Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya danganci glass saida Shadow ya fashi, Ko Ina kwalba ce zube a ƙasa.


Subhanallah Kamal inaga fa kamar taɓin hankali Shadow ya samu, saboda wannan abun yafara wuce mizani, yakamata aɗauki mataki tun kafin abun yaci Tura cewar Haidar idanunsa fall hawaye.
Gaskiya Kam yakamata iyayen sa Susan halinda Ɗan nasu yake ciki. katsaya anan tare dashi ni Bara naje nakira Ayiya tazo cewar Kamal Yana fita daga ɗakin cikin sauri.
Haidar baima sami damar ba Kamal amsa ba.
Sai ma Maida hankalinsa da yayi akan Shadow, Wanda yanzu kayan zanensa ne yaɗauko yanata faman Zane a Bangon ɗakin, Yana surutai.


Jikin ƙofa Haidar ya jingina hawaye Sai zarya suke akan fuskarsa Na matsancin tausayin Shadow, saboda yagama ƙissimawa aransa cewa tabbas taɓuwar kwakwalwa abokin nasa ya samu.
Allah wadan iyaye masu irin wannan halin Na jefa yaransu cikin masifa akan Wani dalili Nasu Na banza.
Anya ma kuwa da gaske su suka haifi Shadow? Haidar yayi ma kansa wannan tambayar da bashida mai bashi amsar ta.
Saboda Shi a iya sanin sa da Shadow Muhammad Imran Abba shine mahaifinsa, kuma su biyu ne Kawai yaran sa shida ƙanensa Ƙaseem.
Amma izuwa yanzu yafara shakka akan wannan lamarin.
Tsayuwar sa ya gyara afili ya furta tabbas akwai wata sarƙaƙiya a ƙasa.





________________ Idanunta tafara buɗewa a hankali har tagama buɗesu tas akan fuskar Meenal, wace take zaune a gefen gado tana facing ɗinta, ta buga uban tagumi tazubawa ƙawar Tata IDO cike da tausayawa. "saboda Mommy ta sanar da ita duk Abunda yake faruwa" Meenal taci kuka har ta godewa Allah.
Amma ga mamakin ta Sai Gani tayi Norr Na mata murmushi.
Tashi tayi ta zauna tare da cewa Hi Madam wannan kallon fa? Ni Dan Allah Karki cinyeni, Ta faɗa Tana kai hannuna kan fuskar Meenal kamar zata tsone mata idon din cikin Wasa.

Kauda Kanta Meenal tayi gefe cikin Al ajabi, tace Norr kina lafiya kuwa Ko kin manta ƙalubalen da ke gabanki ne? daura auren ki fa akayi da Ƙaseem Mai makon Shadow? Amma Naga kamar baki damu ba?

Yamutsa fuska Norr tayi tace eh Ina sane Mana,
Dady ya gaya min Kuma yace yanaso nayi Masa biyayya, wannan dalilin yasa ma kikaga nasaki Raina, Zan zauna da Dashi Meenal ai dukansu Abu ɗayane,
Amma tunda har Dady ya yanke hukunci tohm tabbas banida Ja akan wannan lamarin Norr takarisa maganar tana murmushi.

Tirkashi Abunda Mommy tasamu damar furtawa Kenan, Dan duk taji bayanin da Yar Tata tayi yanzu.
Ita Meenal Suman zaune ma tayi saboda Takasa cewa Kala Sai bin Norr take da Ido kamar wata sokuwa.

Kosa da ita Mommy ta zauna ta rungumeta ajikinta tana bubbuga bayanta a hankali tace Norr kinutsu kidawo cikin hankalinki Kisan Abunda bakinki yake furtawa, cewa fa kikayi kin Aminta da auren kaseem? Wanda dazu da dadinki yafadi haka ihun Kika dinga zunduma wa kina bakison auren, Kuma Nima nasan bakison sa, Amma Mai yasa yanzu daga tashinki faga bacci kice Wai kin amince kamar wata Mai Anjanu?

