Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne na Maida Haj Ladi ta zama Babbar ƙawata ba Abunda zanyi batare da tasani ba.
A sannan ne nafara galazama Ahanaf a Bayan idon Muhammad, Idan yana kuka ba ruwana dashi, saina Lura mahaifinsa ya kusa dawowa sannan nake ɗaukarsa nayi masa wanka na bashi Madara.
Har yafara cin Abinci yayi wayau ina gallaza masa, lokacin da ya fara iya Magana wata rana muna zaune tare dashi Muhammad yadawo daga gurin aiki, Yana ganinsa ya yatafi da gudu ya rungume shi yace "Abba Ayiya bugani" a Ranar naga tsantsar ɓacin rai agurin Muhammad yadaina kulani Idan nayi Magana baya tankawa, kuma Idan zai tafi kasuwa sai ya shirya ɗansa ya tafi dashi, nashiga damuwa sosai Hakan yasa na faɗawa Haj Ladi Abunda yake faruwa, Anan tace "mu koma gurin Malam mu faɗa masa Abunda yake faruwa.
Mun faɗa masa yayi Dube duben sa yace "duk abunda zakuyi bazaku iya Shiga tsakaninsa da ɗansa ba Saboda Shaƙuwa ce mai tsanani a tsakaninsu, kuma shi uban nashi yanzu ya Tashi tsaye da addu'a ba abunda zamu iya yi masa.
Haka muka dawo gida jiki ba ƙwari Anan ne Haj Ladi tace "yanzu yakamata kiyi aiki da kissa muddin kina son zamanki Lafiya da Muhammad, dole ki ɗauki son Ahanaf na ƙaraya kisa a zuciyarki, Dan yanzu yayi wayau duk Abunda kika masa zai gaya ma mahaifinsa, kiyi anfani da kwakwalwarki ki jefi tsuntu biyu da dutse ɗaya, Idan kika nuna masa matsancin So har ya gamsu da ke ɗin mahaifiyarsa ce, to zuwa gaba duk abunda kika masa ba ma wanda zaiyi tunanin kece.

Haka nayi aiki da shawarar ta nafara nuna So da damuwa ta Akan Ahanaf.
Lokacin da yacika shekara ukku a lokacin Na Samu cikin ƙaseem nayi murna sosai dan ganin nima Zan aje ɗa da Muhammad.
Bayan Wata Tara na haifishi akayi bukin suna yaro yaci Suna Al ƙaseem.




Bayan shekaru da dama tun Bayan ƙaseem ban ƙara ko ɓatan wata ba, hakan yasa na ɗauki son Duniya Na ɗaura Masa, Ina kallonsa a matsayin magajin dukiyar da Muhammad yake Tarawa.
Sai kuma Wani Abunda yake damuna shine na Lura akwai Shaƙuwa sosai tsakanin ƙaseem da Ahanaf, Suna ƙara girma Shaƙuwar su tana ƙara ƙaruwa Suna masifar son junan su, nayi ƙoƙarin hana kaseem Shiga harakar Ahanaf, Amma sai ya jefomin tambayar da banyi tsammani ba, yace "Ayiya Kodai ba ke kika haifi ya Ahanaf ba? Na matuƙar girgiza da Naji haka, nayi masa faɗa sosai daga lokacin na daina Shiga tsakaninsu.

Lokacin da aka fitar da Ahanaf America karatu lokacin Naji matsancin baƙin ciki, Har nace ma ƙaseem Shima yace mahaifinsa ya fitar dashi ƙasar waje, Amma sai yace shikam bashida sha'awar haka, yafiso yayi karatun kasuwanci kamar mahaifinsa kuma a makarantar da mahaifinsa yayi, hakan yasa ya Shiga Usama ɗan fodiyo University, yafara karatun sa, ba dan Raina yaso ba na haƙuri da Hakan.


