Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Wani Babban Mall dan siyo saƙon Shabana.
Chocolate ya kwaso mata Kala Kala, Sannan yaje gefen turaruka ya ɗauko mata masu tsadar gaske.
Saida yagama siyan abubuwan da yake buƙata sannan ya biya Kuɗin yafito.

Zai Shiga Mota yaga wasu mutane ukku Suna kallonsa kuma ɗayan ma har nuna sa yake da yatsa, da Alama gardama sukeyi a Kansa, kuma kallo ɗaya zakayi musu kasan ba Mutanen kirki bane.
Ahanaf bai kawo komai a ransa ba yashiga Mota ya ja ya Fara Tafiya. Amma sai yaga kamar Shi Mutanen suke bi Hakan yasa ya ɗauke hanya dan tabbatar da zarginsa. Ga mamakinsa Sai yaga har yanzu Shi suke Biya, da sauri Ahanaf ya taka motar yaƙara gudu, Suma gudun suka ƙara, ɗaya daga cikinsu ya leko da kansa yana nuna motarsa, Ahanaf ya gama tabbatar wa kansa Shine suke bi, hakan yasa yaƙara bawa motar wuta bai tsaya ko Ina ba Sai bakin police station. Suna ganin yatsaya a police station sukayi saurin juyawa da motar su suka tsaya da ita ɗan nesa da police station ɗin. Ciki Ahanaf ya Shiga ya sanarwa ƴan Sanda Abunda yake faruwa, da sauri wasu daga cikin police ɗin suka fito dan tabbatar da maganar Shadow, Ai kuwa sun hango motar su kamar yadda ya faɗa.
Suna hango ƴan Sanda sun fito, suka tada motar su suka hau hanya.
Suma ƴan sandan Motarsu suka Shiga suka bi bayansu da gudu, duk da sunyi musu nisa sosai Amma suna hango su Hakan yasa sukaci gaba da bin bayansu.

D.p.o ya Kalli Shadow yace ya sunanka? Shadow yace Ahanaf. "Tun daga Ina suke binka? Shadow yace "tun daga F&H Mall"
D.p.o yace "kasansu? Kai Shadow ya girgiza yace hasalima ban taɓa ganinsu ba Sai yau" d.p.o yace "wace unguwa kake?" Yace "Goriba road" gidan wa a Goriba road ɗin?" Shadow ya fara gajiya da tambayoyin Wannan d.p.o cikin ɗan Jin haushi yace "gidan Alh Usman Wasagu" cikin mamaki d.p.o yake kallonsa zaiyi Magana wayarsa tafara ringing ɗagawa yayi yakara a kunne, Taya akayi kuka Bari suka ɓace muku? Wannan Ai shashanci ne. Tsaki yayi tare da katse Kiran.
Kallon Shadow yayi yace "Kaji wai sun gudu ka kwantar da hankalinka ba abunda zai faru, Alh Usman abokina ne, yanzu Abunda za'ayi katashi muyi Sallar magrib sai mutafi gidan naku, Amma saidai ba zamu tafi a cikin Motar ka ba, Cox yanzu sun riga da sunsan wannan Motar.

Shadow yace "Okay ba matsala" Tashi yayi suka gabatar da Sallah.
Sannan Ahanaf ya buɗe Motar ya cire saƙon Shabana yasaka acikin motar d.p.o suka tafi.
Koda suka Isa gidan d.p.o a waje ya tsaya Shadow ne Kawai yashiga cikin palon bakinsa ɗauke da sallama, gabaki ɗaya Suna Palo Suna Hira Har Maleek da Suhail sunzo gaida iyayen nasu.
Amsa masa sallamar sukayi Bayan sun gaisane, Suhail yace "tun ɗazu nake jiran zuwanka, Ina ka tsaya ne? Murmushi Shadow yayi, yace "Wallahi wani ɗan uzri ne ya tsayar Dani" Maida kallonsa yayi Kan Dady yace "Dady tare da baƙo nake" Dady yace "Bako Ahanaf, Allah Dai yasa lafiya?" Murmushi Shadow yayi yace "lafiya ƙalau Dady" Dady ya kalli Shabana Yace "Tashi kije kisa hijab baƙo zai shigo" tashi tayi ta nufi ɗakinta. Dan ita Ammi da Hijab ɗinta tinda tayi Sallah bata cire ba.
Dady Yace "shigo dashi Ahanaf" fita Shadow yayi ba jimawa sai gashi da tare da d.p.o cikin mamaki Dady Yace "wanake Gani Kamar Abdul_Rahman?" dariya d.p.o yayi yace "ba kama bace nine Alh Usman" gaisawa sukayi cikin barkwanci kamar yadda suka Saba, Ammi ta gaidashi ya amsa tare da cewa ya haƙuri Kuma? Ammi tace "alhmdllh" masha Allah yafaɗa Yana Murmushi, Maleek da Suhail gaidashi sukayi ya amsa cikin sakin fuska.


Dady yace "d.p.o Ina ka haɗu da yarona? Allah yasa ba wata matsala bace" d.p.o yace "gaskiya ba wata matsala bace, ɗazu ne dab da magrib wannan Yaron yazo station ɗinmu yace wasu mutane Suna binsa, koda Jami'an mu suka fita sun Gansu Amma sun bi su kuma basuyi Nasarar kama su ba sun gudu, tohm Ina cikin yi masa tambayoyi ne naji daga wannan gidan yake, shiyasa nace ya bari Idan munyi Sallah sai muzo tare dashi" d.p.o ya ƙarasa Maganar Yana kallon Dady.
Mamaki ne ya kamasu gabaki ɗayansu Dady Yace "Ikon Allah to suwaye waɗan nan Mutanen? Menene dalilin da yasa suke bibiyar Shi?" D.p.o yace inda ace Mun Samu Nasarar kama su da duk waɗan nan Amsoshin zamuji su a bakinsu. Amma ko yanzu zamu ci gaba da farautarsu.
Saidai kaima yana da kyau ka ƙara kiyayewa, kasan gurinda zaka dinga zuwa karka yadda kayi nesa da mutane, saboda makashinka dama ƙalilan yake nema yaga bayanka. D.p.o yafaɗa Yana kallon Shadow.
Ajiyar zuciya yayi batare da yace ƙala ba. Cox Shi waɗan nan abubuwan da suke faruwa dashi yanzu har sun daina bashi mamaki.
Yanzu ya ƙara gasgata maganar Shabana da tace "wasu ne suke bibiyar rayuwar Shi, kuma ko suwaye a ɓoye suke.
Maganar d.p.o ce ta dawo dashi hankalinsa da yace "Nikam Zan tafi Idan kunga Wani Abun da bai muku ba zaku iya kirana insha Allah zanzo cikin lokaci" Har bakin Mota suka rakashi suna masa godiya.
Zai tada motar idonsa ya faɗa kan Ledar Shadow, ɗaukota yayi yace "ɗan saurayi ka Manta kayanka" karɓa Shadow yayi tare da Kara yi masa godiya.
Saida su kaga tafiyar sa sannan suka dawo gida.
Sun Jima a Palo Suna fira tare da jimamin wannan lamarin Na Ahanaf.
Dady yace "tabbas waɗanda suka aikata maka wannan mummunan aikin, Suna kan bibiyar rayuwarka, babban tashin hankalin ma Shine ba Wanda yasan su waye, balle a ɗauki mataki da wuri tun Basu illata maka rayuwa ba, dan dai ba abunda suke buƙata bayan ganin bayanka. Amma ka kwantar da hankalinka insha Allah ba abunda zai sameke" Ya Maleek yace "gaskiya Dady yakamata ace har office ya daina zuwa tukkunna" murmushi Dady yayi yace ai daga Yau har zuwa Ranar da zamuyi Tafiya bazai ƙara fita ko Ina ba" ya Suhail yace "gaskiya Kam haka yakamata"
Ammi tace "wannan lamarin Akwai ɗaure kai a ciki, wannan wace kalar ƙiyayyace haka?" Dady yace Sai dua'i kawai.


Haka suka ci gaba da tattauna matsalar har kusan ƙarfe goma Na dare. Dady yace "su Maleek su tafi gida dare Yanayi" haka suka bar gidan Badan ransu ya so ba.
Shima Shadow Saida safe yayiwa su Ammi ya tafi ɗakinsa.
Ledar hannusa Kawai ya aje tare da tuɓe kayansa yashiga toilet, wanka yayi koda yafito Mai kawai Shafa yasaka Jallabiyarsa mai kyau Maroon colour, tayi masifar yi masa kyau, turare ya ɗauka ya fesama jikinsa, ya ɗauki Ledar da yazo da ita yafita, direct ɗakin Shabana ya nufa, Yana Tura ƙofar yajita a Buɗe, Shiga yayi tare dayin sallama.
Amsa masa tayi tare da Jan blanket ta rufe jikinta.
Bakin gadon ya zauna kusa da ƙafafunta yace "ya ƙarfin jikin?" A hankali tace "da sauƙi" kin tabbata?" Kai ta gyaɗa masa Alamar eh.
Yace "Toh meyasa da Dady yace kije ki Saka Hijab ki fito, kikaƙi fitowa?" Har nasaka Hijab ɗin zan fita naji kaina yana Sarawa kawai Sai nafasa" Shadow yace "Ina ga fa da alama yarinyar nan sai kinsha Allura" kwaɓe fuska tayi kamar zatayi kuka tace "Wallahi nikam bana so" kwakwayon muryarta yayi yace "Sai kuwa kinshata" cikin shagwaɓa tace "Ni dai Naji sauƙi dan Allah ka daina maganar allurar nan" murmushi Shadow yayi yace "tohm na daina, tashiga saƙonki na siyo miki? Tashi tayi ta Jin Gina bayanta da gado, Ledar ya miƙa mata, karɓa tayi tace "Nagode Allah yaƙara buɗe" murmushi yace ameen.


Shadow yace "yau na haɗu da wasu mutane bansa su ba kuma ban taɓa ganinsu ba.......... Nan Shadow ya Bata labarin Abunda ya faru tunda yafito gurin sayen chocolate ɗin ta.
Shabana tace Innalillahi wa'inna Ilaihi Raju'un, Hasbunallahu wani'imal Wakil, Ahanafff su waye suke sun son ganin bayanka har haka? Kuma me ka musu? Kai ya girgiza yace Wallahi ban sani ba Shabana, Ni a iya rayuwata Banida wani abokin faɗa Wanda zance ma na riƙeshi araina Ina zarginsa da bibiyar rayuwarta.
Ajiyar zuciya tayi Sannan tace koma suwaye kar Allah ya Basu sa'a a kanka, Allah ya tona asirinsu" Shadow yace ameen ya Allah.
Tace "yanzu kuma tafiyar tanan kamar yadda Dadi yace?"
Yace "eh Dady yace tafiyar ba za'a ɗagata ba" tace "Allah yasa ƙarshen matsalar Kenan" Yace ameen ameen. haka sukayi ta fira har 11:49 koda Shabana ta ga lokacin zare Ido tayi tace "Ahanaf Wallahi Ashe dare yayi sosai, Tashi katafi Zan rufe ɗaki" Shadow ya faɗa Saman gadon yace nikam tsoro nakeji Bazan iya kwana ni kaɗai ba.
Baki Shabana ta saki galala Tana kallonsa, Murmushi Shadow yayi yace "rufe bakin Karna faɗa plx" murtuƙe fuska tayi tace "Dan Allah tashi katafi zan kwanta" Shadow yace "Wai Idan na kwana anan haramun ne? Shabana tace "Ƙaton haramun ma Kuwa" dariya Shadow yayi yace "ta Yaya Kenan yimin bayani?" Plxx nidai Dan Allah tafi ɗakinka"
Shadow yace da gaske nake anan Zan kwana fa..........✍️✍️✍️












Nabeela Binji ce💃💃💃







More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏.


♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MO



TIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM



PAGE

3️⃣ 7️⃣














________________Sauka tayi daga kan gadon ta nufi ƙofa, Shadow yace "Ina zuwa?" Tace "Palo zanje na kwana" yace Palo kuma? Tace "eh ba kace kana Jin tsoro ba, to ni Zan kwanta a Palo nayi gadinka" Wata dariya ce ta suɓuce masa cikin dariyar yace "yanzu ke Uwar tsoro dake zakiyi gadina?" Tace "eh mana tinda Zan iya kwanciya ni kaɗai a ɗaki Bana Jin tsoron Kumi ba" tashi yayi ya nufi gurinda take, ai tuni tafita waje, ƙarasawa yayi gurinta ya marairaice fuska yace "yanzu dan Allah bazaki taimaka mu kwana tare ba? da gaske fa tsoro nake ji" dariyar da tazo mata ta Danne Dan ta lura Idan ta sakar Masa fuska ba abunda ba zaiyi ba, tace "a'a Bazanyi ba Nikam" yace "Kawai natafi su Kamani?" Kai ta ɗaga masa Alamar eh. ya fara Tafiya ya tsaya yace "tafiya fa zanyi bazaki tausaya min ba dan kinga Ayiyata bata kusa" dariyar da take Dannewa ce ta su ɓuce Mata tace "Allah yana nan Allah ya tsareka Ahanaf" murmushi yayi yace "Ameen, Allah ya tashemu lafiya" ɗaki Takoma ta rufe Sannan ta hau Kan gado ta kwanta. Murmushi tayi aranta tace "Ahanaf kanada abun ban dariya.











_____________ "Da gaske kake Kagan Shi?" Yace "Wallahi munganshi yafito daga wani Mall Haj, da ya fahimci muna binsa sai ya shiga wani police station, anan yasanar wa da ƴan Sanda suka bimu da kyar muka waske musu" tace "Tirr ƙashi lallai Akwai Babbar matsala, dawowar sa gida ita ce Babban tozarcin dazan Samu a rayuwata kuma babban wulaƙanta ta, dan haka ku Sani ko nawa kuke So zan baku nidai buƙata ku kawo min shi naganshi a Mace ko a Raye" Jibgege yace "Wannan ba matsala bace Haj, ai yanzu mun riga da munsan yana wannan Garin, Toh nemansa ba Abu bane mai wahala, tabbas zamu kama shi kuma zamu kashe Shi kisa na wulaƙanci, sannan mu binne Shi a gaban idonki" ajiyar zuciya tayi tace "Idan har kukayi haka ba abunda Bazan muku ba"




Bayan ta gama waya da su Jibgege takira ƙawarta ta sanar da ita halinda ake ciki, duk inda hankalinta yake ya tashi tace yanzu wane mataki zamu ɗauka yanzu Haj?" Tsaki tayi tace nima nan cike nake da Al hini akan lamarin wannan shegen Yaron, gashi yanzu Malam yace ba Abunda zai iya yi masa, wai yanzu yafi ƙarfinsa ko aljannu ya tura masa haka suke dawowa suce sun kasa ƙarasawa gurinda yake. Yanzu Dai mafitar mu ɗaya ce su Jibgege, Dole mu sakar musu kuɗi su kashe Muna Shi, Idan dai ba haka mukayi ba tofa bamu ba kwanciyar hankali Haj" tace "Tabbas zancenki hakane.








______________ "kiyi haƙuri ki tashi muje Haj Mama take nemanki" ɓata fuska Norr tace "ƙaseem Bawai Bana son zuwa bane wallahi har cikin zuciyata kunyar su Abba nakeji" ajiyar zuciya ƙaseem yayi yace "haka zaki daure mutafi Norr ƙaddara ta riga fata, Dukan mu ba wanda yaso wannan lamarin Amma dole ne Mutum yayi haƙuri da jarabawar ubangiji" ba yadda Norr ta iya dole ta tashi ta shirya suka tafi.
Koda suka Isa gidan direct ɓangaren su Haj Mama suka Shiga, cikin farin ciki Haj Mama ta tare su, Norr zata zauna ƙasa Haj Mama tariƙo tace "a'a ƴata zauna nan" Haj Mama tafaɗa tana zaunar da Norr kusa da ita.
Haj Mama tace "ya jikin naki?" Cikin Jin kunya Norr tace alhmdllh" murmushi Haj Mama tayi tace "Allah ya baki lafiya, yaraba lafiya" a hankali tace Ameen. Haj Mama ta Kalli kaseem tace Malam fita kabamu guri Zan gana da ƴata" murmushi ƙaseem yayi yace wato korata ma Ake ko? Tohm Anjima Bazan zo tayaki fira ba" murmushi Haj Mama tayi tace "Naji Dai tashi katafi" Bayan ya fita Haj Mama ta Maida hankalinta Kan Norr tace "ƴata ya haƙuri da Wannan rayuwar?" Kai Norr ta sunkuyar tana Jin wani irin raɗaɗi aranta.
Haj Mama tace "ba Wanda yasan Abunda kikeji aranki Sai Allah, kinga Kenan ba Wanda ya dace ki kaiwa kukanki ya share miki hawaye sama dashi, Inason ki fawwalawa Allah kumi ki rungumi ƙaddaraki Norr.
Idan kin Kalli wannan lamarin Allah ne ya hukunta Shi wasu suka zama sanadi, tun ran gini tun ran Zane Allah ya ƙaddari ke Matar Al kaseem ce ba Ahanaf ba, shiyasa duk waɗan nan abubuwan suka faru, kuma dan Allah ya Kara tabbatar da Aurenku rubutaccen Al Amari ne sai yasa rabo a tsakaninku, Yasaka ɗan Al kaseem a mahaifarki ba tare da saninin Ku ko kuma son ranku ba.
Ni Bazan ce dole Sai kin zauna da kaseem ba Wai Dan yanzu kuna da rabo a tsakaninku, a'a har yanzu kina da ƴancin zaɓen Wanda kikeso ki rayu dashi. Amma kiyi tunani Akan Yaron da Zaki Haifa.
Ɗan wani da Uwar Wani Sai Allah. Idan kika barshi a hannu mahaifinsa dole zai ƙara Aure, kinsan wace kalar Mata zai Aure? Kinsan kalar riƙon da zata yiwa ɗanki? Kisani Sai jarumar Uwa ce zata iya aje muradin Ranta Dan inganta rayuwar yaronta. Sau da yawa zakiga wata ta Aure Namiji Bata sonsa, Amma da ta haihu dashi zata haƙura ta zauna dashi saboda inganta rayuwar yaranta, Wannan JARUMA UWA ce Norr.
Ni shawara Kawai nake baki saboda yanzu na Shiga tsoron riƙo Norr, Idan har Allah ya haɗa ɗan riƙo da kishiyar uwa mara Imani Wallahi ya Shiga ukku, kullum burinta ta mayar dashi Baya, nata Yaran su shiga gabansa tsabar bata tsoron Allah.

