Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nufi? Kana so kace Wani ne yazo gurin Nan ya Buɗe wannan ƙofar Shadow ya fita?

Tabbas Kuwa, Haidar ya faɗa Yana gyaɗa kansa alamar tabbatarwa.

Tabɗijam to waye wannan da yake aikata waɗan Nan abubuwan?
Kuma menene dalilinsa nayin hakan?
A Ina yake?

Amsar da ya kamata mu nemo Kenan Kamal.
Amma Koma waye yake wannan aikin tabbas yasan cikin gidan Nan sosai.
Kuma Kai tsaye baza muce a cikin gidan Nan Mai laifin yake ba,
Sai dai Zamu iya cewa akwai Saka hannu Wani agidan Nan, kodai ma menene bincike ne zai nuna Mana gaskiyar wannan lamarin.
cewar Haidar Yana Ƙara Duba gurin da kyau.

Wannan key ɗin shine Abu Na farko da Zamu Fara bincike akai,
Saboda dole ne zanen hannu Wanda yabuɗe ƙofar yafito Idan anyi bincike, baza mu tabashi da hannu ba gudun matsala. "Kamal Shiga ka duba Mana handkerchief Sai mu cire key din Nan.

To Kamal yace, "Ya Shiga ɗakin Yana Dube Dube Kamar Wanda za'ace ma kyat ya gudu, Dan Kamal badai tsoro ba gabaki ɗaya ya tsorata da lamarin wannan gidan abubuwa Sai ƙara Rincaɓewa suke.
Maimakon a Samu Wani haske Sai ƙara tsunduma cikin DUHU akeyi.

Dakyar ya samo handkerchief acikin kayan shadow ya kawowa Haidar,
karɓa Haidar yayi ya buɗe Shi sosai sannan ya cire key ɗin tare da
Dunƙulesa acikin handkerchief ya saka cikin aljihunsa yace "Kamal muje gurin Ayiya mu faɗa Mata halinda ake ciki Sai a san matakin da ya kamata a ɗauka tunkafin wannan Abun yayi Nisa, Haidar ya faɗa Yana Tura ƙofar ɗakin ya rufe ta.


Tafiya suke kowanne su da Abunda yake saƙawa acikin rayuwar sa Har suka ƙarasa part ɗin Ayiya zasu Shiga Kenan sukaci Karo da ita Tana ƙoƙarin fitowa.

Cikin ladabi suka gaidata
Amsawa tayi cikin kulawa tare da tambayar su Ina Ahanaf yake? Batama Bari sun Bata amsa ba ta sake cewa Dama fitorwa danayi dubashi zanje nayi Naji A halinda ya kwana.

Sunkuyar da Kai Kamal yayi idanunsa fall hawaye da mashi ba Dai saurin kuka ba,

Haidar ne yayi gyran muraya sannan yace "Ayiya muje part ɗin Abba Sai muyi maganar a can"


Ba Inda zanje Haidar,
wane Abba Kuma Anya Kana cikin hankalinka Kuwa? Abba Wanda ya wufantar da rayuwar ɗan sa Akan Wani muradinsa.
Ya aikata son ransa batare da ya bayar da Wani dalili ba,
Shine kake cewa muje gurinsa? Ko munje ba Abunda zaiyi Sai Ƙara min ciwon zuciya.
Dan Allah Idan Wani abune yasamu Ahanaf Ku gayamin nice Nan mahaifiyarsa komai Zan iya aikata Akan yarona, Dan Allah Ku faɗamin a wane hali Ahanaf yake?

Kiyi haƙuri Ayiya Amma gwara Dai muje gaban Abba ɗin zaifi,
Zatayi Magana Haidar ya dakatar da ita ta hanyar cewa yanzu fa kikace zakiyi komai dumin ceto ran Yaronki Ayiya,
Dan Allah Ki ajiye duk Abunda kikeji a ranki yanzu muyi Abunda yake shine mafita.

