Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tashi zaune.
Hana mata tashi yayi ta hanyar riƙeta sosai ajikinsa.
A hankali tace "kabari na tashi kar Haj Mama tazo ta ganmu a haka" ya mutsa fuska yayi yace "Allah ya kawota lafiya, wato beloved dake ake haɗa baki a cutar da Mijinki ko? Kinsa a wane hali nake? Wallahi ina cikin damuwa sosai ki taimawa Mijinki plxx ƴar aljanna" ya ƙarasa maganar cikin marairaice murya.
Murmushi tayi tace "ba haka bane loveline kasani bana son ganinka cikin damuwa but ya zanyi? Kayi haƙuri nayi maka alƙawarin Idan naje kastina bazan jima ba zan dawo" ɗan Jim tayi tace "ni dan kawai Haj Mama ta matsane sai naje Katsina kafin na koma ɗakina, Badan da haka ba ai da saina koma sannan mutafi tare dukanmu" ajiyar zuciya yayi yana kallonta yace "to yanzu wane kalar taimako zakimin Allah ina cikin wani hali beloved" Sajen fuskarsa ta shafa a hankali tare da kai lips ɗinta kusa da nashi tana sakar masa wani lafiyayyen kiss mai rikita lisafi.
Nan take Shadow ya ruɗe mata yana ƙara Janta jikinsa.
Shabana tayi ƙoƙari sosai gurin debewa mijinta kewa duk da iya romance ne sukayi, koda yasamu nutsuwa rungumeta yayi a jikinsa yana saka mata Albarka.
Daidai lokacin Ilham ta fasa kuka dama ita ce mai rigimar. Tashi tayi tsaye tare da saka rigarta ta ɗaukota ta dawo kan gadon ta zauna tana ƙoƙarin shayar da ita.
Tashi yayi ya zauna gefenta yana kallonsa cikin burgewa, shidai yana son yaga uwa tana shayar da yaronta Abun yana masifar burgeshi, kodan sau ɗaya mahaifiyarsa ta sharya dashi ne Oho.
A hankali ya kama ɗayan breast ɗinta tare da kaiwa bakinsa yafara sha, Idonta ta lumshe a hankali cikin kasalalliyar murya tace "Idan ka shanye yaran fa?" tafaɗa tana ture kansa. Ko motsi baiyi ba sai ƙara shige mata yake zatayi magana kenan sai ga Haj Mama ta shigo bakinta ɗauke da sallama, da sauri ya ɗauke kansa jin muryar Haj Mama, Wanda ko Karar buɗe ƙofar basuji ba.
Cikin jin kunya yatashi tsaye ya nufi hanyar fita daga ɗakin, harara Haj Mama ta dinga zuba masa, murmushi kawai yake ko ajikinsa cox yasamu farin ciki daga gurin matarsa.
Yana fita Haj Mama ta Maida hankalinta kan Shabana wace taji muguwar kunya kamar ta kurma ihu.
Gabanta Haj Mama ta ƙarasa tare da bata kofin hannunta tana cewa "Nikadai ce nake Wahala ina nema miki Abunda zakisha kisamu Ruwan Nono Saboda Yaran nan, Ashe ubansu kike bawa yana shanyewa tsabar bakuda tausayi" Ji Shabana tayi kamar ta kurma ihu tsabar kunya.
Duƙawa Haj Mama tayi ta ɗauki Ilham tace "Idan kin gama ki ɗauki ɗayar ki goyata magrib tayi" kai kawai ta gyaɗa batare da tace uffan ba.
Haj Mama na fita ta sauke ajiyar zuciya tare da ɗaukar cup ɗin ta shanye Abunda yake ciki, tashi tayi ta ɗauki Islam ta goya abaya.









Shabana ta tafi Katsina taga gida, Ammi tayi farin ciki sosai ganin yadda ƴar tata tayi kyau, ga yaranta Masha Allah sunyi wayau kuma sun ƙara kyau. Sosai take Kula da ita, kuma tasha gyara sosai gurin Ammi, mommyn Hafeeza da su Hidaya, kwananta huɗu tafara shirin zuwa gida cox tana masifar tausayin Mijinta da halinda yake ciki.

Lokacin da ta dawo gidan su Shadow ta sauka, Sai Bayan magrib tayi wanka Haj Mama ce tayima tawayen wanka, sunyi shirinsu cikin Kaya na Alfarma.

Yana dawowa daga masallaci direct ɓangaren Haj Mama ya nufa, a parlour yaci karo da ita gaidata yayi yana sosai bayan kai kamar wani Shugaban makaryata, murmushi tayi tace "yau dai kam za'a sakar min mara nayi fitsari, Idan na baka Matarka ina ce ba wani bin bashi ko?" Murmushi yayi batare da yayi Magana ba.

Ɗakin ta nufa bakinta ɗauke da sallama,
Amsawa tayi tana sauke waya daga kunnenta tace "Goty Ina zuwa" bata jira cewar Hafeeza ba ta katse Kiran. Tare da gaida Haj Mama.
Murmushi tayi tace "wai mai kike jirane? Ga maƙalallen Mijinki nan yazo ya tare min a parlour" murmushi jin kunya Shabana tayi tace "nazata sai 10 zamu tafi Mama" hararar wasa Haj Mama tayi Mata tace "a Ina zaki kai 10 ɗin? ai Idan kika kai 10 agidan nan bansan Abunda zai faru ba kuma" murmushi tayi.
Haj Mama tayi Mata nasiha sosai mai ratsa jiki.
Sannan aka firar da kayansu aka saka Mota, sukayi sallama suka nufi gida.

Koda suka ƙarasa gidan a parking lot yayi parking, dukansu fita sukayi ta ɗauki Islam Shadow ya ɗauki Ilham. Suka nufi cikin gidan, ɗakin ta suka nufa Wanda yasha gyara sai kamshi ke tashi. Akan gado ya aje Ilham yace "Bari naje na ɗauko kayan" murmushi kawai tayi masa.

Bayan ya kawo kayan ƙara fita yayi.
Zama tayi ta shayar da Yaran Saida ta tabbatar sun ƙoshi, sannan ta ajesu tare da tashi ta shiga toilet tasake sabon wanka, tana fitowa ta shafe jikinta da turaruka masu kamshi, ta ɗauko wata rigar Bacci tsirara tsirara ta saka, hula ta sakawa Kanta a daidai wannan lokacin Shadow ya shigo, wani mayataccen kallo yake mata kamar Yau yafara ganinta.
Murmushi tayi tace "ya da kallo haka? kasan kawai ya gyaɗa batare da yayi Magana ba, dan Idan ma yace maganar zaiyi da Wahala ta fito.
Ɗaukan Islam yayi a hankali yace "ɗauki Ammina mutafi" ba musu ta ɗauketa sukayi hanyar ɗakinsa, suna zuwa suka shinfiɗe Yaran Shadow ne ya shafesu da addu'a tare da juyowa kan Shabana yana mata wani shu'umnin Murmushi.
Matsawa tayi gabansa Tare da rungumeshi ajikinta bakinta takai daidai kunnensa a hankali tace "nayi missing ɗinka loveline" ɗaukarta yayi direct sai kan gado yana faɗa mata wasu kalamai masu sanyaya zuciya.
A Daren ranar sun raya Sunna sosai kuma sun nuna ma Junansu kowa yayi kewar ɗan uwansa. Shabana tasha wuya sosai a gurin Shadow but haka ta daure dan kawai fa farantawa Mijinta rai.

