Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace "Akan me zai dakeki ba kin iya ba?" Kai ma "kasan ban iya ba" yanzu fa kika ce min ba abunda bazaki iya Zanawa ba"
"Wasa nake maka"
Murmushi Shadow yayi sannan yace "tohm kawo kiga" mika Masa pepper tayi yafara Zanawa tare da cewa "ki Maida hankaliki sosai Idan Na Gama Zan baki kema kiyi" Ai Kuwa Shabana ta zuba Ido Ko kyabtawa batayi.
Nan take Shadow ya Zana ya Suhail ya ɗaga pepper Yana murmushi.
Wow Shabana ta faɗa tana karɓar pepper daga hannunsa murmushi tayi tace "Wallahi ya Suhail ya fita tsab" murmushi Shadow yayi.
Nan take Shabana ta ɗaure fuska, Shadow ya kalleta yace "lafiya, Mai yafaru Kuma?" "Kana nufin ni bazaka Zana ni ba"
Murmushi Shadow yayi yace "zan Zanaki Amma Sai Ranar da kika zama kwararriyar ƴar Zane kika Zana ni. a sannan ne nima zan Zanaki Zanen da ban taɓa yiwa kowa irinsa ba. Ɗan Jim tayi kafin daga bisani Kuma tayi murmushi tace "zan baka maki"
Murmushi kawai yayi batare da yace Mata ƙala ba.




A Zaman da Shadow da Shabana sukayi Shaƙuwa tashiga tsakaninsu sosai, Dan har takai Idan ya dawo aiki ko bai Ganta a Palo ba yakan Shiga Har cikin ɗakinta sugaisa Su ɗanyi hira ya tafi ɗakinsa.


Yau ma koda ya dawo ba kowa a palon Kai tsaye ɗakin Shabana ya nufa. Tura ƙofar yayi ya Shiga tare da yin sallama.
Shabana wacce yanzu Nan ta fito gurin wanka daga ita sai Wani gajeren Towel tana ƙoƙarin Shafa Mai. Zare Ido tayi tare da furta Innalillahi wa'inna Ilaihi Raju'un, "Ahanaf menene haka Dan Allah kafita" kamar da dutse take magana Ahanaf Sai ƙara matsowa yake kusa da ita. Zata gudu ya riƙe ta tare da haɗata da Bango yana bin ilahirin jikinta da kallo. Ahanaf Dan Allah kasakeni kagafa ba Kaya ajiki.. Bai Bari ta ƙarasa ba ya haɗe bakinsu guri ɗaya. zare Ido nayi Wani irin adrenaline rush ne yazo min.
dukkan emotions din da nake gani a idon Ahanaf su yake zuba min, his sadness, loneliness, anger and his love for me. And I find myself responding back. Daga Ni har shi karkarwa muke yi tamkar waɗan da ake karkaɗawa.
Babu abinda muke yi sai ajjiyar zuciya one after the other. I feel my senses slipping away from me. A lokacin da za'a tambayeni sunana ma ban sani ba.......✍️✍️✍️







Nabeela Binji ce💃💃💃







More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏.


♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MO



TIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM



PAGE

3️⃣ 3️⃣








______________ Tayi iya ƙoƙarin ƙwace Kanta Amma ta kasa, hannunta tasa tana turashi Ji tayi kamar tana tura Bango Cox ko motsi bayayi.
Zare bakinsa yayi daga nata ya mayar kan wuyanta yana kissing ɗinta da sauri sauri kamar zai haɗeta, yana yawo da hannunsa ko Ina ajikinta. Hannunta tasa taƙara jimƙe Towel ɗinta. Ganin Abun nasa Yana neman wuce saninta yasa tasaki kuka mai ƙarfi tana roƙonsa Dan Allah ya rabu da ita.
Kamar a mafarki Shadow yaji Kukan Shabana a hankali ya Fara buɗe idonsa ware su yayi da ƙarfi tare da ja Baya.
Gefen gado ya zauna tare da dafe kansa.
Tsabar ta rude hanyar fita ta nufa, zata murɗa handle ɗin ƙofar taji yace "Ina zaki tafi haka?" Tsawa tayi cak da ta tuna ba kaya ajikinta. Durƙusawa tayi agurin saboda wata irin kunyar Shadow da takeji bazata iya sake gibtawa ta gabansa ba.
Hakan yasa ta ƙara fasa wani sabon kuka da sauri Shadow ya ɗago kansa ya kalleta yaga yadda ta haɗe jikinta guri ɗaya tana kuka.
Kawadda kansa yayi gefe Yana duba ɗakin ko zai samu Abunda zai bata ta saka. Hijab ɗinta ya gani tashi yayi ya ɗaukesa ya nufi gurinda take.
Tanajin takonsa taƙara matse jikinta tare da rufe idonta gam.
Murmushi Shadow yayi tare da cewa "Amshi hijab kisaka" da sauri ta ɗago kanta da gaske kuwa Hijab din tagani amsa tayi tasaka, sai a sannan ta sauke ajiyar zuciya. Tashi tayi zata wuce ta gabansa ya riƙota, cikin sanyin murya tace "wai menene haka?" Gyaran murya yayi tare da cewa "kishirya Idan anyi magrib zamu fita dama Shine nazo faɗa miki" Yana Gama faɗar haka ya buɗe ƙofar yafita. Baki ta saki galala, eh Lallai wannan mutumen ya gama rainani. Tohm ba inda zanje yazo ya ɗaukeni ta ƙarfi ya tafi dani, kwafa tayi tare da zuwa ta fara Shirinta koda ta gama bata fito palon ba saboda taga lokacin magrib yayi.


Yana fitowa palo yaci Karo da Ammi Wata irin kunya yaji da sauri ya sunkuyar da kansa ƙasa tare da ɗan russunawa ya gaidata. Amsawa tayi cikin fara'a tare da tambayarsa ya aiki.
Alhmdllh Ammi
Masha Allah.
Tafiya yake Yana Sosa kansa. murmushi Ammi tayi tare da girgiza Kanta.
Koda yaje ɗaki kasa taɓuka komai yayi gabaki ɗaya jikinsa ya Mutu.
Ba abunda yake sai murmushi tabbas Shabana ta matuƙar bashi dariya bai zaci tsoronta yakai har haka ba. A fili ya furta na samu lagonki yarinya yanzu zamu fara wasar.





Yana dawowa daga masallaci direct ɗakinta ya nufa ya murɗa handle ɗin yaji ƙofar a rufe dariya ce ta suɓuce masa Lallaima wannan Yarinyar.
Kwankwasa ƙofar yayi Shiru bata buɗe ba kuma baiji motsinta ba.
Palo ya dawo ya zauna yafi mintina goma da zama baiga kowa ba, can saiga Ammi tafito kallonsa tayi tace "lafiya ka zauna kai kaɗai Ina Shabana take ne?" Ita nake nema Ammi, naje ɗakinta kamar bata ciki, kuma da Naso muje gidan Malam Ibrahim mugaidashi ne kafin dare yayi" Murmushi Ammi tayi tace "tana ɗakin nan saboda ba inda zataje yanzu, Saidai Idan taƙi budewa ne kawai. Bari naje nafito maka da ita" yawwa Ammi nagode Ahanaf yafaɗa yana Murmushi dan Shima yasan tana cikin ɗakin.


