Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsaye yace "muje kimin wanka" hannu tasa ta rufe fuskarta, murmushi yayi yana ƙoƙarin tayar da ita tsaye yace "plx muje beloved" cikin sanyi murya tace "nidai a'a katafi kayi abunka zan jiraka" yace "nifa yau sai kimin wanka" ganin da gaske yake yasa tace "to kaje kayi wankan idan ka fito zan shafa maka Mai" murmushi yayi yace na yarda.
Har yafara tafiya ya tsaya yace "kizo muje to" a hankali tace "kaje zanzo akwai Abunda zanyi yanzu" ɓata fuska yayi yace "alƙawari?" Murmushi tayi tace "insha Allah"
Koda ta koma ɗakinta wayarta ta ɗauka ta kira Hafeeza bayan sun gaisane Hafeeza tace "Malama ya da kiran dare haka? Jeki kama Mijinki yafi miki wani sunne sunne, nasan halinki da mugun raki, dan Allah ki dinga daurewa kinji Sulty ko wace Mace da kike gani gidan miji da haka ta saba" murmushi Shabana tayi tace "kinji min mata ƴar rainin hankali ke ina kikasan duk wannan" Hafeeza tace "inda kika san gulma" suna cikin firar taji an turo ƙofar an shigo, kallon ƙofar tayi taga Shadow sanye da rigar wanka, kawar da kanta tayi tare da cewa "Hafeeza zan kiraki da safe Goty" murmushi Hafeeza tayi tace "nattaccen naki yazo kenan, Allah ya tashemu lafiya" murmushi tayi tare da katse Kiran ta kalleshi. hararar wasa yayi mata yace "haka ake alƙawarin" murmushi tayi tare da tashi ta nufi gurinda yake tace "tohm shigo na cika alƙawarin shikenan?" Kafaɗa ya make kamar wani ƙaramin yaro yace "Ai man shafawata Yana ɗakina muje can ki shafa Mun" ɗan Jim tayi sannan tace "tohm muje ɗin" koda suka shiga ɗakin nasa direct dressing mirror suka nufa, kollon mayukan shafawar tayi tace "wannan menene banbancinsu da na matan" murmushi yayi tare da warware rigar jikinsa ta faɗi ƙasa, sunkuyar da kanta tayi ƙasa, murmushi yayi tare da kai hannunsa yana ƙoƙarin zare gajeren Wandon jikinsa da sauri ta riƙe masa hannu cikin rawar murya tace "dan Allah karka cire" murmushi yayi tare da janye hannunsa dama tsokanarta yake.
Hijab ɗin jikinta yayi ƙoƙarin cirewa batayi yunƙurin hana shi ba cox tasan bazai bari ba.
Wata ajiyar zuciya yasauke tare da kara zuba mata idanunsa yana kallonta, cikin jin kunya tace "nidai bana son kalar wannan kallon" dariya yayi yace "tohm na daina shafa min man Bacci nakeji sosai" a hankali ta buɗe man ta fara shafa masa, idonsa ya lumshe yana jin yadda hannunta ke zagaye ko ina na jikinsa.
Ji yayi ta dakata da shafan, a hankali ya buɗe idanunsa da suka fara sauya kala yace "lafiya kika daina" murmushi tayi tace "na gama shafa maka ne shiyasa" jawota yayi ya rungumeta yafara shaƙar kamshin jikinta tare da shafata ta ko Ina, taso ta kwace Kanta Amma tuno na nasihar danginta yasa tabarshi yaci gaba da shafata, lips ɗinsa yakai kan nata yafara kissing ɗinta cikin wani irin Salo na musamman, nan take saƙonsa yafara ratsa sassan jikinta a hankali tafara mayar masa da martani, nan take yaƙara hargitse mata, a hankali ya fara Janta har bakin bed suna zuwa yafaɗa kan bed ɗin tare da ƙara rungumeta yana murza ta son ransa ita ma haka.



Wannan karon ma taji zafi sosai but bakamar farkon ba, janyota jikinsa yayi ta zille, dariya yayi cikin tsantsar farin ciki yace "Menene beloved?" Fuskarta ta rufe alamar kunya, dariya yayi tare da sauka daga bed ɗin yace tashi muje muyi wanka.
Hannu yasa ya tayar da ita suka shiga toilet ɗin, ruwan zafi ta fara shiga ta jima ciki sannan ta fito tafara wanka.
Taga tsantsar rashin kunya a gurin Shadow, Saida ta zulle masa ta fito daga toilet ɗin, sannan shima ya fito.





