Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗakin Sai sautin kukansu Abba ne yadaka musu wata irin gigitaciyar tsawa yace Sufitar Masa daga ɗaki Shi ɗakinsa ba gurin kuka bane.

Cike da mamaki Ayiya tabishi da kallo tace "Anya kuwa yau Abba kana cikin hankalinka kasan mekake cewa kuwa?"

"Bana cikin hankalina Haj Shuwa duk abinda yazo bakinki Zaki iya fada kinji, Amma Dan Allah abinda nake so daku shine kufita kubarmin ɗakina plxx"

"Ba in da zamuje Abba har Sai ka Gaya Mana menene dalilin da yasa ka ɗaura auren Norr da Ni saɓanin Yaya Shadow" Al ƙaseem ya faɗa hawaye kwance a idanunsa,

Wani irin Jiri ne ya fara daukan Ayiya Wanda yasa taji gabaki ɗaya duniyar ta tsaya Mata Cak, zaunawa tayi dabar a kasa cike da matsancin tashin hankali tama kasa buɗe baki tayi Magana, Kuma ta daina Jin duk Wani Magana da suke a tsakaninsu tunda take a Duniya Bata taɓa Shiga tashin hankali irin wannan ba.

Tsawar da Abba yadakawa Al ɗaseem ce tayi nasarar dawo da ita Duniyar da muke ciki.

Yace "Kai yanzu Al ƙaseem har kayi kwarin gwiwar da Zaka tsaya a gabana Ina Fadi kana Fadi? Tohm wallahi bari kaji na faɗa Maka kana kuskuren sakin Noor Kai ba Ɗana bane Kuma Allah ya'isa ban yafe Maka ba"

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un, Lahaula Wala kuwatah illah Billah Shadow yafada cikin sautin kuka.

Al ƙaseem ya bude baki da nufin sake Magana cikin sauri Shadow ya Tashi tsaye ya rufe Masa baki tare da girgiza Masa Kai alamar Kar yakara wata Magana.

Hanyar fita Abba yakama da nufin bar musu ɗakin gabaki ɗaya.
cikin sauri Ayiya Tashiga gabansa har tana tangadi kamar wata Yar maye tace "Abba ba inda zakaje baka faɗa Mana menene dalilin ka Na aikata wannan abun ba"

Tsayuwar sa yagyara yana kallon cikin idanunta yace "bawani dallili Shuwa kawai nadaiyi ra'ayin haka ne, shiya nayi saboda da Ahanaf da Al ɗaseem dukansu ƴaƴana ne ina da ƴancin yanke hukuncin da Naga Dama akan su, sbd haka ki matsa daga Nan na wuce Shuwa"
"Ba inda zakaje baka faɗa Mana dalin wannan abun da ka aikata ba Wallahi Muhammad"

Cikin mamaki ya Kalle ta yau Shuwa da Fadin sunansa ba kunya ko Kara? Abunda Bai tabaji ba Kenan a tsawon rayuwar sa da ita, murmushi yayi yace "lallai kuwa kin Isa Shuwa Kuma Nagode sosai da tsayayya"

Zagayeta yayi da nufin fita daga ɗakin tayi saurin riƙo rigarsa tana cewa "Ina Zaka tafi kabar mu a cikin DUHU? tabbass bazaka fita daga ɗakin Nan ba har Sai ka...." Wani wawan Mari taji a kumatun Wanda ya razana ta tare da yin baya kamar zata Faɗi.

Dasauri Shadow yatare ta tafaɗa jikinsa ya rungeme ta ajikin sa Yana Jin Wani irin baƙin ciki Wanda tun zuwansa Duniya Bai taɓa cin karo da makamancinsa ba.
Idonsa yaɗago wa ƴanda sukayi ja kamar garwashi ya zubasu akan fuskar mahaifinsa,
Wanda izuwa yanzu ya kejin baya ma ƙaunar ganinsa gabaki ɗaya,
Tabbass da a ce ba mahaifinsa bane yataɓa masa Ayiya da ko waye sai ya ɗanɗana kuɗarsa. hannunta yakama yakaita bakin gado ya zaunar da ita.

