Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Janta da fira, tana amsa masa kaɗan kaɗan.
Tare suka fito parlourn, Shabana ce ta fara hangosu tace "munafuka Yau duk sai na famshe Abunda keki Mun" murmushi Shadow yayi, yace ai daga ganin wancan banzan yana Murmushi yaciyo kanta, muje mu titsesu" fita sukayi daga cikin Motar, suna fitowa saiga Motar kaseem tashigo gidan, tsayawa sukayi har suka ƙaraso gurin, buɗe Motar kaseem yayi yafito tare da zagayawa ya buɗewa Norr ƙofa, fitowa tayi da cikinta wanda ya ƙara girma.
Meenal ta buɗe Mota ta fito tace "Allah yasa inada hannuna bana jira a zo abuɗe ni" murmushi ƙaseem yayi Saboda tun gida suke rigima da ita, har cewa tayi ta fasa binsu sai da kyar ta yarda ta bisu.
Murmushi yayi yace "Allah ya huci zuciyar ki, baki ganin ita bata da lafiya ne" ya mutsa fuska tayi tace "kuyi ƙoƙari ku fusatani Allah ba abu bane mai wahala nayi Tafiya ta" kaseem yace "toh Mun daina ayi haƙuri" koda suka ƙarasa gurinda su Shabana suke, sallama sukayi Ahanaf ya Amsa, Norr tace "Ina wuni ya Shadow" murmushi yayi yace Lafiya lau" kallon Shabana tayi tace "Sannunki" saida tayi ƴan sec's sanna tace "yawwa" Shadow ya Kalli Meenal yace "uwar rigima kina nan dai har yanzu baki sauya ba" murmushi tayi tace "kai ai daman ba fari nakeyi a idonka ba" murmushi yayi yace "Bismillah muje ciki su Haj Mama Suna nan" dukansu tare suka rankaya parlourn.

Norr da Meenal sun gaida Haj Mama da Ammi cikin girmamawa, amsawa sukayi cikin sakin fuska suna tambayar sun zo lafiya?, Lafiya lau, madallah Haj Mama ta faɗa tana murmushi.




Shabana ta lura da irin kallon da Norr take mata, aranta tana tunanin me yasa take kallonta haka, Hafeeza ta matso kusa da Shabana sosai a hankali tace "kiyi maganin wannan guzumar naga wani kallo take muku keda Mijinki" murmushi Shabana tayi tace "ai yanzu ma da kika ga na ɗaga mata ƙafa Albarkacin Ammi da haj mama taci, but bari mu bar nan kiga abunda zanyi" murmushi Hafeeza tayi tace "haba sai yanzu nasan Ina tare da Shabana, Amma me zan gane ana miki wani kallo kina ɗauke kai kamar ba keba" murmushi Shabana tayi Dan Sarai tasan Hafeeza zugata take, dama ko makaranta Idan Suna faɗa ita ce mai ƙara tunzura ta ayi masifa. yanzu kuma koda batayi Magana ba tana da niyar nunawa Norr cewa Ahanaf nata ne ita kaɗai.

Tashi Ammi tayi tace "Haj bari naje na ɗan kwanta kafin ajima" murmushi Haj Mama tayi tace "nima tashi zanyi akwai abunda zanyi" bayan su Ammi sun tashi ne fira ta karaɗe parlourn, Shabana, Shadow da Kamal suka tasa Hafeeza da Haidar gaba Suna tsokana, Haidar yana tare musu faɗan. Sun jima suna fira kafin Kamal yace "plx kutashi mutafi" Shadow ya Kalli Shabana yace "my beloved kinji wai zasu ja miki miji gurin yawo" ya faɗa yana ƙara narkewa cikin kujera alamar baya son zuwa.
Wani sanyi Shabana taji har cikin ranta, cikin sanyi murya tace "kayi zamanka loveline ba Wanda zai ja min miji yaje dashi yawo, ya gajiyar min dashi" tunda ta fara Magana Shadow ya ƙure ta da Ido ko kyabtawa bayayi, wani farin ciki yaji ya rufe shi, tunda yake da Shabana yau kaɗai yaji ta kirashi da Sunan soyayya.
Gyara zamansa yayi yace "Toh kunji abunda beloved wife tace ba inda zanje" sakin baki Haidar yayi yana kallonsu sannan yace "mun shiga ukku tun baku tare ba ka zama mijin Haj? Wannan Idan kuma kun tare sai Yaya?" Kamal yace "ai ni na rasa abun cewa ma tsabar mamaki" Shadow yace "kuyi ku gama Idan har ba ita tace naje ba Toh fa kusani ba inda zani" Hafeeza tace "tsabar kazama mijin tace ko?" Shadow yace "Idan akwai abinda yafi mijin tace to nine."
Haidar ganin da gaske Shadow yake Idan Shabana bata bari yaje ba to bazai tafi ba yasa, ya kalleta yace "sorry Haj Shabana Dan Allah ki bamu Aron Mijinki muje mudawo" murmushi tayi batare da tace uffan ba. Ƙaseem yace "plx Aunty Shabana Allah ba jimawa zamuyi ba" murmushi tayi tace "tohm zan barshi Amma dan kai kawai ƙaseem ka kula min dashi sosai fa" Hafeeza tace "Ikon Allah wannan tsaron har ina? Duk wannan faman ɓoye shi da kike ba shi zai hana yaga wata yace yana so ba" murmushi Shabana tayi tace "Ahanaf na Shabana ne ita kaɗai har abada da yardar Allah?" Murmushin Shadow yayi yace "Shakka Babu a cikin kalamanki beloved" da sauri Norr ta ɗago kanta ta kalleshi, dan tun ɗazu da suke magana tana dai jinsu amma kanta yana ƙasa tana danna wayarta, Wani ƙunci taji a zuciyar ta, ta kuma tuna Ranar da Ahanaf yake ce mata daga ita ba ƙari cox shi bashida ra'ayin Mata biyu a rayuwarsa, sai gashi yau agaban Idonta Shadow yake cema wata da ita kaɗai zai rayu, tabbas mahaifiyarta ita ce silar duk wannan Abun, to wa zata zarga bayan ita. Allah ne sheda taso Ahanaf fiye da kowane ɗan na miji a rayuwarta, sai Kuma Allah ya ƙaddari bazasu rayu da juna ba. Hawaye taji suna bin kumatunta da sauri ta sun kunyar da Kanta ƙasa kar agani.


Bayan mazan sun fita ne sukuma suka ci gaba da fira musamman Meenal da Hafeeza uwayen surutu nan take fira ta tashi, jefi jefi Shabana Kan saka bakinta a cikin firar tasu, sun ɗauki lokaci a parlourn suna fira.
Norr ta Kalli Shabana tace "Matar ya Shadow zanyi fitsari" da sauri Shabana ta ɗago ta kalleta, a hankali tace "muje daga nan ma kuyi Sallah naji kamar an fara kira" gabaki ɗaya ɗakin suka shiga, Norr tashiga toilet tayi fitsari tayi alwala, koda ta fito Shabana ta shin fiɗa mata sallaya, Sallah ta fara.




Har Bayan magrib su Norr suna gidan suna jira ƙaseem ya dawo daga masallaci ya Maida su gida.
Koda suka dawo sun tarar dasu parlour, direct gurinda Shabana take ya nufa tare da zama saman hannu kujerar da take kai, kansa ya ɗan sunkuyu kusa da kunnenta yace "Chinaza Okoson wato kowa yayi Sallah kina nan kina Danna waya ko?" Shagwaɓe fuska tayi tace "haba dan Allah Sunan Cristan ne fa" dariya yayi yace "ai kema naga yau kaf bakiyi Sallah ba" gyaran murya Hafeeza tayi tare da cewa "muna kusa fa kar a wuce gona da iri ah to dan yanzu na lura kun zama mayun juna" gyara zamansa yayi yace "to sannu sa'idinawa ana ruwa kuna ƙirgawa" ai yafi" Haidar ya faɗa yana harararsa, murmushi Shadow yayi.
Ƙaseem ya Kalli Norr yace "Madam tashi muje" tashi tayi tace ina zuwa, Haj Mama tayi wa sallama sannan ta fito. gabaki ɗaya packing lot sukaje Domin yi musu rakiya.


Koda suka Isa buɗe ƙofa Meenal tayi ta fito tayi cikin gida.
Gyara zamansa yayi yana kallonta yace "Norr kiyi haƙuri kinji duk Abunda kika ga ya faru ƙaddarar wannan cikin ce tasa, Allah ya ƙaddari akwai rabo a tsakaninmu ba yadda zamuyi, dan Allah ki bar kumi ya wuce muyi zaman mu kamar komai bai faru ba Albarkar cikin jikinki kinji" hannunsa Norr ta kama tare da yin wani murmushin takaici tace "ai banida wani zaɓi da yawuce ka yanzu ƙaseem tunda har kaine Allah ya bani na karɓa, nasan insha Allah Anan Alkhairin yake" wani kayataccen murmushi yayi yace "Nagode sosai Allah yayi Miki Albarka ya saukeki lafiya" ameen ya Allah tafaɗa tana ɗan murmushi.

Ƙaseem yace "sai maganar komawar ki, Abbu yace ki Koma ɗakin ki, yaushe kike so ki koma?" tace "a wannan gidan kuma?" Murmushi ƙaseem yayi yace "eh aciki" tace "mai yasa bazamu canza shi ba? kasan fa asalinsa ba naka bane" murmushi yayi yace kafin ke nayi wannan tunanin kuma nayi maganar Amma sai Yaya Shadow yace ya bani wannan gidan Halal Malak, daga farko naƙi saida naga ɓacin ransa sannan na karɓa, Kuma ya roƙi Alfarma akan muzauna a ciki yanzu in yaso daga baya sai mu canza Idan mun gaji dashi" ajiyar zuciya tayi tace "tohm ka gode Allah yaƙara rufa Asiri" murmushi yayi yace Amin ya Allah.

Kallonsa tayi tace "kaje gida dare Yanayi" ɓata fuska yayi tare da cewa "korata ma kikeyi ko?" Murmushi tayi tace "ni na Isa na koreka? Kawai dai bana so kayi dare a hanya ne" murmushi yayi yace "Idan nayi dare Sai na kwana anan ai nima gidan mu ne" murmushi tayi tace "hakane Kuwa ga ɗakin Yassar nan sai ku kwana tare" ɗakin Yassar kuma? ai duk inda kika kwanta Anan nima zan kwana" harararsa tayi tace "a gidanmu?" gyaɗa kai yayi yace "eh mana menene to?" Ba kumi ta faɗa tana gyara zamanta alamar ta gaji, cikinta ya kalla Murmushi yayi tare da saka hannunsa ya shafa shi a hankali, lumshe Idunsa yayi yace Allah kabani yara nagari wa ƴanda Al ummar musulmi zasuyi alfahari dasu" murmushi Norr tayi tace "Ameen ya Allah" Rigarta ya fara ƙoƙarin ɗagawa kallonsa tayi tace "lafiya Malam" ba tare da ya daina abunda yake ƙoƙarin yi ba yace "babyna zan duba lafiyarsa" da sauri ta riƙe masa hannu ganin yana ƙoƙarin yin sama gabaki ɗaya da Rigar. Ɓata fuska yayi yace "wai menene haka?" Nidai ka daina bana so" yace ni kuma ina so" kyaleshi tayi ya fara shafa cikin a hankali, bakinsa yakai yayi kissing ɗin cikin.
Kansa ta tallafo sama tace "Malam kaje saida sa... Bai bari ta ƙarasa ba ya haɗe bakinsu guri ɗaya yana zuba mata kiss, Ido ta ware sosai, saboda a halin yanzu bata taɓa tsammanin haka daga Ƙaseem ba..........✍️✍️✍️













Nabeela Binji ce💃💃💃







More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏.




♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM



PAGE

4️⃣ 7️⃣

















_______________ Saida yayi son ransa sannan ya Saketa, sunkuyar da Kanta tayi ƙasa, Murmushi yayi tare da ɗago fuskarta yace Menene?" Lumshe Idanunta tayi a hankali tace "Dan Allah kabari na koma gidansu Meenal da zama kafin lokacin komawata yayi" kaseem yace "har kwana nawa kika ɗiba kafin ki koma?" ɗan Jim tayi sannan tace "ni inda zaka yarda ma ka bari har sai na haihu sai na koma gabaki ɗaya" wani kallon kina lafiya ya zuba mata batare da yayi Magana ba. Murmushi tayi tace "Tohm zanyi sati ɗaya sai na koma" fuskarta ya kama ya jawota dab da tashi yace "Norr bazakiyi sati ba gaskiya, toh menene ma Abun ɗaukar lokacin? Gobe za'a iya kammala gyaran gidan, sai kuma mai ya rage?" Tace "nidai dan Allah kabarni nayi koda kwana huɗu ne" ajiyar zuciya yayi yace "Na bari Allah ya nuna muna lokacin" murmushi tayi Tare da cewa "ameen ya Allah na gode" Sallah ma sukayi da kyar yaja Motarsa ya tafi.





Shabana zaune gefen gado, Hafeeza tana kan sallaya suna abunda suka fi kwarewa wato faɗa, Shabana tace "wannan Kam ko kina so ko bakiso sai kin aureshi" Hafeeza tace "sannu uwa Shabana, zo kisa nayi abunda banyi niya ba" murmushi Shabana tayi tace "kinsan Allah Idan kina son zamanki Lafiya dani ki ƙarbi soyayyar Haidar" Hafeeza zatayi Magana sukaji an turo ƙofa, dukansu ƙofar suka Kalla Haj Mama suka gani ɗauke da cups biyu, gaidata sukayi ta amsa tare da bawa Shabana kofin hannunta tace "ƙarbi kisha daughter" hannunta ta miƙa ta karɓi kofin, wasu kalar ruwa tagani ciki, ɗagowa tayi ta Kalli haj Mama, murmushi Haj Mama tayi tace "Kisha ba maganin Mutuwa bane" ita ma murmushin tayi tare da kai kofin bakinta tafara sha, kaɗan tasha ta ba Haj mama, hararar wasa tayi mata tace "ai Idan aka fara sha ba'a ragi duka zaki shanye" bisa dole ta ƙara kai kofin bakinta ta Runtse idanunta ta shanye ruwan tass taba Haj Mama kofin.
Karɓa tayi tare da bata ɗayan, Ido ta waro cikin sanyi murya tace "Allah na ƙoshi Mama" Haj Mama tace "bafa Abinci bane Shabana, kisha wannan kiji yana da daɗi ba kamar na farkon ba" ba yadda ta iya dole ta karɓi kofin ta kai bakinta, wani garɗi taji ya gauraye bakinta nan take ta shanye ta bawa haj Mama kofin.
Murmushi haj Mama tayi tare da karɓa kofin ta fita.

Kallon juna sukayi ita da Hafeeza, wata dariyar mugunta Hafeeza tayi tace "zakici gidanku yarinya harda wani tanɗe baki ke ga mayya" harararta Shabana tayi tace "me kuma yafaru ne? Hafeeza tace "Kinsan me Mama ta baki kika sha? Kai Shabana ta girgiza a hankali, Hafeeza tace "wane kalar test kikaji? Shabana ta faɗa mata, dariya Hafeeza tayi tace "kin manta Abunda mommy take bamu mu kaiwa Maimoon da Hidaya?" Shabana tace "nima naji kamshi kamar iri ɗaya" dariya Hafeeza tayi tace "ba kama bane Abunda ake bawa matan Aure ne aka fara Banka miki tun baki shiga ba, Wallahi sunanki sorry, cox ita Haj Mama Yaron take ma, ke kuma him" Hafeeza ta faɗa tana dariya. Ɗan jim Shabana tayi tanajin yadda ƙirjinta ke harbawa da sauri, nan take tayi wani silent kamar ba ita ba.

Ai kuwa Hafeeza ta samu Abunda take So Saida tayi dariya mai isarta sannan ta dawo kusa da Shabana ta zauna, cikin serious voice tace "ke uwar tsoro kwantar da hankalinkii ba Abunda zai faru, Wallahi haj Mama taimakonki take ba sharri ba, nima da kikaga ina dariya kawai ina yi ne dan na ƙara tsorata ki, ki saki jikinki duk Abunda Haj Mama ta baki ki karɓa kisha ƙima da darajar kine, haj Mama ƴar asalinsa sokoto ce bakiga komai ba ma sai kin tare gidanki zakiga irin waɗan nan abubuwan" kallonta Shabana tayi tace "nifa ban yarda dake ba Hafeeza" murmushi Hafeeza tayi tace "kar Allah yasa ki yarda" wayar Hafeeza ce tayi ƙara no ɗin ta Kalla ba Suna saida aka ƙara kira tayi picking tare da karawa a kunnenta, muryar Haidar taji yayi sallama, amsawa tayi, ɗan Jim yayi yace "dan Allah idan da hali kifito parking lot zamuyi magana" ya mutsa fuska tayi tace "ina wani abune" yace "plx ba jimawa zakiyi ba" tace "Okey katse Kiran tayi tare da cewa "ba inda zanje" kallonta Shabana tayi tace "Haidar ne ko?" Gajeren tsaki tayi tace "eh shine wai naje parking lot zamuyi magana, ni ba inda zanje" Shabana tace "dan Allah kije Goty bakisan maganar da zaiyi ba" Hafeeza tace "bazanje ba" da kyar Shabana ta lallaɓata ta tafi.
Tana fita Shabana tashiga toilet tayi wanka tana fitowa ta gyara jikinta tasa kayan bacci riga da Wando dogaye har kasa marasa nauyi.
Kayansu tafara haɗawa guri ɗaya dan tasan gobe tafiyar safe zasuyi, takardar da Shadow ya bata ta gani, murmushi tayi tare da ajeta gefe saida ta kammala haɗa kayan tas ta cire wa ƴanda zasu saka gobe.

Kan gado ta koma ta kwanta tare da ɗaukar wayarta da take gefe, miss calls ta gani from Endocardium 💞 murmushi tayi aranta tace "ayyyaaah kayi haƙuri na saka wayar silent ne" ji tayi an turo ƙofar an shigo, ba tare da ta Kalli ƙofar ba tace "har an gama soyayyar kenan? Muryar Shadow taji yace "yanzu dai za'a fara" ai da sauri ta tashi zaune ta kalleshi, gurinda take ya nufo, kalle kalle ta fara tana neman Hijab ɗin da zata saka, ba wani Hijab agurin ƙoƙarin tashi tayi daga kan gado Shadow ya riƙe ta yana Murmushi yace "ina zuwa Auta? ba zaki tsaya muyi bankwana ba?" zama yayi very close to her, yace "bakiga miss call ɗina bane?"shiru tayi kamar bataji Abunda yace ba.
Wani kallo ya fara binta dashi kamar wanda yake so ya tantance wani abu ajikinta. Jitayi gabaki ɗaya ta takura, cikin sanyin murya tace "dan Allah kabari nasaka Hijab sai muyi Magana" ƙara riƙe ta yayi sosai yace "keda waye a ɗakin da har kike neman Hijab beloved? naga ni Mijinki ne idan muna tare ba wani Hijab da zaki buƙata, a haka kinfi min kyau" yafaɗa yana zame hular kanta, hannunsa ya cusa cikin gashin kanta ya ware shi gabaki ɗaya, a hankali yace "meyasa baki son kitso" cikin sanyin murya tace "zafi nakeji, kuma bana jure zaman kitso" murmushi yayi yace "ke raguwa ko? ki shirya dan nikam kitso nake so yafi kyau" "toh" tace tana ƙoƙarin janye jikinta dan Allah yasani a takure take.
Ƙara matseta yayi yace "ba inda zakije kamata ma yayi yau mu kwana tare tunda gobe da safe zaku tafi" ajiyar zuciya yayi yace" Allah ji nake kamar karki tafi zanyi masifar kewarki" murmushi tayi batare da tace uffan ba.

A hankali ya cusa kansa gefen wuyanta yana shaƙar kamshin jikinta, lumshe Idanunsa yayi cikin cool voice yace "ina son wannan kamshin turaren na jikinki sosai" murmushi tayi tace "ba turare bane Humrace" cikin wata irin murya taji yace "ina so kici gaba da sakawa kinji" kasa amsawa tayi jin hannunsa na yawo ko ina ajikinta, kuma ta rasa dalilin da yasa takasa hana shi.
Fuskarta ya riƙe sosai tare da kai tasa fuskarsa kusa da tata, da sauri ta rufe idanunta dan tasan duk yadda tayi bazata iya kwacewa daga hannunsa ba.
Halshensa yasa a hankali yana lasar fuskarta, yana zuwa kan lips ɗinta ta manne su sosai, murmushi yayi tare da sa halshensa ya danne mata hanci, da sauri ta saki bakinta jin numfashinta ya kusa ɗaukewa.
Murmushi yayi tare da kama lips ɗinta ya fara tsotsa kamar ya samu lollipop, har wani zaki zaki yake ji cikin bakinta hakan yasa yaƙara matseta a jikinsa ya ci gaba da kissing ɗinta.
A hankali ita ma tafara mayar masa da martani, halshensa da yake yawo a bakinta tafara tsotsa, nan take Shadow ya ƙara narke Mata yana sauke ajiyar zuciya.
Sun ɗauki lokaci Suna abu ɗaya, Shadow yafara ƙoƙarin cire mata riga, da sauri ta riƙe masa hannu, cikin wata irin murya kamar wace ta farka daga Bacci tace "plx karka cire loveline" ƙara matseta yayi a hankli yakai bakinsa daidai kunnenta ya ya raɗa mata wasu kalamai, murmushi tayi. Bayana wasu ƴan mintina Shabana ce kwance a jikin Shadow, yasa hannunsa ya rungumeta sosai yana sauke ajiyar zuciya, murmushi yayi yace "yau da ace normal kike ko uhm da sunanki sorry" fuskarta ta tura cikin ƙirjinsa tana ɓoye wa. Murmushi yayi yace "ki buɗe fuskar mana" duvet taja ta rufe jikinta tare da sauka Saman ƙirjinsa ta kwanta gefe.
Jawota yayi ta noƙe, murmushi yayi yace "wai kunya kikeji? Allah Idan baki buɗe fuskarki ba zan yaye blanket ɗin gabaki ɗaya" Shiru tayi kamar bataji Abunda yace ba, Saida taji ya fara ƙoƙarin yaye blanket ɗin ta fitar da fuskarta da sauri, kamar zatayi kuka tace "plx kayi haƙuri dan Allah" murmushi yayi yace "na daina karki min kuka plx" Runtse idanunta tayi saboda wata irin kunyarsa takeji yanzu Amma shi ta lura ko ajikinsa.
Sauka yayi daga kan gadon yace "ina zannen yake" batare da ta buɗe Idonta ba tace "yana kan bedside" ɗauka yayi ya buɗe ya duba, ya Maida kallonsa kanta yace "yanzu haka zan tafi kin wani kama fuska kin rufe" a hankali tace "katafi zamuyi waya" murmushi yayi yace "inada Babban aiki a gabana Kenan, wannan kunyar haka ai ni zaki cuta" Shuru tayi, sallama yayi mata tare da fita daga ɗakin.
Saida ta tabbatar ya fita sannan ta buɗe fuskarta, rigarta ta ɗauka ta saka tana tunanin Abunda ya shiga tsakaninsu yanzu nan, aranta tace "Ashe ba salihi bane ina Masa kallon shuru shuru ashe iya shege ne fall cikinsa" sauka tayi daba kan gadon ta fara gyarashi dan tasan muddin waccan jarabbiyar ta dawo taga gadon haka sai ta samu Abunda tace.
Tana kammala gyaran ta kwanta sai ga Hafeeza tashigo, kallonta tayi tace "iyayen soyayya sai yanzu aka dawo kenan?" Murmushi Hafeeza tayi tace "ku kuma iyayen tsotsetse sai yanzu aka kammala ke nan" aranta tace "ai yau ma ya wuce tsotsetse" a fili kuma tace "an gaya miki kowa irinki ne" dariya Hafeeza tayi tace "ai tunda naga ya shigo ɗakin nan nasan Abunda zakuyi kenan, karin abun ma gobe gida zamuje shiyasa na ƙara baku lokaci ku gana da kyau" Hafeeza ta faɗa tana ƙanne Idonta ɗaya. Kai Shabana ta girgiza tace "Allah ya jiƙan Haidar Badan ya Mutu ba" ameen tafaɗa tare da shiga toilet.


11:28 kwance yake yana juyi Bacci ya kasa ɗaukarsa ba abunda yake gani cikin idonsa face halittar Shabana lumshe Idanunsa yayi na ɗan wani lokaci yana tunanin romance ɗin da sukayi ɗazu, nan take yaji tsigar jikinsa na tashi, wayarsa ya ɗauka tare da Nemo no ɗinta ya kira.

Cikin Bacci taji kamar wayarta na ringing a hankali tasaka hannunta ta ɗauka tare da karawa a kunne.
yace "Har kinyi bacci?" Tace "eh" gyara kwanciyarsa yayi yace "kiyi haƙuri da tashinki da nayi, nima gani nan kin hana Idona rintsawa, ba abunda yake yawo acikinsu face ke da kuma kyakywar surarki" uhm kawai tace.
Yace "Allah Idan baki buɗe baki kikayi Magana ba zanzo har ɗakin naku yanzu, nasan Idan nazo Hafeeza fita zatayi" cikin shagwaɓa tace "to Mai zance maka Nikam" "Idan nayi Magana ki buɗe baki ki bani Amsa" fira sukayi sosai har baccin da ke idanunta ya fita.





Tinda sukayi Sallah asuba basu kwanta ba suka hau Shiri.
Gabaki ɗaya parlour suka taro Banda Ahanaf.
Abba yace "Ina Ahanaf me ya tsaya jira har yanzu? Ƙaseem je ka Kira shi" Haj Mama tace "a'a Muhammad bari dai Matarsa taje ta kirashi" maida kallonta tayi kan Shabana tace "daughter je ki kira Ahanaf yazo kuyi sallama" Shabana Ji tayi kamar ta ɗaura hannu aka ta kurma ihu tsabar kunya.
Ba yadda ta iya dole ta nufi hanyar ɗakinsa.
Tana zuwa tura ƙofar tayi tare da sallama.
Mamaki ne ya kamata ganinsa zaune yana danna laptop ɗinsa, shiga tayi cikin ɗakin ɗagowa yayi ya kalleta yace "har kun shirya?" Harararsa tayi tace "kai muke jira kazo ka shirya mu" murmushi yayi yace "Allah ya baki haƙuri" matsowa yayi kusa da ita yace "wallahi ji nake kamar naje na cewa Abbu Abar min Matata ba inda zaki tafi" murmushi tayi tace "kaje ka faɗa masa mana" murmushi yayi kawai Batare da yace uffan. Wani zobe ya ɗauko kan table mai masifar kyau har wani shining yake, hannunta yakama mai bima ƙarami ya saka mata zoben, masha Allah ya faɗa tare da kai hannunta kan bakinsa yayi kiss ɗin sa.
Murmushi tayi tace "Nagode sosai Allah yaƙara buɗi na Alkhairi" murmushi yayi tare da matsawa dab da ita yasa hannunsa ya kama ƙugunta ya matso da ita jikinsa.
Kallonsa tayi tace "muje su Dady sun fito zamu tafi" cikin sanyin murya yace Jinake kamar kar kitafi, gaskiya bazan iya jiran wata biyu ban ganki ba" hannunta ta kai kan fuskarsa ta fara shafa sajensa har zuwa gemunsa, cikin sanyi murya tace "zamu dinga waya Insha Allah, nidai burina ɗaya ka Maida hankali kan Abunda kake ka koma gurin aikinka, sannan ka riƙe Askhar insha Allah bazaka tozarta ba" murmushi yayi yace "Nagode sosai Allah yayi miki Albarka, mai zaki bani wanda zan dinga tunawa naji sanyi araina" murmushi tayi tace "mai kake so?" Yace "Abunda kikasan zanyi farin ciki sosai Idan kika mun" murmushi tayi tare da matsa fuskarta dab da Tashi lips ɗinsa ta kama tafara tsotsa a hankali tare da lumshe Idonta.
Da sauri Shadow ya rungumeta yanajin yadda Shabana take zuba masa wani sassanya kiss mai kashe jiki.
Saida tayi kissing ɗinsa sosai Sannan ta janye jikinta daga nashi.
Da sauri ya maidata yaƙara rungumeta kamar zai tsaga ƙirjinsa yasata yakeji.
Tace "muje loveline ana jirana" ba yadda Shadow ya iya haka ya kama hannunta suka fito daga ɗakin, kwace hannunta tayi tace "Idan kai bakajin kunya ni inaji" murmushi yayi yace "zaki daina kunyar kema indai muna tare" ko da suka fito parlourn ba kowa comfort ɗin gidan suka fito har kowa ya shiga mota ita kaɗai ake jira.
Suna zuwa Abbu yace "ai da karka fito da ita kaci gaba da riketa kai ga mai mata ko?" Kansa yaɗan Sosa yace "ayi haƙuri Abbu" Haj Mama ta kama hannun Shabana suka ɗan matsa daga gurin Shadow, takai bakinta daidai kunnenta tace "saƙon ki yana cikin Mota, dan Allah kidinga sha kinji, takarda tana ciki na rubuta miki yadda zakiyi aiki da kayan, Sannan zan

Please Login or Register in order to submit comment