Sosai suke sunama junansu soyayya, zaman Aure suke Wanda yake cike da fahimtar Juna, Ko wannensu so yake ya nunawa ɗan uwansa ya damu dashi hakan yasa suke cikin farin ciki.







Shiri take cikin sauri koda tafito baya parlour direct bedroom ɗinsa ta nufa, sallama tayi tare da tura ƙofar tashiga, sallamar ya Amsa yana zuba mata wani mayataccen kallo, gabansa ta matsa cikin shagwaɓa tace "haba loveline dan Allah ka fito mutafi, na matso muje naga Haj Mama, tinda fa nazo gidan nan sai yau zan fita ai nayi ƙoƙari Allah" dariya yayi tare da janyota jikinsa yace "Masha Allah kinyi kyau sosai beloved wife" murmushi tayi tace "Nagode sosai, muje plx" ƙugunta ya kama ya matso da ita dab dashi, ɓata fuska tayi tace wai mekake jira ne....... Bai bari ta ƙarasa ba ya haɗe bakinsu kissing ya fara zuba mata masu tarwatsa harda, a hankali yafara ƙoƙarin zare zip ɗin jikinta.
Daga ƙarshe dai sai da Ahanaf yayi nasarar ɓata mata wanka, sauka tayi daga bed ɗin tana tura baki gaba alamar tayi fushi, toilet ɗinsa ta nufa.
Murmushi yayi tare da bin bayanta Amma saidai me yana tura ƙofar yajita a rufe, murmushi yayi.
Daga ita sai wani gajeren towel ta fito ko kallon gurinda yake batayi ba tanufi hanyar fita daga ɗakin, murmushi yayi sannan shima yashiga yayi wankan.
Yana fitowa yafara Shiri sauri sauri cox yasan idan ya juma ba ƙaramar rigama Shabana zatayi masa ba.


Suna tafiya cikin Mota yana tsokanar ta shareshi tayi kamar bada ita yake ba, ganin tayi masa banza yasa yace "Oh su Auta manya dan Allah yanzu menene laifina anan bayan kece kika.... Dukan wasa takai masa tana Dariya tace "nidai ka daina bana so" murmushi yayi yace "na daina ranki yadaɗe da girman kujerarki" yafaɗa yana yimata yadda ake yiwa sarakuna. Murmushi tayi tare da girgiza Kanta tace "Allah ya shirya min kai loveline" ameen ya Allah beloved.


Koda suka Isa gidan Haj Mama rasa tayi gurinda zata ɗaura Shabana, kallon ƴar cikinta take Mata, cox kumi na Shabana yayi mata nutsuwarta sanin yakamata da kuma kunyar ta.


Tsarabar da Shabana tayi musu ce tabawa Haj Mama tace "turarukan nasu Abbu ne sauran kayan kuma naki ne" sosai Haj Mama taji daɗin kyautar Shabana, tayi Mata godiya da addu'a sosai.

Sai around 9 suka fara Shirin tafiya gida, Haj Mama taja hannun Shabana ɗaki, Shadow yace "dan Allah karku juma Mama dare fa yayi" Haj Mama tace "katashi ka tafi ita anan zata kwana" Dariya yayi yace "Ai Saidai mu kwana nan ɗin gabaki ɗaya" kai Haj Mama ta a girgiza tace "ai yanzu duk abunda zakayi Bazanyi mamaki ba, Cox kagama zarewa" Suna Tafiya cikin Mota ya kalleta yace "wai kuskus ɗin mai kuke keda Haj Mama ne?" Murmushi tayi tace "Ina ruwanka kaji min saka eyes" yace "Idan ta ruɓa maji" tace "bazama ta ruɓan ba in sha Allah.

Koda suka Isa gida wanka kawai sukayi suka fito Parlour suka fara fira, wacce ba abunda suke sai jaddada ƙaunar da suke ma junansu........✍️✍️✍️









Nabeela Binji ce💃💃💃







More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏.




♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM



PAGE

5️⃣ 3️⃣

















______________Wanka tayi tasaka wasu ƙananun kaya karamar riga da three quaters direct ɗakin Shadow ta nufa, ɗebo kayan drawing ɗinsa tayi ta dawo ɗakinta.
Tace "I am not a good artist but I am going to try my best. Ta zauna a nutse ta fara zane, sai da ta dauki 3 hours sannan ta gama, ta tafi parlour ta dauko fresh milk ta dawo ta zauna tana duba zanen da tayi. Ahanaf ne a tsaye, da sleeveless riga a jikinsa da three quaters wando. Ya zura hannayensa a aljihunsa ya dan juya kansa yana kallon side ɗaya. Fuskarsa ɗauke da murmushi. Yayi kyau sosai kamanninsa sun fito dan duk wanda ya sanshi in yaga zanen zai gane shi. ( naso ace na iya zane dana zana muku. Lol 😜😆😂). Kitchen tashiga da ɗaura girkin yamma tana kammalawa Ana kiran Magrib jeresu tayi a dinning table, ɗaki tashi direct bathroom tashiga tayi wanka tayi alwala, Saida tayi Sallah sannan tafara shiri simple makeup tayi tasaka ƙananun kaya sunyi masifar yi mata kyau, tana ƙoƙarin fitowa daga ɗakin taci karo da Shadow zai shigo, jikinsa ta faɗa tana murmushi tace "barka da zuwa loveline ya aiki?" Murmushi yayi tare da saka hannayensa ya ƙara rungumeta yace "lafiya ƙalau beloved ya kewa?" Kwaɓe fuska tayi tace "kaima kasan dole nayi" murmushi yayi yace "nasani beloved, muje ki rakani nayi wanka nagaji sosai."


Zaune yake akan kujerar dinning ita kuma tana kan ƙafarsa, abincin sukeci suna fira, cikin shagwaɓa tace "dan Allah loveline kabarni naje naga lefen Goty Allah na ƙosa naje Katsina." Murmushi yayi yace ki kwantar da hankalinkii beloved akwai Abunda nake shiryawa ne, insha Allah zaki tafi Katsina bada jimawa ba, so nake bikin yarage saura one week sai mutafi kinga shirye shiryen komi dake za'ayi, wannan dalilin ya hana na barki kije ganin laife" gyaɗa kanta tayi duk da haka baiyi mata daɗi ba, cikin sanyi murya tace "Allah yakaimu lokacin" murmushi yayi ɗaya daga cikin halinta Kenan da yake burge shi, duk yadda yayi mata umarni da abu zatabi koda hakan baimata ba.
Bayan sun gama ciki Abincin ne suka dawo parlour suka zauna suna fira, kallonta Shadow yayi yace "uhmmm beloved kinji wata Magana gwanin ban dariya" kallonsa tayi taba Murmushi tace "a'a sai kafaɗa me yafaru ne hala?" Dariya yayi sosai sannan yace "ranar Friday Abba zaiyi Aure wai" Yanayin yadda yayi maganar ne ya bata dariya, harararsa tayi tace "tohm menene Haram ne ai gwara yayi aurensa" murmushi yayi yace ai Abbu ne ma ya tilastashi but shi baiyi niya ba, ƙanwar Haj Mama ce zai Aure mijinta ya rasu shekara ɗaya da ya wuce, shine fa Abbu yace "Abba ya Aureta" Shabana tace "Allahi Allah yasa haka shine mafi Alkhairi" yace "ameen ya Allah yawwa ɗazu nayi waya da Suhail yace su Abdul zasu dawo bada jimawa ba, Allah yasa yayi daidai da bikin Hafeeza kinga sai musha zama Katsina muga ƴan uwa kafin mudawo" murmushi Shabana tayi tace "nima haka ya Abdul Haleem ya faɗa min, gaskiya da nayi farin ciki loveline"
Murmushi yayi.
Kallonsa tayi tace "muje ɗaki na nuna maka wani abun" murmushi yayi tare da tashi tsaye yace muje nagani Hajiyata" suna zuwa ɗakin ta zaunar dashi gefen gado, papper yaga ta ɗauko Ido ya zuba mata har ta zauna kusa dashi, a hankali tafara ware pepper, Ido ya zuba Mata yana kallonta bako kyabtawa, "Wow masha Allah" yafaɗa fuskarsa ɗauke da yalwataccen murmushi, pepper ya karɓa yana yaba Zanen yace gaskiya ke ƴar baiwace Shabana Zanen ya zanu sosai kuma kinyi ƙoƙari Nagode Allah yayi miki Albarka, yanzu ni yarage na zanaki" murmushi tayi.
"Kinsan yadda zan zanakin?" Kai ta girgiza masa Alamar a'a, dariya yayi yace "yadda bazan taɓa zana kowa ba har Abada, kuma Idan nayi zaren dagani sai ke ne kawai zamu gani" ta fahimci yadda yake nufin baki ta tura gaba tace "bana so gaskiya" murmushi yayi yace "nikam sai na zana wannan kyakywar halitta mai ruɗu bawan Allah" murmushi tayi.


