Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ba tare da Maman Zahra ta sake cewa komai ba ta jüya ta nufi falo. Zahra ta yi wuf ta afka cikin falonta gami da datse kofar da mukulli, ta dade a jikin kofar a jingine, ta yi ajiyar zuciya mai fitar da tsantsar tashin hankali. Sannan zuciyarta ta tuno mata da addu'ar da ake karantawa idan ka gamu da wata masifa.
"Inna lil laahi wa innaa ilaihi raju'un, Allahumma ajirni fii musiibatii wa aq-likini khairan minhaa."
Ta fada ta maimaita ta sake ta maimaita har sau uku, sannan ta ji numfashinta ya fara dira daidai. Ta wuce bandaki domin dauro alwala. Rabon Zahra da ta rasa sallar Asuba har ta manta, amma yau saboda tsananin tashin hankalin da Abdul majid ya jawo mata ya sa ta rasa sallah akan lokaci, sai da gari ya waye tangararai.
Sallamar sallarta ke da wuya. sai wayarta ta dau ruri. Ta yi ta maza ta suri wayar gami da dubawa, sai Ta ga lambar Abdulmajid ce, a take ta ji wani takaici da daci a ranta. Ta danna a fusace ba tare da ta ce masa komai ba ta kasa kunne tana sauraronsa. Ya yi ta magana tamkar da itace yake waya.
Ya yi gyaran murya ya ce, "Ko ba Zahmajid ba ce, shin kin ga sakonnina na jiya da na yau da safe kuwa ??" da tsurawa aljihun Bakura ido.?JUT







Tun daga nan Zahra ta sake susucewa tabbas shi ne ya turo wannan sakon mahaifinta ya karanta. Babbar matsalar Zahra shine ita ba ta iya tsiwa ba, ba ta san yadda za ta cashewa Abdulmajid ba. Muryarta na karkarwa cikin kuka take masa magiya ta ce "Abdulmajid me yasa kake son jawo min masifa da bala'i a rayuwata? Ba ka sanni ba, ban sanka ba, na fada maka ni yarinya ce qarama yar makaranta. Abbana ya hana ni kula samari, wani lokacin wayata a hannunsa take, sai ya kusan kashe ni a duk lokacin da ya kama text massages dinka ko kiran wayarka. Ka rabu da ni ba na soyayya, ba na sonka."
Ya yi wata shamilalliyar dariya mai kara takaici ga wanda ake yiwa.
Ya ce, "Zahrah wallahi ba zan rabu dake ba, ko da za a kashe ki, nima a kashe ni. Ban taba hanuwa ba idan ina son yarinya ko da iyayen yarinya za su hadiyi zuciya su mutu."
Zahra ta razana ta dora hannu aka ta fasa kuka tana cewa, "Wa iyazubillah, Allah ya yi min tsari da kai."
Ta murtsike waya ta katse. Hannunta na karkarwa ta bude inbox don ta karanta sakon dazu, don taga me mahaifinta ya karanta. Sakon Hassana Ummi Sulaiman ne ta rubuto mata akan maganar yau ba makaranta anjima zata zo a ta koya mata lissafi. Zahra ta yi ajiyar zuciyar jin dadi. Amma sai ta tuna cewa Abdulmajid da bakinsa ya ce ya turo da sako da sassafen nan. "Anya kuwa ba sakon Abdulmajid Abba ya karanta ba kuwa da gama ya goge? Kai sskon Hassana ne ya shigo dazu da na Abdulmajid ne a take zai yi magana ba zai yi shiru ba ya kyale ta ya gyada kai ya wuce ba. Zahra ta shiga wani matsanancin kokonto da wasi-wasi. Abdulmajid ne yake ta tutturo mata sakonni a jere a jere wannan na bin wannan wancan a bayan wancan. Yana kara jaddada mata shi fa yana sonta, kuma ba zai rabu da ita ba. Kuma ko a ina take sai ya nemo ta. Tun tana karantawa ma har ta daina sai dai tayi ta gogewa, daga ya shigo sai ta goge.
