Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce "Wannan ba wata matsala b8 ce, in har za ki iya riqe shi a dalilina za a baki shi. Daman ya kamata a ceto rayuwar yaron nan yana shan wuya a wajen mahaifiyarsa. Sai dai sai kin daure, za ki dinga kawo shi lokaci-lokaci ana ganinsa yana ganin iyayensa."
Hakimi ya shaidawa Zuhuriya ai su na da alaqa ta jini da mahaifiyar Bakura, don haka dangimsu sun san komai.
Washe gari ba tare da kowa ya sani ba Zuhuriya ta dauki abincinta na safe koko da qosai ta tafi bakin kasuwa ta kaiwa Bakura da mahaifiyarsa suka ci. Kan ka ce kwabo hira ta gauraye tsakanin mahaifiyar Bakura da Zuhuriya. Bakura kuwa tuni ya haye cinyar Zuhuriya kamar ya sami wata uwar. Da rana ma ta dibi abinci ta kai musu, bata tashi dawowa ba sai daf da magariba, sai ga ta goye da Bakura a bayanta, mahaifiyarsa na biye da ita ta ce mata ta zo Hakimi yana kiranta.
Cikin dabara da wayo hakimi yake yi wa Fatukamba bayanin cewa Zuhuriya za ta dauki Bakura ta dinga goya shi, tana bashi abinci, za ta dinka masa Sabon kaya ya yi kyau, ita ma za a dinko mata sabuwar atamfa. Abin ka da marar hankali. sai ta hau murna tana tsalle, aka cika mata kwanon ta da abinci ta tafi ta bar shi. Hakimi ya sa aka kira Baban Bakura aka sanar da shi, shima ya yi amanna ya yi murna da wannan taimako da aka yi masa.
Daman iyayen Fatukamba sun rasu, yayanta ne guda daya a garin mai suna Bukar Shima hakimi ya kira shi ya shaida masa cewa Zuhuriya 'yarsa ce a Kano ba ta da d'a tana so ta riqe Bakura za su dinga zuwa akai-akai yana ganinsu. Bai yi musa ba, saboda shi ma baya taimakonsu korarta ma yake ita da danta daga gidansa, don haka ya yi farin ciki da jin haka.
Kafin mu bar Mangono Bakura ya canja, Zuhuriya tana yi masa wanka tsaf-tsaf, ta samar masa kwancen riguna da wanduna a wajen matan hakimi. Abinci kuwa idan ta dinga tura masa bai san ya qoshi ba sai an hana ta. Goyo kuwa riqi-riqi ko sallah a bayanta yake yi. Farin ciki da shaquwarsu kuwa cikin 'yan kwanaki sai ka rantse sun shekara da sabawa ko ka zata ita ta haife shi. Ni kuwa haushinta nake ji don babu yadda zan yi in hana ta, so nake mu je gida in mata duka. Abinda babba ya hango yaro ba zai hango ba ko da kuwa ya hau bishiyar rimi. Kunyar sirikina nake ji Hakimi da na hana ta daukar yaron nan, idan na hana ta gari gaba daya za'a ce baqin hali gare ni, daman na yi qaurin suna a wajen dangin miji su na cewa ba ni da kirki, don a garin muka yi zaman zauna har mijina ya mutu mahaifin Zuhuriya.
Ranar da za mu tafi, jama'a suka raka mu har tasha su na ta shi albarka su na yaba yadda Bakura ya canja cikin dan qanqanin lokaci. Jama'ar gari kacokan sun yi amanna da daukar Bakura. Ni kuwa wacece da zan ce ban yarda ba? Amma tun daga mota na fara dunguri, ina rankwashi, ina zagin Zuhuriya. Bakura ba zan boye maka ba idan ma na qi fada ai ka san komai, tun da tun baka fahimta har ka girma ka fahimci bana son zamanka da mu. Bakura ka yafe min, domin na zalunce ka, na zalunci kaina."
Iya Azumi ta rushe da kuka
Hawaye ya surnano daga idanuwan Bakura Ya ce "Ka da ki yi küka Innono, kada ki damu na yafewa wasu ma a dalilin Zuhuriya balle ke da kika haife ta da kanki."
Babu wanda idonsa bai cika da hawaye a wajen ba, don tausayin Bakura. Hatta Sajidar da take iqirarin ta tsani Bakura kamar yadda ta tsani mutuwarta dan yaron nan Bakura ya bata tausayi har sai da hawaye ya surnano daga idanuwanta.
Bakura ya ci gaba da cewa "Mu ka isa Cinkilawa, garin da Zuhuriya da mahaifiyarta suke aure a nan ne na fara bude ido, na fara sanin menene rayuwa. Sunan mijin Innono malam Audu ba shi da wata mata sai Innono. Sunan mijin Ummata Zuhuriya kuma Hashimu, shi ma yaro ne ita ce matarsa ta farko. A da an ce su na zamansu lafiya, amma tunda ya kyalla ido ya ga Zuhuriya da yaro ta yi masa bayani sai ya bata rai ya nuna baya so, ba zai riqe ni ba. Ita kuma ta ce duk wanda baya sona ba ta sonsa, dan haka sai dai ya sake ta. Daga nan dai zama ya rikice kullum ba dadi, domin duk wanda ya taba ni sai inda qarfinta ya qare da yake ita ma in an taba ta ba kyalewa take yi ba, akwai ta da tsiwa, yanzu nan idan ta jiyo kukana zata figo gyale ta fito a yi fada da wanda ya dake ni ko da iyayen yaran. Daga qarshe dai zama ya wi dadi, Hashimu ya saki Zuhuriya a kaina. Muka kinkimo kayanmu a amalanke da Magaruba muka taho gidan Innono.
Tana ganinmu ta ce "Bakura ya kashe miki aure ko?"
Ta kwana tana dukanmu, ni da Zuhuriya muka takure a jikin katanga kamar wasu qadangaru ta hana mu abincin dare har na yi barci a haka, amma sai da Zuhuriya ta tashi da tsakar dare ta gutsirar min tuwon dumame ta tashe ni ta ba ni a baki har na qoshi."
Samira ta yi ajiyar zuciya ta ce "Allah sarki, Allah Ya saka mata da alkhairi."
Bakura ya ce" Amin, na gode Samira."
Ya ci gaba da cewa "Haka muka yi zaman zawarcin nan da wahala, saboda tsangwama. Abin ka da qauye da zarar an ji bazawara tun bata gama iddah ba zawarawa sai su fara kawo hari balle Zuhuriyar da duk surquqin qauyukan nan tafi kowacce mace kyau. Idan bazawari ya zo sai ta aika ni in leqa in gani da jaki ya zo ko keke, idan jaki ne ko keke sai ta kama hannuna mu fita da gudu ta ce ya yi ta dana ni akan jakinsa ko keke, ina jin dadi. Idan kuwa ba shi da jaki ko keke, daman ba za ta fito ba. Wannan al'amari namu yana batawa Innono rai, wanda take kiransa rashin hankali. Don haka kullum fada take da kumfar baki a kan Zuhuriya ta fitar da miji ta yi aure. Ni kuma ta mayar da ni gidanmu kada in sake kashe mata aure. Ko kadan Zuhuriya ba ta yarda da zancen mahaifiyarta ba, ta nuna akan ta mayar da ni gara ta goye ni mu tafi mu bata a rasa mu. Duk wanda ya fito aurenta sai ta sanar masa cewa tana da d'a da shi za ta je, idan ya ga bai yarda ba kada ya sake dawowa. Da yawa idan sun tafi basa dawowa, amma Mutari wanzami ya yarda ya amince zai aure ta tare da ni, sunan qauyensu B'alle bantai, qauye na kusa da Cinkilawa daga kudu.
