Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a wayar dake a kwatar miki 'yancinki amma kin k'i yarda, kin zauna ki na bin dokar 'yan gidanku gidadawa. Wai ku ustazai, malamai kuma almajirai."
Babu abinda Sajida take yi sai karkarwar jiki, babu furucin da yake fita daga bakinta sai " Abdul majid kayi hakuri, dan Allah dan Annabi ka yi hakuri."
Abdul majid ya yi mata wani kallo na wulakanci ya zare bakin glashin dake fuskarsa ya tabe baki.
Ya ce "ki na nufin da wadannan kayan na jikinki za ki bi ni party? Ki na nufin da dogon wando da gyale zan shiga dake wajen hadadden party da hadaddun abokaina? Ke bakauyiya ce har yanzu kin kasa wayewa."
Sajida ta dubi jikinta sama da kasa ta rasa illar dake tattare da ita. Wandon jeans ne hadadde kuma matsatstse shine ma ya siyo mata daga America, haka itama rigar a matse take.
Tunanin da take yi ya katse ya ce "dole in kai ki wani kanti in siya miki kaya, mini skirt za'a saka iya cinya da zurmukeken takalmi mai tsini irin mai zif din nan har gwaiwa da riga shimi iya kirji wacce ba ta rufe cibiya ba, kuma babu ke ba zancen dankwali, kin ci sa'a ma ki na da gashi ba sai an qara miki ba."
Sajida ta zabura ta dubi Abdul Majid cike da fargaba ta ce "riga iya kirji?"
Ya daka mata tsawa ya ce "to meye, ki na nufin ba za ki iya sawa ba ne?"
Tsoransa take, sonsa ta ke don haka ba ta iya yi masa musu.
Ta ce "zan saka mana." Ta dubi agogon dake daure a hannunta daga dukkan alamu ta qagu ta koma gida don kada a nemeta. Wannan karon ma tsawa ya daka mata mai firgitar da wanda ke kusa da su, ba ma wacce aka yiwa ba. Nan da nan jikinta ya hau karkarwa.
Ya ce "duba agogon me kike yi, ko yau ma an baki lokacin da za ki komą gida ne?"
Sajida ta na karkarwa
ta ce "a'a ba duba agogo nake yi ba, yi hakuri."
Ya ce "to zagaya ki shiga mota mu tafi."
Sand'a ta ke kamar wacce kwai ya fashe ma ta a ciki, saboda ba ta son shiga motar amma tsoransa ta ke ta kasa ce masa ba za ta je ba.
Bakura ya dago da sauri zuciyarsa tamkar ta fashe, tashin hankali ya rufto masa lallai kuwa zai shiga wani mummunan hali idan har ya bari yaron nan ya fita da yarinyar nan ya je ya ba'ta mata rayuwa ba tare da sanin iyayenta ba. Tabbas abin zai dad'e bai fita daga cikin zuciyarsa ba zai ga kamar ya ci amanar musulumci da iyayenta da ita kanta.
"Tabbas yaron nan ya na niyyar ruguza tarbiyyar da iyayenta yarinyar nan su ka dade su na gina mata." Ya fada a ransa.
Sai ya ji wani hawaye mai zafi ya surnanu masa, yaransa ne kawai su ka fad'o ma sa a rai, gaba d'aya ya ji ya shiga zargi anya kuwa shima ba ci gaban mai haqar rijiya ya ke yi ba kuwa, kullum haqa ya ke amma ya na qara yin qasa. Anya kuwa ba tufka ya ke yi wani ya na warware masa a waje ba kuwa? Ya tuna hadisin da Manzon Annabi (S.A.W) ya koyar damu ce wa "idan ka ga ana aikata 6arna to ka hana da hannunka, idan ba za ka iya ba to ka gyara da bakinka, idan ba halin haka to ka qi abin a zuciyarka wannan shine mafi raunin imani."
Nan da nan ya ji a ransa zai iya zuwa ya hana da baki tunda bashi da ikon gyarawa da hannu. Ya zabura zai je wajensu kenan don ya ba ta shawara da baki ya ce kada ta bi shi. Sai ya ji Abdul Majid ya ce da ita "da fatan kin fad'a a gida cewar kwanaki biyu za ki yi ko?"
Gabanta ya fadi 'rass' ta dafe kirji ta tambaya cikin firgici "kwana biyu?"
Ya yi mata tsawa ya ce "toh meye abin fargabar, ban isa da ke ba ne? A Abuja Nicon Hotel za'a yi casun kuma sai qarfe d'aya na dare za'a fara dan haka daga nan ma Abuja za mu wuce.