Sallamar kaninta Usman ce ta tunasar da ita a duniyar da take, don tuni ta zurfafa a fagen tunanin yadda za ta yi da rayuwarta. Ya shigo ya durkusa a gabanta ya gaishe ta. Zahra na zauno akan sallayar da tayi sallah a tsakar dakinta, ta zubawa Usman ido tana kallo sai can ta bude baki dakyar ta amsa gaisuwar, saboda ba ta kaunar yin magana, ba ta so a kusance ta
yau.
Ya ce "Sister Zahra, Mama ta ce ki fito mu yi break fast ke ake jira tun dazu."
Ta yi kamar ta ce ta koshi, sai ta tuna ashe bata Isa ba lafiyarta kalau ta ce ta koshi mahaifinta na raye a doron kasa tabbas zai hukunta ta.
Ta fada cikin siririyar murya. "Ina zuwa."
Fitarsa ke da wuya ta mike da sauri ta fada bandaki bayan ta yi brush sai tasa sabulu ta wanke fuskarta tas, ta zo ta rangada kwalli a kodadden idanuwanta. Ta saka doguwar jallabiya mai hade da hula ta fito, Kai tsaye ta wuce babban falo kan dining table. Ta iske su su dukka a zazzaune ba wanda ya fara ci ita ake jira. Ta yi musu sallama, gaba daya suka amsa mata. Ta jawo kujera ta zauna ba tare da ta yarda sun hada ido da daya daga cikin mahaifanta ko qannenta ba. Kowa ya zuba nasa a plate bayan sun yi Bismillah da addu'o'i, kamar yadda Bakura ya koyar da iyalinsa tun su na kanana. Dole idan sun zo cin abinci su yi addu'a su ce, "Ya Allah ka kara bamu lafiya, ka raba mu da yunwa, kishirwa, talauci, da fatara. Allah ka raba mu da rowa da hassada da bakin ciki. Allah Ka bamu ikon taimakon mabuqata. Allah Ka taimaki mai nemowa duk sanda ya fita nema kada ya rasa."
Ire-iren wadannan addu'o'i Bakura da iyalansa suke yi, duk sanda suka zo cin abinci sun haddace tsaf kamar karatu. Bayan sun shafa addu'ar a fuskokinsu, sai kowannensu ya farwa plate din dake gabansa ga kofin shayi a gefe. Soyayyen dankali ne da soyayyen kwai, ga farfesun talo-talo a gefe. Sannan ga ferarrun yankakkun kayan marmari kamar gwanda, ayaba, lemo a cikin katon faranti a tsakiyar teburin kowa da cokali mai yatsu (folk) a gabansa wanda zai nutsa ya danko ya kai bakinsa.
Duk wannan rashanar ba dadinta Zahra ke ji ba, tamkar dusa take cusawa a cikinta. Kallon kurillar da mahaifinta ke.yawan yi mata shi yake sake tayar mata da hankali, sai ta ji abincin ya tokare makoshinta ta kasa hadiya. Ta yankewa kanta shawata gara ta fita da gudu ta kelaya aman karya ko ta sami sukuni, ta fake da rashin lafiya dan kar a gane ta na cikin matsala.
Hankalin Maman Zahra ya yi matuqar tashi haka ma qannenta a lokaci guda su dukka suka zabura za su bita bakin qofa inda ta fita ta durqusa tana kakarin amai, Bakura ya daka tsawa ya ce duk su koma su zauna, su ci gaba da cin abincinsu su qyale ta. Wannan al'amari ya yi matuqar ba su mamaki musamman Zahra.
Hankalinta ya tashi matuqa a yanzu bata tantama ta san dalilin da yasa ya yi mata haka, tabbas yaga sakon da Abdulmajid ya turo mata. Ta shigo tana layi yayin da ta nufi hanyar dakinta.
Bakura ya fada cikin bata fuska."Zo ki dauki plate din abincinki da kofin shayinki ki shiga da shi dakinki ki ci a can."
