Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ya addabi idonsa.
Malam ya girgiza kai ya ce "Lallai ka dandana maraici da wahala a rayuwarka."
Cikin kuka Zahra ta ce "Abba, menene dalilin rabuwar lya Zuhuriya da Malam Isah?"
Bakura ya ci gaba da magana cikin marainiyar murya "Wai ashe Sahura ta kullace ni, haushi take ji danta-bai ci jarrabawar tafiya sakandire ba, ni kuma na ci na tafi. Ina tafiya ta je ta hada mana munafunci."
Abubakar ya tambaya, "Abba, wanne irin munafunci?"
Bakura ya yi murmushin qarfin hali ya ce "Zuwa wajen mahaifin Malam Isa ta yi ta dinga kuka tana cewa wai bai kamata a ce ina kwana a cikin gidan nan ba, tare da yaranta dakinmu daya akwai mata, tunda na je sakandire yanzu na girma dole a mayar da ni gidanmu. Daman dakunan gidan uku ne. Daya na Sahura, daya na Zuhuriya, daya namu ni da 'ya'yanta. Shi mai gidan ba shi da daki, dakunan matan yake bi. Iyayyen Malam Isah suka kira shi, suka shaida masa cewar dole ya fadawa Zuhuriya ta fitar da yaron nan daga gidan. Dole ya sami Zuhuriya ya sanar mata halin da ake ciki, Da ya zo ya fada mata buqatar iyayensa sai ta ce muddin tana raye to tana tare da danta ta yarda za ta dauke ni daga ckin ya'yan Sahura, sai in dawo dakinta da kwana, In ya so ta hakura da mijin ya dinga kwana a dakin Sahura kullum. Malam Isah ya hau fada ya ce bai yarda ba sai na bar gidan. Ita kuma ta ce sai dai mu bar gidan tare, sai ya sake ta tun kafin in dawo. To wannan shi ne silar rabuwarsu.
Na fara wayo, na fara sanin zafin magana, dan haka na shiga damuwa. Na fara tunanin yadda zan yi da rayuwata, don in daina jawowa Zuhuriya mutuwar aure, don an fara qirga mata yawan mazan da ta aura an mata shaidar ba ta zaman aure kowa ya san ni ne sila.
A lokacin alalar gwangwani Zuhuriya take siyarwa da rana har gida ake shigowa ana siya. Ni da ita muke wanke wake in kai markade in kawo ta hada mu zuzzuba a gwangwanaye mu dora akan wuta. Idan ta dahu ni ne mai zubawa ina miqawa kofar gida. Mu ka tara kudi sosai a cikin hutun nan. Zuhuriya ta lalashe ni ta lallaba ni har sai da na yarda zan bi ta Mangono wajen danginmu. Domin ba na son zuwa gani nake idan ta kai ni ba za ta dawo da ni ba, kamar yadda Innono take fada kułum tun ba na fahimta har na gane cewar nan ba gidanmu ba ne, iyayena na can kuma can din ukuba ne tunda sai na yi laifi ake cewa a kai ni.."
Umma Furera ta sharce hawaye ta ce "Ka san ba ita ta haife ka ba kenan?"
Bakura ya nisa ya ce Eh, na sani dan na ji ana fada, amma ban damu ba, na sa a raina Zuhuriyą, ce uwata ita ce ubana don ita kadai na budi ido na gani babu mai sona mai wahala da ni sai ita. Dan a lokacin da aka fara kai ni makaranta dakyar na yarda Malam Isa ya saka min Bakura Usman Mangono dan ni tuburewa na yi na ce Bakura Zuhuriya sunana.
Saboda duk sanda na yi laifi Innono tana cewa a mayar da ni Mangono na tabbatar babu alkhairi a tattare da Mangono tunda sai na yi laifi za a kai ni, don haka na ji na tsani garin duk da ban san shi ba. Zuhuriya kadai na şani a rayuwata, ita ce mai share min hawayena, idan ina cikin damuwa da ita nake so in kasance har karshen rayuwata."
Sai yanzu Umar ya yi magana dan tunda ya zauna- yake kallon mahaifinsa yana sauraron wannan abun al'ajabi.
Ya ce "Abba, ka yarda kun je Mangono a lokacin'?"
Bakura ya ce
"Mun je har da Innono ma tare muka je da ita. A wannan lokacin ne na fara ganin mahaitiyata, na ga mahaifina, dan a lokacin da na baro su ina qarami sosai ba zan iya tuno su ba. Har na ga qannena guda biyu da aka sake haifa. Babban namiji ne su na kiransa Babagana, qaramar da aka yaye kuma su na kiranta
Yaana."
Abubakar ya tambaya cike da mamaki "Uncle Babagana da Aunty Yaana kake nufi?"
Bakura ya gyada kai ya ce "Kwarai kuwa qannena ne uwa daya, uba daya. Kamar yadda na tashi cikin wahala suma haka suka tashi cikin wahala da garari."
Zahra ta ce "Su ba a sami mai karbar su ba?".
Bakura ya yi murmushi ya ce "Babu wanda ya karbe su a wajen mahaifiyarmu suka girma sai dana
girma ne na je na tallafa musu na sa su a makaranta nake yi musu aiken kudi a koda yaushe."
Usman dan auta ya ce "Abba, mamarka ta gane ka kuwa, ba ta manta ka ba tunda ka girma?"
Gaba daya aka kwashe da dariya.
Bakura ya co, "Very good Usman, ashe kana fahimtar labarina Mamana ba ta manta ni ba, tana ganina ta shaida ni ta yi ta murna. Ashe bayan tafiyata ta yi ta zuwa gidan hakimi neman danta, kuka da ihu kullum. Aka yi a lallabata da kyar aka samu sauqin abun aka ce za aje dauko ni. Amma da ta sami wani cikin ta haifi kanina Babagana sai ta daina damuwa da ni.
Innono ta san ma Zuhuriya ba za ta bar ni acan ba, nima ba zan yarda in zauna ba, dan haka ma ba ta fara cewa a bar ni ba, muka dingumo muka dawo Cinkilawa."
Samira ta ce "A iya sanina Mama Fatukamba bata jin yaren Hausa sai Barbarci. Da wanne yare ku ke magana kai da sauran 'yan uwanka saboda na ga a qasar Hausa ka girma?"
Bakura ya yi murmushi ya ce "Hausa ai a Cinkilawa na koya, kin manta ba na jin Hausa sai Barbarci sanda Zuhuriya ta dauko ni, kun manta Zuhuriya babarbariya ce ta wajen uwa da uba. Mahaifinta dan Mangono ne, mahaifiyarta kuma 'yar asalin Gashuwa ce aure ya kawo ta qasar Kano. Dan haka Barbarci muke a gidan, a wajen yara na koyi Hausa.
Mun dawo Cinkilawa ba dadewa hutuna ya qare, Zuhuriya ta harhada ta ba ni duk abun da nake bukata, motar qaramar hukumarmu ta kwashe mu zuwa makaranta. Duk garin babu mai taimaka min da sisinsa sai Zuhuriya, babu mai agaza mata ita kuma.
Ta yi min alkawari idan ribar alalarta ta taru za ta yi min aike makaranta. Ina son a yi hutu, saboda in ga Zuhuriya, amma na fi sakewa a makaranta fiye da a gida. Ni da Zuhuriya a rabe muke, saboda fada ko gore-goren da ake yi min. A haka a daddafe har na kai aji uku na gama qaramar sakandire.