Shikuwa Abba ficewa yayi daga ɗakin
Ransa a matuƙar ɓace.

Shadow Juyawa yayi ya kalli Al ƙaseem cikin murya wace take nuna tsantsan damuwa yace "karka kuskura ka musawa Abba akan duk wani abunda kaga zai aikita, kuma karka kuskura sakin Noor idan dai bashine yayi maka umarni da hakan ba"

Buɗe baki yayi da nufin magana Shadow ya ɗaga masa hannu yace "bana son jin komai daga bakin ka dan Allah Ƙaseem"
juyawa Ƙaseem yayi fuuuuh yabar ɗakin kamar zai tashi sama saboda tsananin ɓacin rai.

Gurin Ayiya ya nufa wace take zaune tun ɗazu a inda ya ajiye ta kamar wata butun butumi.
Zubewa yayi ƙasa akan gwiwoyinsa ya kamu hannayen ta yace "Ayiya dan Allah ki saurari abunda zan faɗa miki, kar kiyi wani abu wanda zaisa mutanen da ke gidan nan susan Halinda muke ciki.
koma menene kibari har mutane su watse dan Allah Ayiya" yafaɗa tare da matse hannayen ta sosai acikin nasa.

Zare hannayenta tayi cikin nasa cikin ɓacin rai tafara magana. Ahanaf bazan taɓa lamuntar wanan abunba, wannan zalincin yayi yawa ko da ace ba akan ƴaƴana wannan abun yafaru ba to ni nan mai iya tsayama koma waye ne dan ganin yasamu adalci. bare akan yarana.
Ahanaf saidai kayi haƙuri a wannan ƙaron bazanja bakina nayi shuru ba wallahi, kuma kaji na rantse"

Kansa yadafe tare da furta ya Allah wannan wace kalar jarabawa ce ya Ubangiji ina neman afuwarka ka sassauta mana wannan lamarin, wannan Rana ce dana ci buri akanta najima ina tsumayin zuwanta da muradin ganinta.
dana san haka zata kasance dani da na roƙi Allah karma ya nunamin wannan BAƘAR RANAR.
Yaƙarisa maganar cikin matsanan cin kuka tare da ɗaura kansa akan ƙafafun Ayiya, bayansa ta dinga bugawa a hankali cikin sigar rarrashi.

A gidansu Noor kuwa tuni labari ya riski mahaifiyar ta najin saɓanin da aka samu gurin ɗaurin auren. cikin tashin hankali ta miƙe tsaye tare da cewa wllhy bazai yuyu ba wannan ai hauka ne ma.



Nabeela Binji ce💃💃💃


Nabeelah Shehu Binji

09064314811
Or
09161107610




More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏🙏🙏.




♣️DUHUN INUWA♣️



STORY

AND

WRITING ✍️✍️✍️

BY

NABILA S BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM



Page

0️⃣3️⃣








____________Wannan abun ba zai taɓa faruwa ba Wallahi. saboda ko a lokacin mullkin mallaka ban taɓa jin irin wannan zalincin ba.
Kallonta tamaida kan Yassar wanda ya kasance yaya ne a gurin Norr kuma shine wanda ya kawo mata wannan baƙin labarin
Saboda a gaban idonsa kumai yafaru ba labari aka basa ba.
Tace "Yassar ka tabbata Maganar da ka faɗa min gaskiya ce kuwa? saboda muddin na bin cika nagane ba gaskiya bane tohm fa kasani ranka sai yafi nawa ɓaci wllhy"
Ta faɗa ba alamar wasa a tattare da ita.