Bayan Ahanaf ya Kamala karatunsa ne ya dawo gida, naga ya ƙara girma yazama cikkaken saurayi, Duk da cewa ba harakar kasuwanci ya karanta ba Amma duk wata shawara dashi mahaifinsa yakeyi.
Ana cikin haka yazo yasameni da maganar Auren Norr nashiga matsanancin ruɗu saboda nasan munyi magana da Haj Ladi Akan zata bayar da auren Norr ga Al ƙaseem, Anan na tambaye shi ya sanar da mahaifinsa yace "eh yasanar dashi ɗazu da safe" nace masa Toh ba matsala Allah ya Sanya Alkhairi.


Bayan fitarsa na kira Haj Ladi na faɗa mata Abunda yake faruwa, tace "ita ma yanzu Alh Mukhtar ya faɗa mata Wai Alh Muhammad ya kirashi Akan maganar Auren Norr da Ahanaf" nace "Menene mafita?" Tace mafita ɗaya ce mu ɓullowa lamarin ta inda basuyi tsammani ba, kinsan ni tun farko ba son Yaron nan nake ba, kinga ba yadda za'ayi na bashi Auren ƴata.

Su Alh sun gama Maganar Aure tsakanin Norr da Ahanaf, Nida Haj bamu nuna ƙiyayyar mu Akan haka ba,
Lokacin da aka saka Ranar bikinsu Yaya Aliyu baya ƙasar, saidai ayi waya dashi kuma hakan ba ƙaramin daɗi yayi muna ba saboda munsan Shirin mu zai tafi Kamar yadda muka tsara.

Ahanaf ya Gina gidansa yayi tariyar lefensa biki sai ƙara matsowa yake.

A lokacin muka tafi gurin Malam muka faɗa masa Muna so a juye ɗaurin Auren ya Koma Kan ƙaseem a Maimakon Ahanaf. Kuma ya haukatar da Ahanaf ɗin ya bar gida ta yadda Mutane zasuyi tunanin ɗaurin Auren ne ya haifar masa da taɓuwar hankali, Muna son Bayan an ɗaura Auren su yaran su ƙarbi junan su a matsayin ma'aurata.
Nace kuma Kar Yayan mahaifinsa da iyalinsa su halacci ɗaurin Auren har sai an kammala Komai.

Malam yace "Aikinku mai Wahala ne Amma zan Muku saboda Mun Jima a tare, Amma fa kusani aikin yanada haɗari saboda Idan Yaron ya dawo cikin hankalinsa Toh asirin kowa zai karye ba Shine tashin hankali ba Sai Idan ya dawo gida, muddin ya taka ƙafarsa gidan nan Toh asirin zai dawo kanku Daga zarar kunyi Bacci, Saboda suma Yaran ta hanyar Bacci zamuyi musu aikin.

Haj Ladi tace "yanzu ba wata hanya dole Idan Asirin jikinsa ya karye na kowa ma zai karye? kuma Idan ya dawo gidan Muma zamu haukace?
Malam yace ko Shakka Babu, Amma fa asirin da zamuyi masa yana da wahalar warware, bayan Mun haɗa shi da mahaukacin aljani zamuyi masa aikinda dole Sai an ɗaura Masa Aure Zai dawo cikin hankalinsa, kunga kuwa bazai warkeba har Abada, Bayan haka Idan aikin ya tafi yadda muke so Ina so kununa kunfi kowa shiga damuwa ta yadda ba wanda zai zargeku"
Godiya mukayi masa muka dawo gida.
Haka mukayi komai cikin tsari Kamar yadda Malam yace.

Bayan Komi ya tafi yadda muka shirya ne daga Baya nayi tunanin Idan Yaya Aliyu ya dawo zai iya tashi tsaye da nemawa Ahanaf magani, Sai nakira Haj na faɗa Mata, nace "Idan akwai wasu ƴan daba da tasani ta haɗani dasu zansa su kashe Ahanaf Saboda bana son asirin ya tonu har Abada" Anan ne ta haɗani da su Jibgege, adaren na faɗa musu buƙatata kuma a Daren suka yarda zasuyi aikin.

