Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kiyi sangarta son ranki" ɓata fuska Shabana tayi tace "Wallahi Ammi Naji ciwo sosai konewa fa nayi. tafaɗa cikin shagwaɓa.
Tsaki Ammi tayi tace "matsa na wuce kar Na mangaje ki agurin Nan" murmushi tayi tare da zama Kan kujera tafara cin Abinci.
Wayarta ta ɗauka ta fara neman No ɗin Shadow, wace har yanzu batayi saving ɗinta ba, Kiransa tayi taɗan Jima tana ringing kafin ya ɗaga. Cikin sanyin murya tace "kazo kaci Abinci" Shadow yace "plxx ki kawomin ɗaki" Ido ta ware kamar tana gabansa tace "tab gaskiya kafito dai Kaci nikam Ba zanzo ba" yace "saboda mi?" Tace "Idan Ammi ta ganni mai zance Mata?" Murmushin ƙeta yayi yace "kice zakije ɗakin Mijinki ne" Shabana tace "kaje kace wa Ammi ta barni na kai maka abincin ɗakinka, Idan ta Bari ba matsala zanzo" murmushi yayi Dan ya lura Ramawa tayi yace "Ina zuwa."












_____________ Sosai kalaman Haj Mama suka fara tasiri a zuciyar Norr, Allah ya sani bata taɓa Jin son ƙaseem aranta ba ko kaɗan, saiga yadda wannan lamarin ya kasance, tabbas tana jin tausayin Abunda zata Haifa tun baizo Duniya ba, hannunta tasa tana shafa cikinta a hankali Wanda yanzo zai kai 6 months, cikin sanyin murya tace kai ɗin ƙaddarata ne, haka zan haifeka na shayar da kai tamkar kowace uwa, na ɗauki ƙaddara na ɗauki ƙaddara. Tafaɗa hawaye nabin fuskarta.
Ji tayi an turo ƙofar ɗakinta, da sauri ta ɗago kanta ta Kalli ƙofa, Meenal tagani ƴar uwarta kuma ƙawarta.
Da sauri Meenal ta haura kan gadon tare da janyota jikinta ta rungumeta, cikin raunin murya ta Fara Magana tace Mai yasa kika kasa yadda da ƙaddara Norr?
Mai yasa zaki kashe kanki ki kashe Abunda yake cikin ki?
Ke ba baiwar Allah bace?
Allah bai Isa ya jarabce ki bane?
Meyasa kike haka meyasa Norr???

Norr tace "Na yarda da ƙaddarar ubangiji Meenal, nasan wannan Abun duka jarabawa ce.
Amma narasa dalilin da yasa nakasa daina zargin kaina a matsayin mai laifi a cikin wannan Abun" ajiyar zuciya Meenal tayi tace "bakida laifi acikin wannan case ɗin Norr, kisa aranki cewa ƙaddarar wannan cikin na jikinki ne yasa wannan Abun yafaru.
Kafin haka tafaru kina tunanin cewa Idan kinyi ciki ba na Shadow ne?, Sai ubangiji ya juya lamarin yabaki cikin da Wanda baki taɓa tsammani ba, kinga kuwa Idan har kina Son kisamu salama a zuciyarki kibar komai Akan tsarin Allah ne." Sosai Norr ta ƙara samun nutsuwa da maganganun Meenal kuma Taji daɗi Sosai, wunin Ranar tayi Shi bakamar Kullum ba dan kuwa sosai Meenal ta ɗebe mata kewa.


Shima ƙaseem kullum ya kanje ya dubata ya tambaye ta Abunda take So, Sosai yake son cikin jikin Norr Amma Idan yatuna dalilin samuwarsa ya kanji gabaki ɗaya farin cikin ya gushe ya koma tsantsar ƙunar Rai.










______________Dady ya gama Shirin tafiyar su Sokoto dama gobe ne Ranar tafiyar kuma yace Babu fashi da yarda Allah.



Ɓangaren Ahanaf ma Shiri yake but gabaki ɗaya jikinsa yayi sanyi sai faɗuwar gaba yakeji da tsinkewar zuciya, Hakan yasa yadinga nanata Kalmar Innalillahi wa'inna Ilaihi Raju'un.


