Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kowa ya fashe da kuka, musamman Bakura, ji yake zuciyarsa na tafasa tamkar za ta fice, saboda tashin hankali. Ya sunkuyar da kai qasa sai hawaye ke ta shatata. Ya damqe kai dam da hannayensa guda biyu yana jinjina ikon Allah mai yadda Ya so Yake tsaro rayuwar bayinSa.
Malam Yakubu ma hawaye yake yayin da kalaman Sajida ya ji kamar an watsa wuta a zuciyarsa. Ya yi gyaran murya ya ce, "Sajida, hakika za ki ji ba dadi lokaci guda a tare ki a ce iyayenki da kika dauka su suka haife ki ba iyayenki ba ne na gaskiya.To amma sai ki duba ki ga wanne irin riko suka yi miki, wanda ya sha bamban da na dan da suka haifa a cikinsu. Kin ga ai ba bambanci, bambanci daya ne Allah bai kaddaro ta jikinmu za ki tsaga ki fito ba, wannan kuma Allah ne ke tsarowa kowa daga cikin wance, wane zai fito. Domin uwar wani, ko uban wani baya haihuwar dan wani. Allah ya kaddaro Zuhuriya ce za ta haife ki, bayan tsawon shekarun da ta yi ba haihuwa, ta same ki ashe mu ta haifawa ta mutu ta bar ki. Mu ka ga ba anmfanin sanar miki gaskiyar al'amari, saboda ba komai zai qara miki a rayuwarki ba sai damuwa, daman da ace iyayenki na raye ne sai mu kai ki ki gansu, to yanzu ko mun fada miki basa nan, duk da mun san komai dadewa wata rana za ki ji labari, idan na mutu ko Furera ta mutu. Dangin da kike cewa ba a nuna miki ba, ai duk dangin Furera da kika sani sune dangin mahaifinki, kasancewar uwa daya, uba daya suke da mahaifinki Malam Yahuza. Garinku da kike kira ba akai ki ba, ai Shanono ne garinku na ainahi, Yaya Yahuza yawan almajiranci ne ya kai shi can amma ba ku da dangi a garin. Dangin mahaifiyarki kuwa da ba a nuna miki ba, ba da gangan müka qii nuna miki ba, ba mu san su ba ne, kakarki Iya Azumi ita kadai ce a Cinkilawa, ita ma tun ranar da aka taho da ke ba a sake jin labarin inda take ba, domin ita ma mijinta da take zama dominsa a Cinkilawa ya rasu jim kadan bayan mutuwar mahaifiyarki. Ba mu taba sanin Mangono ba, balle mu kai ki wajen dangin baban Zuhuriya. Sajida, ki yi hakuri ki yafe mana kada ki ga laifinmu wajen 6oye miki boyayyen sirrin daya bayyana yanzu. Har yau ban daina jin tamkar ni na haife ki ba."
Kowa hawaye yake har yanzu, babu wanda ya iya cewa komai har zuwa lokaci mai tsawo. Kowa yana saqawa yana jujjuya wannan lamari a zuciyarsa.
Sajida ta fada ta sake maimatawa a ranta Zuhuriya Super Market, ashe ni sunan mahaifiyata ce ban sani ba na ke shiga ina fita koda yaushe. Allah cikin ikonsa ya jarrabe ni da tsananin son Zuhuriya Super Market, komai zan siyo can nake zuwa, ko an hana ni fita can zan aika Yahuza ko almaijirai su yi min siyayya. Allahu Abkbar! Jini daya ba wasa ba ne. Ta sharbe hawaye ta dago da kanta ta duba Bakura, yayin da ta ji wannan tsananin tsanar da qululun baqin cikin da ya tokare a wuyanta tun ranar da ta fara ganinsa a rayuwarta yayi 'zuguf" ya fada, ma'ana ta ji ta daina tsanarsa, ta ji tamkar ya zama dan'uwanta na jini. Idan ta dube shi sai ta ji tamkar ta ga Zuhuriyarta.
Zahra kuwa babu abun da take jujjuyawa a ranta sai tsananin mamaki, ta sake gasgata maganar mahaifinta da ya dage da cewa shi dai fa ya ga mai kama da Zuhuriyarsa. Duk da rashin tarbiyarta ya nace mata ashe shi ya san abun da yake gani, domin shi kadai ya san Zuhuriyya mu ba mu san ta ba. Abba yana son Zuhuriya don haka ban ga laifinsa ba da ya auro mai kama da ita ba."
Samira ma a ranta nanatawa take tana sake gasgata gaskiyar Bakura, a da ta yi tunanin ya so ya kara aure ne kawai ya fake da cewa ya ga mai kama da Zuhuriya, ashe gaskiya ne Sajida 'yar Zuhuriya ce ta cikinta, don haka kamarsu daya sak.
"To bayan Bakuta ya gane Sajida 'yar Zuhuriya ce menene matsaya Sajida a wajensa'? Menene matsayin aurensu kuma?"
Wadannan tambayoyi Samira ta jero a ranta, ta na zaune tana jiran amsoshinsu kafin a tashi daga taro.
