Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gida da direbobinsa don haka tun kafin su Malam su sauka daga jirgi direbansa ya zo yana jiransu.
Su na sauka daga jirgi ya kwaso su ya kawo su gida. Bayan sun gama hutawa a kwana daya washegari suka kama karatu a cikin plaza, suka yi ta saukewa qur'ani su na maimaitawa.

*** *** ****
Zahra da mahaifiyarta Samira kuwa su na kano Su na ta faman shirye-shiryen walima. Don qarfin hali har wani dan qaramin katin gayyata Zahra ta buga ta rarrabawa qawayenta na makaranta.
Ranar asabar ne ranar da za'ayi walimar. Don haka ranar Juma'a da yamma washegarin ranar da za'ayi. Samira ta iske Zahra a falonta a zaune ta na kallo. Ta ce da ita ta je Zuhuriyya super market ta hado mata kayan qamshin girki (spices) kamar curry, thyme, dakekkiyar citta da dai sauransu.
Zahra ta shirya tsaf ta fito caras sanye take da wani dandantsetsen leshinta shudi anyi masa zanen fulawa ruwan goro. kallo daya za ka yiwa leshin ka gasgata tsadarsa duk da daman dallar aka siyi leshin idan aka kiyasta kudinsa zai kai Naira dubu dari da tamanin. Kwararren telan da ya sarrafa dinkin leshin da ace qasar America zata sami labarinsa data dauke shi aiki a kamfanin dinka kaya (English wears). Domin idan ka kalli kayan a jikin zahra sai ka rantse daga kamfani leshin ya fito a dinke. Yankan siket din das a jikinta haka rigar, abinka da marar jiki, doguwa santaleliya kai ka ce taliya ce ke nutso a cikin ruwan zafi, idan Zahra ta na tafiya. Duk da tsayin da Allah yayi mata ta qara da wani cogen takalmi mai tsinin gaske a qafarta shima takalmin kalar ruwan goro ne. Ta nada daurin dankwali a gaban goshi, gashi keyarta kuwa lallausa mai raushi ne ta tufke shi da ribbon ruwan goro. Ta dauki dan siririn mayafi ta yafa a jikinta. Ta na rike da mukullin mota a hannunta.
Samira ta dubi Zahra ta yi murmushi ta ce "baby kinyi kyau yau sosai. Ko za ki bar leshin nan gobe ki saka? Kamar zai fi na gobe kyau."
Zahra ta ce "a'a mama kin manta kudinsu ne? Ai yellow da zan saka gobe ya fi wannan tsada kudinsa da na kiyasta naira dubu dari biyu ne da hamsim wannan kuwa dmdubu dari da tamanin ne. Kin ga ai ba kudinsu daya ba. Allah Ya kaimu goben shima za ki ga yadda zai yi min kyau."
Samira ta ce "Magaji deriba ne zai kai ki ko?"
Zahra ta ce " sabuwar motarki Discussion continues zan tuqa da kaina."
Samira ta ce "ba wai ban yarda da tukinqinki ba ne amma fa har yau mahaifinki bai san kin koyi tuqi ba, ka da ki je wani abu ya faru Allah ma Ya kiyaye ya ce yaya aka yi ma ki ka fita ke kadai?"
Zahra ta ce "Allah ma Zai kiyaye yanzu zan je na dawo."
Samira te ce "Allah ya kiyaye mamana."
Zahra ta saka bakin gilashinta saboda hasken gari, ta sakala hands free a kunnuwanta saboda amsa waya, ta shiga tsaliliyar motar nan mai launin silver nufi ZUHURIYYA SUPER MARKET.
Daf da qofar Zuhuriyya Surper Market ta ja ta tsaya a inda ta dubi gefanta wata baqar mota ce qirar Brama mai bakin gilashi, ko kafi quda na ci ba za ka iya hango abinda yake ciki ba. T
Tabbas ita ma motar ta hadu domin irin sautin kidan da yake tashi daga cikin motar da irin daukar idon da motar ke yi saboda da sheqi.
Kamar yadda shekin motar Zahra take daukar idanuwan masu kallonta har 'yar qarama rigima ce ta tashi tsakanin saurayi da buduwar da ke cikin motar saboda yadda yake kallon Zahra har da leqe.
Ba tare da Zahrar ta san abinda ke gudana ba.
