Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi shigowar ƙarshe agidan Nan bayan Shi ba Wanda yaƙara Shiga Ko Kuma fita daga gidan Nan Har lokacin rufe gidan yayi.
Mlm Muntari yafaɗa cikin tsoro da kuma ƙoƙarin ganin ya kuɓutar da kansa daga zargi.

Numfashi d.p.o ya furzar sannan yasa ke ce masa Kuma Kana Zaune a bakin gate ba kaje Ko Ina ba Har lokacin rufe gidan yayi?

Wallahi ba Inda naje ranka yadaɗe Ina zaune a gurin Har lokaci yayi.

Bayan Kai akwai Wanda yake da makullin gate ɗin?

Gaskiya bazance akwai Wanda yake da makullan gate ɗin ba, saboda Nidai sanan iya Ni kaɗai nake amfani dasu Kuma Ina tunanin sune kaɗai makullan gate ɗin.
Dan bazan manta lokacin da Alh ya Bani kuɗi nasiye Wasu makullan ba Saboda wa ƴancan sun lalace.
Kuma gaskiya Ni nasan ban Bama Kowa makullan ba.
Sannan Koda ma ace akwai Wanda yake da makullan agidan Nan ba yadda za'ayi a Buɗe wannan gate ɗin banji ba, saboda gate ɗin Yana ƙara Idan anzo ɓuɗesa Ko Kuma rufesa.

Nagode sosai mlm Muntari ina fatan zaka bahi haɗin kai idan na sake dawowa?


Eh insha Allah zan faɗa maka gaskiyar duk abunda ka tambayeni.

Wani malalacin Murmushi D.P.O yayi tare da buɗe motar sa yashiga yabar gidan da mugun gudu...............✍️✍️✍️



Kaina bisa wuya Ina Matuƙar baku haƙuri ƴan uwana. Wallahi na ɗan shiga wasu sabgogine kwana biyu, kuma bayan haka naje wani gari da ake fama da matsalar network ɗin MTN dalilin da yasa kuka jini shuru kenan Ina fatan Zakumin Afuwa🙏😥




Nabeela Binji ce💃💃💃







More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏







♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*


BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM


PAGE

1️⃣0️⃣


Wani malalacin Murmushi D.P.O yayi tare da buɗe motar sa yashiga yabar gidan da mugun gudu.





____________Zaune suke a part ɗin su Shadow Suna fira Haidar ne ya kalli Abbu yace "Abbu wai dan Allah dagaske su Abba ne suka haifi Ahanaf?

Iska Mai zafi Abbu ya furzar, tare da gyara Zaman sa ya fuskanci Haidar da Kamal,
Cikin ɗacin rai da ƙunar zuciya Abbu yace
"Tabbas Ahanaf Yaron sune, Muhammad shine mahaifin Ahanaf Kuma shine Ɗan sa na farin, Sai Daga baya Allah ya bashi Al kaseem, Muhammad Yana matuƙar son Ahanaf fiye da Kowa a rayuwar sa, ba yason ganin ɓacin ransa Yana riritashi fiye da tunanin Ku"

Haka ita ma Haj Shuwa "Bata ƙaunar Abunda zai taɓa yaranta Ko kaɗan" Shekarun baya da suka wuce Idan nazo gidan nan Ko Kuma su sunje gidanmu
Nakan tasa su gaba nayi musu faɗa Akan su rage nunawa yaran Nan So a gaban idon su,
Saboda Hakan zai iya sadin lalacewar tarbiyar su.
A iya sanina su iyaye ne masu nuna damuwa Akan yaran su, Basu ƙaunar Abunda zai taɓa ɗaya daga cikin su.


Amma babban Abunda ya bani mamaki Kuma yake Kan Bani mamakin Har yanzu shine "ganin yadda Muhammad ya jefa rayuwar Ahanaf a cikin haɗari, Kuma ya nuna halin Ko'in Kula Akan sa"
Tabbas wannan lamarin akwai wata kullalliya a ƙasa, ba Abunda zaiyi maganin wannan matsalar Sama da Addu'a,
Dole Sai Mun Tashi tsaye Akan wannan lamarin, Idan har Muna so mukai ga Nasara da tonuwar Asirin Wanda yake son ganin bayan mu. Cewar Abbu Yana bin su Kamal da kallo.