Shabana ma ta gama Shirinta tsab ta saka duk Abunda take buƙata acikin trolley bag ɗinta.
Suna fira da Hafeeza wacce da ita za'ayi tafiyar Cox Ammi takira Mommyn Hafeeza ta roƙeta tabarta su tafi tare, kuma sunyi Nasara Cox an bar Hafeeza.




10pm zaune suke Kan gado Suna fira ba Abunda sukeyi sai gardama Kamar zasu tayar da ɗakin.
Sallama yayi batare da yashiga ba Cox yasan ba Shabana kaɗai bace a ɗakin.
Da sauri Hafeeza ta ɗauki Hijab ɗin Shabana tasaka, tare da amsa masa sallamar tace shigo.
Cikin mamaki Shabana take kallon Hafeeza ita da take da kayan kirki ajikinta ita ce ta ɗauke mata Hijab tasaka kuma ta bashi umarnin shigowa ba tare da ta Bari ita ma ta nemi hijab ɗin tasaka ba.
Shigowa yayi jiki a sanyaye tare da zama a bedside.
Sauka Hafeeza tayi daga kan gadon tare da cewa Ina zuwa, ta fita.
Tashi Ahanaf yayi ya dawo kan gadon ya zauna kusa da Shabana, tana kallonsa ta kawar da Kanta da sauri saboda Ganin yadda idanunsa sukayi ja kamar Wanda yayi kuka.
Hannayenta ya kama ya jimƙe a cikin nasa ita dai Shiru tayi tana saurarensa ba tare da tayi Magana ba.
Ajiyar zuciya yayi cikin wata kalar murya yace Shabanaaaah, cikin sanyin murya tace "Na'am"
Shiru yayi naɗan lokaci kafin daga bisani yafara Magana a hankali yace "tabbas Ina So naje gida kodan naga iyayena, Allah yasani nayi matuƙar kewarsu, Amma inajin zuciyata tana tsinkewa, inajin faɗuwar gaba inajin ƙunci sosai araina narasa dalilin wannan lamarin Shabana" Shadow yafaɗa hawaye Suna bin kumatunsa. Shabana tace Innalillahi wa'inna Ilaihi Raju'un, da sauri ta janyo Ahanaf a jikinta ta rungumeshi, gabaki ɗaya ta ruɗe ganin hawaye nabin fuskar Shadow, duk jarumtarsa da ƙoƙarin Danne Abunda yake damunsa, Amma Yau yake zubar da hawaye tabbas Akwai matsala.
Nan take ita ma Taji hawaye nabin fuskarta, cikin rawar murya tace "Dan Allah kayi haƙuri Ahanaf insha Allah komi zaizo ƙarshe, and ka kwantar da hankalinka ba Abunda zai faru, kawai kayi addu'a kamiƙa lamarin ka gurin ubangiji, nima zan tayaka da addu'a insha Allah, tafaɗa tana share hawayen idonta.

