Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

matsala wajen iya girki da tsaftace gida. Babbar matsalarki itace mummunan tunani da tabarbarewar fahaimta akan kishiya, shi yasa hira ta da ke ba ta dadewa domin daga an fara labari sai ki fara maganganu ki na koke-koke dan haka ni yanzu zan bar miki gidan idan kin gama kukan can bayan sallar isha'i zan dawo."
Ya juya zai fita, ta sake zubo da hawaye.
Ta ce "ashe daman zance ka fara zuwa shiyasa jiya ba ka yi sallar magaruba da isha'i a masallacin qofar gida ba? ka je ka dawo da wata shadda ashe ita ta ba ka. Ai ba a nan kasar ka ke siyan shaddar da ka ke sawa ba."
Tsawa ya daka mata wacce ta razanar da ita ko tari ba ta sake yi ba, ya fara magana cikin fushi. Ya ce "ya ishe ni haka, ba na son ki qara daga wannan maganar, labarin da na ke niyyar baki na fasa kuma kar ki sake tambayata."
Ya juya a fusace ya fice, ya zabi dankareriyar mota wacce ba ta jiya ba ya shiga ya tafi. Bai tsaya a ko ina ba sai a kofar gidan malam Yakubu. Kamar jiya yauma anan suka yi Sallar magaruba suka yi karatu sannan su ka yi sallar isha'i sannan kowa ya watse. Sai Malam da Bakura su na ta zuba hira.
Yahuza ne ya fito dauke da farantin abinci ya ajiye a gabansu, languna ne na tuwo da miya, Yahuza ya durqusa ya gaishe da Bakura cike da fara'a da tsananin saka ran yau ma zai sami wata dari biyar din. Ya sami gefe ya zauna ya ci gabaKai ka fi cancanta 1

