Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aiki mai matuƙar wahala ba kamar nasa.
Amma kuma alhmdllh saboda a Daren jiya nayi Nasarar rabashi da wannan mugun Aljanin.
Duk da yake cewa na wahala, Amma ba Shakka Wanda ya masa wannan aikin ba ɗigon Imani a zuciyar sa, saboda Ko aljanin da aka haɗa Shi dashi mahaukacine kuma kurma. Nasha matuƙar wahala kafin na rabashi da wannan bayawan Allah.

Amma Kuma ba a nan gizo ke saƙar ba, ba iya wannan aljanin ne ya Sa Shi wannan mahaukar ba. An masa a sirine a sanadiyar AURE, kuma a yadda na fahimta Duk Wanda yayi Masa wannan aikin na kusa da shine sosai.

Ido Shabana ta zuba wa Malam Ibrahim Kamar zasu faɗo kasa Amma takasa furta Kumi.
Dady ne yayi ƙarfin halin cewa yanzu Mai ya rage Malam?

Gyara zama Malam Ibrahim yayi tare da cewa gaskiya matsala ce Babba Alh saboda dole ta inda aka hau tanan ake sauka, wannan Yaron bazai warke ba har Sai an ɗaura Masa Aure. Sannan musan mataki na gaba, saboda ba iya auren ne zai warware wannann matsalar ba.


Aure? Dady ya maimaita cike da matsanancin mamaki...........✍️✍️✍️















Nabeela Binji ce💃💃💃





Nabeelah Shehu Binji

09064314811
Or
09161107610




More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏.





♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM


PAGE

2️⃣ 5️⃣








____________ Malam Ibrahim yace "Eh Aure Alh Usman asirin da akayiwa Ahanaf ta dalilin aure aka masa Shi, kuma sai an ɗaura Masa Aure sannan zai warware" Tabbas duk wanda yayi wannan aikin azzalumi ne na ƙarshe, saboda yasan abune mai matuƙar wahala samun Wanda zai bayar da auren ƴarsa ga mahauakaci wanda ba Asan tushe da asalinsa ba" Wallahi Alh Usman da ace Ina da ƴa mace wacce ban aurar da ita ba, da na aurawa Ahanaf ita Dan kawai samun lafiyar sa da kuma tonuwar asirin wanda ya masa wannan Zaluncin. Malam Ibrahim ya faɗa cikin jimami da kuma tausayawa Ahanaf ɗin.

Numfashi Dady ya furzar tare da cire hular kansa Yana goge zufan da ya tsatsafu akan goshinsa, cikin sarƙewar murya yace "Malam Ibrahim ba wata hanya da zata warware wannann asirin dole sai an ɗaura masa Aure?" Kai Malam Ibrahim ya gyaɗa masa tare da cewa "tabbas wannan ita kaɗai ce hanyar da za Abi muddin ana so ya dawo cikin hankalinsa" ɗan Jim Dady yayi kafin daga baya yace "dole sai naje gida Mun tattauna wannan maganar da iyalaina kafin musan hukuncin da yakamata mu yanke akan wannan lamarin. Saboda ba Abu mai sauƙi bane samun yarinyar da zata aminta ta aurin Ahanaf, kuma ma koda ace an samu yarinyar da zata aure shi Toh fa yanada matuƙa wahala iyayenta su yarda. Saboda ba wani uba da zai yadda ya ba yarda da Auren ƴarsa ga mahauakaci wanda ba'a masan daga Ina ya fito ba."

Eh gaskiya maganar ka haka take, Amma kuma ba abune mai wahala ba ga duk wanda yasa Allah a gaba, muddin Mutum yayi komai dan Allah "musamman taimakon Wanda bashida yadda zaiyi ya tamaiki kansa" tohm tabbas Allah bazai bari ka tozarta ba Bi'izinillahi Rabi.

