Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kiraki nayi miki ƙarin bayani" wata kunya Shabana taji dan yanzu tasan akan kayanda haj Mama take mgana, cikin jin kunya tace "Nagode Mama Allah yaƙara nisan kwana" murmushi haj Mama tayi tace "bakumi ƴata shiga Mota kuje Allah ya kaiku lafiya" Mota tashiga sukayi sallama da Mutanen gidan Kamar karsu rabu haka sukeji.
Lokacin da Motar ta fara Tafiya, Shadow Ji yayi kamar an tafi masa da wani ɓangare na jikinsa............✍️✍️✍️















Nabeela Binji ce💃💃💃







More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏.


♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM



PAGE

4️⃣ 8️⃣

















_______________ Haka ya koma ɗaki kamar wanda bashida lafiya, wayarsa ya ɗauka ya rubuta mata tex na fatan Alkhairi, tare da fatan Allah ya sauke su Lafiya.

Ita ma Shabana haka taji masifar kewar Mijinta kamar me, Idonta ta lumshe tana tunanin abubuwan da suka faru a dan zaman nan da sukayi da Ahanaf, idonta ta buɗe jin saƙo ya Shigo wayarta Sunan da ta sakawa Shadow tagani murmushi tayi tafara karantawa.
Tana gama karantawa ta rubuta masa reply.




Bayan sati ɗaya da tafiyar su Shabana, Shadow ya Shiga matsanancin kewarta fiye da tunani, duk da baya ɗaukan lokaci bai kirata ba, ko da yaushe suna chat wani lokacin ya takurata dole sai sunyi video call, Amma ji yake gabaki ɗaya hakan bai masa ba.



Kwance yake a cikin ɗakinsa yana tunanin rayuwa, da tunanin Abunda Ayiya ta aikata, menene dalilinta, menene ribarta? Tashi yayi ya ɗauko pic ɗinsu inda suke su ukku Ayiya ce a tsaka kaseem da Ahanaf suna gefenta sun sakata tsaka, murmushi ne ɗauke a fuskokin su. Cikin sanyi murya yace "dama ace kin cigaba da zama boyayyiyar maƙiyiya agurina Ayiya, zuciya ta ta kasa samun salama akanki, kullum tunani nake a wane hali kike, gashi su Abbu sunyi min shamaki dake" wasu zafaffan hawaye yaji suna bin kumatunta da sauri ya gogesu tare da tashi tsaye yafita daga part ɗin.

Kai tsaye ɓangaren Ayiya ya nufa yana zuba sauri kamar zai kife, yana zuwa yatura ƙofar tare da danna kansa ciki ba wani dar a ransa.
Ƙaseem wanda yanzu nan ya shigo gidan gaida iyayensu, ya hango Shadow yayi hanyar part ɗin Ayiya, da sauri yafito daga cikin Motar tare da mara masa baya, wanda shima Rabonsa da part din tun lokacin da abun nan ya faru.
Koda yashiga Shadow baya parlour, direct bedroom ɗinta ya nufa dan yayi tunanin yana can, koda ya Shiga kuwa Shadow zaune kan gadon Ayiya, ya dafe kansa da hannayensa.
Motsin Mutum yaji da sauri ya goge hawayen idonsa, ya ɗago Yana kallon ƙaseem wanda ya tsaya a ƙofa kamar an dasashi.
Tafiya ƙaseem ya farayi har yaƙarasa gaban Shadow, zubewa ƙasa yayi akan gwiwoyinsa hawaye nabin fuskarsa, cikin tsantsar ƙunar zuciya yace "Yaya Ayiya tayi kuskure, ta biyewa ruɗanin zuciya ya kaita ga mummunan rayuwa, yanzu wa gari ya waya? Yaya ka duba duk ƙiyayyar da Ayiya take maka ta zama ta banza Saboda muguwar zuciya irin...... Hannu Shadow yasa ya rufe masa baki tare da jansa jikinsa ya rungume, yana bubbuga bayansa a hankali, sun ɗauki lokaci a haka kafin Shadow ya janyesa daga jikinsa.
Kallonsa yayi cikin muryar rarrashi yace "karka furta mummunan kalma akanta kaseem ita ma haifiyace, tanada haƙƙi akan ka fiye da yadda kake tunani, koda tafi haka lalacewa kuwa, kayi haƙuri Kaji" da kyar Shadow ya samu kan kaseem yaja hannunsa suka fito daga part ɗin, yana tambayarsa ya jikin Norr ɗin cikin sanyi murya yace "taji sauƙi sosai" murmushi Shadow yayi yace "Allah yaƙara Afuwa, toh yanzu kam ba zama zakayi ba, kamata yayi ka koma gida gurin ƴar Mutane, ka Barta ita kaɗai kuma gata bata jin daɗi" murmushin ƙarfin hali yayi yace "Tohm yaya in sha Allah" Shadow yace "kodai nazo na kaika ne?" Girgiza kai yayi yace "zan iya nagode sosai Ya Anfu"
Dariya sukayi dukansu saboda sun tuna da ƙuruciya ƙaseem bai iya Sunan Ahanaf ba saidai yace ya Anfu.

