Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da yakeji na halinda Ayiya ta jefa Kanta a ciki. Nan take zazzaɓin da yakeji ya ƙaru sosai har wani zafi yakeji yana fita daga jikinsa, ya jima haka cikin matsanancin ƙunci, a hankali ya fara ƙoƙarin janye Shabana daga jikinsa ya Kwantar da ita gefensa, Tashi yayi tsaye nan take yaji Jiri yana ɗibar sa, Bango ya fara dafawa har ya ƙarasa toilet ya ɗauro alwala, da yafito sallaya ya shinfiɗa ya tayar da Sallah, ya jima yana Sallar ya roƙarwa mahaifiyarsa Rahmar Allah, kuma ya roƙi Allah ya yagafartawa Ayiya abunda ta aikata, haka ita ma Shabana yayi Mata addu'a sosai tare da roƙon Allah ya kauda sheɗan a tsakaninsu, ya bashi Ikon kyautatawa rayuwarta fiye da yadda ta masa. Bayan ya kammala Sallar ne ya zauna Yana tunanin abubuwan da suka faru dashi da kuma iyayensa, nan take hawaye suka fara zarya akan fuskarsa.


Cikin Bacci tafara jin shashsheƙar kuka da sauri ta buɗe Idonta, gurin da take jiyo sound ɗin ta kalla, Shadow ta hango ya haɗa kai da gwiwa, a hankali ta fara ƙoƙarin sauka daga kan gadon, tare da dafe Kanta da yake masifar yimata ciwo, direct gurinda Shadow yake ta nufa, zama tayi kusa dashi da kyar ta iya buɗe bakinta tace "Dan Allah kadaina wannan Kuka bafa abunda zai canza, ƙaddara ta riga fata komai ya riga ya faru, Idan kana so kasamu salama Sai ka bawa abunda ya faru baya"
cikin sanyin murya taci gaba da cewa "Ahanaff Idan kana wannan ƙunci kasani har dani kake a zabtarwa, narasa dalilin da yasa a ganina na farko da kai naga kana cikin damuwa a cikin idonka naga kana buƙatar taimako, kayi tunani a lokacin bansanka ba ban taɓa ganin ka ba Amma kuma na damu dakai, to wane hali kake tunanin zan shiga a yanzu Idan kana cikin damuwa?" a hankali ya ɗago jajayen idanunsa yana kallonta ita ma kallonsa take Ido cikin Ido Karon farko Kenan a rayuwarta, murmushin ƙarfin hali yayi tare da janyota jikinsa, wani mugun zafi yaji yana fita daga jikinta, cikin ruɗewa yace "Subhanallah me yake damunki naji jikinki da zafi sosai?" A hankali cikin sigar shagwaɓa tace "Kaine mana" Ido ya ware tare da nuna kansa da yatsa yace "Ni kuma me nayi?" Shuru tayi masa, Saida ya ƙara Magana sannan tace "Ina da sauƙin kurwa sosai Idan har na haɗa jiki da mai zazzaɓi ko na haɗa numfashi da shi sai na ɗauka" cikin jin tausayi Shadow yace "ya Salam! kinsan da haka shine kika yarda muka Kwanta tare?" Shiru tayi masa kamar bataji Abunda yace ba. Ajiyar zuciya yayi yana girmama kawaici irin na Shabana da kuma girman halaccinta a gareshi. Cikin sanyi murya yace "Allah yayi miki Albarka ya kareki da sharrin masu sharri, Allah ya tsare minke ya ƙara kare zuciyar ki daga kyashi da hassada Matar Ahanaf" har ƙasan zuciyarta taji masifar daɗin addu'ar Ahanaf Murmushi tayi tare da cewa "ameen ya rabbil alamin" Suna cikin firar sukaji Kiran Sallar Asuba, tayar da ita yayi tare da cewa "jekiyi alwala kizo muyi Sallah" tashi tayi a hankali ta nufi hanyar toilet, da kallo ya bita har ta shige Sannan ya sauke ajiyar zuciya, Allah ya Sani yana masifar ganin girma da kimar Shabana a idonsa fiye da tunanin mai tunani, ya kaita matsayi na ƙarshe a rayuwarsa har takai yanajin bazai iya rayuwa ba Idan ba ita, iska mai zafi ya furzar.



