Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kumi Ammi ba kuka nake ba" murmushi Ammi tayi tace " ba gaskiya bane baki Saba min ƙarya ba Shabana shiyasa a duk lokacin da kikayi nakanyi saurin ganewa saidai Kawai na kyaleki, Shin matsalar ki batawa bace?
Ko kuma Akwai abunda ya shafeki Wanda bai shafeni ba?" Ammi ta faɗa tana ƙure Shabana da Ido.

Kusa da Ammi ta matsa tare da ɗaura Kanta bissa ƙafafun Ammi, cikin sanyin murya tace "Ammi mafarki nayi Ahanaf yana kuka yana kiran sunana daga cikin Wani Rami mai Duhu,
Hannunsa ya Bani Yana roƙona Akan nafitar dashi Ina ƙoƙarin kama hannun nasa ne iska mai ƙarfi ta wuce dashi"
Har yanzu Ina Jin ƙarar sautin ihun sa a kunne na Ammi.
Kuma nayita Kiran wayar Dr Fahad Baya ɗauka Hakan yasa naji cewa tabbas Akwai matsala taƙarasa maganar muryar ta na rawa alamar kuka.

Kanta Ammi ta shafa a hankali cikin tattausar murya tace " ki kwantar da hankalinki Insha Allah Bawata mummunan matsala bace.
Ba Lallai bane abunda Kika gani a mafarki ya zama gaskiya ba.

Tashi muje kici Abinci.
Indai Dr Fahad ne Baya kusa maybe Kuma da ya dawo Zai kiraki in Allah ya Yarda.

Badan Ranta yaso ba tabi Bayan Ammi. Bayan tagama cin Abinci ne Ammi ta dinga Janta da fira saboda bata so taga ƴar tata cikin damuwa, tanajin tsoron tashin ciwon ta.
Ammi tana mamakin yadda Shabana tasaka lamarin wannan bawan Allah aranta Harda kuka.
Wacce harakar gabanta kawai ya dameta ba ruwanta da Shiga rayuwar Wani Idan dai ba tsokana zatayi ba.

Suna kitchen ita da Ammi Suna girkin Yamma.
Wayarta da take kan table tafara ringing cikin sauri Shabana ta ɗauki wayar ganin sunan Dr Fahad raɗo raɗo a Kan screen ɗin.

Bayan sun gaisane yake bata haƙuri Saboda Bai samu damar ɗaga wayarta ɗazu ba Suna meeting ne.

Okay ba matsala Dr dama nace "Ahanaf fa Yana lafiya? Kun bashi Abinci Kuwa?

Murmushi Dr yayi yace" yana asibitin su Dr Bilal ni kuma tun ɗazu nadawo asibitin mu"
Amma ina da tabbacin Yana cikin ƙoshin lafiya insha Allah.

Ɗan Jim tayi sannan tace "Dan Allah Dr zaka iya zuwa ka dubamin halinda yake ciki?" Murmushi Dr yayi yace "badamu zanje na ganshi anjima kaɗan" duk halin da Ake ciki Zan kiraki insha Allah.

Murmushi tayi har haƙoranta suka bayyana tace "nagode sosai Dr" bakumi Shabana.
Sallama sukayi ta katse Kiran tana murmushi.
Ido suka haɗa da Ammi wacce take kallonta tun lokacin da tafara wayar. kai taɗan Sosa kamar wata marar gaskiya.
Ko ƙala Ammi bata ce Mata ba taci gaba da aikinta.
Yanzu Shabana ce ke zubawa Ammi fira babu birki,
Saɓanin ɗazu da Ammi ce ƙarfin firar Saida tace eh ko a'a.

Fira suke har suka ƙarasa aikin.
Bayan sungama ne Shabana ta jere Abinci akan dining table tana gamawa ta wuce ɗakinta Dan gabatar da Sallar magrib.

