Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kenan?" Harara ta zuba Mata tace "naga gadon na ma'aurata ne, kinga bai kamata ace ni na kwanta akai ba" murmushi Shabana tayi tace "kice yau gulman mai lacing kikeyi" murmushi Hafeeza tayi tace "Wallahi Idan nayi muku Allah ya Isa sai ta kama ku, kawai ina zamana kunsa nayi mugun gani" dariya ce ta suɓucewa Shabana cikin dariyar tace "mune muka saka kikayi mugun ganin? Tohm ai Indian da kike kallo kina ma ganin Abunda yafi wanda mukayi" tsaki tayi tace "yanzu Fisabilillahi baki jin kunyata?" Girgiza kai Shabana tayi cikin dariya tace "bana fatan abunda zanyi naji kunyar idonki cox ba Alkhairi bane, kedai bawani ba bana jin kunyar ki kuma bazanji ba, ke ko fiye da haka kika ganmu bazanji kunyar ki ba Saboda kedin ba Abar Jin kunya bace" gyaɗa kai Hafeeza tayi tare da cewa "wulaƙanci last class, to ki rubuta ki aje in Allah ya yarda sai narama" dariya Kawai Shabana tayi batare da tace uffan ba.





Koda Shadow yaje Kassem, Haidar da Kamal suna parlour suna fira, zama yayi tare da yi Musu Sannu, hararar wasa Haidar yayi masa yace kana can ka liƙewa ƴar Mutane ko kunya babu" murmushi yayi yace "Alhamdulillah dai Matata ce ko na liƙe mata ba haram bane" Kamal ya riƙe haɓa tare da cewa "tab Haidar Magana Shadow ya dasa maka fa" murmushi su kayi dukansu Cox sun san halin Kamal baya kashe wuta.
Sunjima suna fira har 11 sannan su kaje suka kwanta.
Saida ya kwanta Sannan ya ɗauki wayarsa yafara kiran Shabana.

Cikin baccin da ya ɗauketa ba jimawa taji wayarta tana ringing, gajeren tsaki tayi tare da jawo wayar tana duba mai kiranta, No ɗin Ahanaf tagani ɓaro ɓaro akan screen, ɗauka tayi tare da karawa a kunnenta, my wife taji ya faɗa cikin ƙasa da murya, Shiru tayi tana sauraren sa, yace "hello" tace "Na'am inaji" murmushi yayi tare da gayara kwanciyarsa yace "ina ajiyata da na baki?" Cikin mamaki tace "ajiya kuma? tame kenan" yace "kin Manta kenan?" A hankali tace "Allah na manta" murmushi yayi yace "Zanen gidanmu dana baki" laaaaah ni har na manta, ai yana Katsina" da sauri yace "what dan Allah kidaina wasa mana" murmushi tayi sannan tace "ai bakace nazo da shi ba" ya Salam yafaɗa yana dafe Kansa, murmushi tayi tace "nazo da shi yana cikin trolley na" ajiyar zuciya yayi yace "Allah yayi Miki Albarka yarinyar kirki" murmushi tayi sannan tace Ameen ya Allah" "ina so nayi shirin gina gidanmu ne cikin ƙanƙanen lokaci nake so a gama kumi" a hankali tace "Allah ya taimaka" sun ɗanyi fira kafin sukayi sallama.



Yana cikin Tafiya zaije masallaci yaji an taɓo shi ta baya koda ya juyo Ayiya ya gani riƙe da zarmemiyar wuƙa sai sheƙi take, duk inda hankalinsa yake ya tashi cikin matsanancin firgici yace "Ayiya lafiya ina zakije haka?" Wata mahaukaciyar dariya ta saki tare da cewa "kayi tunanin zan barka ka tsira ne? duk da ina cikin hauka nakasa Manta zafin ƙiyayyar da nake maka, burina ɗaya naga baka Duniya Ahanaf, nice ajalinka nice ajalinka ta faɗa tana daba masa wuƙar a gefen ciki. Wani uban ihu ya kwalla tare da kiran Shabanaaaaaaah...........✍️✍️✍️










Nabeela Binji ce💃💃💃







More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏.





♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM



PAGE

4️⃣ 5️⃣















________________ Da sauri ya tashi zaune tare da furta Innalillahi wa'inna Ilaihi Raju'un, gabaki ɗaya zufa ya jiƙa masa jiki duk da sanyin da ya sauka na ruwan da akayi jiya da dare, ajiyar zuciya ya dinga saukewa.
Wayarsa ya duba yaga 5:18 am Tashi yayi yashiga toilet ya ɗauro alwala yana fitowa ya shin fiɗa sallaya yaɗauki Al ƙur'ani yafara karanta, yajima yana karatu kafin yaji ankira Sallah ya tashi ya fito zuwa masallaci, a parlour yaci karo da su Kamal suka tafi tare.



Da ya dawo kiran Shabana yayi saida ta kusa katsewa ta ɗauka, cikin muryar Bacci tace "assalamu alaikum" lumshe Idunsa yayi yana jin sautin muryarta har cikin kwakwalwasa, jin shiru yasa tace "hello" cikin farin ciki yace "anya kinyi Sallah kuwa naji muryarki kamar wacce ta farka yanzu" gyara kwanciyarta tayi tace "eh nayi yanzu na kwanta" tashi Hafeeza tayi tare ninke sallayar hannunta tace "Mutum dai ya faɗi gaskiya yafi ƙarya ba wata Sallah da kikayi, tsabar kun zama mayun juna jiya an cika min kunne yau ma tunda asuba kun tashi da abu ɗaya" Shadow yace "Hafeeza ce ko?" Murmushi Shabana tayi tace "ita ce Aunty bala'i" murmushi yayi yace "mai take cewa ne?" Sirariyar dariya tayi tace "wai cewa take Mun shiga haƙƙinta, mun dameta da waya" Shadow yace "abunda tace a farko, kamar naji tayi Magana kafin tace haka" shiru Shabana tayi kamar mai nazari tace "nidai haka kawai naji tace" murmushi yayi cikin muryar irin ta yara yace "manya fa basa Karya naji Abunda tace" murmushi tayi tace "toh Idan kaji mai tace ɗin?" Gyara kwanciyarsa yayi yace "Hafeeza tace bakiyi Sallah ba, Shine na tambayeki kinyi Salla kika mun ƙarya ko?" uhmmmm kawai tace masa.
Murmushi yayi yace "ko kina fashin Sallah shine kike ɓoyemin?" Wata masifaffiyar kunya Shabana taji, aranta kuma tana ƙara girma rashin kunya irin ta Ahanaf.
Jin tayi Shiru, yasa yayi Murmushi yace "Kenan gaskiya Hafeeza ta faɗa?" Ya mutsa fuska tayi kamar tana gabansa tace "Oho muku" murmushi yayi yace "harda ke ma" tashi tayi zaune tare da cewa "ina zuwa plx" "nikam gaskiya bazan iya katse Kiran ba kawai kiyi Abunda zakiyi Muna maganar" Shabana yace "ikon Allah, toh inda zanje ba'a magana ai" murmushi yayi yace "toilet zaki kenan? kodai inzo in rakaki?"
Da sauri ta katse Kiran tare da cewa "kaji dashi mara kunya kawai"
Dariya Hafeeza tayi tace "ai kece ƙatuwar mara kunya, duk Abunda yayi ke kika koya masa" harara Shabana ta zuba Mata batare da tace uffan ba ta shige toilet.
Murmushi Hafeeza tayi tare da ɗan ɗaga murya yadda Shabana zata jita, tace "ƙaryar iskanci kike ai namasifar Jin daɗi da Allah ya haɗa ki da daidai ke" Sarai Shabana tajita Amma tayi banza da ita tafara ƙoƙarin wanka.





10 am kaf Mutanen gidan sun haɗu a Babban parlour, yau a tare zasuyi breakfast, Abbu yace "hakan zaisa suƙara sakin jiki da junansu" tunda ta zauna idon Ahanaf yake akanta ko kyabtawa ba yayi kamar wani Maye, gabaki ɗaya taji ta takura, motsin kirkima batayi. Abbu ya lura da irin kallon ƙurullar da Ahanaf yake yiwa Shabana.
Murmushin yayi tare da girgiza kansa, aransa yace ko fiye da haka kayi baza aga laifinka ba, saboda Idan akwai abinda yafi so da ƙauna to yakamata a nuna Mata.
Kasan cin Abinci tayi sosai Idan tasaka spoon ɗaya dakyar take haɗewa, ji take kamar zata kware.
Aje spoon ɗin tayi tare da daukar wayarta tana dannawa.
Kallonta Abba yayi yace "Lafiya daughter naga kin daina cin Abincin?"
Kanta ta sunkuyar cikin girmamawa tace "lafiya lau Abba, na ƙoshine" kwafa Haj Mama tayi tace "ina zata ci Abinci kuwa wannan uban ƴan nacin ya Kureta da Ido" kallonsa Abba yayi da sauri ya sunkuyar da kansa ƙasa ya maida hankali kan abincinsa.
Abba yace ₦Idan baka daina takura mata da kallo ba yanzun nan zan koraka kaje part ɗinku kayi break ɗin a can" murmshi Shadow yayi tare da Sosa kansa alamar yaji kunya.
Ita ma Shabana kunya taji kamar ta buɗe Idonta ta ganta a ɗaki.
Murmushi Dady yayi yace "haba dan Allah ku rabarmin da yarona, Idan kuma takurashi zakuyi sai na tafi dashi Katsina inda ba masu saka Ido" gabaki ɗaya dariya sukayi Malam Ibrahim yace "da alama Kan haka za'ayi Alh" cukin dariya Abba yace "Ashe sangartashi kukayi shiyasa" Dariya sukayi.




Bayan sun kammala break ɗin Dady yace "Tohm alhmdllh, gaskiya munyi farin ciki matuƙa da kalar karɓar da muka samu daga gareku, tabbas ku Mutane ne masu karanci, Allah ya bar zumunci ya kawar da sheɗan a tsakaninmu" murmushi Abbu yayi tare da cewa "ai duk wannan yabon agurinku ya cancanta, kun taimaki Yaro da zuciya ɗaya, ba tare da tunani shi wane kala bane kuka ɗauki Auren ƴarku sukutum kuka bashi dan kawai samun lafiyar sa, wannan halaccinaku har gaban Abada bamu da Abun ramashi, sai dai zamu kwatanta hakan ta hanyar riƙe Amanar wannan yarinyar mai cike da Tarin Alkhairai, nayi matuƙar jinjinawa tausayinta da Imanin ta, Tabbas kunsamu ƴa ɗaya tamkar da dubu, tazama Babban Abun Alfahari a wannan dangin, Alkhairinta ba mai dushewa bane a Idanun mu" kallonta Abbu yayi yace "Allah yayi Miki Albarka ya Sanya farin ciki a rayuwar ki fiya da yadda kika mana, Allah ya baki Yara masu zuciyar Alkhairi fiye dake, Allah ya kareki da sharrin Duniya da Abunda yake cikinta" Duk Wanda yake parlourn Saida ya amsa da Ameen Ameen.
Ita kuwa Shabana hawaye taji Suna bin fuskarta, taji Daɗin addu'ar Abbu fiye da tunani, kuma taji ta ƙara son wannan ahalin wa ƴan da suka kasance dangin mijinta a yanzu.

Kallonta Shadow yayi yana jin ƙaunarta na ƙara mamaye duk wani sashe na jikinsa, Aransa yake kiyasta abubuwan da zaiyi dan kawai ya faranta mata.
ta saka shi farin ciki ta saka iyayensa, tabbas tazama majin ginarsa, zaiyi komai Domin farin cikinta muddin ba saɓon Allah bane.


Kallonta Abba yayi cike da So da ƙauna yace "tun lokacin da Allah yabani Yaran nan nake roƙonsa ya basu mata na gari masu tsoron Allah, kuma alhmdllh dukansu da alama sun dace.
Daughter na baki Amanar Ahanaf Ina so ki Maye masa gurbi biyu a rayuwarsa saboda sune ciwonsa, ciwon farko kizama uwa tagari a gurinsa, mai sa yayi Alkhairi da kwaɓarsa da aikata wani mummunan abu.
Na biyu kizama Mata tagari a gurinsa mai kwantar masa da hankali da ɗaura shi kan hanya madaidaiciya. Idan kikayi haka kin zama gatansa gatan ɗan uwansa da mu baki ɗaya" ajiyar zuciya Abba yayi Sannan yaci gaba da cewa "tun lokacin da naji irin taimakon da kika yiwa ɗana gudan jininna, naji araina kema kin zama ƴata kuma ƴa mafi daraja da kima a Idona, dan haka ina neman wata Alfarma agurinki, ina so kiɗaukeni matsayin mahaifinki, idan surukuta zakiyi kiyi da wannan" Abba ya faɗa yana nuna Abbu.
Hararar wasa Abbu yayi masa yace "kunji wani wayau?" Gabaki ɗaya dariya sukayi.
Shabana ji tayi wani matsanancin farin ciki ya rufeta.