Ba yadda Ayiya ta iya haka tashiga gaba su Haidar Na binta a baya Har suka ƙarasa palon Abba,
Zaune yake Akan 2sit Yana kallon News, Idan ka kalleshi zakayi tunanin gabaki daya hankalinsa Yana Kan TV ne,
Amma Ina idanunsa ne Kawai Akai hankalinsa gabaki ɗaya bayama gurin ya Lula wata Duniyar daban.

Saida Kamal ya ƙarayin sallama Sannan Abba yayi firgigit tare da amsa sallamar da suke Masa Yana binsu da kallon da wacce kuka zo Kuma.

Akan kujera Ayiya ta zauna fuskarta ba yabo ba fallasa,
Haidar da Kamal kuma a ƙasa suka zauna gefen Ayiya.
Shuru ne yaratsa palon ba Abunda kakeji Sai ƙarar tv.
Malamai Idan har bakuda Abun faɗa zaku iya Tafiya Dan Allah, saboda a halin yanzu nafi son Na zauna nikaɗai, Abba yafaɗa idanunsu Akan tv kamar badasu yake Magana ba.
Ayiya zatayi Magana Haidar ya girgiza Mata ka Alamar Dan Allah tayi shuru kawar da Kanta tayi gefe batare da tace ƙalaba.

Gyara Zama Haidar yayi cikin nutsuwa ya Fara faɗawa su Abba duk Abunda ya faru tun bayan kulle Shadow da sukayi ajiya da dare, da Kuma dubawar da sukayi Basu ganshi ba bayan sun dawo masallaci.

Wata Matsananciyar faɗuwar gaba Abba yaji cikin tashin hankali ya dubi Haidar Wanda kansa yake a ƙasa,
Har zaiyi Magana Sai kuma yafasa ya dafe kansa da yake matuƙar Sara Masa Kamar ana buga Masa guduma.
Nan take Kuma Sai yaƙara jin duk Duniya ba Wanda ya tsana Sama da Ahanaf.

Ga Kuma kukan Ayiya da yake taɓa Masa zuciya,
Yama Rasa Abunda yake Masa Daɗi a duniya.
cikin ƙaraji yace YA ISA YA ISA da wanne kuke so Naji ne? Ko su kuke Sai kun haukatani?

Dan Allah Ku Tashi kubani guri Abba yafaɗa Yana nuna Haidar da Kamal a ƙufule,
Tashi sukayi suka fita fuuuuuuu Kamar zasu Tashi Sama,
Ita ma Ayiya Tashi tayi da nufin bin bayansu cikin sauri Abba ya riƙe Mata hannu yace "Ina Kuma zakije Haj?


Kasakar min hannu Alh,
Ka damu dani ne bare Har ka damu da gurin da zanje? Zan tafi Nemo yarona ne Kuma kasani muddin nasaka ƙafa Na bar gidan Nan naje Nemo Ahanaf Toh Koda Na ganshi bazan dawo gidanka ba Har Abada.
Cikin sauri Abba ya rufe Mata baki yace haba Dan Allah me kike faɗa ne haka? Kamar bakya cikin hankalinki, Yaron Nan ki rabu dashi duk Inda yaje Shi da kansa zai dawo gida, kituna ba fa kurar sa mukayi ba, shida kansa yabar gidan Nan, Dan haka Shi da kansa zai dawo.
Girgiza Kai Ayiya tayi tace Wai bakaji Abunda su Haidar suka faɗa bane?
Haj Kira bu da zance "wa ƴan can Shashashun yaran duk halinsu ɗaya dashi Ahanaf ɗin.
Abun da suke faɗa ba gaskiya bane.

Kwace hannuwan ta tayi tare da cewa Idan Kai baka yarda Da Abunda sukace ba to Ni na yarda, Dan haka zanje neman Ahanaf yanzu ba Sai anjima ba, Ayiya ta faɗa ranta a ɓace tare da nufar hanyar fita daga palon.