Sallama sukayi ƙaseem yashiga Mota ya tafi, yana cikin tafiya yaji wayarsa ta fara ringing, my Norr yagani akan screen ɗin.
Murmushi yayi tare da ɗaukar wayar bayan sun gaisa tace "Abu baby kana Ina? naga har yanzu baka dawo gida ba" yace "Ina hanya Norr naje gaidasu Abba ne" murmushi tayi tace "ka kyauta sosai, dan Allah Abu baby kazo mun da Ice cream" yace "bakinki ne ice cream ɗin ai, ni ba wani Ice cream da zan zo miki dashi, bakida wani Abun sha sai kayan sanyi, salon kisa babyna yazo da wani rashin lafiya" ɓata fuska tayi cikin muryar shagwaɓa tace "Dan Allah kayi haƙuri wallahi wani zafi nakeji sosai, idan ban sha ba Akwai matsala" murmushi yayi yace "Allah ya rabaki da matsala Norr zan siyo miki but kwara ɗaya tak zan siyo" ameen ya Allah nagode sosai Allah ya kawoka lafiya" Ameen ya faɗa yana karya Motar sa yanufi Abdullahi Fodiyo Mall.



Duk Abunda ya faru ɗazu akan idon Abbu, har lokacin da ƙaseem yashiga Mota ya fita daga gidan. Yaji masifar Tausayin Yaran fiye da tunani, Amma lamarin nasune da wahala sosai.

Koda Shadow ya koma ɗaki ya tarar da Miss call's daga Beloved wife, murmushi yayi tare da ɗaukar wayar ya kirata.
Saida tajima tana ringing sannan ta ɗauka, ajiyar zuciya ya sauke har saida taji.
Cikin shagwaɓa tace "ina ka shiga ne loveline?" Kwanciya yayi kan bed tare da lumshe Idunsa, a hankali yace "Yau muryarki tafi ta kullum daɗi" murmushi tayi tace "Nagode" yace "Anya bazan zo Katsina gobe ba kuwa?" Murmushi tayi tace "laaaaah gobe aikinka fa loveline?" Murmushi yayi yace "uhm bazaki fahimta ba wife, idanuna suna masifar kewar kyakywar fuskarki, hancina yana kewar daddaɗan kamshin turarenki, Jikina yana kewar lallusar fatarki, Ina kewar sweet lips ɗinki" dariya Shabana tayi tace "duk kai kaɗai? lallaikam kayi kewa da yawa" ta faɗa cikin tsokana.
Kwafa yayi yace "dariya ma na baki ko? zaki daina dariyar ne idan na kamaki Allah" uhmm kawai tace.
Ajiyar zuciya yayi yace "wallahi ni gani nake kamar masu aikin ginin basa sauri, nifa na matsosu su kammala gidan, Idan sun kammala ko lokacin da akasa baiyi ba zaki tare" Shabana tace "kai loveline ai kuwa namaga sunyi ƙoƙari, videon da ka turumin naga aikin yana tafiya gaskiya" dama ai nasan haka zakice, saboda bakisan yadda nakeji araina ba" murmushi tayi tace "toh Allah yasa su kammala aikin da wuri, Amma Nikam sai lokacin da aka ɗibar mana zan tare" yace "tsabar bakida Tausayi ko?" Dariya tayi tace "tausayin Kenan" sun ɗauki tsawon lokaci suna waya, dama haka suke kullum.




