan kujera sai yazame ya zauna ƙasa. Dady yace "a'a Ahanaf kaima ka zauna kan kujerar mana" kai Kawai ya girgiza alamar a'a nan ma ya Isa.
Dady yaji daɗin girmamawar da Ahanaf yayi masa sosai.

Kallon Ammi yayi yana murmushi yace "yanzu Kam alhmdllh Kumi yazama daidai da yarda Allah kuma ga Ahanaf Mun dawo dashi gida" murmushi Ammi tayi tare da cewa "masha Allah kuma an ɗaura?
"Eh an ɗaura"
"Allah ubangiji ya Baku ladan wannan aikin Alh" ameen ya hayyu ya qayyum.

Hidaya da Hafeeza Sai kallon Shadow suke, Hidaya tace "yanzu shikenan ya dawo cikin hankalinsa Dady?"

Wata Uwar hararar ya Maleek ya zuba Mata, da sauri tasaka hannunta ta rufe bakinta.

Duk cikin maganar da sukayi maganar Hidaya tafi tsaya ma Ahanaf.
Aransa yaƙara nanatawa "yanzu shikenan ya dawo cikin hankalinsa Dady?" Ruɗani fall zuciyar sa Amma yarasa taka mammen abunyi.

Ya Suhail yace "Ammi a sa mana Abinci Dan Allah" ya faɗa Yana yamutsa fuska.

Gabaki ɗayansu Dariya sukayi Banda Ahanaf da Shabana, Dady ya kalli Shabana Yace "Ammin Yara lafiya Auta take kuwa?" Murmushi Ammi tayi tare da cewa lafiyar ta ƙalau Alh.

"Auta"

"Na'am Dady"

"Waya taɓamin Ke?"

"Hafeeza da Hidaya"

"Laaaaah kiji tsoron Allah Shabana" Hafeeza da Hidaya suka faɗa a tare.



Dariya Dady yayi yace "zo Nan ki faɗamin abunda sukayi miki" duk son kai ƙara irin na Shabana Amma yau Sai taji duk Abun ya fitar mata akai.

Saida Dady ya ƙara Kiranta sannan ta tashi Ido biyu sukayi da Ahanaf wata faɗuwar gaba taji da sauri ta ƙarasa gurin da Dady yake tare da faɗawa jikinsa, dariya yayi yace Oh Ni Usmanu Yau ƙurciyar Auta ta motsa zata ƙarya tsoho.
Gabi ɗaya Dariya sukayi, ita koma ta ƙara shigewa jikinsa a Dole taji kunya.


Ammi ta Kalli Hafeeza da Hidaya tace "kuje ku kawo Abinci Dan Allah Kar kusa Suhail ya Fara Mana kuka anan" dariya akayi wannan Karon Harda Shabana, shi kuwa Suhail yaƙara murtuƙe fuska irin Shi an gama Raina Shi ɗin Nan.



Bayan sun Gama jere Abinci ne Ammi tace "Toh Bismillan ku" Dady ya tashi tsaye yace "Auta muje kici Abincin" hannunsa ya miƙawa Ahanaf yace "taso yarona muje kaci Abinci kaima" kai Ahanaf ya girgiza alamar a'a.
Ido Dady ya zuba masa na ɗan Wani lokaci Sannan yace "ba tambayarka nayi zakaci Abinci ba, umarni nake baka akan katashi muje muci Abinci" Dady ya faɗa Yana ɗan murmushi.

Shadow bai sake Magana ba yabi umarni Dady.
Hidaya da Hafeeza suka zubawa kowa Abincin.
Sunacin Abincin Suna ɗan taɓa Hira, ta gefen Ido Shabana ta Kalli Shadow da yake zaune kusa da Dady. Ta lura ba Abinci yake ci ba tun ɗazu juyashi Kawai yake.

Dady Shima ya lura da haka gyaran murya yayi sannan yace "kodai Akwai wani Abu da kake buƙata ne? Ko girkin ne bai maka ba a sake maka wani?" Da sauri Shadow ya girgiza kansa tare da cewa "a'a Dady"
"Tohm menene matsalar ka?" Dady yaƙara tambayar Ahanaf.
Iska ya furzar tare da sunkuyar da kansa ƙasa cikin nutsuwa yace "Dady Ina son sanin nan ɗin Ina ne? Kuma mai ya kawo ni nan? taya akayi nazo?" Dady ya aje Spoon ɗin hannunsa sa yana murmushi yace duk wannan Abun mai sauƙine, yanzu Abunda nake So dakai shine kaci Abinci, Kuma kasaki jikinka, nan ɗin gidan kune duk abunda kake So kawai kayi Kamar kana gidan ku kaji. Wannan ita ce Ammi amatsayin mahaifiya take ga Duk Yaron da ya zauna nan gidan.
Wannan kuma sunan sa Maleek ga Suhail zaka iya ɗaukansu a matsayin yayannin ka, ga Hidaya ƙanwa ce a gurinka Sai Hafeeza ita ma matsayin ƙanwar kace, Sannan ga Auta Shabana uwar rigima Kenan duk Wanda yake son zama lafiya a gidan nan tohm sai yabi Abunda take So, matsayi biyu take da agurinka, yanzu dai ƙanwa anjima Idan Allah ya kaimu zakaji ɗayan" Dady ya faɗa Yana murmushi.