Har Bacci yafara ɗaukar ta Islam ta farka a hankali ta buɗe Idonta sai kan na Shadow, shagwaɓe fuska tayi kamar zatayi kuka.
Murmushi yayi tare da tashi ya ɗauko ta, yana bata ita Ilham ta farka, ya Allah tafaɗa kamar zatayi kuka, ita ma ɗauko ta yayi yazo ya zauna gefenta yana murmushi yace "Menene beloved" kallonsa tayi cikin sanyi murya tace "tambayar menene ma kake? Yanzu dan Allah da wanne zanji loveline dakai ko da yaranka, suma da alama gadon laƙuwa sukayi a gurin mahaifinsu, Allah Idan ana haka da wahala na maida sati" murmushi Shadow yayi yace "ba Abunda zai sameki insha Allah ƴar aljanna, kidaina kiran Mutuwa Idan kika Mutu kika barmu Allah nima Mutuwa zanyi beloved, kece Ni'imar da ubangiji ya bamu nida yarana kece komai namu bana fatar wani abun ya sameki" ajiyar zuciya yayi yace "Wallahi Sona da ƙaunata dake na gaskiya ne beloved, ba wani abu da zaki nema agurina ki rashi komai tsadarsa ko mai wahalar sa zanyi miki shi da yadda Allah, cox kema kin bani kyautar abubuwa da yawa kuma masu tsadar gaske wacce tsadar su tafi ƙarfin koɗi ko wata ƙaddara, I love you from the my Endocardium beloved" yaƙarasa maganar cikin muryar da take nuna tsantsar soyayyarsa gareta.


Murmushi tayi tare da Saka ɗayan hannunta takama nasa tana sakin wani lallausan murmushi tace "Nima ina matuƙar sonka da ƙaunarka loveline, fatana ɗaya Allah yabani ikon yi maka Biyayya Kuma yabani ikon tarbiyantar da yaranka, muradina ɗaya nazama ƴa tagari agurin iyayena Mata tagari agurin Mijina uwa tagari agurin ƴaƴana, Idan haka ta kasance duk wani burin Shabana yagama cika, fatana kazama mai tayani da addu'a da lurar dani Idan nayi ba daidai ba" farin cikin da Shadow yashiga baya misaltuwa nan take yaji wasu hawayen farin ciki na bin fuskarsa. A hankali yace "kinzama kinzama Shabana Allah yayi miki Albarka³ bana fatan abunda zakayi nayi fushi dake cox ba ƙaramin abu bane" murmushi tayi tare da aje Islam ta karɓi Ilham tana shayar da ita bayan ta gamane suka koma suka Kwanta, Shadow yana maƙalƙale da ita kamar wacce za'a kwace masa.
Bakinsa yakai daidai kunnenta yana raɗa mata wasu daddaɗan kalamai masu sanyaya zuciya. Ba Abunda take Sai murmushi!!!!............









Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah


Godiya ta tabbata ga Allah da yabani ikon fara wannan littafin lafiya kuma yasa na kammala shi cikin ƙoshin lafiya.
Ina roƙon Allah Abunda na rubuta daidai ya bani lada, Kuskuren da yake ciki kuma Ina roƙon Allah yagafartafarta min.






Godiya ta musamman gareki Nafeesat Ismail (Oum Ɗaheerah) Allah yasaka miki da mafificin Alkhairi yasanya haske alamurranki.

Jinjina gareki Safna Aliyu Jawabi (SAJ) Allah yaƙara dubun nasara da ɗaukaka.


Bazan manta da kuba cox kune kwarin gwiwata

Haleesa (Ammin Irfan)
Fateemah (Princess)
Salmat jidda
Maman twins
Ameena S Binji
Babyn babynta
Jannat Mrs Yusuf
Fateemah Mukhtar
Hauwa
Fateemah
Nabeela Lawal tsamiya
Oum husna
Raheela
Da sauransu.

Tabbas comments ɗinku shine kwarin gwiwata.

GODIYA TA MUSAMMAN ZUWA GA DUK ƊAUKACIN MASOYAN DUHUN INUWA WA ƳANDA SUKA JURE BIBIYAR WANNAN LABARIN DAGA FARKO HAR ZUWA ƘARSHEN SA.
NAGODE SOSAI ALLAH YABAR ZUMUNCIN.



Taku har kullum Nabeela Shehu Binji 😍😍

Sai Mun haɗu acikin littafina na gaba mai taken ASLEEM💞💞💞 littafine Wanda ya kunshi tsantsar soyayya ƙauna da kuma ban tausayi, kuma Babban Abun burgewar shine true life story ne.
Tabbas farin cikinku shine nawa masoyan gaske. One luv😘😘😘

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment