Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Abu, ke yanzu Dan Allah me kike so kice ne?" Hidaya tace So nake na baki shawara ki riƙe mijinki da kyau Wallahi Ahanaf yanada haƙuri da kawaici, duk Abunda Keke masa yana ɗauke kai bawai Dan bazai iya maganinki bane." Cikin Jin haushi Shabana tace plxx wait, Hidaya da kike cewa na bashi kulawa nayi kaza nayi kaza, kin san a wane mataki muke ne? Kuma kinsan nan gidan da muke zaune ba gidan mu bane? Anan gidan kike son na nuna zaƙewata akansa? Ko kin manta Ammi da Dady Suna gidan ne? Ke duk ki janye Wannan ma Hala anan faɗa miki Shi Ahanaf ɗin Ina Sonsa ne? Ajiyar zuciya tayi Sannan taci gabada da cewa har yanzu na kasa tantance wane matsayi Ahanaf yake dashi agurina. Nidai nasan tun farko Tausayinsa nakeji ba So ba. kuma har yanzu wannan tausayin bai canja ba Hidaya. Badan Dady ya kirani yace "Nabi kumai a hankali ba da yanzu najima da roƙon Ahanaf ya SAKENI." Ido Hidaya ta zare tare da cewa Saki fa Shabana? Anya kina da hankali kuwa? Naji duk Abunda kika faɗa a Baya hakane kuma ba Shakka kin fini gaskiya. Amma Dan Allah kibi shawarar Dady da yace kibi komai a hankali. kuma karki taɓa nuna wa Ahanaf cewar ya sakeki. Kuma maganar so daki ke cewa baki son Ahanaf wannan mai sauƙine, badai kina Jin tausayinsa ba? Toh Komi zaiyi Norma a hankali a hankali Insha Allah. Sannan kisaki jiki dashi, ku saba da Juna hakan zai baki damar fahimatarsa da kyau." Hidaya tafaɗa tana murmushi.
Tsaki Shabana tayi tace "ke bazaki taɓa fahimatar Abunda nake nufi ba Wallahi. Ahanaf fa yafara sauya takonsa, yanzu daga Mun keɓe ba Abunda yake ƙoƙarinyi face ya taɓa jikina. Wallahi yanzu har bana so mu zauna guri ɗaya dashi. A hakan kike faɗar nasaki jikina dashi Idan nasaki jiki dashi mai kike tunanin zai faru?" Baki Hidaya ta saki tana kallon Shabana Sai kuma can ta bushe da dariya. Iya ƙufula Shabana ta ƙufulu Cox ita a rayuwarta ba Abunda ta tsana Kamar a ta sata gaba ana mata ta dariya. Shiru Shabana tayi dan Idan tayi Magana abunda zata faɗa ba mai daɗi ne ba gwara kwai taja bakinta tayi shuru.
Saida Hidaya tayi dariyarta Mai isarta Sannan tace "Allah sarki Auta gaske dai naga kin fara nutsuwa, Ashe dai akwai wata a ƙasa" nan ma banza Shabana tayi mata. Hidaya ta sake cewa "gaskiya Kam yakamata ki kula Idan baso kike musha biki Amarya da tsohon ciki ba" Hidaya ta faɗa tana wata dariyar shaƙiyanci.
Sauka daga kan gadon Shabana tayi tare da cewa "Idan na dawo gidanki kimun Abunda yafi haka" Hidaya ta Danne dariyar ta tace haba babyn Ahanaf Dan Allah ki tsaya muƙarasa firar Mana" fita Shabana tayi batare da ta Kalli Hidaya ba.
Bayanta tabi har Palo tana bata haƙuri Amma fafir Shabana taƙi ta saurareta. Kallon Ahanaf tayi tace "katashi mutafi gida plxx" Ahmad yace "har angama firar kodai anyi faɗa?" Murmushi Ahanaf yayi yace "kijira ayi Sallar Isha Sai mutafi gida Mana" Shabana tace "Bazan jira kona 5mint ba Idan baza kaje ba sai natafi abuna" Ahanaf ya kalli Hidaya yace "haba Aunty Hidaya Dan Allah me kikayiwa Autar Ammi?" Murmushi Hidaya tayi tace nifa ba anuda nayi Mata fira Kawai muke shikenan ta tashi wai zata tafi gida" Shabana ganin zasu ɓata Mata lokaci yasa ta nufi har fita. Da sauri Ahanaf ya tashi tsaye yace "Sai da safenku gwara na tafi Kar laifin Hidaya ya dawo kaina" dariya sukayi Ahmad yace "lallaikam Dan wannan ƴar ta Ammi rigimammiya ce ta ƙarshe." Koda Shadow yaje Shabana ta buɗe mota ta zauna gefen mai zaman Banza. Gefen driver yashiga yaja motar suka ɗauki hanyar gida.










______________ Yauma ƙaseem ya tafi Duba Norr bisa umarni Abbu. Bayan sun gaisane ta tashi zaune tare da jingina jikinta da gado, Sannu ya ƙarayi Mata ta amsa ciki ciki.
Shiru ɗakin yayi babu mai Magana Sai can Norr tace "Dan Allah ƙaseem Ina neman Alfarma agurinka" gayara zamansa yayi yace "Ina jinki" Saida ta sauke ajiyar zuciya sannan tace "Ina So ka taimaka ka rubutamin takardar saki" murmushi takaici ƙaseem yayi Sannan yace "da ace wannan Abun mai sauƙi ne kamar yadda kike ɗauka Wallahi da basai kin roƙe ni takardar sakinki ba Norr.
Baki kaini damuwa da wannan lamarin ba, Abbu ne ya dakatar dani da tuni na sakeki.
Gajeren tsaki tayi Sannan tace "Wallahi ƙaseem ka bani mamaki da ka yarda da Aurena akanka. ka iya cin Amanar ɗan uwanka da kuke uwa ɗaya uba ɗaya meyasa ka aikatawa Ahanaf haka? Norr tafaɗa tana fashewa da matsancin kuka mai matuƙar ban Tausayi. Cike da mamaki ƙaseem yake kallonta, Yace lallai kin bani mamaki Norr, har ni zaki Kalla kice naci Amanar ya Shadow? Naji ni Idan naci Amanarsa ke mai kikayi masa? Ko kina so kice duk Abunda yafaru nine kaiɗai mai laifi? Abunda ya faru dake shine yafaru dani Norr.
Kamar yadda bakisan taya akayi kika yarda Dani a matsayin miji ba, Toh Nima bansan yadda akayi na yarda dake a matsayin Mata ba.
Sannan ke ko alama bazaki gwadamin son ya Shadow ba, saboda Shi ɗan Uwana ne Duk Duniya banida Wani ɗan uwa da yafi min Shi. Ina Sonsa fiye da tunani ba Abunda Bazan iyayi ba Domin farin cikin Shi. Amma da ubangiji ya tashi jarabtani Sai yasa nazama silar ƙuncinsa nazama silar ɓatansa, kuma nazam silar taɓuwar hankalinsa. Nida Bana so naga fushi a fuskarsa, bana So Naga Yana cikin damuwa. Hawaye nabin fuskar ƙaseem yace kigayamin taya kike tunanin da sanina zanci Amanarsa?" Gabaki ɗaya jikin Norr yayi sanyi tuni hawaye suka Fara ambaliya a fuskarta cikin matsancin kuka tace tabbas Allah ne masani Akan Wannan lamarin da kuma masu ƙullashi.
Al ƙaseem Idan kayi nazari sosai Akan wannan Abun zaka ga ƙullalen al'amari ne da aka jima ana ƙullashi, Idan kayi Duba da Abunda yafaru, Dadynmu da Abbanku gabaki ɗaya irin Abunda yafaru damu ne yafaru dasu. Har suka yanke Wannan hukuncin Wanda su da kansu Basu San dalilin yin haka ba.
Har yanzu Dady mamakin wannan Abun yake da kuma yadda akayi ya faru.
Al ƙaseem Idan ka dubi Wannan abun da Idanun basira ba Wanda a kullama Wannan Abun Sai ya Shadow. Hanashi Aurena Shine shirinsu na farko shirinsu na biyu shine haukatar dashi, Sai kuma shirinsu na ƙarshe da suka ɓatar dashi. Idan ka lura wannan Abune da aka zauna aka tsara. Amma babban tashin hankalin Shine waye yayi masa haka? Mai yayi da zafi aka aikata masa wannan mummunan aikin? Duk wannan Allah ne masani Akai.

