Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dayan su sun yi kama da mahaifiyarsu, amma sun dauko tsayin mahaifinsu dogaye ne sosai. Allahu Akbar!! Allah mai halittar bayinSa duk yadda Ya so.
Kwana biyu Bakura ya kasance cikin yawan tunani da damuwa ga uwa uba rikirkicewar tunani. Ya na cikin damuwa, gigita da tsantsar son binciko wai shin menene alaqar Sajida da Zuhuriyyarsa, idan akwai.
Bakura ya taso daga wajen aiki, sai ya ji a ransa ba zai qara iya daurawa ba bari kawai ya zarce gidan su Sajida ko Allah zai sa ya samu abinda ya ke nema, ma' ana labarin asalin su Sajida. Bakura ya na tsayawa da motarsa a bakin qofar gidan su Sajida sai ya bude qofar ya fito yayin da gardawan da ke zazzaune a qofar gidan su ka zuba masa idanuwa su na kallonsa su na gasgata ni' imar da Rabbul samawati ya yi masa. Ya yi shigar fararen kaya, farin takalmi da farar hula, motarsa kuma kirar BMW 7 SERIES mai launin ruwan zuma. Ya fito ya tsaya yayin daya zare farin gilashin dake fuskarsa ya dubi jama'ar da ke zazzaune a qofar gidan daga dukkan alamu makarantar allo ce karatu su ke dauka.
Malam Yakubu shine mai makarantar wato mahaifin Sajida. Ya na zaune akan kujerar katako rike da zabgigiyar dorina, yara su na gabansa su na daukar karatu, da zarar sun kuskure sai ka ji ya faula musu bulalar. Malam kenan!
Bakura ya qarasa gaban Malam Yakubu ya yi sallama sannan ya durqusa ya gaishe shi. Cikin fara'a Malam ya amsa gami da ce wa "yaro ban gane ka ba."
Bakura yayi murmushi ya ce "watakila saboda ba waccan motar ba ce shiyasa ba ka gane ni ba. Ni ne wanda na zo kwanakin baya da yamma game da maganar Sajida da Abdul Abdulmajid."
Sai Malam ya fahimta ya fada cikin sakin fuska "to, to, to na gane ka yaro, to mu je wajen motarka mu tsaya."
Su ka qarasa jikin motar su ka tsaya. Bakura ya sosa gefen kunne yayi dan murmushi ya ce "Malam yaya yara, yaya jama' a?
Malam ya ce "Alhamdulillahi, mun godewa Allah. Yaro ka taimaka mana fa matuqa domin ni a iya sanina Sajida ba ta da waya. Ashe waya ya hada mata take labewa su na yin magana ba tare da mun sani ba. Har takai ta kawo Sajida za ta yi min dubara ta fita ta je su hadu a wani a waje ban sani ba. Saboda yaron nan fa na cire Sajida daga makarantar boko ta na aji biyar na sakandire. Saboda a hanyar makarantar bokon ne ya ke tare ta su dinga zance. Ni dai na fada duk lokacin da ta yarda Abdul majid ya lalata ma ta rayuwa, ma ana ta bari ya yaudare ta, ya san ta 'ya mace ya cuce ta kuma daga lokacin da na aurar da ita na yi bincike aka tabbatar min ba cikekkiyar budurwa ba ce sai na yanka ta."
Bakura ya yi shiru na wani dan lokaci kansa a sunkuye a qasa kamar mai tunani. Can ya dago da kansa ya yi ajiyar zuciya.
Ya ce "Allah ya kyauta." Malam yakubu ya dubi Bakura ya ce "wai daman ka san Sajida da Abdul majid ne ko ka na da labariKai ka fi cancanta 1

JUT

Jamila umar tanko




0️⃣7️⃣
Ko ka na da masaniya akan taqardamar da ke tsakanina da shi?"
Bakura ya ce "ko daya ban san su ba, na hadu da su ne akan hanya zan wuce, na kalli Sajida na dubi Abdul majid na tabbatar ba abokin huldarta ba ne. Na ba ta shawara ba ta saurari ni ba, sai na ga ya dace in biyo ta don in hadu da mahaifanta in fada mu su don su san halinda 'yarsu ta ke ciki. ka san mu barebari akwai mu da tsawatarwa Baba."
Su dukka suka bushe da dariya.
Malam Yakubu ya ce "ai mu Fulani mu aka sani da kara, kunya da kawaici, ai Sajida ba ta biyo Fulatancinmu ba, na rasa yadda zan yi da ita. Amma yanzu na saka ma ta takunkumin da ko ita ce uwar dubara da wayo ba ta isa su hadu da wannan dan iskan yaron ba, marar tarbiyya."