Zamuyi komai dan ganin Mun ceto rayuwar abokin mu Shadow insha Allah.
Alhmdllh Allah yayi Muku Albarka Abbu ya faɗa Yana murmushi.
Ameen ya Allah.
Nan sukaci gaba da tattaunawa Kan matsalar da Kuma ta yadda zasu Ɓullowa lamarin.




Gidan Amare

_________ Norr ce tsaye a kitchen tana girkin dare, Al ƙaseem tsaye a gefenta ta Yana zuba Mata Salo da kwarewa
Ita Kuwa sai faman dariya take Masa, ya mutsa fuska ya tare da langwaɓar da kansa Kamar Wani ƙaramin yaro cikin shagwaba yace baki yarda da Abunda Na faɗa ba Ko my Norr?
Cikin dariya tace wacece Ni da zan ki yarda da maganar yallaɓai, ta faɗa cikin sigar zolaya.
Kwafa yayi yace wata Rana Sai munyi gasar girki Sai anga Wanda yafi iya girki Nida Ke a cikin gidan Nan.

Murmushi Norr tayi Sannan tace a'a Ai basai anyi ba Kawai na yarda mijina gwani ne agurin girki, shikenan Nan maganar ta wuce Ko? Tafaɗa tana kallon sa Tana dariya ƙasa ƙasa.

Bata wuce ba Kam Sai anyi girkin Nan insha Allah munyi maganin Raini, Al ƙaseem ya faɗa cikin kwarin gwiwa irin Shi ga kwarrare agurin girki.

Toh Allah ya kaimu ranar wannan gasar cewar Norr tana Maida hankalinta Akan Abunda takeyi, Cox dare yafari Kuma har yanzu Bata Gama aikinta ba, ta tsaya gardama da Al ƙaseem.


Gabaki ɗaya Kona su zanyi wallahi, Ai wannan rainin hankali ne Taya zai cika mana gida da pic's din sa, Al kaseem ya faɗa Yana faman huci Kamar Wanda yaci gudu.
Pic's ɗin Shadow ne zube a ƙasa gurin da yake Shi kaɗai, da gurin da yake tare da Norr.
Masu glass Har sun farfashe saboda jifar da Al ƙaseem yake da su, babban baƙin cikin sa shine ganin Zanen da Shadow yayi Shida Norr kamar pic's akayi musu ba Zane bane yayi masifar kyau.
Saboda Shadow ya kware sosai agurin Zane, Idan ya Zana mutum Zaka iya rantsuwa cewa pic's ne ba Zane ba.

Norr ce ta riƙe sa tace Dan Allah kayi a hankali Mana Kar kajiwa kanka ciwo, basai ka Kona "Masa abuba ka hadasu guri ɗaya ka Tura Masa kayansa"

Kina da hankali kuwa Norr? Pic's ɗin naki ne Zan turama Wani gardi ya dinga Kalla? Toh wallahi bazan tura su ba, gabaki ɗaya Kona su zanyi ni ba Shashasha bane,
Al ƙaseem ya faɗa cikin masifa da ɓacin Rai.
Baya Norr taja Dan ta lura ran mijin nata yayi masifar ɓaci,
Sannan ga matsancin Kishi da yake faman Ɗawainiya dashi. Hakan yasa taja bakin ta tayi shuru Bata ƙara ce Masa ƙala ba.

Bayan yagama haɗa pic's ɗin gabaki ɗaya ne ya kwashe su ya Kai su hara bar gida ya Cinna musu wuta,
Saida yaga sun Gama cinyewa Tass Sannan ya Koma cikin gidan Yana Jin Wani irin zafi a zuciyar sa.