Sajida ta zagayo da sauri in da yake ta tsugunna a gabansa ta fashe da kuka ta ce "Abdul majid ka taimake ni, ka rufa min asiri kada ka yi fushi da ni. Da ka san ta yadda aka yi na fito yanzu ma da sai ka tausaya min. Sai da na yi dubara da magiya Babana ya bari na fito da zummar zan je gidan su Asiya kawata in karbi qur'ani. Mintina talatin ya ba ni kasancewar gidan babu nisa ya na gida ya na jirana. My dear, idan na bi ka Abuja har kwana biyu kashe ni ne kawai ba za' a yi a gidanmu ba, ka rufa min asiri. Ina sonka Abdul Majid fiye da yadda na ke son rayuwata."Kai ka fi cancanta 1
Na

Jamila umar Tanko
(JUT)




0️⃣3️⃣

Abdul Majid ya dakatar da ita da hannnun ya katse ta.
Ya ce "ba na bukatar bada hakurinki, ai na fad'a miki a baya hakurin da na yi ya isa nan gaba ba zan sake ba. Kin manta alkawarin da kika daukar min har na yarda na sake dawowa muka shirya? Ban taba gayyatarki fita kin yarda kin bi ni ba, sai kin kawo min ba'adi da qa'bali, rawawul Baba rawawul Umma. Kar ki manta na ce miki na gaji na daina zuwa wajenki, ki ka lallaba ni na dawo a bisa sharadin kin yarda ko a ina ake party za ki bi ni shine yanzu ki ke duban kwayar idanuwana kike fada min Babanki ya na jiranki a gida? Ma'ana dai ba za ki bi ni ba ko? To shikenan daga yau ba za ki sake ganina ba, kada ki kira ni a waya. Baby kina da kyau, ke kalar shiga taro ce amma ki na kwabsawa da yawa iyayenki sun tauye rayuwarki dan haka sai anjima."
Ya juya ya shiga zai shiga motarsa ta na tsugunne ta na magiya. Idanunta kamar za su fita dan kuka, hawaye su na zuba ratatata. Ta yunkura ta rike kofar motarsa ta na bashi hakuri. A fusace ya daga qafa ya cije baki zai mangare ta da tafkeken takalmin qafarsa. Sai ta yi tsalle gefe bai same ta ba, ya shiga motarsa ya fisga da qarfi gami da qure sautin kid'a kamar zai tashi kunnuwan wanda ke wajen.
Bakura ya durkusa' a gaban fanfo ya na ajiyar zuciyar dad'i, domin sanda Sajida ta yi kamar za ta shiga motar sai da numfashinsa ya fara cikewa baya dirawa huhunsa saboda tashin hankali. Da Allah Ya sa ba ta bi shi ba ya ji dadi, kuma ya godewa Allah. Ya kunna famfo ya na wanke fuskarsa ya na satar kallon Sajida wacce ta zo ta wuce ta bayansa ta na sharcar hawaye.
Ta yi wuf ta fada lungun nan ta zurmuqa hijabinta ta fito tsaf a kamilarta, ta na tafe tana kwararar da hawaye. A rude take tamkar wacce aka yi mata aitken cewa uwarta ta mutu ko kuma tamkar wacce aka sace d'anta ta yi duban duniya ta rasa shi. Ta dauko wayarta ta na ta gwada kiran Abdul majid sai ta fara ringing sai ya katse daga qarshe ma ya kashe wayar gaba daya.
Kukan da Sajida ke sharba sai ya qaru, tashin hankali ya qaru sai taji ta tsaní kowa a duniya babu kuma kyautar da za'ayi mata ta ji dadi idan ba Abdul majid dinta aka kawo ma ta ba.
Bakura ya tura hula qeya ya nad'e hannayen rigarsa kamar wani dan garuwa ya biyo ta a baya da sauri, ya na isa gare ta sai ya rafka ma ta sallama. Ta ki daga ido ta dube shi sai da gefen ido ta dan waiwaya sannan ta dauke kai ta ci gaba da tafiyarta ta na sharbar kuka.
Bakura ya sake biyo ta ya na yi mata sallama, Sajida ta ki sauraransa balle ta amsa.
Ya ce " 'yan mata kukan me kike yi ne?"
