Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mai zaki masa ta Ina zaki taimakeshi? Hafeeza ta faɗa Tana ƙure Shabana da Ido.

Numfashi Shabana ta furzar tare da gyara Zamanta tace Nima kaina banida amsoshin waɗan nan tambayoyin naki Hafeeza, Abunda nasani kawai shine Ina son sake ganinsa.
Kallonta Hafeeza tayi ta girgiza Kai tace okay Bari nashiga na shirya Sai muje.
Murmushi Hafeeza tayi tace nagode Goty.
Harara Hafeeza ta ɓalla Mata tace eh Ai duk lokacin da kike son yaudara ta haka kike kirana da Wani Goty na cuta.
Gabaki ɗayansu dariya suka Saka.




Nifa gaskiya na Fara gajiya Shabana tun ƙarfe Nawa muke nan gurin Kamar wasu marasa mafaɗa
Muna zaman jiran Abunda ba tabbas.
Maybe fa Ina ga bawan Allah nan ba lafiya yake ba Hafeeza.
Idan baki Manta ba farkon ganin mu dashi irin lokacin ne
Kuma kullum irin wannan lokacin nake zuwa Nan nayi ta faman jira but Shiru.
Tsayuwa Hafeeza ta gyara tace to Kodai zamu tambayi masu Saida Man nan muji yaushe ne last ɗin zuwansa nan.
Kai Shabana ta gyaɗa tabbas Abunda ya kamata muyi Kenan tun farko.

Gurin masu Saka Mai su kaje, Bayan sun gaisa ne Shabana ta tambayeshi Shadow.
Tana masa kwatance ya gane Wanda take nufi.
Jim yayi kaɗan sannan yace tabbas Na gane Shi Amma gaskiya ya kwana biyu baizo nan gurin ba Hajiya.
Hannunta ta dunƙule taɗan daki goshinta tace kashhhhhh!
Kuma dan Allah bakasan gurin da zan iya samun sa ba?
Kai ya girgiza yace gaskiya ban Sani ba Hajiya.
Godiya suka masa sannan suka Shiga Mota suka nufi hanyar gida.

Hanyar da sukabi ɗazu ba ita Shabana tabi ba, wata hanyar tabi daban.
Kallonta Hafeeza tayi tace Madam ina zaki kaini ne? Kodai kema kin Sami taɓuwar hankali ne?
Ko kulata Shabana batayi ba taci gaba driving ɗinta, dalilin da yasa Shabana ta canza hanya shine ganin Yamma tayi za'a iya samun cinkosun ababen Hawa.
Ta wata sabuwar unguwa suka biyo unguwar sit ba hayani.

Ke Dalla Malama kashe Mana wannan banzar waƙar Shabana tafaɗa tana hararar Hafeeza.
Bazan kashe ba
ba ruwanki da waƙata hausawa sunce Shan Koko buƙatar Rai dan haka ki barni da ra'ayina
Tohm Wallahi baki Isa ba Sai kin kasheta, Shabana ta faɗa Tana ƙoƙarin kwace wayar hannu Hafeeza, gabaki ɗaya hankalinta ya bar Kan driving ɗinda take ya Koma Kan Hafeeza.
Saiji tayi tabugi Abu kamar mutum da sauri ta take Burki kuuuuhhhhh tare da furta Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un, cikin tashin hankali suka fito daga cikin Motar gabaki ɗaya Shabana ta ruɗe jikinta har rawa yake tsabar ruɗani,
Cikin kuka tace na Shiga ukku Hafeeza nayi Kisan Kai Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un.
Riƙeta Hafeeza tayi tace kinutsu kidawo cikin hankalinki Shabana, nifa Gani nake kamar wannan Mahaukacin ne da kike nema......✍️✍️✍️




Nabeela Binji ce💃💃💃







More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏






♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM


PAGE

1️⃣3️⃣


______________Ware idonta tayi da kyau tana kallon wanda ta buge ba Shakka wannan Mahaukacin ne da ta shafe sati ɗaya tana nema.

Ya Allah yanzu ya zumuyi dashi Hafeeza?
Ya Kuwa zamuyi dashi in Banda mukaishi asibiti cikin gaggawa, cewar Hafeeza Tana kwala Kiran Wasu samari da su kazo wuce wa ta gurin,
Suna zuwa Hafeeza ta roƙesu dan Allah su taya su Saka Shadow a Mota,
daga farko har sun so suƙi Amma ganin magiyar da Shabana take Musu ne yasa su kama Shadow suka saka musu Shi a Motar.
Godiya suka Musu sosai sannan suka Shiga Mota suka bar layin da gudu Kamar zasu tashi Sama.

Ki tafi a hankali mana Shabana haka ai Sai kisa mu sake Wani accident, kina driving na ganganci Kuma kina kallon Baya haba dan Allah.

Shiru Shabana tayi Kamar bataji Abunda Hafeeza tace ba,
ita Bata da burin da yawuce taganta A asibiti,
gabaki ɗaya ta ruɗe ba Abunda zuciyarta keyi face bugawa da sauri sauri.

Cikin Wani katafaren asibiti tashiga parking tayi a daidai gurinda ake parking motoci, cikin sauri ta fita har tana haɗawa da ɗan gudu gudu, takira waɗan da zasu shigar da Shadow ciki,
A kan gadon asibiti suka ɗaura Shadow da ko motsi Baya yi suka Fara Tafiya dashi cikin sauri,
Bayansu Shabana tabi har bakin ƙofar Wani ɗaki,
shigar dashi ciki sukayi.
Shabana tafara ƙoƙarin Shiga Amma sai suka hanata.
Kiyi haƙuri kijira mufito Shabana ba'a Shiga nan ɗin kinji.
Dan Allah kabarni nashiga Dr tafaɗa tana goge hawayen idonta.
Da hakan zai yiyu da ba Abunda zaisa na hanaki Shiga kiyi haƙuri plx, cewar Dr Yana rufe ƙofar ɗakin alamar Baya so taƙara yi masa wata Maganar.

Zama tayi a hankali Kan kujerun da suke gefen ɗakin tare da dafe Kanta da yake matuƙar Sara mata.
Kusa da ita Hafeeza ta zauna ta dafa kafaɗarta tace dan Allah ki daina zubar da hawaye haka Shabana, ba kuka ne Abunda ya dace muyi ba, kamata yayi muyi masa Addu'a Allah yabashi lafiya kinji, Hafeeza ta faɗa cikin sigar lallashi da son kwantar wa Shabana da hankali.
Saboda ita ma da Kanta ƙarfin hali take bataso tayi hawaye ne har Shabana tagani.

Yanzu ya zanyi Hafeeza? Me zancewa Ammi? Kima janye zancen Ammi mezan cewa Dady? Kinfi kowa sanin halinsa Baya yiwa kowa uzri,
yanzu abun nan da yafaru bazai taɓa yadda ƙaddara bane Saidai yace tuƙin ganganci ne.
Dan Allah ki faɗamin menene mafita Hafeeza.
Ta ƙarishe maganar tana fashewa da kuka mai sautin gaske.
Rungumeta Hafeeza tayi tana bubbuga bayanta a hankali kidaina kuka Shabana insha Allah komai zaizo da sauƙi.
Karɓi waya ki Kira Ammi ki faɗa Mata halinda ake ciki, dan wannan ba Abun aja baki ayi shuru bane.

Wayar ta karɓar ƙirjinta ta Sai ƙara bugawa yake,
No ɗin Ammi ta danna wa Kira cikin fargaba da tsinkewar zuciya, a ringing na biyu Ammi ta ɗaga tare dayin sallama,
Cikin sanyi murya ta amsa sallamar tare da cewa barka war haka Ammi.
Barka dai Shabana, kina lafiya Kuwa? Mai yake damunki? Naji sautin muryarki Kamar kina cikin damuwa.