Kwankwasa ƙofar Ammi tayi Shiru Shabana bata motsa ba Dan tayi tunanin Ahanaf ɗin ne ya dawo. Saida taji muryar Ammi na cewa Wallahi Idan baki buɗe ƙofar nan ba ranki zai ɓaci. Da sauri ta wuntsulo daga kan gado ta buɗe ƙofar. Hararar ta Ammi tayi "wane kalar rainin wayau ne kinajin ana Kwankwasa miki ƙofa kiƙi budewa?" Kiyi haƙuri Ammi wallahi banzata ke bace" Ammi tace "au inda Bani bace bazaki buɗe ba Kenan?" Girgiza kai tayi alamar a'a. Kwafa Ammi tayi tare da cewa "Toh kifito ku tafi yana jiranki tun ɗazu a Palo" kallon Ammi tayi tace "Ina Kuma zamu yanzu dan Allah fa Ammi" baki Ammi tasaki Tana kallonta tace "lallai Shabana kin rainani, Toh bansani ba Idan kinfito sai ki tambayeshi inda zaku je" turu baki tayi tace "Nikam gaskiya ba inda zanje Ammi kaina ke ciwo" cikin ɓacin Rai Ammi tace "mintina Biyar Na baki ki shirya ki fito ku tafi Wallahi Idan har kika ɓata masa lokaci ranki saiya ɓaci kinji dai na faɗa miki" tana gama faɗar haka ta juya tatafi abunta.

Ji tayi kamar ta fasa ihu tsabar takaici ita yanzu da wane Ido zata Kalli Ahanaf? Allah ya Sani kunyarsa takeji sosai.
Ba yadda ta iya haka tafara Shiri Wani ƙaton Hijab ta ɗauko tasaka Kamar wata Sayyada.


Tana fitowa suka haɗa Ido da sauri ta sunkuyar da Kanta tare da turu baki gaba.
Murmushi yayi cikin sigar zolaya yace "Sannu da fitowa Auta" ya mutsa fuska tayi batare da tace masa uffan ba.
"Muje" Ahanaf ya faɗa Yana yi gaba. Ba yadda ta iya dole tabi bayansa.

Tafiya suke cikin Mota ba Wanda yake Magana a cikinsu. kallonta yayi tana Danna wayarta Murmushi yayi.
Batare da ta kalleshi ba tace "Wai Ina zamuje ne haka?"
"Hotel" Shadow ya faɗa batare da ya kalleta ba Shima.
Wani Tari ne ya kwace Mata cikin sauri ta kalleshi tace "hotel kuma?" Saura kaɗan dariya ta ƙwace masa Amma ya danne. Yace "eh hotel" Wani zufa ne taji yana tsatsafu mata cikin danne firgicin da tashiga tace "Toh me zakayi a can?" Shadow yace "me zanyi, kodai mai zamuyi?" Duk inda hankalin Shabana yake ya tashi gabaki ɗaya ta gama tsorata da lamarin Ahanaf. Shuru tayi tanajin yadda zuciyarta ke halbawa da sauri da sauri.
Ganin tayi sun nufi hanyar gidan Malam Ibrahim, ajiyar zuciya ta sauke Mai ƙarfi har Saida Shadow yaji. Kallonta yayi yace yadai?
Bata ce masa ƙala ba.

Koda suka Shiga gidan direct palon Malam Ibrahim suka nufa suna zuwa sukayi sallama. Amsawa yayi tare da Basu izinin Shiga. Shiga sukayi palon suka gaidashi ya amsa yana murmushi tare da yi Musu Sannu da zuwa.
Ƙasa suka zauna Malam Ibrahim yace ku zauna Kan kujera mana.
Ahanaf yace "a'a Baba nan ma ya Isa" murmushi Malam Ibrahim yayi yace Allah yayi muku Albarka yasa Albarka a cikin rayuwar Aurenku" Ahanaf yace "ameen ya Allah" ita kuwa Shabana a cikin Ranta ta amsa.
Suna cikin Hira aka Kira Sallar Isha Malam Ibrahim yace "Shabana Kishiga ciki Ummanki tana nan ku gaisa zamu tafi masallaci yanzu.
Toh Shabana ta faɗa tana tashi tsaye.

Koda tashiga ɓangaren Umma a Palo ta Tarar da ita, sallama tayi Umma ta amsa tana cewa "lalle Marhaba wanake gani haka kamar Auta?" Dariya Shabana tayi "tace nice kuwa Umma Ina wuni"
Lafiya ƙalau Ina su Haj Suna lafiya?"
Lafiya ƙalau Umma.
Masha Allah, "Ina Mai gidan naki?" Kanta taɗan Sosa tace sun tafi masallaci tare da Baba.
Allah sarki Muma Ai kamata yayi muyi Sallar kafin su dawo.