Tohm Mommy ya kikeso nayi kefa da be kike cewa Nabi duk Abunda Dady ya umarce ni akai, yanzu Dan kawai Nabi umarnin nasa Sai kuma abun yazama laifi? Nifa Mommy banida JA akan maganar Dady, Kuma yanzu naji duk Duniya ba Wanda nake so sama da kaseem. Kuma Zan zauna dashi a matsayin mijina Kamar yadda Dady yace insha Allah.

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un shine Abunda Meenal ta fada cikin tsantsar mamaki da tashin hankali saboda tasan wannan abun bana lafiya bane.

Taya Norr Zata yadda da auren Wani akanta ba Shadow ba? A da Idan ka kwatanta fadar haka tohm fa Norr Bata da makiyin daya wuce Kai, kullum maganar shine Idan munyi aure da Yaya Shadow zanyi kaza zanyi kaza, ba Wanda zaiyi Zaman 30min tare da Norr baisan Shadow ba saboda yawan maganar sa datakeyi ako Ina Idan tazauna.

Amma babban abun Al ajabin sai yau data kasance ranar daurin aurenta da Shadow dinta, aka fasa auren dashi aka daura da kanensa, Kuma har ta iya cewa ta yadda zata zauna dashi Tana son sa. Tabbas wannan abun ba lafiya ba.

Ita ma Mommy Kanta ne yaɗauki zafi harma tarasa abun cewa Sai bin Norr din da Ido take wacce ita sabgogin gabanta mantake tana kokarin Shiga toilet.




_________ Kanada hankali kuwa ƙaseem Norr ɗin ce Zaka bude baki kace kana so agaban Ahanaf? Ai Wallhi banyi tunanin hakan daga gareka ba Ko kaɗan.

Gyara zama ƙaseem yayi tare da dafe kansa da yake Masa matsancin ciwo gashi Kuma yasha naɗi da bandage duk Wani iri yake jinsa.
Yafara Magana cikin zafin ciwon da yakeji, yace Wallhi Ayiya tunda ɗazu da wani irin bacci ya ɗauke ni Wanda tunda nake Duniya Ban taɓa Jin irin sa ba shine fa Ina farkawa daga baccin, naji duk Duniyar Nan ba wacce nake so sama da Norr, Kuma da ita kaɗai nake ra'ayin Zama a matsayin Mata. duk Wanda yace zai rabani da ita tohm fa tabbas Sai Idan ba raina Ayiya............✍️✍️✍️



TIRKASHI 🙆🙆🙆


WAI MAI YAKE FARUWA NE?

WANANAN WANE KALAR BACCI NE?

TABBAS AKWAI WATA A KASA KOWAYE YAKE SHIYAR WANNAN MAKARKASHIYAR?



Masu cewa sun matsu suji menene dalilin su Abba, tohm Dan Allah kuyi haƙuri Kuma kudaina ganin laifinsu plzz😥😥

Kudai Kawai ku ƙara haƙuri tabbas zakusha mamakin wannan lamarin 😭😭



Dan Allah kuyi haƙuri da Taping erro fita nayi yau hankalina baya kwance 🙏🙏🙏





Nabeela Binji ce💃💃💃





Nabeelah Shehu Binji

09064314811
Or
09161107610




More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏




♣️DUHUN INUWA ♣️




TAPING......📲📲📲


STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*


BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM




Page

0️⃣5️⃣


Saukar Wani firgitaccen Mari Al Ƙaseem yaji akan kumatun Wanda yayi sanadiyan Ƙaruwar ciwon kansa, cikin tsantsar masifa Ayiya tace "kana da hankali kuwa Ƙaseem kasan Mai bakin ka yake furtawa? Norr Ɗin ce Kuma kake so yanzu? Tabbas ba lafiya kake ba, yakamata ka dawo cikin nutsuwar ka kasan Mai yake fita daga bakin ka kaseem, Norr fa?"

Ni Ina cikin hankalina Ayiya, Kuma nasan Abunda nake faɗa, menene Abu marar kyau anan Norr Dai Matata ce Kuma Ina da damar furta cewa Ina son ta, saboda haka Zan Koma faɗar cewa Ina son No.. hannu Ayiya ta ɗaga da nufin sake Zabga Masa Wani Marin Sai ji tayi an riƙe Mata hannu ta Baya, juyowar da zatayi sukayi Ido huɗu da Kamal.
Cikin tashin hankali Ayiya tace Kamal Kanafa jin Abunda kaseem yake faɗa. Anya wannan Abun bawata kullalliya aciki kuwa?

Bawata kullalliya Haj Shuwa saidai Idan kece Zaki kullata a yanzu, cewar Abba da yake ƙoƙarin shigowa cikin ɗakin, fuskar sa ba alamar Wasa yace "kifita daga idona Na rufe Shuwa, zamanki lafiya da kwanciyar hankalinki agidan nan shine ki daina kalubalantar wannan auren saboda akan wannan auren Zan iya samun matsala da kowa Wallahi" Abba ya faɗa Rai a ɓace.

Kallonsa ya mai da Kan Ƙaseem Wanda yake tsaye a gefe ya rasa Abunda yake Masa daɗi a wannan rayuwar, shidai yanzu ba wacce yake burin Gani sama da Norr, sonta ne yake azalzalar zuciyar sa.

Maganar Abba ce tadawo dashi cikin hankalinsa inda yake cewa, subhanallah Ƙaseem Mai yaji Maka ciwo haka? Ko kayi accident ne? Abba ya tambyi Ƙaseem hankali a tashe saboda ba Ƙaramin ciwo yaji ba.

Kai kaseem ya girgiza alamar a'a ko ɗaya sannan yabuɗe baki da kyar yace Abba Yaya Shadow ne ya dakeni.

Duka fa Abba ya tambaya cike da masifa, Kai jakine da zai dakeka haka? Ah lallai wannan Yaron Dani yake zance, ai bakai yakamata yasamu yadaka ba, Ni yakamata yadaka Nida Na ɗaura auren. Ina Ahanaf ɗin yake yatambaya cikin faɗa.


Gyaran murya Kamal yayi cikin girmamawa yace Yana ɗaki Abba, Kuma gaskiya Ina tunanin Kamar bashida lafiya saboda Yana can Sai faman farfasa Kaya yake a part ɗinsu Kamar Wani Wanda yasami taɓuwar hankali,
shine nace Ko zakuzo muje kuga halinda yake ci...

Dan Allah da kata Abba ya faɗa Rai a ɓace, ba Wani taɓuwar hankali da yasamu tsabar rainin hankali ne da yayi Masa yawa.
Kuma tinda Har Ahanaf ya nuna ban Isa dashi ba kuma ban isa nasaka doka yabita ba, tohm kusani daga yau ba ruwana da lamarin rayuwar sa yaje yayi duk Abunda yake ga yafi Masa a rayuwa Abba ya faɗa cikin sound Na gaskiya da gaskiya.

Kamal da Ayiya mutuwar tsaye sukayi saboda tsabar mamakin wannan lamarin Na Abba.

Janyo Ƙaseem Abba yayi kusa dashi tare da cewa Allah yayi Maka Albarka Ƙaseem naji daɗi sosai Kuma nagode da kamun biyayya akan Abunda Na umarce ka.

Ita ma Kanta matar taka ta amince da kai a matsayin mijinta, ɗazu mahaifinta ya kirani a waya yake gayamin, kaga yanzu Sai kaje kayi duk Wani Shiri da zakayi katafi gidanka saboda natura motocin ɗaukar amarya tun ɗazu.

Cike da matsancin farin ciki Ƙaseem ya rungume Abba Yana dariyar murna yace nagode sosai Abba Allah yasaka Maka da mafificin Al khairi, Amma Abba wane gida za'a kaita.

Gidan da wancan shashan Yaron yagina Mana Ƙaseem, ai tinda daman dan ita Norr ɗin aka Gina Shi tohm shakka Babu a ciki zata zauna.


Wallahi wannan Kam ƙarya ne Alh ai wannan Zalunci yayi yawa da wanne zaiji? "Budurwarsa, Sadakinsa, gidansa? Bazan bar haka tafaru ba Alh Yaron Nan fa Shima ɗanka ne Kuma jininka, ko menene ya aikata Maka Bai cancanci wannan mummunan hukuncin daga gareka ba" Idan ma ka Hana Shi auren yarinyar Nan kamata yayi kabar Masa duk Wani Abu da yake mallakinsa.

Bazanyi haka ba Shuwa, "ba fa kece Mai mulkina ba nine Nan nake mulkinki, Ni nakeda hakki akan ki Dama yaran naki gabaki daya Dan haka Na gama yanke hukunci Akan kaseem zai tare a gidan da Ahanaf ya Gina saboda ana iyayen yarinyar suka Saka kayan Yar su, kinga Kuwa ba Inda yakamata su zauna sama da can.

Bazan musamaka ba Alh saboda nasan Kaine mahaifin Ahanaf Kuma Kaine mahaifin Al kaseem, Amma Abunda nake so kasani shine bazan zauna Nan gidan ba, Zan bar Maka gidan ka, Kuma Zan tafi da Ahanaf gidanmu Naci gaba da kulawa dashi acan Amma alfarma daya nake rokonka shine kamanta damu arayuwarka Dan Allah tafada tana hada hannayenta guri daya alamar roko hawaye Sai zarya suke akan kumatun ta.

Ba Inda zakije Shuwa kina gidan nan Insha Allah, Amma Shi duk gurin da zaije yaje Bani da matsala da haka, ya faɗa cikin nuna halin Ko in kula Akan Ɗan nasa, Wanda ada yake mutuwar so da kauna saboda shine ɗansa Na farko aduniya.

Wannan Kuma kayi kaɗan Muhammad dole nabar Maka gdnka tunda ka nuna Ni ban isan nasan Abunda kake shiryawa ba, ban Isa nasan dalilin wannan hukuncin da ka yanke ba, tohm menene an fanina agurinka ai kaga gwara Kawai natafi.

Abba yarasa abinda yasa Aduk lokacin da Haj Shuwa ta furta cewa zata tafi ta bar Masa gidansa Sai yaji Wani matsancin ɓacin Rai da fargaba sun dirar masa a zuciya.

Ba Inda zakije Shuwa cewar Abba, wallahi muddin Kika fita daga gidan Nan to fa kisani bakin aurenki.
Yana gama Faɗin haka yaja hannu Al ƙaseem suka bar ɗakin cikin sauri Kamar wa ƴanda zasu Tashi Sama.


Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un ita ce Kalmar da Kamal keta nanatawa, cikin tashin hankali da Al ajabin wannan lamarin shidai tinda yake arayuwa Bai taɓa Jin makamancin wannan abun ba, Ko a film Ko a novel Amma a yanzu ga abun yana faruwa agabansa Yana kallo.

Gurin Ayiya Kamal ya ƙarasa Kamar Wanda kwai yafashewa a ciki, tare da Kama hannayenta ya zaunar da ita a gefen gado yace ki daina wannan kukan Dan Allah Ayiya,
kuka fa bashine mafita ba a wannan halin, Kawai Neman mafita shine Abunda ya kamata muyi,
Yanzu kitashi mutafi gurin Ahanaf ɗin kiga halinda yake ciki saboda lamarin Sana Sai ƙara ta'azzara yake.

Bazan iya ba Kamal bazan iya kallon Ahanaf acikin halinda bazan iya taimakonsa ba Kawai kuje kuyi Masa Abunda yadace, Idan ma asibiti zaku Kaisa kukai sa Dan Allah Kamal.

