Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nutsuwa idan a gabanta ne? Jiya-jiya ne fa."
Haka dai suka dinga fafatawa har suka gama cin abinci.
Bakura ya yi zunbur ya mike, gami da duba agogo. Ya ce, "Kaduna nake so in je akan maganar wadannan motocin da nace an turo min daga America sun zo, sai kin zaba kin darje kafin kowa ya zaba, saboda ke ce gimbiyar gidan."
Ta harare shi, ta ce, "Ka ce dai ka yi sauti a siyowa amaryarka mota ba ni ba."
Ya kwashe da dariya ya suri mukullin mota yana shirin ficewa.
Ta sa hannu ta kamo hannunsa, ta ce, "Ka fita ka je ina? Ai dole ka shiga kaga lafiyar abar qaunarka, kafin ka fice tunda ba ita ta kawo kanta ba, kai ka ajiye ta."
Bakura ya yi dariya ya ce, "Kai! Kai! Nima na jawowa kaina, na zama kamar waina sai juya ni ake ta ko'ina. To mu je ki raka ni dakin."
Samira na gaba yana biye da ita har falon Sajida. Sajida na ganin su ta daina fara'a ta dauke kai ta juya musu keya. Sai kawayen ne suka gaishe su. Su Kuma su Samira suka gaishe da tsohuwa.
Tsohuwa ta amsa, gami da cewa "mu yanzu za mu koma gida, ga Sajida nan amana, kuma ku yi hakuri da halinta, har Allah Ya sa ta gane."
Samira ta danne zuciyarta ta kalli Sajida ta ce, "Amarya ina kwana. Ko ba ki gaisa da ni ba kya gaisa da angonki ai ko."
Sajida ta yatsune fuska ta tabe baki ta amsa gaisuwa a ciki-ciki. Bakura kuwa ba a raba shi da qurawa Sajida ido. Ya tafi can wata duniyar tunani yana tuno kamannin Zuhuriyya, yana hadawa da abinda idanuwansa suke gane masa.
Kamar daga sama yaji muryar Samira ta katse masa tunaninsa da yake.
Ta ce "Sai ka sa direba ya kai su gida, kuma ka kawo kudin budar bakin amarya a bawa qawayenta su raba."
Nan da nan qawayen amarya suka warware kowacce fadi take, "A ba mu kudin siyan bakin amarya."
Bakura ya yi dariya ya ce, "To zan bawa Samira za ta sallame ku."
Ya juya ya fice, Samira na biyo da shi su na tafe Su na kallon dakwalkwalallen darning table din Sajida kaca-kaca da abinci da kwanukan da suka ci. Kowanne a watse ba tare da an kinkintsa wajen ba, balle a kwasa a kai kicin. Kowacce da ta gama ci sai ta koma Kan kujera ta nade. Don haka Samira na fita ta kira Grace ta ce ta shiga ta kwaso mata kwanukanta ta gyara musu kan tebur.
Bakura da Samida suka dinguma wajen motoci, ya zabi wacce yake so ya shiga, ta zo ta dafa murfin mota.
Ta ce, "Kawo kudin 'yan mata da ka yi alkawari."
Ya ce, 'Ke za ki sallame su ba ni ba, tunda baqinki ne."
Kafin ta ce wani abu ya jawo kofar motarsa ya rufe ya ja dogon ribas yana sheka mata dariya. Ta tsaya tana kallonsa kawai tana takaicin wannan al'amari, domin ita tafi jin haushin kanta da take shiga safgarsa da amaryarsa, ga shi ta zame masa abar tsokana tamkar wata kakarsa. Ta gyada kai ta yi qwafa, gami da cije baki alamar za ka dawo ka same ni.
Ta na shiga falo ta yi kicibus da qawayen amarya da tsohuwa sun fito za su tafi. Cikin fara'a take yi musu magana. "Ba dai har kun fito ba, ba za ku yinin mata ba har ta sake warwarewa ba?"
Su ka amsa cike da murmushi, "A'a daga gida aka yi waya aka ce mu dawo."
Samira ta ce, "To ku jira ni ina zuwa."
Ta shiga dakinta zuwa wani dan lokaci ta fito dauke da kudi, gami da wata leda a shaqe da sabulai kala-kala.
Ta miqa musu ta ce "Ga shi dubu ashirin ce yace a baku, wannan kuma sabulai ne kwa yi wanka ni na baku."