Murmushi Dady yayi yace "zamu San abunyi insha Allah"
Malam Ibrahim yace "Allah ya yadda kuma ya Ida nufi Na Alkhairi"

"Ameen ya Allah"

Kallon Shabana Dady yayi wacce tayi Nisa a duniyar tunani.
Cikin murmushi yace "tun ɗazu muke Magana baki ce Komai ba daughter, Kodai bakida Abun cewa ne?" Ko motsi Shabana ba tayi ba.
Dady yace Shabana Shabana ana ukku yace Shabanaaaa da ƙarfi yana taɓa hannayensa.
Firgigit tayi tare da cewa "na'am Dady"
"Ya Ilahi tunanin me kike haka?"
"Bakumi Dady" tafaɗa tana sunkuyar da Kanta ƙasa.

Murmushi Dady yayi yace "ki kwantar da hankalinki daughter Komai Zai zo da sauƙi da yardar Allah. Niyar ki ta taimako ba zataje a banza ba,
Nima yanzu ina bin Bayan ƙudurinki" Wata sassanyar ajiyar zuciya ta sauke tare da yin murmushi.
Tace "nagode sosai Dady Allah ya baka Ikon cika Alƙawari"

"Ameen ameen"

Dady ya Kalli Malam Ibrahim yace "yanzu zamu iya ganin Ahanaf ɗin?"

Malam Ibrahim yace "Eh zaku iya ganinsa"

Gabaki ɗayansu ɗakin da Ahanaf yake suka Shiga, Koda suka Shiga sun tarar dashi zaune ya haɗa kai da gwiwa kamar wanda yake Jin tsoron wani Abu.

Ido Shabana ta zuba masa ko kyabtawa Batayi, Allah kaɗai yasan Abunda take tunani game dashi acikin zuciyar ta. saidai da ka Kalli fuskar ta zaka fahimci Akwai matsancin tausayin Ahanaf a tare da ita.

Kamar an ce ya ɗago fuskar sa sukayi Ido huɗu da Shabana.
Wata faɗuwar gaba taji cikin sauri ta Maida Kanta ƙasa tanajin yadda ƙirjinta ke harbawa.

Dady yace "alhmdllh gaskiya sauƙi yana samuwa Malam Ibrahim, dubi yadda ya zauna ya nutsu guri ɗaya kamar bashi ba"
Hakane Alh "Ai yanzu ko shikaɗai zai iya zama a ɗaki ba tare da wani Abu ya sameshi ba" murmushi Dady yayi yace "tohm Allah yaƙara bashi lafiya"

Ameen ameen cewar Shabana da Malam Ibrahim.

Shidai Shadow da Ido Kawai yake binsu saboda baimasan Akan me suke Magana ba.

Sallama sukayi da Malam Ibrahim Sannan suka tafi gida.








_________ Malam Taya zaka faɗa min wannan maganar Anya Kana cikin hankalinka Kuwa? Ahanaf ɗin da ya Mutu zaka ce wai Wani yana ƙoƙarin warware asirin da muka Masa. A wannan Karon dai Kam kasamu matsalar bincike gaskiya.

Wata mahaukaciyar Dariya Boka ( wanda suke Kira da Malam) yadingayi Saida yayi Mai isarsa Sannan yace "bincike na Bai taɓa nuna min ƙarya ba, tabbas waƴanda kuka Saka su kashe wannan Yaron Basu kashe Shi ba Yana Raye jiya da dare aka ƙona Aljanin da na haɗashi dashi. Kuma Suna ƙoƙarin warware asirin da ke jikinsa yanzu haka.
Idan har sukayi nasarar warware wannann asirin ba Shakka a jikin Ku zai dawo, Kuma duk Wani Asiri da Ku kayi Zai warware.
Boka yafaɗa yawa wata Dariya Hhhhhhhhhhhh tare da katse Kiran.