Ba da yawuna ba muddin Kika fita daga gidan tohm tabbas kisani Akan tsinuwar mala'iku Zaki fita, indai Ni Muhammad Imran nine mijinki Toh ban lamunce Miki kije neman wannan Yaron ba, Yana gama faɗar Hakan ya nufi hanyar bedroom ɗinsa ba tare da yajira yaji Abunda zata ce ba.



Haidar Bai fa kamata muyi haka ba gaskiya, Idan har mukayi haka mu ba abokanan kirki bane, abokin kirki shine Mai tsayawa abokin sa a cikin wuya Ko Daɗi, Kaine kafaɗi haka. Yanzu Kuma Zaka ƙaryata kanka. Kamal yafaɗa Yana kallon Haidar Wanda Sai faman saka kayansa yake a cikin jaka Rai a ɓace.
Kaga Kuma Abbu zaizo anjima Idan yazo betarar damu bafa? "A yadda Abba yatsane mu ma zai iya cewa da sanin mu Shadow yafita daga gidan nan" Kaga bamuda ruwan wanke Kan mu, Haidar idan hankali ya gushe hankali ake sakawa gurin Nemo sa, ya kamata kayi tunani kafin ka yanke hukunci. Cewar Kamal Yana marairaice fuska.

Wani irin iska Mai zafi Haidar ya furzar tare da cewa wllhy Abba yaci Albarkacin furfurar da Ke ɗauke a fuskarsa da Kuma mutunci haihuwar Shadow da yayi da Sai Na Masa Rashin mutunci da Ko Sunana yaji an Kira Sai gabansa yafaɗi, Amma kashh ba damar haka.

Zan tsaya Har Abbu yazo muyi Magana dashi baki da baki in yaso daga Nan Sai Sai mu tafi abun mu, Shadow Dai shine abokin mu Kuma Zamu cigaba da neman sa tare da yi Masa addu'ar neman tsarin Allah a duk Inda yake.

Murmushi Kamal yayi yace Hakan ma yayi Boss dan wallhi Nima Bana son Zama a gidan Nan, gabaki ɗaya lamarin gidan tsoro yake Bani,
gidan da Ada Idan kazo ko kai waye Sai rayuwar iyalin ta Burge ka,
Saboda soyayya da shakuwa da take a tsakaninsu.
Amma yanzu gidan ya Koma Kamar gidan wasu enemies. Allah ya tona asirin duk Wanda yake da hannu a cikin wannan lamarin.

Ameen ya Allah cewar Haidar Yana jingi jikinsa da Bango.


Misalin ƙarfe 20:15 Na Rana Abbu ne zaune a katafaren palon Abba fuskarsa a turnuƙe Kamar Wanda aka aikowa da Mala'ikan mutuwa,
Cikin ɗaure fuska Abbu yace Muhammad Ina So kafaɗa min Menene dalinlin da yasa ka ɗaura auren waccan yarinyar da Ƙaseem maimakon Ahanaf?

Cikin rawar murya Abba yace Amma Yaya Ai da Kabari ka huta kaci abinci tukkunna.
Ɗaga Masa hannu Abbu yayi tare da cewa Ai Na huta 1 da Yan mitina muka sauka ƙasar Nan Toh Ina ga ba Wani hutu da nake buƙa yanzu.

Kabani amsata shine Kawai Abunda nake buƙata,
Menene dalilin aikata duk wannan Abun Muhammad? Abbu yafaɗa Yana ƙure Abba da idanunsa da suka Fara sauya Kala zuwa ja tsabar ɓacin Rai............✍️✍️✍️


Yanzu ma a kafara😥😥

Duk fa abun Nan da Abbu yakeyi be San cewa Ahanaf baya gida ba.

Me zai faru Idan Abbu yasan yasan Ahanaf baya gida?




Nabeela Binji ce💃💃💃





Nabeelah Shehu Binji

09064314811
Or
09161107610




More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏.