Suka ji wani tsagoron farin ciki ya rufę su, sai suka zube su na godiya.
iyayye ta lankwashe murya ta ce, "Hajiya Samira, gaskiya ba zan 6oye miki ba ko a bayan idonki za mu fada kina da kirki, kuma samun mace kamar ki sai an tona a cikin mata."
Samira ta yi dariya ta ce, "Ba komai ai mun zama daya. Ku je bakin get ku tambayi Lurwanu direba ku ce na ce ya kai ku gida da mukullin mota a hannunsa."
Haka tsohuwar nan ta dinga shi wa Samira albarka, har suka fice.
Samira ta dawo ta zauna a falo tana huci, tana fitar da zazzafar iskar da ta mamaye huhunta. Saboda ba karamin karfin hali ta yi ba wajen danne kishinta, duk wannan kissar da kisisinar ba ta kai zuci ba. Zuciyarta tafasa take tamkar ruwa akan wuta. Daman Sajida jira take kowa ya watse, Allah- Allah take duk su tafi su barta ta kunna sabuwar wayar da Abdulmajid ya aiko mata, don su yi magana. Fitar su iyayye ke da wuya ta dauko wayar ta saka a caji, ba tare da ta bari cajin ya cika ba ta kunna, gami da saka sabon layi da recharge card ta matso lambarsa wacce daman tuni ta haddace ta akai. Koda kuwa daga barci aka tashe ta za ta karanto lambar a Kwakwalwarta.
Bugu daya ya dauka, duk da bai gane kowace ce ba, Kai ka fi cancanta

Balle karya kumallo, bashi da shirin yin wanka ya fita. Daga dukkan alamu zafin rabuwa da Sajida ya shige shi, don a da yana ganin wasa ne ba auren za ta yi ba yanzu kuwa ya tabbata. Har suka gaisa bai
fahimci ita ce ba, sai da ya ji kalamanta masu ratsa masa jiki, sannan ya farga. Kan ka ce kwabo ya ware murya.
Tambayar da ya fara jero mata ita ce, "Da fatan dai baki yarda wani abu ya hada ku ke da wannan banzan mutumin ba kö? Ina fatan ba kya sakar masa fuska, balle ya yi hira da ke ko?"
Ta amsa masa da, "Shi ya isa ma ya matso kusa da ni. Ai ko kallon inda yake ba na yi."
Ana badakala, haka Sajida da Abdulmajid suka dau lokaci mai tsawo su na waya, har sai da kudin wayarta ya qare, shi ma ya kira kudin wayarsa ya qare. Sai ya turo mata text massage cewar ta yi hakuri idan ya fita waje zai sa kati zai kira ta.
Yau farin ciki a zuciyar Sajida baya faduwa, ta sumbaci wayar ta rungume filo, gami dą lumshe ido tamkar tana tare da Abdul a kusa da ita. Yini guda Sajida na nade a daki, sallah ce ke tashinta daga kan gadonta.
Grace ce take kai kawo tsakanin kicin da dakin Sajida. Samira ba ta gaji ba ta aika aka kai mata abincin rana, da a ka kai na dare aka kwaso kwanukan rana. Ba kunya ba tsoro Allah Sajida take nadar abinci ta koma ta kwanta. Bakura bai shigo gida ba sai bayan sallar Isha'i.Bayan ya yi wanka ya ci abinci ya zauna a babban falo, tare da 'ya'yansa da uwar gidansa Samira. Ya taya yara Home work, suka yi 'yar hira, sannan ya sallami kowanne yaro ya je ya kwanta. Samira ma ta yi zumbur ta mike, gami da yi masa sallama ta nufi dakinta. Bakura ya yi kiran duniyar nan Samira ta qi dawowa, ta shige dakinta ta rufe. Yana qoqarin kiranta a waya ta murtsike wayar ta kashe. Ya dade a zaune, sannan ya miqe don tafiya dakinsa ya kwanta, domin ya gaji.Daidai qofar dakin Sajida ya jiyo muryar Sajida na hira har da kyalkyala dariya. Hakan ta ja hankalinsa ga tsayawa tsai yana sauraro. Da farko ya dauka talabijin ce, amma da ya kara kunnensa ya tabbatar muryar Sajida ce ya yi mamaki, sai ya shiga tunanin da wa Sajida take hira haka, to ko qawayen nata ba su tafi ba ne? Sai ya yanke hukuncin shiga dakin ya gani. Yana murda kofa, sai qofa ta bude ya ci sa'a a bude take ba an datse ba. Tsuru-tsuru ya ga Sajida ita kadai, ta yi daidai a kan doguwar kujera tana waya. Sanye take da atamfar dazu, amma kanta babu dankwali ta zubo gashinta har baya tana shafawa, Saboda dadin hira. Ya kalle ta, ta kalle shi kallon Kallon ake yi.
Sai yaji ta ce, "Ka gan shi ma ya shigo dakina ya tsaya yana ta muzu-muzu da ido, ka san kallo ne da shi kamar wani baqauye."
Da jin haka sai Bakura ya sami kújera a setinta ya zauna cike da mamaki.
Can ya yi qarfin hali ya tambaya. "Da wa kike waya, Sajida?"
Ta fada cikin gadara ta ce, "Abdulmajid."
Yadda ta ga Bakura ya tunkaro ta a fusace kamar mai shirin mauje ta, sai ta tsorata, ta wurgar da wayar ta qanqame akan kujera.
Bakura ya tsugunna ya dauki wayar a qasa, sai ya ga har yanzu wayar a kunne take Abdulmajid ne ke ta magana. Bakura ya kara wayar a kunnensa yana sauraronsa, kalmar da yaji yana cewa. "Baby, are you there?"
Bakura ya yi gyaran murya, gami da' cewa, Ba baby ba ce, wannan mai gidanta ne."
Abdui majid ya fada cike da gadara, "Alhamdulillahi, daman ina nemanka. Kai wawa ne, banza, jahili, ta yaya za ka auri yarinya bata sonka, saboda kana da kudi? To wallahi ka kuka da kanka.
idan ba ka saki Sajida ba sai na sa an farfarda min
cikinka."
Bakura ya yi murmushin haushi ya gyada kai. Ya ce "Yaro, idan ni da kai zaa hado mutane masu hankali mu zauna akan teburi daya kowa ya bada labarin abin da ya faru, to jama'a za su tantance waye wawa, banza, jahili. Ka san kai ne wawa, tunda ka bari na kwace maka Sajida a cikin dan qanqanin lokaci, alhali kun dade tare har kun shaqu, don da kana da wayo ba za ka bari in kwace ta daga hannunka ba. Idan jama'a suka ji haka zasu tabbatar maka kai banza ne, tunda aka baka dama ka fito ka aure ta ka kasa fitowa ka qi yin amfani da damar da aka ba ka, har sai da ta subuce maka. Sannan daga karshe ko jama'a ba su fada maka ba, kai da kanka ka san kai jahili ne, marar tarbiyyar addini, tunda za ka raba dare kana magana da matar aure, wacce ba matarka ba. Kuma ina jiran ranar da za ka sa a farde min ciki."
Bakura ya katse wayar ya kashe ta gaba daya ya juya ya dubi Sajida wacce tuni ta kufula tana harararsa. Ya koma ya zauna a kan kujerarar da take fuskantarta, ya dube ta. Ya ce "Abdul majid din ne har yanzu ba ku rabu ba, shin idan shi bai san darajar aure ba ke ba ki sani ba? Ina tabbatar miki halaka ce da azabar Ubangiji akan matar auren da take magana da da namiji, wanda ba muharraminta ba. Sajida ba kya jin maganar iyayenki, ba kya jin maganar mijinkı, alhali mu ne masu qaunarki da gaske."
Ta ji tamkar Bakura yana mata yayyafin ruwan zafi a sassan jikinta, domin kalamansa tamkar zaginta yake haka take ji a kanta.
Ta miqe tsaye tana mai sharara kuka, tana zubar da hawaye ta rike kugu tana girgiza ta ce, "Malam ka rufe min baki ka daina shiga rayuwata, na fada maka na sake maimaitawa na tsane ka, kuma ba zan zauna da kai ba. Wannan wayar da ka kwace ita ce ginshiqin zamana a gidanka, amma tunda ka kwace wallahi sai an neme ni an rasa."
Bakura ya ce "Babu inda za ki je Sajida, ina da kyakkyawan tsaro a gidana, wanda ko jikin get ba za ki iya tabawa ba balle ki bude ki fita, kin shigo gidan nan kenan. Yanzu kin zama killatacciyar kwaryar da na rataye a ragaya, don yin ado da ita, kin fita daga sahun kwarya mai garari a tsakar gida."
Daman kalmar da Bakura ya fara fada mata kenan ita ce ta jawo tsanar da ta yi masa tun farko, yanzu ma an kuma.
Ta sharbe hawaye ta ce "Zahra 'yarka ita ce kwarya mai garari a tsakar gida ba ni ba."
