Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce "Zahrar nan wacce Baba ya shigo da ita kwananakin baya ya ce 'yar gidan mai daukar karatu ce a kofar gida. Har na ari wayarta na bugawa Abdul majid. A dalilin bamu bata kunu ba Baba ya hana ki yin kunun siyarwa har sati guda."
Umma Furera ta ce "kwarai kuwa na tuno ta
tabbas anyi haka. Ba lallai ba ne ita ta fada amma akwai alamar tambaya. Da farko ma a ina ya santa har zai kawo ta ya tafi ya barta a cikin gida? Na biyu bayan tafiyarta ne ya shigo yayi miki wannan dukan har muka dauki alhakin Yahuza. To ko budurwa Abdul majid ce take bibiyarki don ta san ya fi sonki, ko daman ita take hada miki tuggu don babanki ya raba ku duk motsin da ki kayi da Abdulmajid sai an fadawa mahaifinki?"
Sajida ta girgiza kai ta ce "Abdul majid bashi da budurwa, ni kadai ce budurwarsa a duniya haka ni kadai ya taba so kuma yayi min alkawari har karshen rayuwarsa ba zai taba son wata 'ya mace ba. Yayi min
rantsuwa tun sanda ya hadu dani bai taba jin yana son wata ba. Umma, wallahi na rantse da ubangijin daya halicce ni tunda Zahra ta zo har gida tayi min gulma tayi min sanadiyyar da na daina samun damar yin magana da Abdulmajid a waya har tsawon wata guda kenan. Asanadiyyar wannan na daina cin abinci, na daina bacci sai kuka, ga zazzabi da ciwon kai. Na yi alkawari duk ranar da na yi ido hudu da Zahra sai nayi mata rashin mutuncin da ' ban taba yiwa kowa ba ldan ma son
Abdulmajid take ko a dangin Abdul majid take daman da yawansu basa sona hakika sai na nakasta ta, nakasar da itama nata sauranyin zai daina sonta ta ji yadda nake ji data rabani da nawa masoyin."
Umma furera ta rike baki ta ce "a'a Sajida kada ki jawo mana abinda za a maka mu a kotu daga mu har ke. Kada kiyi kisan da zaki jawo a kashe ki a dalilin wani Abdulmajid. klnga yarinyar nan daga gani 'yar gidan masu kudi ce, ko bata da gaskiya ubanta ya na da halin da zai fada aji a hukunta mu balle ma ki nakasta ta ko ina aka je ke ce marar gaskiya. Sajida ina raba ki da wannan banzar zuciyar taki, saurin fushi da yawan dacin rai, tsiwa da futsara."
Sajida ta hasala ta mike tsaye tana gatsine, tana murguda baki, tana zare ido irin na tsantsar futsarar da ta saba.
Ta ce "Umma, me naji kina cewa? Kina nufin in hadu da Zahra ta wuce in wuce ban tanka mata ba? Haba ashe ba'a haifeni da jini ba, daga sama na fado. Don ubanta yana da kudi sai tayi min laifi in kyaleta? Wallahi na yarda in dauwama a daure a kurkuku har karshen rayuwata da in zubawa makiyiyata ido. Ni kuwa a rayuwata me zanyi da mutumin da baya kaunata da Abdulmajid?"
Kafin Sajida ta rufe bakinta mahaifinta ya sako kai cikin gidan, domin har kofar gida yake jiwo tsiwar
Sajida duk da cewa baya gane abunda take fada amma ya san zancen bana dadi ba ne.
Sajida na ganinsa tayi shiru amma taci gaba da harare-harerenta.
Ya dubeta cikin fushi Ya ce "ke kuma hayaniyar me kike yi kamar kina magana da sa'arki? Mahaifiyar taki kike dagawa murya har kofar gida?"
Sajida tayi shiru tana ta fusge-fusgen kai alamar ko a mutu ko ayi rai, ayi duk wacce za'ayi wai da bera ya zubar da garin mage.
