Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sun san Ayiya ba ita ce mahaifiyar Ahanaf ba, Basu San dalilin da yasa yau ta Karya alƙawarinda ita ce ta ɗauke sa da Kanta ba.

Su kam su Shabana Ido suka zuba Suna kallon ikon Allah, dan sun rasa taya zasu fassara wannan lamarin da Basu San Kansa ba.


Abbu ya kalli Ayiya da Mommy cikin Bada umarni, yace "kuzo ku zauna" ba Wanda ya musa a cikinsu suka zauna kamar yadda ya Basu umarni, saboda Abbu Mutum ne mai kwarjini sosai, komai tsageranci Mutum Idan dai ya kallesa yayi masa Magana Toh zaiyi Abunda yace.


Ba Abunda Norr take Sai kallon Shadow, Shabana ta lura da irin kallon da Norr takewa Shadow, ita ma Hafeeza ta lura tace "kinga jarabbabiyar mata? Da cikinta ta wani ƙure mijin Mutane da Ido, ajiyar zuciya Shabana tayi batare da tace uffan ba.


Abbu ya Kalli Dady yace "Alh kuyi haƙuri Muna son musan Ina kuka haɗu da Ahanaf kuma a cikin wane Hali Kuka tsincesa?"

Gyaran murya Dady yayi cikin nutsuwa yace "Wannan yarinyar ita ce ta fara zuwa Muna da Batun Yaronku" yafaɗa yana nuna Shabana, a lokacin yana cikin taɓuwar hankali, tazo muna da muradinta Naso a taimake masa........................ Nan Dady ya Basu labarin duk Abunda ya faru har izuwa yau da suka zo su haɗu da iyayen Ahanaf"

Tirƙashi Abbu ya faɗa yana goge zufan goshinsa.
Shi Abba Tsabar mamaki kasa furta Kumi yayi.
Hajiya Mama Sai Girmama lamarin ubangiji take.
Haidar da Kamal kuwa su Kalli Shabana su Kalli Shadow.
Ita ma Norr kallon Shabana take, ita kaɗai tasan Abunda takeji aranta

Nan take Ayiya Taji Kamar zuciyarta zata faɗo ƙasa tsabar ɓacin Rai, Kuma Taji ta tsani Shabana fiye da tunanin mai tunani.

Cikin farin ciki Haj Mama ta Kalli Shabana tace "zo nan yarinyar kirki"
Sunkuyar da Kanta ƙasa tayi.
Saida Haj Mama ta sake Magana Sannan Shabana ta Tashi ta nufi gurinda Haj Mama take, Kanta ƙasa har taje gurinta tare da zama a ƙasa.
Murmushi Haj Mama tayi tace "Allah ya saka miki da mafificin Alkhairi, ya baki ladan wannan aikin da kikayi"
A hankali tace "Ameen ya Allah.


Ajiyar zuciya Abbu yayi tare da cewa "bakin mu yayi kaɗan yayi godiyar Alkhairin ku a garemu, a wannan zamanin yanada matuƙar wahala samun masu zuciya irin taku, Allah ya ƙarbi aikin ku yabiya ku da mafificin sakamako" Malam Ibrahim yace "ameen Ai ɗa na kowa ne bare kuma yanzu da wata alaƙa tashiga tsakani Wanda shine ma dalilin zuwan mu nan" Murmushi Abbu yayi yace "Wannan jajircewar taku, Allah ya Saka muku.
Ameen ameen cewar Dady.



Gyara Zama Abbu yayi cikin matsancinyar damuwa yace "banyi tsammanin zuwan wannan Ranar ba Amma kuma Allah ya ƙaddari tazo. Yau Dole ne mu tona Wannan sirri Wanda yayi shekara Ashirin da tara a binne ba Wanda ya sanshi, Sai mu huɗu a iya sanina Kenan, but ita bansan
iya Mutum nawa ta fallasa ma wannan sirrin da ita ce tayi alƙawarin riƙeshi " shuru Palon yayi Kowa Yana son Jin bayani daga bakin Abbu........✍️✍️✍️












Nabeela Binji ce💃💃💃







More comment
More taping 😉😉






Share Fisabilillah 🙏.




♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM



PAGE

4️⃣ 0️⃣












_________________ Abbu yace "Yau zakuji asalin mu, tushen mu da Kuma dalilin Zaman mu Sokoto" Ajiyar zuciya yayi kafin yaci gaba da Magana.
"Mu ƴan asalin Bilisko ne wani kauye a Sokoto garine na Fulani makiyaya, duk da yake ƙaramin gari Amma akwai abubuwa da yawa a ciki na more rayuwa, anan aka haifemu anan muka tashi mukayi karatu har muka kammala secondary school, munyi rayuwa cikin farin ciki kafin rasuwar mahaifin mu Malam Imrana, Bayan rasuwarsa ne muka Fara fuskantar matsalolin rayuwa saboda tun wannan lokacin mahaifiyarmu bata ƙara samun Lafiya ba, haka mukayi ta fama da rayuwa.
A wata Ranar juma'ah da dare Ƴan bindiga suka Shigo Bilisko sukayi sanadiyar tarwatsewar garinmu gabaki ɗaya sun kashe Mutane fiya da tunani sun kora Muna Shanu sun tafi dasu gabaki ɗaya.
Munyi Nasarar kuɓuta daga hannunsu, tare da mahaifiyarmu da kuma wata yarinyar makwabtan mu Khadeeja wacce mahaifinta da mahaifinmu Aminan Juna ne sosai, agurin wannan harin da suka kawo ne sukayi Nasarar kashe iyayenta, ita ma Allah kaɗai neya tsiratar da ita lokacin da sukazo bata gida, Muna gudun ceton rayuwarmu muka haɗu da ita, hakan yasa muka jawota izuwa cikin gari, lokacin da muka shigo Sokoto kusan ƙarfe biyun dare ba musan gurinda zamu dosa ba, bamu San Kowa ba, gurin Wani chemist muka zauna ba Abunda Khadeeja take sai kuka, ita Kuwa mahaifiyarmu tana Kiran Ruwa, gabaki ɗaya Mun ruɗe saboda ganin yadda take sauke numfashi da kyar kuma ba alamar inda zamu Samo mata Ruwa a cikin wannan Daren. Tashi nayi nace Muhammad ya zauna tare dasu zanje na Nemo mata Ruwa, nayi yawo Har nagaji banga alamar Mutane ba duk an rufe gidaje da shaguna, Wani gida na dosa cikin sauri nafara buga gidan aƙalla nakai kusan 10min Ina buga gidan Amma ba'a Buɗe ba, har na juya cikin fitar da tsammani naji ana buɗe ƙofar da sauri na juya wani Mutum nagani, kallona yayi tare da cewa "lafiya kake buga min gida? Nace "dan Allah Alh ka taimaka min da ruwa na ba mahaifiyata ƴan bindiga suka Shiga garinmu da kyar muka tsira" Saida ya kalleni tsab sannan yace "Ina zuwa" rufe gidan yayi ya koma, ya jima kafin ya fito ya bani Ruwan pure water, Kwara biyu. Godiya nayi masa sosai, sannan na koma gurinsu Muhammad, koda naje jikin mahaifiyarmu yayi tsanani sosai har jikinta na rawa.