Hannuwanta na karkarwa ta zo ta kwasa, kallo daya za ka yi wa mahaifiyarta da qannenta kaga alamar tausayinta a fuskokinsu.
Sai kalmar "Sannu, sannu, sannu." ce ke fita daga bakunansu.
Zahra na amsawa dakyar ta wuce zuwa dakinta. Ta na shiga sai ta bude wani shafin kuka, musamman da ta jawo wayarta taga missed calls din Abdulmajid da text massages guda biyu, sakonnin dai na soyayya ne har yanzu.
Samira ta dubi maigidanta Bakura ta ajiye cokalin da yake bannunta ta yi ajiyar zuciya.
Ta ce, "Abban Yagana, ko dai tsananin son karatų da naci ne ya jawowa yarinyar nan ciwon ulcer saboda rashin maida kai ta ci abincin kirki?"
Shiru yayi bai ba ta amsa ba. Aka jima Samira ta kasa daurewa ta dube shi ta ce "Oga baka ganin rashin baccin da yarinyar nan ke yi shi ya jawo mata kasala da jan ido? Ya kanmata a kaita asibiti tun dazu na lura da ita kamar tana fama da zazzabin cikin kashi. tana zazzabin dare ne?"
Wannan karon ma danna abinci yake a cikinsa ko kallonta bai yi ba.
Samira ta fusata ta miqe ta yi wuf ta fada dakin 'yarta Zahra, a rigingine ta iske ta ta na kallon silin da fankar da ke jujjuyawa a hankali. Daga dukkan alamu tunani ke damunta. Zahra ta yi firgigit ta miqe zaune da ta hango mahaifiyarta na shigowa. Kafin Samira ta ce wani abu wayar Zahra ce ta dau ruri. Ta na dubawa sai taga lambar Abdulmajid ce.
Tashin hankali marar musaltuwa ne ya rufto mata, ta kalli wayar ta daga kai ta kalli mahaifiyarta.
Sai Samira ta ce, "Ki amsa wayar mana."
Zahra ta ce "Mama ban san lambar ba." Samira ta ce "Sai an san lamba ake amsawa, ko ke ma mulkin ne irin na Abbanki maganarsa ma sai an siya wataran?"
Zahra ba ta daga wayar ba har ta katse. Samira ta zauna a gefen gado ta dubi plate din abinci da kofin shayin, dankar yake da abinci ko dandanawa bata yi ba.
Ta juya ta dubi Zahra ta ce, "Yagana me yake damunki ne yau?"
Zahra ta lumshe ido ta yi murmushin karfin ta ce, "Mama bani da lafiya."
"Ciwon mai yake damunki?" Samira ta tambaya.
Kafin ta ba ta amsa shigowar Bakura ce ta katse su, Samira ta miqe a fusace ta fice daga dakin dan ta ji haushin share ta da yayi dazu tana yi masa magana.
Zahra ta firgita ta daga kai ta dube shi ta zabura ta gyara zama. Ta ce, "Abba sannu da gida," Ya ce "Yauwa, Mamana ya jikinki? Wai me yake damunki ne."
Ta sosa weya ta ce "Abba, ciwon kai ne."
Ya ce "Ba wani ciwon kai rashin barci dai. Ki ci abinci ki sha maganin ciwon kai ki kwanta ki yi barci,
rashin bacci ne yake damunki. ...."
Kafin Bakura ya rufe bakinsa wayar Zahra ta dau ruri. Yayin da zuciyarta ta fara dukan uku-uku, musamman data duba ta ga lambar da ake kiranta, Abdulmajid ne. Saboda gudun zargi ta yi sauri ta danna yayin da hannunta ya dauki rawa, cikin karkarwar murya ta yi sallama.
Ya amsa mata da cewa "Wa'alaikis salam ya abar qaunata. Zahra, me yasa kike azabtar da ni, kike wulakanta ni a dalilin tsantsar son da nake yi miki?"