Umma furera tayi caraf
Ta ce "ah, ba wani abu ba ne malam. Zafin zazzabi ne yake sakata surutai barkatai."
Malam ya ce surutan zazzabi daban haka rashin kunya daban. Nasan dalilin zazzabin nata ai shiru nayi muku kawai, a dalilin raba ta da dan iskan yaron nan Abdulmajid shine yasa take kokarin kashe kanta saboda taurin kai irin nata. To bari kiji in fada miki Sajida ko ki warware ki ci gaba da walwalar ki, ko ki ci gaba da takura kanki cikin kunci ki hadiyi zuciya ki mutu a wajena duk daya ne kuma ina nan akan bakata har abada ba zaki sake haduwa da Abdulmajid ba balle ya lalata ki, daman ba aurenki zai yi ba."
Sajida ta fusata ta murguda baki ta fada cikin tsiwa "an takurawa rayuwata a gidan nan, gara in mutu ma in huta. Haka kawai kowacce yarinya ana barinta ta kula wanda take so sai ni za'a takurawa. An kulle ni a gida, an hana ni karatu, an hanani fita makarantar Islamiyya da makarantar dare sai duka da zagi kullum ba kakkautawa.."
Ba ta rufe bakinta ba ta ga ya wurgo tabarya ta gefen fuskarta, saura kiris ta same ta a kunci. Malam ne a fusace ya wawuro tabaryar ya wurgo mata bai damu da ko zai fasa mata kai koma ya kasheta ba. Da turmin zai cicciba ya wurga mata, yaji da nauyi ba zai ya dauka ba.
Ihun Umma Furera ne ya qara tunzura shi ya ji dama ace ya same ta tayi ihun da hujja.
Sajida ta zura da gudu ta shige dakinta da gudu ta sakale da şakata.
Malam na huci yana ta "har fitsarar taki ta dawo kaina ina fada kina fada saboda kin raina kowa. To wallahi ba'a gidana ba, inyi wahala dake tun da aka haifeki zuwa girma sannan kice ban isa in fada miki ki ji ba to sai dai idan ba'a karkashina kike ba ki tattara kayanki ki tafi kiyi zaman kanki tunda kina ganin ke kika haifi kanki, kin girma kinfi karfin kowa. Ni kuwa idan ni na haifeki kuma da sauran numfashina a duniya wallahi ba zaki auri Abdulmajid ba ko zaki mutu.
Ya juya ya dubi furera ya ce "ke ce uwar banza da ba kya tsawatarwa 'yarki.Banga amfanin zama da ke ba tunda ya'ya biyu kin kasa ba su tarbiyya da sun kai guda goma ma ban san tabarar da za'ayi min a gidan nan ba. To bari in fada miki zamanki a gidan nan ya kusa karewa, ke ki rasa aurenki itama ta rasa Abdul majid din kuyi biyu babu. Dan haka kisa ido, idan na sake jin maganar dan iskan yaron nan Abdulmajid a gidan nan zaku ga yadda zanyi muku.Sajida albishirinki a cikin satin nan zan yi miki miji ko kina so ko bakya so shi zaki aura kuma dole ki zauna, ba zaki sake yin wata guda a gidana ba insha Allah"
Ya kade babbar rigarsa ya fice yana huci ya bar umma furera a takure a lungu ta buga tagumi. Zuciyarta sai dukan uku-uku take saboda tashin hankali. Yayin da Sajida ta kwalla ihu ta fada kan katifa tana rusa kuka kamar ranta zai fita.
Umma furera tayi ta buga kofa tana magiya Sajida ta qi bude kofa. Sai da tayi kuka ta gaji da kanta sannan ta bude kofar. Umma furera ta shiga lallashinta akan ta daure ta ci abinci amma Sajida ta qi ci.Paid book #300


Bakura ya iso qofar gidan Malam Yakubu daf da magariba kamar yadda ya saba zuwa. Ya iske Malam tare da dalibansa wato manyan mazan da suke daukar karatu tsakanin sallar magarib da isha'i. Kamar yadda su ka saba bayan sun idar da sallar magariba sai suka shiga daukar karatu, har zuwa lokacin da Isha'i ta yi, su na idarwa sai kowa ya watse.
Bakura da Malam ne kadai su ka rage. Hira suke kamar abokai, hirar dai ba ta wuce hirar siyasa ba. Da aka fito da abinci sai Bakura ya nemi afuwa akan yau dai sai dai Malam ya yi masa hakuri ba zai ci abinci ba saboda duk randa ya je gida cikinsa a qoshe rigima ake da uwargida.
Malam yayi dariya ya ce "kwarai kuwa na fahimce ka, mata su na da wannan dabi'ar."
Malam ya bude kwanon tuwo da miya kamar kullum tuwon tsari da miyar busashshi kubewa ce babu nama a cikin miyar sai dai qamshin wake da daddawa ne ya ke tashi. Bakura yana hira ya na satar kallon Malam. Tausayinsu ya rufe shi ya shiga sake-saken yadda zai taimakawa wadannan bayin Allah. Sai ya yanke shawara a ransa in dai ya tashi tafīya yau zai yiwa Malam alkawarin wani kudi mai tsoka da buhunhunan abinci wanda zai agaza masa wajen samu ya ciyar da iyalinsa da abinci mai kyau.
Malam cin abincinsa yake kai kace ba garau- garau yake ci ba kamar wanda yake cin naman talo-talo.
Malam ya gyara zama ya dubi Bakura ya ce "Alh.
Babura na yaba da hankalinka, ka zama tamkar d'a na cikina ko in ce dan uwana na jini. Na yarda da kai sosai ina so ka bani shawarar da zata amfane ni. Bakura ina so ka tsaya cikin nutsuwa ka bani shawara akan wata matsala da ta addabe ni"
Bakura yayi quri yana duban Malam zuciyarsa cike da tsananin mamaki ya na tambayar kansa shin wacce irin alfarma haka Malam yake nema a wajensa yake jero irin wandannan kalamai?
Malam ya ci gaba da cewa "Bakura, ka bani shawara akan Sajida."
"Shawara akan Sajida?" Bakura ya tamabaya cikin murya mai tafe da tsananin mamaki. Ya qara da cewa "me yake faruwa ne game da Sajida?"
Malam ya nisa ya ce "so nake in aurar da Sajida domin in sami nutsuwa da kwanciyar hankali. Saboda yaron nan Abdulmajid ba zai barta ba. Kuma duk garin nan kowa ya san ba aurenta zai yi ba lalata ta yake niyyar yi. A dalilinsa na hana ta karatu, a dalilinsa na hana ta fita amma duk da haka basu rabu da juna ba kwanciyar hankalina shine kawai in sami wani babba mai hankali wanda zai riqe min Sajida a matsayin matarsa. Wallahi Bakura ko baccin kirki ba na iya yi saboda kullum gani na ke Sajida zata bude qofa cikin dare ta je wajen Abdulmajid."
Bakura yayi shiru kamar wanda ruwa ya cinye ya rasa abunda zai ce. Can ya nisa ya dubi Malam ya ce "bayan Abdulmajid akwai wasu masu neman ta?"
Malam ya girgiza kai ya ce bayan Abdulmajid ba ta tsayawa da kowa. Akwai wani mai naci da ya qi tafiya duk wulakancin da za ta yi masa baya fasa zuwa shima yanzu ya hakura ya daina zuwa.Yanzu al'amarin Sajida ya kai ya kawo akan
Abdulmajid za ta iya rufe ido tayi tsiwa a gabana ta ce babu mai hanata auren Abdul Abdulmajid."
Sai hawaye ya surnano daga idanuwan Malam.
Hankalin Bakura yayi mutuqar tashi yayi shiru ya na tunanin irin shawarar da zai bawa Malam a matsayinsa na mai ilimi.
Malam ne ya katsewa Bakura tunani, ya ci gaba da cewa "ranar wanka ba'a boyen cibi. Bakura,
KAI KA FI CANCANTA ka auri Sajida."