Kwanki sunja sosai akwana a Tashi har Shadow ya cika wata ɗaya rabonsa da Shabana, Idan yace zaizo, sai tayi masa dabara ta hana shi zuwa, saboda yadda yake mata rashin kunya a waya tasan muddin yazo sai tayi fama dashi sosai.


Zaune yake a parlourn Haj Mama yana danna wayarsa, gani yayi an fara sanarwar mata Babbar mota ta take wasu mahaukata goda biyu yayinda suka zo sallaka Babban titi, mai Motar yayi iya ƙoƙarin kauce musu Amma hakan ya faskara, a Saboda haka ake neman dangin waƴan nan mahaukata da idan Allah yasa sun gani suzo su ɗauki gawarwakin ƴan uwansu.
Tv ya ƙure da Ido ba ko kyabtawa fuskar Ayiya da mommyn Norr aka nuna wace gabaki ɗaya suka ɓaci da Jini, gasu cikin wani Yanayi na datti kayan jikinsu ba kyaun gani.
Wani uban ihu Shadow ya kurma Wanda duk gidan saida ya amsa da sauri Haj Mama da Abbu suka fita cikin matsanancin tashin hankali suna tambayarsa lafiya?
Kasa Magana yayi sai TV da yake nuna musu, gabaki ɗaya jikinsa rawa yake.
Innalillahi wa'inna Ilaihi Raju'un Abbu da Haj Mama suka dinga nanatawa cikin tashin hankali.
Tashin hankalin da suka shiga baki yayi kaɗan ya furta, Suna cikin wannan halin ƙaseem yakira wayar Shadow, kallon wayar yake amma yakasa ɗagawa, saboda yasan a halin yanzu ƙaseem yaga duk Abunda yake faruwa Idan ya ɗauka mai zai ce masa ta Ina zai fara? Saida yaƙara kira Abbu yace "kaɗauki wayar mana Ahanaf" bisa dole ya kai hannunsa da ke rawa ya ɗauki wayar tare da karawa a kunne.
Innalillahi wa'inna Ilaihi Raju'un Shadow yafaɗa cikin masifar tashin hankali, cikin rudewa yace "kuna ina yanzu?" Ɗan Jim yayi kaffin yace "tohm Kanutsu ganinan zuwa ƙaseem" yana sauke wayar da sauri yayi hanyar fita, Abbu ya riƙeshi yace "mai yake faruwa Ahanaf ina zakaje haka? Cikin tashin hankali yace "Abbu Norr ce ta faɗi ta suma sakamakon ganin Abunda aka nuna yanzu a TV, ƙaseem yace tana zubar da jini sosai" Abbu yace subhanallah "tana wane hospital?" Shadow cikin zaƙuwa da son barin gurin yaje gurin ɗan uwansa yace "tana Saraki hospital" Abbu ya kalli Haj Mama yace "je ki ɗauko mayafinki kizo kuje asibitin tare, Ni kuma zanje kasuwa gurin Muhammad muje mu ɗauko gawar Shuwa" Toh Haj Mama tace tare da Shiga ɗaki ta saka hijab ta fito, Mota suka Shiga Shadow yaja da mugun gudu suka nufi Saraki hospital.
Koda suka Isa kaseem sai kai kawo yake cikin masifar tashin hankalin, yana hango su yayo kansu da sauri ya rungume Shadow, cikin wata irin murya mai cike da rauni yace "Ya Shadow Ayiya ta Mutu ita ma Norr zata Mutu ta barni, dan Allah ya Shadow ka taimakeni" matseshi yayi sosai ajikinsa yana jin wani raɗaɗi Aransa Allah yasani baya son ganin kukan kaseem ko kaɗan.
Cikin sanyin murya yace "bazata Mutu ba insha Allah ƙaseem ka nutsu ka dawo cikin hankalinka, yanzu Norr addu'arka take buƙata" jan hannunsa yayi yaje ya zaunar dashi kan kujera yana ci gaba da yi masa nasiha Akan rayuwa da kuma jarabawa.