Suna tsaka da Shaye shayensu, wayar Jibgege ta Fara ringing wayar ya Kalla tare da buga uban tsaki yace "ƴan lawaha, ai tunda buƙatar Ku ta biya baku ƙara ne manmu ba Sai yanzu" Kwalele yace "suwaye halan mutumena?"
Tsaki Jibgege yayi sannan yace "waƴan da suka sakamu Kisan wannan saurayin Watannin Baya" cikin sauri Ɗan tsunke da yake kwance ya Tashi zaune yace "kai Shine har kuka tsaya Wani Jan Aji? Kun fasan suna sakin kuɗi sosai, tun lokacin da mukayi musu aiki suka bamu maƙudan kuɗaɗe sune muke Kashi har yanzu. Yakamata mu ɗaga Muji ƙilama Wani aikine mai tsoka zamu ƙarayi musu" gabaki ɗayansu sun yarda da maganar Ɗan tsunke, Kwalele yace "gaskiya Kam Idan sun ƙara kira mu ɗauka Kawai" Bayan ƴan mintuna aka ƙara kira.
Cikin sauri Jibgege ya ɗaga zaiyi Magana yaji an lailayo Mata Uwar Ashar an maka masa, sauke wayar yayi a kunnensa yana mamaki Kwalele da Ɗan tsunke suka Kalle Shi sukace lafiya mai yafaru?

Jibgege ya saka wayar a ansakuwa saboda suji abunda yake faruwa.

Ɓangaren da suka Kira wayar sukaci gaba da masifa "mubiya ku maƙudan kuɗaɗe muce ku kashe muna yaro Sannan kuje ku sakeshi Tsabar kun Raina Mana da hankali?" Cikin hasala Jibgege yace Kamar ya Mun sakeshi? Mutumen da Saida muka tabbatar baya numfashi Sannan muka jefar dashi.

To kusani be Mutu ba kuma dawowar sa babbar Barazana ce a rayuwar mu gabaki ɗaya.
A saboda haka muke baku shawarar ku nemo shi a Duk Inda yake ku kasheshi. Kisan da ko ƙaho aka busa sai yajima bai farka ba.( Kai jama'ah kuji fa Wai ko ƙaho aka busa Sai yajima bai farka ba. Allah ya tsare Muna Imanin mu, ya karemu da Biyar son zuciya)

Kwalele yace "Toh mu yanzu ta Ina zamu fara nemansa?"

"Agurin da kuka san kun jefar dashi" aka Basu amsa daga cikin wayar.

"Nawane ladar wannan aikin" Ɗan tsunke ya tambaya?

Ninkin Na farkon, kuma yanzu zahiri muke son muga Kisan ba labari ba.

Jibgege yace "wannan ba matsala bace kudai Kawai kuɗinku su Zama cikin Shiri" saboda aikin bashine matsalar mu ba canji shine matsalar mu.

Bakuda matsala Kawai ku aiwatar da aikinku.............✍️✍️✍️





Nabeela Binji ce💃💃💃







More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏




♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM


PAGE

2️⃣ 6️⃣






___________ Shuru su kayi Dukan su Bayan sun Gama Jin bayanin Dady.


Ya Maleek yace "yanzu ina za'a samu wacce zata aminta ta aure Shi Dady?"

Dady Yace "Nima tunanin da nake Kenan Maleek"

Ya Suhail yace "za'a iya Samu Mana, Ai taimako ne saidai Idan ba'a bincika ba" hararar sa Maleek yayi sannan yace "waye Zai ɗauki Auren ƴar sa ya bawa mahaukaci? Kai yanzu ko cewa akayi ka Nemo Masa Mata zakaje ne? Duk Wanda kaje gurinsa zaiyi tunanin ka Raina masa da wayyo ne saboda kaima kana da ƙanwa budurwa Mai yasa bazaka aura masa ita ba" haka Mutane zasuyi tunani. Kuma kaima kasan hakane.

Sun Jima Suna tattauna matsalar, Kowa ya faɗi Al barkacin bakinsa Amma Banda Shabana da take zaune Kamar gunki ba Abunda yake mosti ajikinta Bayan idanunta da take binsu da su.

