Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙura masa Ido yayi Yana Tina lokacin da yayi drawing ɗin, ajiyar zuciya yayi tare da buɗe ɗayar pepper, da drawing ɗin Norr yayi arba wata muguwar faɗuwar gaba yaji. Da sauri ya ɗauke kansa ya mayar gefe yanajin wasu zafaffan hawaye na bin kumatun sa.
Tabbas ya So Norr fiye da tunani Amma a yanzu dole ya haramta wa kansa ita saboda an ɗaura Aurenta da Al kaseem, a tsarin sa ko rigarsa ƙaseem ya saka tohm ya bar masa ita bazai ƙara saka ta ba har Abada, bare Kuma kaseem ya Aure Mace Shima yazo daga baya ya Aureta Ina impossible.
Takardun ya yayyaga yana sauke wata irin ajiyar zuciya, Allah kaɗai yasan halinda zuciyar sa take ciki. Jakar ya ɗauka ya bar gurin cikin tashin hankali.





Har ta kwanta taji ƙishi ya addabe ta Tashi tayi tafito Palo tun daga nesa ta hango takardun ya yayyaga su, Saida ta ɗauko water bottle sannan ta dawo gurin ba Shakka takardun ne ya yayyaga, ɗan Jim tayi tana nazari kafin daga bisani ta ɗauko tsintsiya ta kwashe pepper tazuba a basket. Ɗaki ta koma Saida tasha Ruwan Sannan tayi addu'a ta kwanta, tunani fall Ranta menene dalilin da yasa Ahanaf ya yaga takardun.
Kishi zuciyar ta ta bata amsa, gyaɗa Kanta tayi alamar gamsuwa.


The next day
12pm fitowar ta daga toilet Kenan tana Shafa Mai taji an turo ƙofar an shigo, da sauri ta ɗago, Ido suka haɗa da Hafeeza.

Hararar ta Shabana tayi Sannan tace "Madam ya da shigo min ɗaki ba neman izini da yanzu zuwa kikayi kika Tarar ba kaya ajikina fa?" Dariya Hafeeza tayi tace "da Sai na runtse idona na koma inda nafito" gajeren tsaki Shabana tayi tace "Allah ya shiryaki"

"Ameen ranki ya daɗe amarya" Hafeeza ta faɗa tana Zama agefen bed.

Cigaba da Shirinta tayi batare da tasake bi takan Hafeeza ba.

Hafeeza gwanar tsokana ta sake cewa "Ina angon namu yake ne? naga ban ganshi ba"
"Gashi nan a kaina" Shabana ta faɗa tana ƙoƙarin ɗaura ɗan kwalinta.
Murmushi Hafeeza tayi tare da cewa "saurin me kike yarinya?"


Bayan Shabana ta Gama Shiri suka dawo Palo Suna fira Duk da cewa Rabin firar tasu Duk faɗa ne.

Suna cikin haka ya Suhail ya shigo tare da Aunty Fatee da Aunty Aisha, Ya Maleek ne ya kirashi yace "Idan zai kai Fatee yaje ya ɗauki Aisha ya tafi da ita saboda aiki ya riƙe Shi sai ya gama zai zo" Da gudu Shabana taje ta rungume su tana Dariya Tare da Yi musu Sannu da zuwa.
Cikin dariya Aunty Fatee tace kiyi a hankali fa Amarya tsautsayi ne da ita, Kar ki faɗi kisa angon ya Mana hukuncin bamu jiba bamu Gani ba" murmushi Aunty Aisha tayi tace "lallaikam" ya mutsa fuska Shabana tayi tare da cewa "daga zuwanku zaku Fara tsokana ta ko, Wallahi ku bini a hankali Idan ba haka ba na ƙaro muku kishiya" Aunty Fatee tace "kefa matsala ta dake Kenan bakida Magana Sai ta kishiya, Hafeeza kidinga mata wa'azi Mana" riƙe haɓa Hafeeza tayi tare da cewa "rufamin Asiri Aunty Fatee wannan da kike Gani rigimarta Sai Ammi da Dady, koda yake yanzu saidai muce Ahanaf Ko?" Gabaki ɗaya dariya sukayi har ya Suhail da ya nufi ɗakin Ammi.
Murtuƙe fuska tayi tace "Wai me kuke nufi dani ne ba halin nayi Magana Sai kumin caaah kamar zaku cinye ni" Aunty Aisha tace a'a fa Amarya baki dai fahimce mu bane, yanzu Bari muje mugaida Ammi mudawo musha fira kinji Auta" Aunty Aisha ta faɗa tana Dariya.