Haj Mama taji masifar Tausayin ƙaseem, aranta tace "albasa batayi halin ruwa ba tabbas ƙaseem bai ɗauko baƙar zuciya irin ta mahaifiyarsa ba.

Likitan da yashiga duba Norr ne yafito daga ɗakin ma'aikaciyar asibiti a bayansa ɗauke da baby, da sauri suka tashi suka nufi gurin su, atare kaseem da Shadow suka tambaye Norr.
Likita yace "gadai Abunda ta haifa, tasamu baby girl" cikin zaƙuwa kaseem ya ƙara cewa "Norr ɗin fa" Dr yace "Muje office" kwalarsa ƙaseem ya riƙe, cikin hargowa yace "Ina Norrrrr...........✍️✍️✍️














Nabeela Binji ce💃💃💃







More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏.



♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM



PAGE

4️⃣ 9️⃣
















____________ Matar ka tana Raye, kuma ba abunda zai sameta da yarda Allah, dama ta jigata ne sosai sakamakon koda aka zo da ita bata cikin hankalinta, kuma tashiga tashin hankali sosai wanda sanadiyar haka ne ma na ƙuda ta taso Mata"
Sakinsa ƙaseem yayi yana sauke ajiyar zuciya.
Karɓa babyn haj Mama tayi ta kalleta tana murmushi alhmdllh ta faɗa cikin farin ciki.
Ƙaseem yace "yanzu zamu iya ganinta?" Kai Dr ya girgiza yace"yanzu tana buƙatar hutu munyi Mata allurar bacci zata ɗauki tsawon 3hours, sannan akwai drugs ɗin da zan rubuta na baka ka siyo mata" kai ƙaseem ya gyaɗa cikin gamsuwa da maganar Dr.
Shadow ya ƙarbi yarinyar hannun Haj Mama yana Murmushi a hankali yace "Amatullah rabonki ne yazama silar sauyawar abubuwa da yawa" addu'a yayi mata sosai sannan ya bawa ƙaseem ita yace "karɓe ta ni bari naje office ɗin Dr na amshi takardar maganin" karɓarta ƙaseem yayi ya kalli fuskarta, wani matsanancin Sonta yaji har cikin ransa, ranar Yau tazo masa da abubuwan da bazai manta dasu ba har Abada.
Shadow ya Kalli haj Mama yace "Mama dan Allah a kira gidansu Meenal a faɗa musu Norr ta haihu, idan ta farka zatafi jin daɗi Idan taga wani nata a kusa" Haj Mama tace "in sha Allah Ahanaf" Tafiya yayi office ɗin Dr ya ƙarbi takardar magani yafita.