Zaune take Akan Sallaya tana lazimi wayarta ta fara ringing Dr Fahad murmushi tayi ta ɗauki wayar tare da yin sallama.
Amsawa yayi yace Gani a asibitin.
Amma kuma gaskiya Sai kuma yayi shiru.
Amma kuma me Dr Mai yafaru ne?
Ina fatan ba wata matsalar bace Shabana ta faɗa ƙirjinta na Dukan Tara Tara.
Gaskiya matsala ce Babba Saboda.............✍️✍️✍️







Nabeela Binji ce💃💃💃





Nabeelah Shehu Binji

09064314811
Or
09161107610




More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏.



♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM


PAGE

2️⃣ 2️⃣










_____________Gaskiya matsala ce Babba yanzu na samu zuwa "gurinsa Saidai koda naje natarar dashi a sume Baya cikin hankalinsa jikinsa duk rauni kamar Wanda aka daka bakowa a ɗakin shikaɗaine, kuma ba komai a ɗakin Wanda zai daki kansa dashi.
Gaskiya akwai haɗari a rufeshi da Ake shikaɗai a ɗaki Cox watara za'a iya Tarar da ya mutu.

Subhanallah Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un tace "yanzu yana Ina Dr?" Ana dubashi ne Idan angama Zan dawo dashi asibitin mu Amma gaskiya ya kamata Kisan matakin ɗauka Dan yana cutuwa sosai.
Idan Dady yaƙi yarda, ki Bari a sallameshi ya Kama gabansa kawai.
Shabana tace "a'a Dr karka sallameshi Dan Allah Wallahi bazan Samu sukuni ba Idan yatafi, nasan ta yadda Zan shawo Kan Dady ya amince Amma Dan Allah kaci gaba da kulamin dashi Dr" Shabana ya faɗa hawaye nabin kumatun ta.

Dr yace "Ni bansan abunda Zan Masa ba Shabana, tun farko Na faɗa miki matsalar sa bata asibiti bace, nifa Ina tsoron Wani Abu ya sameshi a hannuna gaskiya" kiyi tunanin Abunda zakiyi a Daren nan. Idan ba Dama kibarshi Mana.
Ba shikaɗaine a cikin irin wannan halin ba gasu nan da yawa a gari.
Mafiya ya wansu duk daga baya Abun ya samesu.
kuma Badan Allah Baya Son su bane ya ɗaura Musu saidan hakan yana cikin ƙaddarar rayuwar su.
Kina ganin Kamar taimakonsa kikeyi a haka Wallahi ƙara azabtar dashi kikeyi saboda ba yaso a rufeshi a ɗaki, Idan Kuma ba a rufeshi ba zai iya guduwa a rasa gurinda yake.
Kiyi tunani Akan haka sosai, Idan dai taimakonsa zakiyi kikaisa gurinda za'a masa magani.
Ko kuma ki sakeshi yaci gaba da rayuwar sa kamar da, saboda tafi masa Wannan wahalar.

Iska Shabana ta furzar tare da dafe goshinta da ɗayan hannunta tace "Dan Allah Dr ka taimakeni zan shirya Wani planning ne wanda nasan In dai nayi shi ba Shakka za'a dace insha Allah" okay Ina saurarenki me kike ƙoƙarin shiryawa?
Murmushi tayi sannan tafara yiwa Dr Fahad bayanin abunda ta ƙudurta a Ranta.
Ɗan Jim Dr yayi Yana Nazari kafin yace "Kuma kina ganin Kamar ba za'a Samu matsala ba?" Bawata matsala da za'a Samu insha Allah Dr.
Aikin farkon Nawa ne kuma nasan yadda zanyi Shi cikin tsari.
Okay fatan Nasara Shabana
Murmushi tayi tace "Nagode sosai Yayana angon 6s Jiddah insha Allah, Allah yaƙara sutura" Shima murmushi yayi yace "Ai kin iya fasawa mutum Kai Bayan kin ɗaurasa Akan igiyar ruwa" tsorona ɗaya Kar Dady ya gane.
"Ba Abunda zai gane insha Allah"
Toh Allah ya yadda
Ameen ya Rab
Sallama sukayi ta katse Kiran tana tunanin ta Ina zata ɓullowa Wannan lamarin.