Ruwan na Buɗe na bata tasha kaɗan tafara tari Tayar da ita nayi zaune na Jinginata da jikina, munayi mata Sannu.
Hannuna ta kama ta haɗa da na Muhammad cikin murya mai rauni tace "Aliyu nabaka Amanar ƙanenka Ina so kazama mahaifiyarsa kazama mahaifinsa, ka zame masa Gata kazame masa GARKUWA, Dan Allah Komai tsanani komai Wahala karka wufantar da lamarin ɗan uwanka, duk Abunda zai faru ka kasance a tare dashi, kariƙe Amana kariƙe Amana Aliyu.
Tana tari ta Maida kallonta kan Muhammad tace "ban yafe maka kayi masa rashin ɗa'a ba, kasani Idan kayima Aliyu biyayya Kamar ni kayiwa, Idan kuma ka bijire masa ni ka bijirema. Ku zauna lafiya ku riƙe sirrin junanku, kuyima junanku uzri" tarine ya sarƙafe mata, tayi Shiru ba Abunda muke Idan ba kuka ba.
Murmushin ƙarfin Hali tayi tare da yafito Khadeeja da hannu, ƙarasa gabanta Khadeeja tayi, a hankali tace "ki riƙe kima da mutuncinki na ƴa mace, kizama Kamila hakan zai saka iyayenki Alfahari dake Dije, ke yarinya ce mai ƙananun shekaru, Karki kashe rayuwar ki abanza Idan kin zama salihar baiwa sai kiga keda kanki kin sake kafa taki zuri'a wacce zakiyi Alfahari da ita.
Kum ki kwantar da hankalinkii Idan iyayenki suna Raye Aliyu zai maidaki gabansu, ɗan Jim tayi sannan tace Idan kuma Allah yayi musu cikawa kibisu da kyakywan addu'a, kuma kiyi Abunda zasuyi Alfahari dake kinji" kai kawai ta gyaɗa hawaye na bin fuskarta. Haka taci gaba dayi muna nasiha Akan rayuwa, muna zaune har aka fara Kiran Sallar asuba, a lokacin jikin mahaifiyarmu ya birkice sosai, tana kwance ajikina Allah ya ɗauki Ranta, munyi kuka matsanancin, Mun Shiga tashin hankalin a garinda ba musan kowa ba kowa baisan mu ba ga gawa a gaban mu, ko Sallar asuba bamuyi ba, muna cikin haka ne sai ga wani mutume yazo gurinmu dawowarsa daga masallaci Kenan.
koda na kalleshi sainaga wannan mutumen ne da yabani ruwa jiya da dare, Ashe Shima ya ganeni, anan yake tambayar mu Abunda yafaru? nafaɗa masa, duƙawa yayi Ya dubata, ba Shakka ta rasu yafaɗa yana kallon mu cikin tausayawa.
Yajima yana yi Mana tambayoyi muna bashi amsa Sannan ya tashi cikin jimami yace "yanzu Abunda za'ayi a fara yi Mata sutura a binneta"
A takaice dai Alh Nura ya zama gata a rayuwar mu ba Abunda baya Muna ya zama tamakar mahaifinmu, munyi zama na mutunci tare dashi da iyalinsa saboda Mutane wa ƴanda suka San kimar ɗan Adam.