Saida dare ya raba Kowa yayi Bacci na ɗauko key's ɗin ɗakin Ahanaf na baya, nasa kyalle a hannuna na buɗe ɗakin gudun kar ayi bincike a gane nice na buɗe sa yafita, ni Naja Ahanaf da hannu, tare da mai Gadi muka haɗa baki ya buɗe min ƙofa na fitar dashi, dama su Jibgege Suna waje Kawai na basushi nace su kashe Shi su jefar da gawarsa ba a wannan Garin ba Amma.
Wannan Shine gaskiyar Abunda yafaru sai kwanakin baya da Malam yace min Ahanaf yadawo cikin hankalinsa, nasaka su Jibgege nemansa cikin Garin Katsina.
Sun ganshi Amma basuyi nasarar Kama Shi ba Saboda sunce ya Shiga police station, yanzu haka suna can Akan suna neman Ahanaf.......✍️✍️✍️








Nabeela Binji ce💃💃💃







More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏.







♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM



PAGE

4️⃣ 2️⃣













_____________ Innalillahi wa'inna Ilaihi Raju'un ita ce Kalmar da duk Wanda yake palon ya dinga nanatawa, Norr Yassar ƙaseem Kuka suke Kamar ransu zai fita, Wannan wane kalar Abun kunya ne iyayensu suka tabka haka?

Abba Cikin matsancin baƙin ciki har muryarsa na sarƙewa yace "kin cutar dani kin cutar da Khadeeja duk da bata Raye, kin ci Amanar yarda, Kin sakamu a cikin DUHUN INUWARKI, kinyi Muna lulluɓin Sharri Shuwa.
Ada nazata cikin Ni'imtacciyar INUWA kikasaka mu Nida yarona ashe cikin DUHUN INUWA kika jefamu Hakan ya hanamu gane ai Nahin kalarki.
Amma da yake Allah mai Rahma ne Sai ya haska Mana fitila muka fahimci ke guba ce a rayuwar mu.
Bazan yi miki Allah ya Isa ba Amma kije keda halinki, zaki girbi Abunda kika shuka. Ni Muhammad Imran nasakeki Saki biyu bani bake har Abada" ya subhanallah Abbu yace "kana da hankali kuwa mai yasa kake yanke hukunci cikin fushi?" Me zanyi da Shuwa Yaya? Bazan taɓa iya Zama da ita ba duk da cewa na haɗa zuri'a da ita Amma zuciyata tafasa take yanzu da nake kallonta, natsaneta natsaneta Yaya" Abba ya faɗa hawaye nabin fuskarsa?

Abbu yaji tausayin ƙanen nasa sosai wannan Abun da yafaru tabbas abune mai matuƙar ciwo a zuciya.

Tashi Ahanaf yayi yafara Tafiya Kamar wani ɗan Maye yanufi hanyar fita daga Palon, ba Wanda yayi ƙoƙarin hanashi saboda sun san tun yana yaro Idan ransa ya ɓaci yafi So yaje ya rufe Kansa a ɗaki baya so kowa ya kulashi.

Da kallo Shabana ta bishi cikin masifar Jin tausayi, Allah yasani in banda Taron Mutanen da suke palon da tuni ta bishi Abaya, saboda ita da Kanta tashiga tashin hankali dajin labarin Ahanaf, Toh ina dashi da Abun yasama? Hawaye taji Suna bin fuskarta.

Tashi ƙaseem yayi ya nufi gurin Ayiya ya zube agabanta cikin matsanancin kuka mai tsuma zuciya yace "meyasa meyasa meyasa kikayi muna haka Ayiya? Menene ribarki? Kin cutar dani, kowane Ɗa Yana son ace yana da mahaifiya tagari.
Ni da wane Ido Zan Kalle Duniya na faɗa musu tarihin mahaifiyata? Ada nasha alwashin ɗaukar fansa ga duk Wanda ya cutar da ya Shadow Ashe da mahaifiyata zanyi yaƙi" ƙaseem ya ƙarasa maganar cikin kukan da yake fitowa daga ƙasan zuciyarsa.
Shuru Ayiya tayi dan har a zuciyarta bata son ganin Yaron nata cikin damuwa, Amma sai gashi yau ita ce silar kukansa agaban Mutane.