Bayan sun dawo daga gaida Ammi ne suka zauna Palo Suna fira.
Ya Suhail ya Kalli Shabana yace "ke Ina Ahanaf ne?"
Ya mutsa fuska tayi kamar bazatayi Magana ba Sai kuma tace "maybe Yana ɗaki" Aunty Fatee tace "Abu Muneef Dan Allah kaje ka fito Mana dashi muganshi wallahi Idan baiyi ba kin Shiga ukkunki, kinfi kowa ganin Mata da miji kice Basu dace ba. Muma Yau kalar wannan halin naki zamuyi miki" Dariya ya Suhail yayi sannan yace "wannan karon dai Zan shigarwa ƙanwata ku daina tsokanar ta haka nan, kuma indai Ahanaf ne zaku sha mamaki saboda Bashida wata makusa" Bari naje nazo dashi murmushi Aunty Aisha tayi tare da cewa "mudai bazamu yarda ba har sai mungan Shi Suhail"

Me kikeci na baka na zuba Bari kigani yanzu zaizo ya Suhail ya faɗa yana fita daga palon.

Anan sukaci gaba da firar su wacce duk rabi tsokanar Shabana suke.

Tun daga nesa suka hango zuwansu Masha Allah Shine Abunda Aunty Aisha tace tana kallon Shabana "Lallaima wannan yarinyar wato saboda kinsan bazamu ɗaga miki ƙafa bane yasa kika zaɓi handsome guy haka?"
Murmushi Shabana tayi tare da kallon gurinda suke. Riga ce a jikinsa Scan blue da Wando baƙi takalmin da ke ƙafarsa ma scan blue ne. Shadow ya fito ai nahin Shadown sa kamar yadda yake ada, ita Kanta Shabana ta kasa ɗauke idonta daga kallonsa, gani take kamar bashi ba.


Gaidasu yayi cikin girmama yana ɗan murmushi, amsawa sukayi Suna tsokanar sa wai ango Auta.
Shidai murmushi kawai yake zubawa, batare da yayi Magana ba.
Hafeeza ta kalleshi tace "ya fama da rigimarta kuma?"
Kallon Shabana yayi yana murmushi yace "ai batada rigima saidai Idan Kun tsokaneta ne" riƙe haɓa Hafeeza tayi tace "eh Lallai ba ayi ba yanzu za'a Fara, wato kai Ahanaf matar ka kake karewa ko?" Aunty Fatee tace "yo Ke Hafeeza Menene na tambaya ga Abu nan a bayyane, ita ya shigarwa Mana."
Ya Suhail yace " da so kuke yayi Shiru ku ciwa matarsa mutunci? Ai gara kawai ya baku amsa daidai daku."

Haka sukata fira har aka Kira Sallar azahar. Ya Suhail da Shadow suka tafi masallaci. Su kuma suka Shiga ɗakin Shabana don gabatar da Sallah.
Bayan sun kammala ne aka buɗe chapter Ahanaf kowa da abunda yake faɗa.
Aunty Fatee tace "Ku Baku lura da kalar kallon da yake mata ba?"
Cikin dariya Hafeeza tace "Wallahi Kuwa Kamar zai janyeta da idonsa"
Duk shaƙiyanci da surutun Shabana haka ta koma Kamar kurma a cikinsu. Tashii tayi zata bar musu ɗakin gabaki ɗaya Hafeeza ta riƙota tace "ba inda zaki, wato ke ga wanzam ko anan zaki zauna mu ƙarasa magananinki tunda mai shigar mikin ma Baya nan."
Aunty Aisha tace "Dan Allah kubar ta haka ta huta, duk da ita ɗin ba abin Tausayi bace Cox halinta ne takurawa Mutum tayi masa abunda baya so."