Bayan sun kammala Sallar ne Umma ta fara Jan Shabana da fira' a cikin firar take mata nasiha da kuma bata shawarwari akan Zaman aure. Shiru Shabana tayi tana sauraren ta kuma alhmdllh ta fahimci abunda Umma take nuna Mata. Cikin sanyin murya tace "nagode sosai Umma Allah ya ƙara girma" Murmushi Umma tayi tace bakomi Shabana Ai dole ne mu;faɗa muku gaskiya, Allah Dai yabaku Zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin rayuwar Aurenku.
A hankali Shabana tace "Ameen"
Palo suka dawo sukaci gaba da firar su.


Bayan sun dawo masallaci Malam Ibrahim ya bama Ahanaf wata Gora yace ya dinga sha kafin Kaci Komi da safe. Wanca ɗin ya ƙare?" Ahanaf yace "eh ya ƙare, "Nagode sosai Allah ya Kara girma da tsawon Rai mai Albarka" ameen ya Allah Ahanaf.

Malam Ibrahim yayi gyaran murya yace "Ahanaf ya maganar tafiyar da mukayi?" Shiru Shadow yayi Cox baisan Abunda zaice ba Allah yagani yana kewar Garinsa Ahalinsa da Kuma gidansu. Amma yarasa dalilin da yasa ya kasa Tafiya.
A hankali yace "Nima Abun yana cikin Raina Baba, kuma Yana damuna Amma Sai nakeji Bazan iya komawa gida ba. Allah yasani Inaso na tafi gida Baba Ahanaf ya faɗa cikin ɗacin Rai.
Ajiyar zuciya Malam Ibrahim yayi Yace "ba komi Ahanaf da yarda Allah Komi zai wuce. Zan tayaka da addu'a kaima ka ƙara dagewa. Koma kasani ba wai ina takura maka bane Akan maganar ganin ƴan uwanka ba a'a, kawai dai Ina hango Wani Abunne. Kaga ko maganar Aurenku da Shabana ya kamata ace kun tare hakanan saboda kai ba yaro bane, ya kamata ace yanzu kuna gidanku na kanku bawai ƙarƙashin iyaye ba.
Kuma kaga Hakan bazata faru ba Saida yardar iyayenka" Ahanaf yace insha Allah Baba zanyi ƙoƙari Komi yatafi daidai.
Toh Allah ya baka Iko Ahanaf.
Murmushi yayi yace "Amin ya Allah" Bari mutafi gida dare Yanayi Baba.
Toh Masha Allah ka tafi ɓangaren Umman taku Sai kakira Shabana kutafi.

Sallama sukayi Ahanaf ya nufi ɓangaren Umma, koda yashiga fira sukeyi.
Shabana Sai zuba dariya take, cikin dariyar tace "Wallahi Ummu da nice Bazan yarda.." sallamar Ahanaf ce ta hanata ƙarasa maganarta. Amsa sallamar Umma tayi Ahanaf ya gaidata ta amsa cikin sakin fuska tare da tambayarsa ya aiki" lafiya ƙalau Umma Masha Allah, Allah yataimaka ya bada sa'a. Ameen Ameen Ummah.
Umma tace "badai har zaku tafi ba?" Ahanaf yace "Wallahi Kuwa Umma dare Yanayi" Toh ba matsala Ahanaf tana zuwa" Sallama yayi mata tare da fita daga palon ya koma Mota.
Tashi Umma tayi tare da cewa "jirani Ina zuwa Shabana" Toh Ummu"
Bajimawa Umma ta fito da Leda a hannunta ta miƙawa Shabana. Ƙin karɓa tayi Saida Umma tayi Mata faɗa sannan ta karɓar, Umma tace Ai ba Kumi bane Humrace kawai.
Murmushi Shabana tayi tare da yiwa Umma godiya.



