Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ibrahim Abunda Dady ya faɗa Shine ya nanata, tare da cewa kazama mai yawan Askhar Ahanaf Ko yayane kasamu katashi Idan dare ya raba kayi Sallah koda raka'a biyu ne, sannan ka miƙa damuwar ka agurin ubangijinka, ba Wanda bashida magauta a duniyar Nan saidai na Wani sunfi na wani haɗari. Sakaci da Ibadah ya kansa Duk Wanda yake biyarka da sharri yayi saurin kamaka, Amma Idan kazama mai yawan Askhar Sai kaga duk ƙiyayyar Mutum dakai Wallahi saidai ya barka, kadage kadage sosai Ahanaf mu Abunda muka maka Allah ne masani Dan Shi kawai mukayi Badan kowa ba.
Sannan da taimakon Shabana saboda ita ce ta tsaya kai da fata Dan ganin kasamu lafiya sanadiyar haka har kwanciya ciwo tayi kamar yadda kaji a labarin.

Dan Allah ka riƙe Amana Ahanaf ka Maida halacci da halacci Kaji.
A halin yanzu Kana da damar ci gabada mallakar ƴata Shabana a matsayin mata Idan ta amince, saboda wannan auren tayi shine kawai Domin samun lafiyar ka saboda tausayin ka, Idan kayi sa'ar mayar da wannan tausayin ya Zama soyayya mu duka Abun farin cikin mune. Kaga daga nan Saika kaimu muga iyayenka musan juna dasu saboda an zama ɗaya in sha Allah." Malam Ibrahim ya faɗa Yana murmushi




Godiya Shadow ya ƙarayi musu sosai, Shi Abu ɗaya ne kawai baya so shine maganar komawar sa gida baya Jin zai iya taka ƙafarsa gidansu, saboda wata irin ƙiyayyar mahaifinsa da yakeji a ransa.


Dady ne yace "Allah gafarta Malam a rufe Muna taro da addu'a dare Yanayi" Bayan an gama addu'ar ne kowa ya shafa, Malam Ibrahim ya miƙe zai tafi Dady yayi masa rakkiya tare da sa Maleek ya sauke sa gida.

Hidaya ma Motar Suhail ta Shiga da kyar wai a cewar sa mijinta yazo ya ɗauketa Shi ba driver ba ne. Saida Ammi tasaka baki sannan ya ɗauketa.

Ammi tace wa Shabana "ki tashi kikai Ahanaf ɗakin su Abdul Dan Inaga shikaɗai ne a gyare"
Ko motsi batayi ba alamar taji abunda Ammi tace, kallonta Ammi tayi tare da cewa "zanfa makeke agurin nan Allah Shabana,
Nasan Sarai kinji Abunda nace Amma Tsabar kin rainani shine ko motsi ba kiyi ba ba Ko?"

Tashi tayi tana Dariya Tare da cewa "Allah ya huci zuciyar Sarauniyar Dady banji bane shiyasa"
"Zakiji ne Idan na kamaki"
"Tashi kuje Ahanaf" tashi yayi yabi bayanta cox har tayi gaba.

Tashi Ammi tayi ta nufi nata ɗakin.

Suna Isa ɗakin ta tura ƙofar tare dayin sallama (yana da kyau idan kun shiga gida ko ɗaki kuyi sallama koda Kuwa ba kowa a ciki Domin hakan yana taimakawa gurin korar sheɗanu da kuma gayyato mala'ikun Rahma Allahu ta'ala a'alam Allah yasa mudace) Shiga tayi Shadow yabi bayanta, ɗakin tabi da kallo bashida wata dauɗa sosai saboda ana gyarashi duk Bayan kwana biyu.

Juyawa tayi ta Kalli Shadow ai Kuwa nan take idanunsu suka gwauraya cikin na juna da sauri ta kauda Kanta tareda jan ɗan gajeren tsaki.
Kawai dan ance baƙonka Annabin ka ne yasa zata gyara masa ɗakin.

Gado tafara gyarawa ta canja Zanen gadon, ta gyarashi tsaf, ta ɗauki lokaci tana aikin Saida ta gama Komai sannan ta buɗe toilet shima ya ɗanyi datti ba sosai ba shima wankewa tayi. Koda ta gama ta fito A gefen gado ta Tarar da Shi.
"kana bukatar wani Abu?" Ta tambayeshi ba tareda ta Kalli gurinda yake ba.

"Aa nagode" shine Kawai abunda da yace yana kallonta.

Hanyar fita tayi Har ta buɗe ƙofar zata fita taji sautin muryar sa a dodon kunnenta Shabanaaah!........✍️✍️✍️












Nabeela Binji ce💃💃💃







More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏.




♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM


PAGE

3️⃣ 0️⃣










_______________Dakatawa tayi batare da tajuyo ba.

"Kiyi haƙuri"

Da sauri ta kalleshi cikin mamaki tace "dami Kenan?"

"Da Abunda naji ya faru a asibiti lokcin da kika je duba ni ke da Dady, wallahi bansan nayi ba kiyi haƙuri" Murmushi Shabana tayi sannan tace "nasani kuma ni dama banga laifinka ba" tana gama faɗar haka ta buɗe ƙofar ta fice daga ɗakin.

Ajiyar zuciya Shadow ya sauke tare da tashi ya rufe ɗakin ya dawo ya kwanta Kan gadon yana kallon sama. Tunani Kala Kala ne a ransa Wai Shine yayi hauka? Lallaima ɗan Adam ba a bakin komai yake ba, kuma Idan kana Duniya bazaka daina haɗuwa da jarabawoyin ubangiji ba, Adaren Ranar Shadow bai samu ya runtsa ba yadda yaga Rana haka yaga dare, tunini kawai yake akan halaccin Al ummar wannan gidan musamman ma Shabanaah. Saidaga baya ya Tashi yashiga toilet ya ɗauro alwala yazo yafara Sallah saboda dare ya Fara rabawa.



Ɓangare Shabana ita ma Bacci ya gagari idonta tunani Kawai take da Nazarin rayuwar Ahanaf, Kai tsaye ba Wanda zai ce ga magaucinsa saboda a duk cikin labarin nasa ba Wanda yake nuna ƙiyayyar sa akansa.
Tashi tayi ta ɗauko pepper da ke ɗauke da Zanensa da wacce take ɗauke da Zanen Norr, kallon Norr tayi sosai ajiyar zuciya tayi a fili tace Allah ne masani akan wannan lamarin naku.
Ko ta yadda da Auren ƙanen nasa? Idan kuwa ta yadda tabbas tazama maha'inciya ta ƙarshe.
Ƙirjinta ne taji ya harba da ƙarfi sakamakon wani tunani da yazo mata yanzu.
Anya wannan Abun da yafaru ba Ahanaf ɗin bane mai matsala?
Idan ba haka ba mai zaisa mahaifinsa ya yanke masa wannan mummunan hukuncin?
Anya ba yaudarar Kanta tayi ba da ta yarda ta auri wannan mutumen?
Yanzu ya zatayi menene mafita?
Ɗayar zuciyarta tace mafita ɗaya ce ya SAKEKI Shabana tunda dama ba sonshi kike ba.
Idan har shine mai matsalar me yasa aka masa Asiri to?
Nan take Shabana taji Kanta ya Fara ciwo ta kwashe pepper ɗin ta mayar a cikin jakarsa da alƙawarin Idan Allah ya tashemu lafiya zata bashi kayansa.

Toilet Tashiga ta ɗauro alwala ta fito ta tada Sallah.
Ta roƙi ubangiji ya kawo ɗauki a cikin lamarinta ya zaɓa mata abunda yafi zama Alkhairi.