Ta yi caraf ta ce "Wrong number." Ta katse wayar. Kafin ta ce wani abu tuni Bakura ya juya ya fice ba tare da ya yi mata salama ba.
Zahra ta shiga halin la'ila hau ilahi da matsananciyar damuwa. Zuciyarta ta shiga zullumi.
Ta ce a ranta" Anya kuwa Abban bai jiyo abin da Abdul majid ke fada ba? Tabbas rayuwata tana cikin garari, hakika za mu raba gari da Abbana."
Ya iske Samira a falo tana tsaye, ya zo ya wuce ta da sauri ya nufi kofar fita gami da ce mata "Mun tafi, sai mun dawo."
Ta bi shi a baya tana masa fatan alkhairi har sai da ta ga fitarsu daga cikin gidan, Sannan ta dawo ciki, ta dawo zuciyarta cike da mamakin irin wannan hali na maigidanta. Wani murdadden mutum ne, mai rikakken ra'ayi, kamar ba yanzu ta dinga yi masa maganar rashin lafiyar Zahra ba, ya yi shiru kai ka ce da dutse take magana. Amma gashi da kansa ya shiga ya duba ta.
Tayi murmushi ta Ta fada a bayyane"Malam Bakura kenan, Kanuri na
Samira sarkin mulki."



Tafi-tafiya kwanaki uku kenan da Abdul majid ya fara takurawa Zahra ta waya, don haka kwanaki uku kenan da susucewar Zahra. A takure take ta kasa sukuni, ba ta kaunar zama a cikin 'yan gidansu, saboda takura ma ta da Abdulmajid yake a waya. kullum tana qunshe a daki tana cutar karya. Tana ji tana gani aka kai ta asibiti aka tulo mata magunguna iri-iri tana sha, dan dolenta. Don haka take yawan kwanciya, jikinta duk kasala, sai yawan barci kullum a kwance a daki.
La'asar sakaliya Samira da Bakura za su fita unguwa, gaisuwar mutuwa zasu je gidan wani abokin
Bakura da mahaifiyarsa ta rasu a unguwar Na'ibawa. Samira ta iske Zahra a kishingide akan doguwar kujerar falonta ta kafawa akwatin talabijin ido, amma hankalinta baya kan abin da yake gudana, babu abin da take fahimta tunaninta na kan halin da Abdulmajid ya jefa ta. Wayarta na gefenta ta saka ta a silent saboda damun da Abdulmajid yake yi mata da kira da text massages.
Samira ta dubi Zahra ta ce "Ya ya jikin naki, kin sha magani?"
Zahra ta langwabe kai ta yi magana cikin marainiyar murya ta ce "Mama da sauki."
Samira ta dafa kanta ta ji ba zafi. Ta yi murmushin jin dadi ta ce "Yau babu ciwon kan, na ji kan ki ba zafi. Za mu fita ni da Abbanki, za mu je gaisuwa gidan su Maman Zulai yau kwana uku. Ki fito babban falo ki zauna tare da yara ki kula da masu shigowa. Ki fadawa cook abin da kike so su dafa miki, kada ki zauna da yunwa, ba'a son masu ulcer su dinga zama da yunwa."
Zahra ta mike tsaye ta yi murmushin karfin hali.
Ta ce "To Mama sai kin dawo."
Su ka dunguma suka fito tare. Kafin su fito har
Bakura ya shiga mota yana jiran Samira, don haka da sauri ta fice.
Zahra ta kishingida akan doguwar kujera tana kallon talabijin yayin da Abubakar qanninta yake Zaune akan kujerar gefenta yana kallon shi ma, a jima kadan ya dube ta ya girgiza kai don tausayin yanayin da yaga take ciki.
Ya ce," Sister Zahra sannu."