Zahra ta yunkura ta fito daga cikin motar in da ta danna remote alamar ta rufe motar. Ta na fitowa ta fuskanci wasu 'yan mata guda biyu sun fito daga cikin wannan baqar motar, daya daga gaba ta fito daya kuma daga gidan baya. 'Yan matan dukkansu sanye suke da wandon jeans da riga iya gwaiwarsu, sai dan gyale yalolo a maqale a kansu da cogen takalma a qafafuwansu. Nan da nan suka dunguma tare da Zahra suka shiga cikin Super market din. Daga yadda 'yan matan nan biyu suka ga ma'aikanta super market su na dukawa Zahra su na kwasar gaisuwa Hajiya sama Hajiya qasa sun san tabbas yarinyar nan 'yar wani ce a qasar nan. Inda su ka sake tabbatar da hakan sai sanda suka ji ta umarci daya daga cikin ma' aikatan cewar ya samu leda ya je ya zabo mata spices kalą-kala masu qamshi daban-daban kamar roba ashirin ya kai mata mota.
'Yan matan biyu sun ci gaba da zazzagayawa su na zazzabar abinda suke so. Kicibus su ka yi da Zahra a daidai kantar greeting cards. Yayin da su dukka ukun suka duqufa wajen karantawa don su zabi wanda yayi dai-dai da kalaman da suke buqata, kamar daga sama kunnuwan Zahra su ka jiyo mata daya daga cikin 'yan matan ta ce da dayar. " Iyayye, kin ga wani kati wanda yayi daidai da wanda zan bawa Abdulmajid." Jin sunan Abdulmajid ne ya sawa Zahra wata mummunar faduwar gaba ta dago da sauri ta dubi mai maganar. Zahra ta zare bakin gilashin dake fuskarta ta dube ta sosai inda ita ma mai maganar ta tsaya cak ta na duban Zahra yayin da su ka dauki 'yan dakikai ba su daina kallon juna ba kowa ya na qoqarin tuno inda ya san wannan fuskar. Lokaci guda kwakwalwarsu ta sanar musu cewa wannan Zahra ce, kwakwalwar Zahra ta sanar mata wannan Sajida ce. Qara-qara- qa-qa, ga Zahra, ga Sajida. Ya za'ayi kenan'?
Zahra ta yi murmushi ta ce "kamar na sanki, ba ke ce Sajida ba?"
Cikin gadara Sajida ta ce "Sajimajid ce, kwarai ashe kin tuna ni kamar yadda na tuna ki Zahra. Ina neman ki daman tamkar ruwa a jallo. Na dade ina addu' ar Allah ya nuna min irin wannan rana."
Sai Zahra ta ji gabanta ya yanke ya fadi kan ka ce kwabo zuciyarta ta fara harbawa ta na dukan uku- uku.
Ta tambayi Sajida cikin kidemewa "me ya faru?" Sajida ta yi murmushin mugunta ta dubi kawarta Iyayye ta ce "ki taya ni duban yarinyar nan, Ki taya ni fada mata ko ni wacece ko kuma yaya nake. Dan rainin hankali ma wai tambayata take me ya faru? Ba ta ma san me ta yi min ba ko? To bari ki ji Zahra babu yadda za ki yi da ni da Abdulmajid sai dai kallo da Ido babu mai raba mu, ke ko uban daya tsugunna ye haifeni ma sai dai ya yafe min amma ba zai iya hana ni son Abdulmajid ba."
Gaban Zahra ya sake faduwa ta shiga saqe-saqe a ranta "tabbas Sajida ta ji labarin Abdul majid ya na yi min waya ada."
Sajida ta rike kugu sai girgiza take tana huci tana hararar Zahra, tamkar mayunwacin zakin da yaga nama.
Zahra ta juya ta dubi Ibrahim ma'aikacin da yake biye da ita a baya. Ta ce ya matsa ya bar wajen ta na son ta yi magana da qawarta, ya amsa mata cikin ladabi ya tafi da sauri ya bar wajen.
Zahra ta matso kusa da Sajida ta ce "Sajida, wallahi ban san Abdulmajid ba, ban taba sanin yaya kamanninsa su ke ba, ba ni da wata alaqa da shi dan haka ne ma nake mamakin tuhumar da kike yi min a akansa."
Sajida ta ji tamkar Zahra ta soka ma ta mashin wuta a qahon zuci.
Ta fada a fusace "dubi bakin qofar shigowa."
Zahra ta waiga da sauri, sai ta hango wani dan kyakykyawan saurayi a tsaye.
Sajida ta ce "to Abdul majid dina kenan, ki koma ki sake fadawa Babana kin ganmu tare."
Sajida ta kwallawa Abdul majid kira nan da nan ya qaraso in da suke. Ta ce da shi "ga Zahrar da nake fada maka wacce na taba kiranka da wayarta, daga qarshe ta hada min tuggu wajen Baba."
Abdulmajid ya ji gabansa ya yanke ya fadi kamar yadda na Zahra yake faduwa lokaci guda suka zubawa juna ido har wani lokaci mai dan tsawo kowannan su ya na tunani a ransa. Abinda ya fara fadowa Zahra a ranta sai kalmar "inna lillahi wa'inna ilaihi rajiî'un. Yau me ya ke shirin faruwa da ni ne haka? Na rabu da Abdulmajid a waya ga shi na gan shi yau a zahiri?"
Abdulmajid kuwa kan ka ce kwabo farin ciki ya lullube zuciyarsa da Allah Ya nuna masa Zahra a zahiri, kwakwalwarsa ba ta taba kwatanto masa haduwar Zahra ta kai haka ba, ba makawa Zahra itace irin kalar macen da yake burin ya mallaka a rayuwarsa.Tun fitowarta daga motarta tun ma bai san wacece ita ba zuciyarsa ta fara muradinta domin ta cika gaba daya abubuwan da namiji yake bukata a wajen mace. Nan da nan ya ji qafarsa ta kasa daukar jikinsa.Ya kidime ya fita daga hayyacinsa, amma gudun kada Sajida ta gane halin daya shiga sai ya juya da sauri ya fice ya nufi wajen motarsa ya shiga ya zauna ba tare da ya ce uffan ba.
Iyayye ta ce "au daman itace munafukar da kike fada min ta na hada miki tuggu?"
Idan hankalin Zahra yayi dubu ya tashi, nan da nan idonta ya cika da hawaye.
Ta girgiza kai ta ce "actually I don't understand what is happening here...."
Kafin ta rufe bakinta Sajida ta daka tsalle ta kinkimo qaton gwangwanin madara babba wato (giant size) ta datsa mata wajen kaifin a goshi, ko sakon daya ba'a qara ba jini ya wankewa Zahra fuska.
Zahra ta kwalla ihu mai tsanani ta yanke jiki ta fadi qasa. Kafin kiftawar ido Sajida da kawarta Iyayye sun bace daga cikin kantin.
Ma'aikatan shagon kacokan dinsu suka taru su ka zageye Zahra su na mamaki, su na al'ajibi yadda gwangwanin madara zai fado mata a goshi. Daya daga cikin ma'aikanta ne ya ke bayani wato Ibrahim cewar akan idonsa wannan budurwar ta jawo gwangwanin madara ta rotsa ma ta a goshi Sauran ma' aikatan gaba daya suka yiwa Ibrahim caaa
akai su na tuhumar sa da cewar me yasa bai damqe yarinyar ba har ya bari ta gudu?"
Hankalinsu a tashe suka garzaya da Zahra asibiti dan tsayar da jinin da yake zuba, aka kuwa ci sa'a ba a yi mata dinki ba, iodine da plasta aka saka mata aka liqe suka kawo ta gida.
Samira suka iske a falo, ta na ganin goshin Zahra sai ta dauki salati mai hade da kuka dadin dadawa ma bushashshen jinin da ta gani a jikin tufafinta. Abinda ya fara fado ma ta a rai shine ko hadari ta yi a hanya, amma ganin ma aikantan shagon sai ta fara tunanin ko a bakin kantin hadarin ya faru.
Zahraa rungume mahaifiyarta tana rusa kuka, Samira ta zaunar da Zahra akan kujera itama kukan ta fara yi tana tausayin 'yarta tana tausayin kanta, domin arangamarta da Bakura ba zai yi kyau ba dalilin da ya sa ta bari Zahra ta dauki mukullin motarta ta fita ita kadai.
Ga gargadin da yake yi mata cewar ta sa ido sosai akan Zahra, yana fatan, yana kumå addu'a Zahra bata fita ta raqashe a bayan idonsa.
Cikin karkarwar jiki
Samira take tambayar ma' aikatan da suka rako Zahra har su hudu.
Daya daga cikinsu ya ce "ina jin tuntube tayi ta daki jikin kanta gwangwanin madara ya datso mata a goshi."
Daya yayi karaf ya ce "ba gaskiya ba ne babu yadda za' ayi dan mutum ya dan daki kanta gwangwani ya fado, wannan ba abin rufa-rufa ba ne don idan muka rufa mu kuma zai iya shafar aikinmu, idan maigida ya zo zai iya korar dukkan mu ya ce bama lura. Akan idon Ibrahim abin nan ya faru dan haka Ibrahim ka yi bayani."
Ibrahim ya matso ya ce "îna biye da Zahra a baya sai wasu 'yan mata suka hau zaginta sai ta ce da ni in matsa daga wajen zasu yi magana. Matsawata ke da wuya sai na ga daya daga cikin 'yan matan tayi tsalle ta ciccibo gwangwanin madara qato ta kirba mata a goshi amma ko Sama ko qasa ban ga ta inda 'yan matan suka bi suka gudu ba."
Samira ta juya ta dubi Zahra ta ce "wadanne 'yan mata ne waɗannan? Me kika yi mu su haka har da zasu fasa miki kai? Ke da baki da abokin fada tun ki na yarinya. Me kika yi musu har ya tunzura su suka fasa miki kai?"
Zahra hawaye take ba tare da ta iya bada amsa ba.
Ana cikin wannan hali
Bakura ne ya kira wayar Samira tana jin ringing sai ta ce "yauwa ga Abbanki nan ya kira bari na fada masa tunda ni kin qi fada min gaskiya."
Samira na dannawa ko gaisawa basu yi ba ta ji Bakura ya na fada har da kumfa baki, hankalinsa a tashe. Ya ce "wai me yake faruwa ne aka yi min waya aka ce wata yarinya ta fasawa Yagana kai a cikin Super Market? Wacce yariya ce, kuma waye Ubanta a Kano?"
Samira ta ce "yanzun nan su ka shigo min da ita ban ma gama jin abinda ya faru ba. Yagana kuka take ta qi yin magana, sai dai ga Ibrahim wanda abin ya faru akan idonsa zai yi maka bayani."
Samira ta miqawa Ibrahim kan waya, Ibrahim ya karba gami da yin sallama.
"Me ya samu 'ya ta?" tambayar da Bakura ya yiwa Ibrahim kenan kafin ya amsa masa sallamar.
Ibrahim ya hau bayanin iya abinda ya gani akan idonsa.
"ina yarinyar take?" in ji Bakura.
Ibrahim ya ce "kafin na ankara na neme su na rasa sun gudu."
Nan da nan Bakura ya hau Ibrahim da bambamin fada yi yake yana dukan teburin da yake gabansa. Ya na yiwa Ibrahim barazanar rasa aikinsa akan wannan sakacin da yayi.
Malam Yakubu ne a zaune a gefen Bakura yana lallashinsa, yana bashi baki cewar ya kwantar da hankalinsa abi abin a hankali.
Bakura ya kashe waya sai huci yake yi, wani gumi mai zafi ne yake ta keto masa.
Ya ce da Malam Yakubu "wallahi, wallahi sai na dau fansa akan wannan yarinyar da ta bi Yagana har cikin kantin Mahaifinta ta dau katon gwangwani ta fasa mata kai, sai na ga mahaifin yarinyar nan inji ko shine ya sa take rashin mutunci a Kano. Ban taba rigima akan yarana ba, ban taba rigima da kowa ba tun sanda na zo Kano, amma zan fara akan wannan yarinya."
Malam Yakubu ya ce "daman bai kamata a bar maganar nan ba, saboda idan aka bar maganar nan gaba waya san abinda zata yi mata idan taga ba'a dau mataki ba, amma abi abin a hankali saboda yanke hukunci cikin fushi yana jawo dana sani ko nadama."
Bakura yayi ajiyar zuciya ya ce "to malam, na ji zan bi a hankali amma Ko me Yagana ta yiwa yarinyar nan bai kamata ta bi ta har cikin shagona ta fasa mata kai ba, har da jini face-face. A iya sanina Yagana ba ta fada, ko an tsokane ta bata tankawa. Ba ta iya fada ba, bata ma san yadda ake yinsa ba. Haka kawai ta bi ta har cikin kanti ta fasa mata kai ni kuwa sai na ji da wa take taqama a qasar nan kuma sai na ga mahaifinta inji dalilin da yasa 'yarsa ta fasawa 'yata kai, shari'a ni da shi babu mai saka ni na janye."
Malam Yakubu ya ce "tabbas kar ka bar maganar nan nima ban goyi da bayan ka bar maganar nan ba,zan tambayi Yagana da kaina ta fada min gidan su Yarinyar sai mu je har da ni mu ji dalilin da yasa 'yarsa ta fasawa Yagana kai. Idan ya nuna 'yarsa bata yi laifi ba ko tayi daidai to ya cancanci a kai maganar kotu suyi musu tsakani."
Bakura ya gyada kai ya ce "Allah ya kai mu
Kano lafiya."
Malam ya ce "amin Allah Ya kai mu lafiya."
Na

JUT


Paid book




Washegarin ranar ne ranar walima, taro yayi taro sai dai shagalin ya raunana saboda da goshin Yagana ya kunbura suntum duk wanda ya dube ta sai gabansa ya fadi, kowa yana tambaya me ya sami Yagana a goshi?
"faduwa ta yi." Amsar da Samira take basu kenan. Itama Yagana amsar da take bawa kawayenta kenan.
Tun ranar da abin ya faru, safe da rana da yamma da dare Bakura sai ya bugo waya yana tambayar Zahra me ya hada ta da yarinyar, kuma wacece yarinyar? Sai Zahra ta hau nuku-nuku tana kame-kame da alama bata da niyyar fada masa,
Malam Yakubu ma ya sha kar6ar wayar yana lallashinta yana lallaba ta akan ta fadi sunan yarinyar don ayi musu tsakani amma Zahra ta qi fada idan aka takura mata da tambaya sai ta fashe da kuka duk da Zahra bata san da wanda take magana ba ma'ana bata san mahaifin Sajida ba ne.
Idan ran Bakura yayi dubu ya gama baci a yanzu ya fi jin haushin Zahra akan yarinyar da ta fasa mata kai. Allah- Allah yake kwanakin su cika ya dawo Kano ayi wacce za ayi.

*** *** ***
Ranar da su Bakura suka cika kwanaki goma sha biyu, a ranar suka dungumo suka dawo Kano, daga filin jirgi ba'a wuce da su Malam gidansu ba sai suka zarto gidan Bakura kai tsaye sai suka kutsa farfajiyar gidan. Malam da almajiransa sun ga aljannar duniya, sai kallon gidan suke zuciyarsu cike da sha'awa, suka wuce cikin katafaren falon inda suka iske an shinfida katuwar darduma an jera abinci kala-kala da abubuwan sha iri-iri. Bayan sun zazzauna Samira da Zahra sanye da dogayen hijabai tare da kannen Zahra gaba daya suka biyo layi suka zo gaban su Malam suka zube suka kwashi gaisuwa. Zahra na ganin Malam Yakubu ta tuno da fuskar cewa Mahaifin Sajida ne, sai taji gabanta ya fadi.
Daman ita Samira bata san shi ba bata san ma daga in da Bakura ya samo su ba, ita dai ya bata umarni a dafa abincin mutane goma sha biyu zai zo da su, kuma ta dafa shikenan abinda ta sani bata damu ta tambaye shi su waye ko daga ina suke ba.
Bayan sun gaisa sai Samira ta ce da yaranta "to mu shiga ciki mu barsu su ci abinci. Har sun juya baya za su tafi Bakura ya kwallawa Zahra kira, gabanta ya yanke ya fadi ras, Jikinta ya dau karkarwa kan ka ce kwabo sai hawaye ya dinga kwararowa daga idanuwanta.
Ta zo ta durkusa a gabansu. Bakura ya harare ta, ya juya ya dubi Malam ya ce "dubi goshin yarinyar nan ka gani. Yau wajen sati kenan amma har yanzu da sauran kunburin a goshinta. Wa yasan yadda gurin yayi a lokacin da akayi abin?
Wallahi Yagana ban taba dukanki ba amma idan ki ka yi min taurin kai sai na bubbugeki."
Zahra ta fashe da kuka yayin da jikinta ya dau rawa. Malam yasa hannu ya dakatar da Bakura. Ya ce ka ""kyale ta a hankali zan tambaye ta za ta fada cikin lumana da kwanciyar hankali."
Malam ya shiga jawowa Zahra ayoyin Kur'ani da nasihai kała-kala masu ratsa jiki, ita dai kuka shaf-shaf-shaf take. Ta na tunanin yadda zata dubi kwayar idon Malam ta fada masa 'yarsa ce ta fasa mata kai. Ta kudiri niyyar yau ko mahaifinta zai kashe ta ba zata iya fada masa wacce ta fasa mata kai ba.
Bakura ya ce "Malam ka ci abincinka ka rabu da ita har ta gama kukan, ko kukan jini zata yi yau sai na saka ta a gaba ta nuna mana gidan su yarinyar. Ta yaya za'ayi ma tace bata san yarinyar ba, kuma ta qi fadar abinda ya hada su?"
Ya dakawa Zahra tsawa ya ce "koma can gefe ki zauna ki gama kukan, ko ki fada ko karki fada muna gama cin abincin nan zamu saka ki a gaba ki nuna mana gidan, idan kika qi za ki ga abinda zan yi miki a yau. Me za'ayi da irin shiru-shirun nan naki? zurfin cikinki yayi yawa."
Zahra ta koma gefe tana ta rusar kuka ta rasa abunda yake yi

Please Login or Register in order to submit comment