GIDANSU SHADOW






____________Misalin 9:30pm Abbu ne Zaune a Kan kujera Yana Danna wayarsa.

Hajiya Mama ce tashigo ɗakin bakinta ɗauke da sallama.
Amsa sallamar yayi hankalinsa na kan wayarsa.

Zama tayi kusa dashi tace "barka da hutawa"

"Yawwa Haj"

Zamanta taɗan gyara cikin sanyin murya tace "Ina da Magana"

Hankalinsa yamaida Kanta yace "Ina saurarenki"

Ajiyar zuciya tayi sannan tace "A yau naji Abunda yayi masifar tada hankalina a cikin gidan nan Kuma ya ƙara ƙarfafa zargina" da sauri Abbu ya ɗago yana kallonta, cikin zaƙuwa yace "Mai kika ji Haj?"

Nan Hajiya Mama ta faɗa masa duk abunda taji.

Nan take idanun Abbu suka sauya Kala tsantsar ɓacin Rai ya bayyana a cikin su. Ya Kalli Hajiya Mama yace "Dama nayi tunanin haka, kuma naji ajikina wannan dalilin ne Kawai zaisa Muhammad ya aikatawa Ahanaf haka" Kar kuma kinunawa kowa kinji wannan zancen saboda Komai Zai iya faruwa.
Shi makirin mutum a koda yaushe makircinsa ƙara girma yake, Idan kana son kamashi da laifi tohm Bari zakayi sai ka kamashi da Babbar hujja wacce Bashida gurin guduwa.
Amma Idan ka tunkareshi da ƙaramar hujja mara tabbas tohm ba Shakka Sai ya sarƙafeka ya mayar da laifin a kanka karasa hannyar fita, daga nan sai ya canza salon takunsa saboda tuananin ana bibiyarsa.

Kai Haj Mama ta gyaɗa alamar ta fahimci abunda yake nufi.

Abbu yace "Tabbas zan ɗauki matakin da ya dace Amma kafin haka ganin Ahanaf shine gaba da komai agurina, Ina yawan mafarkinsa Kuma inaji ajikina yana raye"...........✍️✍️✍️.





Nabeela Binji ce💃💃💃





Nabeelah Shehu Binji

09064314811
Or
09161107610




More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏




♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM


PAGE

2️⃣ 3️⃣








______________ Abbu ne Zaune a Kan kujera Yana Danna wayarsa,

Sallama Abba yayi tare da shigowa tsakiyar parlourn.

Amsawa Abbu yayi batare da ya Kalli gurinda Abba yake ba.

"Barka da Yamma Yaya ya gajiya?" Abba ya faɗa yana ƙokarin Zama kusa da yayan nasa.

"Lafiya" Shine Kawai abunda Abbu ya faɗa Yana ci gabada da Danna wayarsa.


Abba yana so yayi Magana Amma yayi Shiru saboda ya lura yayan nasa cike yake dashi.

Ɗagowa Abbu yayi ya kalli Abba yace "Akwai wata matsala ne?"


Kai Abba ya gyaɗa Kamar wani ƙaramin yaro.

"Okay ina saurarenka"

A hankali ya fara Magana yace "Ina neman afuwarka Yaya na lura fushi kake dani sosai Akan abunda ba laifina bane"
"Yaya Ahanaf bayajin Magana kuma baya bin umarnina. ɗaya daga cikin taurin kansa ne ma yasa yatafi ya bar gida, Dan Kawai ya nunawa duniya ban Isa dashi ba" da Ido Abbu ya ƙuresa kamar ya Samu hoto, gyara zama Abbu yayi tare da ƙoƙarin danne ɓacin ransa yace "gayamin laifi ɗaya tak Wanda Ahanaf yayi maka?"