Bayan shekara takwas da faruwar haka dukan mu mun kammala karatun digree ɗinmu a Usman ɗan fodiyo University Sokoto, inda muka karanci fanni kasuwanci, Alh Nura ya bamu damar fara kasuwanci a shagunansa da suke centre market Sokoto kuma alhmdllh muna samun cigaba sosai.
A lokacin Alh Nura ya bani Auren ƴarsa Halimatu wacce Yara suke kira da Haj Mama. Mun zauna cikin farin ciki ba Abunda na nema na rasa agurinta. A haka dai har muka shekara ukku da Aure lokacin tana da yaro ɗaya Muhsin kuma tana ɗauke da ciki na biyu. Ariziƙi sai ƙara bunƙasa yake mun samu ci gaba sosai.

Alh Nura ya taso Muhammad gaba da maganar Aure, lokacin da ya sameni da maganar Sai nake tambayar sa wacece yake So? Sai yace shidai indai Khadeeja zata aminta dashi Toh zai Aureta" nayi murna sosai da Jin ƙudurin Muhammad, saboda Khadeeja yarinya ce nutsitsiya kamammiya wace tasan abunda takeyi.

Koda Alh Nura yaji bayanin Muhammad yayi matuƙar farin ciki da haka.
Ita ma Khadeeja tayi na'am da Muhammad a matsayin mijin aurenta, an saka Ranar bikinsu ba Jimawa aka ɗaura Musu Aure, nayi anfani da nasihar mahaifiyarmu gurin yi musu nasiha Suma, Kuma alhmdllh dukan su sun zama Abokanan zama na gari.
Zaman Muhammad da Khadeeja bai taɓa kawo min Karar ta ba.

Bayan Watannin da Aurensu ne tasamu ciki munyi murna sosai da kuma fatan Allah ya sauketa Lafiya.
A Wannan lokacin ne Muhammad yazo min da wata Magana wacce hankalina ya kasa kwanciya da ita kuma nakasa hanasu, ita Khadeeja ce ta haɗu da Shuwa a matsayin ƴar gudun hijra kuma tana da muradin taimakonta ta zauna da ita tamkar ƙanwarta.
dalilin da yasa na kasa hanasu Shine Muma taimakonmu akayi har muka tsayu da ƙafafun mu, Toh Muma yakamata mu taimakawa duk wani mai buƙatar taimako, hakan yasa na barsu suka zauna da Shuwa a matsayin ƙanwar Khadeeja.


Rayuwa taci gaba da Tafiya cikin farin ciki da kwanciyar hankali, kwatsam wata rana Allah ya jarabce mu da rashin Alh Nura da matarsa umma, accident sukayi a hanyar su ta zuwa airport, ba jimawa Allah ya ɗauki ransu.
Munshiga matsancin tashin hankali munyi kuka Kamar ba gobe, Mun ƙara zama cikkakun marayu, misalta ƙuncinda muka Shiga ma ɓata lokaci ne.
Bayan ƴan Watannin cikin Khadeeja ya Shiga Watan haihuwa.
Ranar Assabar Khadeeja ta Tashi da naƙuda, Muhammad yakirani hankali tashe ya faɗamin Abunda yake faruwa, yace Suna asibitin Uduths, koda mukaje tana labour haka muka kasa zama muka kasa tsayi, Bayan ƴan a wanni Dr yafito yace "congratulations Allah ya sauketa Lafiya ta Samu ɗa Namiji" farin cikin da muka Shiga Baya kwatantuwa.
Anan aka bamu damar Shiga mu Gansu. Bayan Mun Shiga ne Muhammad yayi Kan Khadeeja ni kuma na ɗauki jariri, murmushi nayi Ganin kyakywan yaro Mai kama da mahaifiyarsa sak.
Ya jiki nayi mata, ta amsa.
Muhammad ya zauna gefen gado kusa da ita.
Cikin wani irrin rauni takama hannunsa hawaye na bin fuskarta tace "Muhammad ga Amanar ɗana gudan jinina na bar maka, naso ace na rayu dashi nabashi kulawa kamar kowace uwa, Amma abune mai Wahala, Allah kaɗai yasan halinda nake ciki Muhammad dan Allah kariƙe min yarona Amana, Idan kasakashi kukan rashin uwa baka kyauta Mun ba, Ina So ka bashi kular da bazai san raɗaɗin rashin uwa ba. Naji zafi da raɗaɗin maraici, Idan da Hali kar yarona yayi wannan Kukan Dan Allah Muhammad kaɗaukar min alƙawari" tafaɗa hawaye nabin fuskarta. Duk jikinmu yayi sanyi da Jin kalamanta, Nan take hawaye suka Fara bin kumatun Muhammad, cikin dauriya yace "a'a Dan Allah ki daina waɗan nan kalaman insha Allah Ke kika haifi wannan Yaron kuma kece zaki raini abinki" hawaye na bin fuskarta tace "buƙata ta ɗaya agurinka ka kula min da yarona ka riƙe alƙawari dan Allah Muhammad" nan take Muhammad yafara kuka cikin kukan yace "Karki Mutu ki barni Khadeeja Idan kika Mutu Nima Mutuwa zanyi" hannu tasa ta rufe masa baki tace "Idan kamutu wa zai zama gatan ɗanka wa zai Kalla yaji sanyi?" Halimatu tace "Khadeeja ya Isa waya gaya miki Idan Mutum ya haihu mutuwa yakeyi ne? Dan Allah kidaina ɗaga muna hankali kinji" murmushi tayi batare da ta sake Magana ba.
Halima ta karɓi Yaron a hannuna ta Bata tace ta shayar dashi, karɓa Shi tayi tana kallonsa hawaye nabin fuskarta.