Wunin Ranar haka Shabana tayi Shi tana Shan tsokana, har Yamma lokacin da zasu tafi Shabana tace "Allah ya raka taki Gona, Ai dama ba gayyarku mukayi ba"
Cikin ƙasa da murya Aunty Fatee tace "wato yarinyar nan kin matso mu tafi kije gurin mijinki ko?" Ita kuwa Shabana ganin Aunty Fatee Bata So Ammi taji Abunda tace "yasa ta ɗan ɗaga murya tace "haram ne Idan naje gurinsa?" Da sauri Aunty Fatee ta ɗauki Muneef ta saɓa a kafaɗa, Saboda ta Lura Shabana kunyata ta takeso tayi gaban Ammi.
Saida suka tafi sannan Shabana ta Samu ta sarara.


Shadow ne zaune gaban Dady ya sunkuyar da kansa ƙasa.
Dady yace "kanaji na Ahanaf?"
"Eh inaji Dady"

"Kana son wannan auren ko a'a?"

Da sauri Shadow ya kalli Dady cikin mamaki yace Dady Mai kagani halan?

Dady Yace "a'a ba Kumi Ahanaf Ina dai so ne Naji amsa ne daga bakinka kafin na ƙarasa faɗar Abunda Zan faɗa"

Dady ni banida bakin cewa bana son Shabana, Wallahi Dady Idan nace Maka Bana sonta nayi maka ƙarya saboda a duk tarihin rayuwata ba Wanda ya taɓa kwatan yimin kalar Abunda tamin.
Dady Idan dai kaga na rabu da Shabana to ita da Kanta tace bata Sona na saketa.
Anan Kam dole na saketa kodan narama kalar halaccin da tamin.

Dady ya gamsu sosai da bayanin Ahanaf Kuma ya ƙara yabawa da hankalinsa, yace Masha Allah dama "Abunda nake so da kai biyu ne zuwa ukku.
Na farko Ina So ka saki jikinka nan gidanku ne, Wannan Maganar na yita nanata maka ita, ya kamata ace ka fahimci Abunda nake nufi.
Na biyu kuma maganar Aurenka da Auta duk da cewa dai an ɗaura shine Domin ceton rayuwarka, Amma dai kasani Aure ne kamar kowanne igiya ukkunka ne akan Shabana. Yakamata kafara Shiri Akan rayuwar da zaku fuskanta nan gaba, dole Idan kana son wannan auren ya ɗaure Saika nemi soyayyar Shabana Idan ta aminta zata zauna dakai, tohm sai katafi mataki nagaba, wato haɗuwa da iyayenka dan dole sai sun San Abunda yake faruwa kafin ayi biki ku tare a matsayin ma'aurata.
Sai Abu na ukku kuma na ƙarshe Shine maganar aikin ka, na Samar maka office Wanda zaka ci gaba da zuwa kana harakar Zanen ka kuma Insha Allah zan Samar maka kwangila Zana gidaje, mall da sauransu. Nasan hakan zai rage maka kaɗai ci sosai saboda maganar gaskiya zama gida ba daɗi agurin namiji.


Ajiyar zuciya Dady yayi Sannan yace "Duk cikin abubuwan da Na faɗa Idan Akwai Abunda bai maka ba zaka iya magana Kaji"


"Dady me zance maka Nikam? Bakina ba Zai iya furta godiyar da take cikin zuciyata ba, Saidai Abu ɗaya da Zan iya yi maka Shine nayi maka addu'a da fatan Alkhairi.
Haƙiƙa kunyi min halacci sosai Dady Ina roƙon Allah ya bani Ikon kwatanta irin wannan halaccin a gareku. Shadow ya faɗa yana goge hawayen idonsa.