Ajiyar zuciya Shabana tayi tace akwai matsala Ammi, Wani na buge da Mota, yanzu haka Mun Kaisa asibiti nida Hafeeza, Ammi bansan awane hali yake ba, tsorona ɗaya Kar ya mutu a ta dalilina, Shabana tafaɗa cikin sautin Kuka.

Ya subhanallah Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un.
Yanzu Mai Dr yace muku? A wane hali marar lafiyan yake?


Basu fito ba Ammi Suna can tare dashi.
Okay gani nan zuwa asibitin yanzu insha Allah zan kira mahaifinki na faɗa masa halinda ake ciki.
Tohm Ammi na gode sosai Shabana ta faɗa Tana goge hawayen idonta.
Ki kwantar da hankaliki kinji zai Samu lafiya da yardar Allah.
Tohm Ammi insha Allah.

Sun shafe awanni biyu suna jiran likitocin sufito daga ɗakin da aka Shiga da Shadow, da sauri Shabana ta miƙe tsaye tana tambayar Dr ya jikin nasa.
Ku biyoni office shine Kawai Abunda Dr ya faɗa ya juya ya tafi Abunsa.
Cikin sauri Ammi Hafeeza da Shabana suka bi Bayan Dr.

Suna Shiga Dr Fahad ya Basu izinin zama,
Gyaran murya yayi tare da zare glass ɗin dake saƙale a idonsa.
Magana yafara cikin nutsuwa jikinsa da sauƙi alhmdllh, bawata matsala yanzu saidai ƴan raunukan da yasamu a kafa da Kuma gefen kansa, Suma ba wasu masu yawa bane, zai warke nan bada jimawa ba Insha Allah.

Kallon Juna Shabana da Hafeeza sukayi cike da Al ajabi.
to ya akayi Dr baiyi Magana akan taɓin hankalin wannan mutumen ba? Tambayar da take saƙale acikin zuciyoyinsu Kenan.

Shabana ce ta kasa daurewa tace Dr Fahad kace bawata matsala fa? Kuma har gwajin kwakwalwa kun masa ba matsala? Shabana tafaɗa cikin mamaki.

Ko Ina Mun Duba Shabana bawata matsala Kamar yadda na faɗa Miki tun a farko.

Tabɗijam shine Abunda Shabana tasamu damar furtawa.

Dr wannan mutumen Mahaukaci ne fa Yana da matsalar kwakwalwa. Anya kun bincikesa da kyau Kuwa? Cewar Hafeeza Tana kallon Dr Fahad tana son tasami cikakken bayani daga bakinsa.

Mahaukaci Kuma Hafeeza? Koda yake ba Abun mamaki bane, tun daga Yanayin kayansa da kuma dattin da nagani a jikinsa nasan cewa Mahaukaci ne.
Amma fa tabbas ba Abunda yake damun kwakwalwar sa.............✍️✍️✍️



Nabeela Binji ce💃💃💃






More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏.




♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM


PAGE

1️⃣4️⃣











__________________Tabɗijam to Kodai sanadiyar accident ɗin da ya samu ne kwakwalwar sa ta dawo normal? Shabana ta faɗa Tana kallon Dr Fahad.
Aa gaskiya cox raunin da yasamu kwata² ma bai Shafi kansa ba raunin iya hannu da ƙafarsa ne.
Kuma tabbas Mun bincikesa sosai ba abinda yasamu kwakwalwar sa. Dr Fahad ya faɗa cike da kwarin gwiwa

Iska Mai zafi Shabana ta furzar tare da cewa Iko Sai Allah, Kenan Dama wannan bawan Allah ba haukaci bane?
Tohm Taya akayi mu kaganshi cikin yanayi na taɓuwar hankali?

Hakan zata iya faruwa bisa dalilai guda biyu,
Kodai shi ma'aikacin Sirrine
ko kuma criminal ne
Yake ɓuye kama a matsayin mai taɓin hankali, cewar Dr Yana kallon fuskar Shabana.

Sunkuyar da Kanta tayi ƙasa Batare da tace komai ba,
Amma har ranta Bata yarda da maganar Dr ba.