Bakura ya ji dindirin kansa ya yi masa nauyi ya fada a ransa "su Sajida Fulani ne kenan ashe babu hadin Sajida da Zuhuriyya."
Hikimar Bakura daman ita ce ya ambaci Barebari ne don ya ji ko su Sajida su na da alaqa da Barebari idan da alaka to ta ina, waye da waye ko kuma ta ina alakar ta hada zuhuriyya da ita. Amma babu wata alaka kwata-kwata.
Bakura ya nisa ya ce "Malam ku fulanin ina ne?"
Malam ya yi murmushi ya ce "fulanin Shanono ne amma mazauna Kano, tun ina yaro na zo Kano yawan almajiranci, daga nan ban koma ba."
Bakura ya sakc jin ya kidime yayin da yake jinjina da yabo ga Rabbul samawati wanda Shine ya halicci Sajida tayi kama da
Zuhuriyyarsa sak. Bakura ya dubi malam Yakubu yayi murmushin nan nasa mai faranta zuciyar wanda ya yiwa. Ya ce "Malam ina son in zama daýa daga cikin almajiranka domin nima asalina almajiri ne yawon almajiranci ne ya rabo ni da garinmu Maiduguri zuwa Kano."
"Almajiranci fa ka ce?" malam ya tambaya cike da mamaki.
Bakura ya gyada kai ya ce "kwarai kuwa malam." Malam ya nisa ya gyada kai yå na shafa dogon gemunsa ya ce "Allahu Akbar!!! Yanzu yaro kai almajiri ne ada? Allah ya rufa maka asiri ya maka arziki? Haka Allah' Ya ke ikonsa. Yaya sunanka?"
Bakura yayi murmushi ya ce
"Sunana Bakura, sunan mahaifiyata
Yagana, mahaifina kuwa sunansa Bahna. Ina da mace daya mai suna Samira. Yarana hudu babbar sa'ar Sajida ce shekarunta goma sha shida sunanta Zahra, ina kiranta da Yagana don sunan mahaifiyata ne. Na biyun Abubakar sai Umar da
Usman. Ina zaune a unguwar Amadu Bello Way."
Malam Yakubu ya dubi Bakura cike da sha'awar dama nine na sami irin wannan ni' imar taka.
Ya ce "yanzu yaro ka haifi yarinya budurwa kamar Sajida 'yar shekara goma sha shida? Amma a haka kamar baka yi auren fari ba ma."
Bakura ya yi dariya ya ce "haka ne, nayi aure da wuri ina dan shekara ashirin da uku, yanzu shekaruna arba'in kenan."
Qaunar Bakura ta sake shiga zuciyar malam.
Ya ce "'yaro ka zo duniya a sa'a, Allah ya yi maka baiwa wacce ba kowa ya samu haka ba, ka godewa Allah."
Bakura ya ce "Alhamdulillahi Ala kulli halin."
Malam Yakubu ya ce "Allah Ya sanya albarka a cikin dukiyarka da iyalinka, Allah ya qara budi. Yaro Allah ne Ya hada mu, Allah ya dad'a mana dankon zumunci."
Bakura ya ji dadin addu'ar malam Yakubu ya na amsawa da "amin summa amin malam.
Bakura ya sake gyara tsayuwa ya ce "Sajida da Yahuza ne qananan yaranka kenan?"
Malam ya gyada kai ya ce "na' am, su ne qanana kuma su ne manya."
Bakura ya tsurawa malam ido ya na kallonsa duba irin na rashin fahimta.
Sai Malam yayi murmushi ya ce "ni da matata Furera mun yi aure tun quruciya amma Allah bai ba mu haihuwa ba sái da muka manyanta, Su biyun nan da ka gani su ne kadai 'ya'yanmu."
Bakura ya yatsune fuska kamar mai ciwon kai wanda har hakan ya ja hankalin Malam Yakubu ya tambaye shi "Bakura lafiya ko kwaro ne ya fada ma ka ido?"
Bakura ya ce "a'a Malam na dai ji dadi da Allah ya ba ku haihuwar kafin kų tsufa yadda ba za ku iya haihuwar ba ma kwata-kwata."
Nan kuwa tsabar firgita ce, ya ji gabansa ya fadi kasancewar babu sauran wani tunani ko bincike akan alakar Sajida da Zuhuriyyarsa kuma da zai sake yi.