Ajiyar zuciya ƙaseem yayi yace "ni Babbar damuwa ta ma Shine Allah yasa Ya Shadow yana raye.
Idan yana raye Allah ya karkato hankalinsa ya dawo dashi gida, koda cikin halin haukane.
Idanuwana Suna mararin ganinsa, kunnuwana Suna muradin jin muryarsa, gangar jikina tana kewar rungumarsa.
Ina Ji Kamar ba Wani ƙane a Duniya da ya kaini sa'ar Yaya.
Ya Shadow Yana Jin tausayina, Yana duba lamarina, Yana nuna tsantsar ƙauna da damuwarsa dani.
Wallahi Duk Wanda yake da hannu a cikin lalata rayuwar ɗan Uwana kowaye shi Saina ga bayansa.........✍️✍️✍️







Nabeela Binji ce💃💃💃







More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏.



♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MO



TIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM



PAGE

3️⃣ 5️⃣













_______________ Dawowarsa daga masallaci Kenan yaci Karo da ita zata Shiga kitchen, a hankali yace "Shabanaaaah" juyowa tayi tare da cewa "Na'am" yace "Idan kin kammala Abunda kike kizo zamuyi Magana plxx" ganin fuskarsa ba alamar walwala yasa tace "Toh" dan da alama maganar serious ce.
Saida tagama abunda take kamar yadda yace Sannan ta nufi hanyar ɗakinsa. Tana cikin Tafiya taji Ammi ta kirata juyowa tayi tace "Na'am" Ammi tace "Ina zakije ne?" Wata faɗuwar gaba taji, sunkuyar da Kanta ƙasa tayi. Ammi tace "tambayar ki nake kin min Shiru Sai kace ni sa'ar kice" Kamar zatayi kuka tace "cewa yayi wai naje zamuyi Magana" Ammi tace "Toh idan kun gama maganar kiyi sauri ki koma ɗaki dare ya fara yi" Toh Ammi"
Koda tashiga ɗakin kwance yake Kan gado ƙafafunsa na ƙasa.

Ƙarasawa tayi gabansa taga yana Bacci.
Sai a lokacin ta Samu damar kare masa kallo da kyau, chocolate ne amma very handsome, yana da manyan ido, fuskarsa irin mai natural murmushin nan ce, ga kayataccen Sajen da ya ƙarawa fuskarsa kyau.
A hankali Shadow yafara buɗe idonsa ya ware su tar Kan fuskarta.
Da sauri ta ɗauke kanta kamar bashi take kallo ba. Murmushi yayi tare da tashi zaune. Kallonta yayi yace "Bismillah zauna" zama tayi batare da tayi Magana ba.