Kallonta Ammi tayi cikin ɗaure fuska tace Ina kiksan Mahaukacin nan Shabana?
Menene a cikin zuciyarki kike ƙoƙarin ɓoyemin?
Kwana biyu naga kin canza sosai ba Kamar daba,
Nida a iya sanina ba Abunda kike ɓoye min a rayuwa, duk Abunda kikayi daidai da ba daidai ba Sai kin faɗa min, saidai nayi miki faɗa Idan kinyi Rashin kyautawa,
Amma kwana biyu kin canza Mai yasa? Ammi ta faɗa cikin ɓacin Rai.

Dan Allah kiyi haƙuri Ammi Bari Idan Mun fita zanyi miki bayanin komai da komai insha Allah. Cewar Hafeeza cikin sigar rarrashi.

Tashi Ammi tayi tafita daga office ɗin Hafeeza ta mara Mata Baya cikin sauri.

Dr Zan iya Shiga na duba shi?
No Shabana yanzu Yana buƙatar Hutu gaskiya Sai ƙarfe 9 zaki Samu damar ganinsa.

Okay godiya nake Dr
Ba kumi ranki yadaɗe.


A parking lot ta Tarar dasu Ammi tsaye tana Magana da Hafeeza, Tana ƙarasowa Ammi ɗaure fuska tana ƙoƙarin Shiga Mota, Hakan yasa tabawa Shabana Baya.
Rungumeta Shabana tayi cikin sauri tafara Magana Dan Allah kiyi haƙuri Ammi tabbas ni Mai laifi ce agurinki Amma Ina Neman afuwarki dan Allah, Idan kikayi fushi Dani a yanzu bansa waye zai tallafi lamarina ba, Dan Allah kijuyo ki fuskance ni Ammi zuyawar da kikayi kika Bani Baya ya Sare min gwiwa yasani cikin ƙunci fiye da tunani, Dan Allah kigafarceni Ammi, Shabana tafaɗa tana fashewa da kuka Mai tsuma zuciya.

Cikin sauri Ammi tajuyo ta rungume Shabana Tana ɗan bubbuga bayanta a hankali.
Kukan ya Isa haka kinji, nifa Dama ba fushi nake dake ba, Kawai Abunda ya ɓata min rai shine ɓoye min gaskiyar da kikayi Akan wannan mutumen.
Ammi ta faɗa cikin sigar rarrashi tana cigaba da shafa Bayan Shabana.
Ajiyar zuciya Shabana ta sauke tare da janye jikinta daga na Ammi Tana ɗan murmushin yaƙe tace nagode sosai Ammi.

Ita ma Ammi murmushi tayi sannan tace tohm yanzu yaushe Zaki Kuma gida? dan nikam yanzu zan kuma Cox da misalin ƙarfe 8 Dadyn ki zai dawo gida, Inaso na Kuma kafin ya iso tafaɗa tana kallon Shabana.

Ɗan sosa Kanta tayi sannan tace Ammi Dr yace Sai misalin ƙarfe 9 Zai farka,
Toh ke yaushe zaki kuma gida kenan?
Sunkuyar da Kanta tayi sannan tace Ammi nan nake so na kwana Dan Allah.

Ido Ammi ta ware cikin mamaki tace kina cikin hankalinki kuwa?
Ki kwanta Ina? kuma gurin wa? Baki Shabana ta buɗe da nufin sakeyin Magana Ammi ta ɗaga mata hannu alamar ba tason jin komai Daga bakinta.
Hakan yasa taja bakinta tayi Shiru.

Ammi tamaida kallonta Kan Hafeeza tace 9:30 tayi muku a gida Hafeeza wllhy Idan kuka wuce haka ranku Idan yayi dubu sai ya ɓaci, Ammi tafaɗa cikin ɗaure fuska.

Yah Salam tohm agurin wa zamu barshi Ammi? Majinyaci ne fa, Kuma nice nan nayi sanadiyar shigarsa wannan halin Idan mukayi haka bamu kyauta Masa ba Ammi.