Tana zuwa ta buɗe Motar tashiga.
Tada Motar yayi suka fita daga gidan.
Kallonta yayi cikin sigar zolaya yace "Menene Umma ta baki kika karɓo tsabar bakida kunya?" Kallonsa tayi tace rashin kunya kuma da akayi me?" Da kikazo Mai kika kawo Mata?" Wannan kuma laifin kane da Baka fadamin gurinda zamuje ba" tafaɗa tana murguɗa masa baki.
Murmushi yayi yace "Ai na faɗa miki gurinda zamuje naga kin tsorata, Sai kawai na fasa muka zo nan ɗin.
Shuru tayi Dan yau ɗin nan ta lura Ahanaf wani Salo ya ɓullo mata dashi gwara kawai ta lallaɓashi ya maidata gida sumul ƙalau kamar yadda ya ɗauko ta.

Haka dai har suka ƙarasa gida yana parking ta buɗe ƙofar ta fita.
Bayanta yabi har cikin palon inda suka Tarar da Ammi da Dady Suna fira, Gaidasu sukayi.
Dady Yace "ya gurinsu Malam Ibrahim din Suna lafiya Dai ko?" Shadow yace "Suna lafiya ƙalau Dady sunce a gaidaku" yayi kyau Dady yafaɗa Yana murmushi.
Tashi Shabana tayi tashiga ɗakinta humarar ta aje tare da cire Hijab ɗin jikinta. Gefen gado ta zauan tare da ɗaukar wayarta ta Danna Kiran wayar Hidaya. Bajimawa ta ɗauka Bayan sun gaisane Hidaya tace "Wai Nikam Sai yaushe zaki zo ne Shabana? Gajeren tsaki tayi tare da cewa "ke nifa ba fita ce bana sonyi ba. Wai dole Idan zaka fita Sai kaje kana lallaɓa wani sannan abarka katafi" Ta ƙarasa maganar kamar zatayi kuka. Hidaya tace "laaaaah yanzu Mijin naki ne Wani? Wai Nikam Sai yaushe zaki girma ne Shabana? Ahanaf Mijinki ne dole ko kina So ko baki So kiyi masa biyayya kibi dokokinsa" Shiru Shabana tayi batare da tace uffan ba.
Hidaya tace "Dan Allah ki taimaka ki tambaye shi ya barki kizo kinji" Toh Zan gwada insha Allah.
Sallama sukayi ta katse Kiran.
Tashi tayi tafito Palo, tana zuwa direct dinning ta nufa.
Saida taci Abinci taƙoshi sannan ta tashi zata tafi ɗaki. Ammi wacce tazo ɗaukar ruwa ta Kalli Shabana cikin mamaki tace Ina Ahanaf ne? kika ci Abincin ke kaɗai kuma naga zakije ɗaki.
Ya mutsa fuska tayi tace "maybe yana ɗaki" Yana ɗaki kika zauna kikaci Abincin kika kyaleshi?" Ya Allah Wai Ammi Shi yaro ne da za'a ce komi Sai anyi Masa? Nida Naji yunwa Wani ne yace nazo naci Abincin? Ta faɗa Cikin shagwaɓa.
Girgi kai Ammi tayi tace "Allah ya shiryaki Shabana, Toh ɗaukin Abincin kikai masa" gaskiya Ammi Ni...... Dakatar da ita tayi tare da cewa "ba musu na nemeki ba Kawai kiyi Abunda nace" tafiyar ta Ammi tayi batare da ta sake Magana ba.