Ajiyar zuciya yayi tare da gyara zamansa yana fuskantar ta yace "shawara nake so kibani plxx" shawara kake so kuma daga gareni?" Tafaɗa tana nuna Kanta da yatsa. Kai ya gyaɗa Mata alamar eh.
Ajiyar zuciya tayi Sannan tace "Ina saurarenka." A hankali ya fara Magana cikin nutsuwa, yace "dama Akan maganar tafiya ta gida ne Ina son kafin natafi nafara magana da abokanai na Kamal da Haidar, Naji Suna Ina Domin Ina buƙatar rakkiyarsu. Mekika Gani?"
Murmushi tayi tace "gaskiya kayi tunani mai kyau Ahanaf, yakamata katafi gida ko hankalin iyayenka zai kwanta. Amma Wani hanzari ba gudu ba Idan ka dubi Wannan Abunda ya sameka, zaka fahimci shirya maka Shi akayi. Su waye suka shirya maka? menene dalilin su? Allah kaɗai yasani. Komawarka gida ba Shine matsalar ba, haɗarin da yake tattare da hakan zaka duba. A labarin ka ba Wani Mutum ɗaya a danginka ko Abokanan ka da suke nuna Basu sonka. Kaga kuwa yakamata ayi nazari sosai kafin ka aikata Kumi. Bawai Ina nufin karka Kira abokanna naka bane a'a koda ma ace ka kirasu Ina so ka roƙe su Akan maganar ta tsaya iya Kai dasu, Kar su sanar da iyayenka Abunda yake faruwa, Saidai Kawai suganka kazo Ina tunanin kamar haka zai Samar da salutation" Shabana ta faɗa tana kallonsa.
Wani kayataccen murmushi yayi tare da Jan kumatunta yace "Wow nice idea gaskiya na gode sosai Ashe haka Auta take da baiwa?" Ya ƙarasa maganar cikin sigar zolaya. Hararar Wasa tayi masa tace "da can me kaɗaukeni? Murmushi Shadow yayi "yace ba Komai" tace "da dai kafaɗa" hannu yasa ya dafe bakinsa yace "bakina da taba" Murmushi tayi tace "yanzu yaushe kake ganin zaka kira sun?
Yace "yanzu dai Sai na sayi waya tukkunna, maybe gobe ko Banda goben" kai ta gyaɗa masa tace "ba matsala, Allah ya taimaka yashiga lamarinka yayi Maka katangar tsari da duk masu son ganin bayanka, Allah yasa duk Wani sharri da suka kulla maka Ko suke ƙoƙarin kulla maka ya koma kansu Dan Alfarma fiyayyen halitta" tunda ta fara maganar ya Kureta da Ido ko kyabtawa bayayi, Wani matsancin farin ciki yaji ya rufeshi.
Da sauri ya rungumeta ajikinsa Yana Shafa bayanta. A hankali yace tunda nake a rayuwata ba Wanda ya taɓa min kalar wannan addu'ar, Naji daɗi kuma Nagode Allah yayi Miki Albarka yasaka miki da mafificin Alkhairi. Tabbas kin min Komai a rayuwata ko mai zan miki Bazan iya biyanki ba. Allah yayi Miki Albarka, Allah yayi Miki Albarka" Ahanaf yafaɗa yana ƙara matseta ajikinsa. Lumshe Idanunta tayi tana sauke ajiyar zuciya, a hankali cikin sanyin murya tace "Ameen ya hayyu ya qayyum. Sun Jima a haka kafin daga baya tafara ƙoƙarin janye jikinta daga nasa, tace "sakeni zanje ɗaki" ƙara matseta yayi yace "Yau ɗaya a tayi Bacci mana" Ai da sauri ta Fara ƙoƙarin kwace jikinta.
Dariya yayi tare da sakinta, yace "matsoraciya Kawai" Saida Takai ƙofa tace "Ni ba matsoraciya bace, kai kanka ka..... Yiya yi Kamar zai biyota Ai kuwa nan take ta kwasa da gudu.
Dariya Shadow yayi harda riƙe ciki yace Ƙaryar rashin kunya kike yarinya, da kin tsaya da kinsha mamaki.
A Ranar Shadow ya kwana cikin matsancin farin ciki Wanda tun lokacin da ya dawo hankalinsa bai taɓa Shiga kalarsa ba.