Dady yayi gyaran murya yace "ya Isa haka ba cewa nayi kuzo ku cikamin kunne da haniya ba.
Dama shawarar ku nake nema saboda ko da ace ba raina kune masu yanke hukuncin akan rayuwar Shabana.
Kafin nayi wannan maganar daku nayita da ƙanena Alh Umar kuma na fahimci Wasu abubuwa a cikin baya nan sa.
Yayi zaton naje nemawa Ahanaf Auren ƴar sa Nawwara ne. Buɗar bakinsa cewa yayi Ina Shabana halan da Bazan aura mashi ita ba?" Allah ne shaidata ba zuwa nayi na nemawa Ahanaf Auren Nawwara ba.
Zuwa Kawai nayi muyi shawara dashi a matsayin sa na ɗan uwa na. Amma Sai na lura Shi fahimtar da Yamin daban.

Hakan yasa na yanke wata shawara.
Gabaki ɗayansu Ido suka zubawa Dady ba ko kyabtawa Suna So suji wace shawara ce ya yanke.
Murmushi Dady yayi sannan yace "Na yanke shawarar aura wa Ahanaf Auta" What Ya Maleek, Ya Suhail da Hidayat suka faɗa da ƙarfi cikin kiɗimewa.
Ammi ce Kawai batayi irin kiɗimar da sukayi ba Cox ita tariga da tasan zance, Amma Har yanzu tanajin ba daɗi aranta. saboda ba su San komai dangane da rayuwar Wannan Yaron ba, Basu San Kowa nasa ba.
Kuma ta rasa dalilin da yasa takasa buɗe baki ta cewa Dady bata Aminta ba.

Ita ma Shabana haka taji zancen Kamar saukan Aradu, nan take bugun zuciyar ta ya ƙaru, dakyar take iya fizgar numfashi, Tarasa gane a wane kalar yanayi take.

Acikinsu ba wanda ya lura da halinda da Shabana take ciki.

Ya Suhail ne yace "gaskiya Dady bazamu bar haka ta faru ba wannan ai cin zarafine taya zaka dubi yarinya kamar Shabana ƴar Gata Mai tushe da asali ka haɗa ta da mahauka......." Ya Isa haka Suhail Dady ya faɗa cikin tsawa da ƙunar Rai, sannan ya cigaba da cewa ba Kaine ka haifamun Shabana ba. ko mahaifiyarta bata musa wa zance na ba saikai mara kunya Ko?" Ya Maleek zaiyi Magana Dady ya dakatar da Shi ta hanyar ɗaga masa hannun, yace Idan har kuka ga wannan Auren ya fasu Saide Idan Shabanar ce da Kanta tace Bata So ta fasa taimakonsa.
Anan Kam banida Wani Iko Akan wannan lamarin.
Kuma ku Sani Ba'a saurin yanke wa jaraba hukunci Idan tazo ba gudunta ake ba Maida ita Ake jiki a zauna. Dan haka Idan Allah ya kaimu gobe Jummu'a zamu ɗaura wannan Auren da Yar da Allah. Gabaki ɗaya sun ƙara ruɗewa dajin furucin Dady. Maleek Suhail da Hidaya Sai Magana suke ƙasa ƙasa ba Mai jin Abunda suke faɗa.

Kutashi muje masallaci lokacin Sallah yayi Dadi yafaɗa tare da miƙewa tsaye yafita, ba yadda Maleek da Suhail suka iya dole suka bi Bayan Dadyn nasu.

Ita ma Hidaya Tashi tayi ta nufi ɗakin Shabana tana zuba sauri kamar zata tashi Sama.

Parlourn ya rage saura Shabana da Ammi kawai.
Tashi Ammi tayi tare da komawa gurinda Shabana take, ta kama hannayenta ta riƙe tace "kiyi Magana Mana Shabana Idan har baki son wannan hukuncin da Dadyn ku ya yanke kigayamin Sai nayi masa bayani" ita ma Shabana hannayen Ammi ta matse a cikin nata sosai kafin da kyar ta buɗe bakinta tace "ki tayani addu'a da kyakyawan fata Ammi" tana gama faɗar haka ta saki hannayen Ammi tare da tashi tsaye ta nufin hanyar ɗakinta, Tana Tafiya kamar wata ƴar Maye.

Da kallo Ammi ta bita har ta Shiga ɗakinta Sannan ita ma ta tashi tashiga nata ɗakin dan ta gabatar da Sallah kuma ta saka lamarin ƴar Tata a cikin addu'a.


Tura ƙofar Shabana tayi ta Shiga zaune ta tarar da Hidaya Akan Sallaya da alama Sallah tayi.
Direct toilet ta nufa Bata wani Jima ba tafito, Koda ta fito ta tarar Hidaya ta Koma Kan gado sallayar ta hau tare da ɗaukar hijab ɗin da Hidaya tayi Sallah dashi ta saka. Bawan da yace ko ƙala a cikinsu.

Bayan ta idar da Sallah ta sunkuyar da kansa ƙasa tama rasa abunda yake mata daɗi a wannan lokacin.

Tasowa Hidaya tayi ta dawo gaban Shabana ta zauna, tare da ƙure ta da Ido. Cikin sanyin muryar da Shabana batasan Hidaya tana da ita ba, ta Fara Magana "ya kamata ki nutsu kisan abinda kikeyi Shabana, Ina jiye miki faɗawa kogon nadama, karki biyewa zuciyar ki da take So ta kaɗa ki kogon halaka.
Meyasa zaki cutar da kanki ki cutar da Yaran da Zaki Haifa, ki cutar da iyayen ki da mu ƴan uwanki kai da duk ma Wani masoyinki?
Kika Sani koshi mutumen banza ne,
kika San rayuwar da yayi a Baya kafin yasamu taɓuwar hankali?
Wallhi Ina jiye miki tsoron Kar kije ki yankawa rayuwar ki ticket ɗin wahala" Kuka Shabana ta fasa Mai ƙunar Rai.

Cikin kukan tace ya zanyi Hidaya?
Dama Idan ƙaddara tazoma Bawa Yana da gurin guduwa ne?

Ko Kuma yana da Ikon canza ta saboda Kawai Bata masa ba?

Kina tunanin kowa da yake rayuwa a duniya Shine ya tsarama kansa yadda zai rayu?

Ko angaya miki a rayuwa ta na taɓa zaunawa nayi tunanin mahaukaci?

Ina son kisan Wani Abu, ba Wani Bawa da ya Isa ya yanke hukunci Akan abunda Zai faru.

Allah kaɗai yasan abinda ya tsara tun kafin na haɗu da Ahanaf, Bayan na haɗu dashi kuma a gani na farko lamarin sa ya tsaya Mun a zuciya, Idan Bacci nake sai nayi mafarkinsa Idan Ido biyu nake Zan tunashi sau ba adadi.
Tun lamarin Baya damuna har yazo yana hanani sukuni.

Ki gayamin duk ni natsarawa kaina haka?

Ban taɓa SON Ahanaf ba ban taɓa kallonsa Naji Yana burgeni ba.
Saidai nasan Ina matuƙar tausayin sa wannan Kuma tsari ne na ubangiji.

Idan an ɗaura Auren "ya samu lafiya Zan roƙeshi alfarmar Akan ya SAKENI saboda dama ni ba sonsa nake ba" Kuma zanci gaba da kallonsa a matsayin yayana kamar ya Maleek ya Suhail ya Abdul Hameed da ya Abdul Haleel. Shabana ta faɗa tana kallon Hidaya Ido fall kwalla.

Tashi Hidaya tayi ta ɗaura ɗan kwalinta Sannan ta Kalli Shabana tace "kibani Hijab ɗina Zan tafi gida dare yanayi" batare da tayi Magana ba ta cire Hijab ɗin ta bata.