"Laifinsa Shine musun da yayi dani ya nuna ban Isa ba" okay Ni Zan iya "tambayar ka" cewar Abbu, eh "Ina saurarenka Yaya" "menene dalilin da yasa Ka ɗaura auren Wannan yarinyar da Al kaseem? Idan kabani kwakwaran dalili anan zan gane Ahanaf ne Bai kyauta ba ko kai" Shiru Abba yayi tare da sunkuyar da kansa ƙasa. "Kai nake saurare fa"
Maganar gaskiya Yaya Bazan ce ga dalilin da yasa na yanke shawara Akan auren Noor da Al kaseem ba, hasalima Sai Ranar ɗaurin Auren naji wannan tunanin yazo min.
kuma dana tuntuɓi mahaifin yarinyar Akan zance Sai yace "Ba matsala da kaseem da Ahanaf ai duka ɗayane agurinmu,
kuma Shima yaji hankalinsa yafi kwanciya da ya bayar da aurenta ga Al kaseem a Maimakon Ahanaf" wannan Shine dalilin da yasa muka ɗaura wannan Auren. Cewar Abba Yana kallon Abbu.
Ajiyar zuciya Abbu yayi, tabbas duk abunda Abba ya faɗa masa shine abunda Alh Mukhtar Salah mahaifin Norr ya faɗa masa, saboda ya nemesa sun tattauna akan maganar.
kuma duk yaji bayaninsu Kala ɗayane. Bawani kwakwaran dalili a bayaninsu Cox duk kamekame ne. Hakan yasa ya ƙara gasgata maganar da Haj Mama ta faɗa masa jiya.

Girgiza kai yayi yace "nasan a Ina matsalar take Muhammad zaka iya Tafiya" Nima zan tashi tsaye domin ɗaukar matakin da ya dace, dama Shi yaƙi ɗan Zan bane. Da Ido Abba ya bishi dan har ga Allah bai fahimci abunda kalaman Abbu suke nufi ba.

"Yaya akwai Wani Abun ne?"

"A'a zaka iya Tafiya"

"Sai da safe"

"Tasbihu alal khair" Abbu ya faɗa Yana bin Abba da kallo har ya bar parlourn ajiyar zuciya yayi tare da cewa Allah ka kawo mana karshen wannan lamarin cikin sauƙi.











_______________"Alh yamakata muje ka Duba jikin yarinyar nan, nifa Ina jin tsoron tashin ciwon ta, kasan halinda take Shiga Idan ciwon ya Tashi Kamar bazata rayu ba Dan Allah kazo muje" Ammi ta faɗa kamar tayi kuka saboda hankali ta ya tashi da ganin yadda ƴar tata ta wayi safiyar yau cikin matsancin ciwo. Dady yace "na Kira Dr Fahad yazo ya ƙara duba ta Idan takama a kaita asibitin gabaki ɗaya sai akaita.
Amma maganar gaskiya bazan yadda da maganar wannan mahaukacin ba" nasani duk Shine yasa take wannan ciwon zata warware ne insha Allah.
Dady ya faɗa yana ƙoƙarin danne tashi damuwar, Allah yasani bawai bayaso yaje yaga Shabana bane a'a kawai baya so yaje ya ganta cikin halinda bazai iya taimakonta ba, saboda bayajin zai iya barinta ta sake Shiga lamarin wannan mahaukacin mai neman ɗaukar Ranta. Duk Abunda take buƙata zai mata Amma Banda wannan Dady ya ƙissima haka Aransa.



BAYAN KWANA BIYU

Abu Wasa Wasa yafara zama gaske Cox da farko Shabana tayi planing ɗin ciwon ne ita da Dr Fahad saboda a tuananin ta shine Kawai mafita. Amma fafir Dady yaƙi yarda da ƙudurinta, gashi yau kusan 5days Kenan bata saka Ahanaf a Ido ba, Dr Fahad Sai ƙorafi yake Mata Akan ta Bari Kawai a sallami Shadow ya tafiyar sa tunda Dady yaƙi ya haƙura.
wa ƴan nan abubuwan ne suka taru suka tsaya Mata Arai Har yayi Sanadiyar tashin ciwon zuciyar ta da gaske.