Dadyn Norr ya Tashi tsaye ya Kalli Norr da Yassar yace "kutashi mutafi gida, Ke kuwa ki koma gidan ubanki bani bake Ladi, kinci mutuncina kin tozarta ni, Allah yasakawa waƴanda kuka zalunta"
Maida kallonsa yayi gurinsu Abbu yace "Yaya Mun tafi, zan dawo insha Allah muyi Magana daga baya"
Ajiyar zuciya Abbu yayi yace "Allah ya sauke Ku lafiya" tashi Norr tayi tsaye kawai saiji tayi Jiri ya ɗebeta tayi luuuuu zata faɗi da sauri Yassar ya riƙota ta faɗa jikinsa.

Tayar da ita yayi ta ƙara shigewa cikin jikinsa cikin muryar kuka tace "riƙe ni Yassar Jiri nake ji zan iya faɗuwa" rungumeta yayi yafita da ita waje, buɗe mota yayi yasaka ta baya ya Kwantar da ita, ya buɗe gefen Mai zaman banza Dady ya zauna, sannan ya zagaya yashiga Motar yaja suka bar gidan da mugun gudu.
Wani irin ƙuna Yassar yakeji a zuciyarsa, mahaifiyarsa da zuwa gurin mushuruki dan kawai ta illata rayuwar wanda ba abunda ya shiga tsakaninta dashi, wasu zafaffan hawaye yaji suna ambaliya a fuskarsa, da kyar yaga ya Isa gida.




Abba yatashi tsare tare da dafe kansa har ya fara Tafiya yatsaya ba tare da yajuyo ba yace "Karki yadda na ƙara Ido biyu dake, Wallahi muddin kika yadda Idona ya ƙara tozali dake saina shayar dake mamaki" Yana gama faɗar haka ya fita daga Palon.

Ajiyar zuciya Abbu yayi tare da tashi yakama kaseem da yake ta zuba kuka Kamar ransa zai fita ya zaunar dashi a gefensa Yana share masa hawayen fuskarsa, cikin sanyi murya yace ya Isa kaseem kayi Shiru karka cutar da kanka kaji, kai ba Mai laifi bane kuma ba Abunda zai rabamu dakai Saboda kai jininmu ne, kaci gaba da Abunda kake mai kyau, Allah yana fitar da matacce a cikin rayayye, dubi tarihin Annabi Ibrahim kagani, mahaifinsa ɓatacce ne shi kuma shiryayye kuma mai shiryarwa, Idan har ubangiji zai jarabci Annabinsa to kai waye da bazai jarabce ka ba? Ka nutsu ka fawwalawa Allah Komi insha Allah komai zai zama labari, kai ka Gina rayuwarka akan gaskiya kaga yadda Nasarori zasu baibaye ka.
Shuru ƙaseem yayi yanajin nasihar Abbu. DA kyar Abbu yasamu ya Kwanta masa da hankali.


Tashi mommyn Norr tayi tare da Jan hannun Ayiya tace "ki tashi muje, menene Ma'anar Zaman mu Anan?" Tafaɗa tana zuba Uwar hamma.
Tashi Ayiya tayi tana Ganin Kumi da yake Palon yana zamar Mata biyu² fita sukayi daga palon ba Wanda yayi yunƙurin hanasu.