Cike da mamaki Kamal yake kallonta duk da yaga Kamar da ya nayin tausayawa a fuskar ta tayi maganar, Amma Bai kamata tace Wai bazata iya Zuwa taga a wane hali Ɗan nata yake ciki ba. Har zai buɗe baki yayi Magana kome yatuna Sai kuma ya rufe bakinsa, tare da Tashi yabar ɗakin ransa bace.

Tabbas wannan jarabawar bama tabuwar hankali yakama a ce Shadow ya samu ba, kamata ma yayi ya mutu Ko zai Sami salama a rayuwa, haba wannan Bala'in Har Ina cewar Kamal hawaye nabin fuskar sa.

Koda ya Koma ɗakin a yadda ya barsu a haka yasame su, Shadow Sai zuba zanensa yake a Bango, Kuma babban abun mamakin shine duk da Baya cikin hankalinsa zanensa yake Kamar yadda yasaba, cikin kwarewa irin ta kwararren Ɗan Zane.

Kamal ya kalli Haidar yace Dan Allah ɗan zo Kaji, ba musu Haidar yabi Bayan Kamal tare da rufe k
Ƙofar gudun Kar Shadow ya fito.

Bayan sun dawo Palo ne sun zauna Kamal ya kwashe duk Abunda yafaru Bayan fitar sa daga dakin da sunan Kiran Ayiya ya fadawa Haidar.

Tirkashi shine Abunda Haidar yasami damar furtawa Yana goge zufan da ya zubo daga goshin sa,

Sun dauki lokaci Mai tsawo ba Wanda ya iya cewa Kala a cikin su, kowa da tunanin da yake a cikin zuciyar sa.

Haidar ne ya dago ya kalli Kamal yace Kamal yanzu ya zamuyi Dan ganin mun taimaki Shadow?

Nima tunanin da nake Kenan Haidar Amma duk iya tunanina nakasa samu Mana mafita.
Dukan su shiru sukayi Suna tunani.
Sai can Kamal ya dago ya kalli Haidar yace Na samu mana mafita Haidar
Ciki zakuwa Haidar yace Mai Cece mafitar Kamal?

Gayara Zama Kamal yayi tare da cewa Abbu, tabbas Abbu Shi kaɗai ne mafitar mu,. saboda nasan duk Wanda Abun da yake faruwa bashida masaniya Akai Shi Kawai yakamata mukira mugaya Masa Abunda yake faruwa Insha Allah Shadow zai Sami a dalci.........✍️✍️✍️



Wane ne Abbu?


Shin waye Abbu agurin shadow?


Kuma wane matsayi yake dashi agurin Abba da Har su Kamal suke tunanin Kai ƙarar Abba agurinsa?


Kuma Idan sun Kai Masa ƙarar zasu samu Abunda suke so?




Nabeela Binji ce💃💃💃





Nabeelah Shehu Binji

09064314811
Or
09161107610




More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏





♣️DUHUN INUWA ♣️




TAPING......📲📲📲


STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*


BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM


Page

0️⃣6️⃣



________________Haidar ne ya ciro wayar Shadow daga cikin aljihunsa yace bara mugwada Kira muga Ko zata Shiga.

Cikin Sa'a wayar tafara ringing shiru sukayi Suna jiran ya ɗauka, Amma har ta tsinke ba'a ɗauka ba sake Danna Kiran Haidar yayi Sai da suka Kira sau ukku kafin suji an ɗaga tare da sallama,
Amsa sallamar Haidar yayi tare da gaida Shi,
Amsa gaisuwar Abbu yayi tare da cewa Yan samari lafiya Dai Ina Ahanaf?

Gyaran murya Haidar yayi sannan yace gaskiya Dai Kam ba lafiya ba Abbu, saboda........ Nan Haidar ya gayawa Abbu duk Abunda yake faruwa.