Jikin nata ya rikice sosai, kana ganinta zaka san tana masifar jin jiki, kuma fafir taƙi bari a kaita asibitin a cewar ta a Barta a gida har kwananta su ƙare.
Baya yadda Ammi batayi da ita ba Amma taƙi taje asibitin.

Wannan dalilin yasa Ammi ta Kira ya Maleek, ya Suhail da Hidaya akan suzo su Saka baki Dadyn su ya haƙura Akai Shabana ta ga Shadow koda sau ɗaya ne.

Su daga farko sun ɗauka Abun wasane da rigima irinta Shabana, Amma ganin halinda take ciki yayi masifar tada hankalinsu, Hidaya har da kuka take gurin roƙon Dady yayi haƙuri yabar Shabana taje gurin mahaukacin kar ta mutu.
Shuru Dady yayi baiyi Magana ba Kamar baiji abunda Hidaya tace ba.

Maleek yace "Dady ka hanata zuwa gurin mahaukacin saboda kar ya kasheta Amma kai kana ƙoƙarin kasheta da kanka" wannan ciwon nata kasani Idan yatashi sai an mata Abunda take so kafin a samu ta dawo hayyacinta.
Nan ma Shiru Dady yayi yana saurarensu Kawai.

Suhail ya Kalle Shi yace "karka shiga hurumin ubangiji Dady bakasan menene hikimar Allah ba da yasa Shabana ta damu da lamarin wannan mahaukacin"
Ba shikaɗaine mahaukaci a wannan garin ba kuma ba shikaɗai ta fara gani a cikin yanayi na hauka ba, Amma ta nace akan zata tallafa masa" kwarin gwiwa yakamata mubata bawai mu Sare mata gwiwa ba Dady.

Yanzu ma baiyi Magana ba saima tashi da yayi tare da ɗaukar glass ɗinsa dayake kan table ya nufi hanyar fita. Da Ido suka bishi har ya ɓacewa ganinsu.

Ajiyar zuciya Ammi tayi tace dama nayi tunanin haka " Na lallaɓashi har nagaji Amma yaƙima furta komai akan zance" Hidaya ta share hawayen fuskar ta tace "Toh haka zatayi ta zama da ciwo ajikinta Ammi? Yakamata ace anyi wani Abun gaskiya" Mai za'a Hidaya ita ma kinsan taurin kaine da ita kamar mahaifinku, tunda tace bazataje asibitin nan ba tohm fa ba yadda za'a ta yarda taje.

Ai basai an jira ta yadda ba Kawai mu ɗauketa mukaita Ko bata so, taya zamu tsaya muna biyewa shashancinta Suhail ya faɗa cikin ɓacin Rai, Cox abunda Dady yayi ya masifar ɓata masa rai.


Harara ya Maleek ya watsa masa yace "tsabar bakasan abunda ya kamata ba ko? Idan ba haka ba wacce take cikin halin jinya Zaka nunawa zafin kai? Idan Dadyn bai kasheta ba Inaga kai zaka kasheta" muje mu rarrasheta muga ko za'a dace ya Maleek ya faɗa yana tashi tsaye ya nufi ɗakin Shabana, gabaki ɗaya mara masa baya sukayi.

Suna Shiga ɗakin suka Tarar da ita tana kuka cikin sauri sukayi Kanta ya Maleek ya zaune gefenta tare da janyota jikinsa cikin muryar rarrashi yace ya Salam "Dan Allah kidaina wannan kukan Shabana kina ƙara tada mana da hankali ne" ya faɗa yana goge mata hawayen fuskar ta.

Hannunsa ta riƙe cikin sautin Kuka tace "Dan Allah Ya Maleek ka taimaka ka kaini naga Ahanaf, wallhi Ji nake Kamar zan Mutu Idan banga Shi ba.
Yaya na Rasa dalilin da yasa na damu da lamarin Ahanaf, naso na Manta dashi Kuma na Manta da lamarin sa dan Kawai na farantawa Dady rai Amma hakan ya gagara, Kullum tausayin sa ƙaruwa yake a zuciyata" ta faɗa tana ƙara sautin Kukanta.