Kamar yadda Shabana ta bashi shawara haka yayi, da zaije office ya tsaya shagon Saida waya, yasayi waya Mai kyau da layi aka masa register.
Saida yaje office ya zauna sannan ya saka Number Haidar a wayarsa wace ya ɗauko ta a Facebook.
Yana gama saka Number yayi Jim yana Jin yadda zuciyarsa ke harbawa da sauri sauri. Sadaukarwa yayi ya Danna kira. saida yayi kira biyu ana ukku aka ɗaga. Assalamu alaikum. runtse ido Shadow yayi ba Shakka wannan muryar Haidar ce, Saida yasake maimaita sallamar Sannan Shadow ya amsa. Da sauri Haidar ya wuntsulo daga kan gadon da yake kwance da ƙarfi yace "Shadoww Hallo Shadow Kaine Dan Allah Kana ina? Dama kana cikin hankalinka? Haidar yafaɗa cikin matsancin ruɗani da son jin amsa daga bakin Shadow." Shadow yace ka saurara Kaji Haidar, nine Kuma Ina cikin ƙoshin lafiya yanzu. Plxx ka nutsu Magana na Kira muyi dakai" to na nutsu faɗamin Ahanaf kana Ina Kuma mai ya sameka? Ya akayi ka dawo cikin hankalinka?" Haidar ya faɗa cikin zaƙuwa. Shadow yace wannan labari ne dogo bazai yiyu a waya ba Haidar Amma Idan ka kwantar da hankalinka zakaji komai insha Allah" alhmdllh alhmdllh Haidar ya faɗa Yana sauke ajiyar zuciya. Murmushi Shadow yayi Allah yasani Yana son Abokanan nashi kamar yadda suke sonshi koma fiye da haka. Yace "Ina So na Koma gida ne Amma nace Bazan aiwatar da haka ba har Saina nemi shawararku. Haidar yace "gaskiya yakamata ka koma gida Ahanaf saboda hankalin kowa ya kwanta, munshiga cikin matsancin tashin hankalin da muka wayi Gari muka nemeka muka rasa." Shadow yace "da kuka nemeni kuka rasa kuma?" Ajiyar zuciya Haidar yayi yace "tabbas kuwa Ahanaf Amma Wannan Maganar bata waya bace Yana da kyau mubarta sai mun haɗu saboda Akwai tambayoyi da yawa araina, kuma akwai kulle kulle da yawa da nake son ganin warwarewar su. Ahanaf kwakwalen mu sun Shiga cikin matsancin DUHU Wanda dawowarka gida ne Kawai Zai bayyana Mana gaskiyar Wannan lamarin, Kuma dawowar ka ce zata yaye DUHUN DA YAYI WA IDANUWAN MU INUWA ya Hana mu ganin haske Akan lamarinka" wasu hawaye Shadow yaji Suna bin kumatunsa masu matuƙar zafi. Wa yake bibiyarsa haka? kuma me yayi da zafi aka masa Wannan mummunan hukuncin?.
Sun ɗauki kusan one hour Suna Magana. Ahanaf ya sake nanatawa Haidar Kar yasanar da kowa wannan maganar Bayan Kamal, Kuma zasu dinga waya Dan sanin yadda tafiyar tasu zata kasance. Da kyar sukayi sallama kamar kar su rabu haka sukeji.

Jinginawa yayi da kujera Yana juyi a hankali idanunsa a lumshe. Wani raɗaɗi yakeji a cikin zuciyarsa.




Bayan two weeks ba Abunda Shadow yake Batare da ya sanar da Shabana ba. Ita kuwa takan tsaya tayi nazari sosai kafin taba Shi shawara Akan Abunda ya dace yayi.
Hakan kuwa ya taimaka Dan ya haifar da Shaƙuwa mai tsanani a tsakaninsu. Kullum Idan ya dawo office Suna tare yana koya Mata zane, kuma yanzu ba laifi tafara iya Zanen duk da bata ƙware ba.