Cikin son tabbatar mata da gaskiyar Al'amarin Yassar "yace wllhy Mommy ba ƙarya nake faɗa miki ba, Har fa suma Ahanaf yayi agurin ɗaurin auren sakamakon jin da yayi an ɗaura auren Noor da Al ƙaseem"
Nan fa Yassar ya kwashe duk abunda yafaru agurin ɗaurin auren ya faɗa mata cikin nutsuwa

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un ita ce Kalmar da Mommy tayi ta nanatawa, cikin kiɗima da tashin hankali Mommy ta nufi hanyar fita daga ɗakin.

Cikin zafin nama Yassar ya Kama hannunta yace "Mommy Ina zakije haka? Dan Allah Kar kice zakiyi Wani Abu a cikin wannan Taron, saboda Hakan ba ƙaramar matsala zai jawo ba" Yassar ya fada cikin sigar rarrashi.

"Yassar kasakar min hannu Idan ba so kake Na Ɓata Maka Rai ba yanzu"

Mommy Dan Allah "ki tsaya kiyi tunani kafin ki yanke hukunci saboda yanke hukunci cikin fushi ba Abunda yake janyowa Sai nadama Mai matuƙar muni" Yassar yafaɗa cikin marairaice fuska.

Wane hukunci Zan yanke Yassar? Ai Ni bani da abun cewa yanzu har Sai naji gaskiyar Magana agurin Dadyn Ku da Kuma dalilin yanke wannan danyen hukuncin" sannan nasan wane mataki yakamata Naɗauka.

Sakin hannun nata yayi.

Jiki ba ƙwari tabar ɗakin .

Shima Yassar mara Mata baya yayi cike da jimamin wannan abun, Dan shi Allah yasani ba Wanda yake tausayi kamar Shadow. ganin halin da yashiga dazu yayi matuƙar daga Masa hankali sosai,

Wane hali Norr zata Shiga Idan taji wannan abun? Gaskiya su Dady Basu kyauta ba kwata kwata. Ai da wannan abun da sukayi gwarama ace fasa ɗaura auren sukayi gabaki ɗaya zaifi sauƙi sosai akan wannan abun da suka aikata.

Ko wannen su da Abunda yake tunani a ransa a haka har suka karasa part din Dady.
Yassar yaja yatsaya yace "Mommy Dan Allah kibi komai a hankali, har muji menene dalilinsu Na aikata haka,
"Duk abunda kwanciyar hankali beyi ba tohm fa tashin hankali ba Zai taɓa yinsa ba"

To Insha Allah zansan ta yadda zan Ɓullowa lamarin, Zaka iya tafiya Allah yayi Maka Albarka.
Ajiyar zuciya Yassar ya sauke tare da cewa ameen ya Allah, Nagode sosai Mommy.

Juyawa Yassar ya Tafiyar sa.
ita Kuma Mommy ta Shiga parlourn bakinta dauke da sallama,

Dady ta hango tsaye agaban TV Yana kokarin canza channel. "sallamar da tayi ya amsa hankalinsa Yana Kan TV karasawa cikin palon tayi, ta zauna a Kan ɗaya daga cikin kujerun parlourn tare da cewa Ashe ma kana ciki ya gajiya.
Alhmdllh ya amsa fuskar sa dauke da murmushi.

Ya jama'ah dafatan kumai dai lafiya Ko? Ya tambaye ta cikin kulawa.

Zamanta ta gayara tare da sauke ajiyar zuciya tace Ina fa lafiya Alhj? Yanzu nake Jin Abunda yafaru agurin ɗaurin aure Nan shine nace Bari nazo naji daga bakinka, saboda kasan ba a ɗaukar maganar Yara a haukai a zauna ba tare da ƙwaƙwaran bincike ba.

"Alhj Shin da gaske Abunda naji yafuru gaskiya ne Ko kuwa shatifaɗi ne?"