Murmushi Dady yayi yace "ba Kumi Ahanaf zaka iya Tafiya Allah ya tashemu lafiya."

Sallama sukayi Sannan yafita.

Har tayi shirin kwanciya taji wayarta tafara ringing, ɗagawa tayi tare dayin sallama.
Toh Dady shine abunda ta faɗa tare da kashe wayar.


Koda tashiga ta Tarar da Ammi a ɗakin gaidasu tayi sannan ta zauna a ƙasa tana sauraren taji Abunda Dady zaice.
"Shabana" Dady yafaɗa cikin serious voice
Saida taji wani dummm a zuciyarta tace "Na'am Dady"
Inaso ki buɗe kunnenki da kyau ki saurari abunda zan faɗa miki.
Dama Magana ce kan Auren Nan naku, kifa Sani duk Aure sunan sa aure kamar kowanne, duk wasu haƙƙoƙin Aure sun rataya a wuyanki. Duk da cewa bazamu Bari kutare a matsayin ma'aurata batare da munga magabatansa ba Amma kisani Shi mijinki ne. Dalilin da yasa muka ce Sai munga iyayensa, Ba Wai bamu yadda dashi bane a'a kawai dai Ina gudun abunda zaije ya dawo Bayan Mun haɗu da a halinsa.
Sannan yanzu Idan har zaki fita dole ne ki nemi izininsa ba wai ki tambaye Ni Ko Amminki ba, Idan ya barki tohm mu bazamu hanaki ba Idan kuma yace a'a saikiyi haƙuri ki zauna gida.
Yawwa sannan wani hanzari ba gudu ba Shabana Idan har kinsan baki son Ahanaf ko kuma bazaki iya zama da shiba a matsayin miji to ba dole, Sai kiyi bayani a San ta yadda za'a ɓullowa lamarin. Amma ga shawara a matsayina na mahaifinki kuma ba umarni nake baki ba, duk hukuncin da zaki yanke yana da kyau kiyi nazari sosai Akai kuma kibi kumai a hankali. Aikin gaggawa na sheɗan ne karki yanke hukuncin da zakiyi nadama akansa nan gaba.
kiyi shawara akan komai zaki aikata Shabana, Idan ma bazaki iya maganar da mu ba Akwai Hidaya ƴar uwarki ce, duk da ba wani Shiri a tsakaninku Amma nasan Insha Allah bazata baki mummanar shawara ba. kuma ga Hafeeza Nida kaina na yaba da hankalinta ita ma zaki iya tuntuɓar ta akan lamarin."
Tun lokacin da Dady ya Fara Magana Shabana ta nutsu ko dogon motsi Bata son tayi.
Dady ya kalli Ammi yace "Ammin Yara akwai abunda zaki ce?" Murmushi Ammi tayi tace "Abu ɗaya zan faɗa tunda yanzu ba huɗubar zuwa gidan miji muke Mata ba. Kallonta ta Maida Kan Shabana tace "Ina so ki ƙara nutsuwa Kisan Abunda kike, yanzu da da ba ɗaya bane, kina kan matakin da dole Sai kinyi taka tsantsan saboda Abu ɗaya zaki iyayi ki ƙona kanki.
Ko agurin Magana Yana da kyau Kisan kalar maganar da zaki faɗa masa, Idan dai har kika ƙuntata masa da saninki tohm basai na faɗa miki ba Cox kin karanta kinsan komai. Idan har kinsan bazaki masa biyayya ba tohm kiyi nazari akan shawarar mahaifinki kinji" wasu siraran hawaye ne suka dinga binta kumatun ta.
Ammi tayi ta bata shawarwari, kafin sukayi sallama ta fita daga ɗakin.