Ba yadda ta iya dole ta haɗa Masa kayan Abincin. Ɗaki ta koma tasaka Hijab sannan ta ɗauki Abincin taje ɗakinsa.
Sallama tayi ya amsa tare da cewa shigo.
Shiga tayi, sau ɗaya ta kalleshi ta ɗauke kanta. T-quater ne ajikinsa da ƙaramar Riga.
Abincin ta aje gabansa tace gashi inji Ammi.
Murmushi yayi yace nagode "Allah yayi Miki Albarka" Wani sanyi taji aranta Ameen ya Allah nagode.
Murmushi kawai yayi ba tare da yace mata ƙala ba.
A hankali tace "Saida safe" ba yanzu ba"
Sai yaushe Kenan?" Saida safe zaki tafi" Ido ta waro "tab wallhi Bazan kwana anan ba haka kawai" murmushi Shadow yayi yace "Ai kuwa kin rantse a banza" hanyar fita tayi da sauri.
Kafin Takai har Shadow ya rigata, yana Isa bakin ƙofar ya murza key a ƙofar ya cire Shi ya riƙe a hannu. Idanunta sunyi raurau alamar kiris take jira tafasa masa kuka. Cikin rawar murya tace "Dan Allah ka buɗe min ƙofa" Sai Idan Zaki tayani cin Abinci" Allah na ƙoshi. Tafiya ya fariyi ya koma Kan gado ya zauna tare da cewa "baki shirya ba ƴan Mata" gurinsa tazo cikin sanyin murya tace "Wallahi naƙoshi Ahanaf"
Yanzu Mai Zaki min?" Ajiyar zuciya tayi tace me kake so?" Hug me.
Kai ta girgiza alamar a'a.
Shadow yace "Okey Sai mu kwana anan tinda haka kika zaɓa" yafaɗa yana kanne Mata Ido ɗaya.
ƙafafunta tafara bugawa ƙasa tana yayyarfe hannunwanta fuskarta kamar zatayi kuka tace "Dan Allah kayi haƙuri" ba Abunda kikamin just hug me and go. Ido ta lumshe tanajin zuciyarta na halbawa. A hankali tace "Idan nayi bazaka sake neman Wani Abun ba?" Yace "Idan kinyi da kyau Bazan ƙara neman Wani Abun ba" ganin batada wata dama data wuce wannan yasa ta ƙarasa gabansa. Idonta ta Runtse da ƙarfi tare da rungumeshi ajikinta. Wata sassanyar ajiyar zuciya Shadow yayi tare da sa hannunsa ya ƙara rungumeta gam ajikinsa.
Da sauri ta Fara ƙoƙarin kwace Kanta daga jikinsa Amma Abun yaci tura dan riƙon da yamata bana Wasa bane........✍️✍️✍️








Nabeela Binji ce💃💃💃







More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏.


♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MO



TIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM



PAGE

3️⃣ 4️⃣












________________"Alkawari fa kayi kace just hug. dan Allah kasakeni na tafi" tafaɗa cikin muryar kuka. A hankali ya janye hannayensa daga bayanta Ai Kuwa nan take ta miƙe tsaye. Key ɗin ya Bata, karɓa tayi tana buɗe ƙofar next second a waje tayi Shi.
Dariya Shadow yayi ya girgiza kansa wannan yarinyar Akwai matuƙar tsoro.
Tana zuwa ɗakinta da sauri ta Tura ƙofar tare da Danna key ta murza. Ajiyar zuciya ta sauke tare da lumshe Idonta, a hankali ta buɗe su. Canza kayan jikinta tayi izuwa na Bacci, addu'a tayi Sannan ta kwanta. Abunda yafaru tun lokacin da yadawo gurin aiki har zuwa yanzu tafara tunawa. Iska ta furzar "gaskiya da sake haka Kawai, Shi gaya masa akayi Ina sonsa da zai fara min irin wannan iskanci, tabbas Zan ɗauki mataki kafin Abun ya wuce haka" haka dai tayi ta saƙesaƙe a ranta har Bacci yayi awon gaba da ita.