Ta kuwa yayi a hankali har ya Isa gurin da take zaune Shima ya zauna tare da Kama hannayenta yafara Magana, "Eh Abunda kikaji gaskiya ne ba shatifaɗi ba. mun ɗaura auren Al ƙaseem da Noriya Maimakon ita da Ahanaf"

Gaban ta ne ya Faɗi sosai, Sai kuma ta danne cikin sanyin murya tace tohm Alh Ko Zan iya sanin dalilin haka?

Murmushi yayi tare da murza hannayenta yace wannan ba hurumin ki bane ba Hjy.
Ni yanzu Abunda nake so da ke shine kije kisami Noor ki Gaya Mata Abunda yake faruwa Kuma ki fahimtar da ita falalar yiwa iyaye biyayya akan duk Wani hukunci da suka yanke akan yaransu Idan har ba saɓon Allah bane.

Cikin sauri ta kwace hannuwan ta a cikin nasa tace Wai da gaske kake kun daura auren Norr da Al kaseem? Kuma har kake tunanin ni naje nasami Norr Na faɗa Mata wannan maganar? Wllhy wannan abun bazai taɓa Saɓowa ba.
Alh niba Zan faɗawa Norr wannan lamarin ba saboda Ina matukar sonta Kuma Ina son farin cikin ta sanin kan kane Norr Tana son Ahanaf Kuma so Bana Wasa ba,
Har Takai Ga Bata iya Ɓoye wannan abun agurin kowa, Hatta Kai da kake mahaifin ta kasan haka.
Batare da kayi tunanin halinda Ƴarka zata fada ba ka yanke wannan mummun hukuncin.
Kuma abun baƙin cikin Wai bama fasaaura auren kukayi ba Sai kuka ɗaura da ƙanensa.
Ina zakuje da hakkin Yaran Nan Alh? Ai Haihuwa ba hauka bace,
bafa Dan kun haife su bane Zai baku Damar aikata duk Abunda kuka Ga dama a kansu ba.

Allah da kansa a cikin Al Ƙur'ani Mai Girma Yana cewa ƴaƴayenku da matayenku ababen kiyone agareku, kuma zamu tambaye ko wannanne ku akan abinda muka baku kiyo.
Kenan kaga Ko tsakanin iyaye da yaransu akwai hisabi ranar gobe ƙiyama.

Alh "yakamata kuyi gaggawar canza wannan ba hagon tunanin naku tun kuna da sauran lokaci, saboda har yanzu kuna da Damar gyara kuskuren da kuka TAF KA tun lokaci Baiƙure muku ba.

Ya'isa haka Dan Allah, Dady yafada tare da ɗaga Mata hannu, cikin matsancin fushi wanda tunda take Bata taɓa ganin yayi irinsa ba yace "Haj Ina Dai ce Norr ƴata ce Ko? Kuma Ina da hakki akan nasakata ko Kuma Na hanata, tohm Dan Allah Ina roƙonki da kija bakinki kiyi shiru akan wannan abun Kar ki tunzurani nayi Abunda bakya tunani" yafaɗa a hasale tare da ciro waya daga aljihunsa ya Danna Kira.


Amaryar Shadow wannan wanka haka kin ganki kuwa? Wallahi kamar mutum ya saceki ya gudu dake tsabar kyau "cewar Meenal datake ta faman yiwa Norr picture's "ni ce Nan zan turawa Shadow su saboda abani kyakyawan Goro taƙarisa maganar tana dariya.

Murmushi Norr tayi tare da cewa kanki akeji Kuma, Ni Kam nagaji da wannan ɗauke ɗauken naki da yaƙi ƙarewa tun dazu kike Abu ɗaya Dan Allah kibarshi haka Mana, nasamu nakira my Shadow naji muryar sa Ko zanji sanyi a Rai.. ringtone ɗin wayar tane ya hanata ƙarasa maganar da ta fara. hannu tasa takarɓi wayar daga hannu Meenal, tare da cewa Ɗan Halak kamar kasan yanzu nake Shirin kiranka.

My Dad💞
Sunan da taga Yana yawo a screen din wayar ta Kenan, laaaah Ashe ma bashi bane Dady ne, tafaɗa Tana Kara wayar a kunnenta bayan tayi picking.
Tare da cewa Assalamu alaikum "Norr kizo yanzu Ina nemanki a part Dina" Kitt yakashe wayar cike da mamaki take bin wayar da kallo a ranta Kuma tana ƙissima tabbas ba lafiya ba.

Tashi tsaye tayi jikinta ba ƙwari, tacewa su Meenal Dan Allah kujirani Ina zuwa yanzu.

Murmushi meenal tayi tace "yarinyar Nan fa tafara hankali daga daura aure, tohm Ina ga ta tare Sai a Zama Saliha ko"
Dariya suka Saka gabaki ɗayansu Suna tsokanar ta.

Ita dai ko ƙala Bata samu damar cewa ba Sai ma ƙokarin barin ɗakin da take cikin sauri,
Cox ta Matso taji wannan Kiran da Dady yake Mata,
Tun da aka wayi safiyar yau take jin faɗuwar gaba. Amma data gayawa Meenal "Sai tace Mata ai haka ko wace yarinya takeji Idan za'a ɗaura aurenta" Hakan ne ma yasa ta ɗauki abun ba Komai ba.
Amma a yanzu faɗuwar gaban nata Sai tsananta yake sosai.

Cikin sassarfa ta Isa part din Dady,
ta Danna Kanta cikin palon Kai tsaye bakinta ɗauke da sallama, Amma ga mamakinta daga Mommynta har Dadyn nata ba wanda ya amsa Mata sallamar da tayi.

Ƙarasawa tayi gabansu ta zauna Kanta a ƙasa tace Dady Gani,

Gyaran murya yayi tare gayara Zaman sa yace "Noriya Ina So ki buɗe kunnuwanki da kyau kiji Abunda Zan faɗa Miki, Kuma Bana son musu a cikin umarnin da Zan Miki yanzu kina Jina ko"?

Cikin sanyin murya wacce take tattare da tsoro fargaba tsinkewar zuciya tace Insha Allah bazan bijirewa umarnin ka ba Dady muddin Dai beci Karo da umarnin Allah ba.

Masha Allah Allah yayi Miki Albarka.

Ameen ya Allah Dady..

Dama dalilin da yasa na kiraki shine Ina son na faɗa Miki cewa Na ɗaura auren ki da Al ƙaseem ba Ahanaf ba, Kuma da Shi nake ra'ayin ki zauna a matsayin mijinki Na har abada. Ina fatan kinji Mai nace?


Wani firgitaccen ihu Norr ta zuba Wanda gabaki ɗaya falon Sai da ya karbi Amon muryar ta, ciki Wani irin fitinan ne kuka tace "Dan Allah Dady ka rufamin Asiri, karaba wannan auren wallahi ni Bana Son kowa Sai Yah Shadow Kuma bazan taɓa iya rayuwar aure da kowa ba Sai shi, Dan Allah Dady kaji tausayina ka warware wannan auren.

Da Jan gwiwa ta karasa gurin da Mommynta take, "tace Mommy Dan Allah kitaimake ni kibawa Dady haƙuri ya warware wannan auren wallahi Bana Son ƙaseem Ni Duk Duniya Yah Shadow kaɗai nake so Kuma kunsan da Haka Mommy.


Kamata Mommy tayi ta rugumeta tare da bubbuga bayanta a hankali tace "ki kwantar da hankali Noor indai Ina numfashi ba Wanda ya Isa yasaka ki a cikin kuncin rayuwa, bazan taɓa barin haka tafaru ba Sai Inda ƙafina yaƙare insha Allah.

Murmushi Dady yayi yace "wannan Karon kuwa kin ɗauki Alƙawarin da yafi ƙarfin ki Haj dan wallahi ba wanda ya isa ya raba wannan auren indai ina Nunfashi Noriya bata da wani miji bayan ƙaseem" sosai vulome ɗin kukan Norr ya ƙaru har tana shiɗewa tsabar tashin hankali.