Tafiya take tana nazarin kalaman iyayenta.
"Ji mana Dan Allah 2mint" taji sautin muryar sa ya daki kunnenta.
Juyawa tayi ta kalleshi "plx kizo zamuyi Magana" Yana gama faɗar haka ya juya ya Fara Tafiya.
Sakin baki tayi tana binsa da Ido har ya ɓacewa ganinta, wani mugun haushinsa taji, da har taso ta wuce ɗakinta ba tare da taje taji Kiran da yake mata ba. Sai kuma ta tuna da maganar Ammi. ya mutsa fuska tayi kamar zatayi kuka tabi bayansa.
Sallama tayi ya amsa sannan ta Tura ƙofar tashiga........✍️✍️✍️











Nabeela Binji ce💃💃💃







More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏.





♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MO



TIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM




Page

3️⃣ 2️⃣












__________________ A ƙofar ɗakin ta tsaya batare da ta ƙarasa Shiga ciki ba.
Ɗagowa yayi ya kalleta yace "zo ki zauna Mana" ya faɗa yana nuna mata gefensa. hararar sa tayi ƙaƙasa sannan taje ta zauna ɗan nesa dashi.
Gyara zama yayi Yana fuskantar ta sosai.
Sunkuyar da kanta tayi ƙasa.
Ajiyar zuciya Shadow ya sauke yace "da farko dai ina ƙara miƙa dubun godiya ta ga ubangiji da ya haɗa ni da Mutane masu matuƙar kirki, kisani Banida bakin gode muku, musamman ma Ke" ya faɗa yana nunata da yatsa. Ajiyar zuciya tayi batare da tace masa ƙala ba.
Nan ya faɗa Mata maganar office ɗin da Dady ya Samar Masa. Yace Dan Allah ki ƙara tayi godiya a gurinsa kinji?
Murmushi Shabana tayi tace "ba matsala insha Allah"
Ɗan Jim yayi kaffin yace "Shabanaaaah" da sauri ta ɗago ta kalleshi Jin yadda yaja sunan nata. Bai damu da kallon da ta masa ba yaci gaba da maganar sa yace " Dan Allah Ina neman Alfarma ɗaya agurinki" a hankali tace "Ina saurarenka" yace "Ina so kibani dama na kwatanta yi miki halacci Kamar yadda kika min, Bima'ana ki Bani dama nazama silar farin cikin ki. Ya ƙarasa maganar yana kallon fuskarta yaga bawata alama a fuskanta wacce ta nuna amincewar ta ko rashin amincewar ta.
Shiru ɗakin yayi ba Wanda yayi Magana a cikinsu. Kallonsa tayi ta ɗan marairaice fuska tace "Bacci nakeji" murmushi yayi tare da cewa "zaki iya Tafiya Allah ya tashemu lafiya"
"Ameen" da Ido ya rakata Har ta ɓacewa ganinsa. Ya sauke ajiyar zuciya tare da faɗawa Kan bed.





Mintina sun shuɗe sun zama awanni, awanni sun sun shuɗe sun zama kwanaki. A kwana a Tashi ba wuya a gurin Allah Yau har Shadow ya cika one month da dawowarsa cikin hankalinsa. Kuma alhmdllh Yana cikin matuƙar farin ciki zaman sa tare da su Ammi, saboda ba Abunda ya nema yarasa. Saidai matsalarsa ɗaya Shine ya kula baya gaban Shabana. Idan Dai bashi ya fara Janta da fira ba toh Sai su kwashe awanni a guri ɗaya ba tare da tayi Magana ba.
Koda tace "masa tana so ya Koya mata drawing Idan tazo koyar eh a'a ne kawai tsakaninta dashi" Amma Sai yaga lafiya Lau take fira da sauran Mutane, musamman ma Hafeeza da ya Lura Basa zama basuyi faɗa ba, hakan ya tabbatar masa dashi ne dai bata So ta zauna tana fira. Shi kuma ya ƙuduri aniyar Sai yasa dole ta saki jikinta dashi kamar sauran ƴan gidan koma fiye da haka.









____________ "Norr kitashi ki Karya kisha magani kinji Bana son sakarci" Mommy ta faɗa ciki masifa. Tashi Norr tayi tare da jingina jikinta da gado. Mud ɗin Mommy ta miƙa Mata, tace "ƙarbi Kisha, ga magani nan shima sai kisha" ba yadda Norr ta iya dole ta karɓa ta Fara sha. A hankali taji zuciyarta na wata zunkuɗa, ta daure ta ƙara kai Mud ɗin bakinta ai kuwa nan take taji Amai ya taso mata da gudu ta sauka daga kan gadon tayi toilet tafara kwarara Amai Kamar Ranta zai fita.
Baki Mommy ta saki tana kallonta ciki zuciyarta kuma tana fatan Abunda take zargi ya zama gaske. Toilet ɗin tashiga koda taje tarar da Norr ta galabaita kamata tayi tare da taimaka mata ta gyara jikinta tafito da ita waje, ta kwantar da ita Kan bed tare dayi mata Sannu. Wayarta ta ɗauka takira family Dr ɗinsu akan yazo ya Duba Norr. Bayan yazo yayi gwaje gwajensa ya tabbatar da Norr tana ɗauke da Juna biyu na tsawon Wata 3 da sati ɗaya. Alhmdllh Mommy ta faɗa cike da matsancin farin ciki. Ta ɓangaren Norr kuma ji tayi gabaki ɗaya duniyar tana juya Mata Wani Jiri taji yana ɗibar ta. da sauri ta Runtse idanunta Tana fatan wannan Abun yazama mafarki ne take bawai gaske ba. Jin maganar Dr da Mommy ne ya tabbatar Mata da gaske ne tana ɗauke da Juna biyu. Kuma ba Saita ɓata lokacinta gurin tambayar cikin waye ba, saboda Wannan amsar a bayyane take cikin jikinta Na kaseem ne. Ya Ilahi tafaɗa hawaye na bin kumatunta duk cewa wannan cikin bana shege bane Amma raɗaɗi da azabar da takeji a zuciyarta yafi na wacce tayi cikin shege.
Bayan Dr ya tafi Mommy ta dawo ɗakin ta Tarar Norr tana kuka kamar Ranta Zai fita.
Kusa da ita Mommy ta zauna tare da janyota jikinta ta rungumeta. A hankali cikin sigar rarrashi Mommy tace "Duk wannan kukan na menene Norr? Dan Kawai an ce kina ɗauke da Juna biyu Sai kifara irin Wannan kukan? Kodai baki gode ni'imar da ubangijinki ya miki bane? Karfa ki manta haihuwa kyauta ce da ba mai iya maka ita sai Allah. Ki godewa Allah da yabaki kyautar ɗan Adam a mahaifarki. Kinsan yawwan Mutanen da ke neman haihuwa Ido rufe, sunyi addu'a sun kashe kuɗinsu Amma Duk da haka Allah bai Basu ba? Ke mai kikayiwa ubangiji ya ɗauki kyautar ɗa sukutun ya baki? Ya kamata kinutsu ki dawo cikin hankalinki. Wannan cikin naki Abun Alfahari na ne kuma Abunda najima Ina jiran bayyanar sa Norr" dakatar da kukan nata tayi tana sauke ajiyar zuciya tabbas kalaman Mommy sunyi tasiri sosai akanta, Amma ita kukan rashin Ahanaf take kuma Kukan tausayin kansu takeyi. Da ace wannan cikin da yake jikinta na Ahanaf ne da ba Shakka farin ciki ne Zai Maye gurbin wannan ƙunci da yake damun ta yanzu. Amma ina ƙaddara ta riga fata. Taƙuduri niyar Sai kaseem ya Saketa Saidai ta ƙarasa rayuwar ta ba Aure da ta zauna dashi a matsayin miji. Ko Abunda ya faru har yanzu tana mamaki a kansa dan har ga Allah batasan ta zaɓi kaseem Akan Ahanaf ba. Haka dai Norr tayi ta saƙe saƙe aranta.








_______________ Ayiya ta faɗawa Abbu cewa Norr tana ɗauke da Juna biyu. Abbu yace "Allahu Akbar khabeeran, waɗan da sukayi wannan aika aikar gaggawa kawai sukayi Domin lamarin Allah rubutacce ne, koda wannan Abun ko Babu tunda Allah ya nufi Akwai zuri'a tsakaninku tohm fa ba mahani dole sai hakan tafaru" cikin sanyi murya Ayiya tace "hakane Yaya Amma Shi ƙaseem yace ba ruwansa Wai ba cikinsa bane" Abbu yace "wannan kuma Bai Isa ba, Ina Shi ƙaseem ɗin yake?" Ayiya tace "tunda na faɗa masa maganar cikin yafita har yanzu bai dawo ba" Okey ba matsala "Idan ya dawo ki gaya masa Ina nemansa" Toh insha Allah Yaya.
Har zata tashi Sai kuma ta fasa tace "Yaya ya labarin neman Ahanaf, Har yanzu Shiru" tafaɗa cikin marairaice fuska.
Murmushin takaici Abbu yayi yace "har yanzu Shuru ba wani labarin Shuwa, kidai ƙara tashi tsaye da addu'a saboda ke uwa addu'arki bata da shamaki Akan Yaronki" Kai ta gyaɗa tare da cewa "munakanyi Yaya fatanmu dai Allah ya karɓa" Toh ameen.



Abbu ya faɗawa Abba duk yadda sukayi da Ayiya yaƙara da cewa Shi kuma kaseem yace ba ruwansa da cikin.
Abba yace "Yaya ni ba wannan matsalar bace a gabana burina da muradina shine naga Ahanaf" Abbu yace ita ma wannan matsalar dole kasakata cikin matsalolinka Muhammad tunda dai wannan Abun duk lamarin ahalinka ne, saboda haka bana so nasake ji ka faɗi haka" Shiru Abba yayi Dan Shi Magana ta gaskiya daga Ƙaseem din har Norr haushinsu yakeji. Kawai dai dan Bashida bakin Magana ne Akan Abunda duniya ta bayar da shedar cewa Shine ya bayar da goyon Bayan sa.


Ƙaseem ne zaune agaban Abbu ya sunkuyar da kansa ƙasa yana sauraren faɗan da Abbu yake masa. Shiru yayi bai ce Kala ba.
Cikin Bada umarni Abbu yace "kuma katashi kaje kabduba yarinyar nan ka tambayeta Idan akwai abunda take buƙata" zaiyi Magana Abbu ya ɗaga masa hannu yace umarni na baka ƙaseem, Bana so Kaji tsorona Kaji tsoron Allah da ya halicceka, Norr tanada haƙƙi akan ka Idan ka saka taurin kai zaka iya ƙona kanka. Kaɗauki jarabawa kaseem ka yarda da tsarin ubangiji akanka, kasani ba Mai Ikon canza ƙaddarar ubangiji, idan har kayi Imani da haka tohm Ina son ka fawwalawa Allah Komai yanaji Kuma yana gani Zai kawo karshen Sharri da masu yinsa.
Duk inda Wata gaɓa take ajikin kaseem ta saki zuciyarsa ta ƙare sosai Nan take yaji saukar hawaye kan fuskarsa, da sauri yasa hannusa ya goge. Cikin sanyi murya yace "insha Allah zan tafi Na dubata Abbu" murmushi Abbu yayi tare da ɗan buga kafaɗar sa yace "Allah yayi Maka Albarka kaseem kagaida Mai jiki" ameen Abbu nagode.