Haɗe fuska Shabana tayi Kamar zatayi Kuka cikin shagwaɓa tace "haba haba Dady yanzu dan Allah daga zuwansa zakaja ya rainani, Kowa anan ka gabatar dashi Amma baka faɗi halinsa ba Saini" Ta faɗa kamar zatayi Kuka

Dukansu dariya sukayi Ahanaf Kuwa murmushi yayi Yana kallonta.

Ganin rigimar Tata tana neman yawane yasa Dady Yace "haba Auta nifa a tunani yabaki nayi bakiji nace Idan ana so a zauna lafiya abiki yadda kike so ba? Dady ya faɗa yana murmushi.

Da kyar dai aka Samu Shabana tadaina rigimar tata, sukaci Abinci alhmdllh Wannan ƴar gabatarwa tasaka Shadow yaɗan saki jikinsa dasu Idan akayi Abun dariya yakanyi murmushi.




Bayan Sallah Isha'i Zaune suke Suna Hira wayar Dady ce tafara ringing da sauri ya ɗaga tare da cewa "Allah gafarta Malam" shuru yayi sai can yace ma sha Allah, "Kawai kashigo Ai Kai kaɗai muke jira" yawwa

Sauke wayar yayi ya Kalli Ammi yace "Malam Ibrahim ne"

"Allah sarki" shine Kawai Abunda tace Dan dama Akwai Hijab ajikinta, Hidaya da Shabana ma haka, Hafeeza kuma ta tafi gida tun Yamma.

Sallama yayi
Suka amsa masa
Bayan sun gama gaisawa Malam Ibrahim ya Kalli Shadow yace "ya jikin naka Ahanaf" Shadow bashida Wani zaɓi da ya wuce yace "da sauƙi"
"Masha Allah"


Malam Ibrahim yayi addu'a Bayan kowa ya shafane yace "tohm dalilin Zaman mu anan shine tattaunawa da kuma sanin wasu sirruka da suke ɓoye"

Malam Ibrahim ya Kalli Shadow yace "Ahanaf Muna So musan wanene kai? Kuma daga Ina kake? menene dalilin shigarka cikin wannan halin?

Shiru Ahanaf yayi ya kasa Magana Saboda Wani Abu da yaji ya danne Masa zuciya mai masifar nauyi ya ɗauki tsawon lokaci a haka.

Dady Yace "Ahanaf ko baka shirya bane mu barka har wani lokaci"
Kai Ahanaf ya girgiza tare da cewa "a'a Dady nafi kowa son Jin taya akayi Na haɗu daku saboda haka dole ne na faɗa Muku wanene Ni" Nan ma Shiru yayi na ƴan wasu mintina kafin da kyar ya buɗe bakinsa yace "SUNANA AHANAF MUHAMMAD IMARAN Ada, Amma a wata Rana da tazo na Fara Shakka Akan Muhammad ɗin shine mahaifina.

Gabaki ɗayansu zuba Masa Ido sukayi cikin mamaki.

Malam Ibrahim yace "menene dalilinka Ahanaf?"

Dalilina Shine Muhammad ɗin Shine sanadiyar tarwatsa rayuwata dalilin Kukana. Dalilin Maida Ranar da nake muradi fiye da kowace Rana tazama Mai DUHU da ƙunci fiye da tunani............✍️✍️✍️









Nabeela Binji ce💃💃💃







More comment
More taping 😉😉







Share Fisabilillah 🙏







♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM


PAGE

2️⃣ 9️⃣









_______________A iya sanina Mun tashi cikin gata da soyayyar iyaye Nida ɗan Uwana Al kaseem ba abunda muka nema muka rasa. Tun Ina yaro ƙarami Allah yabani baiwar Zane ba abunda Bana zanawa.
Ganin haka yasa Bayan na kammala secondary school Abba ya fitar dani ƙasar America ya sakani wata shahararriyar makarantar Zane. Anan naƙara samun gogewa a harakar Zane, har ma Na koyi waƴan da ada banayi sosai wato Zanen gida, mall da sauran abubuwa, a can ne na samu a salin sunan Shadow agurin abokan karatuna.
Shekara ukku na kwashe a ƙasar America kafin Na kammala karatuna kuma alhmdllh nayi nasarar fitowa da kyakyawan result.

Bayan Na dawo gida ne Shaƙuwa mai tsanani tashiga tsakanina da Norr ƴar gidan aminiyar Ayiya wato mahaifiyarmu. Daga farko na ɗauki Shaƙuwar tamu a matsayin gamon jinine kawai sai daga baya na fahimci Sone yake ɗawainiya da zuciyoyinmu.
Mun kwashe shekara ɗaya har da Watannin Muna soyayya da ita akwai Shaƙuwa sosai da fahimatar Juna a tsakaninmu.

Lokacin da aka saka mana Rana da Norr Abba yaso matuƙa ya gina min gidan da zamu zauna,
Amma fafur naƙi yarda. nace "masa ya barshi Kawai Zan iya da kaina" saboda a lokacin ina samun kwangila sosai. Ni na Zana gidan da hannuna Nayi masa kalar tsarin da nake So, sannan na nemi kwararrin masu aikin Gini na sakasu su gina min gidan Kamar yadda yake a Zane.


Bayan an kammala duk wani Shiri na ɗaurin Auren mu. A Ranar ɗaurin Auren ne duk wasu matsaloli suka faru.
A wannan Ranar Na ɗanɗani baƙin cikin da tun zuwa na Duniya ban taɓa cin Karo da irinsa ba. Na gwammace mutuwa da zuwan wannan Ranar.
Da nasan haka Ranar zata zo da ko kaɗan banyi mararin zuwan ta ba.
Dana roƙi ubangiji ya ɗauki Raina kafin ganin Wannan Ranar Mai ɗauke da ƘUNCI da matsanancin DUHU. Yana kaiwa nan ya dakata saboda kukan da yake so yafi ƙarfinsa, Amma yayi Jarumta danne kukan.

Dukansu sun ƙara natsuwa Cox suna So suji menene ya faru a Wannan Ranar.

Shiru Shadow yayi yana ƙoƙarin saisaita Kansa, ya kwashe tsawon mintina Biyar baiyi Magana ba. Kuma ba Wanda ya nemi Shadow yaci gaba da bada labarin saboda sun fahimci ƙuncin da yakeji a zuciyar sa.

Gyaran murya yayi sannan yace "a Maimakon a ɗaura Auren Norr da Ahanaf Kamar yadda mutane sukayi tunani, Sai aka juya ɗaurin Auren zuwa kan ƙaseem ƙanena da kuma Norr din"
Anan Shadow ya Basu labarin Duk Abunda ya faru Bayan ɗaurin Auren.
Ya ƙara da cewa ƙarshen abunda Zan iya tunawa shine Ayiya ta lallaɓani naci Abinci daga nan kuma na Kwanta kan gadonta Bacci yayi awon gaba dani.
Shine Kawai abunda nasani Sai ɗazu da Na farka naganku a tare dani.


Hidayat da Shabana kuka suke Kamar ransu zai fita, Ammi ma hawaye sun cika Idonta fall, ya Suhail da ya Maleek ma idanunsu sun canza Kala.

Innalillahi wa'inna Ilaihi Raju'un ita Kalmar da Malam Ibrahim da Dady suƙa riƙa nanatawa.

An ɗauki tsawon lokaci ba Wanda ya ƙara Magana a cikinsu sai can Malam Ibrahim ya sauke ajiyar zuciya yace "tabbas wannan lamarin Akwai ƙullalliya, maƙirci da kuma sihiri" da sauri Shadow ya kalli Malam Ibrahim cike da mamaki.
Kai Malam Ibrahim ya gyaɗa masa.



Shiru yayi yana tunani kafin daga bisani ya ɗago da kansa ya Kalle su yace "Toh Taya kuka haɗu Dani?" Ajiyar zuciya Dady yayi tare da cewa "naso mubar Wannan maganar har zuwa da safe Ahanaf"
Da sauri Shadow ya girgiza kansa tare da cewa "Dan Allah Dady kutaimaka kusanar Dani ko na samu salama, Wallahi Idan kuka barni na kwana a cikin wannan halin Jini zai iya Hawa kafin safe, saboda tunani Kala Kala ne zasu da baibaye kwakwalwata.



"Gaskiya ya kamata a sanar dashi Alh Usman" cewar Malam Ibrahim.


Murmushi Dady yayi sannan yace "Ai Inaga ba Wanda ya dace ya bayar da wannan labarin Sai Auta saboda ita ce ta Fara zuwar Mana da lamarin ka, ita ta kawoka rayuwar mu da nufin mu taimaka maka" Ido Shadow ya zuba Mata.