♣️DUHUN INUWA ♣️




TAPING......📲📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*


BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM

Allahumma salli 'ala Muhammad, wa-'ala ali Muhammad, kama sallayta 'ala Ibraheema wa-'ala ali Ibraheem, innaka Hameedun Majeed, allahumma barik 'ala Muhammad, wa-'ala ali Muhammad, kama barakta 'ala Ibraheema wa-'ala ali Ibraheem, innaka Hameedun Majeed.

Allahumma a'innee 'ala zikrik, washukrik, wahusni ibadatik.
Allahumma innee as-alukal-jannah, wa-a'u'zu bika minan-nar.🤲




PAGE

0️⃣8️⃣



____________kayi haƙuri Yaya wallahi nima bansan dalilin da yasa n...... tasss Abba yaji saukar mari akan kumatunsa, hannunsa yasa ya dafe gurin da Abbu ya mare sa,
ɗago yayi yana kallon Abbu cike da mamaki.
"Kana da hankali Muhammad kasan abunda ka keyi kuwa? ka aikata wannan gagarumin laifin sannan harka iya buɗe baki ka faɗamin cewa bawani dalili? kar kazama Maha'inci Muhammad katuna fa Ahanaf amana ne agurinka Alƙawari kayi zaka kula da shi, zaka bashi farin ciki zaka mantar dashi ƙuncin rayuwa zaka zamar masa Garkuwa.
Ina duk wannan Al'washin naka yake? Ashe dama bada gaske kake ba? Ashe dama raɗaɗin mutuwane yasa kafurta duk waɗan nan abubuwan? Mai yasa kake so kazamar ma Ahanaf DUHUN INUWA Muhammad?


Wani matsanan cin kuka Abba ya fashe dashi wanda shida kansa bai san dalilin yin saba,
Saidai yasan duk abunda yayansa yafaɗa gaskiya ne Ahanaf amana ne agurin sa kuma abun so da ƙauna agurinsa, amma yarasa taya akayi hakan tafaru.

Agaban Abbu Abba ya zube akan gwiwoyinsa, yace "ka yanke duk hukincin da kaga yayi maka a kaina yaya" ni mai laifine agurin ka.
Amma fa kasani har yanzu ina kan bakata bazan warware auren Norr da Al ƙaseem ba.
"Ahanaf ya kasa yimin biyayya kamar yadda ɗan uwansa yayi,
Ya nuna min cewa shi yaro ne mai taurin kai ba wanda ya isa dashi" yaya bari kaji daga yau na fitar da hannu acikin duk wani lamari na rayuwar Ahanaf yaje yayi duk abunda yaga dama bani bashi" Abba ya faɗa cikin ɗacin rai.


Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un, Muhammad yau Kaine kake wannan furucin Akan Ahanaf? Kuma har kake haɗa masa da ƙarya da ƙage? Tabbas da wata a ƙasa wannan abun bayin kanka bane.
Ni bawani hukunci da zan yanke ma wanda ke fama da Matsalar taɓin kwakwalwa,
Amma kasani daga yau Ahanaf zai bar hannunka ya dawo ƙarƙashin kulawata.
Sanna zan tayaka da addu'a kuma zan sanya manyan malamai su taimaka mana da addu'a, saboda bazan zuba ido ina kallon ka cikin wannan halin ba.

Muhammad kai Amana ce agurina zanyi kumai dan ganin na kiyaye wannan amanar da iyayenmu suka bani.
Bana so koda da kan a kaifane Allah yakama ni da Hakkinka agobe ƙiyama, zan tsaya tsayin daka akanka da kuma iyalanka dukanku hakkine da ya rataya a wuyana.