Ta amsa da "Yauwa." Sauran kannenta kuwa Umàr da Usman suna farfajiyar gidan su na kwallo. A hankali a hankalin bacci mai nauyi ya kwashe Zahra. Kamar daga sama take Jiyo muryar Abubakar yana ta magana. Inda hankalinta ya sake karkata da sauraron abin da yake cewa ambaton sunanta da ta ji yana yi a hirar. Dakyar take bude idonta ta hango shi a zaune da alama waya ce a hannunsa. Abin mamakin shine ta san Abubakar ba shi da waya. A ina ya sami wáya yake ta magana tun dazu? Me yake cewa kuma da wa yake magana har yake ta ambaton Zahra, Zahra? Cikin magagin bacci ta laluba gefenta za ta dauki wayarta sai ta ji wayam babu komai. Ta zabura ta miqe zaune ta dubi Abubakar ya dube ta shima.
Ta tambaye shi "Wayata
ce a hannunka?"
Ya gyada kai ya ce "Ita ce kina barci ake ta kira ba ki ji ba kin saka a silent? Ya sake kara wayar a kunnansa ya cewa mutumin da suke magana a waya "hold on ga ta ma ta farka daga barcin bari in bata."
Ya taso da sauri ya dungura mata a kunne gami da cewa "Sunansa Abdulmajid."
Kafin Abdulmajid ya yi magana Zahra ta yi sauri ta dauke wayar daga kunnenta kai ka ce garwashin wuta aka dana mata. Ta yi sauri ta katse wayar. A fusacc take yi wa Abubakar magana.
Ta ce "Ba ka da hankali, ya zaka amsa waya? Ba ka san mutum ba, baka san lamba ba ka hau hira da shi. Watakila ma wrong number ya kira don ni ban san wani Abdulmajid ba."
Abubakar ya ce "Shi ya sanki har ya fadi sunanki."
Zahra tayi shiru ta kasa magana don ta rasa abinda zata ce masa.
Cikin sanyin jiki tayi ajiyar zuciya. Ta ce "meya ce maka?"
Abubakar ya ce "ce min yayi ni kaninki ne, a wacce makaranta muke? In ne gidan mu?"
Zahra ta zabura ta dafe kirji ta ce "meyasa zaka bashi address dina har ka fada masa makarantarmu?"
Abubakar ya rude gaba daya ganin yadda idanuwanta suka firfito suka cika da hawaye saboda damuwa.
Ya ce "ban fada masa ba, mun fara wayar kenan kika farka."
Ta ji zuciyarta tayi sanyi kadan, hankalinta ya kwanta. Ta mike ta nufi dakinta dauke da wayarta a hannu. Tana shiga daki ta bude wayar ta zare sim card din ta balla shi gida biyu taje ta jefa a toilet ta kwara ruwa ya tafi. Ta dawo ta kwanta a kan gado tana huci don takaici.
Can ta tuna a ranta ai kuwa tayi aikin banza da ta karkarya sim card shi kadai. Ya za'ayi ace sim card ya bata waya bata bata ba? Ai hankali ma ba zai dauka ba. Tayi zumbur ta mike zaune tana tunanin hanyar da zata bi ta salwantar da wayarta ta hanya mafi sauki ba tare da an gane ba. Da farko tayi tunanin ta jefa wayar a toilet tayi flushing, sai ta tuna ashe ba zai wuce ba zai toshe toiet din. Tayi tunanin ta je swimming pool ta jefa, Sai ta tuna ai za a tsinta idan aka tashi wanke wajen. Idan ta jeta a shara masu zubar da shara zasu tsinta su kawo. Sai ta yanke shawara ta tafi bayan Katanga ta wurgar. Da ta isa bayan katangar sai ta cire bayan wayar daban, sannan ta wurga ta cire batir din wayar ta koma wata kusurwar ta wurgar ta sake koma wata kusurwar ta wurgar da fuskar wayar. Haka ta aiwatar amma sai da ta faki idanuwan 'yan gidan ta tabbatar babu wanda yake ganinta ta je ta wurgar ta dawo ta kwanta tana mai shakar iskar farin ciki da kwanciyar ta hankali. Ta ci gaba da tunanin karyar da zata zabgawa iyayenta a game da batan wayarta. Ba ta damu ta fada musu ba ta san babu wanda zai yi mata fada a cikinsu. Matsalarta su gane Abdulmajid yana yi mata waya amma ba ta batan wayarta ba, waya ba komai ba ce. Jinta take wasai tamkar ta sauke wani kaya daya dame ta da nauyi a kanta. Salwantar da wayar da tayi ta farfado mata da dumbin farin ciki da walwalar da ta rasa a kwanakin baya a sanadiyyar takura mata da wayar da AbdulAbdulmajid yayi. Kan kace kwabo Zahra ta dawo kamar da,ta sa karatunta a gaba.