Kowa agidan ya kwana a cikin jimami da mamakin abunda ya faru.
Abba yayi kuka wanda Rabonsa da yayi irinsa tun bayan rasuwar mahaifiyarsa da Khadeeja.
yayi kukan rasa mahaifiya wacce ta kasance garkuwa a gurinsu
Kuma yayi kukan rasa mace tagari kamar Khadeeja, a ɗan Zaman da sukayi da ita na shekara ɗaya sunyi Sabo da juna fiye da tunani, Wanda beyi shi da Ayiya ba tsawon shekaru ashirin da tara da suka shuɗe, kullum sai ya tuna Khadeeja kullum cikin kewarta yake.
Cikin matsancin ƙunci yace "bazan taɓa yafe miki ba Shuwa zamu haɗu dake gaban Allah ya Kwatar min hakkina agurinki da na yarona da kika zalunta, haka Abba yayi ta surutai kamar wani zararre.


Ɓangaren ƙaseem Shima kuka yake da baƙin cikin kasancewar Ayiya amatsayin mahaifiyarsa, Da yana ɗaukarta a matsayin uwa tagari mai matuƙar so da ƙaunar ƴaƴanta Ashe ba haka bane ita ɗin azzaluma ce mai manta Alkhairi wacce son zuciya ya rufe mata Ido. Yanzu da wane Ido zai kalli Yayansa Abun Alfaharinsa, Allah yasani har zuciya So na tsakani da Allah yakewa Ahanaf bai taɓa tunanin ƙuntata masa ba ko kaɗan, sai gashi mahaifiyarsa ta Zama DUHUN INUWA a rayuwar Yayansa. Ƙaseem yayi Kuka Kamar ba gobe tare dayin tirrrr ga duk wata Mace mai halin Ayiya.







Suna kammala Sallar kwanciya tayi Akan sallaya tare da dunƙulewa guri ɗaya alamar tanajin sanyi.
Kusa da ita ya matsa tare da yi Mata Sannu, ganin kamar tanajin sanyi sosai yasa ya ɗauketa cak kamar wata yarinya ƙarama. hannanyenta tasa ta riƙe Shi sosai kamar wacce take tsoron faɗuwa, murmushi yayi yana kallonta ganin yadda ta rufe idanunta Shif.
Direct kan bed ya nufa da ita tare da Kwantar da ita yaja blanket ya lulluɓeta, zama yayi kusa da ita ya kama hannunta ya jimƙe a cikin nasa tare da yi mata Sannu.
Shuru tayi, shima kwanciyar yayi tare da jawota jikinsa ya rungumeta, taɗan jima kafin Bacci yayi gaba da ita.
Ganin tayi Bacci Shima ya lumshe Idanunsa.

Sun ɗauki tsawon lokaci suna Bacci sai can Ahanaf ya farka jin yadda jikin Shabana yayi mugun zafi kamar wuta, cikin tashin hankali ya yaye blanket ɗinda ya rufeta dashi ɗazu, Shabanaah Shabanaah, a hankali ta buɗe Idonta tana kallonsa, cikin sigar rarrashi yace"kitashi kiyi breakfast kisha magani dan Allah" Shiru tayi masa, tashi yayi tsaye yace "bari naje na samu miki abun kari kisamu kisha magani.
Da sauri ta riƙe masa hannu cikin sanyi murya tace "a'a kabari zan tafi da kaina" kallonta yayi cikin mamaki yace "to saboda mi Kenan?" Sakin hannunsa tayi ta tashi zaune tana gyara wuyan Hijab ɗin ta tace "bana So kaje ka cewa Haj Mama Banida lafiya kawai kabari natafi" ta faɗa tana ƙoƙarin tashi tsaye tafara Tafiya.