Da safe misalin ƙarfe 10am Ammi ce tashigo ɗakin Shabana ta tayar da ita.
Tashi tayi tana mutsuke idanunta tace "Ammi ina kwana"
Hararar ta Ammi tayi Sannan tace "eh Ai dole kice Ina kwana tinda sai yanzu Allah yayi kika tashi" turu baki gaba tayi tace "tun ɗazu fa natashi Ammi kawai dai naga ba abunda zanyi ne yasa na koma Bacci"
"Ba Wannan na tambayeki ba Dan Allah tashi kije ki kaima bawan Allah Abinci yasamu ya Karya tun ɗazu nake jiran fitowarki Amma kin kama gado kinyi kwanciyar ki" tasan Sarai Ahanaf Ammi take nufi Amma tsabar tsokana irin tata sai tace "Ammi wa Kenan?"
Cikin ƙufula Ammi tace "Alh Usman"
Dariya Shabana tayi tace "haba Ammi zagi da Uwar safiyar nan"
Ammi ganin Shabana zata ɓata mata lokaci yasa ta nufi hanyar fita daga ɗakin tana faɗin "Ke kaɗai nake jira Idan kin iya ki kai 12 kafin ki fito"
Dariya Shabana tayi Sannan tashiga toilet.

Saida tagama Shirinta tsab sannan ta fito tana zuwa zata zauna kusa da Ammi tare da gaida Dady.
Dakatar da ita Ammi tayi tare da cewa wai baza kije ki kai masa breakfast ɗin nan bane Ko Yaya?
Oh Allah nagode maka, Nima da kaina ban Karya ba fa Ammi.
"Wannan kuma ruwanki ke da Idan kikaga dama Sai kikai 1 baki Karya ba, Ai ba za'a haɗa ki da Shi ba."

Murmushi Dady yayi yace "daughter je kikai masa ki dawo Yau ba inda zanje Ina gida fira zamu sha tare da Auta ta"
Murmushi Shabana tayi tace "yawwa my Dady na gode sosai"
Kallon Ammi tayi tana Dariya Ammi tace "kin dariye ubanki" ba iya Shabana ba hatta Dady Saida yayi dariya Dan ya Lura Ammi ta fara ƙufula da lamarin Autar tata.

Dady Yace "Idan kinje kice masa Idan ya gama break ɗin yazo parlour"

"Okay insha Allah Dady"


Breakfast ɗin ta ɗauka ta nufi hanyar ɗakin su Abdul.

Ta Kwankwasa ƙofar yafi sau ukku Amma Shiru ba abuɗe ba, ɗan gajeren tsaki tayi tare da juyawa zata koma taji an buɗe ƙofar.

"Sorry Bacci nake banji ba" Shadow ya faɗa yana koma wa cikin ɗakin.

Bayansa tabi batare da tayi Magana ba, Kan table ta ɗora Abinci, tace "Dady Yace Idan kagama yana nemanka a parlour"

"Ina kwana kin Tashi lafiya?" Shadow ya faɗa yana ƙoƙarin zama kan kujera.

Wata irin kunya Shabana taji sunkuyar da Kanta tayi ƙasa ta kasa ce masa ƙala.

Ganin tayi Shiru bata ce masa ƙala ba yashi ce mata "zanzo insha Allah."

Juyawa tayi tafita daga ɗakin, da Ido ya rakata har ta ɓace ma ganinsa.













______________ Wannan zaman ba munyi shi bane dan cin zafarafin kowa ba munyi shi ne dan magance matsalar da take ƙoƙarin tun Karo mu.

Mukhatar da Muhammad Tambaya ɗaya zanyi muku amsa kawai nake son ku bani ba Wani surutu ba.

Gabaki ɗaya parlourn yayi tsitt kowa jira yake yaji Abunda zai fito daga bakin Abbu.


Saida ya Kalli kowa da yake ɗakin sannan ya mayar da kallonsa Kan Abba da Dadyn su Norr da suke Zaune a kujera ɗaya yace Menene dalilin da yasa kuka ɗaura Auren Norr da Al kaseem Maimakon da Ahanaf?


Ruɗu firgici kiɗima tashin hankali gabaki ɗaya sun bayyana a fuskar Abba.

