Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tanufa tafara Shiri cikin sauri, tana gamawa ta fito parlour anan ta Tarar da iyayenta Bayan ta gaidasu ne Ammi take tambayar Ina zuwa haka? Langwaɓar da Kanta tayi tare da cewa asibiti zanje Ammi yanzun nan Dr Fahad ya kirani yace wai nazo akwai matsala.
Matsalar me? Dady ya tambayi Shabana.
Nima bansani ba Dady yace dai sai nazo zanji.
Kai ya gyaɗa tare da cewa tashi muje asibitin.
Cikin sauri ta tashi tsaye Cox ta ƙosa ta Gakanta a gaban Dr Fahad.
Sai Mun dawo Hajiya Dady ya faɗa yana kallon Ammi.
Murmushi Ammi tayi tare da cewa Allah ya tsare hanya.
Ameen ameen.


Zaune suke a office ɗin Dr Fahad, Bayan sun gaisane yafara musu bayani yana duba takardun suke gabansa.

Shakka Babu ban taɓa cikin karo da case ɗin Rashin lafiya irin wannan ba.
Akwai ruɗani sosai a cikin wannan lamarin.
Jiya da Misalin 1am Ina gida a kwance masu kula da wannan mutumen suka kira hankali tashe suke faɗamin cewa wai ya farka Sai jifa yake da kaya ya hargitsa Kumi da yake a ɗakin.

Cikin sauri nazo asibitin natarar da abunda suka faɗa tabbas hakane, Kuma daga an buɗe ƙofa sai yadaina Abunda yakeyi yasamu guri ya tsaya cak kamar wani Robert.

Hakan tasa nakira Wani abokina Dr Bilal Shi kwarraren likitan brain ne.
A Daren muka tafi dashi asibitin su Dr Bilal suka sake Shiga dashi ɗakin na'ura suka Duba Shi.
Amma Kuma kinsan menene Babban abun ban mamakin?

Kai ta girgiza alamar a'a.

Brain ɗinsa lafiya Lau take tamkar taki, tawa, Dama ta sauran mutane Dr ya faɗa yana kallon Shabana da taƙuresa da Ido tana kallonsa tun lokacin da yafara Magana.

Sunkuyar da Kanta tayi ƙasa tama rasa mai zatace..........✍️✍️✍️




Nabeela Binji ce💃💃💃






More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏.






♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM


PAGE

1️⃣ 7️⃣













________________ Dady ne yayi gyaran murya tare da cewa Toh wannan wace kalar cutar brain ce Dr? Wacce ba'a ganin ta a brain ɗin.

Muna cin karo da irin haka sosai Dady sai ayita magani daban cuta daban.

Kamar ya Kenan? Dady yaƙara tambayar Dr Fahad.

Sihiri ko Aljanu, wa ƴan nan sune kawai zasu addabi mutum a baɗini Amma kuma babu Shi a zahiri,
Idan dai irin wannan matsalar tafaru tohm Babu Shakka duk binciken da likitoci zasuyi bazasu taɓa ganin abunda yake damun mutum ba, Cox cuta ce da aka Samar da ita. ba ita ce ta Samar da Kanta ba.



Mafiya yawan likitoci zasuyi bincike basuga komai ba Amma sai wahalar da Mutane gudun kar ace sun kasa.
Kowa da kalan baiwar da Allah yayi masa wani Abun sai an haɗa da maganin Islamic Saboda ba aikin asibiti bane. Amma sai su ɓoye haka Saboda da yawan likitoci Basu yarda da maganin gargajiya ba.


Sai kuma issue na biyu Wanda a yanzu nafara Shakka a kansa.

Shine cewar da nayi a farko shi ma'ikacin sirrine, ko kuma babban criminal, a yanzu na janye wannan zance Cox ganin abubuwan da suka faru a daren jiya.
Tabbas Mai basaja bazai iya wannan acting ɗin ba cox shima yana cutuwa sosai.