Mukhtar wallahi idan har yarinya ta tamutu bazan taɓa ɗaga maka ƙafa ba, kasani zanyi shari'a da kai har ƙarshen raina, wannan ai zalunci ne.
kamata yayi ku faɗi dalilinku nayin haka idan akwai ƙwaƙwaran dalili kaga sai kowa yasan halin da ake ciki amma ai wannan cin haƙƙin yayi yawa wallahi. ko kallon inda take Dady baiyi ba barre tasaka ran zai mata magana.

Ƙwafa tayi tare da kama Norr ta miƙar da ita tsaye muje kinji ba yadda za'ayi nayi shiru akan wannan lamarin zansa abunyi insha Allah, tana riƙe da ita har suka ƙarasa sashen Mommyn,
Duk wanda yagansu sai yatambayi lafiya kuwa? Mommy ce mai ƙoƙarin cewa ba kumi bata jin daɗi ne.
Har bakin bed ta kaita ta zaunar da ita akai tace ki kwantar da hankalinki Norr bana son wannan kukan naki, kiyi haƙuri musamu mafita.

Mommy Ahanaf Al ƙaseem haba haba Mommy dan Allah kitaimaka mun karki bar hakan ta faru wallahi bazan iya zama dashi amatsayin miji ba Norr ta faɗa tana fashewa da wani irin kuka wanda da kajishi komi rashin imaninka dole ka tausayawa mai yinsa.

Runtse idanunta Mommy tayi tanajin zafin kukan da ƴar ta guda ɗaya tilo take rairaiwa, zaunawa tayi kusa da ita tare da janyota jikinta ta rungume ta tafara karanta mata Addu'ar Sanyaya zuciya tana tofa mata, taɗauki tsawon lokaci tana haka can saiji tayi Norr ɗin tafara sauke ajiyar zuciya alamar bacci ya ɗauke ta.

Gyara mata kwanciya Mommy tayi tare da ɗaura mata kanta akan pillow, tana goge Mata hawayen da ke Kwance akan fuskar ta.

Ta Jima tsaye akanta tana ƙare mata kallo cikin tausayawa.
"wannan ranar agurin kowace amarya rana ce ta daban wace take ƙunshe da duk wani farin ciki wanda bazata manta dashi ba a tarihin rayuwar ta,
amma sai gashi yazo da matuƙar saɓani agurin ƴar ta. jiki ba ƙwari tabar ɗakin cike da tausayin halinda Norr da Shadow suka tsinci kansu aciki.

Gidan su Shadow
Abunda yafaru yagama kewa lungu da saƙo na cikin gidan, saboda mazan da sukaje gurin ɗaurin aure, tuni Suka bawa matan su da iyayen su labarin abunda yafaru agurin ɗaurin auren, kowa sai tofa Albarkacin bakinsa yake.

Maganar duniya bata taɓa ɓoyuwa😰😰😰


Shadow zaune agaban Ayiya ta tasa shi gaba akan dole sai ya karya, shikuma bayajin akwai abunda zai iya sakawa bakinsa koda kuwa ruwa ne,
Ayiya tace nasani ba abunda yake maka daɗi yanzu amma dan Allah ka daure kaci wani abu ko hankali na zai kwanta,
bazan iya jurar ganinka cikin wannan halin ba dan Allah kaci ko kaɗan ne ta faɗa tana share hawayen da suke zubowa daga idanunta.

Cikin danne tashi damuwar yace zanci Ayiya dan Allah kidaina kuka, ki bani wallahi zanci ya faɗa yana goge mata hawayen da ya zubo mata,
Abincin ta bashi ya buɗe bakinsa
Ta saka masa,
Ya mutsa fuska yayi kamar wanda yake tauna maɗaci haka yake tauna abincin yana ya motsa fuska kamar ƙaramin yaro.
Haka taci gaba da bashi abincin yana haɗiyewa dakyar,
Duk lokacin da ya janye kansa alamar ya ƙoshi sai ta ɓata fuska. bisa dole yake ƙara buɗe bakinsa ya karɓa a haka har ya ƙoshi.