Har yau bazan manta mutuwar mahaifiyar muba bazan manta yadda ta dankamin amanar ka a hannuna ba Muhammad,
duk duniya banida wani ɗan uwa sama dakai, kaima bakada wani ɗan uwa sama dani mu biyun nan mune kawai dangin juna bamuda kowa face Allah. Muhammad katuna yadda mukayi fafutuka da rayuwa kafin muzo wannan matsayin.
Munyi fama da rayuwa
Munyi fama da maraici
Maunyi fama da rashin gata, uwa uba Munyi fama da ƙuncin talauci da rashin majingina.
Amma duk da haka baisa munguji juna ba kuma baisa muka yada zumunci ba baisa nakasa riƙe amanar kaba Muhammad.
Kuma kasani har yanzu bazan karya alƙwari ba. ni bakamar kai bane Muhammad kuma kasani bana fatan zama kamar kai har abada.
Abbu yana gama faɗar haka ya miƙe tsaye da nufin barin palon saboda ransa yakai ƙololuwar ɓaci akan wannan lamarin na ƙanensa.

Cikin sauri Abba ya bi bayansa tare da rungume shi ta baya yana kuka, yace "dan Allah ka gafarceni yaya wallahi ni kaina bansan dalilin akaita wannan abun ba.
Yaya taɓa kirjina kaji bugawa yake da sauri. Hannun Abbu yakama yaɗaura a saitin zuciyar sa.
Da sauri Abbu yajanye hannusa tare da furta Muhammad kashe kanka zakayi kaji yadda zuciyar ka ke bugawa da sauri? Mai yasa kake son kashe kanka ne? wannan abun duk fa kaine ka aikata shi.
Ni fa gaskia kawai na faɗa maka.

Wallahi Narasa dalilin da yasa nayi haka yaya, "dan Allah karka gujeni wallhi idan katafi kabarni mutuwa zanyi kaine Babana kaine mamana kuma kaine yaya na banida kowa sama da kai dan Allah kar katafi" Abba yafaɗa yana ƙara rungume Abbu ajikinsa tare da ƙara sautin kukansa kamar wani ƙaramin yaro.


Tohm naji bazan tafi ba Muhammad ka kwantar da hankalinka, nima faɗa kawai nake ba gurin da zan iya tafiya nabarka a cikin wannan halin. cewar Abbu yana goge kwallar da tazubo masa.
Shiru Abba yayi sai ajiyar zuciya da yake saukewa kamar wanda yayi gasar gudu.

Bari naje na duba Ahanaf ɗin naga awane hali yake ciki, kafin nasan wane mataki yakamata naɗauka akan wannan case ɗin.
Abba yace"Ahanaf baya nan fa Yaya ya tafiyarsa, dama na faɗa maka yanzu wannan yaron bayajin magana kwata kwata ba wanda ya isa da shi" Abba yafaɗa yana yamutsa fuska alamar ko ajikinsa baiji tafiyar ta Ahanaf ɗin ba.
Abbu yace Subhanallah "Ahanaf yatafi kuma? ina yatafi? meyasa kuka barshi yatafi?"
Nima bansan tafiyar tasa ba "ɗazu ne abokanan Shashancinsa suke faɗa muna wai baya nan Suma bayan sun dawo daga Masallaci ne suka nemesa suka rasa" Ni bam ma gama yarda da zancen Nasu ba saboda nasan duk bakinsu ɗaya dashi maybe ma da sanin su yatafi.
Amma sunzo suna faɗawa Mutane maganar ban....
Tsawa Abbu ya daka masa cikin hargowa yace kasan mai kake faɗa kuwa Muhammad "Ahanaf ɗin ne baya nan kuma kake nan hankalinka kwance?"
Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un Abbu ya faɗa yana fita daga ɗakin cikin sauri kamar zai tashi sama, direct part ɗin Su Shadow ya nufa ransa a masifar ɓace, ƙofar palon ya tura da ƙarfi ya Shiga ba ko sallama yana kwaɗa kiran Haidar.

Haidar da yake tsaye a tsakiyar palo yana waya da wani abokinsa D.P.O Abdul-Naseer akan wannan case ɗin na Shadow.
Da sauri Haidar yajuya dan ganin waye yashigo haka ba ko sallama, kuma yana ta ihun kiran sunansa.
Ido huɗu sukayi da Abbu wanda yake cikin matsanan cin tashin hankali.
kallo ɗaya Haidar yayi masa ya gane Shine Abbu,
Saboda yana ganin pics ɗinsa a cikin wayar Shadow kuma ko bayan haka suna matsananciyar kama da Abba.
Ina zuwa D.P.O Haidar ya faɗa tare da katse wayar da ya keyi.
Ina wuni Abbu barka da zuwa ya hanya?
Duk a cikin gaisuwar nan da Haidar yakewa Abbu ba wacce ya Amsa,
Saima tambayar da ya jefa masa, yace Haidar ina Ahanaf?

Abbu dan Allah ka zauna mana sai muyi maganar.
Ba musu Abbu ya zauna dan ya ƙagara yaji gaskiyar wannan batun.
Shima Haidar zama yayi a ƙasa kusa da ƙafafun Abbu, ya sunkuyar da kansa ƙasa cikin nutsuwa ya fara bawa Abbu labarin duk Abunda yafaru jiya bayan sun gama yawa dashi.
Da neman da sukayiwa Shadow basu ganshi ba har izuwa lokacin da sukaje faɗawa Abba Abunda yake faruwa da kuma irin koyar da Abban yayi musu.

Iska mai zafi Abbu ya furzar ya ɗauki kusan 3min baiyi magana ba, a hankali ya maida kallon akan Haidar yace wane mataki yanzu kuke ganin yakamata a ɗauka? ko kuma akwai wanda kuke zargi?

Gaskiya ba wanda muke zargi Abbu.
Amma kuma akwai wani Abu da yayi matuƙar ɗaure muna kai, bayan mun duba ko ina bamuga Ahanaf sai muka ga wata ƙofa ta baya
bayan mun bi hanyar sai muka ɓulla ta gurin garden, muna dudduba gurin sai mukaga key ajikin ƙofar ɗakin ta baya tohm a nan ne muka tabbar lallai wani ne ya buɗe ƙofar ta baya Ahanaf yafita.
Yanzu ma haka key ɗin yana nan na aje muna su ayi bincike akansa dan gano zanen hannun waye akan key ɗin, Yanzu ma da kaga ina waya magana nake da wani abokinmu, shi ɗan sanda ne babba da ya ƙware agurin harka bincike.
Yanzu ma haka yana hanya zaizo nan gidan saboda a ɗauki zanen hannu duk wanda yake gidan nan har masu aiki domin gano waye mai wannan laifi, kuma menene dalilin da yasa ya buɗe Ahanaf. Haidar ya faɗa cikin nutsuwa.


Tabbas wannan tunanin naka abune mai kyau Haidar,
Ba Shakka ku friends ne Nagari kuntsaya tsayin daka dumin abokin Ku.
Ba kutafi kun barsa ba duk da Abunda mahaifinsa ya Muku.
Banida Abunda Zan Saka Muku dashi Allah yayi Muku Albarka Kuma ya kare Ku Aduk Inda kuka Shiga.
Ameen Abbu Mun gode.
Wayar Haidar ce tafara ringing Yana dubawa yaga D.P.O ne Ke Kiransa, maybe ma ya karaso Haidar yaɗada Yana Kara wayar a kunnensa.
Okey jirani agurin ina zuwa Haidar ya faɗa yana tashi tsaye, ya kalli Abbu yace Abbu muje D.P.O ya ƙaraso yana waje.
Tashi Abbu yayi yabi bayan Haidar suka fita tare.


ƙara gaisawa Sukayi da D.P.O
Sannan D.P.O yace yakamata muyi Abunda ya kamata saboda inada meeting anjima kaɗan Insha Allah.

Abbu ya kalli Haidar yace ina wannan Abokin naka da kake magana?
yana gurin wanka Amma zai fito yanzu insha Allah.



Duk wani Mahaluki da yake
Rayuwa agidan ya Hallara a babban palon Alh Muhammad Imran.

Cike da mamaki Abba yake bin kowa na falon da kallo, kafin daga ƙarshe ya maida kallonsa akan Abbu
yace mai yake faruwa haka ne? menene dalilin duk wannan taron yaya? zaka kasani yanzu Abbu yafaɗa yana maida kallonsa akan D.P.O Abdul Naseer.
Yace zaka iya fara aikinka D.P.O.