Nida Halima muka fita muka barsu a ɗakin, bamu Jima da fitowa ba saiga Muhammad yafito hankalinsa tashe yana tamabyar likita, da sauri mukayi kansa Halima ta ƙarbi Yaron hannunsa, na tambaye shi lafiya? Cikin tashin hankali yace "Khadeeja ba lafiya"
Da sauri muka dubo Dr yashiga zai dubata binsa Muhammad yayi Amma sai Dr ya hanashi Shiga yace "yajira shi a waje"



Mun ɗauki lokaci Muna jiran fitowar Dr Amma shuru.
Muhammad Sai kai kawo yake a ƙofar ɗakin.
fito Dr yayi tare da cewa "mu bishi office" koda mu kaje dukan mu bamu cikin kwanciyar hankali. Bayan Mun zauna ne Dr yafara yi Muna wa'azi, ba abunda zuciyayoyin mu suke sai Halbawa da sauri sauri. Da kyar nayi ƙarfin halin furta Dr mai yake faruwa ne?" cikin sanyi murya yace "kuyi haƙuri Allah yayi Mata rasuwa" Nan take Muhammad ya zube a ƙasa sumamme nashiga tashin hankali sosai nayi kuka kamar raina zai fita, da addu'a da Kumi Muhammad ya dawo cikin hankalinsa.

Anyi Suna aka sakawa Yaron Suna AHANAF, Ahanaf ya kasance sanyi idon Muhammad, Muhammad Yana sonsa tare da Tausayinsa Yaron da yasha Nonon uwa sau ɗaya, yaji ɗumin jikinta sau ɗaya Abun Tausayi ne agurin duk Wani mai Imani. Madara Ake bashi, Muhammad yaƙi Bari Kowa ya shayar da Ahanaf.

A lokacin Shuwa ta ɗauki Ahanaf Kamar ɗan cikinta, ta nuna masa so, tayi masa ko wane Kalan gata da uwa take nunawa ɗanta, dukanmu Mun yarda tana Sonsa kuma tana tausayinsa. Bayan Wata shida da rasuwar Khadeeja, Halima tace "yakamata Muhammad yayi Aure saboda ya samarwa Ahanaf uwa wacce zata riƙesa da Amana, tunda a lokacin ba yadda bamuyi dashi ba akan ya bamu shi mu riƙeshi tare da Muhsin da Nuraddeen Amma fafir yaƙi yace shi dai Abar masa yaronsa zai iya riƙeshi.

Bayan ƴan kwanaki da yin haka Muhammad yazo min da maganar Auren Shuwa, Magana ta gaskiya a lokacin ban tantance mai yakamata nayi ba. na barshi ya Aureta ko kuwa dai na hanashi, ganin ya matsa ya ta yarda hankalinsa na amince da Auren.
Shuwa tayi alƙawarin riƙe Ahanaf da Amana ta ɗauki alƙawarin ma yarda dashi tamkar ɗan cikinta, Kuma Anan tayi Muna alƙawarin bazata taɓa nunawa Ahanaf ba ita ce mahaifiyarsa ba balle kuma har ta furta da bakinta cewa ba ita ta haifesa ba, munyi alƙawarin ɓoye Wannan sirrin ga Ahanaf da ma sauran yaranmu.
Amma bansan dalilin da yasa Shuwa ta zaɓi fallasa wannan sirrin na tsawon shekaru a gaban Mutane ba.

Abbu ya ƙarasa maganar cikin rauni da karewar zuciya.