Na

Jut


0️⃣8️⃣

Malam Yakubu ya gallawa Yahuza harara ya fada cikin tsawa "tashi ka shiga gida. Waye ya ce ka zo ka zauna anan?"
Sum-sum Yahuza ya miqe har ya wuce zaure ya fito da sauri
Ya ce "ah Baba na manta Sajida ta ce ka ba ni kudin igiyar leko(mosquito coil) in siyo ma ta."
"Malam Yakubu ya b'ata rai kai ka ce ruwan zafi aka watsa masa.
Ya ce "ba zan siya ba, ai na fada ma ta jiya, igiyar lokon kwana biyu ne, domin guda biyu na ba ta amma ta qi ji ta kunna dukka biyun jiya, daya a wajen kanta wata a wajen qafarta wai ita isasshiya. Igiyar lekon biyu naira goma sau biyu a rana daya sai ka ce buga kudin nake yi. Dama guda shida na siyo jiya na miqawa Sajida biyu, na ce ma ta jiya daya yau daya.
Na miqa ma ka guda biyu, na kai biyu dakinmu mu ka kunna daya, yau zamu kunna daya. Ko kaima dukka biyun ka kunna jiya?"
Yahuza ya zabura. Ya ce "a'a ni saura daya da rabi da asuba na tashi na kashe dan kar ta qare."
Malam yayi murmushin jin dadi. Ya ce "yauwa ka ji yaro mai tattali haka ake so ka ga kai kwana hudu za ka yi kana kunnawa, ita kuwa Sajida yau idan za ta mutu don cizon sauro babu mai ba ta maganin sauro a gidan nan. Ka je ka ce ma ta ba zan siya ba, ai ta kwana biyu na ba ta kuma kar ta sake damuna."
Bakura ya ciro kudi naira dubu zai bawa Yahuza malam ya hana. Ya shiga roqar Malam, ya na yi masa magiya ya taimaka ya bari Yahuza ya siyo shaltos, malam ya fisge kudin daga hannun Bakura ya tura masa a aljihun gaban rigarsa.
Ya ce "Bakura ba za mu yi musu da kai ba ko jayayya tunda na ce ka bari ka bari, Sajida zuma ce sai da wuta ta na da taurin kai da rashin jin magana. Kuma laifin mahaifiyarta ne, ita ta shagwabata ba'a kwabarta, ada muna ganin kamar yarinta ce sai da ta girma na ga tsiwar ta yi yawa sannan na tabbatar tantiriya ce sannan na fara saka mata takunkumi."
Bakura ya yi shiru kawai zuba tagumi."
Malam ya dubi Yahuza ya daka masa tsawa. Ya ce "tsayuwar me kake yi ne har yanzu? Na ce ka je ka fada ma ta ba zan siya ba."
Yahuza ya shiga gida da sauri.
Malam ya ce "shi kuma Yahuza bashi da matsalar rashin jin magana amma fa akwai shi da kwadayi da son kudi kamar wani quda idan ya ga koko haka ya ke wajen kwadayi."
Bakura ya kwashe da dariya ya ce "haka yara suke a ko' ina ma, sai dai fatan Allah Ya shirya mana zuriyarmu baki daya."
Malam ya ce "amin summa amin."
"Bakura bismillah ga abinci fa an fito mana da shi, tun jiya na ce daga yau abincin mutum biyu za'a dinga zubawa ni da kai." Malam ne ya fada.
Bakura ba zai iya cin abincin gidan Malam ba, ga kunyar malam da nauyinsa yana ji.
Malam ya jawo farantin abinci ya bude tuwon dawa ne da miyar kuka ta sha daddawa da wake amma ba nama. Babu shakka Bakura ma'abucin son miyar kuka ne, to amma tambayar ita ce ta yaya aka sarrafa miyar shine bai yarda ba, ma'ana tsaftar mai girkin, da tukunyar miyar da ruwan da aka dafa miyar, da tsaftar dan aiken da ya siyo kayan hada miyar shine babban tashin hankalinsa. Domin Bakura mutum ne mai tsaftar gaske ga yawan tsantsani. Sannan miyar kukar da ake yi masa a gidansa ta sha bamban da irin wannan kasancewar sai an jefa kaji biyu ko uku a cikin ruwan miyar sun dahu luguf, qashin ya sallube sannan atsame qashin sai a kada kukar a kai.
Malam ya sake maimaitawa "Bismillah Bakura ga abinci, kuma kar ka ce min ka qoshi domin anan mu ka yi magriba ka ga kenan ba ka ci abinci a gida ba. Sai dai idan ba za ka iya cin abincin almajirai ba marar kaji da naman talo-talo."
Bakura ya yi dariya ya ce "haba malam miyar almajirai, nima ai almajiri ne sai dai kawai na ci abinci da yamman nan na qoshi."
Malam yayi turus da alama bai ji dadi ba. Ya ce "bari na kira Yahuza ya karbo ma ka balangun naira dari a zuba maka a miyar ko dan ka ga babu nama shiyasa ba za ka ci ba."
Bakura ya zubura ya ce "a'a malam ka bari kawai, ba dan rashin nama ba ne." Gaban Bakura yayi mummunan faduwa saboda har ga Allah ko ba'a bude kwanon abincin ba ya san ba zai iya ci ba.
Ya ci gaba da cewa "wallahi ba rashin nama ba ne.Ni waye da zance dole sai da nama a abinci zan ci, nawa rayuwar duniyar take? Na qoshi ne kawai."
Malam ya yi zugum kamar mai tunani da alama bai ji dadin qin cin abincin da Bakura ya yi ba. Can ya dubi Bakura.
Ya ce "ba zan boye maka ba d'ana, amma ban ji dadin qin cin abincin nan da ka yi ba, ai sai ka saka albarka ko ba za ka ci da yawa ba. Ni da na ke ganin ka zama dan gida, zá ka iya zuwa ka ce min Malam yau abu kaza nake so a dafa min, in saka Sajida ta dafa maka ko menene ma."
Bakura ya tambaya cike da zumudi."Sajida ta iya girki ne?"
Malam ya ce "ai fiye da shekara biyar Sajida ta hutar da mahaifiyarta, girkin dare da rana, safe da yamma ita take yi sai dai idan ta tafi makaranta a lokacin da take zuwa makaranta kafin a cire ta. Ita mahaifiyarta ta na fama da abincin siyarwa yaushe za ta samu damar dafa mana abincin gida. kwalla-kwallar kunu da daro-daron dan wanke take dafawa ta sayar a rana."
Babu abinda Bakura ya tuna da aka ce masa Sajida ce ta dafa sai lokacin da Zuhuriyyarsa take dafa masa tuwo miyar kuka sai yaji kamshin miyar kuka iri daya da na Zuhuriyya. Bai san sanda ya sa hannu suka fara cin tuwon ba, a idonsa ya na tuna yadda Zuhuriyya take kada miyar komai a cikin tsafta don haka bai sake jin kyamar miyar da yake ci ba. Malam ya ji dadin ganin yadda Bakura ya ke loma ba tare da kyama ba. Sai ci suke har sai da su ka kusa cinyewa. Sannan Bakura ya cire hannunsa.
Malam ya cinye tas ya sude kwanon sannan su ka wànke hannu, bayan sun taba 'yar hira Bakura ya ce da Malam zai koma gida sai küma gobe idan Allah ya kaimu.

Yauma kamar jiya Malam ya tsayar da Bakura ya shiga gida ya fito dauke da turare. Ba laifi ya na da kamahí amma ba irin designer da Bakura yake fesawa ba ne shi da iyalinsa.
Bakura zai ki karba, malam ya ce ba zai yiwu ba sai ya karba dole. Bakura yayi godiya ya karba ya tafi zuciyara cike da mamakin halin kyauta irin na Malam Yakubu.Tabbas ko ba'a fada ba malam Yakubu ya na matukar kaunar Bakura a ransa, Bakura ya shiga sake-saken shin shi kuwa wacce irin kyauta zai yiwa wannan bawan Allah don ya fitar da shi da iyalinsa daga cikin qangin talauci da wahala?
Amma kuma can a cikin ransa ya na son ya jira zuwa wani lokaci mai tsawo don ya sake tabbatarwa shin Malam saboda Allah ya ke kaunarsa, yake yi masa wadannan kyaututtukan ko don ya linka masa ne a gaba?
Samira ta lura yau ma Bakura ya shigo da leda a hannunsa ya wuce dakinsa don haka ta sake tabbatarwa lallai maigidanta ya Shiga sabuwar rayuwa ba irin tasa ta da ba. Idan hankalinta yayi dubu ya tashi, sai zagaye take cikin gida ta rasa wanda zata tara da wannan matsalar ya share mata hawaye sai shi kansa Bakura.
Ya shiga dakinsa fiye da awa guda bai fito ba, a tunaninta wanka ya shiga yi zai fito ya ci abincin don haka ta ci gaba da jira, ta ji shiru bai fito ba, sai ta shiga dakin ta iske shi har yayi wanka ya kwanta ya kashe fitilar dakin.
Ta tura kofar ta shiga can cikin dakin yayin da duhu ya hana ta hango shi. Ta laluba zata kunna fitilar dakin sai ta ji muryarsa.
Ya ce "kada ki kunna min fitila na- riga na kwanta."
Ta laluba ta qarasa jikin gadon ta zauna a gefe cikin sanyi jiki ta ke magana.
Ta ce "Abban Zahra tun dazu ina daning area ina jiranka ka zo ka ci abinci ashe shigowa kayi ka kwanta."
Ya fada cikin gadara "eh na kwanta, a qoshe nake."
Ta rusa kuka kai ka ce mutuwa ya fada mata.
Ta ce "yau me zan gani, yau me yake shirin faruwa da ni? Me nayi na kuskure da har haka yake faruwa da ni, wacece wannan mai matsayi a wajenka wacce har ta fi ni?"
Bakura ya ji hankalinsa ya tashi matuka, yayi figigit ya yaye bargon da yake ciki a lullube. Ya kunna fitiila ya matso gare ta ya na tambaya cike da tashin hankali.
Ya ce "Samira lafiya, me yake faruwa? Dan na ce na qoshi shine abin da zai sa ki duki kukan irin na mutuwa haka? Mu je dining in ci abincin, shikenan?"
Ta sassauta da kukan ta fara goge hawaye. Ta fice ya na biye da ita a baya su ka fito zuwa danning area da yake a babban falo, ya jawo kujera ya zauna. Ya dubi teburin yaga abinci ne burjik kala-kala kamar kala shida. Ga taliya fara da miyarta, farfesun kaji, farfesun kayan ciki, ga gasasshen kifi, ga hadaddan salad, Gefe kuma yankakkun kayan marmari ne wato (fruit Salad) ga lemuna nan kala-kala woto (Juices) nikekkiyar abarba ce da markadaddiyar kwakwa kamar yadda ta san Bakura bai cika son lemon kwali ba ko na gwangwani sai dai ta siyo kayan marmari ta markada ta sarrafa masa a gida.
Yayi murmushi ya dube ta wacce ke tsaye qiqam, ido ya yi mata jawur don kuka da ta sharba, ta cika ta yi fum kamar za ta fashe don fushi.
Ya ce "Gimbiya zauna mu ci mana, yaya za ki tsaya min a kai ?"
Ta jawo kujera a can gefe ta zauna.
Ya yi dariya. Ya ce "haba Gimbiya yau ba za ki zauna a kusa da ni ba ma, balle a bani a baki, ki dawo nan kusa da ni mana."
Ta girgiza kai ta ce "nan ya isa ba sai na qaraso ba."
Bakura ya miqe ya jawo kujerarsa kusa da ita ya zauna ya ci gaba da lallashinta ya na mata magana mai kwantar da hankali har sai da ta saki fuskarta ta fara cin abincin.
Bakura zura abincin nan yake yi a cikinsa kawai ba don ya na jin yunwa ba, sai don gudun bacin ranta. Duk lauma daya da zai kai bakinsa sai ya ji malam Yakubu da iyalinsa sun fado masa a rai, sai ya ji inama zai iya kwashe abincin nan ya kai kofar gidan malam su hadu su ci tare. Sai yake ji kamar rashin adalci ne ya zo gida yana cin dadi shi kadai. Domin Malam ya zame masa tamkar dan uwa na Jini.
Ya na ci yana tunani, daga Samira ta harare shi sai ya hau yi mata hira don kada ta ci gaba da zarginsa. Bayan sun gama cin abincin ta kwashe kwanukan ta kai kicin ta goge kan teburin tsaf sai ta kunna masa wani wasan kwaikwayo da tasa aka suyo masa yau, wato fim din Boloko a Kano.
Su ka koma kan doguwar kujera su na kallo cike da nishadi su na kyalkyala dariya, idan maganar budurwa ta fado ma ta a rai sai ya ga ta tsuke fuska. Mamakinta ya rufe Bakura ya dubeta.
Ya ce "Samira lafiya kina dariya kuma kina fushi?"
Kan ka ce kwabo idanuwanta sun cika da hawaye, ta yi narai-narai da ido.
Ta ce "budurwarka na tuno, wacce ta fara dauke maka hankali kwana biyu."
Ya gyara zama ya yi marmushi ya dubi ta.
Ya ce "da ban yi niyyar fada miki ba, har abada ba za ki ji wannan labarin ba saboda abunda kika yi min dazu. Baki da wayo ashe har na ke yi miki kallon mai wayo, ai ya kamata ki tsaya ki daure ki ji karshen darin sannan ki dauki mataki, amma daga farawa kin fara surutu ga shi ke baki fahimci komai ba kin shiga damuwa da sumbatu ki na kuka. To, bana son irin haka daga yau don ki sani."
Ta matse hawaye ta ce "na yi kuskure Sweety, zan kiyaye nan gaba."
Ya yi murmushi ya ce "Allah ya yi miki albarka.
Kamar yadda kika san halina, ba na boye miki komai yau idan na hadu da wata na yaba da hankalinta na ji ina son in aure ta a ranar zan sanar miki. Me za ki iya yi min, ko za ki dake ni ne, ko kuwa za ki zage ni?"
Samira ta amsa da "A'a." Ya ce "ke kin san bana boye miki komai, to amma me ya sa kika fara zargin na ci amana ko ina miki nuku-nuku?
Samira tayi kulu-kulu tana muzurai, ba tare da ta san amsar da zata bashi ba. Ta na rayawa a ranta tabbas ta yi kuskure, da batan basira wajen zartar da hukunci akansa. Ya yi shiru na wani dan lokaci sannan ya ce "wata yarinya ce mai suna Sajida, mai kimanin shekaru goma sha shida. Iyayenta sun yi mata tarbiyya amma wani saurayi na kokarin ya russ mata rayuwa. Na yi kokarain haduwa da mahaifinta na sanar masa, Alhamduliliahi ya dauki kyaukykyawan mataki ya hana ta fita. Mahaifin Sajida Malam Yakubu babban malamin karatun alkur ani ne, don haka na zama almajirinsa nake daukar karatu a ranakun Jumaa, asabar da lahadi zan dinga zuwa tsakanin sallar magriba da isha' i. Dadin abunda na yi masa ya sa dúk sanda na je sai yayi min kyauta, shine kike ganina da leda.
Hankalina ya na tashi matuka akan yadda naga a boye Sajida ta na zaluntar iyayenta shine yasa na kasa samun nutsuwa ina fargabar kada dai ace Zahra ma haka take yi mana."
Samira ta dafe kirji ta fada cikin fargaba
"Abban Zahra ina Yagana ta sani ko wa ta sani da za ta fita ba'a sani ba? Abban Yagana kai kanka ka fi kowa sanin halin Yagana, ba za ta yi haka ba."
Bakura ya ce "tabbas na san Yagana, amma na san zamani ya canja dan haka ki taya ni saka ido sosai ki taya ni da yi mata nasihohi ta sigar tatsuniya ko labaru masu dauke da gargadi da darasi ki tsoratar da ita."
Samira ta yi ajiyar zuciya ta sunkuyar da kai kasa. Ta ce "zan yi mata nasiha Allah må zai kiyaye ta insha Allah ba zata bamu kunya ba."