Mikewa yayi tsaye yace kamar kar naci abincin nan Ayiya sai nakejin wani irin bacci sosai,

Tohm ka kwanta anan mana Ahanaf kaga part ɗinku mutane sunyi yawa ba lallaine kasamu yin baccin a can ba.
tohm nagode sosai Ayiya Allah yaƙara miki lafiya da nisan kwana,
Ameen ya Allah yaron kirki Allah yayi maka Albarka yayi maka maganin damuwar ka.
Ameen ya rab my Ayiya, ya faɗa tare da cire rigar jikinsa,
ya faɗa kan gadon ya kwanta, yana ƙoƙarin yayi Addu'ar bacci amma abun ya gagara, saboda wani irin matsananci bacci da yaziyar ce shi wanda tunda yake bai taɓa jin irinsa ba, cikin seconds ɗin da Basu wuce 15 ba bacci yayi awon gaba dashi.

Bayan awa huɗu da faruwar haka
Shadow ne yafarka daga baccin da ya ɗaukesa tare da kurma wani raza nanne ihu..............




Nabeela Binji ce💃💃💃





Nabeelah Shehu Binji

09064314811
Or
09161107610




More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏






♣️DUHUN INUWA ♣️




TAPING......📲📲📲


STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*


BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM


Page

0️⃣4️⃣


Bayan awa huɗu da faruwar haka
Shadow ne yafarka daga baccin da ya ɗaukesa tare da kurma wani raza nanne ihu..............

Yana ƙoƙarin saukowa daga kan bed
Sai cewa yake Wallhi sai na kasheku ni zaku ciwa Amana dukan ku nine Nan ajalinku.......


Ayiya ce tafito daga toilet cikin sauri Wanda yanzu Nan tashiga Domin ta ɗauro Alwalar sallar magrib.

Kai tsaye gurin da Shadow yake tanufa cikin tashin hankali tace Ahanaf lafiya kake kuwa? su waye Kuma Zaka kashe? Tafada Tana kokarin rike Masa hannaye,
tureta Shadow yayi da karfi tayi baya zata Fadi ƙasa, cikin sauri Al ƙaseem Wanda shigowar Kenan yanzu ɗakin ya tareta tafaɗa jikinsa.

Ɗagowa yayi ya kalli Shadow yace Yaya kana cikin hankalinka kuwa? Ayiyar ce kake ture.. kafin ya rufe bakinsa tuni Shadow ya kamo wuyansa ya shaƙesa sosai, Nan take idanun Al ƙaseem suka firfito waje saboda tsabar shaƙar da yasha, cikin ƙaraji Shadow yace wallahi nine Ajalinka ƙaseem ni zaka ciwa amana ka aurar min mata? tohm wllhy daga kai har ita sai na KASHEKU yafaɗa cikin ƙaraji.

Hunnu Ayiya ta ɗaura akai tare da fashewa da kuka tace dan Allah Ahanaf kasarmin yarona karka kashe shi, Ahanaf kodai kasamu taɓuwar hankali ne? nashiga ukku. Ayiya tayi iya ƙoƙarinta don ganin ta ƙwaci ƙaseem amma abun yaci tura, hakan ne yasa tafito ɗakin da gudu dan ta samo wanda zai ƙwaci Ƙaseem daga hannun Shadow.
Tun daga nesa ta hango Haidar da Kamal zaune suna alwalar magrib tafara kwala musu kira, da sauri suka nufu inda take suna tambayarta lafiya kuwa? Ina lafiya Kamal ga Ahanaf can ɗakina yana ƙoƙarin kashe Ƙaseem.