_______________ A palo ya haɗu da Mommy gaidata yayi tare da sunkuyar da kansa ƙasa, Murmushi Mommy tayi tace "kashiga ciki tana ɗakinta"
Ɗakin ya Shiga kwance ya Tarar da ita Kan bed ta dukunkune cikin blanket, Zama yayi kusa da ita Tare da cewa "ya jikin naki?" cikin sanyin murya tace "da sauƙi"
"Allah ya ƙara Afuwa, yanzu Mai yake miki ciwo?" Shuru tayi Saida ya ƙara tamabayarta Sannan tace "kaina ke ciwo Kuma Ina Jin Jiri"
"Kinci Abinci?"
"Aa"
Haba Norr Ai dole ne kiji Jiri tunda ba kici Komi ba. yanzu faɗa min mai zakici?" Yamutsa fuska tayi tare da cewa "ba kumi"
Blanket ɗin ya yaye, yace "kitashi ki faɗa min Abunda zakici" Shi bai San Wani mugun haushinsa taje kamar ta shaƙeshi ba. "Dan Allah ka rufeni sanyi nakeji ta faɗa tana ƙoƙarin Jan blanket ɗin" rufetan yayi Kamar yadda ta buƙata tare da ƙara tambayar ta me zataci.
Ganin ya hanata sakat ne yasa tace masa "tuwon semo da miyar ɗanyar kuɓewa" Tashi yayi yace okay Ina "zuwa" bayansa tabi da harara har ya fice daga ɗakin, taja gajeren tsaki tare da gyara kwanciyarta.

Ba jimawa ya dawo ɗakin zama yayi tare da cewa "tashi kici Abincin" Banza tayi masa kamar bataji Shi ba.
Norr Norrrr
Na'am ta faɗa kamar zatayi kuka.
"Plx kitashi ga Abincin nan na kawo miki" Tashi tayi tashiga toilet ta wanke bakinta ta fito. Sallaya ta Shin fiɗa ta zaune ƙasa.
Abincin ya kawo gabanta tare da zama gefen gado Yana facing ɗinta.
Tana cikin cin Abincin taji tashin zuciya da sauri ta turashi gefe.
"Badai Har kin ƙoshi ba?" Toilet yaga tashiga da gudu bai gama mamaki ba yaji tana zuba Amai. da sauri ya shiga toilet ɗin tare da kamata ya taya ta gyara jikinta. Sai Sannu yake Mata, yace "kin gani ko har yunwa ta kamaki" da sauri ta janye jikinta daga nasa wani Aman ne ya ƙara zuwa mata. Ya Salam kaseem ya faɗa yana dafe kansa.
Norr ta galabaita sosai Tarasa mai zatayi Kawai Sai tafara Kuka.
Da kyar ya samu tayi shuru ya ɗauki wayarsa yakira Dr Maryam yace "tazo taƙara dubata asa Mata drink."












______________ Zaune suke a harabar gida table ne agabansu Kanya drawing Suna Sama, kallonta yayi yace "Bismillah fara" shagwaɓe fuska tayi tare da cewa "Mai Zan Zana to" baki yasaki yana kallonta cikin mamaki yaɗan Harare ta yace "Zana ni to" murmushi Shabana tayi tare da gyara pepper ita a dole ga Artis, zata Fara Zanen Shadow ya riƙe mata hannu yace" rufamin Asiri Idan kika zanani Ai saiki fitar dani kamar wani horo" dariya tayi tare da cewa "Allah kabari kagani zan fitar da kai yadda kake" Shadow yace "a'a nayafe Kawai ki nemi wani Abun kizana" Nikam mai zan Zana?" Murmushin ƙeta yayi sannan yace "ki Zana fuskar ya Suhail" Ido Shabana ta ware kamar zasu faɗo ƙasa tace "haba karufamin asiri Wallahi nasan Idan ya Suhail yagani Sai ya dakeni" Shadow

Please Login or Register in order to submit comment