Tare suka fito daga ɗakin direct ɓangaren haj Mama suka nufa Wanda tana tunanin Amminta tana can.
A parlour sukaci Karo da Ammi da haj Mama zaune suna fira, Suna hangosu suka Maida hankalinsu kansu.
Wata irin kunya Shabana taji ta rufeta wacce tinda take bata taɓa jin irinta ba, dakyar take ɗaga ƙafarta ji take kamar zata faɗi.
Gaidasu sukayi Haj Mama ta amsa cikin farin ciki, Ammi kuwa ɗauke kanta tayi dan ita ma taji kunya sosai aranta tace "Yaran zamani ba ta Ido.

Murmushi Haj Mama tayi tana kallon Shabana wacce ta sunkuyar da Kanta ƙasa, cikin jin daɗi tace "zo nan ƴata Allah yayi Miki Albarka kinyi ƙoƙari sosai da ki kayi nasarar fito mana da wannan fusataccen Yaron" Haj Mama ta faɗa tana janyo Shabana kusa da ita, zafi taji sosai ajikinta cikin tashin hankali tace "Subhanallah me ya sameki Daughter, bakida lafiya ne?" Shiru Shabana tayi tana jin wata masifaffiyar kunya.
Haj Mama ta Maida kallonta kan Shadow tace "me yasameta ne Ahanaf?" Ajiyar zuciya yayi tare da cewa "Wallahi zazzaɓi ke damunta Mama kusan ma dashi ta kwana" Haj Mama tace "ya Salam tare da Maida kallonta kan Shabana tace "Sannu ƴata tashi Kishiga wancan ɗakin, ƴar uwarki tana ciki yanzu zanzo na kawo miki abun breakfast" haj Mama ta faɗa tana nunawa Shabana wani ɗaki.
Da sauri Shabana ta tashi, dama ta matsu ta bar gurin ganin irin kallon da Ammi take Mata sai taji gabaki ɗaya ta tsangwama.

Da kallo ya bita har tashige ɗakin, ita kuwa Haj Mama sai kallonsa take yana juyowa suka haɗa Ido murmushi yayi yana sosa kansa, hararar Wasa tayi masa sannan tace "zanyi maganinka yaro Idan har naji kayiwa ƴata ba daidai ba" Murmushi yayi batare da yayi Magana ba.
"Kaje gurin ɗan uwanka kuyi Magana dashi kasamu ka rarrashe Shi ya fito kuci Abinci tunda kai anyi nasarar fitowa da kai" ta ƙarasa maganar cikin sigar zolaya
Murmushi yayi batare da yayi Magana ba saboda ganin idon Ammi yasa bece Kumi ba saboda yana masifar jin kunyarta.