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un Abbu ya faɗa cikin tashin hankali, ruɗu da Kuma Al ajabi.
Abbu Yace yaro ka tabbar Abunda kake faɗamin gaskiya ne Kuwa?

Wallahi gaskiya Na faɗa Maka Abbu,
Ai wannan lamarin yafi ƙarfin ayi Wasa da Shi, yanzu ma haka maganar da nake Maka shine an kai Norr agidan da Ahanaf ya Gina, a matsayin matar ƙaseem. Haidar yafaɗa cikin ƙunar Rai.


Subhanallah Lallai shigowa Nigeria ya Kamani gobe, zanzo insha Allah naji menene dalilin da yasa Muhammad ya yanke wannan mummun hukuncin, tabbas Idan har Bai gayamin dalili ba Toh wallahi ransa Sai yafi nakowa ɓaci.

Sosai Haidar yaji daɗin furucin Abbu, Allah yakawo ka lafiya Abbu Haidar yafaɗa Yana ɗan murmushi saboda yasan Insha Allah Shadow zai Sami ƴan cin kansa.

Ameen ya Allah yaro ya sunanka? Abbu ya tambayi Haidar.
Haidar ne Sunana Abbu, Masha Allah Allah yayi Maka Albarka Haidar,
Dan Allah kaciga da Kula da abokin Naka insha Allah gobe Zan zo.
Tohm Insha Allah Abbu Allah Dai ya kawoka lafiya.
Ameen ya Allah cewar Abbu Yana kashe wayar.

Haidar ya kalli kamal cikin sakin fuska yace insha Allah kumai zai Zama tarihi abokina.
Murmushi Kamal yayi yace Allah ya yadda Boss,
Ameen ya Allah.


Ɓangaren Abbu Kuwa yakasa koma wa bacci Sai Safa da Marwa yake Yana tunanin wannan lamarin, tabbas yasan Irrin son da Muhammad yakewa Ahanaf, baya Son Wani Abu ya same Shi ko kaɗan, harma Takai ga baya iya ɓoye son da yakeyi masa agaban Koma waye.
Iska Mai zafi ya furzar Tabbas ba banza ba Abbu yafurta a Zahiri.

Kai da waye Kuma cikin wannan tsohon Daren? Cewar Hajiya Mama wacce ta kasance Mata agurin Abbu.

kusa da ita yaje ya zauna Yana dafe kansa yace Haj Ina ga gobe zamuje gida Nigeria,

Nigeria Kuma tafaɗa cike da mamakin sa, saboda ita dai tasan ba yadda batayi dashi ba Akan yabarsu su tafi bikin Ahanaf ita da Yara,
Amma Sai yace a'a tinda Shima Bai samu zuwa ba to ba Wanda zaije, dalilin da yasa yace haka kuwa shine saura kwana biyar ya su Koma gida Nigeria gabaki daya,
a cewar sa Idan sunje Sai suga amaryar.

Amma Kuma shine yanzu yake cewa zaije Nigeria gobe.

Mai yafaru Mai zai kaika Nigeria Kuma? Bayan Nan aka Ɗaura auren ɗan ka Ahanaf bakaje ba Kuma muma baka barmu munje ba, sannan yanzu kace zakaje akan Wani aikin gabanka?
Kasani fa Abunda kake Babu kyautawa a ciki Ko kadan Abbu, cewar Hajiya Mama wace da alama Dama acike take dashi.

Ɗagowa yayi da idanunsa waƴan da sukayi Ja tsabar ɓacin Rai ya zuba su Akan fuskarta Yana kallonta.

Cikin sauri tace subhanallah Mai yafaru ne Abbu Mai yasameka Wani Abu yafaru ne? Saboda tasan muddin taganshi a cikin wannan yanayin tohm tabbas tasan ba lafiya ba.

