Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga fuskarta, sai tafukan hannayenta. Daga dukkan alamu daga makarantar Islamiyya take, domin ga jakarta a rataye a kafadarta cike da Kur'anai.
Ta juya ta dubi mahaifinta wanda ke kallon gabansa yana tuki da alama ya na cikin matsanancin tunanin da ya saba yi a kwanakin nan. Ta mika hannu ta kunna C.D da ke jikin motar. Kan ka ce kwabo wakar Sani Aliyu Dan Dawo wacce ya yi wa gwamnan Sokoto ta fara tashi, yayin da speakers din da ke kusurwoyin motar suka fara fitar da sautin ganguna.
Bakura ya juya ya dubi Zahra, sai ta yi murmushi. Ya sa hannu ya kashe radiyon ya juya kansa ya ci gaba da kallon gabansa ba tare da ya ce mata komai ba.
Ta yi shiru na wani dan lokaci mai tsawo. Can ta murda makulli ta bude gaban motar inda gaba daya disc din C.D kala-kala a layi ta zabo wani, shi kuma na karatun Kur'ani ne wanda Sudes limamin masallacin Makkah ya yi. Ta cire wancan na ciki ta saka wani. Cikin 'yan sakonni qira'a mai dadi ta fara tashi. Bakura ya juya ya dubi Zahra sai ta yi murmushi a karo na biyu, ya sa hannu ya kashe. Sai mamaki ya rufe Zahra kamar za ta yi magana sai ta fasa don ba ta ga fuskar yin magana ba. Ta sake bude wajen ajiyar za ta dauko wani C.D na-wakar Shata sai Bakura ya ture hannunta gefe ya mayar da wajen ya rufe.
Ya ce, "Wai yaya haka ne Mamana. Kin cika kiriniya kamar wata karamar yarinya, ko ke ce Usman dan auta?"
Ta yi dariya ta gyara zama ta zare farin gilashin da ke fuskarta.
Ta ce "Abba, kwana biyu kamar kana cikin damuwa, Umma ta ce wai ka ga wata mai kama da Zuhuriyya?"
Ya yi shiru yana dubanta yayin da amsa ta qauracewa bakinsa.
Can jimawa Zahra ta sake cewa. "Abba, ni kuwa zan so in ga mai kama da Zuhuriyyarka ko ba komai zan dinga tuna kamanninta a rayuwata."
Wannan karon ma da sauri ya waiwayo ya dube ta ba tare da ya ce mata komai ba, sai ta ga ya juya kan mota sun canza titi sun baude daga hanyar gida su na ta tafiya ba tare da wani daga cikinsu ya sake magana ba.
Zahra ta yi shiru tana tunani a ranta. "Shin me yasa Abba ya juya da kan mota, ina za mu je ne?"
Musamman da ta ga an wuce Lamido Cresent an shiga Badawa Layout. Su ka wuce sai ta ga su na ketawa cikin gidajen gargajiya. Zahra ta gyara zama ta dubi unguwar sosai ta juya ta dubi mahaifinta.
Ta ce "Abba, ya sunan nan unguwar?"
Ya dube ta ya kawar da kai gefe kamar ba zai ba ta amsa ba, dan daga dukkan alamu baya son yin magana. Can ya bude baki da kyar.
Ya ce, "Sunan nan unguwar Kawon Alhaji Sani."
Zahra ta gyada kai sannan ta maimaita sunan unguwar.
Ta ga yana sake danna kan motar cikin lunguna, ga kwata ga gidajen kasa. Sai Zahra ta ji hankalinta ya fara tashi a tunaninta wani kauye ne suka shigo ba cikin Kano ba.Tsoro ya hana ta sake yi masa wata tambayar. Daidai wani kofar gida ta ga ya ja burki ya tsaya. Zahra ta dubi kofar gidan da suka tsaya ta daqa-daqa babu ko fenti ga almajirai nan tsibiri-tsibiri a qofar gidan su na ta karatu.
Ta juya ta dubi mahaifinta cike da mamaki take tambayarsa. "Abba, ina ne nan?"
Ya yi dan murmushi ya ce, "Na kawo ki gidan mai kama da Zuhuriyya. Ba kin ce ki na so ki ganta ba, ko kin fasa mu juya?"
Ta yi dariya ta ce, "A'a mu shiga mu ganta."
Ya yi dariya ya ce, "Ki shiga dai ni ina kofar gida, ya ya zan shiga gidan matan aure? Ki shiga tana ciki Sunanta Sajida."
Zahra ta tambaya, 'Sajida sunanta? What a nice name? I like the name Sajida."
Su ka bude kofar mota suka fito gaba daya. Malam Yakubu cike da mamaki mai hade da farin ciki ya mike ya tari Bakura ya na fadin, "Lale marhaban, yau muna da manyan baki sannunku da zuwa. Kai da 'yar jikar tamu ce?"
Bakura ya duqa ya gaishe da Malam. Nan da nan Zahra ta zube har kasa ta kwashi gaisuwa.
Bakura ya nuna Zahra ya ce, "Malam ga Zahra 'yata ta fari na dauko ta daga Islamiyya na ce bari in biyo da ita ta gaishe ku saboda wata rana, kar a hadu a hanya ba a san juna ba."
Malam Yakubu ya fada cikin jin dadi, "Lallai na ga Zahra ai daga gani babu tambaya naga kamarta da kai sak, Zahra kai ta biyo kama daina wahalar da kanka wajen gabatar da ita duk inda ku ka shiga kallo daya za'asan 'yarka ce,na dade banga irin dan da yayi kama da uba ba haka. kuma ka kyauta daka kawo min Zahra, amma fa na ji dadi. Allah ya yi muku albarka, Allah ya qara zumunci. Zahra shiga cikin gida gani nan zan shigowa zan yi musu bayani. Alh. Bakura bari in dauko maka tabarma in shimfida maka a kofar gidan makwabtanmu saboda kofar gidan namu yau a cike yake da yan makaranta."
Bakura ya yi dariya ya ce, "A'a babu komai Malam, zan koma cikin mota in jira har ta fito saboda ba dadewa za ta yi ba, za mu wuce Magriba ta kusa."
Malam Yakubu ya ce, "To bari in shiga cikin gidan in gabatar da ita a wajen Sajida da mahaifiyarta, don ba su sanku ba, ita ba ta san su ba."
Bakura ya ce, "Haka ne, lallai ba ta san yadda za ta gabatar da kanta ba, don nima ban yi mata bayani ba."
Malam na shiga cikin gidansa ya iske Zahra a Zaune kan tabarma, mahaifiyar Sajida kuwa Furera na Zaune akan kujera a gaban murhu tana hidimar siyar da kunun kanwarta da dan wake.
Yahuza kuwa ya zo ya saka Zahra a gaba a jima ya faki idonsu ya ce mata. "Bakuwa za ki ba ni naira hamsin idan za ki tafi?"
Sajida kuwa ta dauko turmi ta hau tana hira da makwabta. Wayar da aka hana ta yi shi ne take lekawa makwabta ta katanga kawarta Hajiyayye tana ba ta aron waya tana kiran Abdulmajid. Don haka tana jin muryar mahaifinta ta yi sauri ta wurga musu wayarsu ta daka tsalle ta diro.
Malam ya daka mata tsawa ya ce, "Sajida ban hana ki hirar nan da kawayenki ta katanga ba? Idan hirar suke so da ke su zagayo mana dan dai ke ba zan bari ki leka kofar gida ba, balle ki shiga makwabta mutaniyar banza. Ga bakuwa nan kin yi ko kula ta ba ki yi ba, baki iya sannu da zuwa ba, balle ga ruwa. Kun qi shimfida mata tabarma kowa ya juya yana harkokinsa, ko ruwa ba ku iya kawowa bakuwa ba. Yanzu Furera da girmanki a matsayinki na uwa sai an fada miki, sannan za ki kula bakuwa dan baki san ta ba."
Furera ta zabura ta ce, "Wallahi ni na dauka bakuwar Sajida ce ko 'yar makarantarsu ce ta ga kwana biyu ba ta zuwa ta zo ta gani ko lafiya. Ta shigo ta yi sallama na ba ta tabarma ta zauna muka gaisa, ai ban san daga kofar gida ka ce ta shigo ba."
Malam ya fusata ya daka tsawa, "rufe min baki, bakya kula ni, ni kaina idan kina gaban kunun nan baki da lokacin kowa ta sayar da kununki kike yi kawai. To wallahi ząn hana sana'ar nan."
Ya juya ya dubi Yahuza ya yi masa tsawa ya ce, "Me ye kai kuma ka zo ka saka ta a gaba? Tashi ka dauko mata ruwa ta sha."
BFurera ta tambaya,
"Malam yar gidan waye wannan din."
Malam ya ce, "Tsagwaron zumunci da girmamawa ce tsakanina da mahaifinta, shi ne mai zuwa daukar karatun nan wanda nake cewa a dinga zubo min abicin mutane biyu ni da shi. To 'yarsa ce ya kawo ta ta gaishe mu."
Furera na budar baki sai ta ce, "Wai wa yaga dorin dosano 'yar gidan mai daukar karatu a kofar gida. To mu da ba kofar gida muke lekawa ba yaya za a yi mu sa mahaifinta, balle mu san 'yarsa? ka ga dole sai ka shigo ka yi mana bayani."
Zahra ta dago da sauri ta dubi Furera da alama kalaman Furera bai yi mata dadi ba. Malam ma bai ji dadin maganar ba, sai ya ji kunya ta lullube shi. Yahuza ya kawo wani dakalallen ruwa a cikin wani ragargajejjen kwano mai lamba da tsatsa. Sajida na tsaye ta na kallon Zahra kasa-kasa, Allah-Allah take Malam ya fita ta kara hawa turmi ta leka katanga kawarta ta miko mata aron waya ta kira rabin ranta Abdulmajid.
Malam ya harari Sajida ya ce, "Ki dauki ruwan ki ja ta dakinki ku gaisa mana ki dawo ki zuba mata kunu."
Furera ta zabura ta dube shi ta ce, "Kunun nawa zan zuba?Ai ka san na siyarwa ne."
Zahra ta yi saurí ta ce, "Ah! Alhamdulillah, a bar shi na koshi."
Malam ya ji wani mummunan bacin rai, ya kudira a ransa idan Zahra ta tafi sai ya tozarta su kamar yadda su ka tozarta shi a gaban baquwarsa. Bai ce komai ba sai ya kada kai ya fice.
Ya na fita Sajida ta dubi Zahra ta ce, "Ke dan Allah ki na da waya?"
Zahra ta tambaya "Wacce irin waya?"
Sajida ta ce, "Ashe fa 'yar gayu ce ba ki san waya ba, ina nufin hanset."
Zahra ta ce, "Yes, ina da hand set."
Sajida ta yi fari da ido ta ce, "Akwai kudi kuwa a wayar? "
Zahra ta ce, "Akwai dubu shida a ciki."
Sajida ta yi ihu ta fada cike da mamaki mai yawa ta ce, "Dubu shida? Lallai wannan 'yar gidan masu maiko ce. Saurayinki ne ya hada miki wayar ya ke sako miki kati haka da yawa?"
Zahra ta bude baki tana kallon Sajida cike da mamaki, yayin da kalmar saurayi take yi mata reto a kwakwalwa.
Furera ta tsaya tsai daga zuba kunun da take yi. Ta ce "Wayar ce dubu shida ko kudin cikin wayar?
Sajida ta ce, "Umma! kudin cikin wayar ne dubu shida, wayar kuma ai sai dubu hamsin."
Furcra ta gyada kai ta fada a hankali, "Cafdijam dan qarawa mai karfi-karfi za a ce in zuba ma ta kunu kyauta."
Sajida ta ce "To kawata dan ba ni áron wayar ta ki in ci ko dubu daya ne."
Zahra ta bude jaka ta dauko wayarta tsaleliya kirar N85 ta miqa mata. Sajida ta latsa wasu lambobi kan a jima network ya hada ta da abin kaunarta Abdulmajid.
Ta fada cikin lallausar murya. "Hello darling Abdulmajid, Sajimajid ce, kar ka damu ba flashing nake ba wallahi wayar wata girl ce 'yar gidan masu naira. Ka san nawa ne a cikin wayar?
Naira dubu shida, ka ga za mu iya kaiwa tsakar dare muna magana."
Furera ta dubi Sajida ta ce, "Shegiyar yarinya. marar jin magana, ai sai ki shiga daki ki yi wayar kafin Malam ya shigo ya hada mu dukka ya zage."
Sajida ta ce, "Umma ba abin da nake fada muku kenan ba, ga Zahra nan ita iyayenta sun yarda ta kula samari, na tabbata saurayinta ne ya hada mata wayar nan, yake zuba mata kudi."
Furera ta ce, "A to 'ya'yan masu hali ma kenan balle mu 'yan Allah Ya baku ku ba mu. Laifin mahaifinki ne da ya hana."
Abdulmajid da yake kan layi har yanzu yana jin abin da Sajida da mahaifiyarta su ke fada.
Ya yi murmushi ya ce, "Ki ce kina magana a wayar big girl, wanne irin model ce." Sajid ta ce, "N85 ce."
Ya ce, "Lallai babbar harka take yi. Ya ya sunanta ko Allah zai sa wani lokaci in kira layin kuna tare ta ba ni ke mu yi magana?"
Sajida ta ce, "Ina jin Zahra sunanta, but l'am not Sure, kar ka damu ta zo ne za ta tafi ba lallai ne mu sake haduwa ba, mu yi maganarmu kawai."
Sajida ta dubi Zahra, ta juya ta dubi mahaifiyarta sai ta ga gaba daya sun zura mata ido su na kallonta su na sauraronta. Sai ta ji kunya ta tashi ta shiga daki ta cigaba da yaryada masa zakakan kalamai na so da Kauna.
Malam ya turo Yahuza fiye da sau biyar kiran Zahra ta fito za su tafi, babanta ya gaji da jira. Ba Zahra, ba dalilinta, domin har yanzu Sajida ba ta gama da wayar ba. Ita kuma nauyi da kunya ya hana ta je cikin daki ta sami Sajida ta karbi wayarta. Sai da Malam ya shigo da kansa ya sami Zahra a zaune a inda ya barta ya dube ya yi dariya.
Ya ce, "Zahra hira ta yi dadi ko? Abbanki ya ce ki zo ku tafi, nayi-nayi ma ya barki ki kwana ya ce gobe da safe akwai makarantar boko:"
Zahra ta sunkuyar da kai kasa ta ce, "Baba yanzu zan fito Sajida nake jira tana daki tana..."
Furera ta katse ta ta yi sauri ta mike tsaye ta ga asiri zai tonu. Ta ce "Sajida take jira ta fito ta raka ta, ka san har sun zama kawaye, wato dai yau rakiyar kura za a yi idan ta raka ta ita ma sai kaga ta rako ta. Bari in kira Sajidar a daki ina ga kuka ma take yi na rabuwa da zahra in ce ta zo ta rakata."
Malam ya ce, "Kai rakiyar meye za a yi ta yi mu tafi kawai."
Zahra ta mike ta bi Malam a baya suka nufi qofar waje. Har sun kai zaure sai ta ji Umma Furera ta jawo hannunta ta cikin hijabi ta sunna mata wayar a hannunta, gami da yi mata rada a kunne. Ta ce, "Yarinya kar ki fadawa Malam ko mahaifinki sai ya yi fada."
Zahra ta gyada kai ta duqa ta ce, "Na gode."
Malam ya waiwayo a fusace ya ce da Furera. "Me ye kuma kike yi ma ta rada?"
Umma Furcra ta yi sauri ta ce, "Lah! Ba komai kudin mota na ba ta." Sai ta tuna da mota suka zo sai ta ce, "Au! Kudin da za ta sayi 'yar alewa ta kaiwa Kannenta."
Malam ya yi murmushin jin dadī ya ce, "Madalla Allah ya saka da alkhairi, to ki koma ciki rakiyarta isa."
Mamaki marar musaltuwa ya rufe zuciyar Zahra da ta ga babba tana karya. Furera ta dade a zaure tana leken Zahra da mahaifinta har suka shiga mota suka tafi.
Zahra ta na zama a cikin mota ta dubi mahaifinta.
Ta ce "Abba ka yi hakuri na dade."
Ya girgiza kai ya ci gaba da tuki. Ya ce, "Ba damuwa. Ina fatan kin ji dadin ziyarar da kika kai?"
Ta ce "Eh, to gani nan dai, na yi farin ciki ban yi farin ciki ba."
Bakura ya waigo da sauri ya dubi Zahra yayin da ya ji zuciyarsa na bugawa, don fargaba.
Ya tambaya ya ce, "Me yasa kika fadi haka MamaKai ka fi cancanta

Na

👇🏻👇🏻👇🏻



Ta yi dan murmushi ta ce "Abba Sajida da Umma Zuhuriyya ta yi kama ko Mamarta Furera?"
Bakura ya yi shiru na dan wani lokaci sannab ya ce "Sajida da mahaifiyarta Furera su na kama ne?"
Zahra ta girgiza kai
Ta ce "Ba sa kama kwata-kwata. Mamar Sajida fara ce sol, amma duk fuskartka tsage-tsage irin na Fulani kuma ita mai qiba ce sosai. Hancinsu ba iri daya ba, bakinsu, idonsu, kafarsu, qirar jikinsu, duk daban-daban ko kadan ba su yi kama ba. Sajida tana da kyau sosai ta fi mahaifanta da wannan qanin nata Yahuza kyau."
Bakura ya yi shiru yayin da tsananin rudanin da yake ciki ya sake linkuwa a zuciyarsa. Ya dade ya na tunani a ransa. Ya na kuma tambayar kansa da kansa, "Shin ya ya aka yi haka? Ta ina Sajida ta samo kamanninta, tunda ba ta yi kama da mahaifinta ko mahaifiyarta ko qanninta Yahuza ba? Ita kadai kamarta daban, kuma sak kamar Zuhuriyata. Qalu innalillahi wa'inna ilaihir raju'un."
Kamar daga sama ya ji Zahra ta ba shi amsar duk wadannan tambayoyin da ya jero a cikin zuciyarsa.
Ta ce "Abba, ikon Allah ya wuce haka. Allah Ya na tsara halittarsa yadda ya nufa. Zai iya halittar d'a bai yi kama da uwa ko uba ba, a can cikin dangi sai ya yi kama da wani d'orin d'osano. Ko kuma ma sai su yi kama babu danganta ko daya."
Ya gyada kai ya ce " zai iya faruwa kadan daga cikin ikon Allah."
Zahra ta gyara zama ta ce " bana son Sajidar nan don bata da tarbiyya bata jin maganar iyayenta kuma mamarta ke taya ta."
Wannan karon kallonta ya yi da sauri cike da mamaki har da bude baki.
Cikin rawar murya ya tambaya " me ta yi ?"
Zahra ta tabe baki ta ce " da alama Babanta ya hana yin waya da samari sai ta taka turmi ta leqe maqwabta ta ari waya ta yi masa."
A tsakiyar titi ya taka burki ya tsaya Allah Ya sa babu mota a daf da shi da an buga masa. Zahra ta firgita matuqa ganin yadda ya razana abin har ya bata tsoro.
Da kyar ya dawo hayyacinsa sannan ya gangara gefen hanya ya tsaya. Zahra tana jero masa tambayoyin da ya gagara bata amsa mata. " Abba me ya faru? Me ya as ka taka burki? Me ya as muka tsaya?"
Ya dade a kishingide a jikin kujera ya rufe ido ya dago ya gyara zama muryarsa na rawa ya ce " bank labarin abinda ya faru dalla dalla."
Zahra ta bashi labarin komai amma bata ce an karbi aron wayarta ba, dan kada ya huce akanta yadda ta ga ya hasala yana cije baki.
Ya daki sitiyarin motar da qarfi ya na magana cikin jin kakkausar murya da fusata.
" daga yau babu ke babu Sajida, kada ki sake cewa in kai ki ki ga me kama da Zuhuriyya. Na yi kuskure, na yi nadama, daman ban kawo ki ba."
Haka yake fada yana nanatawa kamar karatu. Ya tashi mota ya fisga kamar zasu tashi sama.
Zahra ma ta yi nadamar zuwanta gidan su Sajida da kuma bawa mahaifinta labarin abinda ya faru. A lokacin fadan yin samari a boye ya taso har suka isa gida gargadi ya ke yi mata akan kada ta biyewa qawaye masu yin samari kada itama ta ce za ta yi saurayi ko a makaranta kada ya ji ko ya gani. Duk ranar da ya kamata da maganar saurayi sai na lahira ya fi ta jin dadi.
Da alama Bakura ya kwana bai yi baccin kirki ba, walwalarsa ta ragu kowa ya kasa gane kansa. Zahra ce kadai ta sani ita kuwa ba zaa ji mutuwar sarki a bakinta ba.
Aiki ya shawa Bakura kai bai samu ya je wajen Malam Yakubu daukar karatu ba sai bayan kwanaki hudu. Ranar da ya

Please Login or Register in order to submit comment