Duk Wanda yake Palon yaji tausayin rayuwar Ahanaf.
Da Ido Shabana ta Kureshi Ko kyabtawa batayi, abubuwa da yawa sun taro a cikin zuciyarta, tausayin Ahanaf yaƙara linkuwa acikin Ranta, tabbas Ahanaf ya haɗu da jarabawar ubangiji daga zuwansa Duniya, Nan take taji hawaye sun jiƙa Mata fuska.

Zaune Ahanaf yake kamar Wani gunki ba Abunda ke motsi a jikinsa, banbancin sa da matacce kawai numfashi da yake fita daga jikinsa, gabaki ɗaya duniyar juya masa takeyi.

Ƙaseem Kuwa hawaye ne fall idanunsa, wannan wace kalar Rana ce haka? Mai yake Shirin faruwa ne? Shida Ahanaf ba mahaifiyarsu ɗaya ba, Toh mahaififa? Tabbas yana son jin ci gaban wannan labarin.


Ita ma Norr tausayin Ahanaf ya kamata sosai, dama ba Ayiya ce ta haifi Ahanaf ba? Tohm menene duk tushen wannan lamarin da ya faru Ranar ɗaurin Auren ta da Ahanaf?


Haidar da Kamal ma sun ɗanyi mamaki but ba sosai ba, Cox su tun ba yanzu ba suka dasa ayar Tambaya Akan iyayen Ahanaf saboda Abunda ya faru dashi a Ranar ɗaurin Auren sa.

Malam Ibrahim, Dady da Ammi, sun ƙara Jin tausayin Ahanaf sosai, ba Shakka rayuwarsa cike take da ƙalubale.

Ammi a Ranta tace to ko waye yayi masa asirri Kuma menene dalili?.


Tunda aka fara maganar Abba ya sunkuyar da kansa ƙasa cikin ƙunar zuciya da begen Matar sa Abar Alfaharinsa.
Tabbas yakasa ciki alƙawarin Khadeeja, hawaye nabin fuskarsa ya Kara duƙar da kansa ƙasa.


Ayiya Kuwa wani mugun baƙin cikin ne ya kamata, zuciyarta har wani tururi take mata tsabar takaici, a ɗaya ɓangaren kuma fargabar faɗawarta cikin halaka takeyi.


Abbu ya kalleta yace "Shuwa yanzu wannan lamarin ya juyo kanki, menene dalilin kalaman ƙiyayyar da kika furta agurin Ahanaf? Yaronda yake ɗaukarki uwa majinginarsa, meyasa a Maimakon kiyi murnar ganinsa da godewa Allah Sai kikayi abubuwa a kasin haka, me yasa kika ƙarya Al ƙawarinda kika ɗauka?..........✍️✍️✍️














Nabeela Binji ce💃💃💃







More comment
More taping 😉😉






Share Fisabilillah 🙏.




♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM



PAGE

4️⃣ 1️⃣













_____________ Duk Wanda yake Palon ya mai da hankalinsa gurin Ayiya, wace take zaune tana tunanin makomarta da taji ɗazu agurin Malam, saboda yace Idan har Ahanaf ya dawo gida to ita ce zata faɗa halinda yafito, daga zarar ta bari Bacci ya ɗauketa. wannan Shine dalilin da yasa ta kasa control ɗin Kanta a lokacin da tayi Ido huɗu da Shi. Tabbas yanzu tasan bata da mafita Kuma bata da gurin guduwa, Dole ta girbi Abunda ta shuka kuma tafaɗi gaskiyar lamarin.


Zata fara Magana mommy ta harareta,
Shuru tayi sai can tace "Ni bakomi tsakanina da Ahanaf face Alkhairi, kalaman da nayi yanzu kuma suɓutar bakine, Amma Ai dukanku kun shaida ina son Ahanaf kuma na riƙe shi da Amma, dan Shi da Kansa Idan ba yanzu ba bai taɓa sanin Bani na haifishi ba, Toh Menene kuma sai an ƙureni?"