____________ kwance yake a gefen hanya ba alamar numfashi a tare da Shi, Saboda yasha Duka Na fitar hankali.
Sanyi asuba ne da ya fara bugawa yasa ya Fara motsa hannunsa a hankali,
Ya ɗauki tsawon lokaci a Haka kafin Daga baya ya fara motsa jikinsa alamar Yana so ya Tashi zaune Amma ya kasa.

Sai da kyar ya samu damar Tashi zaune tare da sa hannuwan sa ya riƙe kansa da yake masifar yimasa ciwo Kamar zai Rabe gida biyu.
Sai Wanda yayi Masa farin sani ne zai iya gane SHADOW a cikin wannan halin,
Saboda yafita daga hayyacinsa sakamakon dukan da yasha Na fitar Ariƙi.

Yayi yunƙurin Tashi yafi sau ukku Amma yakasa Saboda Ko Ina na jikinsa ciwo yake Masa ga Jiri da yake Gani Har idanunsa Na ƙoƙarin sake rufewa da kansu.

Sake rufewa idanun sukayi yayi baya luuuuuh yaƙara zubewa ƙasa sumamme.......✍️✍️✍️😥



Tirƙashi wannan lamarin Anya ba tuggu a ciki Kuwa?

Suwaye suka jefar da Shadow agefen hanya?

Waƴanda suka jefar dashi yin kansu ne ko kuma saka su akayi?

Idan saka su akayi tohm waye yasaka su?

Idan kuma yin kansu ne menene dalilin su?

Laifin me Shadow yayi musu?

Da Shi suke faɗa Koda iyayenshi?

Wace kalar yaruwa Shadow zaiyi a wannan garin da bai masan ko ina bane?

Waye zai taimaki Mahaukaci a wannan zamanin da ko mai hankali yakasa samun taimakon Al ummah?







Share Fisabilillah 🙏





♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*


BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM


PAGE

1️⃣1️⃣





Sake rufewa idanun sa su kayi yayi luuuuuh yaƙara zubewa ƙasa sumamme..




__________Wasu dattijai ne su biyu suka zo wucewa, tun Daga nesa ɗaya yace "Kamar mutun nake Gani kwance agurin can" Sai ɗayan yace toh muƙarasa mugani,
Cikin sauri su ka ƙarasa gurin da Shadow yake kwance ba alamar numfashi a tare dashi,
Ba shakka mutum ne dattijon guda ya faɗa cike da mamaki.
Ɗayan ne ya durƙusa ya Kama babban farce Shadow Na ƙafa yayi Jim Yana saurare Sai can ya ɗago ya kalli abokin tafiyar sa yace Masa Yana da Rai Saidai ya Suma ne.
Gorar ruwan ya ɗauko Yaba ma dattijon da yake riƙe da Shadow yace zuba Masa Muga Ko Zai Tashi.

Ana zubawa Shadow ruwan cikin sauri ya buɗe idonsa Saboda ruwan ya Shiga Har cikin raunin fuskarsa Wani Irin raɗadi yaji Yana ratsashi.
Da sauri ya Tashi zaune Yana binsu da kallo,
Sannu yaro dattijon guda ya faɗa Yana ƙoƙarin Kai hannunsa a jikin Shadow, da sauri Shadow yaja baya alamar Baya Son su taɓa Shi.
Ɗan samari Daga Ina?
Mai ya sameka haka?
Ko azzaluman Mutanen Nan ne suka Kama ka?
Da Ido Kawai Shadow yake binsu Amma ya kasa Buɗe baki yayi Magana, Sai ma ƙoƙarin Tashi yake tsaye, "kayi a hankali yaro Kar ƙarawa kanka Wani raunin"
Ko kulla su Shadow bayi ba, ya Tashi tsaye ya saka hannunsa ya dafe kansa da yake Masa ciwo Kamar zai Rabe gida biyu tangaɗi yake kamar Wani ɗan Maye.
Duƙawa yayi da ƙyar ya ɗauki jakar kayan Zanen sa wace yagani yashe a gefe.
A hankali yafara Tafiya ba tare da ya juya ya kalli waɗan Nan tsofaffin ba.
Cike da mamaki suke binsa da kallo.
Anya Yana da hankali kuwa? Cewar dattijon da ya zubawa Shadow ruwa.
Gaskiya Kam ba alamar hankali anan Saboda Idan yana da hankali Ko da Baice Mana komai ba Ai yakamata yayi Muna godiyar ceton ransa da mukayi.
(Allah sarki rayuwa su Basu ma San Bada Mai Hankali suke tare ba)