Ammi ta Lura Shaƙuwa Mai tsanani tashiga tsakanin Shabana da Ahanaf, Hakan yasa ta zaunar da Shabana tayi mata Magana cikin hikima, ta nuna Mata Karta kuskura tabari wani Abu yashiga tsakaninta da Ahanaf a gida batare da sun tare ba. Kuma ba wai nace kidaina kulashi bane a'a kici gaba da kulawa dashi yadda ya dace Amma kiyi taka tsantsan kinji" Shabana ta fahimci abunda Ammi take nufi, kuma dama koda Ammi batayi mata Magana ba ita bazata yadda wani Abu yashiga tsakaninsu ba. Saboda ita har yanzu bata masan matsayin Ahanaf aranta ba. Cox bata taɓa Jin Sonsa ba kwata².
Idan ta faɗi haka Hafeeza Saita ƙaryata ta tace "Wallahi tana Son Ahanaf" ita kuwa Shabana taƙi ta yarda.





Yau har karfe Goma na dare Ahanaf bai dawo gida ba. Duk inda hankalinta yake ya tashi, tagama Duk Abunda zatayi tayi Shirin kwanciya Amma Bacci ya gagari idonta. Sai tunanin inda yaje take, aranta tace koma ina yake Allah yasa yana lafiya. Sake sake take aranta har Bacci ɓarawo yayi Nasarar ɗaukar ta.

Cikin bacci taji ana shafa fuskarta a hankali.
A tsorace ta tashi tana rarraba ido Ahanaf ta gani a zaune a gaban gadonta yana dariya. tayi sauri ta ƙara Jan bargo ta lullube jikinta duk da cewa ɗakin da akwai duhu. Tace "Ahanaf me kake yi anan ne? Na shiga uku, ka tashi ka fita, yanzu in Ammi ta shigo ta ganka fa?" Yana dariya ya saka hannu ya kunna bedside lamp. tayi sauri ta kashe, tace "babu kaya fa a jikina dan Allah ka tashi ka fita" ya mike tsaye yace "OK, bara in juya bayana sai ki saka kayan sai in juyo muyi magana" tace "kowacce magana ce ka bari mana sai da safe mayi, dan Allah Ahanaf.
Idan Ammi ta shigo ta ganka a ɗakina cikin dare me kake tunanin zata ce" ya zagaye gadon yaje bakin ƙofa yayi locking ya zare key ɗin yace "problem solved" ta sake cewa "me kake yi a ɗakina?" yace "zuwa nayi inga amaryata" harararsa tayi tace nidai kafita plxx. Yace "Sai na faɗi Abunda ya kawo ni sannan" Hijab ɗinta ta nuna masa ya ɗauko mata ta saka sannan ta fito daga cikin bargon,
Ta zauna bakin gado, ta kunna fitila. Gabanta yazo ya zauna ya harɗe ƙafafuwansa yana kallonta da murmushi a fuskarsa.
Ɓata rai tayi tace, "shine ka kaje kayi zamanka kaƙi ka dawo gida da wuri ko?" yace"ina office wallahi ina zane" da mamaki tace "zanen me kuma cikin dare?" Yace "zanen gidan mu, I made all the plans, " ta saki baki tana kallonsa. Tashi yayi tsaye yayi miƙa yace "yunwa nakeji" Kallonsa tayi batare da tace masa ƙala ba.
Daga tsayen da yake straight ya faɗo kan gado, tayi sauri ta mike tace "Ahanaf menene haka kuma, tashi min daga gado" yace "nace miki yunwa nake ji, ni bani da energy ɗin tsayawa" ya tashi zaune yace "please ki samo min abinci inci, Allah yunwa nake ji" tashi tayi ta ɗauki key ta buɗe ɗakin, tana fita ta sake rufewa da key ta waje. Ta duba kitchen ta zubo masa abincin ta haɗo Masa da fresh milk ta taho. Tana shiga ɗaki taga agogo ya nuna 11:20. Tana shiga ta kuma rufe ƙofar, yana kwance ya miƙe ya zauna ya harɗe ƙafa. ta ajiye masa a gabansa ta koma gefe ta zauna.
Yace "Al bishirinki" cikin ƙosawa tace "goro" "me zaki bani?"
"Me kake so?"
yace "a hug will be very much appreciated" ta harare shi tace "only in your dreams" yana murmushi yace "it happens only in my dreams now, it will happen in reality very soon" ta sauko daga gadon tace "tashi ka fitar min daga ɗaki" ya gyara zamansa yace "da ace zan yi miki wani abu Auta, da tun lokacin da na shigo kina kwance kina ta sharar bacci a lokacin zan miki koma menene. so relax, Ni ba Abunda Zan miki.