Ya kawo kayan aurensa atamfa uku, sai sadaki a kowacce atamfa sai da aka dinka min ma'ana anko muka yi ni da amarya. Aka daura aure muka kwashi kayanmu kacokan muka koma qauyen Balle bantai muka bar Cinkilawa.
Sabuwar rayuwa a Balle bantai, ga uwar miji ga kishiya, gani kuma agola dan haka ba zaman lafiya a gidan. Zuhuriya ba ta da aiki sai goyona ko'ina rabe- rabe abun ka da marar jiki har rinjayarta nake kamar Za mu fadi, ga shi duk atamfar da za ta saka anki muke nima irinta take sa tela ya dinka min riga da wando. Na Zama dan shagwa6a idan na ga dama sai in qi taka qasa in ce sai dai ta goya ni, abinci in qi ci sai dai ta bani a baki. Wannan al'amari nawa yana bawa mutanen gidan nan haushi.
Uwar mijin har wani suna ta saka min wai "tarar ni wuce ni. Wato na zo na sami 'yan gida har na fi su zaqewa. Mutari wanzn ya na sona, saboda yana son Zuhuriya, dan haka Zuhuriya ita ma take sonsa saboda yana sona. Amma kishiyarta Rahi da mahaifiyarsa Ingade ba sa son ganina a gidan. Don haka fadan safe daban, na rana daban. Idan ranar girkin Zuhuriya ne abinci tun yana kan wuta ake fara ba ni tabi, idan ranar girkin Rahi ya zagayo ba ni da kashi sai dai Zuhuriya ta ba ni nata in ci, idan na qoshi ta ci sauran idan na cinye dukka ta kwana da yunwa.
A haka a daddafe muka yi wata takwas a Balle bantai, sannan uwar miji ta tubure ta tilasta dole har sai da danta ya sake mu.
Dolensa ya sake ta yana son mu a nan ma Zuhuriya ba ta samu ciki ba. Ba na mantawa da hantsi rigimar ta taso don haka da muka hada kwanukanmu na tsakar gida muka datse a daki, sai yan kayanmu seti biyu muka kullo a dankwali muka taho. Da qafa ake tafīya a lokacin, duk nisan tafiya babu mota. Don haka muka kamo hanya zuwa Cinkilawa tana riqe da hannuna idan na cije na qi tafiya ta goya ni, idan ta gaji da goyon ta dauke ni, haka muka yi ta yi.
Na dube ta na ce "Juhuliya, lokacin ba na iya cewa Zuhuriya ta ce na'am Bakura. Na ce, "Tsoro nake.ji kada Innono ta dake mu."
Sai ta fashe da kuka, don tausayina ba ta damu da dukan da za a yi.mata ba, ni take tausayawa ta san akwai matsala, idan ta je gida ta ce an sake ta, kuma su ji labari a kaina ne. Innono za ta tubure ta ce sai ta mayar da ni garinmu ni nake hana ta zaman aure. Dan haka muka yanke shawarar kada mu koma gida mu yi zaman mu a cikin dawa qarqashin wata bishiya. Muka yini a dawa muna tsalle-tsalle, ta dora ni akan wuyanta in tsinko mana dinya, aduwa, dorawa, tsamiya da dai sauransu. Idan na kasa tsinkowa ita sai ta hau bishiyar ta tsinko mana. Haka muka, yini muna ta walagigi har Magruba.
Akwai gidan gonar wani tsoho a kusa da inda muke. Ashe tun da safe yake lura damu ya ga har rana ta fadi ba mu da niyar tafiya, don haka ya zo da bulala ya ritsa mu. A tunaninsa Zuhuriya yayata ce aka aike mu da qulin kaya muka zo muka zauna muna wasa, dan haka yake yi mana fada mu hanzarta tafiya inda aka aike mu. Simi-simi ya saka mu a gaba har kusa da garinmu Cinkilawa ya raqe da bulala.
Kan ka ce kwabo an hango mu, yara suka hau tsalle su na fadin "Ga Zuhuriya, ga Bakura."
Labari ya iske kunnen Innono, tana jin haka ta san ba zuwan lafiya ba ne da magrubar nan, dan haka ta girka kujerarta a tsakar gida ta tanadi bulalarta ta na jiranmu. Mu ka qi shiga cikin gidan muna jikin katanga a labe. Can Zuhuriya ta dora ni a wuya na leka cikin gidan daidai lokacin muka yi ido hudu da ita.
Ta ce "Waye wannan?" Na ce "Bakura ne, Inonono an sake mu."
Su Malam suka kwashe da dariya, har da Bakura. Da alama labarin nan ya na ratsa zuciyar duk wani mai sauraro. Akwai hikima a wajen shi kansa mai bayar da Labarin. Babu abin da zuciyar Zahra ke aiyanawa sai sha'awa da marmarin ta je wadannan qauyukan ta dandana yadda suke rayuwa. Ji take dama ita marubuciya ce ta rubuta' labarin nan har take tunanin sakawa littafin su na LABARIN BAKURA.
Bakura ya katse mata tunani ya ci gaba da cewa "Takaici ya qara rufe Innono. Ta ce "An sake ku ko? Ni kuma zan daure ku. Ka sake kashe mata auren ko? Za ku shigo ku same ni."
Mu na bin katanga muna rabewa, ga yunwa da kishirwa. Can na sulale na zauna na fara gyangyadi. Da sauri Zuhuriya ta tashe ni ta kama hannuna muna sauri muka je gidan wata mai abincin siyarwa. Ta kwance gefen zaninta ta kwanto wasu 'yan kudadenta sulalla fa kwabbuna ta siya min tuwo malmala guda na cinye, ta bani ruwa na sha, ta kai ni bandaki na yi fitsari sai ta saba ni a baya na yi barci. Ban tashi farkawa ba sai da tsakar dare da na ji tururruwa ta baibaye ni tana cizona. Ashe zauren qofar gidan Innono ta shige ta labe bayan Malam Audu ya shigo gida ya rufe ba tare da ya san muna labe ba anan ta yi mana shimfida da zani muka kwanta, ashe da ramin tururuwa. Sunanta na kwallawa kira cikin kuka na ce wani abu yana cizo na ga tsananin duhu. Zuhuriya ta daka tsalle ta tashi ta ciccibe ni ta kade min jikina muka koma tsakar gida muka qarasa kwana.
Da duku-duku gari bai waye ba Innono ta tsara mu a lungu. Zuhuriya ba ta bari dukan ya same ni sosai ba, karewa take yi tana fadin "Bakura yaro ne ni ki dake ni bai san komai ba."
Sai Bakura ya surnano da hawaye zazzafa ya ce "Zuhuriya na sona a rayuwarta, haka nima nake matuqar qaunarta a rayuwata. Muna cikin wannan hali na tsangwama ga aiki, kamar bayi sai Zuhuriya ta ga gara ta sake aure ko gidan mijin zai fiye mana kwanciyar hankali. Ta auri wani tsohon malami don a lokacin ana ta surutun wai ta auri tsohon mutum tana yarinyarta son kowa qin wanda ya rasa,
Malam yana da makarantar allo duk karkarar nan babu makaranta mai yawan almajiransa. Sunansa Malam Idi mahaddacin Kur'ani ne sosai matarsa daya ta rasu a shekarar da zai auri Zuhuriya. 'Ya'yansu kuwa sun yi aure har suma sun hayayyafa, don haka muka ji dadin zaman gidan ba mace, ba 'ya'ya.
Alhamdulillahi, a wajen malam idi muka fara samun ilimin addini daga ni har Zuhuriya. Don idan aka fara karatu tun da Asuba har sai rana ta fito. Haka da yamma ma har sai Magaruba. Bayan sallar Isha'i kuma har kusan sha biyun dare ana karatu sannan mu kwanta. Ina cikin almajirai ina wadaqata ga abinci a gidan ba yankewa. Duk da dai dawa ce da masara sai gero kullum. Shckarar mu kusan uku a gidan malam ya rasu. kasancewar ba ta haihu da shi ba, bata da gadon komai dole muka tarkato kayanmu bayan ta gama takaba muka dawo Cinkilawa gidan Innono.
Rayuwa ta dawo irin ta da, dole Zuhuriya ta fara sana'a tana danwake da safe mu dauka aka mu kai makarantar boko da ke Jalawa da qafa muke tafiya tunda ga Cinkilawa kullum. Idan an yi break 'yan makaranta su yi ta siya.
Ni ba dan makaranta ba ne, amma ina jiyo abin da ake koyarwa caraf sai na riqe ABCD har zuwa Z. Akwai wani Malami mai suna Isa, dan asalin garin Jalawa ne sai ya nuna yana son Zuhuriya kullum sai ya sayi dan wakenta. Ya ba ta shawara mai zai hana ta saka ni a aji daya, nima in yi karatun maimakon zaman gindin bishiya muna jiran yara su fito, ai gara ni in dinga shiga aji. Sai ta jira a tashi mu tafi gida. Zuhuriya ta qi amincewa amma ni na ce ina so har da kukana.
Malam Isa ya ce shi zai karbar min uniform lokacin komai kyauta ake bayarwa har littattafai. Sai ta yarda ta saka ni a makarantar tunda ta ga ina so. Har na zo na fi duk 'yan ajin qoqari. ldan mun fito break da gudu zan taho wajenta ta zuba min danwake har yara suke kirana dan gidan mai dan wake.Kai ka fi cancanta

Idan an tashi da rana sai mu doro daron d'an wakenmu aka mu koma garinmu Cinkilawa. Innono ta huta ciyar da mu yanzu, muna da sana'armu don haka rigimar ta dan lafa, ba ma yini a gidan ma balle a ce mun yi laifi.
Abu kamar wasa Malam Isa ya ce yana so ya auri Zuhuriya su zauna a Jalawa, saboda mu huta zirga- Zirga kullum, gidansa ba nisa da makaranta ya yarda zai riqe ni, zai kuma bar ta ta dinga zuwa tana sayar da danwakenta. Ta amince suka yi aure, muka dawo Jalawa da zama. Lallai mun sami ci gaba, saboda gidan Malam isa na siminti ne, ga shi da babur dinsa na hawa. Yana da mata daya mai suna Sahura da 'ya'ya biyar. Ko ban fada muku ba, kun san za a yi dauki ba dadi a gidan nan. Inda aka sami saukin rigimar Sahura na tsoron Zuhuriya, dan sun goga ta ji karon bai yi mata da dadi ba. Zuhuriya ta iya tsiwa bakinta caicai baya mutuwa, damara take ci a yi ta fada ga ta ba ta da kiba, amma ko a dambe ba a kayar da ita.
Ta kwatar min 'yancina, duk da ni ba dan gida ba ne amma ba ta yarda wani ya takura min ba. Dole Sahura da 'ya'yanta suka daga min qafa na miqe qafata na yi dayday a gidan kamar gidan ubana.
Karatu nake tukuru ba na fashi har Allah yasa na Kai primary 4. Kokari da cancanta aka saka ni a cikin masu daukar jarawar tafiya sakandire na zana. Allah CIkin ikonsa na ci, na sami tafīya makarantar 'yan maza ta Wudil. Malam Isa ya taimaka min wajen karbo min akwati, katifa da bokiti daga qaramar hukuma, amma sauran siyayyar Zuhuriya ce ta quge 'yan kudadenta ta siya min duk abin da zan buqata. Duk da a lokacin ba a matsalar abinci a makarantu.
Na je makarantar kwana na dace da abokai na gari na ci sa'a shugaban makarantarmu (pricipal) mai suna Malam Abbas Shagari yana sona, saboda qokarina. Aka yi jarrabawa na zo na daya, aka ba mu hutu, local government dinmu ta kai mota aka kwaso mu. Ina isowa gidan Malam isa na iske shi a qofar gidansa yana zaune a kan tabarma. Da murnata na qaraso wajensa na duqa na gaishe shi na zaro report card dina na miqa masa cike da murna.