Koda ya dawo daga siyen maganin Meenal tazo da mamanta da wata ƙanwar Haj Ladi. Gaidasu yayi tare da kallon Meenal da takama babyn ta rungume ajikinta ta hana kowa taɓawa.
Ruwan zam zam ya ciro daga cikin Leda ya bata tare da dabino yace "taɗan tauna ta sakawa yarinyar a baki" karɓa tayi.
Mai da kallonsa yayi kan ƙaseem yace "Dr baice wani Abu ba?" kai ƙaseem ya girgiza masa. Zaiyi Magana wayarsa ta fara ringing ɗauka yayi tare da karawa a kunne, "ya Allah yafaɗa cikin tashin hankali yace "yanzu kana ina Abbu?" Ɗan jim yayi kafin yace "Okay ganin nan zuwa yanzu in Sha Allah" Ledar maganin ya bawa Haj Mama yace "Ina zuwa" ƙaseem yace "me kuma ya faru" murmushin ƙarfin hali yayi yace "ba kumi ƙaseem ka kwantar da hankalinka yanzu zan dawo" a hankali yace "Allah ya tsare" ameen ya Allah Shadow ya faɗa.


Koda yaje gurin Abbu ya tambaye shi Abunda yake faruwa, ajiyar zuciya Abbu yayi yace "Muhammad yace bazai taɓa zuwa kan gawar Shuwa ba, kuma yayi ranstuwar kar Akaita gida" iska mai zafi Shadow ya furzar a hankali yace "bari muje da gawar gidan ƙaseem" Abbu yace "yanzu dai mufara cika takardu muyi signing mu ƙarbi gawar tukkunna.
Bayan sun kammala duk wani cike cike sun ƙarbi gawar Shuwa.
Ahanaf yaga Yassar da wani Ɗan uwar mahaifiyarsa sunzo karɓar gawar Mommyn Norr, dan Shima Alh Mukhtar cewa yayi ba hannunsa ba ƙafarsa a lamarin Haj Ladi. Anan sukayiwa juna gaisuwa, Shadow yace "kasan Norr ta haihu ai ko?" Kai Yassar ya girgiza alamar a'a yace "Amma naga miss calls ɗin Meenal inaga shine zata faɗa min" gyaɗa kai Shadow yayi yace "maybe kam, Yassar ya Kalli Shadow yace "ya Ahanaf dan Allah ka yafewa su mommy Abunda suka aikata maka, kaga ko iya nan duniya Allah ya fara cire maka haƙƙinka akansu" murmushi Shadow yayi yace "ni ban taɓa riƙe su a Raina ba Yassar, hasalima Idan kaga na shiga damuwa akan lamarin ina tunanin irin halinda suka jefa kansu a cikine, Amma ni Allah yasani na jima da yafe musu, kuma nasan Abunda ya faru ƙaddarata ne koda su ko bada su ba sai hakan ta faru, saidai kawai muce sune sanadiya, Allah yasa mudace ya kuma gafarta musu" ameen ya Allah Yassar yafaɗa yana goge hawayen idonsa dan yanajin raɗaɗin Abunda mahaifiyarsa ta aikata kawai dan wani burin duniya, wanda yanzu gashi tabar duniyar cikin mummunan Yanayi.
Sallama sukayi. Shadow yace "Abbu mubi ta asibiti mu ɗauki ƙaseem mutafi dashi ayiwa Ayiya sutura" asibitin suka bi Shadow ya ɗauki waya yakira ƙaseem yace "kafito gani waje" yana gama faɗar haka ya katse kiran.
Ba jimawa yafito, Shadow yace "shiga Mota mutafi" ambulance ɗin da take bayan Motar su Shadow ya Kalla yasan ba ko Shakka gawar Ayiya ce aciki. Batare da yace uffan ba ya shiga suka tafi, an suturta gawar Ayiya anyi mata Sallah a ƙofar gidan ƙaseem.
Ba laifi ta samu Mutane.
Bayan an binneta ne suka dawo gida, Shadow ne ya haɗawa ƙaseem kayan sawarsa a cikin trolley, yace "zai koma gida gabaki ɗaya saboda bazai zauna shikaɗai a gida ba"
Gida suka koma dukansu Bayan sun aje kayan ne Shadow yace ma ƙaseem "kazo mu koma hospital maybe Norr ta farka" haka Shadow yaƙara jan Motar suka koma Saraki hospital, ƙaseem a ransa yana ƙara jin masifar ƙaunar Ahanaf fiye da tunani, yana kuma jinjinawa kawaicinsa da manta sharrinsa.