Tafiya yake bai masan gurin da yake jefa ƙafar sa ba, Abu ɗaya yasani yanzu shine ciwon da yake ji ajikinsa Wanda baibsan yadda zaiyi dashi ba.
Tafiya Mai matuƙar Nisa Shadow yayi kafin yasamu ƙarasawa cikin gari,
(Da ace Shadow cikin hankalinsa yake da koda da kuɗi aka haɗashi bazai iya wannan uwar tafiyar ba.)

Ji yayi ya kasa Tafiya ya Samu gefen Wani gidan Mai ya zauna tare da sunkuyar da Kan sa ƙasa. Kamar Mai tunanin Wani Abu bayan mintina kaɗan ya Tashi yaci gaba da tafiyar sa Tafiya Kawai yake bai masan Inda ya dosa ba, Saidai Idan yaga Wani Abu Ko yaga Taron mutane yakan tsaya ya Kalla Idan yagaji da tsayi yayi tafiyar sa.

Kusan kwanaki ukku Kenan Shadow Yana yawo a wannan Garin dashi baima san Ina ne ba.
Gabaki ɗaya Alamar hauka tagama bayyana a tattare dashi Saboda kayan jikinsa sunyi masifar Datti. Ga ciwon da yaji Har ya fara caɓewa Saboda Rashin Samun Kulawa. Ba abinci ba drugs babu kyakyawan makwanci.

Ahanaf yaga rayuwa agarin da baisan Kowa ba bashida Wani Wanda zai taimaki rayuwar sa Sai Allah.

Yanzu ma Tafiya yake cikin yanayi na Wanda yunwa tagama rarakewa, tun safe ba Abunda yaci, Har Kuma gashi Yamma tayi Yana yawo Yaran gari na Kiransa da mahaukaci.

A haka har ya ƙarasa Gurin wata Mai awara ya tsaya Yana kallonta. Matsananciyar yunwa yakeji Amma baisan yadda zaiyi ba.
Gefe ya Koma ya tsaya tare da buɗe jakar hannunsa ya ajeta ƙasa fitar da kayan Zanensa, ya fara Zana wannan matar Mai Awara.
Wani ne Wanda Shima awarar yazo Siya shine ya nuna Mata Zanen da Shadow yayi nata.
Cike da mamaki take kallon Zanen tabbas Koda Bata taɓa ganin Kanta a madubi ba tasan ba Shakka ita ce wannan Mahaukacin yazana a Bango.
Kai tsaye gurin da Shadow yake ta nufa sauran Mutanen da suka lura da Abunda yake faruwa suka mara Mata Baya.
Tsayawa su kayi Suna kallon Zanen tabbas wannan kwarraren Mai Zane ne.
Kayan Zanen sa ya kwa she ya mayar acikin jakar sa.
Duk maganar da suke Shadow Baice musu Kala ba.
Da matar ta lura Mahaukacin Nan Dai bazaiyi Magana ba Sai Takoma gurin da take soya awarar ta tazuba Masa ta 200 a Leda baƙa ta Kai Masa.
Ai Kuwa cikin sauri ya warci ledar a hannunta yafara cin awarar Kamar wanda Bai taɓa tozali da abinci ba a rayuwar sa.
(Ilimi Wani abune Na musamman a rayuwa, shine kaɗai Abunda zai Zama mallakinka a Ko wane hali kake ciki, Idan ka mutu ba Mai gadon ilimin ka, haka zalika Idan kasamu taɓuwar hankali ba Mai gadon ilimin ka, duk ƙiyayyar da Wani Bawa yakeyi gareka bazai iya kwace Maka ilimin da Allah ne yabaka Shi ba. Kamar Shadow yanzu iliminsa ne ya ciyar dashi a yanzu duk da Baya cikin hankalinsa. Allah yasa mudace)