Cikin rawar murya yace "yaushe mukayi haka Yaya?"

"Tambayar Ku nayi ba cewa nayi ku Maida min da tambaya ba amsa nake So" Abbu ya faɗa Yana ƙara murtuƙe fuska kamar Bai taɓa dariya ba.


Dadyn su Norr ya shiga cikin matsancin ruɗani Shima, saboda sai yanzu yake tabbar da Yassar da Norr gaskiya Kenan suka faɗa ya ƙarya tasu a ɗazu?

Ita kuwa Norr dalilin da yasa tayi maganar Shine tana So taji gaskiyar Abunda ya faru da ita bayan an ɗaura Aurenta da Al ƙaseem.

Yassar da Meenal suka sanar da ita Abunda ya faru a lokacin tas.
Iya firgici Norr ta firgita Kuma ba halin ta Musa musu saboda Abunda tagani ɗazu, yanzu kuma ga Abun Yana ƙara tabbar da kansa a gabanta.


Haka ɓangaren ƙaseem ji yake kamar zai mutu tsabar raɗaɗin da yake Ji a zuciyar sa, ganin abunda ke faruwa yake kamar a mafarki ko drama.




Abba ya kasa Magana saboda Idan ma yace zaiyi Magana baisan Abunda zaice ba.

Dadyn Norr yace "Yaya kayi haƙuri bawai Mun Raina ka bane Amma dan Allah ka ƙara yi mana fashin baƙi a Kan wannan sarƙaƙƙen lamarin da ya sarƙe mana kwakwalwa."


Numfashi Abbu yaja da ma yayi tunanin haka.
A hankali ya warware musu komai yadda zasu fahimta.
Harda maganar ɓatan Ahanaf da kuma fafutukar da sukayi gurin nemansa.


Innalillahi wa'inna Ilaihi Raju'un Hasbunallahu wani'imal Wakil Abba da Dady suka faɗa cikin kiɗima da tashin hankali.

Hawaye fall Idanun Abba yace "Dan Allah Yaya ka ƙaryata wannan lamarin kagaya min cewa wasa kake bada gaske kake ba"

Abbu yace "ba wani ɓoye ɓoye Muhammad wannan maganar da Kaji shine gaskiyar Abunda kuka aikata"

"Yaya taya haka ta faru?" Abba ya faɗa cikin kaushin murya.

"Ku muke saurare ku faɗa mana taya haka ɗin tafaru?"

Dadyn Norr yace "Wallahi Yaya banida masaniya akan haka nidai a iya sanina har Ranar da za'a ɗaura Auren nasan auren Norr da Ahanaf za'a ɗaura bansan Abunda ya faru ba daga baya ya sauya wannan lamarin ya zama yadda kuke bada labari a yanzu" Kai Abbu ya gyaɗa yace Ni dama ba wai Na ƙaryataku bane Amma lamarin ne da ɗaure kai.
Dukanku bakusan dalilin da yasa ku kayi haka ba.
Wannan haƙin ba a kanku ba, zamuci gaba da addu'a insha Allah kumi zaizo da sauƙi.

Sannan Maganar Auren ƙaseem da Norr aure ne kamar kowannen, tunda iyaye ne suka ɗaura Auren kuma suka shaida dan haka bazamu yanke hukunci Akai ba yanzu, har sai mun sake Zama.


Da sauri Norr da kaseem suka Kalli Abbu, baki na rawa kaseem yace "a'a Abbu Dan Allah karka Mun haka, kaifa ka hanani rubuta mata takardar saki tun ɗazu kace na Bari Idan anyi wannan Zaman sai na saketa"


"Ƙaseem Na canja shawara, Norr tana nan a matsayin matarka har Sai munga matakin da yakamata mu ɗauka tukkunna"

Da ƙarfi Norr ta Runtse idanunta Allah kaɗai yasan mai takeji Akan wannan lamarin. wannan wace kalar jarabawa ce? Tabbas wannan jarabawar tazo mata da matuƙar ƙarfi da Muni. Ya Shadow ta faɗa cikin matsancin kuka, duk Wanda yake parlourn hankalinsa ya Koma Kanta saboda ganin Kukan da take na fitar hankali.

Mommy ta watsa mata harara tace "Dan Allah Malama ki rufa mana baki ke kika fi kowa anan ne? ko kuwa kinfimu son Ahanaf ɗin ne? Lokacin da aka ɗaura Aurenki da ƙaseem me yasa kika karɓa bayan kinsan baki So?
Ai Ina ce a Ranar ba kalar rashin kunyar da ba kimin ba Akan cewa da nayi ba zakii tare a gidan ba muddin ba a Maida Auren Kan Ahanaf ba"

"Ki bita a hankali mana Dan Allah, ki Barta da ɗaya mana, wannan Idan ba'a Tausaya mata ba to fa bai kamata a muzguna mata ba" cewar Hajiya Mama tana kallon Norr cikin tausayawa.

Ajiyar zuciya Ayiya tayi Sannan tace "kema dai Kya faɗa Aunty Ai a halin yanzu tausawa shine abunda Norr take buƙata saboda Allah ne kaɗai masani Akan Abunda take Ji a zuciyarta.
Kowa yasan kalar son da sukeyi wa juna ita da Ahanaf, Amma lokaci ɗaya tace ta zaɓi ƙanensa ƙaseem a kansa kuma kunsan wannan lamari ne da yakamata a Tausaya mata Akai.


Abba ya kasa cewa ƙala kuma ya lura tabbas wannan Abun ya faru da gaske Kenan.
Yanzu Ina zaiga Ahanaf?
A wane Hali yake?
Da gaskene ya Samu taɓuwar hankali sanadiyar wannan lamarin?
Abba Ya tambayi kansa

Iska mai zaifi ya furzar Sanna a zahiri yace Wallahi Yaya muddin gaskiyar wannan lamarin ta bayyana Saina....... Dakatar dashi Abbu yayi yace "ba Alwashi bane gabanka tashin hankalinka zaka duba. bana so kayi kowane furuci anan. Kariƙe niyarka acikin ranka, ba'a faɗar Alwashi haka kawai saboda Abunda ya kanje ya dawo.
Dole tasa Abba yayi Shiru ya fasa faɗar Abunda zai faɗa, Amma yayi mamaki sosai da Yayan nasa ya hana Shi ƙarasa zancen sa.


Haka taron ya Tashi kowa da kalar Abunda yake tunani A ransa. Zukatansu duka Babu daɗi.



Abba da Abbu ne zaune a Mota Suna Magana, Abba Sai faman raira kuka yake kamar wata mace.
Yace nakasa Yaya nakasa nakasa riƙe Amanar ɗana Ahanaf. A rayuwarsa na Zama mugum Mutum nakasa zama uba Nagari a rayuwar Ahanaf.
Ya zama dole na nemosa na nema masa lafiya sannan na roƙi gafararsa.
Idan har ba haka nayi ba to wallhi ko mutuwa nayi Ruhina bazai Samu salama ba Yaya.
Abba ya faɗa yana sakin wani kuka mai cin rai Wanda duk rashin Imani Mutum Idan ya Gani dole ya tausayawa Masa.
Share masa hawaye Abbu yayi tare da cewa a'a Muhammad karka zama Mutum Mai rauni da kasa ɗaukar ƙaddara.
A sanina Muhammad Imran jarumi ne Mai dan ne damuwarsa yayi Kamar baya cikin wata matsala.
A yanzu So nake ka ƙara bayyana duk wata Jarumtarka.
Nasan Abunda matuƙa wahala Muhammad Amma inada kyakywan yaƙinin cewa zaka iya.
Akan Batun neman Ahanaf bana so ka dinga tattauna wannan maganar da kowa face ni, Ko D.p.o Abdul naseer, ko kuma abokan Ahanaf ɗin wato Haidar da Kamal. Saboda sun tsaya tsayin daka Akan rayuwar Ahanaf, sun nuna su abokanai ne Nagari masu tsayawa abota a cikin kowane irin Hali.
Da ace abotar da suke da Ahanaf ba Dan Allah sukeyi ba da bazasu tsaya Masa kai da fata ba saboda abubuwan da kayi musu a wannan lokacin. A saboda haka yana da kyau ka kula kasan Abunda yakamata kayi.