Numfashi Abbu ya furzar tare da cewa tabbas nayi nadamar Rashin zuwa wannan ɗaurin auren Hajiya, Ni kaina Na Rasa dalilin haka. Haka Kawai naji bazan iya zuwa ba,
wannan dalilin yasa Kuma Na Hana Ku zuwa,
Nan Abbu ya faɗama Hajiya Mama duk Abunda Haidar ya faɗa Masa.
Ai Ko kafin yagama Bata labarin Tasha kuka Na fitar hankali.

Cikin kuka tace tabbas yazama dole muje Nigeria gobe Abbu, saboda muceto rayuwar Ahanaf. Anya Kuwa Muhammad Yana cikin hankalinsa?

Nima Abunda nake tunani Kenan Hajiya, Amma Koma Menene gobe zamu tabbatar insha Allah.




____________ Ƙaseem ne zaune agaban Abba da kunburarriyar fuskar sa, Yana sauraren wa'azin da yake Masa Akan Zama da Mata. bayan yagama ne yace tohm Ƙaseem Zaka iya Tafiya, driver Yana waje Yana jiranka, Allah yayi Maka Albarka yabaku zuri'a Ɗayya ba.

Ameen ya Allah Nagode sosai Abba, bara naje nayiwa Ayiya sallama Sai natafi.
Kar ka fara Ƙaseem Ayiyar taka data nuna Bata son wannan auren,
Kawai kai dai kayi Abunda nace Maka cewar Abba,
Tohm insha Allah Abba,
Ƙaseem yafaɗa Yana barin ɗakin cikin sauri, saboda yanzu ba Abunda yake da muradi Sama da ganin Norr a gabansa, saboda matsanancin sonta yakeji a cikin zuciyar sa.

Yana fitowa harabar gida direct gurin Motar da yango haske a cikin ta yanufa,
Yana zuwa ya buɗe Motar yashiga tare da cewa driver'n muje.

Tafe suke a hanya Amma Kaseem Gani yake Kamar ba Tafiya ake ba,
ɗan tsaki yayi tare da cewa Dan Allah mlm kayi sauri Mana, Idan Kuma ba Zaka iya bane ka Bani motor Ni Sai na toƙa da kaina.
Kayi hakuri dan Allah oga cewar drivern tare da karawa Motar gudu.

Suna karasawa cikin gidan Ƙaseem ya buɗe murfin motar ya fita Yana zuba sauri Kamar zai tashi Sama,
Audu driver ne yabi bayansa cikin sauri yace oga gashi Wai inji Alh yace a Baka,
karɓar ledar Ƙaseem yayi ya Tafi Abunsa ba tare da yayi wa Audu Magana ba.


________Zaune take Akan gado Sai uban murmushi take zubawa.

Sallama yayi yana Tura ƙofar ɗakin yashiga, fuskar sa dauke da murmushi,

Gefen gadon yazauna Yana ƙare Mata kallo farin ciki fall zuciyar sa.

Gyaran murya yayi tare da cewa Amarya bakya laifi Koda kin kashe ɗan masu gida,
murmushi tayi batare da tayi Magana ba.

Norr ba Magana ne? Ƙaseem ya tambaye ta cike da Nishadi.

A hankali tace Ina wuni Yah Ƙaseem.
Murmushi yayi yace Bana so Sai da Na roƙa ko?

Please sorry Yah Ƙaseem ta faɗa cikin shagwaɓa.

Matsawa yayi gurin da take zaune ya saka hannunsa ya yane gyalen da Ke a Kanta. tozali yayi da kyakyawar fuskarta wace tayi fayau ba Ko dingon kwalliya Akanta.

Murmushi ya sakar Mata tare da cewa Ina godiya a gareka Allah da ka mallakamin wannan kyakyawar yarinya cikin sauƙi.


Ita ma murmushin tayi tare da Saka hannayenta ta rufe fuskarta alamar kunya.







_______________ Ya kamata fa muyi sallar Isha'i mu kwanta saboda wallahi bacci nake ji, cewar Kamal.

Eh Hakan yakamata gaskiya saboda kaga yanzu mun samu mafita.