Cikin tausayawa take binsa da kallo "wannan da Gani sabon Shiga haukane Saboda kallo ɗaya Zaka Masa kagane cewa a cikin Daula da Hutu ya Tashi
Dattin da yayine Kawai Zai nuna Maka cewa bashida cikakkiyar lafiya"

Tafiya yake Yana cin awarar sa Har ya Kai gurin Wani kangon gida Kai tsaye ciki ya shiga, da alama dai ya saba da gurin a kwana biyun Nan da yayi.


A ƙasa Ya zauna Yana cin awarar sa Yana ta faman zare Ido kamar wanda yake gudun Wani yazo ya kwace Masa awarar, bayan yagama cine ya Samu guri gefe ya kwanta ya lumshe idanunsa.
Ba jimawa bacci yayi awon gaba dashi.


A kwana a Tashi Bata bar kumai ba, yau har Shadow yacika wata huɗu a cikin ya nayin hauka, ba Wanda zai ga wannan Mahaukacin yayi tuanani Shadow ne ɗan wanka ɗan ƙwalisa ya Koma haka.


______________ A ɓangaren su Abbu Kuwa har yanzu sun kasa samo Mai laifin Saboda ba wata kwakkwarar hujja.
Wannan lamarin yayi matuƙar tada hankalin d.p.o Cox Shi a rayuwar sa Bai taɓa cin Karo da case ɗin da ya Caza Masa Kai kuma yake ci masa tuwo a kwarya ba Kamar wannan.
Hakan yaƙara harzuƙa d.p.o da Kuma cin Alwashin Sai ya kamo duk Wanda yake da hannu a cikin wannan case ɗin Kota halin Yaya da yarda Allah.


Abbu yayi Rama sosai kallo ɗaya zaka Masa kasan Yana cikin matsancinyar damuwa.

Yana son sanin halinda Ahanaf yake ciki, Yana son ƙara ganinsa Koda sau ɗaya ne a rayuwa. Tabbas Nemo Ahanaf hakkine da ya rataya a wuyansa, Amma ya kasa Hakan,
Duk iya binciken su da sanarwar su sun kasa Samun Wanda ma yace yaga Mai kama da Ahanaf ɗin.
Abbu Yana son ganin Ahanaf Koda a cikin halin haukane shidai muradinsa Kawai ya ganshi Kuma yaga ya sauke duk Wani hakkinsa Wanda Abba ya kasa saukewa.

Shima a ɓangaren Abba yayi Rama sosai Kuma Yana cikin damuwa wadda Shi kansa ya Rasa gane dalilin Hakan, Yana Jin k
Ƙunci sosai a zuciyar sa Amma baisan Ko Na menene ba,
Wani Irin nauyi yakeji a zuciyar sosai.
Baya son Ko kaɗan ayi masa maganar Ahanaf.
Ji yake Kamar zai mutu tsabar
ƙiyayyar da yake yiwa gudan Jinin nasa.
Duk Wani Abu da Abba yasan mallakin Ahanaf ne ya mayar dashi mallakin ƙanensa Al ƙaseem. Batare da Sani Abbu Ko Ayiya ba.






____________ Tsaye yake gefen Wani gidan Mai Yana Zane Zanen sa Sai faman Kore ƙuda yake a fuskarsa da ƙasumba ta taru sosai Saboda Rashin Samun gyara.

Tsaye take a jikin Mota gefen gidan Mai.
Tana bin layin mai
Gajiya tayi da Zama cikin Motar yasa ta fito waje ta tsaya.
Sai faman dan na waya take Tana ya mutsa fuska alamar tagaji da jiran layin Nan.

Shabana! Shabana! Shabana!

Wata matashiyar buduwar ce ke fitowa a cikin Motar tana kwala Kiran buduwar da Ke tsaya tana Dan na waya.

Wace aka Kira da Shabana ce ta juyo cikin masifa da ƙufula Saboda jiran da take famanyi tin ɗa zu tace " Wai Ke Malama lafiya kike kwalamin Kira haka Kamar wacce taci Miki bashi? Tin ɗazu kina Mota zamanki kin barni a waje Ina faman jira Sai kace wata yarinyarki,
Kuma Sai kifito kina min ihu a kunne
Bana son irin wannan Kiran Karki ƙaramin irin sa wallahi.

Dan Allah ya Isa haka masifaffiya Ke ba halin ayi miki Magana Sai ki Wani tasowa mutane da rigima.
Kalla kiga Abunda nake Gani kodai idanuna ne suke gani ba daidai ba.

Saitin hannunta Shabana tabi da kallo,
Cikin mamaki ta ƙara gyara tsayuwar ta tare da Saka hannuwan ta ta murza Idanunta.
Bata ma lura da wayarta da ta faɗi a ƙasa ta tarwatse ba tsabar ruɗanin da tashiga..............✍🏻✍️✍️




♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM


PAGE

1️⃣2️⃣



_____________ Kai tsaye Gurin da Shadow yake Shabana ta nufa cikin sassarfa, dab da Shadow ta tsaya tana kallon Zanen da yake a Bango sake da baki Kamar wata wawiya,
Tama kasa cewa ƙala tsabar mamaki.
Buduwar da ke tare da Shabana ce ta ƙaraso kusa da su tace Ikon Allah Sai kallo.

Haka suka tsaya Suna kallon Shadow Har yaƙarasa Zanensa Tass
Tabɗijam "wannan mutum fa da alama Bashida issashen hankali but Duba kiga aikin da yake Kamar na Wani Mai cikakken hankali" tafaɗa a hankali cikin raɗa.
Wannan ba Shakka Mahaukacine Hafeeza Amma Mai tattare da abubuwan Al ajabi, Taya Mahaukaci ya iya wannan Zanen? Shabana ta faɗa cikin mamaki.

Shadow Yana Gama Zana Shabana ya juya Yana kallonta Yana jiran ta sallame sa, ita hankalinta Baya ma kansa kwata² Zanen Kanta Kawai take kallo,. Sai Daga Baya ta Maida hankalinta Kan Shadow tana murmushi tace "bawan Allah ya sunanka?"
Kawar da kansa yayi gefe batare da yace Mata ƙala ba,
Sake maimaita tambayar tayi Nan ma dai Shiru Shadow yaƙi yayi Magana.
Kodai Baya Magana ne cewar Hafeeza Tana kallon Shadow.
Bai kallesu ba Kuma Bai tan kasu ba.
Jakar hannunta Shabana ta buɗe ta ɗauko kuɗi masu yawa tabama Shadow tace gashi Malam.
Kuɗin ya Kalla ya ɗauke kansa alamar Baya so.
Wasu kuɗin taƙara Akan na farko ta bashi Nan ma yaƙi karɓa.
Shabana batan San cewa "Shadow ba kuɗi yake So ba Shi Abinda yaci yake nema, tunda ya fahimci Idan ya zana mutum Akan ɗauki abinci a bashi,
Sai ya Maida hakan Kamar sana'a duk lkcn da yaji yunwa yakan Zana duk Wanda yake kusa da Shi, Idan ka bashi Abinci ya karɓa yaci Idan ka bashi kuɗi Kuma Sai ya Tafiyar sa.
Yanzu ma Hakan ce tafaru dan fafir Shadow yaƙi ya karɓi kuɗin da Shabana ta bashi.

Tohm Shi wannan me yake so Kenan? Cewar Shabana Tana kallon Hafeeza.
Oho Kuma kinga yaƙi Magana balle musan Abunda yake so.