Jin wannan kalma ta fito daga bakin Malam sai ya ji tamkar an harba bindiga a kirjinsa, ya ji kamar wani abu ya harba a cikin zuciyarsa saboda firgicewa. Ya dago da' sauri ya dubi Malam, duba irin na rashin fahimtar abunda yake nufi.
Malam ya dubi
Bakura duba na fuska da fuska.Ya ce "kai nake so ka auri 'yata Sajida idan kayi haka ba karamin jahadi kayi ba, ka taimaki rayuwarta ka taimaki rayuwata ni ubanta. Babu wanda ya fi ka sanin illar haduwar Sajida da Abdul majid. Saboda a hanya ka tsince su kaga halin da zasu shiga ka garzayo ka fada min don in tsawatar ba qaramar qaunarmu kake yi ba. Na yarda da tsananin tsoronka, saka ido akan tarbiyyar iyalinka. Na yi sha'awar hada zuri'ata da taka ba don komai ba, ko don wani abu ba sai don saboda Allah. Idan kana ganin baka da ra'ayin qara aure ko baka da ra'ayí akan Sajida kar ka boye min Bakura ka fada min, wannan magana muke ta fahimta.
Na yarda a cikin jama'arka ko daga cikin abokanka zuwa yaran gidanka ko Malaman masallacin qofar gidanka ka zabi mai hankali, mai addini mai tsoron Allah ka bashi Sajida. Na amince maka na san ba za ka cuce mu ba, ko ina raye ko ina a mace. Sajida 'yarka ce, kanwarka ce ka dauke ta tamkar Zahra."
Bakura yayi shiru kansa a sunkuye a kasa kamar wanda aka saka igiya aka daure shi tamau ko yatsa baya iya dagawa saboda rikirkitaccen tunanin, kwakwalwarsa ta kasa warwarewa.
Malam ya ci gaba da cewa "wanda zai auri Sajida ba na buqatar ya kawo min komai in banda sadaki. Sadakin ma kalilan ya isa kamar yadda shari'a ta yarda, ina da filina anan ringi road zan saka shi a kasuwa in sayar na san zai isa in yi mata gado da 'yan kujeru da zannuwan daurawa. Me kuma ake nema a rayuwar aure dai? Burina a killace min ita ta zauna lafiya ta cire ranta daga kan dan iskan yaron nan. Na fada ma ta nan da sati guda zanyi ma ta miji ko ta na so ko bata so, nan da wata guda ayi biki. Hankalina bai kwanta da masu zuwa wajena ba ne.
Da yawa sun sha nuna min su na son auren Sajida na qi amincewa saboda ban yarda da rikon da za su yi mata ba haka ina tantama da tarbiyyarsu. Kudi ba komai ba ne, mutunci shine ya fi komai. Ko dan dakon da yake neman halalinsa mai tsoron Allah, wanda ya san Allah ya san yadda zai bautawa Allah mai ilimin addini, wannan mutum shi ya fi cancanta a zauna da shi ba mai kudin da yake takama yana da kudi ba don haka yake ganin yafi karfin ya bautawa Allah ba."
Bakura har yanzu kalma guda daya ta gagari bakinsa ya na kallo, yana sauraron Malam babu abinda yake sai kada kai alamar yana gasgata zancen Malam.
Daga karshe malam ya ce "na baka wuka, na baka nama Bakura ka je kayi tunani nan da sati biyu ka zartar da duk hukuncin da ka ga yayi daidai akan 'yata Sajida."
Ba tare da Bakura ya furta wata kalma ba ya mike zuwa wajen motarsa. Malam ya raka shi har jikin mota yana mai yi masa addu'ar Allah Ya kai shi gida lafiya.
Bakura ya duqa ya cewa Malam "na gode Malam, zan tafi sai kuma gobe idan Allah Ya kaimu."