Ɗakin Shabana tashiga tare dayin sallama, Hafeeza dake zaune gefen gado tana Danna wayarta ta ɗago kanta tana bin Shabana da wani irin kallo mai cike da iya shege, ita Shabana batama lura da kallon da Hafeeza ke mata ba Kai tsaye gurin gadon ta nufa tare da kwanciya tana sauke ajiyar zuciya.
Kallonta Hafeeza tayi tace "lafiya dai Sulty?" ita kuwa Shabana Jin Hafeeza tayi Mata Magana cikin mutunci ba Kamar yadda tayi tunani ba yasa tace "Wallahi Banida lafiya Goty zazzaɓi ne yake damuna sosai" Wata Uwar Dariya Hafeeza ta saki Saida tayi mai isarta sannan ta dakata tace "Wallahi ni Sulty kin masifar bani mamaki yanzu ke dan Allah bakiji kunya ba, agidan surukai? Haba haba" cikin mamaki Shabana take kallonta tace "me kuma yafaru?" Murmushi Hafeeza tayi tace "uhmm ai duk Abunda ya faru ke yakamata a tambaya, kinje kin kwanta tare da miji da Sunan rarrashi kuma agidansu, Shine bake kika fito daga turaka ba sai kusan ƙarfe 10 na safe shine kike so ki hamagantar dani ko? Nan ma dai shiru Shabana tayi, Hafeeza ta ƙara cewa "yanzu how do I even know you are intact?" Shabana ta harare ta tace "ko in buɗe miki ki gani?" Dariya Hafeeza tayi hadda riƙe ciki tsabar shaƙiyanci Cox tambayar da tayi Mata tayi ne kawai dan ta tsokaneta, cikin dariyar tace "wacece ni? rufamin Asiri wannan saidai Ahanaf" banza Shabana tayi mata kamar bataji Abunda tace ba.
Ita kam Hafeeza tasamu aikinyi Cox ba abunda take sai tsokanar Shabana tana dariya.
Suna cikin haka sai ga Haj Mama tashigo ɗakin tare dayin sallama, da kyar Hafeeza ta iya Danne dariyarta ta amsawa Haj Mama sallama, Haj Mama ta Lura Hafeeza dariyar Shabana takeyi.
Kai tsaye gurinda Shabana take Haj Mama ta nufa, tare da tayar da ita zaune tace "ƴata tashi kiyi breakfast kisha magani kinji" tashi tayi haj Mama ta Bata mug ɗin da tashigo dashi tace "ƙarbi kisha" karɓa tayi ba musu Saboda kunyarta takeji sosai.
Kaɗan tasha tare da bawa Haj Mama mug ɗin tace "na ƙoshi" kama hannunta tayi tace "plxx ki ƙara mana koda kaɗan ne" ba yadda ta iya haka ta ƙara kai kofin bakinta ta ƙara sha, magani Haj Mama ta bata, karɓa tayi akan dole tasha tana ya mutsa fuska.
Mamaki Hafeeza tayi sosai eh Lallai Shabana tana masifar kunyar wannan Matar, ai ko Dady ne ya tsaya kanta bazata Sha wannan maganin ba sai anyi fama da ita.


Bayan tasha ne ta fara ƙoƙarin kwanciya Haj Mama ta riƙeta tace "karki kwanta yanzu daughter ki bari har maganin ya faɗa tukkunna" zama tayi kamar yadda Haj Mama tace.