Ya Isa Auta, in sha Allah zakiga Ahanaf nan Bada jimawa ba, munyi Magana da Dady kuma nasan zaiyi Nazari akan Abunda mukace kuma nasan zai amince kiga Ahanaf ɗin, ki kwantar da hankalinki Dady fa naki ne Zai sauko kinji. Cewar ya Maleek yana ɗan bubbuga bayanta alamar rarrashi.


Haka dai sukayi ta bata Baki da kwantar mata da hankali.


Bayan ɗan wani lokaci Yaa Maleek ne yake bawa Shabana Lipton a baki yana so cikin ta yaɗan warware ya bata Abinci taci. Sai sangarta take zuba masa ita a Lallai batajin yunwa shikuma ya nace akan dole Sai taci Abinci Idan tanaso ya kaita gurin Ahanaf. Habawa tajin maganar Ahanaf ta buɗe bakinta yafara bata Lipton Ɗin. Ammi ya Suhail da Hidaya gabaki ɗaya dariya sukayi, ganin yadda Shabana ta buɗe baki Kamar zata cinye kofin.

Suna cikin haka sukaji an turo ƙofa, gabaki ɗayansu ƙofar suka Kalla.

Dady ne yashigo ɗakin fuskar sa ɗauke da murmushi, Dr Fahad ne a Bayan Shi. Gani sukayi ana ƙoƙarin shigowa da Mutum Amma yana faman tokarewa alamar baya so.
Cikin mamaki Shabana ta furta Ahanaf har muryar ta na rawa Tsabar mamaki..........✍️✍️✍️








Nabeela Binji ce💃💃💃





Nabeelah Shehu Binji

09064314811
Or
09161107610




More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏



♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM


PAGE

2️⃣ 4️⃣










________________ Gabaki ɗayansu Ahanaf ɗin suka Kalla, wanda Sai ƙoƙarin kwace kansa yake.
Da gudu Shabana taje gurin Dady tare da faɗawa jikinsa ta rungume Shi, cikin tsantsar farin ciki tace "nagode Dady Allah ubangiji ya biya maka buƙatunka na Alkhairi nagode nagode sosai" murmushi Dady yayi tare da ƙara rungumeta ajikinsa yace "kin fi ƙarfin haka agurina daughter bazan iya jurar ganinki cikin wannan halin ba. Tun jiya nake wannan shawarar araina Amma naƙi aiwatar da hakan ne saboda inajiran Kiran Malam Ibrahim Makama, Dan nayi masa bayani Akan matsalar wannan bawan Allah da kuma yadda Kika damu da lamarinsa, Shine yace nabari "Zai kirani Idan ya gama aikin da yake" tohm Shine fa yakirani Bayan na fita daga gida yace "zaizo anjima da Yamma ya Duba marar lafiyar" shiyasa naje nazo da Ahanaf ɗin kafin Malam Ibrahim ya ƙaraso.


Kowa da yake ɗakin yaji daɗin abunda Dady yayi.
Kuma sunyi mamakin yadda ya sauko da wuri saboda Dady Mutum ne Mai tsatsauran ra'ayi Wanda Idan ya ciza yana da wahala ya busa.

Murmushi Shabana tayi tace "Ina ƙara miƙa godiya ta Dady" Ammi Yaya kutani godiya a gurin Dady plx" ta faɗa tana murmushi.


Suma murmushin sukayi tareda yiwa Dadyn godiya Kamar yadda ta buƙata.



Dady yace yanzu abunda za'ayi Shine "a Kai sa masauki kafin Malam Ibrahim ya ƙaraso"

Ok Dady Amma fa "Kar a kulle Shi plxx saboda za'a iya Tarar da ya daki kansa har yaji ciwo" cewar Dr Fahad yana kallon Shadow dake faman zare idanu kamar Wanda za'ace masa Kyat ya gudu.

Dady yace okay ba matsla ai ba za'a rufesa ba tunda baya so.