Yau Ahanaf yana gida ba inda yaje, Saboda mutuniyar tasa ta wayi gari da zazzaɓi, yace suje hospital taƙi yadda, dama ya matsa mata sai ta saka masa kuka, wannan dalilin yasa yakira Dr Maryam tazo ta dubata.
Murmushi tayi tana kallon Shadow cikin zoyala tace "Allah yataimaki baban baby" kallonta yayi cikin mamaki da son ƙarin bayani, ganin bai fahimce ta bane yasa tace "Matarka tana ɗauke da cikin na wata biyu" wani Yanayi yafara ji kamar wanda yake yawo a gajimare cikin tsantsar farin ciki yace "alhmdllh ala kulli halin alhmdllh ya man layyadid walan wulad" kallonsa ya maida kan Shabana wace taja bargo ta rufe fuskarta tun lokacin da taji furucin Dr Maryam, tarasa a wane kallar Yanayi take ciki.
Murmushi Dr Maryam tayi tare da cewa "Allah ya saukeki lafiya, ni zan tafi Idan taji wani sauyi sai ka kirani nazo na dubata" Murmushi Shadow yayi yace mungode sosai Dr, dan Allah ki turumin account number ɗinkin zan tura miki Kuɗin petrole" godiya tayi masa sosai kafin ta fita daga ɗakin.
Kallonsa ya maida kan Shabana yana zuba wani ƙayatatten murmushi gadon ya hau tare da fara yaye blanket ɗin, hannu tasa ta rufe fuskarta wai ita ala dole kunya takeji.
Hannayenta ya janye yana murmushi yace Mai zanyiwa wannan yarinyar na saka Alkhairinta a gareni? Allah yayi Miki Albarka Shabana Allah ya saukeki lafiya yabamu Yara masu Albarka" murmushi tayi tare da kai hannunta ya shafa gemunsa cikin tsantsar farin tace "Ameen ya Allah Mijin Shabana" murmushi yayi.
A daren Ranar Shabana taga tsantsar soyayya agurin Shadow ya nuna mata ƙauna tabbatacciya.



Shadow yarasa inda zai ɗaura Shabana yarasa Abunda zaiyi mata ya tabbatar da farin cikin da yake ciki.
Mota ya saya Mata sabuwa dal, RR tayi masifar kyau, lokacin da yabata key ɗin takasa ɓoye farin cikinta, tsale kawai take tana murna da sauri ya riƙe ta yana mata hararar wasa yace "kin Manta da farin cikina anan?" Yafaɗa yana shafa cikinta, murmushi tayi.



Kiran Hafeeza tayi bayan sun gaisa Shabana tafaɗa "Matasaya Mata Mota" tayi farin ciki sosai tace "Allah yasanya Alkhairi Goty, but nida kika ce albishir na zata dan Baba muka samu" tafaɗa tana dariya. Murmushi Shabana tayi tace "harda shi kin Samu" Hafeeza tace "kai masha Allah Amma gaskiya nayi farin ciki sosai Sulty Allah ya bamu rayayyu masu Albarka" murmushi Shabana tayi, cikin tsokana Hafeeza tace "yanzu ke dan Allah bakijin kunyar aganki da ciki?" Dariya Shabana tayi tace "kunyar mai zanji Goty ɗan sunna ne fa" sun jima suna fira kafin suyi sallama.

Hidaya ta kirata tana zuba mata dariya tace Allah ka nunamin Ranar da cikin wannan mara kunyar zai tsufa, naga ƙarshen iskanci" murmushi Shabana tayi tace "Ai ki kwantar da hankalinkii zaki gani saraunyar gulman Katsina" dariya Hidaya tayi tace "indai akanki ne ki ƙaramin matsayi ma dan nafi haka"

Maganar cikin Shabana yagama karaɗe dangi, inda Kowa yake mata fatan sauka Lafiya.
Haka Ammi zata kirata tana bata shawara yadda zata kula da cikin jikinta, tanajin daɗin haka cix abubuwa da yawa bata sani ba sai Ammi ta faɗa mata.