Zama tayi a kan bedside tana kallonsa har ya gama cin abincin sa ya tattare kayan. sannan ya koma ya zauna ya ɗauko wata takarda ya warware yace "come let me show you something" zuwa tayi ta zauna ɗan nesa dashi, ya fara nuna Mata wani zane yace "this will be our home, anan zamu rayu muyi raising kids ɗinmu" ya fara Mata bayani dalla2, ta jima da sanin cewa Ahanaf ya kware a aikinsa amma sai yau ta gani in reality, gidan ya tsaru iyakacin tsaruwa, kuma katon gaske ne.
Waya gaya maka zan zauna dakai na dindin din? Ko Na taɓa faɗa maka Ina sonka? tafada a.......✍️✍️✍️









Nabeela Binji ce💃💃💃







More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏.


♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MO



TIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM



PAGE

3️⃣ 6️⃣













________________ A cikin zuciyarta.
Shadow yace "kiyin Shiru baki ce Komai ba, faɗamin ra'ayin ki Akan Zanen" ajiyar zuciya tayi Sannan tace "Zanen yayi kyau sosai" murmushi yayi, yace "Idan akwai abunda bai miki ba ki faɗamin Sai na gyara" murmushi tayi tare da girgiza Kanta alamar Babu Komi. Tashi yayi tsaye, ya naɗe pepper ya Bata yace "ki ajeta a gurinki zan nemeta soon" karɓa tayi. Kallonta yayi yace "ba Wani Abu kawai na tafi?" Kai ta gyaɗa masa. Murmushi yayi yace "Saida safe" a hankali tace "Tasbihu Alal Khair" Yana fita ta rufe ƙofar, ta koma ta kwanta tunani Kala Kala aranta.