Ƙara matseta yayi ajikinsa cikin sanyi murya yace "inaji ajikina kamar wani Abu mara kyau yana Shirin faruwa Dani Shabana, banajin wannan Yanayin sai Idan Wata mummunan ƙaddara zata faɗamin, Bazan Manta ba Naji irin wannan Yanayin Ana gobe za'a ɗaura Aurena da Norr, but Sai Na ɗauki Abun ba kumi ba, Ashe wannan Yanayin da naji Yanayi ne da yake nuna nunamin zuwan wata mummunan ƙaddara a rayuwata, Shabana inajin tsoron zuwa gida, saboda nasan duk yadda akayi Wani mummunan Abu zai faru Wanda zaiyi matuƙar girgiza rayuwata" a hankali ta janye shi daga jikinta cikin sanyin murya tace "ka kwantar da hankalinka Ina tare da Kai a ko Ina kashiga Ahanaf, Sannan wannan tafiyar tare zamuyita, kuma nayi maka alƙawarin zan baka duk wata gudunmuwa da kake buƙata. Ahanaf kasani koda duk duniya ce zasu wufantar da lamarinka Toh Ni Shabana Ina tare dakai, Zan tsaya a bayanka na baka kwarin gwiwa. Allah ne ya haɗamu a lokacin da banyi zato ko tsammani ba, Bayan haka ya ƙaddara Al'amari mai Girma a tsakaninmu, Wanda Allah yanagani duk wannan Abun danayi dansa nayi saboda shine yaɗauki lamarin ka yasa araina, Nida kaina wasu lokutan mamaki nake Akan wannan lamarin, Amma Sai nabar kumi a matsayin ƙaddarar rayuwata ce tazo da haka, kuma bansan abunda zai faru a gaba ba, saidai Ina fatan komai zaije yadawo yazama Alkhairi ne a rayuwata.
Tohm kaima haka yakamata kayi ka fawwalawa Allah Kumi naka Ahanaf ina da yaƙinin bazaka tozarta ba Bi'izinillahi Rabi, kuma kasaka aranka Koda Wani Abun ne ya sameka Toh dama can haka Allah ya nufa, Idan kayi Imani da haka zakaga kumi yana tafiyar maka cikin sauƙi insha Allah" tunda tafara Magana ya Kureta da Ido ko kyabtawa bayayi, mamakin hankali da nutsuwar Shabana yakeyi, yarinya ƙarama da irin wannan nazarin? A hankali yace gifted Allah yayi miki Albarka, tabbas nazarinki ya girmi shekarunki, Wannan jarabawar da ubangiji yamin tazama Alkhairi a gareni dan ita ce silar haɗuwata da Mace ta gari, mai hikimar magana, duk damuwar da nazo da ita gurinki kina iya ƙoƙarinki gurin gusar min da ita, Shukkuran laki Mar'atus_Saliha" Shadow ya faɗa yana Murmushi.
Kanta ta sunkuyar ƙasa tana murmushi.
Sauka yayi daga kan gadon yana gyara zaman Jallabiyarsa, yace "Bari na barki haka ki kwanta kiyi Bacci, cox kinsan Tafiyar safe zamuyi gobe" murmushi tayi tare da cewa Allah ya tashemu lafiya, plxxx Idan ka Tashi Sallah ka kirani, maganin Mura nasha da wuya natashi da dare" murmushi Shadow yayi yace" bakida matsala Autar Ammi" Hararar wasa tayi masa tace "Sannu ɗan fari" yace Lallaima yarinyar nan wato Ramawa kikayi ko? Kai taɗaga masa, "zan kama kine" yafaɗa yana fita daga ɗakin.

Yana fita Palo ya ga Hafeeza Zaune tana Danna wayarta, shi har ga Allah ya Manta da ita, murmushi yayi yace "Afuwan ranki yadaɗe Ina fatan Dai ban ɓata miki rai ba?" Murmushi Hafeeza tayi tace "laaaaah Wallahi ba Kumi Ahanaf" Saida safe yayi Mata sannan ya nufi hanyar ɗakinsa.
Tashii Hafeeza tayi ta koma ɗaki Koda taje Shabana bata ɗakin, zama tayi bakin gado tace to ita kuma Wannan Ina tashiga ne haka? Tana nan zaune saiga Shabana tafito daga toilet, kallonta tayi sama da ƙasa ta bushe da dariya, Banza Shabana tayi mata dan ta lura yau iskancin Hafeeza ya motsa.

Gado ta hau tayi kwanciyarta batare da tabi takan Hafeeza ba da take zubama mata tsiya. Hafeeza ganin Shabana ta Shareta ne yasa ta fara Shirin kwanciya ita ma, Bayan tagama ne ta hauro kan gadon ta kwanta. Kallon Shabana tayi taga ta rufe idanunta kamar mai Bacci, cikin sigar zolaya Hafeeza tace nifa nazata ɗakinsa zaki bishi ku kwana ni kibar min nan na kwanta nayi Son Raina" batare da ta buɗe Idonta ba tace Idan haka kike so kizo ki ɗaukeni ki kaini ɗin" Hafeeza tace ni kuma a Wa? Da kika saba zuwa ɗakin nasa ni nake kaiki ne? Tsaki Shabana tayi tace "Wallahi Allah yayi Miki magananin gulma Gotty" haka suka ci gaba da faɗa har Bacci yayi awon gaba dasu.