Koda yaje ɗakin da ƙaseem yake yana kwance ya dunƙule guri ɗaya kusa dashi ya zauna tare da ɗaura kansa akan ƙafar sa, ajiyar zuciya ƙaseem yayi sun Jima shiru, cikin muryar kuka ƙaseem yace "Dan Allah kayi haƙuri kagafartamin Yaya" da sauri Ahanaf ya kara rungume ƙanen nasa cikin ɗacin Rai yace "Mai kamin kaseem? Ka daina rokona gafara Idan kana rokona zanyi tsammanin akwai banbanci tsakanin nida kai, Nida kai Jini ɗaya ne, Ahanaf Muhammad Imran, Al ƙaseem Muhammad Imran, gaya min banbanci mu.
Nida kai uwa ɗaya uba ɗaya ne haka nasani tun Ina Yaro kuma a haka zamuci gaba da rayuwa har Abada.
Idan dai ka yarda Ni yayanka ne Toh kamanta da duk Abunda yafaru.
Ƙaseem koda Kaine Kamin laifi zan yafe maka balle ba kai kayi ba, ba kuma kai kasa akayi ba hasalima yadda ban saniba kai ma haka baka sani ba.
Dan haka har yanzu Ahanaf Yaya ne agurin ƙaseem kuma garkuwarsa, kai din Jinina ne ba mai rabamu dakai, kuma zan tsaya tsayin daka gurin baka Kariya har ƙarshen Raina, Dan girman Allah ƙaseem kamanta da kumi indai na Isa da kai" Shadow ya faɗa yana share hawayen da suka zubo masa.
Sosai kalaman Ahanaf sukayi tasiri ajikinsa tashi yayi ya rungume shi yace "Nagode Yaya Allah ya barmu tare yafaɗa cikin matsanancin kuka saboda baiyi tsammanin jin haka daga bakin Yayansa ba. Ya Isa menene Abun tashin hankalin kuma bagani ba, Shadow ya faɗa yana Murmushi. Ajiyar zuciya ƙaseem yayi yace "Yaya amma dole ya kamata a ɗauki hukuncin kan Abunda Ayi... Dakatar dashi Ahanaf yayi tare dayin murmushin ƙarfin hali yace "kar kayi Magana akanta kana cikin fushi saboda ita uwace, ko yaya ne tana da haƙƙi akan mu, zuwa Anjima zamuyi maganar sai muje gidansu mommy mu ɗauko ta" cikin wani matsanancin mamaki ƙaseem yace kasan Abunda kake faɗa kuwa? Ayiyar zakaje ka dawo da ita? Wallahi Wallahi baza.......... Ya Isa ba shawara nake nemanka ba Amma kasani koda ka canza Ayiya a matsayin mahaifiyarka to kasa a ranka nidin mahaifiyata ce, da kallo ƙaseem yake bin Ahanaf, gyaɗa masa kai Ahanaf yayi yace "tabbas Ayiya mahaifiyata ce" Shiru kaseem yayi yana tunanin zuciya mai kyau irin ta Shadow.
Ganin ƙaseem yayi Shiru ne yasa ya tashi tsaye ya tayar dashi yace "muje kayi breakfast" dole tasa ya fito daga cikin bargon daga shi sai gajeren Wando Jallabiyarsa Shadow ya ɗauko masa ya bashi ya saka sannan ya kama hannunsa suka fito parlourn part ɗinsu, Haidar yana zaune Kamal a kwance suna fira gaisawa sukayi, Shadow yace kunci Abinci? Kamal yace har ya fara narkewa ma, murmushi Shadow yayi dan yasan Kamal da girki ba wasa, tare sukaci Abincin da ƙanen nasa suna ci suna fira.


Abbu, Dady da Malam Ibrahim ne suka shigo parlourn tare dayin sallama Haj Mama da Ammi suka amsa musu.
Bayan sun zauna Abbu ya Kalli Haj Mama yace "ƙarshen duk wani Zalunci nadama kowane Rami na mugunta Idan ka duba da kyau zakaga mai shine yake afkawa cikinsa, ajiyar zuciya yayi a hankali yace "Shuwa ta karɓi sakamako ita da Ladi sun girbi baƙar shukarsu, ɗazu Mukhtar ya kirani yana faɗamin wai an kirashi daga can gidansu Haj Ladi an faɗa masa ta haukace ita da ƙawarta a Daren jiya, kuma su sunyi iya ƙoƙarinsu gurin hana su fita Amma sun kasa, yanzu haka dai sun fita ba wanda yasan gurinda suke..........✍️✍️✍️













Nabeela Binji ce💃💃💃







More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏.





♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM



PAGE

4️⃣ 4️⃣













__________________ Innalillahi wa'inna Ilaihi Raju'un Ammi ta faɗa tare dasu Shadow wanƴada yanzu suke ƙoƙarin shigowa parlourn sukaji bayanin Abbu.

Duk inda hankalin Shadow yake ya tashi nan take idanunsa suka sauya kala ɓacin rai bayyane a Kan fuskarsa, wani abu yaji ya tsaya masa arai mai masifar ciwo.

Al kaseem wayarsa ya dinga dannawa kamar abun bai dameshi ba, amma acikin zuciyarsa shikaɗai yasan halinda yake ciki, uwa sunanta uwa tagari ko muguwa dukansu dai wannan Sunan suke amsawa kuma sukan samu jinƙai daga gurin yaransu koda azuciyane zasuji ciwo Idan wani mummunan abu ya sami iyayensu.
Hakance ta faru da ƙaseem Shima.