Iya Abunda Zan iya Kenan, Kuma ki tanadi Abunda Zaki faɗa wa mahaifinki Akan mutumen da Kika kaɗe, nariga da nafara faɗa Masa Abunda ya faru ɗazu a waya, Nima nan Inaso naji Taya kika San Shi, kinfi kowa sanin halinsa mahaifinki ba Abunda ya tsana sama da ƙarya, Al Adar shice Idan an faɗa masa Magana Sai ya bincike asalinta kafin ya yanke hukunci.
Ruwanki ne ki faɗa masa gaskiya ko kuma ki masa ƙarya. Ammi ta faɗa tare da buɗe mota Tashiga tabar asibitin.


Cikin asibitin suka Koma Hafeeza ta zauna a kan ɗaya daga cikin kujerun da ke ƙofar ɗakin da akan kwantar da Shadow, Shabana Kuwa tsayawa tayi kusa da Hafeeza tare da jingina jikinta da Bango kamar wacce ke gadin Hafeezar.
Ki zauna Mana Shabana Ai Har yanzu da sauran lokaci kafin ya farka fa 8:11.

Bana buƙata shine Kawai Abunda Shabana tasamu damar furtawa a hankali.

Tohm ai sai kiyita faman tsayuwar cewar Hafeeza a ƙufule.

Ƙarfe 9 daidai Shabana ce tsaye a office ɗin Dr Fahad tace time ya cika Dr Zan iya shga yanzu?

Murmushi yayi rigimammiyar Ammi Idan kina son Abu Toh tabbas ba Wanda zai zauna cikin kwanciyar hankali, Dr Fahad ya faɗa cikin zolaya.
Ita ma murmushin tayi batare da tace komai ba.
Dr yace okay muje muganshi maybe yanzu ya farka Insha Allah.

Dr a gaba Shabana a bayansa a haka har suka ƙarasa ɗakin da Shadow yake, Hafeeza da Ke zaune Sai faman Danna wayarta take ta miƙe tsaye tare da gaida Dr Fahad.
Amsawa yayi cikin sakin fuska tare da cewa ya Fama da rigimammiyar Ammi? Murmushi Hafeeza tayi sannan tace Muna kanyi Dr.
Shabana tanajin duk Abunda suke faɗa Amma taƙi ta kulasu Cox ita Bata da burin da yawuce taga Shadow yanzu.
Dr ne ya murɗa ƙofar suka Shiga zare Ido sukayi tare da furta Innalillahi Wa'inna illaihi Raju'un a tare tsantsar tashin hankali ɗauke a fuskukin su.............✍️✍️✍️✍️






Nabeela Binji ce💃💃💃






More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏.


♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM


PAGE

1️⃣ 5️⃣




________________ Idanun su tar Akan "Shadow da ya gama hargitsa kayan ɗakin, Jini Sai zuba yake a gurinda akayi masa dressing, Saboda ya bubbuge gurin, ya ƙara jiwa kansa ciwo"
Kaga Abunda nake faɗa maka ko Dr na faɗa maka yana da taɓuwar hankali, Shabana ta faɗa cikin tashin hankali Saboda jinin da taga yana zuba daga jikin Shadow.


Tafiya Dr yafara a hankali yana bin ɗakin da kallo har ya ƙarasa gurinda Shadow yake tsaye tamkar an dasashi.
Hannunsa yayi ƙoƙorin riƙewa Amma Shadow yaƙi yarda Dr ya taɓa Shi, cikin sauri yaja da Baya.

Sunyi magana har sungaji Shadow yaƙi yace musu uffan, Dr "kodai kurma ne? haka ma farkon ganin mu dashi nayi masa Magana Amma ko kallon gurinda nake baiyi ba" girgiza kai Dr yayi sannan yace "ba kurma bane Shabana yana Jin duk Abunda muke faɗa, maybe dai akwai Abunda ya hana shi Magana ne" toh mai ya kamata muyi masa yanzu? Shabana ta tambayi Dr Fahad idanunta akan Shadow tana kallon sa cike da tausayawa. Allurar bacci zamu ƙarayi masa tukkunna.

Lokaci fa na Tafiya Shabana, yanzu 9:20 yakamata kizo muje gida
Cewar Hafeeza Tana kallon wayar hannuta, Wani haushi ne yakama Shabana jitake kamar ta laftama Hafeeza Mari ko zataji sanyin a ranta, har tabuɗe baki da nufin tace ba zataje ba Amma tunawa da garganɗin Ammi yasa taja bakinta tayi shuru tare da Maida hankalinta Akan Dr Fahad tace masa zan tafi gida Dr Ammi tace karmuyi dare Dan Allah Dr ka Kula dashi kamasa duk Wani Abunda ya dace kuɗi ba matsla bane, Amma ina neman alfarmar a Kula dashi Kamar sauran mutane Dan Allah Dr, taƙarasa maganar cikin raunin murya.
Ki kwantar da hankaliki inshallah zamu bashi kulawa yadda ya dace, mu ai taimakon mutane shine aikin mu inshallah za'ayi yadda kike So,
Murmushi Shabana tayi tace Sai nakiraka naji halinda Ake ciki, ta faɗa tana kallon Shadow da tun ɗazu yake tsaye guri ɗaya Kamar Robot.

Hanyar fita ta nufa batare da tasake Magana ba.
Girgiza kai Hafeeza tace "Saida safe Dr" murmushi yayi yace Allah ya tashe mu lpia Hafeeza.

Tafe suke cikin Mota ba Wanda yake Magana a cikinsu kowa da tunanin da yake a cikin ransa, a haka har suka ƙarasa gidan su Shabana, ƙofar gidan Hafeeza tayi parking, ta Kalli Shabana tace "madam Sai da safe zan kawo miki Motar ki, dare yayi Kuma kinsan Dai bazan hau Adaidaita ba yanzu.
Buɗe Motar Shabana tayi ta fita, tana gyara mayafin kanta, gidan Baya ta buɗe ta ɗauko jakar Shadow wacce a lokacin da suka bigeshi sun ɗauko har jakar tasa, ta gefen Hafeeza ta koma a hankali ta furta sai da safe nagode Goty.
Murmushi Hafeeza tayi sannan tace Allah ya tashemu lafiya.
Cikin gidan Tashiga, ita kuma Hafeeza ta ɗauki hanyar gidansu a ɗari 360.


Koda Shabana tashiga gida Bata Tarar da Ammi a parlour ba tasan tana gurin Dadyn ta, cikin sauri tashiga ɗakinta tare da aje jakar hannunta ta hau tuɓe kayan jikinta dan yanzu ba Abunda take buƙata sama da tayi wanka, toilet ta faɗa cikin sauri.
Ta ɗauki lokaci kafin tafito.
tana fitowa ta shirya ta saka wata dogowar Riga marar nauyi, hijab ta ɗaura Saman rigar sannan tafito waje cikin sauri, direct part ɗin Dadyn ta tanufa.
Sallama tayi Saida taji an amsa mata sannan ta Tura ƙofar tashiga a hankali.

Gaidasu tayi tare da yiwa Dadyn ta barka da zuwa,
Amsawa yayi yana tsokanar ta da Auta iyayen rigima,
Murmushi tayi sannan tace Dady Ai yanzu na girma na daina rigima ba Wanda nake tsokana ko Ammi?
Taɓe baki Ammi tayi tace Ina Girma anan kullum ana Fama dake Kamar wata ƙaramar yarinya.
Shagwaɓe fuska tayi tare da Maida kallonta kan Dady tace "Dady Kaji Abunda Ammi tace ko?
Murmushi Dady yayi yace a'a Ni ba ruwa kunfi kusa keda Ammin taki, kin manta Wani lokaci Idan Kuka tashi haɗe min kai ku ke nakasa gane gaskiyar kowane lamari.
Tohm yanzu nabar team ɗin Ammi nadawo team ɗinka Dady ta faɗa tare da matsawa kusa da Dadyn.
Dukansu dariya sukayi, Ammi tace badai gyaran gyaran ba tayi Mai, indai Shabana ce yanzun nan zaku ɓata.
Bazama mu ɓata ba ko daughter?
Nodding ɗinkata tayi tana murmushi.