Ya fada a ransa "yanzu babu dangin Zuhuriyya guda daya da zan kalla in ji dadi a doron duniya? kan ka ce kwabo jikinsa ya yi sanyi idanuwansa sun kada sun yi jajawur, muryarsa ta yi qasa sanyi kalau. Amma sai ya daure ya na hira da Malam don kada ya gane.
Hira su ke ta yi tamkar d'a da uba, ko kaka da jikansa kai ka ce sun yi shekara da shekaru da sabawa. Daga karshe su ka yi sallama su ka tsayar da shawara akan Bakura zai dinga zuwa daukar karatu da daddare tsakanin sallar magaruba da isha'i sau uku a sati wato ranakun Juma'a, asabar da lahadi. Ba tare da Bakura ya bawa malam komai ba ya shiga mota ya tafi.
Hikimar hakan kuwa shine Bakura mutum ne mai yawan kyauta amma mai yawan gwada mutane don ya gane masoyansa na zahiri.
Ya na sane sai ya qi yin kyauta don ya ga shin mai zuwa gaishe shi zai ci gaba ko zai daina daman ba don Allah ba ne. Bakura kenan!!!
Bayan tafiyarsa Bakura ya tsinci kansa cikin farin ciki da tsananin qaunar Sajida da mahaifinta. Kauna ta saboda Allah ma'ana ya na son su so na tsakani da Allah saboda albarkacin kamar da tayi da Zuhuriyya, yą sa a ransa cewa Allah ne Ya hada shi da mai kama da wacce ya fi so don su yi zumunci.
Kullum Zuhuriyya ce a ransa Allah ya dubi halin da ya ke ciki Ya kuma amsa addu'ar da yake ta yi shekara da shekaru ya aiko masa da Sajida dan ya dinga ganintaya na jin sanyi. Allah ne kadai Ya san boyayyan sirrin daya shirya. Irin koyar da tarbiyya da jajircewar da mahaifin Sajida ke da ita shine ya sa ya kwantawa Bakura a cikin zuciyarsa, uwa uba yadda ya ke koyarwa da al'ummar Annabi karatun kur'ani mai girma.
Allahu Akbar!!!
Ranar juma'a kafin sallar magaruba Bakura ya dira a kofar gidan malam Yakubu, tare da shi aka yi Jam'in sallar magriba aka idar sai aka firfito da fitilar kwayaye guda uku daga cikin gida.
Manyan maza da dattijai ne suka zagaye malam su na daukar karatu, kowannce da qur'aninsa. Abin ya yi matuqar burge Bakura bai taba zaton haka maza ke cika su na daukar karatu ba, a kalla sun yi su ashirin duk da haka ma mutane da yawa ba su sami damar zuwa ba.
A lokacin da malam ya fara dora musu karatu sai ya fuskanci Bakura ya riga ya haddace duk inda aka bude, sai bayan da aka gama daukar karatu aka yi sallar isha' i kowa ya watse sai Bakura da Malam ne kadai su ka rage.
Malam ya ke tambayi Bakura shin saukarsa nawa?
Bakura ya ce "ba adadi, amma haddata sau bakwai, ną haddace kur'ani, na sake maimaitawa har sau bakwai."
Malam ya gyada kai alamar ya jinjina masa ya ce "sai dai ka zama mataimakina ka dinga taya ni koyarwa amma kai ba dalibi ba ne, malami ne."
Su dukka suka yi dariya. Bakura ya ce "Malam anya ayi haka kuwa?"
Malam ya ce "haka za'ayi Bakura. "
Bakura ya ce "to malam ai kai uba ne ba zan yi ma ka musu ba. A can gidana ma akwai masallaci a qofar gidan, mazan unguwar su na zuwa daukar karatu. Ni da limamin masallacin muke koyar da su, Yanzu ma haka su na can su na yi, na fito ne neman ilmi ko akwai abinda zan samu in koya, ka san ance ilimi kogi ne ya na da yawa."
Malam ya ce "haka ne, ai gobe sai mu yi hadisi, fikihu da tauhidi."
Bakura ya ce "to madalla Allah ya kaimu goben Malam."
Bakura ya miqe tsaye ya na shirin tafiya sai ya ji Malam ya ce "Bakura ka jira ni in shiga gida in fito."
Bakura ya amsa da "to malam."