Gaban Abbu Ahanaf yaje ya durƙusa cikin sanyin murya yace "dan Allah Abbu kataimaka kabani dama na Nemo Ayiya ayi mata Magana inada tabbacin zata warke inshallah zata dawo normal" murmushi irin nasu na manya Abbu yayi yace "kaje ka nemi izinin mahaifinka Idan ya baka dama ni mai maka fatan Alkhairi ne" Nan take Shadow yaji gwiwarsa ta sage, dan yasan ba wata hanya da zaibi ya shawo kan mahaifinsu.

Shadow yayi iya ƙoƙarin sa Abbu ya Saka baki akan maganar amma fafir yace ba hannunsa ba ƙafar sa a Wannan maganar, yace "kabarni naji da mahaifinka na samu ya buɗe kofarsa, ni shine abunda yake damuna a halin yanzu" dole tasa Shadow yaja bakinsa yayi Shiru Amma abun yana cikin ransa kuma yana damunsa sosai.




Koda Abbu yaje ƙofar ɗakin Abba a Karo na ukku cikin fushi ya tafi, yayi Kwankwasa har ya gaji Amma Abba yaƙi ya buɗe, cikin kaushin murya Abbu yace "Wallahi Muhammad Idan baka buɗe ƙofar nan ba sai ranka yayi masifar ɓaci, me kake nufi? so kake kanuna ban Isa da kai bane ko yaya? Idan kabari na juya bayana nabar ƙofar nan baka buɗe ba to kasani na juya baya na Kenan akan duk wani lamarinka" Abbu ya faɗi haka ne kawai dan yasan idan Muhammad yaji haka da sauri zai buɗe ƙofar, Amma banda haka ai ba Abunda zaisa yafita daga rayuwar ɗan uwan nasa.
Ai Kuwa yayi Nasara dan ba'a kara minti ɗaya ba Abba ya buɗe ƙofar wata masifar rama yayi a cikin kwana ɗaya, idanunsa sun kunbura alamar yayi kuka har ya gode Allah.
Abbu yaji tausayinsa fiye da tunani, ɗakin yashiga tare da kama hannunsa yaje ya zaunar dashi bakin gado, toilet Abbu yashiga ya haɗawa Abba Ruwan wanka ya fito, cikin muryar rarrashi yace "je kayi wanka kuma plxx karka jima kaji" kai kawai Abba ya gyaɗa masa.

Yana shiga toilet Abbu yafara gyara masa ɗakinsa, yana jimamin wannan lamarin da yafaru dasu, yana masifar son ƙanensa fiye da tunani.
Koda Abba ya fito Abbu ya kammala gyara ɗakin ya fitar masa da kayan sakawa.
Bayan ya shirya Abbu ya fara yi masa nasiha Akan rayuwa nasihohi yayi masa masu ratsa jiki da ɓargo har Saida yayi kuka.
Abbu yayi nasarar fito da Abba parlour kuma yasaki jikinsa yayi fira kamar ba abunda ya faru, abu ɗaya yake tunawa yaji sanyi shine jin da yayi Ayiya ta haukace, hakan yayi masa daɗi fiye da tunani, kuma ya kara girmama lamarin ubangiji mai sakamako tun a duniya.


Haj Mama ta matsawa Ammi akan taje ta duba jikin Shabana, kuma ta rarrasheta ayi mata Allura. Murmushi Ammi tayi tace "ai indai za'ayi ma Shabana Allura to sai Idan ciwon yakai bazata iya ɗaga hannunta ba, amma muddin zata iya to kuwa bazata bari ba" murmushi Haj Mama tayi tace "kar ku saka wa ƴata Ido, tunda bata so Allah ya Bata lafiya. Murmushi kawai Ammi tayi.