Shiri take cikin sauri ɗakin ya shigo ya ɗauki trolley ɗin yace kiyi sauri mutafi beloved lokaci yana tafiya kar flight ɗin ya tashi, phone ɗin ta ɗauka da bag tace "ai na shirya loveline, mutafi"
Koda Audu driver yakaisu airport sauran ƴan mintina jirgin ya tashi.

Koda suka sauka Katsina ya Suhail ne yaje ya ɗaukosu, kallonsa tayi tace "dan Allah yayi ka taka motar mana na matso naje naga su ya Abdul" harara ya zuba Mata yace "badai kinzo ba shikenan kowa zaiga ta kansa da rigimarki" kallon Shadow yayi yace "Ahanaf ya kake fama da wannan yarinyar?" Murmushi Shadow yayi yace "aini bana fama da ita duk Abunda tayi na ɗauka kuma bana kallonsa a matsayin laifi" baki ya Suhail yasaki yace "Lallaima Ahanaf wato ƙara sangartata kake ko?" Murmushi yayi yace "dole na sangartata Suhail ni ba abunda ba zan iya yima beloved ba Cox ita ce fitilar rayuwa ta" haɓa Suhail yarike ɗayan hannunsa yace "kunfi ƙarfina"



Koda suka Isa gida da gudu tashiga cikin gidan, tana kwalla Kiran Ammi Ammiiii!!!, Su Abdul da suke Zaune parlour suka bita da kallo, Abdul Haleem yace "wannan yarinyar dai Kam ba ƙaramin abu bane zaisa tayi hankali" Abdul Hameed yace "Lallaikam" zuwa tayi ta rungumesu cikin matsanancin farin ciki tace "I really miss you brother's" Suna cikin haka Ammi tashigo parlourn da sauri tayi kanta ta faɗa jikinta, murmushi Ammi tayi "na shiga ukku har yanzu Auta taƙi ta girma duk da girman ya bayyana ajikinta" Ammi ta faɗa tana karewa ƴar tata kallo. Baki ta tura gaba tace "Ammi naga alamar bakiyi kewata ba" Murmushi tayi tace "nikuwa nayi kewar rigimarki Shabana" kallonta ta maida kan Ahanaf da yake gaisheta, amsawa tayi cikin farin ciki tare da tambayarsa su Haj Mama.
Murmushi yayi yace "lafiya ƙalau sunce a gaisheku" muna amsawa.


Sosai Shabana take cikin farin ciki ganin danginta cikin ƙoshin lafiya, har Hidaya tazo gidan da ya Maleek anan suka taru kowa yana faɗin Albarkacin bakinsa.



Da ƙarfe 5am suka Isa gidansu Hafeeza, tana shiga gidan Hafeeza tazo da gudu ta rungumeta, cikin farin ciki suke gaisawa, Hafeeza ta Kalli Shadow tace "mijin tace sannunku da zuwa" dariya yayi yace "daga zuwana bazaki barni na huta ba sai tsokana ko?" Murmushi tayi. Tare dakai hannu ta shafa cikin Shabana tace "hello my baby" murmushi tayi tace "harda Yaron ciki sai kinyiwa iya shege."
Sunyi fira sosai kamar kar su rabu lokacin da Shadow yazo ɗaukar Shabana saida yayi da gaske sannan suka fito suka tafi.



Kwance take kan gadonta suna fira cikin shauƙin Sonta yace "beloved gobe ina so mukae ziyara gidan Man da muka fara haɗuwa" murmushi tayi tace ba matsala Allah yakaimu lafiya.




Saida Yamma suka Isa gidan man parking yayi yana bin Zanen da kallo, nan take hawaye suka wanke masa fuska murmushi yayi a hankali yace "alhmdllh Allah kaine mai tsara komai a yanda kaso kaine ka haɗani da jarumar mata mai halin Mutanen da sadaukarwa tausayawa Imani ke ta musamman ce beloved" yaƙarasa maganar yana zuba mata manyan idanunsa.
Murmushi tayi tare da kai hannunta ta share masa hawayen fuskarsa, "nima wannan Abun da yafaru yazama Alkhairi a rayuwata Cox yayi sanadiyar haɗani da irin Mijin da najima ina muradin samu."

Sunyi pictures sosai agaban Zanen duk da cewa ya ɗan fara gogewa, sunyi yawo sosai sun tafi gidan ya Maleek da ya Suhail Sai dare suka koma gida.