A hutun da zan tafi aji hudu wato babbar sakandire (SS1) a hutun Zuhuriya ta yi aure kuma, ta auri wani mutum a garin Yan lanya mai suna Malam Yahuza. Matansa biyu Aya da Umaima, bai taba haihuwa ba. An sha surutu a wannan auren jama'a suka yi ta ce masa kada ya auri Zuhuriya, ita ma ba mai haihuwa ba ce, ita kuma a ce kada ta aure shi matansa kashe kishiya suke. Daya an yi mata shaidar maita, daya an ce 'yar tsibbu ce bokaye take bi. Sun hada kai su biyu duk wacce ya aura sai sun kore ta ko su haukata ta.
Hankalina ya tashi kafin a yi auren na kira Zuhuriya gefe ina kuka na ce ko za ta hakura da auren.
Ta yi murmushi ta shafa kaina ta ce "Allah yana tare da mu Bakura ba komai. Ni ma bana son auren nan, na gaji da aure-auren nan Innono ce ba za ta kyale ni ba in zauna lafiya ba."
Na yi mata addu'a Allah ya sanya alkhairi.Tun sanda aka kai amarya kauyen Yan lanya na ga yanayin gidan dan tsurkuki, zana ce da qasa zalla ga qanqanta, na tabbatar Zuhuriya ta ci baya ba ta taba aure a quntace irin wannan ba. Na haska na hasko ban ga daki ko zauren da zan yasar da filona in kwanta hakarkarina ba. Na shiga zulumin yadda rayuwa za ta kasance min.
Na san muddin Zuhuriya ba ta Cinkilawa zamana a Cinkilawa ya qare, dan Innono ba za ta bar ni ba. Haka na dinga safara tsakanin Yan lanya da Cinkilawa. In kwana a Cinkilawa a dakin Zuhuriya gari na wayewa in niqi gari in tafi garin Yan lanya wajen Ummata Zuhuriya ta ba ni abincin safe, rana na dare. Idan Magaruba ta yi in dawo Cinkilawa in kwanta. Har hutu ya qare na koma makaranta na shiga S.S.1.
Na fara girma na fara hankali, don a lokacin shekaruna goma sha hudu zuwa goma sha biyar, dan haka na fara tunanin yadda zan canza rayuwata, ba tare da na sake jawowa Zuhuriya matsala a aurenta ba. Don na fahimci kishiyoyinta sun fara harare-harare su na yi mata habaici akan tuwan da take ba ni. Na yankewa kaina hukuncin ko an yi hutu in yi zamana a Wudil ina dako ina cin abinci, har a dawo makaranta. Haka kuwa aka yi da aka yi hutu na ki tafiya har da guduwa na labe dan kada 'yan garinmu su ganni, sai dai na bawa wani abokina dan kusa da garinmu sallahu wajen Mamana Zuhuriya na ce ya ce mata ina makaranta lafiyata qalau ba zan zo huta ba, saboda ina zana jarrabawa. Haka ya je ya shaida mata jikinta ya yi sanyi ya ce min sai hawaye take tana tambayarsa me yasa su ba su zauna sun zana jarrabawar ba sai Bakuranta shi kadai tunda shima ta san ajinmu daya? Duk da ba ta da ilimi, amma tana da kaifin basira."
Umar ya ce "Abba, kai kadai kake kwana a dakin
dalibai (hostel)?"
Bakura ya girgiza kai ya ce "Daf da Magaruba wani Malami ya ritsani a lungun da na maqale ya jawo kunnena har gidan principal. Kamar yadda na shaida muku tun farkon zuwana makaranta principal dinmu ya san ni, kuma yana sona koda yaushe yana yaba qoqarina yana bada misalai da ni a wajen assembly, dan haka yana ganina ya ce da malamin ya sakar min kunne. Bakura yana da hankali akwai dalilin da yasa ya gudu ya buya bai tafi gida ba."
Bayan malamin ya tafi ya zaunar da ni a gabansa yasa matarsa mai suna Asiya ta zubo min abinci na ci na qoshi dan ya ga alamar yunwa da wahala a jikina, Na ci abinci na qoshi, ya fara yi min nasiha hade da dabara gami da lallashi a kan in fadi dalilina na ain tafiya gida.
Da farko na 6oye masa daga karshe na zayyana masa tarihin rayuwata tun daga farko har karshe. Na kuma fada masa dalilina na qin komawa gida hutu. Abun mamaki sai na ga ya tausaya min matuka kamar zai rusa kuka, ya kira matarsa Asiya ya laburta mata labarin rayuwata ya fada mata dukkan labarin dana ba shi. Mutuniyar kirki ce, sai ita ma ta tausaya min ta ba shi shawarar to ya bar ni in dinga yin hutun a nan wajen su mana.
Malam Abbas Shagari ya ce 'A'a sai na je garin ko na aika an tabbatar min haka ne, sannan zan bar shi ya zauna. "
Da ya aika aka tabbatar masa haka ne sai ya qyale ni na zauna a gidansa, kamar yadda na ce masa zan dinga dako ina cin abinci sai ya hana ni yin dako, ya dinga ciyar da ni a kyauta. A lokacin yana da yara guda uku babban Abdul Wahab, sai mace Amina da wani dan jariri da ake goyo shi ma Abdul sunansa. Na ji dadin zama a gidan Malam Abbas Shagari saboda shi da matarsa su na da kirki su na kula da ni kamar dansu.
Kamar yadda na ji dadin zama da su su ma sun ji dadin zama da ni, saboda ba na gajiyawa wajen aikace-aikacen gida kamar mace, babu abin da ban iya ba. Shara, wanke-wanke, wanki, aike, noma Koyawa yara karatu da rainonsu duk ni nake yi wa Aunty Asiya. Kafin hutu ya qare sai ga Zuhuriyya wurjanjan an rakota gidan da nake. Ina ganinta gabana ya fadi, saboda yadda na ga ta rame ta lalace akwai alamar damuwa da wahala a tattare da ita. Na riqe ta ina tambayarta ko lafiya?
Ta rushe da kuka ta ce "yanzu Bakura ni ka ke guda, an yi hutu kowacce uwa ta ga danta ni ban ganka ba, wacce irin jarrabawa ce a cikin hutu? Ba na barci ko da yaushe ina leken hanya, idan na ji maganar wani sai in fito da gudu daga daki in zaci kai ne."
Na ba ta hakuri, sannan na shiga da ita cikin gida na shaidawa Malam da matarsa ga mahaifiyata. Bayan ta zauna sun gaisa ta ci abinci, sai ta fara kuka tana shaidawa Malam irin halin da ta shiga na damuwa da fargabar akan rashin ganina.
Malam ya yi mata bayanin dalilan da na shaida masa. Sai ta sake shiga damuwa ta ce ba ta taba tunanin har akwai gidan da Zaa ce ita kadai zata zauna baa yarda Bakura ya zauna ba kuma ta ci gaba da zama a gidan ba, dan haka in har tana gidan dole Bakura ya zauna tare da ita.
Kasancewar ta tubure ba za ta bar ni ba Malam ya ce in shirya in bi ta mu tafi. Da yake yamma ta yi ya shawarce ta ta kwana gobe sai mu tafi, ta ce maigidanta ya ce lallai-lallai ta koma a ranar, dan haka a lokacin na hada 'yan kayana na bi ta duk da hutun ya kusa qarewa. Kamar yadda na fada muku ba daki a gidan, Zuhuriya sai haya ta kama min daki daya a makwabtansu na zauna duk da surutun akan abincin da ake ba ni kishiyoyin suke yi mata. Na lura cewar su na takura mata tashin hankali da masifa kullum. Wannan ta yi mata yau, gobe wancan ta yi mata. Duk da irin haqurin da nayi ta yi na cije ban je na rama mata ba.
Wata rana kasa daurewa na yi, na shigar mata fadan. Domin sun tarar mata su biyu za su yi mata duka har sun kaita qasa, na zo na tade qafar daya ta fadi qasa, dayar kuwa angaje ta na yi ta fadi gefe. Na tashe ta tsaye na karkade mata jikinta. Da maigidan ya zo suka shaida masa karya da gaskiya sai ya kore mu ni da Zuhuriya, amma bai sake ta ba ya ce dai ta bar masa gidansa.