Cikin zafin Rai Haj Mama tace "ƙarya kike Shuwa ke Annamimiyar mata ce mai fuska biyu, baki son Ahanaf, zaman da kikayi dashi dan kawai kina Son mahaifinsa ne yasa kika nuna masa so da Tausayin ƙarya, kuma kina tsoron ƙuntata masa saboda kinsan mahaifinsa bazai lamunta ba, Akan Ahanaf Zai iya rabuwa da kowa, wannan dalilin yasa kika jashi a jikinki kina nuna kina sonsa agaban ubansa, Allah kaɗai ya ƙi dabararki ya ƙaddari Ahanaf rayayye ne yasa ya kawo yanzu.
Duk Abunda kike ina Lura da duk wani motsinki Shuwa, da kunnuwana Naji Abunda kika faɗa Akan Ahanaf, Wanda banyi mamaki ba saboda inajin yadda wannan Abun ya faru ni ke kaɗai nafara zargi,
Sai ga Shi Allah yasa najiki, kuma yanzu ke da kanki kika ƙara tabbatar Mana da Abunda ya faru, duk wanda yake gurin nan yaji kalaman da kikayi Akan Ahanaf, kuma kowa ya fahimci tsantsar ƙiyayyar da kike masa.
A saboda haka ki fito ki faɗa mana gaskiyar Abunda yafaru tun muna shaida juna dani dake, Ahanaf ba iya Amanar Muhammad bane Amanar mijina ne nima Amana tane, Saboda agaban idonmu mahaifiyarsa take jadda da Amanar ɗanta, a saboda haka Mun ɗauka, yanzu ke kaɗai muke saurare"

Cikin ƙufula Ayiya ta Kalli Haj Mama tace "Ai ke dama ba Sona kike ba, tun wancan lokacin duk abunda nayi sai kin ƙalubalan ceni, yanzu mai kike so kice? Da ace Ina da niyar cutar da Ahanaf ai da tun yana jinjiri na cutar dashi ba Wanda yasani" Haj Mama tace "Ai nace Allah ne yaƙi dabararki, kuma dama Allah ya ƙaddari rayayye ne, kinga kuwa Idan ubangiji yace "Kumfa ya kum ba Wanda ya Isa yace lata kun" Shi kainuwa ne bazaki iya kumi dash.... Ya Isa Abbu yafaɗa cikin tsawa, ba wannan cece kucen bane ya taramu anan ba, Sanin gaskiyar Abunda yafaru ne ya taramu.
Maida kallonsa yayi Kan Ayiya yace "Shuwa kinsan wanene Aliyu, Bana Maida kaina akan Abunda bai dameni ba Amma Idan kika ga nasaka Abu a gaba har ya hanani Bacci, tohm ki sanayi sai nayi Nasara akansa. Ki faɗamin gaskiyar Abunda ya faru Idan ba haka ba Wallahi Wallahi zan ɓatar dake, ba Wanda ya Isa yasan inda kike, dama Ina ɗaga miki ƙafa ne Albarkacin ƙaseem, Amma na Lura ke bakisan Abunda nake nufi ba, ki faɗamin me kuke kullawa keda aminiyar ki? Halimatu ta faɗamin abunda taji kuna tattaunawa a tsakinku, ki kace Malam yace "yana Raye kuma wasu Mutane suna ƙoƙarin taimakonsa ya dawo cikin hankalinsa, kuma muddin ya taka ƙafarsa gidan nan duk Abunda kukayi masa zai dawo kanku, kikace zaki iya kashe ko nawa ne dan a kashe miki Shi" gayar zama Abbu yayi ya kalleta cikin Ido yace "Idan muka haɗa kalaman ki da na waƴan Nan bayin Allah da suka tsinci Ahanaf to ba Shakka kumi a bayyane yake kinada hannu a cikin duk Abunda ya faru, Dan haka ki faɗamuna gaskiya tun ban ƙara fusata dake ba Shuwa.