Murmushi Malam Ibrahim yayi Yace Alhamdulillah Magana ta gaskiya bamu Shakkar bayar da ƴarmu a gurin Mutane masu karanci irinku, Muna da tabbacin ko bayan idonmu zaku riƙe Amana.
Murmushi Abbu yayi yace insha Allah Malam, kuma kaga ga fusattacen mahaifinta agefe ba wanda zai taɓa ta ya kwashe lafiya" Abbu ya faɗa yana buga kafaɗar Abba. Abba yace "sosai kuwa wannan ita ce Auta ta kuma ƙurjin gwita, duk wanda yake son zamansa lafiya a gurina ya kiyaye Abunda zai taɓata Allah" Ammi tayi farin ciki sosai da jin kalaman iyayen Ahanaf, kuma dama irin dangin mijin da take fata kenan ƴarta ta samu.



Abbu yace "Toh ƙarin ƙarfin zaman mu Anan shine su Alh Usman sun ce sun so zuwa gida yau, amma na hanasu tafiyar yau sai gobe saboda maganar Auren Yaran nan, yakamata ace mun san a wane mataki zamu tsaya kafin su tafi. Na farko dai Muji Yaran sun yarda da juna a matsayin ma'aurata, sai kuma na biyun Idan sun yarda mun saka lokacin da zasu tare"
Abbu ya kalli Shadow yace "Ahanaf me ka yanke akan Aurenka da Shabana?" Ajiyar zuciya yayi tare da cewa Ni na jima da karɓarta a matsayin mata, tun lokacin da naji halaccinta a gareni naji Ina ƙaunarta fiye da komai a rayuwata, Wallahi Abbu So na gaskiya da gaskiya nakewa Shabana Ina ƙaunarta, ya faɗa muryarsa na rawa"

Kowa da yake parlourn ya gamsu da maganar Shadow, musamman ma Shabana da akayi kalaman Domin ita,har jitayi tsigar jikinta na tashi.

Murmushi Abbu yayi tare da Maida kallonsa kan Shabana yace "to ƴar Muhammad kinji abunda yarona yace, ke menene ra'ayinki akai?" Rufe fuskarta tayi tare da tashi ta bar gurinda sauri kamar zata tashi sama, ita Hafeeza tashi tayi tana dariya tabi bayanta.

Kallon Abbu yayi yace "Abbu tafa tafi Bata ce Kumi ba" harara Haj Mama ta zuba masa tace "kazata kowa mara kunya ne kamar kai, daka zauna gaban sirikai kana rashin kunya" dariya Abbu yayi yace "ba ruwanki ai maganar tsakani da Allah ake ba ɓoye ɓoye" Abbu ya Maida kallonsa kan Shadow yace "ka kwantar da hankalinka, Idan har kaga an tambaye ƴa mace zaɓi kan mijin da zata zauna dashi tayi haka, to ba Shakka ta amince, insha Allah kai mijinta ne ita ma Matarka ce ta har Abada" murmushi Jin daɗi Shadow yayi.

Abbu yace "maganar tarewa kuma sun saka Watannin huɗu nac......" Ido Shadow ya ware kamar zasu faɗo ƙasa yace "wata huɗu Abbu Wallahi sunyi yawa haba haba" haɓa Abbu ya riƙe yana kallonsa yace "Wai yaushe ka fitsare har haka Ahanaf? mu Idan bakajin kunyar mu surukanka fa? sannan ai baka bari na ƙarasa Maganata ba ka tari numfashina" shiru Ahanaf yayi yana sauraren Abbu, kwafa Abbu yayi Sannan yaci gaba da magana yace "na mayar dashi nan da wata ukku Insha Allah" ɓata fuska yayi kamar zaiyi kuka, harararsa Abbu yayi yace "suma sunyi yawa ko? Shadow da baisan ba'a ba yace "gaskiya Abbu Ina ma laifin 2months" ungo nan Abbu ya faɗa yana ware yatsunsa biyar kusa da fuskar Shadow, "bazai a mayar ba Idan Watan ukku Basu maka ba ka Bari" murmushi Malam Ibrahim yayi Yace "Dan Allah Ina roƙawa ɗana wannan Alfarma, tun lokacin da kuka saka watannin nayi tunanin sunyi yawa, Idan kun duba fa Auren ya ɗauki watanni, ya kamata ace sun tare haka nan, abarshi wata biyun da ya roka Dan Allah" murmushi yayi yace "Tohm yanzu Magana tana gurin Abban yarinya Dadyn Yaron, Idan sun yarda ba matsala" murmushi sukayi suka ce Allah ya Sanya Alkhairi, Wata ajiyar zuciya Shadow ya sauke.........✍️✍️✍️














Nabeela Binji ce💃💃💃







More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏.



♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM



PAGE

4️⃣ 6️⃣

















_______________ Abbu ya kalli kaseem yace "zonan yarona" tashi kaseem yayi ya matsa kusa da Abbu, kama hannunsa Abbu yayi yace "jiya da Yamma munje gidan su Alh Mukhtar, tare da su Alh Usman mun gama magana da shi akan maganar ku kai da Nuriya, tun jiya ma yaso mu zo da ita nace "masa a'a ya Bari idan munzo gida zan turaka kaje ka ɗaukota, abunda yasa na yanke Wannan hukuncin ba tare da na tuntuɓeka ba shine, nasan ba wata mafita da ta wuce wannan, yanzu akwai rabo tsakaninka da ita, yamakata ace kunci gaba da zama ma'aurata kodan abunda zata Haifa, kumanta da abunda iyayenku suka aikata, Idan ka duba Norr yarinya ce tagari kuma na gartacciya, ita abar tausayi ce Idan ka duba abubuwan da suka faru zaka ga ita da kanta tana cikin ƙunci rayuwa fiye da kai, Dan Allah ƙaseem ka taimaka ka ƙarbi Norr a matsayin Matar da ƙaddara ta zo maka da ita, kayi Mata adalci, kamatanta da duk wani abunda yafaru, Kasama ranka Norr ita ce mata tagarin da mahaifinka ya dinga roka maka kaji" Kalaman Abbu sunyi tasiri sosai a zuciyar ƙaseem, wani murmushin takaici yayi yace "banida zaɓi Abbu na ƙarbi Norr a matsayin Mata, tabbas haka Allah ya ƙaddara min kuma na ɗauki ƙaddara" murmushi Abbu yayai tare da buga kafaɗar sa yace "shiyasa nake Sonka yarona, Allah yayi maka Albarka, ya baku zuri'a tagari ya baku yara masu yi muku biyayya kamar yadda kuke muna" Ameen ya Allah suka amsa, Abbu yace "yanzu kaje kayi wanka ka shirya sai kaje ka ɗaukota kazo da ita nan su gaisa da Matar yayanka tunda kaga gobe zasu koma Katsina" insha Allah Abbu.

Abbu yamaida fuskarsa kan su Kamal yace "na dawo kanku, so kuke kuyi min baƙin cikin samun jikoki ko yaya?" Dariya Haidar yayi yace "a'a Abbu Allah ne bai kawo ba" Abbu yace "namesake kaji tsoron Allah yanzu haka daku yara masu kyau masha Allah har kuke cewa baku samu masu sonku ba? Allah Idan baku fitar da mata ba zan saka kafata takalmi naje har Gombe nayi Magana da su Alh aje kauye a samo muku tumba da Tani, ayi muku auren dole" duk Wanda yake parlourn Saida yayi dariya, Abba yace a'a kam Allah ya tsaresu, yadda kowa ya auri zaɓinsa suma zaɓinsu za'a Bari su nema" Abbu yace "Toh Muhammad naga Abun nasu ya zama Shirita" Abba yace "Allah dai ya Basu mataye na gari masu mutunci da Imani" ameen ya Allah.
Haka dai Taron ya tashi suna cikin farin ciki sosai.