Dan Allah Badan ni ba Norr kiyi Nazari akan Abunda Zaki Haifa, da kuma kalar halinda zai Shiga Idan baki. Kowace UWA tagari JARUMA ce Akan yaranta.
Tun tuni hawaye suka Fara an baliya akan fuskar Norr. Tabbas maganar Haj Mama gaskiya ce Amma abune Mai masifar Wahala. Cikin muryar kuka tace Nagode Mama Allah ya saka miki da mafificin Alkhairi, Tabbas zanyi tunani Akan wannan shawarar taki.
Tinda aka fara wannan case ɗin ban taɓa samun nutsuwa da kalamai masu sanyaya zuciya ba kamar naki Mama, Nagode Nagode sosai tafaɗa tana fashewa da matsancin kuka Mai matukar ban Tausayi.
Rungumeta Haj Mama tayi tace "ba kumi Norr ni ƴata na ɗauke ki, ki kwantar da hankalinkii insha Allah bazakiyi nadama ba a rayuwar ki" haka Haj Mama tayi ta Bama Norr shawarwari.
Daga Baya tace "kije ki gaida Ayiyarta ku tana nan" Tohm Norr tace tare da Tashi ta nufi hanyar part ɗin Ayiya.
Koda taje Ayiya na zaune a Palo ita da ƙaseem sallama tayi suka amsa, ta gaida Ayiya ta amsa Mata cikin fara'a tare da tambayar ya ƙarfin jiki? Norr tace alhmdllh" kaseem ya kalleta yace "Na Tashi mutafi?" Kafin Norr tayi Magana Ayiya ta tare numfashinta tace "ba yanzu zata koma ba, kaji min yaro, nan ɗin ba gidansu bane Hala?" Murmushi ƙaseem yayi yace Allah ya baki haƙuri, nifa tambayarta kawai nayi?" Ayiya tace "to ba inda zata sai Anjima" ita Dai Norr tana jinsu Amma ba abunda tace "dan da ace Ayiya Bata tare numfashinta ba da za tace "ƙaseem ya Maida ta gida, ta Samu ta huta kuma tayi Nazarin kalaman Haj Mama. Kallonta Ayiya tayi tace "daughter mai kiso a kawo miki? Dan nasan masu Yaron ciki ba kumi suke So ba" kunya Norr Taji da sauri ta sunkuyar da Kanta ƙasa batare da tace uffan ba. Murmushi Ayiya tayi tace Karki ji kunya Norr ki faɗa zan sa akawo miki kinji" a hankali ta girgiza Kanta Alamar a'a.
Ayiya tace "Ai kuwa dai bazaki zauna haka ba Norr" kaseem yace "nifa tin ɗazu nazo Amma ba ace min mai zanci ba sai ita kike ta faman lallaɓawa kina tambayar ta Abunda zataci" ya ƙarasa Maganar yana ɓata fuska kamar wani yaro ƙarami. Ba Ayiya ba har Norr sakin baki tayi tana kallonsa, Ayiya tace "eh ɗin Bazan tambayeka Abunda kake So ba" Tashi yayi ya nufi kitchen yace Nagode Allah Ai inada ƙafafuna, sai naje na ɗobo da kaina" murmushi Ayiya tayi tace "ban san lokacin da zaka girma ba kaseem" Maida hankalinta tayi Kan Norr Tana Janta da fira.