Duk inda hankalinta yake ya Tashi har wani zufa Taji Yana fita a duk sassan jikinta. Tasan wanene Abbu, tasan duk abunda ya faɗa sai yayi shi koda mutuwa ce zata gibta ta gabansa.
Ajiyar zuciya tayi dan tasan yau Ranar tonuwar duk wani a sirinta ne, koda bata faɗi gaskiya ba zata tsinci sakamako cox taji idonta sun Fara yi Mata nauyi alamar tanajin bacci, saboda Malam yace mata baccin wannan asirin zuwa yake ba Bacci ne Kamar ko wanne ba duk yadda kayi bazaka iya Hana kanka yinsa ba.


Cikin raunin muryar ta Fara Magana tace "ba Shakka nice silar faruwa duk abunda ya faru, tun lokacin da na haɗu da Khadeeja taje asibiti nayi bara a gurinta sai ta tambayeni menene dalilin fitowa ta daga gida? Nan na faɗa mata ni ƴar gudun hijra ce ƴan bindinga sun Shiga kauyen mu sun tarwatsa shi, nan take naga tafara hawaye, anan tace nabita gida zata bani muhali da Abinci indai zan riƙe Amana to zata rikeni a matsayin ƙanwarta.

Bayan tazo dani gidanta ne tayiwa mijinta bayani kuma bai Musa Mata ba,
Muna tare da Khadeeja tsawon Watannin 7 Kawai Amma duk da haka na fahimci ita Matar kirki ce kuma ta gari, ko a fuska bata taɓa nunamin komi ba.
Har izuwa lokacin da Allah ya ƙarbi Ranta Bayan haihuwar Ahanaf,
A lokacin ne nafara wani tunanin mai zai Hana na Aure Muhammad na maye gurbin Khadeeja a gurinsa nima naci daula kamar yadda naga tanayi. Lokacin da gama shawara akan haka saina je gurinsa nayi masa bayani akan ya aureni zan riƙe masa Ahanaf Amana, a lokacin Muhammad yayi masifa kamar zai ari baki, yace Shi koda zaiyi aure ba Abunda zaiyi dani, ya faɗi maganganun marasa daɗi a kaina, wa ƴanda suka hanani Bacci.
Ana cikin haka ne Matar abokinsa Alh Mukhtar Ladidi wato mommyn Norr ta zo min da zance mai zai hana na Aure Muhammad na maye gurbin Khadeeja, tinda ina tayi musu Wahala da yaro nima ya kamata ace na samarwa kaina mafita, Anan na faɗa mata yadda mukayi dashi.
Tace bakida hankali an faɗa miki haka kawai zaki tunkareshi da maganar Aure, Taya kike ganin zai karɓe ki wanda ko jimamin mutuwar matarsa bai gama ba" nace "tohm Ni bansan yadda zanyi bane shiyasa" tace zata taimakeni akwai wani malami aikinsa kamar yankan wuƙa yake da munje gurinsa matsalata ta ƙare. Nan take na amince da shawarar ta mukaje gurinsa ya bani garin magani yace Idan nazo na zuba shi a ƙofar ɗakinsa muddin ya takashi to Magana ta ƙare.
Saida na fuskanci ya kusa dawowa daga kasuwa naje ƙofar ɗakinsa na zuba maganin.
Yana zuwa bai kulani ba, ɗansa kawai da yake kwance a gefe ya ɗauka ya tafi ɗakinsa, can ba jimawa ya dawo fuskarsa a sake kamar ba Muhammad ɗinda na sani ba, ya zauna Kan kujerar da take facing ɗina yace Shuwa dama akan maganar da kikayi Ranar nan ce na yanke shawarar zan aureki saboda na gama tunanina kaf ba wacce ta dace ta riƙe min yarona sama da ke.
Murmushin Jin daɗi nayi Anan dai muka ƙarasa Magana dashi yace zaije ya Samu Yayansa suyi Magana.
Bayan sunyi magana ba jimawa aka ɗaura Aurena da Muhammad Bayan na ɗauki alƙawurra da Dama.
Anan

Please Login or Register in order to submit comment