Abba ya fahimci Akwai Wanda Abbu yake zargi Akan wannan case ɗin Amma kuma yaƙi ya bayyana masa. Koma Dai menene zai bi shi a yadda yakeso saboda a halin yanzu ba abunda yake da muradin Gani Sama da Ahanaf.
Allah masani ne duk Duniya Bayan Yayansa ba Wanda yake so Sama da Ahanaf. A cikin jininsa yake Jin ƙaunarsa, Ahanaf na musamman ne agurin sa da yake tuna masa da abubuwa da dama masu matuƙar daɗi da kuma ƙunci a tawani ɓangare.













_______________ Misalin ƙarfe 3pm Zaune suke Suna Hira Dady, Shadow da kuma ya Maleek, Sai dariya suke cikin nishaɗi saboda Maleek ne yake basu labarin wani tshoho mai darun tsiya.

Ya Suhail ne yayi sallama ya shigo zama yayi tare da cewa Wash Wallahi nagaji sosai Dady.
Murmushi Dady yayi tare da cewa "Allah yayi maka Albarka Yaron Ammi"
"Ameen ya Allah my Dady" ya Suhail ya faɗa yana murmushi.

Mai gadi ne yayi sallama tare da shigowa da kaya niƙi niƙi a tsakiyar parlourn yafara diresu tare da gaida jama'ar parlourn amsawa sukayi tare da yi masa Sannu da aiki.

Suhail ya Kalli Dady yace "ga kayan nan Dady saidai ban kai ɗunki ba kamar yadda kabani umarni kawai na yanke shawarar na dawo gida sai muje tare dashi gurin mai ɗinkina ya ganshi, Sannan Sai a masa kalar ɗinki da yake So" murmushi Dady yayi tare da cewa "eh Lallai kayi tunani mai kyau Suhail. Jawo kayan sai a cire nakaiwa ɗinkin Akai masa sauran ɗaki"

Manyan Shaddodi da Yadidika masu tsada ne Suhail ya fitar Daga cikin manyan jakunku nan da mai Gadi ya shigo dasu.
Dady ya kalli Shadow yace "Ahanaf ga wannan kayi anfani dasu kafin muga Abunda ya dace ayi.
Ka duba Idan akwai abunda kake buƙata Bayan wannan saikayi Magana a siyo maka" cike da mamaki Shadow yake kallon wannan tulin kayan zaiyi Magana Dady ya dakatar dashi yace "a'a Ahanaf na faɗa maka bana son godiya Idan har ka ɗaukeni a matsayin mahaifinka.

Ahanaf yace "Toh Zan iya Yi maka Abunda nakewa mahaifina a duk lokacin da Yamin kyuata?"
Cikin murmushi Dady Yace "yes"
Tashi Ahanaf yayi yaje gaban Dady tare da rungume Shi yace "Allah ya ƙara tsawon Rai da Nisan kwana yabiya maka buƙatunka na Alkhairi yasa kagama da Duniya lafiya" Dady, ya Maleek da ya Suhail gabaki ɗayansu da ameen ya Allah suka amsa. Kwata² Ahanaf ya Manta da Dady Surukin sa ne.
Ai Kuwa yana tunuwa da ba jikin Abbansa yake ba nan take ya janye jikinsa yana Sosa kansa alamar yaji kunya.
Murmushi Dady yayi tare da cewa Bana son Wannan kunyar Ahanaf, karka sa Kumi a ranka Bayan ni mahaifinka ne kaji?
Kai Ahanaf ya gyaɗa tare da cewa "in sha Allah Dady"
"Yawwa yanzu tashi ka kai kayan nan ɗaki Sai kazo kuje gurin mai ɗunkin kaida Suhail" tashi yayi ya fara kwasar kayan Suhail ya Taya Shi har suka gama kwashe kayan tas Sannan suka nufi Mota.