Sunkuyar da Kanta tayi ƙasa ba Tare da tace komai ba. "Ke muke saurare daughter"
Hannayenta ta saka cikin na Ammi ta riƙe sosai, Murmushi Ammi tayi sannan tace "kiyi Magana mana Auta"


A hankali ta buɗe bakinta tafara Magana, Ranar wata Laraba da misalin ƙarfe 5 Na Yamma.
Munfito daga gidan Aunty Maimoon yayar Hafeeza.
Zamu dawo gida, sai muka tsaya Shan Mai a Wani gidan Mai saboda muna tunanin Kamar Man ba zai ƙarasa damu gida ba. Anan ne muka haɗu da kai. Kallonta Shadow yake babu ko kyabtawa.
Anan Shabana ta Fara bada labari tiryan tiryan, har ƙaryar da takewa Ammi Akan zataje gidansu Hafeeza, taje gurin neman Ahanaf. Har tazo gurinda Malam Ibrahim yace Ahanaf ɗin bazai warke ba har sai an ɗaura masa aure.
Tana zuwa gurin taja baki tayi Shiru takasa cewa uffan kamar wacce aka sakawa stop.

Wani kalar kallo Shadow ya kewa Shabana Wanda duk ƙula fucin Mutum ba zai ce ga Ma'anar sa ba.


Kowa da yake parlourn ya lura da kalar kallon da Ahanaf yake ma Shabana. Jin kallon da yake mata yayi yawa ne ya sata ɗagowa, cikin sa'a kuwa suka haɗa Ido, da sauri ta kawar da kanta gefe.


Murmushi Dady yayi dan ya lura Shabana bazata ƙarasa labarin ba. Gyaran murya yayi kowa ya maida idonsa Kan Dady Amma Banda Shadow da har yanzu idonsa yake Kan Shabana.

Dady Yace "a lokacin da Malam Ibrahim yayi min wannan bayanin Sai na zauna Ina tunanin taya zamu ɓullowa Wannan lamarin waye Zai yadda ya aureka a cikin irin wannan halin.............. Nan Dai Dady ya ƙarasa labarin har izuwa yau Friday da aka ɗaura Aurensa da Shabana.


Wasu zafafan hawaye ne suka jiƙa fuskar Shadow Ji yake kamar zasu ƙona masa fuska Tsabar raɗaɗi.



Kallon Dady yayi cikin tashin hankali "hauka nayi Dady?" Shadow ya faɗa Yana nuna kansa, Innalillahi wa'inna Ilaihi Raju'un.
Wani Kuka mai sauti ne ya kwace masa yinsa yake har cikin zuciyar sa.
Duk Wanda yake parlourn yaji tausayin Shadow sosai.

Hakan yasa parlourn yayi tsitt ba Abunda yake tashi sai sautin Kukan Shadow.

Ba wanda yayi yun ƙurin hana Shi kukan Saida yayi mai isarsa sannan ya tashi tsaye yafara Tafiya kamar wani ɗan Maye direct gurinda Shabana take zaune kusa da Ammi ya nufa.


Yana zuwa gabanta ya zube a ƙasa Kan gwiwoyinsa, hawaye nabin kumatunsa murya Na rawa yace "me zan miki na sakawa wannan halaccin naki? Kin cece rayuwata kimin Abunda Dangi da ahalina suka kasamin (Shadow a tunaninsa lokacin da yafara hauka su Ayiya wufantar da lamarinsa sukayi) Bakina bazai iya furta adadin godiyar da ta dace da wannan girman halaccin naki ba.
Amma dan Allah Ina roƙon ki kibani dama Na kwantata miki Irin halaccin da kika min da har na koma ga ubangiji Bazan iya Ramawa duka ba.



Shiru Shabana tayi dan har ga Allah ta rasa Abunda zata cewa Ahanaf ɗin.

Gaban Ammi ya koma da jan ƙafa Jim yayi kamar ba zaiyi Magana ba Sai can kuma yace "nagode sosai Ammi Allah ya saka muku da mafificin Alkhairi, Amma dan Allah Ina roƙonki ki taya ni godiya ga wacce tayi sanadiyar dawo dani cikakken Mutum kamar da" murmushi Ammi tayi tare da dafa kafaɗar sa tace "Allah ya kamata ka godewa Ahanaf Shine ya ƙaddarta haɗuwar ka da Shabana kuma ya saka mata lamarin ka arai ya hana mata sukuni, taji Idan har bata taimakeka ba hankalinta bazai Kwanta ba" kaga Shine yafi cancanta a godema.


Tashi yayi yaje gaban Dady zaiyi Magana Dady ya rungume Shi yace "Bana buƙatar godiyar ka Ahanaf kaima ɗana ne tamkar Maleek da Suhail" kallon Malam Ibrahim yayi Shima Malam

Please Login or Register in order to submit comment