Tsawon lokaci mai dan mai nisa babu wanda yayi magana a cikin su,sai Samira ta dubi mai gidanta ta yi murmushi ta maqale murya. Ta ce "Sweety, yarinyar nan nake tunani Sajida, ka ce shekarunta ba su wace goma sha shida ba ta kuwa gama sakandiri?"
Ya ce "mahaifinta ya ce sun cire ta daga makaranta saboda saurayin ta na S.S 2, kuma duk da talaucinsu makarantar kudi mai kyau ya saka ta mai Suna EL-LITININ COLLAGE.
Wani abun daya sake daure min kai shine kamanin Sajida ya tsaye min a rai, ya zame min wani mummunan fami a cikin zuciyata."
Ra-ga-gas! Haka qirjin Samira ya buga cikin karkarwa murya da fargaba. Ta ce "Abban Yagana ban fahimce ka ba. kamar yaya kamaninta sun zaune maka a zuciya?
Abun mamaki sai ta ga hawaye ya na zubowa daga Idanuwansa.
Hanakalinta ya sake tashi ta fada a gigice "Abban Yagana kuka kuma naga kana yi. wai meke faruwa ne?"
Ya fada cikin lallausar murya mai hade da Jimami. Ya ce "yarinyar kamarsu daya da Zuhuriyyata."
Samira ta zuba masa ido ta na kallo, kallo irin na anya kuwa ba tunanin zuhuriyya ba ne yayi masa yawa har ya fara yi masa gizau?"
Ya juyo ya dubi Samira yayi murmushi ya ce "yaya ki ka zuba min ido kina kallona kamar kina kallon tababbe? Ina cikin hayyacina naga mai kama da Zuhuriyya sak. Shine ma makasudun da ya sa na dage na nemi gidansu don naga mahaifanta. Na ga uwar, naga uban, naga qaninta basu da alaka da Zuhuriyya. Na damu na shiga rudani, fuskar yarinyar nan ta tuno min da Zuhurriya, sai in ji gabana ya yanke ya fadi saboda kamar fuskar Zuhuriyya ce sak, ke har maganarsu iri daya ce sak."
Samira tayi ajiyar zuciya sai yanzu hankalinta ya kwanta da ta ji dalilin daya cika maganar yarinyar nan. Hankalinta ya kwanta, ranta yayi fari kwal musamman yadda ta ga bai yabi tarbiyyar yarinyar ba ta san ba za ta taba burge shi ba.
Nan da nan ta hau kisisina ta na fitar da kalaman bada hakuri da kwantar da hankali.
Ta ce "kama ce kawai, kuma daman a duniya ba'a rasa irin wannan kamar."
Bakura ya mike tsaye, kallon ya fita a ransa hakika ya fara shiga yanayin daya saba shiga idan tunanin Zuhuriyya ya juyo masa. Babu wata kalma, babu wani mahalukin da zai iya hana shi zubar da hawaye da dogon tunani. Sai yayi ta addu'a da zikiri sannan abun yake fada masa. Don haka Samira ta dade da sanin haka, amma bata barinsa haka tana kokarin zama da shi ta bashi baki, ta nuna masa ta fi shi damuwa akan haka.
Ya mike ya nufi dakinsa cikin sauri ta kashe kallon ta bi shi, su ka raba dare tana fada masa maganganun kwantar da hankali, shi dai yayi shiru yana sauraranta bai ce da ita uffan ba. Da ya gaji da kwanciyar sai ya tashi yayi alwala ya dinga salloli ya na addu'a har asuba.


Kwanci tashi Bakura ya shafe watanni hudu yana zuwa daukar karatu wajen malam Yakubu, a sati sau uku bai taba fashi ba. Haka sabon zumunci da shakuwa ya dasu a zuciyoyinsu. Abu kamar wasa har abun ya fara bawa Bakura kunya domin kusan duk haduwar da zasu yi da Malam Yakubu sai ya dauko wani abu ya bashi, kuma ya tilasta masa dole sai ya karba. Ga uwa uba hidimar abinci da yake sawa a dafa masa duk sanda suka gama karatu ya kuma tilasta masa sai ya ci, amma har rana irin ta yau Bakura bai taba ido hudu da Sajida ba balle mahaifiyarta sai dai yakan jiyo muryarsu sama-sama daga cikin gida.

Wata rana, ranar Litinin da yamma Bakura ne ke tafe cikin jibgegiyar motarsa Jeep Murano. Gefansa kuma babbar 'yarsa ce Zahra, sanye take da qaton hijabi. Babu abin da za ka iya gani a jikinta

Please Login or Register in order to submit comment