Tafiya Shadow ya Farayi Yana Sosa kansa da yasha datti Yana Masa ƙaiƙayi.
Bayansa Shabana tabi Tana faɗin
bawan Allah mekake so ne? Ko kulata Shadow baiyi ba ya tsallaka titi ya tafi Abunsa.
Tsayawa tayi tana kallonsa har ya ɓacema ganinta juyawa tayi ta Kuma Gurin Hafeeza jikinta ba ƙwari.
Sai ɗaukar hoton Zanen Hafeeza keyi, kallon fuskar Shabana tayi taga ba ɗigon walwala a tare da ita, Hafeeza tace dan Allah kizo kusa da Zanen Nan Na ɗauki hoton yadda Zan ƙara kafa shaida da kayan jikinki tunda Har su ya Zana.
Ba musu Shabana ta matsa kusa da Zanen Hafeeza tayi Mata hotona masu kyau.


Tafe suke cikin Mota Hafeeza ta kalli Shabana tace "Kai Wallahi Mahaukacin Nan fa ya kwashi gayya kinga fa kusan mutane 27 ne su kace Suna Son wannan Mai Zanen ya Zanasu"
Murmushi Kawai Shabana tayi batare da tace wa Hafeeza ƙalaba.


_________Bayan sati ɗaya
A kullum Shabana Sai tayi tunanin wannan Mahaukacin da Ko sunansa batasani ba, haka Kawai takejin Tana son sake haɗuwa dashi.
Taje gidan Man da tafara ganinsa yafi a ƙirga Amma Bata sake ganin Ko Mai kama dashi ba.
Takan tsaya Gurin da Zanen yake ta ƙura Masa Ido Kamar wacce Bata taɓa ganinsa ba.
Har masu aiki gidan Man sun Saba da ganin Shabana, saboda Idan tazo takan kwashe kusan sa'a ɗaya agurin Tana jira taga ko wannan Mahaukacin zaizo
Idan tagaji da tsayuwa Sai ta buɗe Mota ta zauna.
Amma Haka zata ƙaraci zamanta ba Shadow ba alamar sa.


Cikin firgici Shabana ta tashi zaune Kan makeken gadonta, tana furta Kalmar Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un,
Hannayenta tasa ta dafe Kanta da yake matuƙar Sara Mata tamkar Zai tsage gida biyu.

Runtse idonta tayi tare da cewa
Oh! Allah Gani gareka,
"wannan wane kalar Mahaukaci ne? Kodai da Aljani nayi gamo ne?"
Tun lkcn da nayi tozali dashi nakasa samun sukuni,
kullum Sai Na tunashi yafi a ƙirga na Rasa dalilin da yasa nakasa mantawa dashi.
A hankali tafara buɗe idanunta da suke cike da tsantsar damuwa tafara sau kowa daga kan gadon.
Kai tsaye toilet ta nufa,
bajimawa ta fito kaya tasaka ta ɗauki car key ɗinta tafita cikin sauri.
Wani ɗaki ta nufa Tura ƙofar tayi bakinta ɗauke da sallama.

Matar dake tsaye Tana waya ce ta amsa sallamar Tana bin Shabana da kallon tuhuma.
Dagani Babu tambaya wannan farar dattijuwar mahaifiyar Shabana ce Cox Suna masifar Kama da Juna.
Bayan ta gama ne ta sauke wayar daga kunnenta tare da
Cewa "Sai Ina Kuma? Keda Kika ce kanki na Miki ciwo sosai"
Tafaɗa tana ƙure Shabana da manyan idanunta Dan talura yarinyar Tata tafara sauya halayenta.
Duk Wanda yasan Shabana yasan rigimammiya ce ta ƙarshe,
but yanzu tazama wata silent kamar ba ita ba.