_______________Fitowarta Kenan daga ɗakin Shadow taci Karo da Hafeeza Zaune a Palo, kallonta tayi cikin mamaki tace "laaaaah yaushe kika zo Gotty?" Harara Hafeeza ta zuba Mata tace "yaushe zaki San zuwana kina can kin laƙewa miji, kuma Idan akayi Magana tsabar ke munafukace kice Ni Wallahi ba sonsa nake ba tausayinsa nakeji" Hafeeza ta faɗa tana kwaikwayon yadda Shabana takeyi. murtuƙe fuska Shabana tayi tace "nifa Bana son gulma Gotty, yanzu dan kawai kinga nafito ɗakinsa shine zaki Wani fassarani, kinsan Abunda ya kaini ne halan?" Da sauri Hafeeza tace "Ina Ni rufamin Asiri, Bana maso nasan Abunda ya kaiki, wato Dan yaga Ammi bata nan shine yaƙi fita aiki ya zauna zai Mata aika aika ko? Ke kuwa tsabar bakida wayau Shine Harda wani binsa ɗakinsa.
Wallahi ni Ammi ce take Bani Tausayi, tana kaffa kaffa ta rabu da ku lafiya, Amma kuna Batun kunya Tata" Wani haushi ne yakama Shabana tace "wai ke menene damuwarki Idan ma nayi wani Abun, jikinki ko nawa? Hafeeza tace "jikinki Mana Amma ai nima za'a an bace ni gurin kwatantaki ace Wannan yarinyar ƙawar Hafeeza, ita ce ta tare gidan miji da tsohon ciki" Dariya Shabana tayi tace "Tohm ki godewa Allah Idan na tare da ciki Bada goyo ba" baki Hafeeza tasaki tana kallonta tace "fatan sharrin da kike mana Kenan? Toh Wallahi kumi abunki dole ki jira mukai ki tukkunna" tsaki Shabana tayi tace "nidai ya Mommynah take?" Hafeeza tace "Zaki iya zuwa kigani" murmushi Shabana tayi tace "Wai Yau waya taɓamin Gottyna ne?" Hafeeza tace "Ke" Shabana tace "na Bonu kuwa Bari nazo nayi rarrashi" Dariya sukayi dukansu, sun Jima suna fira kafin Shadow ya fito Palo gaisawa sukayi da Hafeeza. Hafeeza tace "wato kai kake naha Sulty zuwa gidanmu ko?" Murmushi Shadow yayi ya Kalli Shabana yace "kin taɓa cemin zakije gidansu Hafeeza na hanaki?" Shabana tace "ita yaushe nace mata kai kake hanani zuwa gidansu?" Hafeeza tace naga baki zuwa ne shiyasa nayi tunanin haka?" Murmushi Shadow yayi yace "bazata iya tamabayata bane shiyasa?" Sun ɗan jima Suna fira kafin daga baya Shadow yatafi gurin mai Gadi ya zauna.

Shabana ta faɗawa Hafeeza Abunda ya faru da Ahanaf, cikin mamaki Hafeeza tace "lallai wannan bawan Allah Yana cikin matsalar rayuwa Sulty, duk wannan Abun da suka Aikata masa ba zasu barshi ya huta ba?, wannan Zalunci yayi yawwa Wallahi, gaskiya Sulty ki ƙara dagewa wajen Taya mijinki da addu'a, Cox maƙiya sun tasa shi gaba. Nifa So ma nake Ammi tayiwa Mommy Magana ta bari ayi tafiyar nan dani Sokoto, naga wacan tsinnane ƙanen nasa da shegiyar Norr ɗin" baki Shabana tasaki tana kallon Hafeeza, tace "yanzu ke Dan Allah Gotty menene matsalar ki dasu?" Hafeeza tace "ni banida matsala dasu kawai ganinsu nake sonyi" murmushi Shabana tayi tace "Allah ya shiryaki Wallahi.



Bayan Sallan la'asar Hafeeza tace zata tafi, Shabana tace "dan Allah ki zauna har 6 muyi fira kinji" hararar Wasa Hafeeza tayi mata sannan tace "Munafuka aranki kina nan kin matsu natafi ki koma gurin Mijinki Amma kinzo kina min wani fi'ili" murmushi Shabana tayi tace "Haram ko Halal? Hafeeza tace "Halal Malak yarinya" ba yadda Shabana batayi da Hafeeza ba akan ta zauna Amma fafir Hafeeza taƙi ta zauna.


Bayan tafiyar Hafeeza ne Shabana tashiga kitchen ta Fara girki, tana cikin aikin taji kamar ana kallonta, juyawa tayi sukayi Ido huɗu da Shadow, ɓata fuska tayi tace "Har kabani tsoro Allah" murmushi Shadow yayi yace "Afuwan, mekike girka Mana ne? Allah yasa ma dai kin iya girkin, ba girkin ci karka Mutu bane" harararsa tayi tace "duk girkin da kakeci a gidan nan an gaya maka bani nake yinsa bane" Shadow yace "tab ai kuwa da banyi fresh haka ba" Shabana tace "yanzu dai kana nufin ban iya girki ba?" Shadow yace "Ni na Isa nace Auta bata iya girki ba" Aikinta taci gaba dayi Suna fira har kusan 5 40 Suna kitchen a tare. Zata sauke tunkunya ne kyallen ya zame, ta taɓa tunkunyar, da sauri tasaki tunkunyar tana ihu tare da yarfe hannunta.
Hannunta Shadow ya riƙe yana Mata Sannu tare da hura mata iskan bakinsa.