Shakka Babu Wannan mutumen akwai Wani rikitaccen Al'amari atare dashi.
Babban Abunda na fahimta shine Baya Son a rufesa a ɗaki Shi kaɗai Komi nisan baccin da yake Zai farka yafara buge buge wannan matsalar masu taɓuwar hankali ne Kawai Ake Samu da ita. Ko kamar yadda na faɗa maku a farko brain ɗin sa lafiya Lau take kamar ta kowa
Dr Fahad yafaɗa yana gyara Zamansa.

Wannan lamarin dole ne Sai an zauna a kansa Saboda Yana buƙatar nazari da kuma shawara.

Eh gaskiya Hakan yakamata Dady cewar Dr Fahad.

Okay yanzu ina mutumen yake?
Yana nan gurinku ko kuma yana can gurinsu Dr Bilal ɗin?
Dady ya tambayi Dr Fahad.

Yana can gurinsu Dady.
Okay zamu iya zuwa muganshi?
Eh ba matsala Dady.

Dr Fahad ne ya Kalli Shabana wacce jikinta yayi lakwas takasa Ko motsin kirki yace " ki kwantar da hankalikii Shabana insha Allah komai zaizo da sauƙi, yanzu ki tashi muje asibitin da yake" miƙewa tayi tsaye tare da ɗaukar wayarta da ke kan table.

Direct asibitin da Shadow yake suka nufa, Bayan sun Isa Dr Bilal yayi musu rakiya ɗakin da aka Kwantar da Shadow, koda suka Shiga yayi halinsa ya tarwatsa kumi dake ɗakin, Dr Fahad ne ya Kalli Dady yace "kaga abinda nake faɗa maka ko Dady? muddin yana shikaɗai a ɗaki sai ya farka ya fara fasa kayan ɗakin Kumi ƙarfin allurar baccin da aka Masa sai ya tashi" kai kawai Dady ya gyaɗa yana bin Shadow da kallo cikin tausayawa.
A hankali Shabana tafara taku har ta ƙarasa gabansa,
"Mai yasa kake haka? duba kaga duk ka ƙara jiwa kanka ciwo, dan Allah kayi Magana mana" tafaɗa cikin sigar rarrashi.
Ɗauke kansa yayi gefe yana maida kallon gurin window kamar baiji abunda tace ba.

Iska ta furzar a hankali tace "Ahanaf kana jina fa"
Da sauri Shadow ya Maida idonsa Kan Shabana. Wata muguwar faɗuwar gaba taji ganin yadda idonsa sukayi JA Kamar gauta.
Baya tafara ja ganin yadda yake dumfaro gurinda take, cikin sauri yasa hannunsa yana ƙoƙarin..............✍️✍️✍️



Ina mai Baku haƙuri Saboda Yau ban samu nayi taping da yawa ba wlllhy idanuna ne sai a hankali.




Nabeela Binji ce💃💃💃





Nabeelah Shehu Binji

09064314811
Or
09161107610




More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏.



♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM


PAGE

1️⃣ 8️⃣













_________________ Hannu yasa Yana ƙoƙarin Cafkarta, da sauri Dr Fahad yashiga tsakanin su tare da riƙe Hannu Shadow ya jashi Baya.
Har yanzu idon Shadow Suna Kan Shabana ko kyaftawa bayayi.

Dr Bilal ne ya Kalli Shabana yace "Ina kika San sunansa? Wanda baya magana" Ajiyar zuciya tayi tare da cewa acikin jakarsa naga sunan sa.
Taya kika san sunan sa ne bana wani ba? kuma ma kinada tabbacin jakar tasa ce?
Kai tagyaɗa alamar eh sannan tace Zanensa ne Akan pepper da naga sunan sa.
Sai kuma me kika gani acikin jakar?
Wata pepper mai ɗauke da Zanen wata yarinya mai Suna Norr......

Cikin sauri Shadow ya kwace daga riƙon da Dr Fahad yayi masa yayi Kan Shabana wata gigitaciyar shaƙa yayi Mata tare da buga ta da Bango yana gurnani kamar Wani ga wurtaccen Zakin da yafito farauta.

Cikin tashin hankali Dady yace Subhanallah Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un. Wannan ba mahaukaci bane makashine Dan Allah kutaimaka Kar ya kashe min ƴata Dady ya faɗa Yana Dukan Shadow Amma ko girgiza Shadow baiyi ba.

Dr Fahad Dr Bilal Dady ne riƙe da Shadow Suna ƙoƙarin kwace Shabana daga hannunsa Amma sun kasa hakan Cox riƙo yayi Mata Bana wasa ba.
Wani ɓacin rai yaji yana fitowa tundaga ƙasan zuciyar sa yayin da Shabana ta Ambaci sunan Norr.

Dr Fahad ne yasaka hannayensa ya danne baki da hanci Shadow dole tasa Shadow yasaki Shabana yana sauke numfashi tamkar wanda yayi gasar tsere.

Shabana kuwa jikin Dadyn ta ta faɗa ta rungumeshi tare da fashewa da matsancin kuka cox taji shaƙar da Shadow yayi mata harma ta fitar da Ran cewa zata rayu a Yau.


Bayanta Dady ya bubbuga a hankali yace "ya Isa haka ai duk laifinki ne kekika janyowa kanki yanzu ai saiki wuce mu tafi gida" baki ta buɗe da nufin zatayi Magana. Dady ya fizgi hannunta da ƙarfi ya fitar da ita daga ɗakin, kai tsaye gurinda yayi parking Motar sa ya nufa. da Hannu yayi mata alamar tashiga.
Ba musu tashiga Motar. Yaja yabar asibitin da mugun gudu.

Anan cikin asibiti kuma Shadow ya birkice musu Saboda haukarsa ta ƙaru fiye da tuanani.

Dr Bilal ne ya bada shawarar a sa Kashi ɗakin duhu Cox yanzu abune Mai wahala su iya control ɗinsa.

Kana ganin kamar hakan bazai sa ya ƙara tuburewa ba kuwa?

Shine abunda yakamata mufarayi dai yanzu tukkunna. Waya ya ɗauka yakira ma'aikatan gurin tare da Basu umarnin sukai Shadow ɗakin duhu.


Dr Bilal yace "tabbas wannan Norr ɗin da Shabana ta ambaci sunanta wannan mutumen ya santa kuma maybe ta taka wata rawa a cikin samun matsalar sa.
Cikin hauka fa yake Amma yanajin an Kira sunanta nan take ya birkice, a lokacin da zaka Kalli kwayar idonsa da zaka hango tsantsan ɓacin Rai da damuwa a cikinsu.

A duk lokacin da Mai taɓin kwakwalwa yayi irin haka Toh ba Shakka akwai matsala tsakaninsa da mai sunan da aka ambata.

Kuma yanzu kaga Dadyn Shabana yayi fushi sosai mawuyacin abune yaƙara bari tashiga lamarin wannan bawan Allah.
Gaskiya Kam Cox Duk Abunda yafaru agaban idonsa ya faru.
Dady yana matuƙar son Shabana Baya son abunda zai taɓa masa ita ko kaɗan.

Gaskiya bazai mabarta ba Sai Wani hukuncin na ubangiji.
A haka dai sukaci gaba da tattaunawa akan matsalar.




GIDAN SU SHADOW


__________ Zaune suke a Babban parlourn Abba, Kamal da Haidar ne ke Shirin Tafiya gida yau Saboda iyayensun sun matsa musu da kira.

Abbu yace "ba matsala ko yanzu kunyi ƙoƙari sosai kun nuna ƙarfin Amintaka, kuma kun jajirce Akan Abokinku jajircewar da iyayen cikinsa ma suka kasayi a kansa" bamuda bakinyi muku godiya saidai Addu'a da fatan Alkhairi a rayuwar ku.
Tabbas zanyi kewar ku zanyi kewar abokan shawara da tattaunawa wannan matsalar.
A iya Zaman da nayi daku nafahimci abubuwa da dama dangane daku Shakka babu iyayenku sunyi sa'ar samun Yara Nagari. Abbu yafaɗa yana murmushi ƙarfin hali.

Allah yaga zuciyarsa baya Son tafiyar su Haidar ɗin, Saboda yafara fahimtar Wani Abu a cikin firar da yake dasu musamman Idan Suna firar Ranar da Shadow ya ɓata.
Yanzu yafara dasa zargi akan Wannan lamarin.
Amma ba kwakwarrar shaida dole sai Idan Suna tare zai Samu abunda yake so, saidai kuma kashhhhhh yanzu gashi zasu tafiyar su.

Muma ba a son ranmu zamu tafi ba Abbu, da munso muzauna Sai lokacin da abokinmu ya bayyana Amma hakan ya gagara.
In sha Allah Koda Mun koma gida bazamu watsar da lamarin Ahanaf ba zamuyi iya bakin ƙoƙari dan ganin yadawo gida indai yana Raye.
Koma zamu dinga Kiran waya muji halinda Ake ciki.
Haidar yafaɗa yana sunkuyar da kansa ƙasa cox har idonsa sun kawo ruwa.


Masha Allah Naji daɗin wannan bayanin naka Takwarana Kuma Dan Allah Idan kun tafi gida Ku haɗani da iyayenku mugaisa dasu Dady yafaɗa yana bubbuga kafaɗarsu alamar godiya.


Ayiya wace idanunta suka cika da kwala tace mungode sosai Allah yasaka Muku da mafificin Alkhairi. Kunga dai yadda abubuwa suka faru kunzo bikin abokinku da tayashi murnar Shiga sabuwar rayuwa. sai kuma gashi akasin hakanne tafaru.

Najima da muradin Allah ya nuna min auren Ahanaf.
Ashe a haka nasa auren zaizo tabbas nashiga ƙunci wanda tunda nake ban taɓa Shiga makamancin sa ba.
Bansan dalilin da yasa Abban naku da Dadyn su Norr suka yanke wannan mummunan hukuncin ba.
Ayiya tafaɗa tana share hawayen idonta.

Ki barsu Kawai Shuwa in sha Allah komai zaizo da sauƙi kedai Kawai kici gaba da haƙurin da kika Saba kuma kibi yaronki da Addu'a, Addu'ar iyaye Akan ƴaƴansu karɓaɓɓiya ce.

Hakane ki kwantar da hankalinki Ayiya da yarda Allah Ahanaf Zai dawo garemu cikin ƙoshin lafiya cewar Kamal ya goge guntun hawayen da yataru a gefen idonsa.

Allah ya yadda
Ameen ya hayyu ya qayyum

Har bakin Mota Mutanen gidan sukayiwa su Haidar rakiya.

Audu driver yazo da niyar yakaisu tasha Abbu yace a'a barshi kawai nida kaina Zan rakasu.

Haidar yaƙara Bawa Ayiya baki akan taci gaba da haƙuri komai zaizama labari da yardar ubangiji, kuma Sannan Idan Abba yadawo kigaya masa mukam muntafi da munso Sai Idan yadawo muyi sallama. Amma Hakan ya gagara Saboda lokaci Yana Tafiya.
Bakumi Haidar duk yadda yakamata kunyi tsakaninmu daku Kuma saidai fatan Alkhairi.

A haka suka rabu kowa da Yanayin da yakeji a ransa.

Suna cikin Tafiya Abbu yafara Magana cikin sanyin murya yace "kubi rayuwa a hankali, kuma kuriƙe Askhar kudaina tunanin bakuda maƙiya wallhi makashinka yana tare dakai bazaka taɓa fahimta ba Saboda bazai Baka damar haka ba Amma Idan kareƙe Addu'a tohm tabbas ba abunda ya iya dakai saidai ya mutu da baƙin cikinka.

Dukansu Ido suka zubawa Abbu Suna kallonsa Kuma kowannen su da tunanin da yake a ransa.....✍️✍️✍️






Nabeela Binji ce💃💃💃





Nabeelah Shehu Binji

09064314811
Or
09161107610




More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏.



♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM


PAGE

1️⃣ 9️⃣













_________________ Abbu kodai kaima akwai Wanda kake zargi ne?

Girgiza kai Abbu yayi tare dayin murmushi yace a'a Ku yarane bazaku taɓa fahimtar abunda nake nufi ba.
Nidai Kawai Nasiha na muku.

Ahaka sukaci gaba da fira har suka ƙarasa tasha.




GIDANSU SHABANA



______________ Kuka take darza kamar Ranta Zai fita. cikin tashin hankali tace" Dan Allah karka yanke wannan hukuncin Dady Kaji tausayin sa yanzu Idan muka barshi Ina zaije?

Gurin da yafito Shabana wayasan iya mahaukatan da ke yawo agari? da yawansu sunfishi Zama Abun Tausayi kuma da yawansu ƙaddarar su tafi tashi zafi. Dukansu zakije kitaimake su ne? Dady yafaɗa cikin tsawa da ɓacin Rai.


Kuma bari kije Magana ta ƙarshe Karki ƙara taka ƙafarki gurin wannan mahaukacin indai nine mahaifinki. Dady Yana gama faɗar haka yatashi ya wuce fuuuuuuuuuuh Kamar zai tashi Sama.

Hannayenta ta ɗaura aka tare da kurma uban ihu tace nashiga ukku Ammi Dan Allah kibawa Dady haƙuri, wlllhy Ahanaf ba mugu bane, Ammi Bazan iya kyaleshi a cikin wannan Yanayin ba, Ammi tun lokacin da nafara ganinsa kullum Sai nayi mafarkinsa Sai naganshi Yana neman taimakona Ammi. Irin haka Bata taɓa faruwa dani ba Sai yanzu. Ammi Dan Allah kutaimaka muceto rayuwar sa. Shabana ta faɗa ta ƙara sautin Kukanta.

Abunka da UWA da ƴarta Nan take Ammi taji kalaman Shabana sun ratsata kuma taji tana tausayin Ahanaf ɗin.
Tohm kukan ya Isa haka mana saurara kiji.
Jin Ammi tayi Magana cikin sanyin murya ba Kamar yadda tayi tunani ba yasa ta share hawayen ta tare da Maida hankalinta Kan Ammi.

A yanzu dole kiyi haƙuri kibi umarnin mahaifinki.
Saboda wannan fushin da yayi yanzu ba ƙaramin Abu ne zaisa ya sauko ba, Sai daima yaƙara ɗaukar abun da zafi komai ya ƙara lalacewa. Ki kwantar da hankalinki in sha Allah zan fahimtar dashi Amma gaskiya ba yanzu ba Sai lokacin da naga ya sauka Sannan.

Ajiyar zuciya Shabana tayi sannan tace Hakan ma nagode Ammi.

Amma wani hanzari ba gudu ba Shabana taya zaki taimakesa ne? Wanda likitoci da kansu suka kasa gane cutar sa.

Ammi Dr Fahad yayi min bayani Akan haka yace "saidai Idan Sihiri ne ko Aljanu" kinga kuma wannan ba matsalar asibiti bace.

Hakane gaskiya, in sha Allah Zan taya ki lallaɓa mahaifinki tunda aikin Alkhairi zakiyi.

Yawwa my Ammi Allah yasaka Miki da khairan yaƙara Nisan kwana kiga Yaran Autar ki, tafaɗa tana Dariya Kamar ba ita ce tagama darjar uban Kuka yanzu ba.

Dukan Wasa Ammi Takai Mata tace "Ja'irar yarinya wato Ko kunyar Ido nama bakyaji Tsabar kin mayar dani sa'ar ki Ko?

Dariya Shabana tayi sannan tace tohm bakya so kiga yarana ne Ammi? tafada cikin shagwaɓe fuska.

Banida Wani Buri a yanzu da yawuce naga na aurar dake tamkar sauran ƴan uwanki.
Nima nasamu nasarara da Wannan rigimar taki.
Murmushi Shabana tayi kana tace wata Rana Sai kinyi kewar rigimar tawa Ammi.
Aa Nikam Bazanyi kewarki ba Dariya sukayi gaba ɗayansu.
Tashi Shabana tayi tace Bari naje na ɗan kwanta kafin azahar Ammi.
Okay a tashi lafiya.

Tana Shiga ɗakin tafaɗa kan gado wayarta ta ɗauko ta Danna Kiran Dr Fahad.

Bayan ya ɗaga ne take tambayar sa ya Ahanaf ɗin.
Murmushi Dr Fahad yayi bazaki daina ambatar waɗan nan sunayan ba ko.
Ita ma murmushin tayi sannan tace tohm Ai sunayansu Kenan.
Eh kuma hakana gaskiya Amma da Kika kira sunansa bai razana sosai ba Kamar lokacin da Kika kiran sunan macen. Gaskiya Ina tunanin Kamar yana matsala da ita Shabana.
Numfashi ta furta tare da gyara kwanciyar ta tace Nima haka nayi tunani Dr.

Tohm yanzu ya kukayi da Dady?
Gajeren tsaki tayi kana tace "Dady ya hani zuwa gurin Ahanaf yace indai shine mahaifina Karna ƙara zuwa gurinsa.
Subhanallah, tohm yanzu ya za'ayi Kenan?
Nima bansani Dr Amma Ammi tace nabari zata shawo Kan Dady ya amince mutaimaki rayuwar Ahanaf.
Gaskiya kam haka yakamata ayi Saboda yanzu fa gabaki ɗaya yaƙara birkicewa kamar kar ki ambaci sunan wannan yarinyar shikenan Abun nasa yaƙaro sosai.

Zanyi ƙoƙari insha Allah Dr.
Tohm Allah yataimaka
Ameen ya Allah.
Sallama sukayi ta katse Kiran.

Peppers ɗin da ke ɗauke da Zanen Shadow da Norr ta ɗauko, buɗe su tayi tana kallon Zanen. Maida hankalinta tayi akan fuskar Norr ta ƙura Mata Ido.
Wannan mai tayiwa Ahanaf haka?
Kodai sonta ne ya taɓa Shi?
Maybe yaudarar sa tayi sanadiyar haka yasamu taɓuwar hankali. Jim tayi kaɗan sai kuma tace "Kai duk ba haka bane Idan da hakene ai da a brain ɗin sa za'aga cutar, ita kaɗai ke zancenta Kamar wata taɓaɓɓiya.
Ji tayi an turo ƙofar ɗakin ta da sauri ta ɗago Kanta Dan taga wanene.

Ajiyar zuciya tayi tare da banka mata Uwar harara.
Murmushi Hafeeza tayi sannan tace "yaudai saidai kici kanki masifaffiya, Dan ni yau banajin rigima" Hafeeza ta faɗa tana zama kusa da Shabana.

Zanen Shadow take kallo cikin mamaki hannunta ta miƙa ta ɗaukoshi daga cinyar Shabana. Zanen ta Kalla sosai sannan ta Maida idonta Kan Shabana tace "kai Kamar wannan mahaukacin naki, Ina kika Samu wannan Zanen?

Ba kama bane shine Hafeeza.
A cikin wannan jakar tasa nasamesu.
Kinga harda na mace Shabana ta faɗa tana miƙawa Hafeeza Zanen Norr.
Karɓa tayi tana dubawa Saida tagama karanta rubutun da yake ƙasan zannen Norr. ta ɗago tana kallon Shabana wacce ita ma idanunwanta suke Kanta.

Dama yana da Mata ne? Hafeeza ta tambayi Shabana.
Kafaɗa ta ɗaga mata alamar ita ma Bata Sani ba.

Nan dai ta faɗa mata Duk abunda yafaru ɗazu. da kuma shaƙar da Shadow yayi mata Dan Kawai ta ambaci sunan wannan yarinyar.
Iko Sai Allah tohm yayi Magana?