A ɗaki kuwa Hafeeza ta tasa Shabana gaba tana tsonaka, tace "Munafuka kina so kina kai kasuwa, Idan ance kina son Ahanaf kice ni bana Sonsa tausayinsa nakeji kallon yayana nake masa kamar ya Suhail da ya Maleek, makirar yarinya" Hafeeza ta faɗa tana dangware kan Shabana. Murmushi Shabana tayi tace "kiyi jarabarki ki gama ni yanzu banida time ɗinki" Hafeeza tace "ai kuwa dole kiyi time ɗina, kinsan Allah na ƙosa gobe tayi mutafi Katsina, na faɗawa Hidaya kalar iya shegen da kikayi gidan sirikai, ke har tsotsetsen da na kama ku kuna yi sai na gaya Mata" Dariya Shabana tayi tace "ke kika Jima baki faɗa mata ba, kuma da kika ce kin kamamu muna tsotsetse kin manta matsayin mu ne? Idan kin manta Bari na tina miki Shi Mijina ne ni kuma Matar sa, bakisan iya Abunda yake tsakaninmu ba" riƙe haɓa Hafeeza tayi tace "kuttt lallai ba Shakka yanzu Shabana kinfi ƙarfi na, dole na fara nesa nesa da ke" dariya Shabana tayi tace "da yafi miki kam.





Suna shiga parlour Haidar ya Kalli Shadow yace "friend nifa gaskiya na kamu" murmushi yayi yace "serious? Wacece wannan mai sa'ar da tayi nasarar sace zuciyar wannan mai fi'ilin masifar" Murmushi Haidar yayi yace "wannan ƙawar Matarka, Wallahi tinda na fara ganinta naji ina sonta, a farko nayi shuru but yanzu gaskiya na kasa" wani irin fito Shadow yayi yace "Alhamdulillah naji daɗi sosai dama irin Matar da nake so ka samu kenan, Cox ita kaɗai ce zata iya maganin hayaƙin da yake tashi a kanka Hafeeza ce daidai da kai Haidar" murmushi Haidar yayi yace "koma yaya take nidai ita nake so" dariya Kamal yayi yace "eh Lallaima Haidar kana cikin yana yi" Haidar yace "barni kawai tinda ita naji ina so to ita zan aura, sai Idan ita ce tace bata Sona, Anan kam dole na haƙura cox ni a ra'ayina bana so na zauna da Matar da bata Sona, sakata akayi ta aureni" murmushi Shadow yayi yace "Allah yasanya Alkhairi ya baka Ikon ciyo Kanta da wuri, dan wannan uwar rigimar idan ba Allah ya taimaka ba sai kayi fama" murmushi yayi yace "Idan zata karɓe ni banida matsala Akan komi, Dan Allah kira Matar kace tazo min da Matata" dariya Shadow yayi har da riƙe ciki yace "kana da abun ban dariya Haidar wato Matarka?" Tsaki Kamal yayi yace "rabu dashi Shadow da alama kazar Wahala Allah ya yanka masa kaga kuwa dole ya fige" dariya Shadow yayi yace "da alama kam" Haidar yace "Idan bazaka kirasu ba dan Allah kace ma Matarka ta turumin Sha ɗayan ta sai na kirata" murmushi Shadow yayi yace "kwantar da hankalinka zan kirata."




Shadow ya kira Shabana ne yace "Ina Hafeeza?" Kallon gefenta tayi tace "gata Nan sai ta kurani take ta hani sakat wallahi" murmushi yayi yace "rabu da ita lokacin ramawa yazo, kizo da ita part ɗinmu plx" Shabana tace "lafiya dai?" Murmushi yayi yace "lafiya ƙalau kawai kuzo yanzu kinji wife" Okey zamu zo yanzu insha Allah" katse Kiran tayi ta Kalli Hafeeza cikin tsokana tace "plxxx muje ki rakani gurin mijina" harara ta zuba mata tace "Badan haka Allah ya halicceni ba" Shabana tace "naga neman gulma kike Ido rufe shiyasa zan so kije ki ƙara samun wata" Bazanje ba" da kyar Shabana ta samu kan Hafeeza sukaje.
Koda sukaje part ɗin Shadow, Kamal da Haidar ne zaune suna fira.
Zama sukayi kan kujera mai Zaman Mutum biyu.
Shadow ya Kalli Shabana yace "precious kinsan Abunda yasa nace "kizo Muna da wannan Addabatun?" Murmushi tayi tare da girgiza kai, yace "yawwa bari dai nayi shiru ba za'aji mutuwar sarki a bakina ba, yanzu dai mufita waje Haidar ne nake So ya turkemin Hafeeza, Sannan mu rama wulaƙanci da take mana" murmushi Shabana tayi dan taso ta fahimci abunda Ahanaf yake nufi.
Kallonta tayi tana wani shegen Murmushi tace "ina zuwa Goty" Shabana ta faɗa tana tashi tsaye.
Shadow Tashi yayi yace "lallaikam muje waje yadda zai Samu damar titsiye ta da kyau" kallonsu Hafeeza tayi tace "ban fahimceku ba, cewa fa kikayi nazo na rakaki gurin Mijinki, Amma naga kuna nema ku ƙullamin makirci" murmushi Shadow yayi yace "ba kumi fa Magana kawai zakuyi yafaɗa yana jan hannun Shabana, ya kalli Kamal yace "kai zaka zauna ganin kwakwafi ne?" Kamal yace wanene ni ai nima yanzu waje nayi.