Shirye shiryen biki ya kankama, Amarya Hafeeza tasha gayara ta ko ina, koda yaushe Shabana tana hanyar gidansu Hafeeza.
Anyi shagalin biki sosai ango Haidar Sai rawar kai yake.

Su Shabana Saida sukaje Gombe kai amarya lokacin da zasu tafi da sauri Hafeeza ta riƙe hannu Shabana cikin rawar murya tace "plxx ki taimaka ki kwana anan Sulty" wata dariya ce ta suɓuce ma Shabana, tace "haba jaruma ai kince ba abunda kike Shakka, Allah yabada zaman lafiya ya bama Haidar Sa'arki, ki samo muna ƴan huɗu" duk son masifar Hafeeza yau tazama wata silent.

Saida suka kwana biyu a Gombe sannan suka dawo Katsina.
Bayan kwana biyu suka fara shirin dawowa gida..........✍️✍️✍️













Nabeela Binji ce💃💃💃







More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏.


♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM



PAGE

5️⃣ 4️⃣










Last page insha Allah 😍😍






______________ Rayuwa taci gaba da Tafiya cikin farin ciki da Annashuwa, sosai Shabana take samun kulawa agurin Shadow, cikinta ba ya wani wahalar da ita saidai kwaɗayin masifa da take fama dashi bata cin Abinci saidai kayan makulashe.


Shadow kuwa alhmdllh tako ina Kiransa Ake ana bashi kwangilar Zana gidajen gomnati, company, masana'antu e,t,c.


Norr da ƙaseem suna zamansu lafiya cikin farin ciki, suna kula da Junansu sosai, baby Amma Kuwa tayi wayau Idan kaganta sai tashiga ranka.
Akwai fahimtar Juna sosai tsakanin Shabana da Norr suna Zaman lafiya da girmama Juna.



Koda cikin Shabana yakai wata Tara, ta kunbura sosai, Idan ka ganta sai ka tausaya mata.
Shadow ya daina fita aiki Zanen ma a gida yakeyinsa Saboda baya so Shabana ta Wahala ko kaɗan, duk aikin gidan shine yakeyinsa cox Shabana tayi nauyi sosai.








Wata Ranar Monday da dare na ƙuda ta tayar da Shabana, safa da Marwa kawai take cikin ɗakin, kamar ance Shadow ya buɗe idanunsa ya hangota har tafara galabaita, da sauri yayi kanta cikin tashin hankali yace "subhanallah mai yafaru ne beloved?" Kasa Magana tayi sai murƙususu take zufa na keto Mata.
Ganin tana Wahala ne yasa ya tashi ya ɗauki Jallabiyarsa yasaka mata hijab ɗaukar yayi da sauri ya kaita Mota cikin tashin hankali yake driving gabaki ɗaya ya ruɗe kai tsaye asibitin Uduths ya nufa da ita.


Suna zuwa aka karɓe ta direct labour room aka nufa da ita, Shadow sai Safa da Marwa yake yana addu'a da fatan Allah ya sauke matarsa lafiya, hannu yasa cikin aljihunsa zai ɗauko waya Amma baijita ba. Sun Jima sosai akan Shabana.
Da sauri ya juya jin an buɗe ƙofar, cikin sassarfa yayi kan Dr yana tambayarsa ya Shabanan, hannunsa Dr ya kama yana murmushi yace "ka kwantar da hankalinka Matarka ta sauka lafiya ta samu Yara Mata biyu, kuma alhmdllh bawata matsala sai hamdala" wata ajiyar zuciya Shadow ya sauke farin cikin da yashiga baki yayi kaɗan ya bayyana, hanyar ɗakin ya nufa da sauri Dr ya riƙeshi yana murmushi yace "kaɗan jira ana gyara Yaran da mahaifiyarsu ne" murmushi Shadow yayi tare da bin bayan Dr zuwa office.