Bayan an gamawa kowa a kazo kan Abba amma fafir yace shi baisan zancen, ba bazai bayar da hannunsa ba.



Wallahi wannan ne kuma baka isa ba Muhammad........ ✍️✍️✍️



Taya akayi Shadow ya zama Amanar Abba?


Raɗaɗin mutuwar waye yasa Abba ya ɗauki Alƙawarin rike amanar Shadow?


Tohm waye ya Bawa Abba Amanar Shadow?
Bayan Alh Muhammad Imran ( Abba) Shine mahaifin Ahanaf (Shadow).

Tabbas akwai wata ƙullalliya a ƙasa😥






Nabeela Binji ce💃💃💃





Nabeelah Shehu Binji

09064314811
Or
09161107610




More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏.






♣️DUHUN INUWA ♣️




TAPING......📲📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*


BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM


PAGE

0️⃣9️⃣



Wallahi wannan ne kuma baka isa ba Muhammad............





________________Yazama dole ayi bincike a kanka Kamar yadda a kayiwa Kowa, "Idan har Kuma kace baza ka Bari ayi ba tohm ba shakka Kaine ka buɗe wannan ƙofar kuma ka kori Ahanaf daga gidan nan.
Idan har hasashena gaskiya ne wllhy Muhammad sai ka fuskanci mummunan hukunci daga gareni.
Kuma kasani idan har hakan yazama gaskiya Wllhy bani ba kai har abada.

Muhammad kasan wanene Aliyu idan na faɗi magana koda mutuwa ce zata gifta a gabana bazan canza ra'ayina ba. cewar Abbu cikin matsancin ɓacin Rai.

Duk wanda yake a Palon yashiga tashin hankali da jin furucin Abbu.
Shida kasansa Abba ya ruɗe sosai yajima baiga yayan nasa acikin irin wannan fushin ba.
yaya dan Allah k.. ɗaga masa hannu Abbu yayi tare da cewa bana son jin komai daga bakin ka Muhammad, Wallahi dole ne kayi ɗaya daga cikin biyun Nan, kodai kabari ayi bincike akanka Kamar Kowa Ko Kuma ka gayamin gaskiyar Abunda yafaru da Ahanaf a Daren jiya.

Maganar gaskiya bansan Abunda ya faru da Ahanaf ba a Daren jiya, Kuma wllhy Yaya bani na Buɗe ƙofa yafita ba.
Hasalima Ni ban yadda cewa yasamu taɓuwar hankali ba, Kawai ya tafiyar sane Saboda Abunda yafaru, su kuma su kazo da nufin tayar Mana da hankali, Amma Idan har wannan binciken zaisa kadaina zargina Kuma kajanye wancan zance Na cewa Zaka tafi kabarni Na Har abada tohm Na yadda ayi Koma Menene Yaya,
Abba yafaɗa cikin ɗacin Rai tare da ƙarajin tsanar Ɗan nasa Ahanaf, saboda gabaki daya Abba yadauki laifin komai yadaurashi Akan Ahanaf Wanda Idan aka saka shigaba akace ya faɗi dalilin Tsanar da yake yiwa Ahanaf Tabbas ba Wani dalili Dan Shi da kansa Bai San dalilin ba.
Kallon d.p.o Abbu yayi yace Zaka iya Fara akinka Kamar yadda kayi Akan Kowa domin goge zargi.

Bayan d.p.o yagama duk Wani binciken da zaiyine ya Koma Kan ɗaya daga cikin kujerun palon ya zauna tare da zare glass din idonsa ya kalli Abbu yace tabbas akwai sarƙaƙiya acikin wannan case ɗin Ranka yadaɗe.
Mai aikata wannan laifin yanada matuƙar wayau da basira,
saboda ba ta inda yabar wata shaidar da za'a iya kamasa,
Tabbas Bai kwaɓar ba
A Ko Ina ya kiyaye Akan abun harinsa da Kuma goge duk wata hujjar da zata nunasa, Yana aiki da kwakwalwar sa yayin da mu yake Mana Wasa da tamu kwakwalwar
D.p.o yafaɗa Yana gyaɗa Kai cikin mamaki sai kuma yasaki murmushin da shine Kaɗai yasan dalilin yinsa.