Ya bi malam da kallo har ya shige cikin gida Bakura ya shiga zulumi, ya na tunani ya na tambayar kansa da kansa meyasa malam ya ce ya jira, kuma ya shiga gida? Wa zai kira, ko me zai dauko masa daga cikin gida? Allah Ya sa mahaifiyar Sajida zai kira su gaisa ko Allah zai sa ya gane ko wacecc. Ya ci gaba da sake-sake a ransa tabbas Sajida da mahaifiyarta za ta yi kama tunda ba ta yi kama da mahaifinta ba ko kadan, amma qaninta Yahuza kallo daya za ka yi masa ka yiwa mahaifinsa ka ga kama.
Bakura ya na tsaye qikam kamar itacen bishiyar da bata da reshe balle ganye, idonsa kyam akan qofar shiga zauren gidan, ya na jiran fitowar malam Yakubu.
Ba tare da Malam ya dade da shiga ba sai ga shi ya fito dauke da wata baqar leda a hannunsa ya qaraso inda Bakura ya ke tsaye.
Ya mika masa gami da cewa "Bakura ga wannan, shadda ce tsadaddiya wani daga cikin jama'ata dan siyasa ne mu ke yi masa addu'oi shine ya kawo min su kala-kala da yadiddika har kala bakwai shine nace bari in dauko maka daya kaima ka dinka irin taku ce ta manyan 'yan gayu. Ni kuwa ina fama da tuwo da miyar kuka ina faman cakuduwa a cikin almajirai ina ni ina saka farin kaya."
Bakura yayi mamaki matuka, ya bude baki ya na kallonsa sai ya hau jujjuya shaddar,. tabbas babbar shadda ce ta gaske irin shaddojin da ya ke dinkawa ne. Sai ya dubi malam ya yi dariya ya ce "Malam ayi haka kuwa? Me zai hana kaima ka dinka ka caba adonka ga daurin aure, fatiyar suna, kwalliyar idi ko juma'a sai ka saka kayanka. Shima wanda ya baka idan yana gani a jikinka zai ji dadi gobe ya qaro maka wadanda su ka fi haka tsada da kyau."
Malam ya yi dariya ya ce "kai haba, meya yayi Saura da har zamu zauna muna caba ado ai fatanmu yanzu sauran shekarun ko watanni ko kwanakin da suka rage mana ya zamanto zikiri ne, salla, azumi da karatun kur' ani mu cika da imani. Ka sàn Allah Ya ce sittuna au saba'una. Ga shi yanzu ina sittin da biyar. Je ka da ita Bakura ba'a mayar da hannun kyauta baya, kyauta ce na yi maka saboda jin dadin zumuncin daka qulla a tsakaninmu"
Sai Bakura yaji jikinsa ya mutu bakinsa ya kasa cewa komai, kalmar da ta fito daga bakinsa itace
"Allah ya saka da alkhairi, nagode malam. Sai gobe Idan mai dukka ya kaimu da magaruba zan zo."
Ya Juya ya shiga motarsa ya tafi, ya na tafe ya na mamakin malam Yakubu. Lallai Malam Yakubu dattijon arziki ne wanda abun duniya bai dame shi ba. Yadda Malaman zamanin nan da yawa suka lalace saboda kwadayin abun duniya shi kuwa Malam mai bayarwa ne ba mai saka ran zai samu ba.

*** **** ***
Washegari asabar da yamma Bakura da Samira matarsa ne su ke zaune a kan dogowar kujerar babban, falonsu su na kallon wani dadadden bidiyo casset na da can wato wakokin Dan anace wanda ya yiwa Shago.
Yara gaba daya su na makarantar islamaiyya. Domin idan ka ga Bakura ya zauna ya na kallo to ka tabbatar wakokin shata, dan kwairo, Dan anace, Dan maraya, Haruna uji, Garba 'Super, Sani Aliyu Dan dawo, Barmana coge, Uwaliya mai amada ne. Ma' ana wakokin 'yan dambe, 'yan farauta, 'yan tauri da dai sauran finafinan al'adunmu na Hausa wanda gargajiya ce tsagwaro babu kwaikwayon turawa a ciki. Da Samira ta san da haka sai ta bazama ta shiga nemowa maigidanta abinda za ta ja hanklinsa, ta Siyo masa su kala-kala. Na, bidiyo, na CD da na radio, ta zuba masa a mota, wasu a dakinsa, wasu a afalonsa Don haka duk lokacin da Bakura ya ke gida ya na zama tare da iyalinsa su yi ta kallo cikin nishadi annashuwa.
Waqoqin su kan tunawa Bakura labarai na can-can shekarun baya sanda ya ke yaro qarami.