Bakura ya dago da jajayen idanuwansa ya yi Sajida duba na tausayawa da kulawa ya girgiza kal, Sannan ya fara magana cikin wata marainiyar murya sanyayya. ya ce "Sajida, hankalina ya kwanta yadda ba zan iya kwatanto yadda zuciyata ta washe ba a sakamakon da aka tabbatar min cewa ke 'yar Zuhuriya ce ta cikinta. ldan na kalle ki sai in ga tamkar na ga Zuhuriya, haka Idan na ji muryarki. Hakika Allah Ya amsa addu'ata ya Yaye min kokonto da dimuwar da na shiga wajen tantance meye alaqar ki da Zuhuriya har ku kayi kama haka. Ban yi karya ba, ban yi kuskure ba ashe ke jinin Zuhuriya ce.Na rantse da Allah tun lokacin da aka sanar min Zuhuriya ta rasu wani abu ya taso ya tokare min a kirji bai taba sauka ba, sai yau na ji ya diro tsakiyar kirjina da na ga 'yar Zuhuriya ta cikinta, ba zai sauka qasa ba gaba daya, sai ranar da na mutu na hadu da Zuhuriya a lahira insha Allah a cikin Aljanna.
Haka Allah Ya so, kana taka Allah na tasa, ta Allah kuwa ita ce gaskiya. Mahaifana da na ke shaida muku dazu cewar almajirai ne masu bara a titi yanzu idan ku ka gansu za ku rantse ba su taba sanin wani abu shi talauci ba. Na musu gini na gani na fada wanda a garin Maiduguri ana kwatance da gidan da na gina musu, idan za a zano gidaje na alfarma. Na zuba su a ciki na zuba musu ma'aikatan da za su kula da su. Na zuba musu kayan more rayuwa da abincin da ko shugaban qasa iyakar abun da zai ci kenan. Na hada su da manyan likitocin da za su kular min da laifiyarsu.
Wannan mai tabin hankalin da ku ka sani a da ta canja ta nutsu tana shan magani za ku zauna ku yi magana ta hankali da ita tas, daman ba haukan ne kadai yake damunta ba har da talauci da rashin samun kulawa. Makahon nan mai bara ya daina yawo a titi, duk da har yanzu makaho ne, amma yana zaune waje daya duk inda zai je direba zai kai shi a mota. Qannena biyu, Babagana da Yaana kuwa babu wanda baya cikin daula, na dauki nauyin Yaana da 'ya'yanta duk abun da suke bukata su kirani a waya in turo musu. Babagana ma na ba shi jari yana rike kansa da iyalansa a Kaduna. Iyalan marigayi Hakimin Mangono ma ban manta da su ba a dalilin Zuhuriya ko da yaushe ina zuwa in gaishe su in yi musu alkhairi, ina yi musu aike akai-akai. Me ya yi saura? Babu Zuhuriya, babu wanin Zuhuriya da zan taimakawa. A ganina duk wannan taimakon da nake yi wa iyayena da yan uwana ba zai kai kashi daya a cikin goma da na kudira a zuciyata zan yi wa Zuhuriya ba, amma Allah bai yarda ba. Tsakanina da ita sai addu'a, daman ba ta yi min wannan halascin dan in saka mata a duniya ba. Allah ne kadai zai ba ta ladan taimakon da ta yi min. Yanzu da ba Zuhuriya sai ke 'yarta ta cikinta, ga kuma mahaifiyarta da ta tsugunna ta haife ta, babu abin da zai sa nan gaba ku ce wayyo babu, saboda kamar yadda iyalina ba su taba sanin babu ba kuma insha AIlahu daga rana irin ta yau kun rabu da babu in har ina raye kuma Allah Ya ci gaba da buda min kamar yadda ya buda min a yanzu.
Sajida ban ji dadin maganar da kika yi a cikin kuka ba, kike ambaci ba ki da uwa, ba ki da uba a duniya. Sajida, ina so ki dauka Umma Furera da Malam Yakubu sune iyayenki da suka haife ki, kamar yadda kika dauka ada. Sannan idan kina neman dan uwa to ki dube ni sannan ki juya ki dubi kakarki Innono jininki ce. Hakika da ciwo a ce da ya tashi bai taba ganin kamannin mahaifansa ba ko a hoto ba, to ki kudira Allah bai sa ki gansu ba, sannan ki juya ki duba Innono kakarki idan kina so ki ga kamannin mahaifiyarki saboda kamar su daya sak, amma ke har ki kin fi kama da Zuhuriya, tamkar an tsaga kara babu abin da kika rage ta. Don haka ku uku kamar ku daya. Rokon da zan yi miki shi ne ki cire damuwa kada wannan magana ta dame ki, saboda wanda ya mutu ya mutu kenan baya dawowa. Zuhuriya ta tafi ta bar ni, ta bar ki, ba za ta dawo ba. A da baki san ta ba, dan haka ba kya yi mata addu'a, amma daga rana irin ta yau ki saka su a cikin addu'arki duk sanda kika yi sallah, suna kwance a cikin kabarinsu suna jin ki, soyayyar da za ki nuna musu kenan a duniya.