We Kira Kamal, yace "masa ya Shirin Tafiya?" Kamal yace "ai mun riga da mun gama shirinmu gobe Kawai muke fatan gani, Idan mun Samu yadda muke so muriga ku kaiwa Sokoto, Idan munje zamu nuna musu Kawai munzo Gaidasu ne kamar yadda muka saba, kaga koda Bayan 1haur ne sai ku kuzo, ko ya kagani?" Murmushi Shadow yayi yace eh hakan ma yayi dama dai idan kun tashi da wuri dole zaku rigamu Isa" Bayan sun Gama tattaunawar ne sukayi sallama.
Shadow yakira Haidar, duk Abunda Kamal yace shine Haidar yasake nanata masa. Murmushi Shadow yayi yace "nagode sosai Allah yabiya ku ladan abubuwan da kuke min dan Allah yasani banida Abun saka muku, nidai fatana kawai Allah ya bani damar zama ɗan halak Wanda Baya Manta halaccinku a gareni" Haidar yace Shadow ko wani ne haka ta sama zamu tsaya masa kai da fata, balle kuma kai da muka zama ƴan uwan Juna" godiya sosai Shadow yayiwa Haidar sannan sukayi sallama kamar kar su rabu haka sukeji.





Bayan sunyi Sallah Asuba ne suka fara Shirin Tafiya, Saida suka gama shirinsu tsab suka fito Palo, suka Karya, Shadow da Shabana basu Wani ci Abun kirki ba, dukansu fargaba ce fall zuciyoyinsu.

Bayan sun kammala cin Abinci ne ba ɓata lokaci suka Shiga Mota suka ɗauki hanyar gidan Malam Ibrahim, koda sukaje shima ya shirya mota yashiga suka ɗauki hanyar Sokoto.

Koda Shadow yakira su Haidar su kace masa su kam Ai sun Jima da Tashi, yanzu haka suna hanya, tafan Alkhairi sukayiwa Juna Sannan sukayi sallama.



Tafiya suke ba kama hannu yaro, Tafiya tana Nisa fargaba da tsinkewar zuciyar Ahanaf suna ƙaruwa.


Sun kwashe a wanni Suna Tafiya, tun Hafeeza da Shabana Suna fira har sukaja bakinsu su kayi Shuru.

Ahanaf kuwa tinda su ka gama waya da su Haidar bai ƙara Magana ba, Sai Idan Dady yayi Magana Sannan ya bashi amsa shikaɗai yasan Abunda yakeji a cikin ransa.

Wayar Shadow tayi ƙara ɗagawa yayi tare dayin sallama.
Haidar yace "gamu a ƙofar gida zamu Shiga" ajiyar zuciya Shadow yayi yace "Muma Ina tunanin nan da awa ɗaya da mintina zasu ƙaraso cikin Garin Sokoto" Tohm Allah ya kawoku lafiya. Ameen ya Allah.

Su Haidar sun gama waya da Shadow Kenan za su Shiga gidan sukaci Karo da Ayiya, tafito da gudu Kamar zata kwashe su da Mota, ganin su Haidar yasa ta tsaya, cikin mamaki take kallonsu, gaidata sukayi ta amsa tace "yanzu kuke tafe?" Kamal yace "Eh yanzu muka shigo" Ayiya tace "Allah yasa dai lafiya" Haidar yace "Lafiya ƙalau Ayiya" ɗan Jim tayi tace "Kodai an Samu Wani labarin ne dangane da yarona kuke ɓoye min?" Haidar ne ya sake bata amsa yace "ba Wani labarin da muka samu dan gane da Ahanaf, Kawai dai mun zo ne mugaida ku" Shiru Ayiya tayi sannan tace"to kushiga ciki ku huta Haj tana ciki, ni yanzu akwai gurinda zanje, Idan na dawo Sai mu ƙara gaisawa" su kace to Allah ya tsare"
Koda suka Shiga gidan sun Samu tarbar mutunci agurin Haj Mama.
Abbu yayi farin cikin ganinsu sosai, yace "Yau natashi inajin wani Yanayi na musamman Ashe Yarana ne suke tafe" murmushi sukayi su kace Wallahi kuwa Abbu.
Suna cikin fira Abba ya shigo gaidashi sukayi, ya amsa cikin sakin fuska tare da tambayarsu ya iyayensu? Sunyi mamakin ganin yadda Abba ya sakar musu fuska suka gaisa.

Cikin sanyin murya Abba yace "kuyi haƙuri da abubuwan da suka faru, Allah ne shaida bansan yadda akayi nayi muku wulaƙanci ba" Haidar yace "Babu Kumi Abba Wallahi mu dama bamu riƙe ka arai ba" murmushi Abba yayi yace "Nagode sosai Allah yayi muku Albarka" ameen ya Allah.
Abba yace "kunga dai har yanzu abokin naku shuru ba wani labari?" Kamal yace lamarin Saidai addu'a Abba insha Allah duk inda Ahanaf yake indai yana Raye zai dawowa gida" ajiyar zuciya Abba yayi yace "Allah ya bayyana muna Shi" ameen ameen suka amsa.




Suna shigowa Sokoto hankali Ahanaf yaƙara tashi jikinsa har rawa yake, duk wanda yake cikin Motar ya gama lura da halinda Ahanaf ya Shiga.
Malam Ibrahim yace "kayi addu'a Ahanaf, kadinga furta Innalillahi wa'inna Ilaihi Raju'un" kai Ahanaf ya gyaɗa batare da yayi Magana ba.
Driver yace "Ina zamu bi yanzu mun riga mun shigo gari" Dady Yace "Ahanaf ka nuna masa hanya" haka Shadow yafara nuna Masa hanya har suka iso Minannata har ƙofar gidan Shadow yanuna ma driver Suna tsayawa Shadow yadafe kansa Yana.............✍️✍️✍️











Nabeela Binji ce💃💃💃







More comment
More taping 😉😉






Share Fisabilillah 🙏.


♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM



PAGE

3️⃣ 9️⃣















______________Jiyayi kansa na juyawa masa, a hankali ya buɗe Motar yafito waje, Saida ya ƙarema layin nasu kallo Tass Sannan yace "Dady nan ne gidan" yafaɗa yana nuna gidan nasu. Fitowa sukayi dukansu, cikin ƙasa da murya Hafeeza tace Wow wannan gidan ba dai tsaruwa ba.
Dady yace "to kayi mana jagora Ahanaf" gaba yayi suka bishi a Baya har bakin Gate, a hankali yafara Kwankwasa gidan, ba ɓata lokaci aka buɗe.
Da sauri Muntari mai Gadi yaja Baya yana kallon Shadow cike da matsanancin mamaki, cikin rawar murya yace "oga Shadow, kai nake Gani ko kuwa mafarki nake?" Murmushin ƙarfin hali Shadow yayi ya Maida kallonsa gurinsu Dady Yace "Bismillah Dady kushiga " dukansu Shiga sukayi, Masha Allah Shabana ta faɗa Cox tsarin gidan ya Burge ta sosai.
Wani Jiri Jiri Ahanaf yafara Ji Amma ya Danne yana karanto addu'o'i a cikin Ransa, kuzo muje yafaɗa yana nufar part ɗin Ayiya.
Al ƙaseem Wanda yafito daga part ɗin su Haj Mama zaije na Ayiya, wata muguwar faɗuwar gaba yaji cikin firgici da Al ajabi da ƙarfi yace "ya Shadowwwwww" da sauri Shadow ya kalli gefenda yaji an kirashi, Ido huɗu sukayi da kaseem, anan ƙaseem ya ƙara tabbatar da lallai Yayansa ne. Da gudu ya ƙaraso gurinda yake tare da rungumeshi sosai kamar zai shige cikin jikinsa, Shima Shadow rungume ƙanen nasa yayi sosai, Yaya Kaine da gaske Kaine ba mafarki nake ba? Yaya Ina kashiga ka Manta damu, Yaya meyasa katafi kabar ƙanenka? Bayan kasan bana jure rashinka" Kaseem yafaɗa hawaye nabin fuskarsa. Shima Shadow tuni idonsa suka sauya Kala, ɗago kaseem yayi yace "gani nadawo kaseem, ya isa kadaina kukan Idan ba so kake nima nayi ba" Shadow yafaɗa Yana sharewa ƙaseem hawaye.
Su Shabana Sai kallonsu suke, Hafeeza tace wannan ne ƙanen nasa Kenan? Shabana tace "da alama" su dai su Ammi Shiru sukayi suna mamakin Ikon Allah. Shadow yace "Ina Ayiyata?" Kaseem yace "ta fita Amma Haj Mama na nan da Abbu da kuma Abokanan ka" Shadow yace "mushiga ciki kusamu kuhuta" Tafiya suke kaseem Baya so ko iska yashiga tsakaninsu da yayan nasa.
Palon suka Shiga tare dayin sallama, Abbu, Abba, Haj Mama gabaki ɗayansu tsaye suka mike, cikin matsancin mamaki Abba yace "Ahanafffffff" ƙarasowa yayi tsakiyar parlourn yace "su Dady su zauna" zama sukayi tare da gaida su Abbu, cikin matsancin farin ciki Abbu ya amsa tare da yi musu Sannu da zuwa.
Da sauri Abba yazo ya rungume ɗan nasa gudan jininsa Abun Alfaharinsa, cikin wata murya mai rauni yace "Ahanaff Ashe inada Rabon sake ganawa dakai? Ashe kana Raye? Allah ya ƙarbi addu'a ta ya nunamin kai cikin ƙoshin lafiya" Shadow mamaki yake sosai shidai yasan kafin yasamu taɓuwar hankali Abbansa ya daina Sonsa ya daina damuwa da lamarin sa, Toh ya akayi kuma yanzu yake nuna damuwar sa akansa, jiyayi gabaki ɗaya jikinsa yayi sanyi duk yadda yaso ya wufantar da lamarin mahifin nasa kasawa yayi. Abbu yace "barshi ya zauna ya huta Muhammad" Abba ji yake kamar Idan ya saki Ahanaf zai ƙara ɓata ne, murmushi Shadow yayi ganin yadda Abban nasa ya riƙesa sosai, cikin sanyin murya yace "gani na dawo gareka Abba kuma insha Allah ba abunda zai ƙara rabamu face Mutuwa, Shadow ya faɗa Yana zaunar da mahaifin nasa akan kujera.
Gaban Abbu yaje ya durƙusa ya gaisheshi, amsawa Abbu yayi cikin matsancin farin ciki, Ji yake yau kamar duk wata buƙatarsa tagama Biya. Tambayoyi ne da yawa a bakinsa amma dole yabari su huta tukkunna.
Tashi yayi yaje yagaida haj Mama, amsawa tayi tana shafa Kansa, tace Ahanaf kabarmu da kewa da fargaba da kuma matsancin DUHU, Amma yanzu alhmdllh dawowarka gida lafiya kuma cikin hayyacinka yafi komai faranta ranmu.
Murmushi Shadow yayi batare da yace uffan ba.
Hannu ya Bawa Haidar suka gaisa Sannan ya Bawa Kamal, ba abunda da suke Sai murmushi.