Bakura ya dubi Samira duba irin na jin dadin Ya ce "Gimbiya, da ace ni shugaban qasar Nageria ne da na rusa duk wani qyale-qyale da kwaikwayon al'adun turawa, ana ganin shine wayewa alhalin ba wayewa ba ce ci baya ne. Duk wani dan Nigeria mata, yara da manya dole atamfa za su dinga sakawa, kar kice atamfar za su yi dinkin da suke so ko matsatstsan siket da matsatstsiyar riga, a 'a wadatacciyar riga da mayafin atamfa ma'ana falle biyu irin na da, da ake yi riga da zani da mayafi a samo dan kwali daban a daura. Maza kuma yara da manya sai sun saka riga da wando da babbar riga da hula, kowa a qasar nan shigar da zai yi kenan. Saina hana saka mini siket, shirt, jeans, short kneekers, 3 duater, suits da dai sauransu."
Samira ta kwashe da dariya ta ce "haba Sweety, babbar riga fa ka ce? Yanzu ko ma su aikin a bankuna da likitoci babbar riga zasu dinga sawa, ai sai ta hana su aikin."
Ya yi dariya ya ce "to na yarda su cire idan Likitoci za su yi operation, ma su aikin Bakin su cire su ajiye a gefe su na gama kirga kudin sai su mayar da ita."
Ta gyara zama ta ce "yanzu tsakani da Allah yaya za'ayi ka hada Inyamurai da Yarbawa da mayafin atamfa?"
Ya ce "ai har yanzu Matan Inyamurai su na dinkin zannuwa biyu sai dai ba sa yafawa Sai su daura daya akan daya kin ga idan na saka dokar daukar dayan kawai za su yi su yafa a jikinsu."
Su dukka su ka kwashe da dariya.
Samira ta ce in laifin ka ce mata suyi shigar abaya doguwar riga bawa mai dankwali ko hijab. Maze kuma doguwar riga fara da hirami, irin na Saudia ina ganin ai sun dan fi rashin nauyi."
Bakura ya girgiza kai ya ce "na yarda shigar larabawa shiga ce mai kyau itace shigar musulunci, amma al'adar Hausa na ke so in farfado da ita saboda al'adar Hausa al'ada ce mai kyau wacce ke tafiya da Addinin Musulunci."
Samira ta riqe haba ta ce "wai, wa ya ga ka zama shugaban qasar Nigeria 'yan Nigeria sun hadu da doka."
Ya ce lallai kuwa zan takura musu da dokoki kuma kowa sai ya bi. Dole ne ayi da' a, dole ne ayi aiki,dole ne ayi tsafta, babu zalunci. Na qasa dole ne ya yiwa na samansa biyayya, shugaba dole ya biya na qasa hakkinsa da dai sauran matsaloli dake buwayarmu 'yan Nigeria."
Ya sake kishingida kansa akan hannun kujera ya dube ta ya ce "Gimbiya ina cikin wani hali wanda yake rikirkitacce mai daure kai, mai tsoratarwa matuqa."
Ta gyara zama ta ce "me ya faru? Wani abu aka ce maka ya na faruwa a cikin gidan nan, a kaina ko a kan yara ko kuma a cikin masu aiki ne?"
Bakura ya girgiza kai ya ce "ko daya, babu komai game da cikin gidan nan. A can wata unguwa ne da ake kira Kawo."
Samira ta maimaita "kawo? Na san unguwar Kawo me ke faruwa?"
Yayin da ta dafe kirji zuciyarta na bugun uku-uku.
Ya dube ta ya yi murmushi. Ya ce "kwantar da hankalinki ba wata matsala ba ce uwar tsoro."
Su dukka su ka kwashe da dariya.Tabbas kishiya ce ta fara fado mata a ranta.
Ya sosa qeya ya gyara zama. Ya ce "Na ga wata yarinya budurwa matashiya wacce shekarunta ba su wuce goma sha shida zuwa sha bakwai ba."
Tuni hawaye ya cika idanuwan Samira domin ta san qarshen maganar.
Ta fashe da kuka ta dube shi. Ta ce "Abban Zahra, meye hadinka da yarinyar har ka zo ka ke bani labarinta?"
Bakaru ya girgiza saboda har ya ji ransa ya baci, ya dubi agogo ya juya ya dubi teburin da ke gefansa sai ya suri mukullin motarsa ya dora hularsa akai ya miqe tsaye. Ya dubeta duba na takaici Ya ce "babbar matsalata da ke kenan, ba ki da matsala wajen ladabi da biyayyar aure, ba ki da matsala wajen tarairayar miji, ba ki da matsala wajen koyawa yara tarbiyya, ba ki da

Please Login or Register in order to submit comment