Fita dashi Dady yasa akayi daga ɗakin Shabana kafin Malam Ibrahim ya zo.


Bakin Shabana yaƙi rufuwa tsabar farin ciki, Harar Wasa Hidaya tayi mata tace "Wai dama a kan wannan mahaukacin ne kika tashi hankaliki Kuma muma kika tayar Mana da hankali?" Shagwaɓe fuska Shabana tayi tace "haba Hidaya yanzu dan Allah bawan Allah nan bai baki Tausayi ba?" Murmushi Hidaya tayi tace maganar gaskiya yabani Tausayi kuma duk Wani mai cikkaken Imani dole ne yaji tausayin sa, Allah dai yasa sanadiyar wannan taimakon da zakuyi masa ya warke ya Samu lafiya" Wani kayataccen murmushi Shabana tayi tace "ameen ya Allah my Hidayat Ashe dama kina da zuciyar Imani haka?" Shabana ta faɗa cikin sigar zolaya. dukan Wasa Hidaya ta kai mata tare da cewa wai yaushe nafara wasa da kene Shabana? Murmushi Shabana tayi tare da haɗa hannayenta guri ɗaya tace Allah ya huci zuciyar Auntyna matar Khamis Ammin Ƙitwah.
Kai Hidaya ta girgiza dan ta lura Idan ta biye Shabana yau haukata ta zatayi.



Bayan Malam Ibrahim ya zo ne aka kawo masa Shadow.
Da Ido ya ƙuresa Amma Shadow yaƙi yarda su haɗa Ido sai faman sunkuyar da kansa ƙasa yake.

Ajiyar zuciya Malam yayi sannan ya Kalli Dady yace "ya sunansa?" Dady yace Ni gaskiya banma riƙe "sunan nasa ba Amma bari nakira Shabana Muji" Kiran Shabana yayi tare da tambayar ta sunan Shadow, ta gaya masa sauke wayar yayi tare da kallon Malam Ibrahim yace " sunansa Ahanaf" da sauri Shadow ya ɗago Yana kallon Dady.
Malam Ibrahim ya lura da abunda yafaru lokacin da Dady ya an baci sunansa.
Hakan yasa Shima yace "Ahanaf Amma Shadow yaƙi ɗaga idonsa ya Kalli Malam Ibrahim Kamar yadda yayi da Dady ya kirasa. Murmushi Malam Ibrahim yayi ya Kalli Dady yace "baya Magana Ko?" Bansani ba gaskiya Amma nidai sanina dashi Ban taɓa ji yayi Magana ba.

Gyaɗa kai Malam Ibrahim yayi yace ma Dady idan ba damuwa zamuyi Magana.
Ba wata damuwa Malam.


Bayan sun keɓe ne Malam Ibrahim ya fara Magana cikin nutsuwa, yace "gaskiya Akwai matsaloli a cikin rayuwar Wannan Yaron, wannan rashin maganar nashi Aljani ne tare dashi kuma Bayan haka akwai Sihiri ajikinsa" Shiru Dady yayi sannan yace "tohm yanz ya za'ayi Malam?"

Gaskiya matsala ce Babba saboda ban ma san ta Ina Zan fara wannan aikin ba, saidai Kuma mai sauƙine Idan muka tsaya Kan ƙafafunmu da addu'a.


Yanzu ba Abunda zanyi masa sai gobe akwai wani taimakon da zan gwada Masa da dare. Idan Allah yasa mundace Komai Zaiyi sauƙi da yardar Allah.


Ɗan Jim Dady yayi sannan yace tohm Malam Amma Akwai matsala saboda Idan an rufeshi a ɗaki yana Dukan kasansa,. Wani lokacin Har Suma yake Idan ya daku.

Bashi yake Dukan kansa ba, wannan azzalumin aljanin ne na jikinsa kuma shine ya Hana Shi Magana. Idan kuwa hakane saidai kabani Shi natafi dashi gida, a Daren Yau Zan iya gane matsalar sa da yardar Allah.