Kanta taɗan Sosa tare da cewa gidansu Hafeeza zanje Ammi.
Bazakije ba cewar Ammi tana ɗaure fuskarta,
Kusa da ita Shabana ta matsa tare da rungumeta ajikinta cikin shagwaɓa tace Dan Allah kiyi haƙuri Ammi kibarni naje akwai Abunda zamuyi ne.
Harara Ammi ta ɓalla Mata Ai kullum zan cen ki kenan,
Kifita daga idona Na rufe Shabana Naga kina so ki ɓaci da yawo yanzu Wanda da ba halinki bane.
Kije Allah ya tsare Amma Dan Allah Karki yadda mahaifinki ya dawo gida baki dawo ba.
Kinfi kowa sanin halinsa Idan yafara faɗa kamar Zai tayar da gari Ammi tafaɗa tana Dariya.
Ita ma Shabana dariyar tayi tare da cewa insha Allah Zan dawo da wuri Ammi.
Tohm Allah ya yadda
Ameen ya Allah.
Har ta buɗe ƙofar zata fita tajuya tana kallon Ammin taɗan marairaice fuska tace bakimin Addu'a bafa Ammi.
Murmushi Ammi tayi tare da cewa Allah ga ƴata zata fita, yadda tabar gida lafiya ya Rabi ka mayar min da ita lafiya, Allah kayi Mata Albarka Kuma ka tsareta da sharrin mutum ko aljan.
Wata sassanyar ajiyar zuciya Shabana tasaki tare da furta Ameen ya Rab Ammina tana murmushi.

Fita tayi daga gidan ranta fari ƙal ba yaune mahaifiyarta ta Saba yi Mata Addu'a ba
Amma Sai taji tafi Jin daɗin ta Yau fiya da ta kullum.
Duk lokacin da zata fita Sai Ammi ta mata Addu'a sannan take tafiya tun tanada ƙurciya take wannan halin nata shiyasa Ammi ke matuƙar ƙaunarta.

Kai tsaye gidansu Hafeeza tanufa a Palo ta Tarar da ita zaune tana cin Abinci.
Wata uwar harara Shabana ta ɓalla mata tare da cewa acici mala'ikun tukunya.
Dariya Hafeeza zayi tare da cewa oh ni Hafeeza naga ta kaina
da ace ke kike ciyar Dani da na Boni Kenan.
Ba halin kiganni Ina cin Abinci Sai kin min gori?
tohm Bismillah zo kema kici Hafeeza ta faɗa Tana murmushi.
Ya mutsa fuska Shabana tayi sannan tace ke Malama ni ba wannanne ya kawoni ba zuwa nayi ki rakani gidan Mai plz.

Cike da mamaki Hafeeza ke kallonta tare da cewa ba kince bazaki Koma neman Sa ba?
Kirufawa kanki Asiri Shabana maybe fa wannan Mahaukacin ba mutum bane tun fa wannan lokacin bamu ƙara ganinsa ba har Yau.

Kusa da ita Shabana ta zauna tare da sauke ajiyar zuciya tace "Naso matuƙa na manta da wannan Mahaukacin amma nakasa Hafeeza kullum lamarinsa ƙara girma yake a cikin zuciya ta, Hafeeza bansan wannan Mahaukacin ba hasali ma Gani ɗaya na taɓa Masa a rayuwata. Amma narasa dalilin da yasa nakasa mantawa dashi nakasa manta fuskarsa nakasa manta kallon da naga Yana mun"
Hafeeza kallon da yake min kallone Wanda yake ɗauke da abubuwa da dama
Neman taimako neman tausayawa
Amma nakasa taimakon sa Cox ban san Abunda yake so ba bansan menene a cikin zuciyar sa ba Amma tabbas a wannan lokacin akwai Abunda yake so agurina Kuma nakasa sanin Menene"
Hafeeza intaƙaice miki zance yanzu ma daga bacci na tashi Kuma nayi mafarkin wannan "Mahaukacin still irin wannan kallon Naga yana min kamar Koda yaushe Idan nayi mafarkinsa" tafaɗa tana goge guntun hawayen da ya taru a gefen idanunta.

Tohm yanzu ya kikeso ayi Shabana? ta Ina zamu Sami wannan Mahaukacin? Sannan Idan Mun sameshi

Please Login or Register in order to submit comment