Tashi Haj Mama tayi taje ta ɗauko musu drinks Kala Kala, ta zuba musu.
Murmushi Abbu yayi yace "kusha ruwa bayin Allah"
Murmushi Dady yayi yace "Toh mungode" ƙaseem yace "Yaya suwaye waɗan nan? Murmushi Shadow yayi yace "har yanzu dai baka sauya ba ƙaseem hanzarinka yana nan ko? Ajiyar zuciya yayi yace "Yaya nadamu matuƙa nasan halinda kashiga, da kuma wanda ya sakaka ciki, Yaya jinana tafasa yake gurin ɗaukar maka fa..." Abbu yace ya Isa haka ƙaseem komai na Duniya a hankali ake binsa" dole tasa yaja baki yayi Shiru.
Shadow ya Kalli Haj Mama yace "Mama Wai Ina Ayiyata ne? Nifa tun ɗazu da nazo ban ganta ba" Haj Mama tace "taɗan fita ne kuma tace ba nesa zataje ba, Amma kaga har yanzu bata dawo ba" Shiru yayi batare da ya sake Magana ba.
Abba Sai kallon Ahanaf yake cikin matsancin So da ƙauna, Ji yake ko a Yau ya Mutu Toh burinsa ya gama cika, dama tunda yadawo cikin hankalinsa kullum roƙon Allah yake ya ƙaddara saduwarsa da sanyin idonsa, Sai ga shi ranar tazo.

Abbu ya Kalli Dady yace "Alh mutafi masallaci lokacin Sallah yayi" yafaɗa yana tashi tsaye gabaki ɗaya mazan fita sukayi zuwa masallaci.
Haj Mama tace "kutashi mutafi muma musake farali" Ammi Hafeeza da Shabana suka bi Bayan Haj Mama har bedroom, ta nuna musu toilet, Ammi ce tafara Shiga Bayan tafito Suma suka shiga suka ɗauro alwala, Bayan sun kammala Sallar ne suka dawo, Haj Mama tafara Jan Ammi da fira, Suna cikin firar su Dady suka dawo, Bayan sun zauna ne Abbu yace ma Abba ka kira Matarka tazo gida, kaki Amininka Alh Mukhtar yazo shima da iyalansa.
Waya Abba ya ɗauka ya Kira Alh Mukhtar ya faɗa masa Abbu yana nemansa tare da iyalinsa. Alh Mukhtar yace "Lafiya kuwa Muhammad?" Abba yace "Lafiya ƙalau kawai ku zo yanzu inda Hali" Dadyn Norr yace "Okey zamu zo yanzu da yarda Allah Amma fa Haj bata nan sun fita tare da Matarka" Abba Yace "karka damu Kawai kazo tare da su Norr, Suma zan kirasu Idan ba nesa su kaje ba suzo gida yanzu" sallama sukayi.

Abba yakira wayar Ayiya Saida yayi mata 3misscall sannan ta ɗauka, yace "kuna Ina?" Tace "Mun ɗan fita ne" yace "duk inda kuke kuzo gida yanzu" Ayiya tace "lafiya dai Abban Ahanaf?" Abba yace "Lafiya lau" tace "Okey zamu zo yanzu." Katse Kiran yayi ya kalli Abbu Wanda suke ta fira da su Malam Ibrahim Kamar sun Saba, yace "Suna zuwa" Abbu yace "Allah ya kawo su Lafiya"