Shiru Dady yayi kafin daga baya yace "Idan zai Samu lafiya ai ba matsla Malam Ibrahim" Malam Ibrahim yace a'a nifa Bani da tabbacin Zai Sami lafiya nadai ce Maka zanje nayi iya ƙoƙarina da Ilimin da Allah yabani Na sanin makarin sihiri Idan Allah yasa mundace tohm walillahil hamdu Idan kuma hakan bata samu ba tohm fa saidai mu barwa Allah malarinsa.


Okay ba matsala Malam Ibrahim Allah yasa mudace.
Ameen ya Allah tun farko haka zaka ce Alh. murmushi Dady yayi.


Bayan an sha fama da kyar an tafi da Shadow.
Dady ya Kira Shabana ya faɗa mata yadda sukayi da Malam Ibrahim, ya ƙara da cewa yanzu addu'a ce tamu kuma.

Shiru Shabana tayi dan tama rasa Abun cewa, tausayin Shadow ya baibaye ilahirin zuciyar ta, Kuma ta ƙudiri aniyar taimakonsa da kumi nata, Allah ne ya jarabesa.
kuma ya sa mata tausayin sa da ƙudirin taimakonsa, tohm tabbas zatayi Komai Dan ganin ta Ceci rayuwar sa matuƙar ba saɓon Allah bane.

Ita ma Ammi da taji bayanin Dady ta tausayawa Ahanaf sosai kuma tayi ƙudirin taimakonsa ta hanyar addua.


Da dare yayi gabaki ɗaya Shabana Bata suntsa ba yadda taga rana haka tage dare, Sallah Kawai take da karatun Al ƙur'ani. Kuma a kowace Sujada da zatayi addu'arta ɗaya ce shine Allah ya bawa Ahanaf lafiya. A haka har aka kira Sallar asuba Saida tayi Sallah ta nanata buƙatar ta ga ubangiji Sannan ta kwanta, saboda Bacci ne fall idanunta.




Da Misalin 11am zaune take a cikin ɗakinta tana waya da Hafeeza. Ammi ce ta turo ƙofar ta shigo tare da yin sallama.
Amsawa Shabana tayi tana Maida hankalinta akan Ammi duk da cewa Bata katse Kiran ba. "Kizo Dadynki Yana nemanki" Ammi ta faɗa tare da juyawa ta koma Inda ta fito. Wani dam Shabana taji sauke wayar tayi daga kunnenta tace ina zuwa Hafeeza ta katse Kiran.


Bayan taje gurin Dady ne yace "je kishirya kizo muje gidan Malam Ibrahim" Wani kuka taji ƴaƴan hanjinta sunyi a hankali tace Toh Dady, jiki ba ƙwari taje ta zubo ƙaton Hijab dinta ta fito dan batajin akwai wani abinda zata iyayi a halin yanzu.

Sallama sukayi ma Ammi Sannan suka fita, tafe suke cikin Mota ba Wanda yake Magana a cikinsu, saboda Shima Dady yanzu ya masifar damuwa da lamarin Ahanaf, Kamar kar yaji Malam Ibrahim yace Asiri aka masa.

A haka har suka isa gidan Malam Ibrahim ɗin.

Bayan sun gaisane Malam Ibrahim ya Fara Magana cikin nutsuwar sa kamar yadda ya Saba.
Yace dalilin da yasa nace kazo da Shabana Shine cewar da kayi ita ce ta tsin ce Shi kuma take da ƙudurin taimakonsa sa, wannan dalilin yasa Kumi za'ayi Sai da saninta yakamata ayi Shi.
Hakane Allah ya gafarta Malam Dady ya faɗa yana gyara zamansa.

Saɓanin Shabana da takasa cewa uffan ita dai Babbar damuwar ta taji a wane hali Ahanaf ɗin yake.


Malam Ibrahim yace a Daren jiya ban samu na runtsa ba saboda aikin Wannan Yaron, tinda nake ban taɓa cikin Karo da

Please Login or Register in order to submit comment