Fita sukayi daga parlourn, Kamal hanyar gadin ya nufa.
Shadow Jan hannun Shabana yayi har bakin mota, suna zuwa ya buɗe gidan baya yace "zauna anan" kallonsa tayi, ya marairaice fuska yace "plx ki zauna ba fita zamuyi ba, kawai fira zamuyi" shiga tayi ta zauna, ya zagaya shima ya buɗe gidan Bayan ya zauna.
Kallonsa tayi tace "wai me kuke shiryawa Gottyna ne?" Murmushi yayi yace "sayarda da ita nayi gurin Abokina" murmushi tayi tace "ai bazama ka fara ba" Shadow yace Haidar ne yace yana Sonta, kuma yace "shi da gaske son Aure yake Mata Idan zata Aminta" Ido Shabana ta ware tace "Masha Allah nayi farin ciki sosai, Allah yasa ta karɓe Shi, nasan halinta da dizga Mutum Idan yace yana Sonta, Amma Wannan zansa tasoshi kuma ta aureshi da yarda Allah. Akwai Shaƙuwa mai tsanani tsakaina da ita, takansa nayi abu koda bai min ba, ita ma haka, akan kumi na rayuwata Hafeeza ce mai bani ƙwarin gwiwa, duk da faɗan da muke Idan wani abu ya tun karo ɗaya daga cikin mu mukan aje wasa gefe muyi abinda ya kamata, Magana ta gaskiya inaji da Hafeeza fiye da tunaninka" murmushi Shadow yayi yace "nasani my beloved, shiyasa nake jin daɗin zamanku tare, Allah yasa wannan zumuncin naku ya ɗaure har aljanna" ameen ya Allah ta faɗa tana murmushi.


A can parlour kuma Hafeeza tayi shiru ko dogon motsi Batayi kamar ba ita ba, kallonta Haidar yayi yace "Ina kwana ranki yadaɗe" kunya taji yasa tayi shiru batace uffan ba.
Ajiyar zuciya yayi tare da cewa "dalilin da yasa kika ga mun keɓe Anan dalili ne mai girma, Hafeeza ba wani ɗa namiji da zai kalleki yaji baki shiga ransa ba, saidai Idan yayi fargabar fuskantar ki ya faɗa miki. Tun lokacin da na fara ganinki naji zuciya ta ta halba Bima'ana ta Samu mahaɗinta, na Danne abun araina gudun kar na faɗa ki ƙi karɓa ta, sai kuma daga baya zuciyata ta kasa hankuri ta tunzurani akan nazo na sameki na faɗa miki sakonta koda bazaki amince ba, nasan mace Kamar ke bazaki rasa masu sonki ba Amma dan Allah nima ina roƙon Alfarma nashiga cikin masu farautar zuciyarki maybe Allah yaji tausayina ya bani sa'ar samunta" tunda Haidar ya Fara Magana Hafeeza taji zuciyarta na harbawa da sauri, Shiru tayi.
Murmushi yayi yace "bazan tursasaki ki ki faɗamin ra'ayinki yanzu ba, Amma Dan Allah ina baran No ɗinki Idan ban takuraki ba" Nan madai shiru Hafeeza tayi murmushi yayi ya ɗauki yawarsa tare da ajeta kusa da ita cikin sanyi murya yace "ya almajiri sadaka" dariya ce ta suɓucewa Hafeeza ganin yadda ya langwaɓe kai kamar almajirin gaske, murmushi yayi yace Idan baki saka Mun ba zan ta binki duk inda kikayi ina yi miki Bara" murmushi tayi Tare da ɗaukar wayarsa ta saka masa no ɗinta tace basai takai can ba" murmushi yayi yace "kin rufawa kanki asiri" haka yaɗan dinga

Please Login or Register in order to submit comment