Koda sukaje jaririyar sai faman kuka take hannu Shadow yasa ya karɓe ta, yafara jijjigata da kyar yasamu tayi shiru.

Wata Norse ce tazo tace "kune ƴan uwan Norr" ƙaseem yace "eh Lafiya dai?" Murmushi tayi tace "lafiya ƙalau, tafarka zaku iya shiga ku dubata" gabaki ɗaya ɗakin suka nufa ƙaseem ne a gaba, koda suka shiga tana zaune kan gado ta jingina bayanta da pillow.
Direct gurinta suka nufa sunayi mata Sannu, amsawa tayi a hankali kanta yana ƙasa.
Mommy Meenal ta haɗa mata tea mai kauri ta bata, karɓa tayi dan yunwa takeji sosai, kaɗan tasha sai taji ya isheta Saida aka matsa mata sannan ta shanye duka. Shadow ya bawa ƙaseem babyn yace "ka bawa mahaifiyarta ita ta shayar da ita, tun ɗazu take kukan yunwa" amsarta ƙaseem yayi. Hanyar fita Shadow yayi gabaki ɗaya suka mara masa baya.
Bayan sun fita ƙaseem ya mayarda kallonsa kan Norr cike da masifar Tausayinta yace "Sannu ya jikin naki?" Shiru tayi hawaye nabin fuskarta, ajiyar zuciya yayi tare da saka ɗaya hannunsa ya Kama nata, yace Dan Allah kiyi haƙuri Norr nasan Abunda kikeji a zuciyarki nima inajin maka mancinsa, Amma ba yadda zamuyi dole mu karɓi ƙaddarar rayuwarmu, dani dake ciwon mu iri ɗaya ne, murike juna mu rufawa kanmu asiri Norr, Wallahi nidai nayi alƙawarin zama dake kuma zan riƙe ki Amana in Sha Allah" hawayen idonta ta goge batare da tace uffan ba.
Jaririyar ta fara kuka kallonta yayi yace "karɓe ki shayar da ita, tayi ƙoƙari tun ɗazu fa ruwan zam zam da dabino kawai aka bata" kallon yarinyar tayi tanajin ƙuncin zuciyar ta ya fara sauka a hankali.
Zamanta ta gyara tare da karɓar ta ta ɗaura ta saman Cinyoyinta, a hankali ta ciro Breast ɗin tare da gyara yarinyar ta saka mata a baki, da sauri ta fara tsotsar breast ɗin, da sauri Norr ta Runtse idanunta a hankali tace washhh. Murmushi ƙaseem yayi yace Sannu, harararsa tayi batare da tace uffan ba.



Wayar Shabana yakira ringing biyu tayi Shabana ta ɗauka tare dayin sallama tunda taji muryarsa tasan sai a hankali, cikin sanyi murya tace "Lafiya kuwa loveline" ajiyar zuciya yayi yace "ina Lafiya beloved" "subhanallah me ya faru kuma" Saida yaja numfashi ya furzar sannan ya bata labarin Abunda ya faru har da haihuwar Norr.
Sosai Shabana tashiga ruɗani kuma taji tausayin Norr da ƙaseem sosai, cikin sanyi murya tace "Allah yayi musu Rahma ya gafarta musu, yakuma yafe kura kurensu" ameen ya Allah. Tace "dan Allah loveline ka turumin No ɗin ƙaseem da Norr nayi musu gaisuwa da barka" Shadow yace "banida no ɗin Norr Amma zan amsa gurin ƙaseem sai na tura miki" Okey ba matsala" Shabana tace "loveline gobe fa zamu tafi Wasagu tare da Hidaya" yace "yaushe kika sanar dani" tace laaaaah kai loveline na faɗa maka fa kace ba matsala Allah ya kaimu lokacin" yasan anyi haka kawai tsokanarta yake. Yace "nifa yawon nan ne bana so, kullum cikin fita kike yanzu kin ɓaci da yawo" murmushi tayi dan ta lura yau fitinar yakeji, cikin sanyi murya tace "nima ba da son Raina nake wannan fitar ba loveline, kawai dan Abun yazama Al'dah ne idan mace zata tafi gidan miji sai ta zaga dangi shine kawai" gajeren tsaki yayi yace "kina fita ana kalleki shine kike faɗa min wata magana daban" da kyar ta samu ta ciyo kan Ahanaf ya aje wannan maganar.
Suka ɗauko wata firar.