Ya shiga motarsa ya ja ya tafi. Malam ya dawo kofar gida ya ci gaba da tunanin shin wacce shawara Bakura zai yanke akan Sajida?
Bakura kuwa tsabar tunani sau biyu yana shiga layin daba layin gidansa ba, bayan fadawa a ramuka da kwatoci ba adadi. Ya rasa abinda zai zaba wanda yafi cancanta a ciki game da Sajida. Na farko a sanadiyyar tsanananin kamar da Sajida take yi da Zuhuriyyarsa ya
ji baya gajiya da kallonta tamkar wata talabijin haka Idan ya tuna tsantsar rashin kunyar Sajida sai ya ji gwbansa ya fadi saboda shi yana da kunya kuma baya son ayi masa rashin kunya.
Kalmar farko da Sajida ta fara furta masa ido da ido tawa Bakura ita ce "na tsaneka."
Dan haka babu tantama wannan tsanar tana nan a dauwame a cikin ranta babu mai goge ta. Zahra yarinya qarama ba ta san Sajida ba amma har ta gane halin Sajida bashi da kyau a take ta ce bana son Sajida bata da tarbiyya. Ga matarsa mai tsananin kishi muddin ta sami labarin Bakura zai kara aure tabbas zata iya hadiyar zuciya ta suma idan ma bata zarce gaba daya ba. Bakura ya sake Juyawa ya dubi amintar da take tsakaninsa da mahaifin Sajida Malam Yakubu ya san zai ji nauyin ya ce masa baya son 'yarsa. Yaya za'ayi kenan? Sajida ta zame masa kadangaren bakin tulu.

*** *** ***
Washegari da yamma Bakura ya koma daukar karatu gidan Malam, har suka yi hira suka gama babu wanda a cikinsu yayi maganar Sajida. Sai dai sun sha hirarsu har Bakura ya shaidawa Malam cewar sati na sama ba zai sami damar zuwa ba saboda zai je Abuja kuma a qalla zai yi kwanaki goma a can. Malam yayi addu'ar Allah ya kai shi lafiya ya dawo da shi lafiya ya samo abinda ya je nema.
Bakura ya gyara zama ya ce "Malam ka san ina harkar man fetir, ina da gidajen mai kala-kala a garin nan da super market wato ZUHURIYYA STORE da ZUHURIYYA PETROLIEUM STATION. Shekaru biyu da suka wuce na bude branch a Kaduna, yanzu kuma uwargidana Samira na ginawa babbar plaza a Abuja. A unguwar gwarumpa mai suna ZUHURIYYA PLAZA. To shine zan je ayi bikin budewa."
Malam ya gyada kai ya ce "au kai ne mai gidan man nan zuhuriyya? Yanzu zaka bude a Abuja kuma?
Bakura ya ce "Eh, plaza ce, ma'ana qatan gini ne mai hawa-hawa har hawa hudu kowanne hawa akwai kantina manya-manya guda hamsim ka ga kantina dari biyu da hamsin kenan. Kantina hamsim na kasa duk ni zan zuba kaya amma hawa na daya zuwa na hudu dukka haya zan bayar shine zan je ayi bikin budewa."
Malam ya gyada kai ya ce "wane mutum, ikon Allah. Kantina maka-maka har guda dari biyu da hamsim a waje daya wannan ai itace kasuwar duniya."
Bakura ya bushe da dariya ya ce "haba kasuwar duniya, sai dai kasuwar uguwar dai."
Malam ya ce "wanne irin bikin budewa kuma za'ayi?"
Bakura ya ce "ni da matata da ya'yana da abokaina da matansu da 'ya'yansu ne zamu hadu mu je wani hotel mai tsada mu ci abinci a yanka kek."
Malam yayi dariya ya ce "ka ga turawa 'yan boko. yanzu meye amfanin a yanka kek ayi tafi ayi dogon turanci, ina albarka take? Shawarar da zan baka
Bakura shine kar ka tara jama'a ana wani yanke-yanken kek bai yi tsari ba ace ka hada matarka ta aure da wasu mazan ana cin abinci ga 'yarka baliga a cikin maza, abokanka ba muharramansu ba ne. ka kalli matar wani a kalli matarka wanda yake haramun ne. Me zai hana ka dibi mahaddatan alkur'ani daga masallacinka su bazu cikin shagunan su sassauke kur'anai a ciki da zummar Allah Ya kawo ciniki, da kariya daga sharrin 6arayi da 'yan damfara. Matarka kuwa da 'ya'yanka ba'a hanasu su taya ka murna ba sai suyi tasu liyafar a cikin gida iyakacinsu mata kadai su gaiyaci 'yan'uwa da abokan arziki su zo su ci, su sha, ayi karatun kur'ani. Ka dauko mace tayi musu wa'azi a cikin gida. Haka bai fi ba?"
Bakura ya gyada kai ya ce "gaskiya ne Malam, tabbas na yarda cewa abinda da babba ya hango daga zaune yaro ko ya hau bishiyar rimi ba zai hango ba. Sai dai ina neman wata alfarma a wajenka Malam. Babu wanda ya fi cancanta ya je. ayi saukar nan sai kai da almajiranka."
Malam ya girgiza kai ya ce "a'a tunda ka na da naka malaman da almajiran ai su suka fi cancanta su je ba ni ba. Ni fa ban taba zuwa Abuja ba, idan aka ce za'a kashe ni akan sai na nuna hanyar Abuja to sai dai a kashe ni ban san inda take ba. Ga tsufa ina zan iya jure zaman mota daga Kano zuwa Abuja?"
Bakura ya ce "zaman mota ba matsala ba ne daman da jirgi zamu tafi. Zancen cancanta kuwa KAI KA FI CANCANTA ka yi min saukar kur'ani saboda bajintar da ke tsakanin mu. Zan iya samun daci da quna a cikin zuciyata idan ka bijirewa bukata."
Malam yayi shiru ya na dan murmushin jin dadi ya nisa sannan ya ce "Bakura babu wata buqata da zaka nema in qi yi maka ita.Ba damuwa zan baka yardaddun almajiraina dana yarda da qwazonsu su je suyi maka sauka ko ta kwana nawa ce sai dai ina so in ja hakalinka karka biya su kudin aikin da suka yi maka, Baya da ci da sha ba na buqatar ka basu wasu kudi na daban domin tsakanina da kai babu wannan."
Bakura yayi murmushi ya ce "Malam har yanzu baka yi min abinda nake so ba, zan so tafiyar
nan a tafi da kai don kasa min albarka da bakinka."
Malam yayi dariya ya ce "to shikenan Bakura ba zan qi zuwa ba tunda zuwan zai qara maka farin ciki."
Bakura ya ji dadi sosai ya tsayar da ranar tafiya, nan da kwanaki uku su shirya zai sa a zo a dauke su zuwa filin jirgin sama zasu acan Abujar zasu same shi don shi washegari zai tafi.
Kamar yadda Malam ya bashi shawara haka Bakura ya umarci iyalansa su aiwatar, wato su hada walimarsu a gida mata kadai ba sai sun bi shi Abuja ba.
Ya bawa Samira da yaransa izinin su je Zuhuriyya super market dinsa su dibi duk abinda suke buqata komai yawansa, komin tsadarsa daga naira daya zuwa naira million daya ya yarda su kashe. Su gayyaci kowa da kowa daga kan masu kudi zuwa talakawa a dangi da makwabta. Ya umarce su da su ware abinci tukunya daban wacce za'a tara almajirai a qofar gida a rabar sadaka saboda Allah. Sannan Bakura ya tafi Abuja, bayan tafiyarsa da kwana biyu yayi waya Kano ya ce direbansa ya kwaso Malam yakubu da almajiransa guda goma zuwa filin jirgin sama na Malam Aminu
Kano suka hau jirgi zuwa birnin tarayya Abuja.
Kamar yadda aka yi a kano a Abuja ma Bakura yana da

Please Login or Register in order to submit comment