Da safe saida ya kammala Shirinsa tsab sannan yafito Palo, anan yaci Karo da Ammi gaidata yayi ta amsa, Sannan tace "kaje Dadyn ku yana nemanka" Toh Ammi" Ahanaf yafaɗa tare da nufar hanyar palon Dady.
Koda yashiga Dady yana zaune Yana kallon News, gaidashi Ahanaf yayi, Dady ya amsa cikin sakin fuska tare da tambayarsa ya Zanen? yace "alhmdllh Dady" Dady yace "yawwa Akwai wani abokina Alh khabeeru yace yana So ka Zana masa gida Mai kyau zai ginawa ɗansa ne. Zan haɗaka dashi kuyi Magana sai yasan lokacin da Zai Samu aikin" Ahanaf yace "ba matsala Dady insha Allah" murmushi Dady yayi yace "sannan maganar tafiyar ka Sokoto kuma, ba kai kaɗai zaka tafi ba, dukan mu zamuje har Ammin taku da Malam Ibrahim insha Allah nan da kwana huɗu masu zuwa zamuyi tafiyar" wata ajiyar zuciya Shadow ya sauke cikin matsancin farin ciki yace "Nagode Dady Allah ya ƙara girma" Ameen Ameen "zaka iya Tafiya, dama maganar da zamuyi Kenan" sallama Ahanaf yayi Masa tare da barin palon.
Direct ɗakin Shabana ya nufa, Shiga yayi tare dayin sallama, hangota yayi can ƙarshen gado ta dunƙule guri ɗaya.
Ƙarasawa yayi gaban gadon tare da tambayarta lafiya take? A hankali tace "zazzaɓi nake ji" subhanallah Ahanaf yafaɗa yana taɓa gefen wuyanta, ji yayi jikin nata da ɗan zafi. Yace tashi muje kiyi breakfast Kisha magani, ya mutsa fuska tayi tace "ka barshi kawai zai daina zuwa anjima insha Allah" Bazan barshi ba taya zaki zauna da ciwo haka ajikinki? Tashi mutafi plxx Ahanaf ya faɗa Yana ƙoƙarin tayar da ita zaune.
Ba yadda ta iya dole ta sauka daga kan gadon, ta ɗauki wayarta suka fito Palo.
Zama tayi kan kujerar dinning tare da saka duka hannuwanta ta dafe Kanta da yake Mata ciwo.
Sai da ya tabbatar ta Karya Sannan yace "Dan Allah Kisha magani kinji" Kai Kawai ta gyaɗa masa.
Ɗaukar wayarta yayi yasaka Number sa ya Kira Saida yaga number tashiga sannan ya ajiye Mata wayarta yace "Zan kiraki anjima naji ya jikin naki" tashi yayi tsaye Ni zan fita Allah ya baki lafiya.
"Ameen Allah yatsare"

Tajima a palon kafin daga baya ta koma ɗaki ta kwanta, Bacci ne ya sake ɗaukarta, cikin baccin taji kamar wayarta Na ringing. A hankali ta buɗe Idonta tare da jawo wayar, Kuma har ta sake katsewa Bata Samu damar ɗauka ba. Tana ƙoƙarin Duba waye yake kiranta, wani Kiran yasake shigowa. Picking tayi tare da karawa a kunnenta, murya Ahanaf taji yana sallama, amsawa tayi a hankali. Yace ya jikin naki da sauƙi?" Alhmdllh tafaɗa tana gyara kwanciyarta. "Allah ya ƙara sauƙi yasa kaffarane" ameen ya Allah.
Yace "Idan dai na dawo naga baki warware ba tofa gaskiya Sai munje asibitin gurin Dr Fahad ya Duba min ke" zan ma warware kafin ka dawo" murmushi yayi yace "Allah ya yadda ai ni shine fatana" sallama sukayi ta katse Kiran.



Wunin Ranar Shadow ya Kira ta ba adadi yana tambayar yajikinta.
Kuma har aranta taji daɗin Ganin yadda Shadow ya damu da lamarinta.



Yanzu ma da Zai dawo gida Saida ya kirata yace "ta faɗi Abunda take so yazo mata dashi" tace "masa ba Abunda take buƙata" yace muddin baki faɗa min Abunda zan kawo miki ba yau saidai na kwana cikin Mota ba zanzo gida ba" Dariya Shabana tayi tace "Toh Duk Abunda yayi maka ka kawo min" yace "naƙi wayaun, Ke da kanki zaki faɗa dai" Kanta ta dafe tace "Wallahi ka cika takura" murmushi yayi yace na daiji duk Abunda zakice kice kafin nazo gidan na sameke" murmushi tayi tace Tohm Naji yanzu dai kazo min da chocolate mai daɗi sosai" yace shikenan abunda kike So? Tace "eh shikenan" murmushi Shadow yayi yace tohm angama ranki yadaɗe" ita ma murmushin tayi. Ya katse Kiran.



Bayan ya fito daga office ne yaje

Please Login or Register in order to submit comment