Duk Abunda Mutum yayi maka Mutuwa ta da bance, Abba yaji mutuwar Shuwa Aransa Amma yakasa buɗe baki yayi mata fatan Alkhairi.



Bayan sati ɗaya da haihuwar Norr, akayi Zanen Suna yarinya taci sunan mahaifiyarsu Abbu wato Fatima, sunyi mata kinaya da Amatullah.
da Ahanaf Sunan Ayiya yaso ya saka ƙaseem yace "bayanzu ba" Shadow ya tambayi dalili yace "abarshi kawai sai gaba Idan Allah ya yarda" shiyasa kawai Shadow yasaka Sunan kakarsu saboda yasan har yanzu ƙaseem fushi yake da Ayiya.

Baby Amatullah tana samun kula sosai agurin iyayenta ko kukanta ƙaseem yaji sai ya tambayi dalili.
Ita ma Norr ɗin ba Abunda ta nema ta rasa dan kullum sai ƙaseem yaje dubasu.

Har ta Kwanta taji tex ya shigo wayarta ɗauka tayi taga tex daga Shadow kamar haka:
Zuwa gare ki abin alfaharina
Tabbas akwai tazara mai nisan gaske tsakanin duhun dare da kuma wayewar gari, haka yasa na zabi haduwarmu a mafarki, dan kuwa zuciyata ba zata taba lamuntar yin nesa da ke na tsayin lokaci ba
Ki sani a cikin kundin labarina kece idan kuma babu ke tofa babu labarina.
Agurina kece Matashiya Sai ma ranar tarewa ranar ne Zaki tabbatar Na ɓoye so cikin Ido,
bazan ɓoye ba kinsani kimarki a kwaita gwargwado halacci Baya kinyi min kin kyale masu yin zuga. Luv more than anything my beloved wife, Miss you more my happiness mauuuuuhh😘😘

Murmushi tayi wani farin ciki taji ya mamaye zuciyar ta, ita ma cikin shauƙin so tayi masa reply.






Gyara Shabana take sha ciki da waje agurin danginta, hatta Hidaya da Maimoon ba abarsu a Baya ba, ita Hidaya dan mugunta take bawa Shabana wasu abubuwan, dan ba tun yanzu taci burin yimata haka ba, tanaso Shabana ta gane kurenta sosai agurin Ahanaf.
A can Wasagu ma gyara na musamman ƙanwar Ammi ta dinga mata, wani lokacin har kunya takeji Idan tanayi mata bayanin wasu abubuwan.
Sai ana saura sati ɗaya ta tare sannan tasamu zama gida.
Anan ita ma Ammi da mommyn Hafeeza suka ɗaura nasu gyaran, sannan sun bata shawarar zama gidan miji da yadda zata kula dashi, da dabarun shawo kan miji Idan yayi fushi.
Duk Wanda ya Kalli Shabana yasan Amarya ce Babu tambaya Saboda wani kyau da taƙara, fatar jikinta har shining take tsabar gyara.
Ita da Kanta tanajin sauyi sosai a jikinta.
Bawani biki da suka shirya, walima kawai za'ayi bayan sun Isa Sokoto kafin Amarya ta tare gidanta.