Koda safe ma ba ita ta fito ba Sai 11 lokacin ta tabbatar baya gidan. A Palo ta zauna tana Danna wayarta tajima zaune kafin tashiga kitchen tafara girkin Rana, tana cikin aikin Ammi tashigo gaidata Shabana tayi Ammi ta amsa tare da cewa "Gimbiya sai yanzu Allah yayi fitowarki Kenan?" Murmushi tayi, Sannan tace "Ammi Yau Ina so naje gidan Hidaya" Ammi tace "kin faɗawa Mijinki?" Ɗan Jim tayi sannan tace "eh na faɗa masa" Murmushi Ammi tayi tace "ƙaryane baki faɗa masa ba, kin riga da kinsan indai kika min ƙarya sai nagane to menene na wahalar da kanki?" Kai taɗan Sosa tace "Dan Allah Ammi ki barni na tafi" Ammi tace ni kuma Shabana? ai yanzu ba Kamar da bane, Ahanaf zakiyiwa wannan magiyar ya barki Bani ba, Cox yanzu wannan ikon yafita daga hannunmu ya koma gurinsa" Shabana Ji tayi kamar tafasa ihu tsabar takaici. Ammi tace kijira Idan ya dawo Sai ki tambayeshi tinda yaƙi yarda ya riƙe waya a hannunsa, kuma kinsa yau ba ya daɗe wa gurin aiki da wuri yake dawowa, kinga kina da damar tambayarsa Idan ya barki Sai kitafi" ƙala Shabana bata ce ba saima cigaba da aikinta tayi. Saboda ta Lura Ammi yanzu Akan Kumi Bayan Ahanaf take bi.







Sai kusan 5 ya dawo gidan koda yazo tana zaune a Palo tana kallo. Sallama yayi ta amsa masa ciki ciki, tare da yi masa Sannu da zuwa. Amsawa yayi tare da cewa "Kina lafiya?" Alhmdllh kawai tace tana Maida hankalinta Kan TV.
Ɗaki ya wuce batare da ya sake Magana ba. Saida aka kwashe 15 Mint Sannan ta nufi ɗakinsa

A bakin ƙofa ta tsaya batare da Shiga ciki ba. Kallonta yayi yace me kike buƙata? Ina So zanje gidan Hidaya ne plxx"
Wa kika tambaya? Ranta yafara ɓaci Amma ta danne saboda tana so ya Barta ta tafi. Cikin sanyi murya tace "yanzu dai nake tambayar ka" kallonta yayi yaga tayi Wani silent, murmushi yayi tare da cewa "ba matsala je kishirya Muje" da tayi tunanin tace masa ita kaɗai zataje Sai kuma tayi tunanin zai iya hanata. Ba yadda ta iya dole taje tafara Shiri, koda ta kammala shirin kai tsaye ɗakin Ammi taje ta gaya mata zata tafi. Ammin tace "ya barki ne?" Eh Ammi shine zai kaini" kai Ammi ta gyaɗa tare da cewa "ɗauki wannan kayan kikai mata agaidasu" ɗaukan kayan tayi tace insha Allah, muntafi" Allah ya tsare a dawo lafiya" ameen ameen.
Koda ta fito Palo yana gyara Karin hular sa. Shadda ce a jikinsa brown colour tayi masifar yi masa kyau, ga sajensa ya ƙara kwantawa yayi kyau alamar yanzu yana samun gyara. Yana ɗago kansa ta kawar da Kanta kamar bashi take kallo ba.
Gab da ita ya matsa tare da yimata raɗa a kunne yace "wato shine kika saka Hijab kalar kayana ko? Ya mutsa fuska tayi batare da tace masa ƙala ba. Murmushi yayi tare da amsar Ledar da take hannunta a hankali yace "kiyin kyau sosai"
Nagode tafaɗa tana fita daga palon.


A Mota ma Shiru tayi masa Saida yace banfa San gidan ba sannan tafara kwatanta masa har suka ƙarasa.