Zasu Shiga Motar Kenan suka ji muryar Shabana tana Kiran ya Suhail ya Suhail.
Tsayawa yayi tun kafin ta ƙaraso ya fara kwaɗa mata Uwar harara.
Tana zuwa ta sunkuyar da Kanta ƙasa.
Ya Suhail yace "Malama ya akayi kin kirani kuma kinyi shuru?"
"Ya Suhail dan Allah saƙo nake da Idan zaka dawo"
Harara ya sake zuba mata yace "nayi miki kama da wanda zaki aika ne?"
Kai ta girgiza alamar a'a
Kwafa yayi tare da cewa "wai ke Yarinyar na me yasa kika raina ni ne? ga mijinki a tsaye Amma sai kidinga sakani aiki kamar wani Yaron ki"
"Mijinki?" Shabana ta nanata tana kallon ya Suhail...........✍️✍️✍️







Nabeela Binji ce💃💃💃







More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏.




♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MO



TIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM




Page

3️⃣ 1️⃣









________________ "Eh mijinki mana ba gashi nan a tsaye ba?" turu baki tayi tare da cewa "gurin Aunty Fatee ne zaka karɓo min saƙon fa"
"Tohm Madam ba gida zanje ba fita zamuyi kije ki karɓo kayanki da kanki, Oh nama tina kijira zuwa gobe zasu zo wuni gidan nan tare da matar ya Maleek Aunty Aisha" murmushi tayi cikin Jin daɗi tace "Yes Allah ya kai muna Rai" ya Suhail yace "watau daɗi kikaji abokan gulmarki zasu zo ko? Tohm bari kiji tun yanzu na faɗa miki Idan har kukayi gulmata Allah Yana ganinku" zare Ido tayi kamar zasu faɗo ƙasa tace "kai Ya Suhail yanzu Dan Allah dan kaji sau ɗaya muna maganar ka shikenan kuma bamu da aiki sai gulmarka?" Nidai ba dogon turanci na ne meki ba kawai nace karkuyi gulmata" yana gama faɗar haka ya kalli Shadow dake ta zuba murmushin dramar su yace "Shiga mu tafi Ahanaf" Mota suka Shiga Suhail yaja suka bar gidan.
Juyawa tayi ta koma cikin gida tana ta mita ita kaɗai wai a dole ya Suhail yaci mata mutunci tunda yace tana gulma kuma a gaban Ahanaf, kwafa tayi Sannan tace ai tunda kace haka Wallahi sai munyi gulmar taka kayi duk abunda zakayi.



Zaune suke a dining area suna cin Abincin dare ba mai Magana a cikinsu.

Dady ne yafara tashi, Shabana tace "wai har ka ƙoshi Dady?"
Murmushi yayi "eh alhmdllh Shabana dama ba wata yunwa nake jiba shiyasa"
Murmushi Kwai tayi batare da ta sake Magana ba.
Can ba jimawa Ammi ita ma ta tashi gyaran murya Shabana tayi irin na tsokana, ganin Ammi bata Kula taba yasa tace "Dama tunda Dady Yace ya ƙoshi ai kema nasan tashi zakiyi" murmushi Ammi tayi Sannan tace "ko zaki hana ne?"
"Aa Kam rufamin Asiri"
"Allah ya shiryaki Ammi ta faɗa tana barin gurin"
Duk Abunda suke Ahanaf yana jinsu kuma yana mamakin Shaƙuwar da take tsakaninsu da iyayensu kamar ka kanninsu.

Kallonta yayi yace "kin Raina Ammi ko?"
Murmushi tayi Sannan tace "ba raini ta nayi ba Kawai dai inajin daɗin tsokanar ta ne" murmushi yayi batare da yasake Magana ba.