Ya yi dususu kamar bai sanni ba, ya duba galala ya miqo min abu na. Sai mamaki ya rufe ni saboda a zatona zai yi farin ciki da ganin sakamakona, shi yake koda ni yana yabon qoqarina har hakan tasa nake qara dagewa ina karatu sosai.
Saboda shi ne ma yasa na dage ba dare, ba rana ina ta karatu har sai da na fi kowa cin jarrabawa a ajinmu. Na tashi jikina a sanyaye na dauki buhun kayana na shiga gida farin ciki ya rufe ni ina murna saboda zan ga Zuhuriya na sha wahalar rashin ganinta da kyar na daina kukan rashinta a makaranta, ba mu taba rabuwa daidai da kwana daya tun daga sanda muka hadu. Ina shiga na iske dakinta a bude na fara washe baki na san tana ganina za ta rugo da gudu ta rungume ni. Na yi sallama na bude labule na tura kai zan shiga sai na ji an hankado ni waje, na yi tagal-tagal zan fadi a baya.
Sahura na gani ta fito daga dakin ta ce da ni "Kai mahaukacin ina ne da za ka fado min har cikin daki?"
Wannan maganr ta ba ni mamaki, saboda dakin Zuhuriya nè. Yaranta suka yi caa suka fito daga dakinsu suka zagaye ni. Wasu na yi min gwalo, wasu na yi min daquwa su na tsokana ta. Abin da suke fada shi ne an saki Babata ta koma Cinkilawa.
Gabana ya yanke ya fadi sai na fara kuka. Na ce musu to bari in dauko sauran kayana a dakin yara. Nan ma suka hana ni shiga suka ce ta kwashe kayanmu kacokan babu ko tsinke nawa, dan haka in tafi in ba su waje.
Na dora buhuna aka, ga tsananin yunwa da kishirwa ga doguwar tafiyar qafa daga Jalawa zuwa Cinkilawa, na fito jikina a sanyaye. Duba daya Malam Isa ya yi min ya dauke kai, na dube shi duba na takaici da tsantsar tsana tunda ya kori Zuhuriya sai na ji ba na sonsa, na wuce na kama hanyar Cinkilawa. Ban isa garin ba sai daf da Magruba.
Ina isa tsakar gida na wurgar da buhun da ke kaina na fadi yararaf a qasa. Innono ce a bakin murhu tana tuqa tuwo ta dau salati ta kwallawa Zuhuriya kira ta taho da gudu daga daki, don ta ga abinda ya gigita Innono har take kwalla mata wannan kira haka.
Ta na ganina a kwance ta rafsa ihu ta riqo ni ta tashe ni zaune tana tambayata lafiya. Na ce yunwa da kishirwa, a guje ta shiga daki ta dauko min langa a cike da alala na fara ci, kamar ban taba cin abinci ba haka nake turawa a cikina,ta ba ni ruwa a qwarya na sha.
Haushi da takaici ya rufe Innono ta ce Bakura, ka zayyano min da bakinka aure nawa ka kashewa Zuhuriya?"
Na zabura na ce "Innono wannan karon bana nan aka yi sakin."
Ta ce "Ai a dalilinka aka yi rigimar har aka sake ta."
Na shiga rudani hade da fargaba. Zuhuriya na zaune ba ta ce komai ba sai hawaye take sharaf-sharaf.
lnnono ta zaiyano min duk abinda ya faru daga qarshe ta ce to an yi na qarshe tunda na girma dole in koma garinmu idan ma zan yi karatun anan in je makaranta ana yin hutu in hau motar garinmu Mangono. Hankalina ya tashi, domin ba na son a ambaci sunan garinmu ballantana a kai ni."
Bakura ya zubo da hawayen

Please Login or Register in order to submit comment