Wannan karon a fusace ta dago da jajayen idanuwanta a cike da hawaye. Cikin tsawa ta 'ce "dalla malam ka rabu da ni, ni ba sa'arka ba ce, kowacce kwarya da abokin burminta, haka kuma kwarya ta bi kwarya idan ta bi akushi ba za ta moru ba. Ka je ka samu sa' arka, ballagaza marar aji irinka."
Sai a yanzu Bakura ya kalli fuskarta tangararai, ya ji gabansa ya yanke ya fadi ras, kan kace kwabo ya gigice ya fita hayyacinsa, mamaki, d'imuwa, rikirkicewa da d'aurewar kai suka rufto masa. Kallo daya za ka yi masa ka gane haka, babu kalmar da Bakura ya ke fada sai "Inna lillahi wa'inna ilaihi raji' una. Tsarki ya tabbata ga ubangijin talikai. Allah mai iko, Allah mai halittar bayinsa. Yarinya wacece ke? Su waye iyayenki?"
Sajida ta yi masa kama da Zuhuriyyarsa. Ikon Allah ta yaya hakan ta faru? Saboda dimuwa sai ya durqushe ya dafe kai yana jujjuyawa. Sajida ta ga alamar tabin hankali a tattara da wannan mutumin sai ta ci gaba da tafiyarta.
Ya miqe a guje ya sake biyo ta ya na yi mata dan kira.
Ta tsaya cak ta kalle shi ido cikin ido cikin tsiwa da futsara ta ce " kai dabba in baka da tunani zan tuna maka, na fada maka ni ba ajinka ba ce ka rabu da ni."
Ta juya za ta tafi, a fusace ya fisgi hijabin ya juyo da ita ta fuskanci shi ya na magana cikin fusata.
Ya ce "Na haifi kamar ki 'yata tana a gida amma kike kallon idanuwana kike zagina dan baki da kunya. Ga dan iska can mayaudari ya tafi yanzu, ya na zaginki ki na lallaba shi.Sai ni kika raina saboda ni kamili ne na yi shiga ta kamala da manyan kaya. Ni ne abin wulakanci a wajenki ko? To ni shawara zan baki kiyi hankali da samarin zamani, ki daina ha'intar iyayenki su na yi miki tarbiyya ki na biýewa wani qato ya na rusa musu."
Tsananin tsanar Bakura ta cusu a zuciyar Sajida sai hawayen takaici ya kece mata.
Ya ci gaba da cewa "har ki na ce min kwarya ta bi kwarya idan ta bi akushi ba za ta moru ba, ke ba ajina ba ce don haka kowacce kwarya da abokiyar burminta. Shin kin san kwayar da ki ke kira kuwa? Kwarya ai kala-kala ce kwaryar dake tunb'ele a tsakar gida ana rigar tsakuwar shinkafa ko gero da ita, ana bakace, ana zuba tuwon dumame, wacce ake d'orawa gardawan maza a kai su kai gero ko masara surfe da niqa kasuwa. Ko kuwa kwarya ta gari wacce aka rataye a ragaya, aka sakale a daki, mata su na kwalliya da ita, ba'a bari a sauko da ita qasa balle a damqeta ta yi datti? Duk wata kwarya ta gari ta na ragaya asirinta a rufe. kwarya marar kyau ce a tsakar gida in anso a kifa, in an so a bude, idan anga dama a fasa ko kuma a kada ayi kida da ita kowa ya jiyo sautinta ayi rawa. Dan haka ke kwaryar tsakar gida ce waçce take tangaririya a gari. Ke kwaryar kida ce wacce kike barin wani d'a namiji ba mijinki ba ya jiyo muryarki. Duk wata 'ya mace ta gari ta na qunshe a gidansu ba ta bin maza su na yi mata wulakanci domin mace daraja ce da ita har tafi lu'ulu'u idan ta kama kanta, to ita ce nake kwatanta ta da Kwarya ta gari tana ragaya. Ado ake yi da ita ba a wanke-wanke a cikinta."
A fusace Sajida ta dube shi duba na tsana don ba ta taba tsanar wani bil-adamama a duniya yadda ta tsani Bakura ba.
Hawaye ya sake kwararowa daga idanuwanta. Ta ce "yarka da ka ce ka haifa kamar ni ita ce wulakantacceyar kwaryar nan da ka suffanta."
Bakura ya tsinci kansa yana murmushi maimakon ya yi fushi kasancewarsa mutum ne mai yawan fushi, baya son raini daga mutumin daya bawa kwana d'aya ma ba shekara daya ba balle kuma 'yar cikinsa daya haifa.
Ya ce "idan zan dauki kwaryata in mutunta, in adana ta a ragaya, in saqale ta k'i zama, in sake saqalewa a sama ta k'i zama to lallai ta zama kwaryar tsakar gida mai garari. 'Ya ta da kike magana kuwa a tunanina kwarya ta gari ce wacce na sakale ta a ragaya bata fita tsakar gida tayi garari, kamar yadda a tunanin iyayenki sun dauki Kwaryarsu mai kyau sun saqale a ragaya basu san tana ballewa ba ta fita tayi gararinta ta dawo ta d'ane ragaya tayi luf. Don haka had'uwata dake naga abinda yake faruwa yasa ni dole in koma gida in zauna inyi gadin wannan kwaryar dana sakale don karta sauko ta fice ta yi ta garari a gari."
Sajida ta qurawa Bakura ido ta na dubansa dubu irin na tsana da takaici sai wani d'aci ta ke ji a ranta na bacin rai, ji take tamkar ta d'aga hannu ta dora masa mari sai dai tana shakkar aikata haka kasancewar taga shima a tsaye yake ya fita fitsara. Tunda ta ke a rayuwarta bata taba haduwa da mutumin daya cusguna mata irin Bakura.
Ta fada cikin kuka da takaici."Na tsane ka."
Ta juya ta ci gaba da tafiya. Bakura bai bita ba sai ya dawo jikin motarsa ya jingina yana kallon Sajida. Zuciyarsa cike da tsananin mamaki da son yaga shin su waye mahaifan Sajida, ya aka yi ta yi kama da Zuhuriyyarsa? Maganarsu, kallonsu, harararsu, kukansu, kirar jikinsu,. hannayensasu, kafafuwansu. Babu yadda za'ayi mutum da mutum ba dangantaka ayi irin wannan kamar sak, dole sai anga ta inda suka bambanta. Ganin Sajida da yayi sai ta tuno masa da Zuhuriyyarsa. Ya fashe da kuka shi kadai kuma ya lallashi kansa ya goge hawayen ya yi zunbur ya shiga motarsa don kada Sajida ta b'ace masa domin ta fara yin nisan da ya daina hango ta sosai. Sai yake ta bin ta a baya, Idan yayi tafiya kad'an sai ya tsaya har sai da yaga gidan da ta shiga, ba tare da Sajida ta san ya na biye da ita ba.
Ya qarasa qofar gidan ya kashe mota ya fito ya qarewa gidan da unguwar kallo ya tabbatar Sajida 'yar talakawa ce liqis kuma daga dukkan alamu 'yar malamai ce domin daga ka doso zauren gidan allunan almajirai ne cike a zauren kuma kowacce kusurwar bangon zauren kundun kur' ani ne a sassakale. Ga almajirai nan reras su na shige da fice a cikin gidan.
Shi dai burinsa yadda zai yi ya ga mahaifan Sajida ba makawa su na da alaqa da Zuhuriyyarsa. To amma ya san Zuhuriyya, ya san duk wani d'an uwanta, kakaf dangin Zuhuriyya babu ko daya a Kano gaba daya suna qauyensu Cinkilawa. Amma yaya aka yi Sajida ta yi kama da Zuhuriyya? Tambayar da ya ke yi a ransa kenan. Ya jingina a jikin motarsa kamar wani gunki zancen zuciyarsa har ya fara fitowa fili.
Maganar wani yaro ce ta katse shi ya ce "d'anwake za'a kawo maka ko kunun kanwa?"
Bakura ya yi firgigit. ya dubi yaron ya maimaita abunda yaron fada "dan wake, kunun kanwa?"
Bakura ya yi minti biyu ya na tunanin menene ma dan wake, yaya ma kunun kanwa yake?
Yaron ya sake cewa "yanzu akaKai ka fi cancanta 1

Na

JUT



0️⃣4️⃣

Bakura ya yi murmushi ya cewa yaron "yaya sunanka?"
Yaron ya ce "sunana Yahuza."
Sai Bakura ya ciro Naira dari biyar ya miqawa Yahuza. Ya ce "je ka ka sayi kunu kasha sadaka, sauran ka bawa almajirai 'yan uwanka."
Yahuza ya karba cike da murna ya na godiya.
Ya ce "ai gidanmu ne ni ba sai na saya ba sai dai in b'oye in yi dinkin sallah."
Bakura ya zabura ya ce "gidanku daya
Sajida kenan?"
Yahuza ya ce "yayata ce uwa daya, uba daya."
Sai Bakura ya yi turus, ya dubi Yahuza ya ga shi kamarsa daban, Sajida kamar ta daban.
Ya fada a ransa "to lallai kama ce kawai amma ba had'in Sajida da Zuhuriyya."
Bakura ya yi shiru can ya sake tunano fuskar Sajida ya taluna ta Zuhuriyya ya tabbatar sak kamarsu daya, sai ya girgiza kai.
Ya ce a ransa "ruwa baya tsami banza dole da wani boyayyen al' amari a nan."
Yahuza ya katse Bakura daga tunanin da yake yi, ya ce ga Babanmu nan ma ya fito."
Bakura ya dago da sauri ya dubi kofar gidansu Sajida sai ga wani tsoho a tsaye dauke da tafkekiyar dorina a hannunsa ta dukan almajirai. Daga ganin fuskarsa ba wasa, tsoho ne wanda baya son wargi.
Yahuza ya dubi Bakura ya ce "karka fada masa ka bani kudi dukana zai yi, zai ce ni na roqe ka, ya hana mu karbar kudi a hannun baqi."
Bakura ya yi murmushi ya ce "ba zan fada masa ba Yahuza."
Baban Yahuza ya kwalla masa kira, ya amsa ya tafi da sauri wajen mahaifinsa.
Mahaifin Yahuza yą dube shi cikin bacin rai da rashin sakin fuska, ya gyara dorinarsa tsaf tafka kawai yake so ya fara yi. Ya ce "ka san shi ne da za ka je ka naniqe masa, ko kiranka ya yi? Ba na hana ka zuwa wajen baqi kana yi musu surutun banza ba?"
Bakura ya qaraso da sauri ya ce "Baba ka da ka dake shi ba laifinsa ba ne, ni na kira shi na tambaye shi."
Baba ya dan saki fuskarsa ya cewa Yahuza "wuce gida."
Yahuza ya arta gida da gudu, dan har ya saddakar yau sai ya sha duka.
Baba tsoho har yanzu fuskarsa babu walwala ya dubi Bakura ya ce "yaro ina ka ke tambaya ne?"
Bakura ya ce "mahaifan Sajida na ke nema"
Wannan tambayar ta bawa Baba tsoho mamaki, ya dago da sauri ya dubi Bakura. Ya ce "kamar yaya mahaifan Sajida kake son gani, me ya faru?"
Ganin yadda tsohon nan ya razana, ya dimauta shine yasa Bakura ya kasa tambayar kwakwab din nan tasa.
Ya sosa qeya ya ce "an ce min kai ne Babanta ko?"
Baba ya ce "kwarai kuwa."
Bakura ya sake cewa "Babanta wanda ya haife ta ko?"
Baba ya tsuke fuska ya ce "kamar yaya?"
Bakura ya yi ajiyar zuciya ya ce "Baba abunda ya sa nake wannan tambayar ina da dalilina ka yi hakuri a hankali zaka ji komai. Shin mahaifiyar yarinyar nan Sajida ta na raye?"
Baba ya ce "ta na raye in dai ba wannan fitowar ta yanzu-yanzu ba rai yayi halinsa, dan yanzu na bar ta tana juya kunun kanwa. Me kake so ka ji ne yaro? Idan wani bayani ka ke da shi ka fada mana in ji, me ke tafe da kai?"
Bakura ya nisa sannan ya ce "Baba ba komai ba ne, sai dan ina son na sanar mu ku cewa ku na tufka ne wani ya na warwarewa. Ku na yiwa 'yarku tarbiyya wani ya na warware muku, magana na ke akan 'yarka Sajida da Abdul majid."
Sai tsoho ya dauki dogon salati ya ce "au, har yanzu Abdul majid bai rabu da yarinyar nan ba? Duk irin yaqin da mu ka yi da shi a baya. Lallai yau sai na lahira ya fita jin dadi."
Ya juya a fusace zai shiga gida.
Bakura ya tsayar da shi ya ce "na fada maka badan hankalinka ya tashi ba, haka kuma ba dan ka daki Sajida ba, sai don ka sake saka ido ku raba su. Duka ko zagi ba shine a'ala ba, ku yi mata nasiha kuma a karbe wayar hannunta don idan an hana ta fita ai ga waya. Ina da zafin rai kamar ka amma ban cika duka ba ko kuma ince ban taba dukan 'ya'yana ba, ina da tsoratarwa, ina yawan yi musu nasiha da wa'azi

Please Login or Register in order to submit comment