Bayan sun kammala cin Abincin Shabana ta gyara zamanta tana Danna wayar hannunta.
Kallonta yayi yace "Dan Allah Idan ba damuwa ina neman wata alfarma" "Alfarma?" Shabana ta tambaya tana kallonsa.
Kai ya gyaɗa mata alamar eh.
"Okay Ina jinka"
"Ina so ki haɗa ni da wannan Dr ɗin na masa godiya"
Murmushi Shabana tayi Dan Sarai tasan Dr Fahad yake nufi, tace masa "ai baya Nan yaje Jos gurin wani aiki Amma ɗazu da mukayi waya yace cikin satin nan zai dawo" Ajiyar zuciya Shadow yayi tare da cewa "Allah ya dawo dashi lafiya"
Ameen ameen.
Shiru sukayi kamar wasu kurame.

Wayar Shabana ce tafara ƙara ɗagawa tayi tare da karawa a kunnenta tace "mara kirki Sai yanzu kika ga damar kirana?"
Dariya Hafeeza tayi Sannan tace "ke bafa a damun Amare shiyasa kika ga na ɗaga miki ƙafa" tsaki Shabana tayi tace kefa matsala ta dake wani Zubin rashin kirki, Ina amaren suke?"
"Gakunan keda Ahanaf"
"Hafeeza Bana son haka plxxx"
Murmushi Hafeeza tayi sannan tace "Allah ya huci zuciyar Amarya Na daina bazan ƙara ba" banza Shabana tayi da ita kamar bataji mai tace ba.
Hafeeza tace "gobe zanzo insha Allah"
Cikin Jin daɗi Shabana tace "da gaske kike?"
"Sosai Kuwa"
"Yawwa Allah ya kawoki lafiya Goty" ameen
Hafeeza tace "Ina Ahanaf ɗin yake?"
Saida taɗan Kalli gurinda yake Sannan tace "gashi nan zaune"
Wata irin dariyar shaƙiyanci Hafeeza tafara yi har tana shiɗewa tsabar dariya.
Ita Shabana mamaki ma Abun ya bata da kuma tunanin mai Hafeeza takewa Dariya haka?
Dakatar da dariyar tayi sannan tace "Allah yasa dai bake kika tafi gurinsa ba ki bamu kunya Sulty?"
Sai a lokacin Shabana ta gane dalilin dariyar Hafeeza, cikin Jin haushi Shabana tace "ina ruwanki ko zuwan nayi?"
Eh gaskiya ba ruwana tsakanin miji da mata nidai kawai bana son zubar da ajine Hafeeza ta faɗa tana Dariya.
Iya ƙufula Shabana ta ta ƙufulu da Hafeeza hakan yasa ta katse Kiran batare da ta sake Magana ba.

Kallon Shadow tayi taga idanunsa na Kanta wani mugun haushi taji ya ƙara kamata, tashi tayi tsaye ba tare da ta sake Kallon gurinda yake ba tace "Saida safe"

Shadow yace "maganar da kika ce zamuyi fa?"
"Sai da safe zamuyi maganar, yanzu dai kajirani Zan kawo maka jakar ka"

"Jaka?" Shadow ya tambayeta

Ba tare da ta bashi amsa ba ta nufi hanyar ɗakinta.

Bayan mintina kaɗan Sai Gata ta dawo ɗauke da jakar a hannunta.
Cike da mamaki Shadow yake kallon jakar.

A gabansa ta ajeta tace "tun lokacin da na bigeka da Mota take gurina dama Ina So Idan ka dawo hankalinka sai na Baka, Amma kayi haƙuri Cox na buɗa maka sirri Wanda ta dalilin haka nasan sunanka.

Tana gama faɗar haka ta juya ta tafi abunta batare da tajira cewar sa ba.

Jakar ya jawo a hankali kamar Wanda yake Jin tsoron Wani Abu ya Fara buɗe ta. Saida yagama bincike ta Tass bawani Abu aciki Bayan kayan drawing ɗinsa da kuma two peppers, ɗayar ya buɗe drawing ɗinsa ne raɗau Akan pepper

Please Login or Register in order to submit comment