Palo suka Shiga tareda yin sallama. Ba kowa a palon kallonsa tayi tace ka zauna bari naje na kirata.
Okay ba matsala Shadow yafaɗa yana bata Ledar da suka zo da ita karɓa tayi Sannan ta tafi.
Assalamu alaikum Shabana tafaɗa tana Kwankwasa ƙofar.
Amsa sallamar Hidaya tayi tare da cewa shigo Mana.
Tura ƙofar tayi tashiga. Hidaya tace "Amare Sannu da zuwa" harara Shabana ta zuba mata tace "ba Amare ba angwaye" murmushi Hidaya tayi tare da tambayarta su Ammi? "duk Suna lafiya" Suna cikin fira Hidaya tace "Ina angon yake? Ya mutsa fuska tayi tace "Yana Palo" Ido Hidaya ta zaro tace "wane palon?" Harararta tayi tace "wane palon kuwa na gidanki mana" Ya Allah Amma gaskiya Shabana bakida kirki yanzu Dan Allah kizo da Mutum kibarshi a Palo" Shabana tace "nan ɗin kike so nazo miki da shi ne ko Yaya? Tashi Hidaya tayi tasaka Hijab ɗinta ta fita Palo batare da ta sake bi kan Shabana ba.

Gaisawar mutunci sukayi. Hidaya ta tambaye shi ya haƙuri da mutuniyar?" Murmushi yayi tare da cewa alhmdllh" ita ma Hidaya murmushi tayi tace "Allah ya bada Zaman lafiya ya kauda sheɗan a tsakaninku" ameen ya Allah. Tashi Hidaya tayi tare da ce masa Ina zuwa" okay.

Ɗaki ta koma ta Kalli Shabanatace Toh mara kunya Tashi ki kai masa ruwa" Harara Shabana ta zuba mata tace "ai gidanki yazo ke meyasa bazaki bashi Ruwan ba?" Hidaya tace bafa Nason rainin wayau kitashi ki kai masa Ruwa" Shabana tace Ke bafa dan nazo gidanki ba zaki dinga Mun Abunda kikaga dama ba, yanzu nan sai na koma inda na fito" Sanin halinta yasa Hidaya tace "Naji rigimammiya, Dan Allah kiyi haƙuri Ki kai masa Ruwan Badan Halina ba kinji" Tashi Shabana tayi tace "sai yanzu kikayi Magana haka Kawai kitasani gaba kina Bani umarni Sai kace kece Ammi" tafaɗa tana fita daga ɗakin. kai Hidaya ta girgiza tace "Allah ya shiryaki Shabana."


Bayan ta kai masa ruwan da Abun taɓawa ta zauna gefe tana Danna wayarta. Kallonta Shadow yayi yace Dan Allah kidan ara min wayarki 2mint.
Wayar ta bashi batare da tayi Magana ba.
Amsa yayi ya Fara duba abubuwa, Sai can ya Bata wayar yace tnx. Bakumi ta faɗa tana jingina bayanta da kujerar da take kai.


Sun taro a Palo Sai fira suke Suna Dariya, Hidaya da mijinta sai tsokanar Shabana suke Ahanaf Yana kare Mata. Shabana "tace ai wannan halin naku yana ɗaya daga cikin Abunda yasa bana son zuwa gidanku" dariya sukayi Ahmad mijin Hidaya yace to ayi haƙuri mun daina" Kar ma Allah yasa kudaina Shabana tafaɗa tana hararar su. Dariya sukayi.
Fira sukayi sosai Har aka Kira magrib Ahmad da Shadow suka tafi masallaci. Su kuma sukayi Shiga ɗaki dan gabatar da Sallah.
Bayan sun kammala ne Shabana ta kwanta kan gado tana miƙa. Kallonta Hidaya tayi tace "wai wannan wane kalar Zama kuke da Ahanaf ne?" Kallonta Shabana tayi tace "me kika gani halan?" Hidaya tace tambayar ki fa nayi Menene kuma sai kin Maido min da tambayar?" Shabana tace "Ikon Allah tohm ban fahimceki bane shiyasa na maido miki da tambayar" okay Ina nufin a matsayinsa na mijinki me yasa baki kula dashi yadda ya kamata komai Sai ance kiyi masa zakiyi" baki Shabana ta saki galala Tana kallon Hidaya. tab Lallaima wannan Matar kince Wani

Please Login or Register in order to submit comment