Kuma tuni ta tsara mahaifanta akan batan wayarta babu wanda ya tuhumeta ko ya tsareta da tambaya akan dalilin batan wayarta.
Bayan kwana biyu Bakura ya siyo mata sabon layi na Glo da kan waya kirar Iphone.

*** *** ****
Sajida ce a zaune a cikin rana taną Juye-juye. Kallo daya zaka yi mata ka tabbatar bata jin dadin jikinta ga tsananin damuwa. Umma furera ce ta fito daga dakinta dauke da katuwar fanteka a cike da geron kunun kanwarta na Siyarwa zaa kai mata Surfe.Dakyar take tafiya saboda nauyi, ta cije baki ta ajiye a kasa yayin da ta dafe kashin bayanta tana sallati.
Ta juya ta dubi sajida. Ta ce "yanzu Sajida ba zaki tashi daga rana ba? Tun dazu nake faman yi da bakina amma kinki tashi, hantsin har ya fara zafi. Idan sanyi kike ji ki shiga daki ki lulluba, rana ciwon kai da zazzabi zata sake jawo miki."
Sajida ta dago da luhu-luhun idamuwanta wadanda suka kumbura a sanadiyyar koke-koke da zafin zazzabi ta dubi mahaifiyarta.Ta ce "Umma, tabbas kun kusa ku nemeni ku rasa kuma idan na tafi na tafi kenan."
Umma Furera tayi kasake a tsaye ta hada hannu ta rike ciki tana duban Sajida. Can ta karaso inda take ta ciccibo hakarkarinta ta daga ta tsaye. Tana fadin tashi daga rana mu koma inuwa sai muyi maganar. Umma Furera ta mayar da Sajida inuwa ta zaunar da ita akan wata tsohuwar tabarma ta jawo kujera ta zauna a kusa da Sajida.
Ta ce "yanzu Sajida ba zaki hakura ki fauwala Allah komai ba, akan Abdul majid ki ringa kokarin ki kashe kanki. Babu ci ba sha har kike tunanin guduwa a nemeki a rasa ki jefa iyayenki da yan'uwanki da duk wani mai sonki cikin damuwa da bacin rai dauwamammiya. Idan kika gudu kin tashe mu tsaye musamman ni da mahaifinki, zaki tasar mana da ciwon da zai iya zama ajalinmu. Ga mahaifinki ya tsufa fuk daya zuciyarsa zata iya fashewa, nima gashi girma ya zo kece abokiyar shawarata tamkar qawata nake hira dake ga dan karamin kaninki yahuza duk inda ya fita ya samo labari wajenki yake nufowa kai tsaye ya fesa miki. Idan kika tafi kika bar mu yaya zamu yi?"
Ummma furera ta fashe da kuka. Sajida ma kukan ya kece mata. Har tsawon lokaci babu mai iya lallashin wani. Sajida ta dago da jajayen idanuwanta ta dubi mahaifiyarya.
Ta ce "Umma, ina tunanin yarinyar nan Zahra da ta zo kwanakin baya, turo ta aka yi ta zo taga halinda nake ciki da Abdulmajid ta kai rahoto domin ita tasan ina lekawa ta katanga ina aron waya in bugawa Abdul majid."
Umma furera ta tsagaita da kukan ta dubi Sajida fuskarta cike da rudani. Tayi doguwar ajiyar zuciya.
Ta ce "Sajida ban fahimce ki ba. Wacce yarinya kike magana?"
Sajida ta

Please Login or Register in order to submit comment