Ajiyar Dady yayi ya Kalli Abbu yace "Alh bansan ku ba ban taɓa ganinku ba sai yau, kuma a Yau sanadi yasa mukasan tarihin ku, ɗan Jim yayi Sannan yace tabbas sun cutar da rayuwar Ahanaf nesa ba kusa ba, Amma da yake Allah bai ƙaddari zai tabbata cikin Wahala ba, sai ya jiɓanci lamarin sa. Kafin yanke irin wannan hukuncin yana da kyau ayi tunani mai kyau" Murmushin takaici Abbu yayi Sannan yace "Alh ba laifina bane tabbas na Isa da Muhammad kuma nakan saka shi yayi Abu ko yana so ko baya so, Amma Idan naga Abu zai Zama cutarwa a rayuwarsa nakan barshi ya yanke hukuncin da yakejin Shine zai Samar masa da salama, tinda nake da Muhammad ban taɓa sakashi Abu yaƙi yayi ba, Tohm kaga bai kamata ace kullum ina shigar masa rayuwa ba dan kawai mahaifiyarmu tace yayi min biyayya" kai Dady ya gyaɗa yace "Allah yasa haka Shine mafi Alkhairi.


Haj Mama ta Tashi tsaye tare da Tayar da Shabana wacce taci kuka har idanunta suka sauya Kala, tace "tashi mu tafi kisamu kihuta, ta Maida kallonta kansu Ammi da Hafeeza tace ku tashi muje kuhuta Haj" Tashi sukayi tare da bin Bayan Haj Mama.


Abbu ya Kalli su Haidar yace "Haidar Tashi kutafi ɗakinsu kaseem kuyi Alwala lokacin Sallah ya kusa" Maida kallonsa yayi kan ƙaseem yayi yace "tashi kutafi ƙaseem zamuyi maga Anjima Kaji" Abbu yafaɗa yana tayar dashi tsaye.
Tashi ƙaseem yayi ya suka fita tare da su Haidar, koda suka Shiga ɗakin ƙasa ya zauna gefen gado tare da haɗe kai da gwiwa yana kuka mai tsuma zuciya.
Zuwa Haidar yayi ya zauna kusa dashi tare da farayi masa nasiha.
Har aka Fara Kiran Sallar magrib, tashi sukayi suka ɗauro Alwala.
Har zasu fita Haidar ya nufi ɗakin Shadow yafara Kwankwasa ƙofar, ya jima a tsaye yana Abu ɗaya har yagaji ba'a buɗe ba, Dole ya juya yace musu "mutafi yaƙi ya buɗe."




Su Ayiya na fita suka Tari napep mommy tayi masa kwantance gidansu dan batada gurin zuwa da ya wuce can, Kuɗin ya faɗa Mata tace "suje kawai" dan Har idanunsu Suna fara rufewa tsabar Bacci.

Ɓangaren su Shabana kuma Bayan sun kammala Sallar ne suka Fara fira, ita dai saurarensu kawai take Amma Allah yasani hankalinta kacokam yana gurin Ahanaf tunani kawai take a wane hali yake, kuma ta lura ba wanda yabi ta Kansa, Taji dai Haj Mama na cewa "Idan ya rufe Kansa baya So kowa ya kusancesa" ita kam da wuya ta iya jure hakan, dan Allah yasani yanzu tamafi jin tausayinsa fiye da tunani.

Har kusan ƙarfe 9 na dare bata ga idon Ahanaf ba, sai tattauna maganar ɗazu kawai suke.
Haɗe Kanta tayi da gwiwa hawaye na zuba daga idonta kamar famfo. Ji tayi an taɓa ta da sauri ta goge hawayen idonta Sannan ta ɗago kanta.
Haj Mama tagani tsaye a gabanta, ita batama ji tafiyar ta ba.
Key's taga Haj Mama ta Bata tace "kije ki rarrashi Mijinki, ƙila a samu ya sauko da wuri Idan anyi sa'a, Saboda idan yana fushi zai iya kwana biyu bai fito ba, kije ki gwada sa'ar ki, kila a dace ya fito" Haj Mama ta faɗa tana Tayar da Shabana tsaye ta bata keys ɗin, tace "muje na nuna miki ɗakin"
Karɓar key ɗin tayi tare da bin Bayan Haj Mama har ƙofar ɗakin Shadow, Haj Mama tace "ƴata ki ceto zuciyar Ahanaf daga bugawa da kuma mummunan jinya, kiji tausayin Mijinki Duk da nasan ke ɗin mai Tausayi ce Idan akayi duba da Abunda kika masa baya, Amma yanzu ki linka Jin tausayin kinji" kai kawai ta gyaɗa batare da tayi Magana ba.

Saida Haj Mama ta tafi sannan tafara ƙoƙarin buɗe ƙofar, tana buɗe ƙofar ta shiga, hangoshi tayi kwance a ƙasa kan sallaya sai rawar sanyi yake, ƙofar ta rufe tare dayi kansa da sauri, durƙusawa tayi gabansa Tare da tallafo kansa ta ɗaura Saman Cinyoyinta, wani hucin zafi taji yana dukanta, nan take hawaye suka wanke mata fuska, rungume kansa tayi hawaye naci gaba da zubar mata, cikin muryar kuka tace Ahanaf dan Allah katashi, ka buɗe idonka, meyake maka ciwo?" Jin shurun yayi yawa ne yasa tayi ƙoƙarin sauke kansa ƙasa tace "bari naje nayi Magana da Haj Mama a kira Dr yazo ya duba ka" Ji tayi yasaka duka hannayensa ya ƙara rungume ƙugunta, yana tura kansa cikin jikinta kamar zai shige cikinta.
Ɗan Jim tayi sannan tace "kabari Dr yazo ya duba ka plxx" dakyar ya iya buɗe bakinsa yace "bana buƙata, ki zauna abunki kawai" tace "taya zaka zauna da zazzaɓi haka ajikinka kace baka so a dubaka?"
Shuru yayi kamar bazaiyi Magana ba sai can yace "ki zauna anan zan warware kinji" zamanta ta gyara tare da fara shafa Kansa, a hankali tace "So kake ka kashe kanka Ahanaf? Tabbas ƙaddarar rayuwarka Babbar ƙaddara ce, Amma ina so kasani Badan ubangiji baya sonka bane ya jarabeka ba a'a masu Imani kaɗai ubangiji yake jarabta kuma ita jarabawa tana wanke zunubi, Ina So ka ƙarbi jarabawar ubangijinka kayi rayuwa Kamar ba abunda ya faru, ka Manta da komai Ahanaf" gyara kwanciyarsa yayi ajikinta tare da buɗe Idonsa ya zuba Mata su, da sauri ta kawar da Kanta Ganin yadda idon nasa sukayi Ja, ya Jima yana kallon fuskarta, ajiyar zuciya yayi Sannan yace "Ba Wai na kasa ɗaukar ƙaddara bane, ba kuma nayi fushi da abunda yafaru bane.
Baƙin cikina ɗaya halinda Ayiya ta jefa Kanta aciki, Allah ne shaidata kallon mahaifiya nake mata duk da Ina fahimatar wasu abubuwan daga gareta Amma har raina ban taɓa tunanin ba ita ce mahaifiyata ba, son da nake mata na gaskiya da gaskiya ne.
Sannan abu na biyu da yaƙara ɓata min rai shine ɓoye min mahaifiyata da sukayi, bansan labarin ta ba ma balle Idan nayi Sallah na sakata cikin addu'ata.
Sunan tanada Ɗa a duniya Amma bai taɓa buɗe baki yace Allah yaji ƙanta ba, wannan Abun yazama tauye haƙi Shabana da wanne zanji?" Shadow yafaɗa hawaye nabin fuskarsa.
A hankali tasaka hannunta tana share masa hawayen idonsa, cikin sassanyar murya tace "hakane amma su a tunaninsu sunyi hakane kawai dan gudar maka da zafin maraici kamar yadda Ummi ta roƙa, su sunyi tunanin Ayiya zata iya riƙe Amana, Sai kuma ta kasa, kaga kodan haka yakamata ayi musu uzri" ajiyar zuciya yayi batare da yayi Magana ba Shabana tasake cewa ko a films ban taɓa ganin labari makamancin naka ba, rayuwar ka tazo da ƙalubale Kala Kala, Amma ina fatan Allah yasa kumi yazo ƙarshe" hannunta Shadow yakama tare da ɗaura Shi Saman ƙirjinsa gefen zuciyarsa yace saurara kiji Abunda nakeji" Ji tayi zuciyarsa na bugawa da sauri sauri, shuru tayi aranta kuma masifar tausayin sa takeji.
Cikin raunin murya yace "yanzu ke kaɗai ce hope ɗina, gangar jikina da zuciyata sun zama masu rauni sosai akan Abunda ya faru, Idan kema kika barni Toh fa kisani numfashina zai bar gangar jikina sai naje Na Tarar da mahaifiyata, maybe naji sanyi agurinta" ya faɗa hawaye naci gaba da ambaliya akan fuskarsa.

Da sauri Shabana ta rungume shi sosai ajikinta, cikin muryar kuka tace "ka daina waɗan nan kalaman Ahanaf, Wallahi indai nice Bazan gujeka ba ina tare dakai har Abada, Ina jin tausayinka fiye da kowa a wannan duniyar, ba Abunda Bazan iyayi ba saboda kai, Ahanaf inajinka a cikin zuciyata Jinina da gangar Jikina, kasani Bazan iya rayuwa Babu kai ba" Wani irin shock Ahanaf yaji ya kama jikinsa, cikin matsanancin farin ciki Shadow yace "da gaske kike zaki zauna dani zaki rayu dani ki haifamun Yara?" Kanta ta gyaɗa masa Alamar eh. Wata sassanyar ajiyar zuciya yayi yace "Alhamdulillah Allah Kaine Abun godiya, Wannan shine fatana da burina Shabana, a Tarihin rayuwar Ahanaf Shabana ce shafin farko kuma shafin ƙarshe, Kisa aranki cewa kin tsallake ko wane kalar ƙunci na zama gidan miji, Shabana nayi alƙawarin Bazan sakaki kukan baƙin ciki ba saidai na farin ciki, duk abunda zai ɓata miki rai Bazanyi Shi ba, Saidai Abunda nasan zai sakaki farin ciki" Shadow ya faɗa yana wani kayataccen Murmushi.
Hannayenta tasa ta rufe fuskarta alamar kunya, sauke hannunta yayi yace "plx ki buɗe idonki ki kalleni Precious" Ji tayi hannunsa da zafi raɗau, a hankali tace "har yanzu jikinka da zafi dan Allah kaci Abinci Kasha magani" Tashi yayi zaune Yana kallonta yace "Yau ina son samun sauƙi ne daga jikinki ba daga drugs ba" kallonsa tayi da Mamaki tace "kamar ya Kenan?" iska ya furzar a hankali yace "ki yarda mukwana tare yau dan Allah, Wallahi nayi miki alƙawarin ba Abunda zai faru" Kawai ɗumin jikinki nake sonji" da sauri Shabana ta girgiza masa kanta alamar a'a, ajiyar zuciya yayi yace "zaki iya Tafiya, dama na faɗa ai ba mai son Ahanaf a duniyar nan Idan ba Allah'n da ya halicceshi ba, kuma kisani Idan har kika fita daga ɗakin nan zan rufe shi na bar key ɗin ajikin ƙofa duk wanda yazo ya taru Bazan buɗe ba Sai Bayan 3days" Shadow ya faɗa ba alamar wasa a fuskarsa.

Jikinta yayi sanyi sosai tasan a irin Wannan lokacin Shadow yana buƙatar makusancin sa a tare dashi, kodan halinda yashiga Yau kuma ga zazzaɓi har yanzu ajikinsa, Amma kunya takeji sosai ko a gidansu bata yadda sun kwana a ɗaki ɗaya ba sai yanzu agidan surukai.