Sai da tagama abunda take ta nufi ƙofa har tabuɗe zata fita ta dakata tare da sa hannunta ta goge hawayen idonta tace "Ina miki fatan Alkhairi ƙanwata Allah yasa wannan auren yazama sanadiyar farin cikin ki na har Abada" tana gama faɗin haka ta fita cikin sauri saboda hawayen da take ƙoƙarin ɓoyewa sun rigada sun zubo.
Allah yagani Bata son wannan auren saboda tana gudarwa ƴar Uwar ta matsala.
Amma kuma bazata iya ja da hukuncin ubangiji ba. Hakan yasa dole saidai ta bita da addu'a kawai.


Murmushin Jin daɗi Shabana tayi Karon farko a rayuwarta taga Hidaya na kuka saboda tausayin halinda da zata Shiga, wannan ma ya isheta Al fahari.


A can masallaci ma Bayan an idar da Sallah Zama Dady yayi ya tasa Maleek da Suhail gaba yana musu wa'azi.
Kuma an ɗan samu cigaba duk da Basu furta da baki ba Amma kana kallonsu Zaka San jikinsu yayi sanyi sosai akan lamarin. Haka kowansu yatafi gida cikin tunanin Wannan Al'amari.


Shabana ce zaune a gaban Dady Kanta a ƙasa Ko dogon motsi batayi.
Dady yace "kinyi Shiru Auta baki ce komai ba kodai bazaki iya taimakonsa bane? Kinga Idan kin fasa abune mai sauƙi sai munemi wata hanyar In Akwai, Idan kuma Babu Sai mu tayashi da addu'a maybe ƙaddarar rayuwar sa ce a haka" Kai Shabana ta girgiza cikin danne kukan da yazo mata tace "Na amince Dady zan aure Shi saboda Bazan Samu sukuni ba Idan har ban taimaki rayuwar Ahanaf ba" taƙarasa maganar tana duƙar da kanta ƙasa.

Ajiyar zuciya Dady yayi yace "Allah yayi miki Allah barka kuma yasa wannan Jahadin da kikayi yazama sanadiyar cetonmu a Ranar gobe ƙiyama" ameen ya Allah

"Tashi kije ki kwanta dare yayi"

Tashi tayi tare da yi ma Dady Saida safe ta tafi ɗakinta.


Tana zuwa ɗaki ta faɗa kan gado tare da fashewa da matsancin kuka Wanda ita da kanta batasan ko na menene ba. Saida tayi mai isar ta sannan ɗauko wayarta ta Kira Hafeeza.
Bayan sun gaisane Shabana ta faɗa mata halin da ake ciki. Ya Ilahi "yanzu kin yarda da Auren ne Shabana?" Hafeeza ta faɗa cikin jimami.
Tohm ya zanyi Hafeeza? Dole ne na yarda saboda nice nafara kawo Ahanaf gida da buƙatar a barni na taimakeshi.
Sai kuma gashi Allah yayi min Babbar jarabawa akan haka ta inda bani da Ikon guduwa Hafeeza Idan nace Bazan aure Shi ba Kenan iƙirarin da nayi a baya ba gaskiya bane? Nidai abunda nake So dake shine kitayani da addu'a Dan Allah. Shabana ta faɗa muryar ta na rawa alamar zatayi kuka.

Runtse ido Hafeeza tayi tare da danne damuwarta tace "ki kwantar da hankalinki Sulty insha Allah ba zakiyi nadama akan wannan lamarin ba, addu'a kuma zanyi miki sosai fatan mu Kawai ubangiji ya karɓa" haka dai Hafeeza tayi ta kwantar wa Shabana da hankali har Saida taji tana Dariya Sannan sukayi sallama.


Da dare ya raba Misalin 2am Shabana ta tashi ta fara miƙa ƙoƙon barar ta agurin Azza'wajallah. Ba ita ta kwanta ba saida tayi Sallar asuba.