Bayan sun dawo daga gurin sallar ne suka zube a falo, Haidar Akan Capet shikuma Kamal Akan doguwar kujera,
Fira suke Sama Sama Har bacci ya ɗauke su.


Da asuba da suka farka daga bacci, ɗaya daga cikin ɗakunan suka Shiga suka ɗauro alwala. Basu Shiga ɗakin da Shadow yake ba gudun Kar su makara gurin Tara Tara dashi Kuma gashi Har sunji an tada Sallah.




Bayan sun dawo daga masallaci ne suka ci Karo da Abba agurin Shiga gida, murya adakile Kamal ya gaida Shi,
Haidar kam yi yayi Kamar Bai ganshi ba saboda mugun haushinsa yakeji.

Shima Abba haka yayi Kamar Bai Gansu ba Dan Ko gaisuwar da Kamal yayi Masa sarai yaji Shi, Kawai Dai yaƙi amsa Masa ne,
Saboda Shi yanzu duk Wani Abu da ya dan ganci Ahanaf bayama son yayi tozali da Shi, saboda yaji haushin musa Masa da Ahanaf yayi a cewar sa.


Bayan sun Shiga falon Kai tsaye ɗakin da Shadow yake ciki suka nufa, Haidar yasaka hannunsa a cikin aljihu yaciro key din dakin ya bude,
Suka Shiga ciki Amma me wayam suka Gani ba Shadow ba alamar sa.

Tohm Ina yashiga Kuma cewar Kamal Yana kwala Masa Kira Shadow Shadow Shadoww!
Amma shiru Bama alamar mutum a ɗakin.

Cike da mamaki suka hau neman sa ba Inda Basu Duba ba Har cikin toilet, Abu Wasa Wasa Yana so yazama gaske, Dan su Kamal ba Inda Basu Duba ba Amma basu ga Shadow ba. tirkashi Abunda Haidar yasamu damar faɗa Kenan cike da mamaki.

Yace Shadow Dai ba aljani bane balle ya ɓace, Kuma ba tsontsu bane balle ya fira. Tohm ta ina yafita Kenan? Tambaya ce da basuda Mai amsa musu ita a halin yanzu.


Wani kyallen ƙofa Haidar ya buɗe,
Ƙofa yagani cikin sauri ya Tura ta Kawai Sai Gani yayi ta bude,
kofar yabi Kamal ya bishi,
Sai ganin kansu sukayi ta bayan gida gurin Garden.
Kalle Kalle suka fara yi agurin Suna Neman Shadow, Amma ba Ko alamar sa agurin.

Suna tsaye kowannen su da Abunda yake saƙawa a ransa, Kawai idanun Haidar suka faɗa Akan ƙofar ɗakin Shadow.
Ta gurin da suka biyo yanzu, ƙarasawa bakin Ƙofar yayi hannunsa yakai zai cire key ɗin da yagani a jikin ƙofar Sai Kuma yafasa.

Cikin Al ajabi Haidar yace tabbas kowane Mai laifi yakan kwaɓar a yayin aikata laifinsa.
Ma'ana yakan bar wata mafaka da zata tona asirinsa.
Barin wannan key ɗin ajikin ƙofar shine ya nuna cewa tabbas daga baya aka buɗe wannan ƙofar Shadow yafice daga gidan..........✍️✍️✍️✍️


Tohm jama'ah ana wata ga wata

Wanene yake bibiyar rayuwar Ahanaf (Shadow)?

Kuma Koma waye menene dalilinsa?

Mai zai faru Idan Abbu yazo Nigeria Bai Tarar da Shadow ba?




Nabeela Binji ce💃💃💃





Nabeelah Shehu Binji

09064314811
Or
09161107610




More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏








♣️DUHUN INUWA ♣️




TAPING......📲📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*


BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM


Page

0️⃣7️⃣




___________ Cikin Mamaki Kamal yake kallon Haidar yace "Boss nifa ban fahimceka ba me kake

Please Login or Register in order to submit comment