Gyaran murya Dady yayi tare da ɗan ɗaure fuska Kamar bashine yake Wasa da dariya ba yanzu, cikin kakkausar murya wacce ba alamar Wasa a cikinta Dady yace "Shabana Ina so ki faɗa min gaskiya akan batun wanda kika bige ɗazu, mahaifiyarki tafara faɗamin Abunda yafaru a office ɗin Dr Fahad, allamu sun nuna cewa kinsan wannan mutumen, tunda har Dr yana faɗin ba mahaukaci bane Amma kekuma kina ƙoƙarin musa masa akan aikinsa.
Ki gayamin Ina kika san Shi?
Me yake tsakaninku?
Taya ki kasan shi mahaukaci ne?

Wasu yawu Shabana ta haɗe da kyar jikake kut, gabaki ɗaya ta ruɗe tama rasa mai zata cewa Dady, ita Dai tasan bawata alaƙa a tsakaninta da wannan mahaukacin Abu ɗaya tasani shine Yana bata Tausayi, tun Ranar da taɗaura idonta akanshi takasa mantashi takasa Manta kallon da taga yana mata, tundaga ranar kullum sai tayi mafarkinsa.....
Ke muke saurare, maganar Dady ta maidata cikin hankalinta.

A hankali ta buɗe bakinta tafara Magana cikin sanyin murya tace "ba Abunda yake tsakanina dashi Dady hasalima sau ɗaya na taɓa ganinshi a rayuwa Sai kuma Yau Dana Masa Gani na biyu! Nan Shabana tabama iyayenta labarin duk Abunda yafaru, tare da nuna masu Zanen da Shadow yayi nata.
Gyaɗa kai Dady yayi sannan yace zaki iya faɗamin wane gidan Mai ne kuka Fara haɗuwa dashi.
Eh Dady gidan Man AA Rano.
Okay zaki iya Tafiya.
Tashi tayi jiki ba ƙwari tare da cewa Sai da safenku.
Allah ya bamu Alkhairi.

Tana fitowa daga ɗakin direct dining area ta nufa, Abinci ta Saka kaɗan tafara ci cox rabonta da Abinci tun 12pm. tana gamawa ta Koma ɗakinta a gefen gado ta zauna tana danna waryata idanunta suka faɗa kan jakar Shadow, Ido tazuba tana kallon jakar ba Shakka wannan tsadaddar jaka ce kuma daga ganinta kasan bata Wani tsufa ba datti ne Kawai matsalar ta.
A hankali tasaka hannunta ta ɗauko jakar, buɗeta tayi tana Duba abubuwan da ke ciki, duk kayan Zane ne wasu ma har sun Fara bushewa,
Haka taci gaba da duba saƙo da Lungu na jakar Wani zip ta buɗe taci araba da wasu takardu, ɗaukosu tayi ta fara buɗewa a hankali. Ido ta ware tana Duba takardar da kyau tirƙashi shine Abunda Shabana ta furta cikin mamaki..............✍️✍️✍️







Nabeela Binji ce💃💃💃






More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏.







♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM


PAGE

1️⃣ 6️⃣











____________________ Zanen wannan mahaukacin tagani raɗau Akan pepper kamar an ɗauki photon sa, ban banci kaɗan ne ƙasumbar sa da taƙara yawa Kuma Bata samun Kulawa kamar yadda yake a Zanen Amma kallo ɗaya zaka masa kagane shine a Kan pepper.
Rubutun da yake a ƙasan Zanen ne yaja hankalinta,
Ahanaf Muhammad Imran (SHADOW THE BEST ARTIST)
Shine Abunda tagani a ƙasan Zanen ta maimaita sunan yafi a ƙirga tana juya takardar a hannunta tana kallo cike da mamaki.
Ɗayar pepper ta buɗe Shima Wani Zanen taci Karo dashi Amma saidai wannan Zanen na mace ne, ƙurawa Zanen Ido tayi tana kallonta ba Shakka kyakyawa ce ajin farko ga Kuma Zanen ta yafita raɗau Kamar zatayi Magana.
Ƙasa tayi da idonta tana kallon rubutun da yake a ƙasan Zanen wannan yafi na Shadow yawa Cox Shi ba iya Suna bane, a hankali tafara karantawa.
Noriyya Mukhtar Salah
(Norr)
Haƙiƙa ke ɗin haskena ce Kuma Abar so da ƙaunata, Ina sonki fiye da So Ina ƙuanarki tamkar Raina Ke komai nace. I luv u from the bottom of my heart my Norr my wife.
Ta karanta wannan rubuntun yafi sau Biyar, tamabayoyi ne da yawa suke yawo a kwakwalwar ta.

Dama Yana da Mata ne?
Menene dalilin taɓuwar hankalinsa?
Daga wane guri yake?
Kodai maganar Dr Fahad gaskiya ce?

Batada Wanda zai amsa Mata waɗan nan tambayoyin Sai wannan mahaukacin Ahanaf Shadow Amma Taya Kenan?
Wanda Har yanzu Bata Ji Maganar sa ba,
Jin Kanta Yana mata ciwo ne yasa dole ta haɗa kayan tamayar dasu cikin jakar Amma Banda takardun da suke ɗauke da Zanen Shadow da Norr.

Wayarta ta ɗauka ta Danna Kiran Dr Fahad.
Bayan ya ɗaga ne take tambayar sa ya jikin Mara lafiyar?
Tohm da sauƙi za'ace Dan wllhy da kyar na samu aka ririƙe shi na sake masa allurar bacci, Amma wannan Karon biyu nayi Masa Saboda na lura Yana da ƙarfin Jini, Idan akayi Masa ɗaya Zai iya farkwa kafin safe, Kuma kinga ba musan me zai iya faruwa cikin Daren ba.
Hakan ma yayi Dr.

Dr amma har yanzu baka yarda wannan mutumen mahaukaci bane ko?
Aa Shabana bawai ban yarda bane na dai faɗa miki gaskiyar Abunda bincikena ya nuna min ne a kansa, bashida ko wace cuta a kwakwalwar sa gaskiya, Kuma Duk Inda zaki kaishi a duba shi wannan amsar za'a baki.
Ya Allah to wai mai yake faruwa ne?
Shi ba mahaukaci ba kuma ya dinga jiwa kansa ciwo?
Tabbas wannan lamarin a kwai DUHUN INUWA a ciki wanda ya hana mu gane gaskiyar Hasken sa.
Babbar matsalar ma shine Rashin maganar sa Dr.

Hakane Shabana Amma yanzu mufara ganin yasamu sauƙin raunin da ke jikinsa sannan sai musan me yakamata muyi nan gaba.
Okay nagode Dr anan sukayi sallama ta kashe wayarta.
Gyara kwanciya tayi tare da furzar da Iskar bakinta, tambayoyi ne da yawa a Ranta Amma ta rasa mai amsa mata su.
A haka dai har bacci ɓarawo yayi awon gaba da ita.



Da safe Misalin 9am Zaune take a parlour tana breakfast wayar tace tafara ringing da sauri tayi pickup ganin sunan Dr Fahad ne a kan screen ɗin wayarta.
Bayan sun gaisane yace " kizo yanzu Shabana akwai matsala gaskiya" da sauri tasaki fork ɗin da yake hannunta tare da cewa matsala kuma Dr mai yafaru? Kawai Idan da Hali kizo yanzu. yana gama faɗar haka ya katse wayar sa.

Ya Ilahi! Ɗakin ta

Please Login or Register in order to submit comment