Ammi tana shigowa palon taji ihun Shabana, kuma kamar a kitchen take, da sauri Ammi ta nufi kitchen, koda taje Shadow Yana riƙe da ita Yana hura mata iska a hannu, Kamar an ce ya ɗago suka haɗa Ido da Ammi Ai da sauri ya saki hannu Shabana tare da Ja Baya.........✍️✍️✍️










Nabeela Binji ce💃💃💃







More comment
More taping 😉😉






Share Fisabilillah 🙏.



♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MO



TIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM



PAGE

3️⃣ 8️⃣














_______________ Da sauri Ammi tajuya ta koma inda tafito.


Kallonsa tayi da idanunta waƴanda suka sauya kala, ga kuma Ruwan hawaye kwance a cikinsu tace " Ammi ce Ko? Dan ita bata ganta ba cox taba ƙofar baya, Amma ganin yadda Ahanaf yaja Baya da kuma alamun Tafiya da Taji yasa tayi tunanin Ammi ce ta dawo.

Kai ya gyaɗa Mata tare da ƙara matsowa gurinda take ya riƙe hannunta yana dubawa, Yace "Naji kunya sosai wallahi, duk rakinki ne yaja, da baki kwalla ihu ba da Ammi baza tasan Muna kitchen ba" ɓata fuska tayi tace "yanzu Kenan raki ma zaka ce? bakasan ciwon da naji bane shiyasa" ganin yadda ta murtuƙe fuska ita a dole baiji tausayin ta ba. Yasa yayi Murmushi yace "to kiyi haƙuri" zauna anan nayi miki addu'a sai natafi Kar Ammi taƙara dawowa ta ganni" ya faɗa yana zaunar da ita kan kujera.
Addu'a yayi mata ya tofa mata tare da hura mata iska, Wata ajiyar zuciya tayi, cox har Ranta Taji sanyi sosai, ta daina Jin zafin.
Kallon fuskarta yayi yace "kinji sauƙi?" Kai ta ɗaga masa. Murmushi yayi yace "zai daina insha Allah, Zaki iya juyewa ne Ko na juye miki?" Tace "Zan iya" yace "kin tabbatar?" Ta gyaɗa masa kai alamar eh.
Murmushi yayi tare da fita daga kitchen ɗin, koda ya zo Palo ba Kowa, Wata ajiyar zuciya yayi ya nufi hanyar ɗakinsa.
Saida ta gama komi a kitchen ɗin ta nufi hanyar ɗakinta, tana Son taje tayiwa Ammi barka da zuwa but takasa, sai Wata kunya takeji wacce batasan dalilinta ba.




Har akayi Magrib bata fito ba, Sai Bayan Isha ta fito zataci Abinci. Tana fitowa tayi Karo da Ammi a Palo, cikin jin kunya ta gaida Ammi, hararar ta Ammi tayi tace "sai yanzu kika San nadawo Kenan? Murmushi Shabana tayi tace a'a Ammi Kawai dan naji ciwo ne yasa ban samu damar fitowa ba Sai yanzu" kallonta Ammi tayi tace "Ina kikaji ciwon?" Hannunta ta nunawa Ammi, kallon hannun Ammi tayi tana ya mutsa fuska tace "Ina ciwon yake anan? Dama Akan wannan kika cika Mana gida da ihu? Koda yake banga laifinki ba, Wanda yake duba miki kika gani Dole

Please Login or Register in order to submit comment