Ta juya a fusace ta na rusa kuka kamar ranta zai fita. Kukan Sajida tamkar dafi ne a cikin zuciyarsa, saboda ji yake tamkar Zuhuriyya ce take kuka. Ya ji hankalinsa ya tashi, ya miqe da sauri ya bi bayanta har cikin daki tana danna qofa yana turawa, har ya kutsa kai.
Ta tafi jikin bango ta maqale ta zazzare masa jajayen idanuwanta masu zubar hawaye. Ta ce "Ka fita ka ba ni waje, ba na sonka, ba na son ganinka, na tsane ka na tsani mai sonka gara in kashe kaina da in zauna da kai."
Bakura ya yi tsaye yana dubanta, hankalinsa idan ya yi dubu ya tashi. Ya fada cikin sanyayyiyar murya Ya ce "Me kike so in yi miki a duniya, don ki yi farin ciki?"
Ta ce "Ka bar ni in auri Abdul majid."
Ya yi shiru, can ya ce, "Abdul Majid ba zai aure ki ba, da na bari ya aure ki."
Ta ce "To ka ba ni wayata don sai na ji muryarsa nake jin dadi."
Abin mamaki sai Bakura ya kunna waya da sauri ya danno lambar Abdul majid, bugu daya wayar ta shiga, sai ya miqa mata, gami da cewa, "Ga Abdul majid dinki"
Cike da mamaki, gami da sanyin jiki ta miqa hannu ta karba ta kara a kunnenta, tabbas shi din ne kuwa. Nan da nan ya ga ta fara murmushi. Ta zo ta wuce Bakura a tsaye kamar gunki ta koma falo ta luntsuma akan kujera ta na hirar soyayyarta ba tsoro, balle fargaba.
Bakura ya zo falo ya sami kujera ya zauna, ya tsura mata ido ya na kallo. Hakika dariyar Sajida ita ce farin cikinsa, domin ji yake tamkar dariyar Zuhuriyya ce. Sai ya tsinci kansa ya na murmushi, tamkar Zuhuriyya ce take cikin farin ciki. Ta yi ta waya ita da abin qaunarta har sai da suka gaji, sannan suka yi sallama ta kashe waya. Ta harari Bakura ta tabe baki ta mike tana tafe tana girgiza ta shige daki ta datse ta yi kwanciyarta.
Tsawon awa guda Bakura bai motsa ba, yana zaune kansa ya kulle. Ya kan raşa abinda yake faruwa da shi. Abu na farko, ba wai tsananin son Sajida yake ba, kuma baya sha'awarta, amma yana ji a jikinsa ba zai iya rabuwa da ita ba saboda kamar da ta yi da wacce ya fi so a rayuwarsa. Haka ko kadan bai ji kishin wayar da suke yi da Abdul majid ba. Ya rasa dalilin da yasa baya gajiya da duban surar Sajida da sauraron muryarta ba. Ya kasa gane daliin da yasa baya Son ganin bacin ranta, balle ya ga hawayenta. Baya taba jin haushin rashin kunyar da take tafka masa, balle ya ji ya tsane ta. Idan ya zo gabanta baya iya yi mata musu, saboda girmamawa. Amsar ita ce Sajida na cin albarkacin Zuhuriyya a wajen Bakura.
Ya miqe a sanyaye ya fito daga dakin Sajida, ya nufi dakinsa. A jikin labule ya hango Samira tana lekensa ta wundon dakinta. Su na hada ido ta yi sauri ta saki labulen ta koma, da alama kishi ya hana ta barci.
Ya yi murmushi ya ce a ransa, "Kya yi kya gama, da kin san yadda muka yi da Sajida da kin tausaya min. Na san duk bayanin da zan yi miki ba za ki yarda ba, don haka shiru shi ya fi alkhairi."
Yana shiga dakinsa ya kulle ya kwanta, sai dai ya dade yana jujjuya abubuwan da suka faru tsakaninsa da Sajida da Abdulmajid.

*** *** ***
Haka gidan Bakura ya kasance, tamkar gidan 'yan adawa. Bakura da Samira ba dadi, tsakanin Sajida da Samira da 'ya'yanta ba dadi. Tsakanin Bakura da Sajida ba dadi. Sajida ta sake kudirar sai ta damula gidan gaba daya, don haka rashin mutunci kala-kala, na yau daban na gobe daban, sai futsara da tsiwa take yi wa Bakura, ta yi wa matarsa.
Samira ta ce ta gaji, don haka babu ruwanta da abincin Sajida, balle ta taka qafarta a dakinta. Grace ce Bakura ya wakilta kacokan ta kula da ci da shan Sajida da kula da gyaran dakunanta da wankin bandakuna. Kai hatta undies dinta Bakura ya ce Grace ta dinga wanke mata zai biya.