Da Misalin 2:10 pm Bayan an idar da Sallar Jummu'a aka fara Shirin ɗaura Auren Ahanaf da Shabana.

Ahanaf Yana zaune gefe ba Abunda yake sai binsu da Ido.

Malam Ibrahim shine ya yabiya Sadaki Naira dubu hamsin, kuma shiya karɓa ma Ahanaf Auren Shabana agurin mahaifinta Alh Usman.


Ana gama ɗaurin Aure Ahanaf ya kwalla wata gigitaciyar ƙara tare da zubewa ƙasa yana dafe kansa, tun yana Shure Shure har ya daina ya saki jikinsa ya daina motsi.........✍️✍️✍️








Nabeela Binji ce💃💃💃







More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏




♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM


PAGE

2️⃣ 7️⃣




____________ Da sauri su kayi Kansa Malam Ibrahim ya ciro wata gora wacce take ɗauke da ruwan rubutu daga cikin Al jihunsa, ya na yayyafasu Akan fuskar Shadow kuma yana ci gaba da karanta addu'a yana tofa masa.
Sun ɗauki tsawon lokaci a haka kafin daga bisani Shadow ya motsa, Amma har yanzu idon sa a rufe suke.
Malam Ibrahim yace Ahanaf Ahanafff, a hankali Shadow yafara buɗe idanunsa ya sauke su Tar Akan fuskar Malam Ibrahim.

Da sauri ya Tashi zaune yana zare idanu kamar zasu faɗo ƙasa yace "Norr Norr Norrrrrrrrr Karki ha'inceni kigaya wa su Abba Ni kike So Wallahi Idan kika Amshi ƙaseem a matsayin miji Saina kasheku Saina kashekuuuuuun" yana gama faɗar haka yasake yin baya ya zube ƙasa sumamme.

Innalilla wa'inna Ilaihi Raju'un ita ce Kalmar da duk wanda yake masallacin ya rinka nanatawa.

Malam Ibrahim ya ƙarayi kansa Yana ci gaba da tofa masa addu'a.

Ba'ajima ba ya ƙara buɗe idanunsa, Amma wannan karon an Samu banbanci saboda farkawarsa keda wuya ya fara furta Kalmar Innalilla wa'inna Ilaihi Raju'un, Yana ja da Baya.

Da sauri Malam Ibrahim ya riƙe masa
hannu yace "kanutsu Ahanaf ka kwantar da hankalika ba Abunda zai sameka da yarda Allah" kallon Mutanen gurin yake da basuda wani yawa Sai kuma yaga kamar a cikin masallaci ne suke.
Mai da kallon sa yayi kan Malam Ibrahim da ya riƙe masa hannunsa cikin rawar murya yace "Suwaye ku? me nayi Muku? Me yasa kuka kawo ni nan?" Murmushi Malam Ibrahim yayi sannan yace "Idan ka kwantar da hankalika duk zakaji amsar waɗan nan tambayoyin naka Insha Allah" Shuru yayi tare da dafe kansa da yake masifar yi masa ciwo kamar Zai Rabe gida biyu. "Kan Yana maka ciwo ne?" Malam Ibrahim ya tambayeshi.
Kansa Kawai ya gyaɗa a hankali batare da yayi Magana ba.
"Bayan Kan ba Wani Abu da yake maka ciwo?"
Kai Shadow ya girgiza alamar Babu.
Murmushi Malam Ibrahim yace "tohm alhmdllh Shima Kan zai daina maka ciwon Insha Allah." Malam Ibrahim ya Maida kallonsa Kan Dady Yace "yanzu Kam ya dawo cikin hankalinsa saidai addu'a da za'a cigaba da masa dan Abun ya ƙara sakin sa sosai"
Murmushi Dady yayi yace Alhmdllh Allah shine Abun godiya, "Allah yasaka maka da mafificin Alkhairi tabbas ba Mai iya biyan ka sai rabbissawati" murmushi Malam Ibrahim yayi sannan yace ai Shi ɗa Na kowa ne Alh Usman, Idan ka kyautatawa ɗan wani saikaga har bayan ranka Allah bazai bar naka ɗan ya tozarta ba. Yanzu dai Abunda ya kamata kutafi dashi gida ni Akwai gurinda zanje yanzu Idan na dawo zanzo na ƙara dubashi in Allah ya yarda.