Mu ka tafi Cinkilawa da Magaruba, saboda tsoron Innono sai muka qi zuwa gidan muka kwana a gidan wata qawar Zuhuriya mai suna Tabawa. Washe gari muka kama haya a nan Cinkilawa. kan kace kwabo Innono ta ji labari, ta diro mana.Ta yi ta fada ta shaidawa Zuhuriya cewa marmaza-marmaza ta shirya ta koma gidanta, don mijinta ya aiko 'yan uwansa biko, amma kada ta sake komawa gidan da ni. Zuhuriya ta ce ta amince za ta koma, amma sal hutuna ya qare na koma makaranta, sannan zata koma.
Innono ta ce ba zai yiwu ba ta yarda in koma gidanta in qarasa hutun ita kuma ta koma. Daga yadda Innono ta ga na yi ta san ban amince ba. Haka ita ma Zuhuriya ta dai amsa mata ne kawai, sannan Innono ta tafi. Ai kuwa bata koma ba har sai da hutuna ya qare ta harhada min komai na koma makaranta, sannan ita ma ta koma gidanta kasancewar mijin kullum sai ya zo bada hakuri.
Na koma makaranta ina ta karatu, har shakuwarmu ta sake kulluwa tsakanina da principal da iyalansa. Har sai da sauran daliban makarantar suke tunanin ashe daman mu 'yan uwa ne. A gidan nake yin week end haka komai dare Aunty Asiya take aiko maigadinsu ya kawo min abinci har hostel. Ina jin dadin rayuwar makaranta, amma jikina ya kan yi sanyi, kwalla ta cika min ido idan na tuno halin da na baro Zuhuriyata. Na qagu in gama makaranta in fara aiki a local goverment dinmu in gina mata gidan siminti, in dinga ajiye mata buhun-buhunan abinci, in dinga dinka mata suturu kala-kala, ita ma ta huta wahala. Burina kacokan a kan Zuhuriya duk da ina tuno mahaifana da qannena na Mangono.
Aka yi hutu, don haka na koma staff quarters gidan principal, amma da kyar ya bar ni na zauna saboda gudun abinda ya faru wancan hutun. Na sake ba shi labarin abinda ya faru bayan Zuhuriya ta zo ta dauke ni. Ina kuka ina shaida masa cewar ba na so in sake kashe mata aure. Tausayina yasa dole ya kyale ni.Kamar kullum na bawa abokina wasiqa ya kaiwa Zuhuriya, tasa ya karanta mata. Ta ji irin magiyar da na yi mata cewar kada ta damu, kada ta biyo ni makaranta ina nan cikin qoshin lafiya. Kuma idan hutu ya kusa qarewa zan zo in yini sai in dawo makaranta. Abokina ya shaida min cewa yana gama karanta mata sai ta rushe da kuka ta tashi ta shiga dakinta."
Bakura ya matse hawaye yayin da tausayinsa ya rufe masu sauraronsu. Da yawa daga cikinsu suma kwalla suke.
Ya girgiza kai yayin da ya cije baki ya damqe tsakiyar kirjinsa, saboda zugi da radadin da zuciyar ke yi masa.
Ya ci gaba da cewa "Da wayo, da dabara nake ficewa daga gida in shiga cikin garin Wudil ina yi aikin qarfi ina samun kudi mai yawa sai in boye kafin rana ta fadi sai in dawo gida. Idan suka tambaye ni sai in ce ina bakin get wajen masu gadi ina hira, saboda na san Malam Abbas Shagari ba zai bar ni ba, abin kunya ne a wajensa a ce dalibinsa na dako, sara itace, diban ruwa da dai sauransu, musamman ma ni da kowa ya dauka dan uwansa ne. A haka na tara kudi mai yawa ba tare da kowa ya sani ba. Sai da hutu ya rage kwana biyu na shirya na shaidwa Malam Abbas cewa zan je in ga Zuhuriya. Ya dauko kudin motar zuwa da dawowa ya ba ni na tafl na shiga mota na tafi kai tsaye garin 'Yan lanya na nufa wajen Zuhuriya.
Hankalina ya tashi da na ga halin da take ciki daga dukkan alamu kishiyoyin nan nata sun hada kai su na wahalar da ita. Ta rame, ta yi baqi da alamar rashin cikakkiyar lafiya a jikinta.
Mace ce mai fara'a da hira, ga zaqin murya, amma da kyar kake jiyo abun da take fada idan tana magana. Gashi yanzu ba ta sana'ar komai, jarin ya qare. Sai ta yi matuqar yin farin ciki da mamakin da ganin irin kudin da na tule mata a gabanta.
Ta riqe baki don mamaki ta tambaye ni. "Bakura ina ka samo kudi haka?"
Na ba ta labarin duk yadda aka yi, sai ta fashe da kuka ta shaida min cewa daman tana rashin kudi ga bashi a kanta dankar. Su suke siyan omo, sabulu, kudin kitso, ga cikon kudin cefane idan ya ba su tsabar gero, dawa ko masara shi kenan ya gama. Su za su surfa su daka har ya zama gari, sannan su nemo abin kada miya. Na sake tausaya mata, sannan kuma na sake kudirar niyyar zagewa in yi aikatau in samo kudi in ba ta idan an yi wani hutun. Ta raba kudin gida biyu ta miqo min rabi ta ce in yi sayayyar makaranta daman ta hada zannuwanta za ta siyar ta aika min kudin. Na ce ta bar shi pricnipal ya gama siya min komai. Ba ta ji dadi ba da na ce yau zan koma ba zan kwana ba. Kuka take, ni ma ina kuka muka rabu. In takaice muku kowanne hutu haka ake yi har na gama aji biyar (Ss2), muka fara rubuta jarrabawar fita don haka na dade banzo ba. Kowa ya yi hutu ban da masu zana jarrabawar fita, sai dai aka yi mana taron iyayen yara.
Ranar taron iyayen yara(visiting) ban sa rai ba, ko a mafarki ba na tunanin zan ga iyayena. Don haka ban ma tunkari cikin Hall ba na sami bishiya na zauna ina karatun littafina. Kamar daga sama na ga Jamilu abokina ya nufo ni a guje yana shaida min ga mahaifiyata ta zo min.
Na dube shi a shelake na ce "Karya ne."
Ya yi min rantsuwa gami da rike hannuna ya ja ni har karkashin bishiyar da Zuhuriya take tsaye.Hakika ita ce a rakabe a jikin bishiya da kwanon abinci akanta. Yayin da manja ya yi kaca-kaca da kayan jikinta, musamman farin mayafinta, da alamar gajiya da wahala a tattare da ita. Na qaraso da sauri cike da gigita na sauke kwanon da ke kanta na zaunar da ita qasa ta miqe qafafuwanta da suka kukkumbura suntum, kasancewar tsohon cikin dana gani a jikinta.
Idanuwanta a kumbure, leben bakinta a suntume ga bushewa kayau-kayau saboda yunwa da kishirwa, kamanninta ya canja kamar ba ita ba. Na rasa abun da yake yi min dadi na ruga da gudu gidan Malam Abbas Shagari na karbo ruwan sanyi a firji na kawo mata ta sha, na bude kwanon na ga wata cakudaddīyar shinkafa da miya ce wacce ta sha wuya. Na tura kwanon gabanta na ce ta ci.
Ta girgiza kai ta ce "Kai na kawowa Bakura ka ci."
Ta shaida min cewar Babar Jamilu ce ta shaida mata za a yi wa yara

Please Login or Register in order to submit comment