Tsawon wata guda kenan da zuwan Sajida bai fi sau biyu ba Zahra ta ga Sajida. Shi ma a qofar dakin Sajida suka hadu, Sajida ta leqo kiran Grace, Zahra kuma ta zo wucewa za ta shiga dakinta suka yi kallon- kallo kowa ya dauke kai.
Duk ranar girkin Samira, Bakura zai kame a dakinsa, Samira ta zo, amma ranar kwanan Sajida sai dai ya bi ta daki, shi ma datse qofar falon take sai dai ya shigo ta qofar baya wacce shi kadai yake da mukullin. Kada ku ce idan ya shiga dakin wani abu ne zai faru, a'a a gaba take sa shi sannan ta danno lambar Abdulmajid su yi ta soyayya don ta saka shi takaici dan idan ya gaji ya sake ta, amma sai ta ga Bakura ko damuwa ba ya yi. Kai har in credit din wayarta ya qare sai ta ga ya zaro recharged card na dubu daya da dari biyar ya ba ta ya ce ta ci gaba da wayarta, ya na gefe yana kallonta cike da murmushi.
Al'amarin Bakura wani lokaci yana ba ta tsoro, don ba ta san abinda yake hada mata ba, dan wannan kasaqen da ya yi mata akwai magana.
Sajida ta ga an doshi watanni biyu da aure, babu alamar gajiyawa a tare da Bakura, ba shi da niyyar jin haushi, balle ya sake ta.Sai ta yi yunqurin hada kaya ta gudu cikin dare, amma abu ya ci tura.Ta kalli tsawon katangar gidan nan ta ga ba irin katangar gidansu ba ce wacce take iya haurawa ba. Ta nufi get ta tabbatar masu gadi su na aikinsu tun karfi ko da yaushe get a datse yake da manya-manyan kwado. Kafin a bude maka get sai sun jero maka tambayoyi, balle a ce su ganta da kayanta a hannu ba a mota ba ta ce za ta je unguwa, ko daya ba za su bar ta ba. Gashi an hana kowa zuwa daga gidansu.

*** *** ***
Wata rana da daddare, dare har ya fara nutsawa Bakura bai dawo gida ba. Sha daya na dare, har ta wuce ba Bakura babu wayarsa, don haka hankalin Samira da 'ya'yanta ya tashi, ko barci suka kasa yi. Yi suke su na qara yi wajen buga wayarsa, amma wayar a kashe. Babu abokinsa da ba ta kira ba, sai su ce ba sa tare da Bakura a yau. Sha biyu daidai wayar Samira ta yi qara alamar ana kiranta, ita da Zahra suka hau rige- rigen dauka. Samira ta danna wayar, gami da kadawar hanta da fargaba. Ta fada "waye yake Magana?"
Cikin harshen turanci mutumin ke magana da alama Inyamuri ne, ya fara da gabatar da kansa. Ya ce, "Sunana Doctor Isreal daga International Hospital. Dan Allah ina magana da Samira ne Mrs. Bakura ne?"
Ai tuni Samira ta rusa kuka ta fara kwakwazo. "Doctor ni ce Samira. Me ya faru da maigidana, ya mutu ne?"
"Bai mutu ba, amma ya sami rauni." sai ta sake fashewa da kuka ta ce, 'Hatsari ya yi ne?"
Ya ce"A'a an kawo mana shi dai ana tunanin yan fashi ne suka dake shi har an farfasa motarsa. Ki kwantar da hankalinki ga shi nan ya miqe yana magana, shine ma ya ba ni lambarki ya ce in kira kı."
Doctor ya sakawa Samira muryar Bakura yayin da ita ma ta danna speaker yadda yaranta za su jiyo muryar mahiafinsu, don su dukka kuka suka zo suka kewaye ta su na yi.
Cikin kuka suke kiran. "Abba, Abba me ya faru da kai?"
Cikin sanyin murya Bakura yake lallashinsu fadi yake, "Na ji sauki, ku daina kuka."
Dukka wannan abinda ake Sajida na bayansu a tsaye ta jingina à jikin bango ta kama kirji ta qame kamar soja. Da alamar akwai sanyin jiki a tare da ita.
Amma da ta ga sun juyo gaba daya su na kallonta, sai ta tabe baki ta harare su sama da qasa ta wuce zuwa dakinta, don kada ma su đauka ya dame ta.
Samira ta aika Zahra da Abubakar, Boy's

Please Login or Register in order to submit comment