Dady da kanshi ya tayar da Shadow tsaye tare da cewa "muje gida ka huta Kaji" haka Shadow yabi Dady Kamar laƙumi da akala. Tambayoyi ne da yawa a kwakwalwarsa shidai ko a mafarkinsa bai taɓa cikin Karo da fuskokin da yagani a yanzu ba. Shadow da Dady ne a Baya, Suhail yake driving Sai Maleek da yake gefensa. Kowanne su da tunani Kala Kala a ransa tabbas Suna son suji bayani daga bakin wannan bawan Allah.










____________Ringtone ɗin waya ne ya katse musu hirar da sukeyi ɗaga Kiran akayi tare da cewa "Hallo"

Hhhhhhhhhhhh sukaji sautin Dariya Yana tashi Sai can Mai dariyar ya tsagaita tare da cewa "ƙaryar ku taƙare asirin ku yana dab da tonuwa wannan Yaron ya dawo cikin hankalinsa, kuma duk Wani Asiri da kukayi ya warware kowa zai dawo cikin hankalinsa" Kutumar..............Bazan iya faɗa ba😂😂 "Kai har ka Isa ka fada Muna haka ? Kaine fa kace wannan Yaron bazai taɓa dawowa cikin hankalinsa ba har Abada saboda wannan asirin Yana da wuyar warwarewa" Dariya Boka yaƙara fashewa da ita sannan yace "Nima nayi mamakin ganin yasamu lafiya saboda matakan da za'a bi kafin a rabashi da Wannan a sirin. Abunda yasa na zaɓi nayi masa wannan aikin Shine nasan a wannan zamanin yanada matuƙar wahala a Samu Wanda zai taimakeshi ya rabashi da wannan aikin, Amma Abun mamaki Ashe har yanzu Akwai masu zuciyar Imani" yanzu Abu ɗaya ya rage muku Shine kuyi ƙoƙari ku Hana Shi dawowa gida, Dan muddin ya taka ƙafarsa a cikin gidan mahaifinsa Toh kusani Duk Abunda yasame shi Abaya a kanku zai dawo. Hhhhhhhhhhhh sukaji Kitt ya kashe wayar.


Kallon Juna sukayi cikin matsanancin tashin hankali. "Yanzu Idan su Alh sun dawo cikin hankalinsu ya zamuyi Hajiya?" Nima Shine Babban tashin hankali, "gwara ma Norr da ƙaseem a ƙarƙashin Ikon mu suke dole suyi Abunda muke So Ko Basu So" gaskiya yakamata musan yadda za'ayi mu hanawa Wannan "shigen Yaron dawowa gida saboda da ya dawo tamu ta ƙare" ke Dan Allah rabu dashi ƙarya Kawai yake muna Abunda za'ayi gobe ki shirya mutafi gurin Malam mu damka masa maƙudan kuɗaɗe yasake "haukatar dashi na har Abada" gaskiya haka yakamata muyi Haj Dan Wallahi Ni nafara tsorata da wannan lamarin, "ke nifa matsala ta dake saurin Sare wa, ki kwantar da hankalinkii ba abunda zai faru."











_____________ Abba ne zaune a harabar gidansa yana karatun Jarida, wani haske yaga ya gibta ta gabansa tare da Jin wata ƙara har cikin kwakwalwarsa, zubewa ƙasa yayi ba alamar numfashi a tare dashi.

Daga

Please Login or Register in order to submit comment