Koda yashiga ɗakin zaune take ta jingina bayanta da gado, cikin sassarfa yaƙarasa gabanta gefen gadon ya zauna tare da rungumeta yana murmushi, janyeta yayi daga jikinsa yana bin ilahirin jikinta da kallo, baki ta tura gaba tace "wannan kallon fa" murmushi yayi yace "Allah mai Iko Autar Ammi ce da haihuwar Yara har biyu, Shakka Babu Allah kadaine maiyi, Banida abunda zancewa ubangiji sai godiya" Tashi yayi ya ɗauko yaran dake ta sharar Bacci, akan ƙafarta yadaura Mata ɗayan ya rungume ɗayar ajikinsa, wace ya ɗaura mata kan ƙafafunta ce ta farka tafara kuka, murmushi Shabana tayi tare da janyota jikinta tana jijjigata, but taƙi tayi shiru, kallonta yayi yace "plxx ki shayar da ita beloved" a hankali ta gyarata ta fito da breast ɗinta tana ƙoƙarin saka mata a baki, Ido Shadow ya zuba musu cikin wani irrin farin ciki tabbas Shabana hasken rayuwarsa ce Allah ne ya dubi jarabawar rayuwarsa ya haɗashi da ita dan tazama garkuwa a gurinsa.
Da sauri ya kalleta jin tace Wash tana janye breast ɗinta daga bakin yarinyar, aikuwa nan take yarinyar tafasa kuka, Shadow yace "Menene beloved" kwaɓe fuska tayi kamar zatayi kuka tace "Wallahi zafi nakeji loveline" cikin tausasa murya yace "kiyi haƙuri ki bata kinga har ƴar uwarta ta fara kuka ita ma" baki ta tura gaba tare da gyara yarinyar ta saka mata breast ɗin a baki tana runtse Idonta dan Allah yasani tanajin zafi sosai.
Bayan tagama bawa ɗayar ya bata ta hannunsa, karɓarta tayi ta shayar da ita, murmushi Shadow yayi tare da gyara zamansa yace "saura Abbansu Nima zansha" harara ta zuba masa tace "kasheni zakuyi kenan?" Murmushi yayi yace "Idan har muka ga mai kasheki sai inda ƙarfin mu ya ƙare cox kece kumi namu beloved" murmushi tayi.


Saida yayi Sallah asuba sannan yatafi gida ya ɗauki wayarsa yakira haj Mama ya faɗa Mata Shabana ta haihu jiya da dare, faɗa tamasa tace akan mai bai kirata tun lokacin da zaije asibitin ba, haƙuri yabata yace "na manta wayar gida ne shiyasa" murmushi tayi tace "Okey yanzu zan sanar ma Abbunku insha Allah zanzo yanzu" sallama sukayi yakatse kiran.

Haka labarin haihuwar Shabana ya karaɗe dangi inda sukayi farin ciki sosai, Ammi sai miƙa godiyarta take ga mahalicci da ya bama ƴarta kyautar Yara har biyu kuma ya sauketa Lafiya.

Koda aka sallamesu direct gida Haj Mama ta wuce dasu.
Ahanaf ganin ba yadda zaiyi ne yasa yaje gida shima ya ɗauko kayansa ya dawo gida.
Haj Mama tayi korarsa har ta gaji Amma yaƙi Tafiya dole ta kyaleshi ta Maida hankalinta gurin kula da Shabana ita da Momy Hafsa Amaryar Abbu.


Jarirai sun sha kyautoka ta ko Ina, ƙaseem ne yayi musu kayan barka ya kashe kuɗi sosai kamar baisan inda suka fito ba, Shadow yaji daɗin karar da ɗan uwansa yayi masa sosai.

Anyi bikin Suna inda aka sakawa Yaran Suna Maman Shadow da Ammi, Nana Khadeeja da Nana Hauwa'u, ana kiransu Islam da Ilham.


Haj Mama ta Maida hankalinta gurin kula da Shabana, ba Abunda bata mata na gyara, bata bari Shadow yashiga ɗakin saidai ya zauna parlour. Amma Idan yaga bata kusa har ɗakin yake Shiga, shikaɗai yasan Abunda yakeji yana masifar kewar matarsa Amma Haj Mama ta kasa fahimta.

Yauma yana sallama parlourn yaji Shiru ba motsin kowa zama yayi kan kujera na ɗan lokaci, jin Shurun yayi yawa yasa ya nufi ɗakin da Shabana take.
Tura ƙofar yayi ya shiga bakinsa ɗauke da sallama, hangota yayi kwance kan gado da alama bacci take, ƙarasa yayi ya Kwanta gefenta tare da janyota jikinsa. cikin bacci Shabana taji kamar ana taɓa ta koda ta buɗe Idonta da Ahanaf tayi tozali, wani sassayan murmushi ta sakar masa tana ƙoƙarin

Please Login or Register in order to submit comment