Daga qarshe tsakanina da ke sai fatan alkhairi da fatan samun ci gaba a rayuwarki. Ki yafe min laifukan da na yi miki, domin na san na 6ata miki rai da aka tirsasa ki ka aure ni, wannan kamar da kuka yi da Zuhuriya ta ja hankalina na ji ba zan iya barin ki ki fada muguwar rayuwa ba, wannan ne dalilina kawai.
Sajida ina yi miki albishir da komawa sabuwar rayuwa wacce za ta fi miki farin ciki da samun nutsuwa fiye da rayuwar da kike ciki a yanzu."
Kowa ya yi wa Bakura duba na rashin fahimta, musamman Sajida, ta yi sauri ta goge hawaye ta ci gaba da tsurawa Bakura ido.
Ya yi shiru kansa a sunkuye a qasa. Can ya dago ya goge gumin goshi ya dubi Sajida.
Ya ce "Sajida, farin cikinki shi ne farin cikina, don haka zan so ki dauwama cikin farin ciki, domin nima in samu nawa farin cikin. Na fuskanta haka duk wanda ya san ki ya san abun da kika fi so a duniya, wanda idan ki ka same shi to a burinki ya cika. Wannan abu kuwa shi ne Abdul Majid."
"Dadadamdam!" Bugun zuciyar Malam, Umma Furera da Zahra kenan. Haka wannan bugun zuciyar ya farwa zuciyar Sajida suka dago da sauri suka dubi Bakura a lokaci guda, yayin da kowa ya zazzare ido, don mamaki.
Hakika Zahra ta firgita da ta ji sunan Abdul majid ya fito daga bakin mahaifinta sai ta ji tamkar yana da labarin wayar da yake yi mata.
Bakura ya katse tunaninta ya ci gaba da cewa,"Na yarda, na amince, ki je ki auri Abdul Majid ku zauna har karshen rayuwarku, in har yin hakan zai zame miki farin ciki a rayuwarki."
Malam da matarsa suka wangale baki, don mamaki mai hade da dimaucewa, yayin da suka zabura a lokaci guda tamkar an muntsine su.
Sajida ta sunkuyar da kanta qasa tamkar mai jin kunya, yayin da kallo daya za ka yi mata ka ga alamar murmushi a fuskarta. Irin wannan mamaki shi ya ruftowa Samira da Zahra, yayin da wani sanyin zuciya ya dirar musu mai hade da hamdala.
"Bakura, me kake fada ne haka? Me kake shirin aiwatarwa? Ka na nufin saboda Zuhuriyya ce ta haifi Sajida, kana ganin aurenka ya haramta da Sajida?" In ji Malam.
Bakura ya daga hannu alamar Malam ya yi shiru, su ka zuba masa ido kawai.
Ya yi dan murmushin karfin hali Ya ce, "Sajida, baki da idda a kanki, dan haka ki kirawo min Abdul majid ya zo mu zauna mu yi magana idan ya amince zan aura miki shi, kuma na dau nauyin kayan lefe, kudin sadaki, gidan zamanku da motar hawanku da garar da za ku ci har tsawon shekaru. Zan ba shi jari don ya kula da ke, zan dauki nauyin ci gaba da karatunki, idan kina so ki ci gaba, domin ina so ki dauwama cikin farin ciki"
Bakura ya juya da sauri yayin da ya daina duban Sajida.
Kwalla ta cika masa ido ya ce, "Ina fatan Malam da Umma Furera za ku gafarce ni, ku gafarci Sajida a kan hukuncin da na yanke, na fi kowa sanin dalilina. Hakan da na yi shi ne ya fi alkhairi a gare ni da ita Sajidar da ku kanku."
Umma Furera ta bude baki za ta yi magana, Bakura ya dakatar da ita ya ce kada ta ce komai, sai ta koma ta gyara zama ta zuba musu ido.
Iya Azumi ma ta yunkura za ta yi magana Bakura ya dakatar da ita itavma.
Zuciyar Malam ta fara tafasa, ya ji kamar zai kurma ihu, don tashin hankali daga dukkan alamu hukuncin da Bakura ya yanke bai yi wa 'yan uwan Sajida dadi ba.
Sajida ta mike, yayin da take tafiya a hankali ta shiga daki ta dauko gyalenta, gami da turo jifgegiyar akwati shaqe da lefe ta fito ta juya ta dubi mahaifinta ta sake juyawa ta dubi kakarta, ta juya ta dubi Zahra da mahaifiyarta, yayin da su dukka suka zura mata ido tamkar hoto.
Ta juya ta dubi Bakura, sai ya kawar da kai gefe bai dube ta ba. Ta yi ajiyar zuciya gami da sharbe hawaye. Ta qarasa bakin qofar fita, sai kuma ta juyo ta dubi mahaifanta babu wanda ya ce da ita uffan, ta juya ta fice.
Bakura ya dubi Usman ya ce ya je ya ce da Lurwan direba ya kai Sajida gida. Da Sajida za ta tafi, maimakon su Samira su ji ba dadī, amma sai kowa jikinsa ya yi sanyi.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment