Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba, sai dai kada ki yarda wani abu ya shiga tsakaninku. Nan da wani dan lokaci idan na gama shirya abinda nake shiryawa zan san yadda zan fito da ke mu gudu a rasa mu. Kinaji na ko?"
Sajida ta amsa cike da ladabi da tsananin tsoro.
Ya ce, "Ki goge hawayenki ki daina kuka, ki dauka tamkar na kai ki ajiya ne nan da wani loakci zan zo in dau ajiyata."
Su duka suka yi murmushi, Sajida ta goge hawayenta ta ci gaba da kallon abin kaunarta Sajimajid tana sauraron dadadan kalamansa.
Daya daga cikin tsofaffin nan ce ta zuro da kanta tsakiyar Sajida da Abdul majid ta ce "Daman kin san dircban nan ne ku ke hira? Na ga alamar ma Buzu ne, don na ji kuna yaren Buzaye, daman kin iya yaren? Wacce irin hira ku ke yi idan kika yi kuka sai ki yi dariya kuma?"
Haushi ya rufe Sajida da Abdul majid, har suka rasa abun da za su ce mata.
iyayye ce ta ba ta amsa. Ta ce, "Iya, dan Allah ki gyara zamanki, ina ruwanki da hirarsu."
Tsohuwa ta koma ta zauna. Ta ce "A'a, 'yar nan kar ki ga laifina, dole in tambaya, don in sani. Na sani ko wannan dan iskan ne Abdul majid da take so ya aiko Buzu ya sace ta."
Daya tsohuwar ta ce, "Ai kuwa da mun cî ubansu, don idona idon Abdul majid sai na sharara masa mari, saboda wahalar damu da yake yi. Gaba daya ya hargitsawa yarinya lissafi, ya hanata zama lafiya, ga gidan arziki da wadata ta samu, amma ta qi kwantar da hankalinta. Ai shi ma Abdul majid din ko hauka yake ba zai fara tako qafarsa qofar gidanmu ba, ko ya turo a saçe ta ba."
Sajida ta juyo ta dube su, duba na takaici da bacin rai sai ta ja dogon tsaki ta juyar da kanta gefe.
Abdul majid kuwa mudubi ya seta baya yana kallon tsohuwar da take niyyar kwashe shi da mari, sai ya yi murmushi kawai.
iyayye kuwa kunshe baki ta yi da gyalenta tana ta dariya a ciki-ciki. Daidai lokacin ne motocin da suke gaban su Abdul majid suka saka siginal din shiga wani katafaren gida. Nan da nan masu gadi suka wangale get a jere a layi motocin daukar amarya suka dinga kutsa kai su na shiga.
Abdul majid ya ja rawaninsa ya rufe fuskarsa, sai idanuwansa ne kawai a fili, ya wangale idanuwan nan nasa kwala-kwala yana duban farfajiyar gidan. Ya gasgata, ya tabbatar Bakura ba sa'an yinsa ba ne ya cara masa wajen naira, sai dai su goga da babansa, koma Bakura ya fi Babansa kudi.
Kalmar da yake ta fada kenan. "Wonderfiul, fantastic, beatiful. "
Wata tsoka ce daga cikin qirjin Sajida ta yanke ta yi wani qarai, yayin da kuka ya tunkarowa kwayar idanuwanta.
Ta dubi Abdulmajid ta fada cikin harshen turanci.
"Ka kawo ni gidan wanda ba na kauna a rayuwata ka ajiye ni za ka tafi ka bar ni ko?"
Ya cije baki ba tare da ya ba ta amsa ba.
Ta sake cewa "in har kana sona ba za ka so in zauna da wani kato a gida daya ba da sunan mijina. Mai zai hana ka tunkari hatsari, wuya da duk wani wulakancin da za a yi mana kamar yadda na yarda zan gudu koda za a kashe ni."
Ya sami waje ya tsaya ya zare mata jajayen idanuwansa da suka cika da hawaye ya ce, "Fita ki shiga gidan nan kafin wadanda suka sanni su zo su gane ni. Zan bawa iyayye sabon layi da wayar da na siya miki zata kawo miki, za mu dinga magana. Na fada miki ki daina kuka, kuma ina tare da ke a duk inda ki ke."
Kaico! Soyayya gamon jini, sai Abdulmajid ya fashe da kuka .
Cikin shashshekar kuka Sajida ta bude kofa da sauri ta fice tamkar ranta zai fice.
iyayye da tsofaffi suka fita suma suka bi bayan Sajida. Duk wanda yake qoqarin ya riqe ta sai ta fusge. Babu yadda ba a yi ba akan ta sa mayafi ta rufe fuskarta amma ta qi, haka ta shiga gidan mayafinta a kafada, dauri a gaban goshi wato ture ka ga tsiya, ga wani kodadden idon da ya sha koke-koke.
A babban falo suka iske Samira da 'yan uwanta da makwabta jingim suna jiran isowar amarya. Bayan 'yan uwan Sajida sun yi sallama, su Samira suka amsa musu, sai tsofaffi biyu 'yan uwan Sajida suka shiga tsakiyar Sajida suka kaita gaban Samira suka durkusar, sannan kowa ya sami waje ya zauna.
Bayan an gaggaisa aka fara bayani, dangin Sajida ne su ka ce. "To uwargida, ga Sajida mun kawo miki ku zauna lafiya qanwarki ce, koma mu ce 'yarki ce ki gyara mata, idan ta yi kuskure. Ke kuma Sajida yi na yi, bari na bari, ke ce qarama."
Samira na murmushin qarfin hali, dan ba qaramin yaqi ta yi ba da ta danne kishinta ta zauna tana sauraron wadannan bayanai.
Sajida kuwa idonta tsai akan Samira da tawagarta bayan kallon banza ma har da harara take harba musu daya bayan daya. Can idonta ya hasko mata Zahra a zaune a lungu, nan fa ta kafa mata ido tana harara sama da qasa har da girgiza kai wato 'ada kai kawai na fasa miki, yanzu kuma sai na ragargaza kan dukka'.
Zahra ta yi sauri ta sunkuyar da kai qasa, yayin da jikinta ya dau rawa, a halin yanzu tafi tsoron Sajida a kan mutuwarta.
Haka Hajja Farida ta riqe baki tana kallon Sajida tana gyada kai, tana jinjina fitsarar Sajida. Ta tabbatar yarinyar nan ba ta shigo da niyyar zaman lafiya ba. Haka suka dinga kallon-kallo tsakanin Samira da tawagarta da 'yan uwan Sajida.
Tun kafin a gama bayani Sajida ta yi zumbur ta mike tsaye ta yi kiri-kiri da ido tana duban jama'ar, ma'ana idan za ku daina bata yawun bakin ku gara ku daina, don ni babu zaman lafiya a tare da ni. Manufarta kenan duk da ba ta furta ba.
Ba shiri 'yan kawo amarya suka miqe suka saka ta a tsakiya aka ja ta zuwa dakinta, tun kafin ta bude baki ta fadi wata magana da za ta kunyata su. Sajida na tafiya ta na girgiza tana tabe baki.
"Lallai wannan falalliyar 'yar za a yi da ita." ln ji Hajiya Zuwaira. Daya daga cikin yayyun Samira.
Samira ta koma ta jingina da jikin kujera jikinta a sanyaye, sai gyada kai take tana al'ajabin yadda Bakura yana ji yana gani ya dauko wannan halittar ya kawo musu gida.
Hajja Farida ta dau dogon salati ta salallame ta ce, "Tun da nake a doron kasa shekaruna arba'in har da doriya, ban taba ganin fitsararriyar amarya irin Sajida ba."
Nan dai kowacce mace ta fara tofa albarkacin bakinta, tana zayyano abun al'ajabin da idanuwansu suka hango game da Sajida.
Daga karshe suka bawa Samira hakuri da nasihar ta ci gaba da hakuri komai nisan jifa qasa zai fado. Ta ci gaba da yi wa mijinta biyayya ta zuba musu ido ta yi kallon yadda za ta qarqe musu, wato tsakanin ango da amarya. Daga karshe dangin Samira suka kaiwa dangin amarya abinci kala-kala, abun sha da snacks da aka yi musu, sannan kowacce ta kama gabanta.
Sajida ta yi mamaki matuqa yadda Bakura ya kashe kudi ya gyara mata daki, ba tare da sisin yayenta ba. Ta yi matukar mamakin inda Bakura ya santa har ya kamu da sonta haka. Wasu abubuwan ma daga ita har yan uwanta ba su san shi ba, na turai ne, Musamman da suka shiga cikin bandakuna sun hadu an zuba kayan Kamshi da na decoration. Aka yi shawara a bar qawayen amarya guda hudu da tsohuwa daya su kwana da ita ko Allah zai sa hankalinta zai dan kwanta.
Haka kuwa aka yi kafin sha biyun dare gaba daya 'yan rakiyar amarya da masu karbar amarya sun watse. Kawayen amarya ne guda hudu da tsohuwa daya suka rage a dakin Sajida.
Samira da 'ya'yanta ne jugum a zaune a falo har Bakura ya shigo gidan ba su iya tashi sun je sun kwanta ba, abun duniya ya ishe su kasancewar Bakura ya san abinda zai tarar don haka bai bari ko da daya daga abokansa ya rako shi ba.
Haka ya shigo hannunsa ziqai bai siyo kazar amarci ba irin ta al'ada. To duk abinda zai suyo na marmari akwai shi jingim a gidansa, masu aiki ma ya ishe su, balle iyalansa. Kaza ce, juices, fruits, duk su na nan a shaqe a firij. Ya yi sallama ya shigo falon, gami da murda mukulli ya kulle kofar. Su duka suka amsa masa a sanyaye.
Ya dube su ya yi murmushi ya ce, "Yara ba ku yi barci ba, har yanzu? Gobe fa Monday. Yau ba a cewa Abba oyoyo ne?"
Abubakar ya taso ya miqawa mahaifinsa hannu suka tafa, haka Umar da Usman ma a layi suka zo suka tafa.
Zahra ta taso ta dubi mahaifinta a sanyaye ta ce, "Congratulations Abba, ina muku fatan alkhairi."
Sai qannenta duka suka hada baki, "Congratulations Abba."
Mamaki ya kama Bakura ya tabbatar Zahra tana taya mahaifiyarta kishi ba kuma kishin kadai take taya ta ba, wacce ya auro ita ce damuwarta. Da a ce wata ya auro ba Sajida ba, ya san Zahra za ta bi bayansa ba za ta bi bayan mahaifiyarta ba, saboda Zahra tafi son abun da mahaifinta ke so.
Yaran ne suka katse masa tunaninsa suka hada baki, "Good night Abba, Good night Mama."
"Good night children. " Samira da maigidanta suka fada cike da fara'a.
Yara suka nufi dakunansu ba tare da su na jin dadin zuciyoyinsu ba.
Bakura ya matso kusa da Samira ya zauna ya dube ta ya yi murmushi ya fada cikin wata 'yar siririyar murya. Ya ce, "Samira, kin yi kyau, kamar ke ce amaryar, har kin fi amaryar."
Hohoho! Idan ka tona zuciyar Samira za ka yi mamakin irin baqin da ta yi, don takaici.
Ta bata rai, gami da daga hannu ta dakatar da shi.
Ta ce, "Ba na so, kar ma ka fara wannan zancen. Ni a suwa? Ka tashi mu je in rakaka dakin wacce yau za ta ji dadin kalamanka, amma ba ni ba."
Ta mike tsaye zumbur ta rike kugu tana girgiza kamar mai shirin dambe, sai huci take tamkar kasa. Ba musu Bakura ya mike bakinsa cike da magana, haka dariya take son kufce masa, amma yana tsoron furtawa. Su na isa kofar dakin Sajida sai ya ji gabansa ya yanke ya fadi. Samira ta daga hannu za ta murda kofar ta bude, sai Bakura ya rike hannunta.
Ya ce, "Kar ki bude, mu je dakina ki taya ni kwana, ni ba sai na ganta ba."
Haushinsa ya sake rufe zuciyarta, ta fusge hannunta ta murda kofa ta tura kai cikin dakin, gamị da kwada sallama. Sun yi dayday a falo su duka kowacce ta lumtsuma cikin kujera mai laushi, sai lumshe ido suke yi. Ga A.C na ratsa sassan jikinsu, ga talabijin su na kallo.
Lokaci guda suka dago da idanuwansu suna kallon Samira, ta waiwaya bayanta ta tsuke fuska ta ce da Bakura. "Shigo mana."
Ya shigo cikin falon, yayin da idanuwansa suka dira akan Sajida kiri-kiri yana kallonta, kasancewar haske tar gashi ba ta bunjima hijabin nan na ta ba. Ba mayafi, ba dankwali tana zaune ta harde kafa tana saqe-saqen tuggu a zuciyarta. Kan ka ce kwabo Sajida ta murtuke fuska ta fara harbo masa kibiyoyin harara.
"Wai wannan yarinyar wacce irin kama su ka yi da Zuhurriyya haka kamar an tsaga kara ?" Bakura ya fada a zuciyarsa.
Ya yi karfin hali ya durkusa ya gaishe da tsohowar nan, yayin da su iyayye ma suka gaishe shi, ya amsa cike da fara'a, gami da cewa. "Me ku ke bukata a kawo muku?"
Su duka suka hada baki,
"Babu komai."
Samira ta yatsune fuska ta ce, "To amarya ga angonki na kawo miki, babu abinda zan ce sai addu'a, Allah ya bada zaman lafiya, ya kawo kazantar daki. Sai ku dunguma ki bishi dakinsa ni dai na tafi sai da safe."
Samira ta juya za ta fita Bakura ya yi zuruf ya bi ta a baya, suka fice.
Sajida ta ja wani dogon tsaki ta murguda baki ta ce,
"Wa ya ga amarya, amma kuwa kin yi batan kai da ki ka shigo min da wannan mutumin dakina."
Caraf Iyayye ta yi sauri ta toshewa Sajida baki, don kada su Samira su juyo ta.
Nan fa suka hau rokar Sajida akan ta tashi ta shirya ta je dakin ango. Saboda takaici ko kallonsu ba ta yi ba ta tashi ta shige uwar daki ta kwanta kan gado ko kayan jikinta ba ta cire ba.
A kofar dakin Samira suka tsaya suka dauki lokaci mai tsawo su na tataburza har da kokaye-kokaye. Bakura zai shiga dakinta, ita kuma ta ce ba zai shigar mata daki ba sai dai ya tafi dakinsa don ta san in anjima amaryarsa za ta je ta same shi.
Kalmar da ta fito daga bakin Bakura ita ta bawa Samira mamaki da ya ce "Ko Kur'ani ki ka ba ni zan dafa cewar Sajida ba za ta zo inda nake ba, saboda ba ta sona."
Wani kallo na takaici, gami da karka raina min hankali mana, haka Samira ta kalle shi ta tabe baki. Ta ce, "Ai kai kana sonta, tunda ka auro ta sai ku je can ku karata."
Ta yi wuf ta shige dakinta ta datse ta bar shi anan a tsaye. Ya yi shiru yana tunani, ya kalli kofar dakin Sajida, ya juya ya dubi dakin Samira sai ya girgiza kai ya yi murmushi, ya juya ya nufi dakinsa.
Yana shiga dakinsa ya tura qofa ya rufe yasa hannu a aljihunsa ya zaro wasu hotuna guda biyu ya ajiye a tsakiyar gadonsa. Hotunan Sajida ne, wanda aka dauke ta a tsakar gidansu dazu da yamma a wajen yinin bikinta.
Daya kafin ta yi wanka aka dauka, dayan kuma bayan ta yi wanka ta caba ado daidai lokacin da ta yi wannan murmushin nata aka dauka. Wato mai daukar hoton har ya wanko ya kawo masa shi ne ya bar sauran a mota ya zabo guda biyun nan wanda take ita kadai don ya tantance abinda ya ke so ya tantance.
Ya shiga bandaki, ya dade yana kwara ruwa a jikinsa, saboda duk jikinsa danko yake yi masa. Yana fitowa daure da tawul, sai ya zura doguwar riga 'yar yaloluwa marar nauyi. Ya taka gado ya kinkimo wata 'yar akwati akan wadurof ya zo ya zauna akan gado, ya baje wasu hotuna a tsakiyar gadonsa. Ma'ana hotunan Zuhuriyyarsa ne ya hada da hotunan Sajidarsa, don ya ga ta inda suka bambanta. Ai kuwa sak kamarsu daya, kirar jikin ma daya, ga dariya da murmushinsu iri daya. Sai mamakinsa ya sake daduwa. Surutai yake shi kadai cikin dare, kamar tababbe.
Hakika Bakura yana cikin wani hali domin akan ya san asalin wannan kama ya sa ya auro Sajida, amma har yanzu babu wata shaida da ta nuna masa alaka ko kadan tsakanin Sajida da Zuuriyya. Haka Bakura ya raba dare, sannan ya hakura ya kwanta.
Gajiya, gami da dogon daren da ya raba bai yi barci ba basu hana shi tashi da Asuba ya je masallaci ba. Ya na dawowa ya bi dakunan gidan gaba daya yana bugawa har da dakin Sajida.
Kowa ya tashi wuri-wuri ya shiga bandaki, don dauro alwala. Bakura kuwa da ya tabbatar kowa ya tashi sai ya shiga nasa dakin ya kwanta, saboda barcin da ya addabi idanuwansa ya sake kwanciya.
Samira kuwa tana farkawa bayan ta yi sallah, sai ta shiga kicin ita da kukunta suka shiga shiryawa yara 'yan makaranta abinci. Haka abincin mai gidanta da na Sajida da 'yan uwanta daban. Yau Samira ta sake zagewa wajen qara qawata abinci fiye da kullum, saboda tana so ta nunawa su Sajida bakin rijiya ba wajen wasan yara ba ne. Ta na so Bakura ya san ba irinta ake aurowa kishiya ba, saboda babu abin da amaryar za ta fi ta. Bayan komai ya dahu, ta dauko tsala-tsalan food fasks hade da plates da cokula da saving spoons hadaddu wadanda ta suyo su daga Saudiya na sarakai ne, domin an diga ruwan gwal da azurfa a jiki. Burinta ta burge qauyawan nan da suka zo gidanta da sunan amarya da qawayenta. Ta kira masu aikinta guda biyu Hajara da Grace suka dinga diba su na shigarwa dakin Sajida su na jerawa akan Dining table, yayin da farin ciki ya lullube zuciyar qawayen Sajida.
Sai kalmar "Sannu, mun gode." Suke fadi, daidai lokacin Sajida ta fito falo das da ita, ta yi wanka ta caba ado da wata atamfarta Super Holand kalar kore da ruwan dorawa (Green and ycllow) wacce ta sha dinkin riga da zani daidai jikinta. Ta kuwa nada dauri cas da ita kai ka ce ango ta yi wa wannan ado. Sai kamshi ne ke biye da ita a sanadiyar feshe jikinta da ta yi da turare (Designers).
Hakika yunwa ce taf a cike a cikin Sajida, kasancewar jiya ba ta ci abincin kirki ba. Dan yunwar dare ma ta so ta hana ta barci, bakin ciki ne ya hana ta tashi neman abinci cikin dare. Don haka ta yi farin cikin ganin wadannan galla-gallan warmers.
Kai tsaye Sajida ta haye kan tebur ta kalli kawayenta.
Ta ce, "Mai ci ta zo don ni ci zan yi, wanda ya ga bati ya kyale jahili ne. Wahalallun har sun gama abinci da sassafen nan, sai dai su dafa su ba ni dan ni babu wanda zan dafawa abinci a gidan nan, saboda ajiya aka kawo ni in ci in yi gaba."
Suka taso kowacce ta sami tata kujerar ta zauna.
Zainab ta dubi Sajida ta yi dariya.Ta ce "Sajida ba ki da mutunci."
Tsohuwa ta ce, "Ba zan hau tebur ba kar in fado saboda dadi ku zubo min nawa a kasa zan ci."
Tun kafin su Sajida su kai loma daya bakinsu suka fara santin kyawun cokulan da plates din nan. Ai da suka fara ci, sai suka ji cikin kunnuwansu ya dau kaikayi, saboda dadi. Tunda suke ba su taba cin abinci mai dadin irin wannan abincin ba. Wasu abubuwan cusawa suke ba tare da sun san sunansa ba. Kamar bangaren fruits irin su straw berry, inibi, duk sai dai su ganshi a talabijin ko a hoto ko kuwa su ga fukawar su.
Misalin karfe goma sha daya, Bakura ya farka daga barcin da yake yi, ya yi wanka ya fito a shirye tsaf sanye da wata shadda shudiya (blue), wacce aka yi masa gajeren dinki iya gwiwa, wato (boda), ya dora shudiyar hula. Kamar wadanda suka hada baki Samira ya iske a falo ta ca6a ado da wani shudin leshi, sai walkiya take.
Bayan ta gaishe shi sai ya shiga janta da wasa yana zolayarta, duk da ya san haushi yake bata shi kuwa dadin zolayar yake ji. Suka wuce kan tebur don karya kumallo, domin Samira ba ta iya cin abinci ita kadai, duk dadewar da Bakura zai yi a waje ko yana barci sai ta jira shi ya zo sun ci tare tun sanda suka yi aure.
Sun fara cin abincin kenan, sai Samira ta dube shi ta yi gatsine. Ta ce "Af, ya za a yi ka zo ka zauna kana cusawa cikinka abinci, ba ka damu da amaryarka ba, yaya ta kwana, ko me ta ci, ko me za ta ci?"
Bakura ya yi dariya ya ce,
"Ai bakuwarki ce, na san ba za ki bar ta da yunwa ba."
Takaici gami da daci ne ya dasu a zuciyar Samira. Ta tabe baki ta ce, ai gara aje a kira ta ta zo mu hadu mu karya tare ka ga sai ka fi jin dadin cin abinci kana yi kana kallonta, don na ga alamar har wata nutsuwa ka ke idan a gabanta ka ke."
Bakura ya kwashe da dariya Ya ce, "Kishi, kishi, Samira kishi sunanki daga yau. Yaushe aka kawo Sajidar da har ki ka lura ina

Please Login or Register in order to submit comment