Su Ayiya na parking, Yassar Shima yashigo tare da Norr da Dadyn su, parking yayi kusa da motar Ayiya, fitowa sukayi suka nufi part ɗinsu Abbu, Norr ta Kalli mommy tace "Mom Lafiya kuwa wannan Kiran gaggawa haka?" Hararar ta mommy tayi tace "sai kibari Idan munje kyaji koma menene" dole tasa Norr taja bakinta tayi shuru.
Koda ta suka Isa Palon Mamaki sukayi naganin baƙin fuska.
Shadow yana ganin Ayiya ya tashi da sauri ya nufi gurinda take Yana cewa "oyoyo Mah Ayiya" gabaki ɗaya wa ƴanda suka shigo Palon tsayawa sukayi cak Suna kallonsa.
Nan take Norr Taji Duniya na juya Mata, kodai mafarki take ne? Tana cikin wannan tunanin Taji muryar Ayiya da ƙarfi tana furta "Ahanafffffff Kaine? Meyasa zakamin haka? dama burinka ka tozarta Ni Na wulaƙanta? Toh Wallahi baka Isa ba Saika koma inda kafito, zuciyata bazata taɓa hutawa ba Idan Ina ganinka, Banida wata Babbar matsala a rayuwata da ta wuce ka, Sai ka Mutu Wallahi Sai ka Mutu, tinda ka yarda ka taka ƙafar gidan nan" Wani irin shock Shadow ya fara Ji tun daga ya tsar ƙafarsa har izuwa cikin brain ɗinsa.
Duk Wanda yake palon mamakin Kalaman Ayiya yake.
Cikin matsancin firgici Shadow ya ƙarasa gaban Ayiya yace "Ayiya buɗe idanunki kigani ko na canja miki ne? Nine fa Yaronki Ahan..." Wani gigitaccen Mari Ayiya ta zuba Masa tana huci tace "kai ba yaro Na bane, Allah yayi min tsari da haihuwarka, Ni ba mahaifiyarka b.... Kafin ta rufe baki Taji saukar wani gigitaccen Mari Saida ta tangaɗa zata faɗi da sauri Ahanaf ya riƙe ta, duk da cewa Shima Shirin faɗuwar yake.
Da sauri ta janye jikinta daga nasa hawaye nabin fuskarta tace na tsaneka Ahanaf dama ni ban taɓa sonka ba, kuma Wallahi Bazan taɓa sonka ba" Wani mari Abba ya kaimata da sauri Ahanaf ya riƙe masa hannu cikin rawar murya yace "Dan girman Allah Abba kadaina dukanta" cikin Wani irin ɗacin Rai Abba yace 'nayi nadamar saninki Shuwa, tabbas Ke DUHUN INUWA CE a rayuwata da taɗana, me nayi miki me nayi miki ne haka da zafi?" Abba yafaɗa har jikinsa na karkarwa tsabar ɓacin Rai.
Sudai su Ammi sun zura Ido kawai Suna kallon ikon Allah, Amma ko ba'a faɗa musu ba sun lura da wannan matsala ce gagaruma.
Abbu ya kama hannu Abba ya zaunar dashi yace "ka nutsu Muhammad ka dawowa cikin hankalinka, dama ai tsintaciyar mage bata mage a wancan lokacin ba yadda banyi da kai ba Amma fafir kaƙi ka hanu.

Mommy taja hannun Ayiya tare da cewa "Haj muje, wannan Taron anyi Shine Dan kawai a tozarta mu" Alh Mukhtar yace "Wallahi Idan kika taka ƙafarki kika bar palon nan na lahira ma Sai yafiki Jin daɗi, kinsan wanene Ni, kinsa Abunda nake iyawa da Wanda bana iyawa, Idan kuma kin musa gaki ga hanya" dole tasa mommy taja ta tsaya, tana kunkuni.

Da rarrafe Shadow ya Isa gaban Abba tare da riƙe masa ƙafa yace "Abba me yake faruwa ne? Abba da gaske ba Ayiya ce mahaifiyata ba? Abba koda irin rashin lafiyar da tasamenice ita ma ta sameta?
Hannunsa Abba ya kama cikin ɗacin Rai yace "Ahanaf Shuwa lafiyar ta ƙalau, Kuma tana cikin hankalinta" Saida yaja numfashi ya furzar Sanna yace "tabbas Ranar wanka ba'a ɓoyon cibi, Ahanaf Shuwa ba ita ce mahaifiyarka ba, sunan mahaifiyarka Nana khadeejah" wani Yanayi Ahanaf ya faraji gabaki ɗaya, Ji yake duniyar na juya masa. Hannayensa ya janye daga cikin na Abba tare da dafe kansa.

Ƙaseem yaji matsancin tashin hankali da yaji furucin Abba, wacce khadeeja? Taya ma za'ace Wai ba Ayiya ce ta haifi ya Shadow ba, Kenan shima ba ita ce ta haifesa ba? Kansa ya kulle sosai ba Abunda yake buƙata sai jin gaskiyar wannan rikitaccen Al'amari.


Norr, Yassar da su Haidar suma sun Shiga ruɗani sosai dan a tunaninsu Ayiya ita ce mahaifiyar Ahanaf.


Abbu da Haj Mama su mamaki ɗaya suke na rashin mutunci da Ayiya ta shuka yanzu, Amma su

Please Login or Register in order to submit comment