Aa baiyi Magana ba saidai tsantsar bacin Rai ya bayyana a tare dashi dan nan take ya Koma mahaukaci na haƙiƙa.
Kedai kibi komai a hankali Shabana Wannan mutumen dai baki sanshi ba Allah ne ya dasa miki tausayinsa da kuma son taimakonsa, ki dage sosai da Addu'a in sha Allah komai zaizo da sauƙi.

Ni yanzu matsala ɗaya shine hanani zuwa gurinsa da Dady yayi.

Ke yanzu Dan Allah bai baki haushi ba?
Kai Shabana ta girgiza Sannan tace ko kaɗan Sai ma a lokacin naƙara jin kwarin gwiwar taimakonsa........✍️✍️✍️







Nabeela Binji ce💃💃💃





Nabeelah Shehu Binji

09064314811
Or
09161107610




More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏.




♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM


PAGE

2️⃣ 0️⃣






____________ Eh Lallai hukuncin da Dady ya yanke shine daidai da Ke, Hafeeza ta faɗa tana bankawa Shabana harara

Kallon ban fahimceki ba Shabana tabi Hafeeza dashi.

Duk kinji abunda na faɗa mutum ya tashi kashe ki Wai Har kina da bakin cewa Bakiga laifainsa ba.

Tabbas banga laifinsa ba Saboda Baya cikin hankalinsa Hafeeza, inaji a jikina raɗaɗi da azabar da Naji a lokacin da ya shaƙi wuyana baikai raɗaɗi da azabar da yake ji a cikin zuciyarsa ba.
Kuma taimakon Ahanaf yanzu Na ɗaura ɗamara in Allah ya Yarda.

Hafeeza tace "Yayi kyau Allah yataimaka Sayyada Shabana" ameen ya Allah Shabana ta faɗa tare da kwanciya kan bed.

Kallonta Hafeeza tayi tace "nifa ba zuwa nayi na Kalli yadda kike bacci ba zuwa nayi ki rakani Wani guri plxxx" Bazanje ba shine Kawai Abunda Shabana ta faɗa batare da ta Kalli gurinda Hafeeza take ba.

"Haka kika ce?"

"Eh haka nace"

"Dani kike zance"

"Dama ai bance da wani nakeyi ba"

"Bazanga laifinki ba Saboda yanzu da mahaukata kike alaƙa"

"Zama ki iya kirana da mahaukaciyar Amma kisani ba gurinda Zan rakaki" Shabana ta faɗa tana Dariya ƙasa ƙasa.

Hafeeza tace "Gud gobe ma rana ce zaki zo har gida ki min fuskar Tausayi Akan narakaki Wani gurin" anan ne nima zan rama.
"Saidai ki rame" Shabana ta faɗa tana yiwa Hafeeza gwalo.

Dundu Hafeeza ta naɗa mata a baya tare da fita ɗakin da gudu tana Dariya.

Cikin ɗan ɗaga murya yadda Hafeeza zata jiyo ta Shabana tace " Wallahi bashi kika ci yarinya kinfi kowa sanin Halina Idan natashi ramuwa fin haka zan miki Allah" murmushi Hafeeza tayi dan Sarai taji Abunda ƙawar Tata tace, saidai sauri take batada lokacin tsayawa bata amsa yanzu.



WACECE SHABANA?


____________ SHABANA USMAN WASAGU Shine cikakken sunanta.

Mahaifinta Alh Usman Wasagu (Dady) haifaffen Garin Wasagu ne dake Birnin kebbi.
Wanda kuma a yanzu suke Zaune a Garin Katsina.
Kwarraren ɗan kasuwa ne Mai Ilimin Addini dana Zamani Wayayyen Mutum Wanda yasan kima da darajar ɗan Adam.
Matar sa ɗaya Hjy Hauwa (Ammi) cousin ɗinsa ce Suna zamansu lafiya cikin mutunta Juna, Yaran su Shidda.

Maleek Shine Babban ɗansu Wanda yanzu yakeda mata ɗaya da Yara biyu.

Suhail shine na biyu yana da mata da yaro ɗaya,

Sai tawaye Abdul_ Haleel da Abdul_Hameed. Waƴanda a yanzu suke karatun digree a ƙasar Germany.