Kallonsa tayi ta maka masa harara irin ta ka addabe ni ɗin nan, murmushi Shadow yayi yace "zo ki dakeni ko zaki rage haushi.
Uffan bata ce masa ba, a hankali ya tashi tsaye tare da saka ɗayan hannunsa ya dafe kansa, gaban gadon yaje ya zauna hannunsa ya miƙa mata alamar tazo, kafaɗarta ta maƙe, Murmushi yayi yace "Dan Allah kizo ba abunda zanyi miki Allah, baki yarda da abunda nace bane wai? Wallahi Jiri nakeji" tashi tayi a hankali taje gefensa ta zauna.
Faɗawa yayi jikinta ya rungumeta, aranta tace "Wannan Mutum ya cika son jikin masifa" a fili Kuma tace "yanzu dan Allah haka zaka kwanta da zazzaɓi a jikinka?"
Murmushi yayi tare da matseta ajikinsa yace "na faɗa miki zai daina, ni yanzu ko ruwa Bazan iya Sha ba bare har Abinci" shuru tayi tana sauraren saukar numfashinsa.

Sun Jima a haka sai can taji kamar ya Fara Bacci, a hankali tafara ƙoƙarin Kwantar dashi, Saida ta Kwantar dashi zata Tashi Taji ya riƙo ta batare da ya buɗe idonsa ba yace "ni zakiyiwa wayau? a ƙalla na baki shekara goma a duniya" ya faɗa yana janyota ta faɗa jikinsa.
Murmushi tayi tace "bafa fita zanyi ba Zan kwanta gefenka ne" ƙoƙarin cire Hijab ɗin jikinta yayi, da sauri ta saka hannunta ta riƙe Hijab ɗin tace "plxx karka cire min Hijab" ɓata fuska yayi yace "badai haka zaki kwanta min da Wannan Ƙaton Hijab ɗin ba kamar wata Matar Malam" tace masa "eh nidai ka barni da abina haka nake son kwanciya" Cakulkuli ya farayi mata nan take ta saki Hijab ɗin ta Fara dariya da juye juye a jikinsa Anan yayi nasarar zare mata Hijab,
Ta koma daga ita sai doguwar Rigar material ba ɗan kwali a Kanta.
Hijab ɗin tafara ƙoƙarin ƙwata daga hannunsa tace "Bana son haka dan Allah kabani Hijab ɗina" wulgi yayi da Shi ƙasa tare da sa hannunsa ya rungumeta yace "bazaki Kwanta da Hijab ba gaskiya" turu baki tayi gaba tace "Idan bazaka Bari nasaka Hijab ba kasakeni na tafi ab.... Bai Bari ta ƙarasa ba ya haɗe bakinsu guri ɗaya Yana zuba mata Wasu hot kisses..........✍️✍️✍️











Nabeela Binji ce💃💃💃







More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏.








♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM



PAGE

4️⃣ 3️⃣













_____________ Da kyar take numfashi Saboda matsar da Shadow yayi Mata, sun Jima a haka da kyar ta Samu ya Saketa, ƙoƙarin sauka tafara yi daga jikinsa, ya riƙe ta, a hankali yace "Anan zaki kwana plxx" ɓata fuska tayi tace "a haka zan kwana kana Shirin karya alƙawari?" Murmushi yayi yace "na daina uwar ƴan tsoro" Shiru tayi bata ƙara Magana ba har Bacci yayi awon gaba da ita, Shadow ya kasa Bacci ba Abunda yake sai tunani Akan rayuwarsa, tabbas ƙaddararsa ce Amma kuma tayi masifar karantar da shi rayuwa, tasa ya kara fahimtar Duniya.
Hawaye ne suke zuba a idonsa masu masifar zafi, yana son ganin mahaifiyarsa koda sau ɗaya ne a rayuwa saidai ba damar haka, ga raɗaɗin

Please Login or Register in order to submit comment