Shadow ya haɗawa Shabana lefe na ban mamaki saida Haj Mama ta dakatar dashi, tace "sun isa haka Ahanaf waɗan nan kayan ba inda baza akaisu a matsayin kayan lefeba" murmushi Shadow yayi yace "duk Abunda zan yima Shabana bana ganin yawansu Mama, gani nake har Abada banida abunda da zanyi mata na sakata farin ciki kamar yadda tayi min" murmushi Haj Mama tayi tace "ai nagani Ahanaf tunda ka iya zama mara kunya akanta ai ba Abunda bazakiyi dominta ba, kuma banga laifinka ba ɗan halak ne kaɗai yake saka halacci da halacci.


Yau ta kasance Assabar kuma gobe lahadi ce ranar tarewar Shabana.
Ammi ce tashigo ɗakin hannunta ɗauke da cup, tana ganin cup din taji haushi ya kamata dan tasan wannan Abun ne Ammi ta kawo mata.
Bata Ammi tayi tace "ungo shanye kibani kofin" ganin fuskar ammi ba alamar wasa yasa ta karɓi kofin ta runtse Idonta ta shanye ta bawa Ammi kofin, karɓa Ammi tayi tare da fita daga ɗakin.



Dady ya kirata ya fara yi mata nasiha mai ratsa jiki, kuka Shabana tayi sosai kamar ba gobe. Saida ya dawo rarrashi sannan tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya.

Koda ta koma ɗaki ta tarar da Miss call's ɗin Ahanaf, kasa kiransa tayi toilet ta shiga tayi wanka tana fitowa ta shafe jikinta da Humarar da Umma ta bata tace ta dinga shafawa Idan ta fito wanka.
Shiryawa tayi tare da haurawa kan gado addu'a tayi ta shafe jikinta sannan ta kwanta, Bacci take son ya ɗauketa but abun ya gagara, sai tunani take akan sabuwar rayuwar da zata fara gobe, juyi kawai take tana jin zuciyarta tayi mata nauyi sosai na kewar gida da zatayi.
Kiran Ahanaf ne yaƙara shigowa saida ta kusa katsewa sannan ta ɗauka, sallama yayi a hankali ta amsa tare da gaidashi, amsawa yayi cikin farin ciki, yace "kina lafiya?" Alhmdllh ta faɗa a taƙaice. murmushi Shadow yayi cikin tsokana yace "kodai fargaba ce?" Sarai tasan inda ya nufa Amma sai tace "fargabar me?" Murmushi Shadow yayi yace "Idan Allah ya kaimu gobe war haka zanyi miki bayani yadda zaki fahimta" Shiru tayi masa tanajin kamar ta katse Kiran ta huta.
Shadow ne ƙarfin firar, ita eh a'a ne kawai nata, ganin tazamar masa kamar wata bakuwa yasa, yayi Mata Saida safe ya katse Kiran..........✍️✍️✍️















Nabeela Binji ce💃💃💃







More comment
More taping 😉😉





Share Fisabilillah 🙏.


♣️DUHUN INUWA♣️




TAPING......📲📲




STORY

AND

WRITING✍️✍️✍️

BY

NABEELAH SHEHU BINJI




PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM



PAGE

5️⃣ 0️⃣

















_______________ koda ta tashi da safe ba kwari ajikinta, Saida Ammi ta matsa mata tayi breakfast, sai shirin kai Amarya ake ita kuwa tana ƙarshen gado ta dunkunkune cikin blanket, Hafeeza ce ta hau kan gadon tare da Jan blanket ɗin tace "tashi makirar yarinya bawani Ƙaryar ciwon da zaki mana, yau ɗakin Ahanaf zaki kwana yayi ta jinya" tashi

Please Login or Register in order to submit comment