Sai Hidayat ita ma tayi aure tana da yarinya ɗaya.

Sai Auta Shabana wacce ta taso cikin so da ƙaunar iyayenta da yayyenta maza, Suna ririta ta sosai basu son ganin ɓacin ranta hakan yasa ta zama shagwaɓaɓɓiya.

Duk gidan Shabana tana Shiri da Kowa Amma banda Hidaya.
Hidayat tana da zafin rai da saurin fushi.

Ita kuma Shabana tanada tsokana da Shiga lamarin da ba ruwanta Hakan yasa suka zama kamar Tom and Jerry.

Shiyasa Kullum cikin kai ƙara suke, kuma koda yaushe Hidayat ake ɗaurawa rashin gaskiya, haka yasa Shabana take mata rainin wayau son ranta.

Har yanzu da Hidayat tayi aure bawani Shiri ne tsakaninta da Shabana ba.
Dalilin da yasa Shabana bata son zuwa gidan Hidaya Kenan.
Dan indai kaga sun zauna Zaman 30mint lafiya Toh fa sunyi ƙoƙari.
Ammi tana son taga sun haɗa kansu sun zama abokan shawarar Juna Amma Abun ya gagara, hakan yasa take binsu da Addu'ar shiriya.

Shabana tanada son mutane da faran faran Amma duk da haka bata ɗaukan raini indai ka mata ba daidai ba sai ta rama.

Haɗuwar ta da Hafeeza ma faɗa ne sanadiya Saida akayi rashin kirkima juna Sannan aka zama Aminan juna, batada wata ƙawa Sama da Hafeeza Cox ita ba mai ra'ayin tara ƙawaye bace.
Dama hausawa sunce Sai hali yazo ɗaya ake Jin daɗin zama.


Saidai Kuma Shabana da wani ciwo a zuciyarta ciwon yana tashine a duk lokacin da tashiga damuwa.
Kuma Idan ya tashi tana wahala sosai Kamar zata mutu, Hakan yasa Ake mata duk abunda take so indai bai saɓama Shari'a ba.



WANNAN SHINE TAƘAITACCEN TARIHIN SHABANA........✍️✍️✍️









More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏.


♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM


PAGE

2️⃣ 1️⃣






DAWOWA LABARI



_____________ Bacci take har kusan 1:20 tashi tayi cikin firgici tace "Subhanallah me yake faruwa ne?"
Tambayar da tayi ma Kanta Kenan Tare da ɗauko wayarta cikin sauri tafara Kiran Dr Fahad.

Kusan 6 miss call ta masa bai ɗaga ba duk Inda hankalinta yake ya tashi ji take kamar ba lafiya ba.

Ga kuma Dady ya Mata shamaki da zuwa gurinsa.

A hankali ta fara saukowa Daga Kan bed ɗin kamar wacce Kwai ya fashewa a ciki, toilet tashiga wanka tayi tare da ɗauro alwala.
Sallah tayi bayan ta sallame ne tafara Addu'ar Allah yabama Ahanaf lafiya, Allah yasa Dady ya sauko ya bata dama ta taimaki rayuwar Ahanaf.
Bayan tagama Addu'o'inta wayarta ta ɗauko taƙara Danna Kiran Dr Fahad Kamar ɗazu ringing take Amma ba a ɗauka.

Idan hankalin Shabana yayi dubu Toh ya tashi.
Gabaki ɗaya tunani da kumai nata sun koma Kan Ahanaf,
Tana so taji Wani Abu dangane dashi Amma ba Hali.
Wasu siraren hawaye taji suna bin fuskarta.

Ƙofa taji an turo da sauri ta goge hawayen da suka zubo Akan fuskarta.

Ammi ce tashigo ɗakin tana bin Shabana da kallo, gefen bed ta zauna tace "lafiya kuwa Shabana?
Me yafaru kike kuka?" Kai ta sunkuyar ƙasa tace "ba

Please Login or Register in order to submit comment