Koda Ammi tashiga duba Shabana tana zaune kan sallaya bata jima da kammala Sallar la'asar ba.
zama Ammi tayi gefen gado tace "yajikin naki?" Matsowa Shabana tayi kusa da Ammi tare da ɗaura Kanta Saman ƙafafunta a hankali tace "Alhmdllh Ammi" Kanta Ammi tashafa tace "me yake miki ciwo?" Cikin shagwaɓa tace "Ni ba Abunda baya Mun ciwo Ammi" murmushi Ammi tayi tace "Kenan wannan jinyar ba tamu bace ta Ahanaf ce?" Da sauri Shabana ta ɗago kanta ta kalli Ammi, murmushi Ammi tayi tace "eh Mana, ko kuwa Hafeeza" ta faɗa tana kallon Hafeeza.
Su Hafeeza an samu Abunda ake so cikin ƴar dariya tace "lallaikam Ammi, nima Abunda na faɗa mata Kenan Amma sai ta dinga hararata" murmushi Ammi tayi tace "Toh kindai ji" wani haushi Shabana taji ya kamata tashi tayi batare da tace uffan ba tashiga toilet dama wanka take so tayi, aranta kuma tace "zakuyi ku gama baza kuji mutuwar Sarki abakina ba."









______________Haj Ladi da Shuwa da ganinsu ba tambaya zaka san cikakkun masu taɓin hankali ne, saboda duk wata alamar hauka ta bayyana atare da su, Tafiya suke basu ma san inda suka dosa ba, ba mai mayafi a cikinsu ballema takalma, sun yamutsa gashin kansu, duk inda sukabi sai yara sun tsokanesu.


Lokacin da Norr da Yassar sukaji halinda mahaifiyarsu take ciki sunyi kuka kamar ransu zai fita, musamman ma Norr wacce dama tana cikin wata damuwar sai ga wata taƙara riskarta kuma duk mahaifiyarta ce sanadiyar komai.
Da kyar Dady ya Samu kan Norr ta daina Kukan, yaje gidan ƙanwarsa ya ɗauko Meenal tazo taya ta zama.
Hakan yaɗan yi tasiri saboda Meenal tana iya ƙoƙarin ta gurin kwantar mata da hankali.







_____________Misalin ƙarfe 9 pm Shabana ce Zaune a bedside tana Danna wayarta taji sallamar Ahanaf amsawa tayi tare da ce masa ya shigo, yana Shiga gurinta ya nufa zama yayi tare da fizge wayar hannunta, kallonsa tayi cikin mamaki, murmushi yayi yace "yanzu lokacina ne bana waya ba" wata uwar harara ta zuba masa,
Murmushi yayi yace "Ai anan kam kin ƙware, amma yanzu Mutum yace zai taɓa ki a sannan ne zai rainaki" murmushi tayi batare da tayi Magana, ajiyar zuciya yayi yace "kinji abunda ya faru da Ayiya ko?" Ya ƙarasa maganar cikin rauni da alamar Abun ya taɓa shi sosai.
Kai ta gyaɗa masa tace "haj Mama ta faɗamin" numfashi ya furzar yace "gashi su Abbu sunyi fushi sosai da ita, Amma ni naso su duba lamarinta kodan Al ƙaseem" murmushi tayi sannan tace "Abune mai wahala su yarda da haka gaskiya, saboda duk wanda yayi irin abunda Ayiya tayi tohm fa kasani ba abunda bazai iya aikatawa ba, yunƙurin Kisan kai tayi fa, taya kake tunanin zasu yarda da ƙudurinka?" Shiru Shadow yayi na ɗan lokaci, sannan yace "ni naso nasaka sharri da Alkhairi ne" murmushi tayi tace "Toh Allah ya baka ladan niya" fira sukayi har kusan ƙarfe 10, Shabana ta kalleshi tace "katafi zan kwanta" murmushi Shadow yayi yace "ina Hafeeza ne?" Ya mutsa fuska tayi tace "tana can gurin gulma" dariya yayi yace "gulma fa? to ita da waye suke gulman?" Ita da Ammi mana" baki Shadow ya riƙe tare da kai mata dukan wasa yace "Ammin ce take gulma? Lallaima yarinyar nan kin ƙosa" murmushi tayi tace "kai baka gani babe?" Kansa ya gyaɗa yace "ban gani ba, amma bari na gani yanzu" ya faɗa yana jawota ta faɗa jikinsa, suka faɗa kan gadon yasa duka hannayensa ya rungumeta.
Ƙoƙarin kwacewa tayi Amma ta kasa, bakinsu yayi ƙoƙarin haɗawa ta kawar da kanta, murmushi yayi tare da ƙara matseta da hannu ɗaya, yasa ɗayan ya juyo fuskarta ya haɗa bakinsu kissing ɗinta ya fara, lumshe Idonta tayi tanajin yadda saƙonsa ke ratsa duk sassan jikinta, sun jima a haka ta kuma daina ƙoƙarin kwacewa saima ji da tayi jikinta yayi sanyi sosai wata kasala ta lulluɓeta.
Ji tayi an turo ƙofa anshigo da sauri tafara ƙoƙarin janyewa daga jikinsa amma ina Shadow yaƙi ya saketa.

Hafeeza da tashigo yanzu idonta yafaɗa kan su Shabana da sauri ta juya ta fita tare da cewa "subhanallah yau dai kam nakai ƙarshe.

A cikin ɗaki kuwa Shabana tayi iya ƙoƙarin kwacewa amma ta kasa saboda wata matsa da Shadow yayi mata, sakin bakinta yayi yana ƙoƙarin zare mata zip ɗin doguwar rigarta, cikin sauri ta riƙe masa hannu, murya na rawa tace "plxx dan Allah kasakeni kaga fa Hafeeza ta shigo" dakatawa yayi batare da ya zare zip ɗin ba, Saima tura kansa da yayi gefen wuyanta yana shaƙar dadaɗan kamshi turarenta tare da lumshe Idanunsa kamar mai bacci, jin shirun yayi yawa kuma bashida niyar sakinta yasa ta sake cewa "plxx Ahanaf dare Yanayi kuma Hafeeza tana so ta kwanta" cikin cool voice yace "to kizo muje ɗakina plxx" kanta ta ɗago tana kallonsa tace "tab Wallahi idan har kaganni lahira to kaini akayi" Yanayin yadda tayi maganar ya masifar bashi dariya, cikin dariyar yace "idan nine zan kaiki lahirar kuma tare zamu ai zaki tafi ko?" Kai ta girgiza masa Alamar a'a.
Tashi yayi da ita zaune ajikinsa batare da ya Saketa ba yace "plxx ki yarda mutafi" nidai Dan Allah kasakeni katafi abunka" kallonta yayi naɗan lokaci sannan ya janye hannayensa daga jikinta yace "nasan maganinki zanyi maganar tarewarmu da Abbu in yaso naga ƙarshen gudunki" sauka tayi daga Kan ƙafafunsa batare da tace masa uffan ba cox tasan Idan ta tanka masa bazai fita yanzu ba.
Tashi yayi tsaye ya gyara zaman Jallabiyarsa.
yi yayi kamar zai kamota tayi baya da sauri, dariya yayi yanufi ƙofa tare da cewa "zanyi kewarki sosai, yau da alama bazaki bari nayi bacci ba saboda kin hargitsimin tunanina" ya faɗa yana kallonta Shiru tayi masa aranta kuma tana fatan ya fita.
Saida safe yayi mata ya fita bisa dole ganin ba yadda zaiyi.
Yana fita ta sauke ajiyar zuciya tare da faɗawa Kan gado.
Jim kaɗan da fitarsa Hafeeza tashigo, Shabana aranta tace "nashiga ukkuna yau bani ba baccin daɗi kuma.

Toilet tashiga ba jimawa ta fito tare da ɗaukar pillow da blanket, kallonta Shabana tayi tace "ina zuwa madam?" Murmushi Hafeeza tayi tace "ƙasa zan kwanta mana" kallonta Shabana tayi cikin mamaki tace "to Saboda me

Please Login or Register in order to submit comment