Kallonsa ya Maida Kan Abbu yace tabbas Koma waye yake aikata wannan laifin ya iya takonsa sosai ranka yadade,
Amma hausawa sukance Karen Bana shine maganin zomon Bana,
Mai laifi har yake da kwarin gwiwa ayayin da yake cikin ganiyar aikata laifinsa tohm Taya Mai bincike zai Sare agurin gano mai laifin?
Yanzu za'a Fara wannan wasar, tabbas Sai an ban bance tsakanin Ƙarya da gaskiya.
ka kwantar da hankaliki Alh Zanyi iya bakin ƙoƙarina dan ganin Na Nemo Maka Ahanaf tare da binciko Maka Mai laifin a duk inda yake a faɗin duniya insha Allah, d.p.o Abdul naseer yafaɗa cike da tabbatarwa.

Gyara Zama Abbu yayi tare da cewa nagode sosai yaro Allah yayi Muku Albarka, sanna duk Wani Abu da kake bukata Na dangane da bincikenka Zaka iya tuntuɓar su Haidar saboda nasan bazasu ɓoye Maka komai ba insha Allah.

Sannan a duk lokacin da kake son kayi bincike Ko Kuma kayiwa Wani wata tambayar Ni Nan nabaka damar shigowa gidan Nan Kai tsaye Domin gabatar da aikinka yadda yadace.

Wani kayataccen murmushi d.p.o Abdul naseer yayi tare da cewa nagode sosai ranka yadaɗe,
Yanzu Kuma Ina son Na keɓe da maigadin gidan Nan saboda akwai tambayoyin da nake so nayi Masa,
Tabbas binciken da mukayi yanzu duk Wanda yake cikin gidan Nan yayi Nasarar kuɓuta a Karo Na farko ba musan mai bincike nagaba zai haifar ba.
Saboda Kai tsaye baza muce Mai laifin daga waje yake ba, Kuma baza muce daga cikin gidan Nan yake ba.
Bincike da ƙarfin addu'a ne Kawai zasu haskaka Muna wannan DUHUN INUWAR da ya baibaye kwakwalwar mu.
Dukanku Sai kun bayar da haɗin Kai ta yadda Kumi zai tafi cikin sauƙi.
Cewar d.p.o Yana bin kowa da yake palon da Kallo. Insha Allah cewar Mutanen da suke palon Banda Abba da duk Abunda suke haushinsu yakeji matuƙa.
Sallama yayi Musa tare da cewa mlm Muntari Mai Gadi yabiyo bayansa suje.


Malam Muntari tambayar ka nake so nayi Kuma Bana son ka Ɓoyemin kamai gaskiya Kawai nake son ji daga bakinka, saboda Faɗin gaskiyar ne zaisa mu rabu cikin salama,
Amma kasani muddin ka faɗamin ƙarya zanyi bincike Kuma Idan Nagano ƙarya ka faɗamin tohm kasani Zaka fuskanci mummunan hukuncin wallhi cewar d.p.o fuskarsa ba alamar Wasa.

Ba Abunda Zan ɓoye Maka ranka yadaɗe wllahi duk Abunda ka tambayeni Zan baka amsa ta gaskiya insha Allah,
Idan kayi haka kataimaki kanka mlm Muntari.
Tambaya ta a gareka ba Mai wahala bace.
Waye yazo gidan Nan jiya da dare yafita da Ahanaf?
D.p.o yafaɗa Yana ƙuresa da Ido.

Gaskiya ba Wanda yazo gidan Nan yafita da Ahanaf ranka yadaɗe,
hasalima jiya da dare Audu driver ne

Please Login or Register in order to submit comment