Ai basuma tsaya jin ƙarin bayani ba suka nufi ɗakin nata da gudu, koda suka shiga Shadow sai faman dukan ƙaseem yake yana surutai,
da sauri suka riƙesa amma saida ya kufce musu yaƙara ko mawa kan ƙaseem da niyar ya ƙara shaƙarsa, sake cafko shi sukayi suka riƙesa sosai, Haidar yace wai bakada hankali ne Shadow me kake ƙoƙarinyi ne haka? Haidar yafaɗa cike da mamakin abokin nasa da tun zamansa dashi bai taɓa ganin faɗan saba sai yau.

Ku sakeni wallah saina kashe shi daga shi har Norr ɗin yafaɗa yana ƙoƙarin kwacewa daga riƙon da suka masa, amma kuma yakasa Kwacewar saboda ba riƙon wasa suka masa ba.

Shadow ka kwantar da hankalinka dan Allah wannan fa ba laifin Ƙaseem bane laifin su Abba ne (novel ɗin iyan Nabeelah 😜) sune suka tabka wannan kuskuren baruwan Ƙaseem aciki, hasalima baya sonta, kanaji fa agabanka yace shi sakinta zai.. Adaba Al Ƙaseem ya katse Haidar yana gyara tsayuwar sa tare da cewa wallahi yanzu ba wanda ya isa ya shiga tsakanina da Norr saboda ita ɗin matata ce ina sonta kuma bazan saketa ba.

Kamal da Haidar tsabar mamaki basu san lokacin da suka saki Shadow ba, ai kuwa dama abunda yakeso kenan cikin zafin nama Shadow yasake cakumo Ƙaseem tare da buga kansa da bango,
Wani irin kuka Ayiya ta saka tare da cewa dan Allah Haidar kuriƙesa mana kuna fa gani zaiyi kisan kai.

Sunyi iya yinsu amma sun kasa ƙwatar Ƙaseem daga hannu Shadow "sai faman buga kansa yake da bango yana furta cewa sai ya kasheshi"

Sai da kyar sukayi nasarar kwace Ƙaseem ɗin suka reƙe Shadow sai buge buge yake asake shi yaje ya ƙarasa Ƙaseem ɗin ko zai samu nutsuwa, wannan karon riƙon kwarai sukayi masa wanda yakasa kuɓucewa daga hannunsu.

Da sauri Ayiya tayi kan Ƙaseem wanda gabaki ɗaya jini ya gama wanke masa fuska tana girgizashi, dan Allah katashi kar ka mutu Ƙaseem.

"Ki zuba masa ruwa Ayiya ko zai farka sai ki kira Dr yazo ya duba shi ayi Masa dressing" Mu kuma Bari muje da Shadow part ɗinsu musan abunyi dan bai kamata abarsu a nan tare ba saboda kumi zai iya faruwa.


Da kyar suka fitar da Shadow daga part ɗin Ayiya, sai faman turjewa yake shifa ba inda zaije sai sun barshi ya kashe Ƙaseem,
Suna zuwa part Ɗin nasu direct bed room suka kaishi, Suna Shiga suka sake Shi tare da farayi masa fada. bayama sauraron Abunda suke faɗa, Sai suratansa yake marasa Kan gado.

Kallon Juna sukayi cike da mamakin wannan abun da Shadow ya keyi kamar Wani taɓaɓe,
kafin su Ankara tuni Shadow yayi hanyar fita da gudu,
Dafa masa baya sukayi Sai Palo suka samu nasarar Kama Shi, suka sake mai dashi bed room din.
Haidar ne yabada shawarar su kulle Shi a ɗakin, Idan ba haka ba kumai zai iya faruwa, haka kuwa suka kulle Shadow a ɗakin suka tafi masallaci Bayan sungama sallah suka dawo gidan, tundaga Palo suke jiyo ƙarar fashewar abubuwa, da sauri suka karasa dakin Suna budewa su kaci Karo da ɓarnar da Shadow yayi a ɗakin duk Wani Abunda

Please Login or Register in order to submit comment