Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

huci, wanda ya fitar da iska mai zafi ya ce, "Sajida zan aura."
Zahra da ke durkushe sai ta fadi zaune tubus. Can ta fara jan jiki kamar yaron da yake koyar rarrafe. Kafin mahaifinta ya ce wani abu Zahra ta fashe da kuka, ta miqe ta runtuma cikin gida da gudu. Ba ta tsaya a ko ina ba sai cikin đakinta, ta rufe kanta don takaici. Fiye da minti talatin Bakura na zaune a cikin mota ya kasa kunna motar ya tafi, saboda damuwa. Ya rasa madafa, ya rasa yadda zai yi da rayuwarsa. Hakika Bakura ya shiga tsaka-mai-wuya.
Namijin duniya da ya fita daga gidansa gidan su Sajida ya nufu, ita kuma ya je ya ga wanne gumurzun za a yi. Faduwar gaba asarar namiji, amma ya san za a yi gagarumar rigima da fetsararriyar yarinyar nan musamman idan suka hadu ta ganshi, mutumin da ya raba ta da rabin ranta Abdul majid kuma yanzu ya zo ya ce zai aure ta.
A kofar gida ya iske Malam, bayan sun gaisa, sun taba 'yar hira.
Malam ya dubi Bakura ya yi murmushi, ya ce, "Ka bar mu da rigima, Sajida tana da taurin kai, har yau ba ta haqura da yaron nan ba. Inda muka sami sauqin abun da muka ce mata kai dan
sanda ne, tuni kasa an kama Abdul majid an daure shi har sai ta daina tunanin guduwa wajensa sannan za' a sako shi. Ka san yaran yanzu marassa kunya, kullum roqar uwar take wai a ba ka hakuri ka sake shi ba za ta gudu ba."
Bakura ya yi dariya ya ce, "Allah Ya kyauta, ai mata kwakwalwarsu qarama ce, tunaninsu gajere ne. Nima kwanaki ukun nan ina gida muna gumurzu da uwargidana na sanar mata zan yi aure. Amma yanzu Alhamdulillahi rigimar ta lafa, shi yasa ma na samu na fito. Ai mata ba sa son kishiya."
Dadi ya rufe Malam ya ce, "Ikon Allah, har ka sanarwa uwargida, amma wannan abu ya yi min dadi. Nima a nan ni da almajiraina kullum sai mun yi saukar Kur'ani daya, an yi sadaka akan Allah Ya tabbatar da wannan abu, ya kawar da duk wasu fitintinu."
Bakura ya ce, "Amin Malam, ai kamata ya yi a dinga yin saukar nan sau uku a rana daya, zan dinga biyan masu karatun a qaro Malamai, domin abubuwan da yawa. Ka ga har yanzu Sajida ba ta san ko ni wanene ba, don ba ta daga ido ta ganni ba."
Malam ya ce, "Kar ka damu ta fara laushi, jikinta ya yi sanyi kamar ta saduda, saboda Furera tana ba ta baki kullum ba dare ba rana. Sama'ila ma na kira shi na ba shi haklquri, na nuna masa illar da na hango masa idan aka yi wa Sajida tilas ta aure shi. Yaron mai hankali ne bai damu ba, kuma ya fahimce ni. Mu shiga ciki ku gaisa da Sajidar mana."
Bakura ya zabura ya ce,
"Ah! Haba ai ba komai ba sai mun gaisa ba, idan aka yi auren ta ganni."
Malam ya yi dariya ya ce, "Haba, haba kamar a mutanen da, ai gara ku dinga gaisawa, ku san juna kafin lokacin, bari in turo ta ko a zaure ne ku tsaya ku gaisa."
Malam ya shiga cikin gida da sauri, yayin da Bakura ya je zaure ya tsaya, sai kai kawo yake daga wannan bango zuwa wancan, zuciyarsa cike da zullumi da fargabar abinda zai je ya zo. Kamar an wurgo ta haka ya ganta 'dif a gabansa sanye da wani zunbulelen hijabi ruwan toka. Ya ji gabansa ya yanke ya fadi, domin ganinta ya sake tono masa zafin rabuwa da mai kama da ita wato Zuhuriyyarsa. Kallon-kallo ake tsakanin Bakura da Sajida. Kallo irin na qeqe-da- qeqe, ido cikin ido ba tare da daya ya rusuna idonsa ba. Kowannensu ya na nasa tunanin a ransa. Shi al'ajabi yake yadda kamannin Sajida da Zuhuriyya suka zama daya. Ita kuwa kallo daya da ta yi masa ta tuno inda ta taba sanin fuskarsa. Tabbas wannan shi ne mutumin da ya taba musgunawa rayuwarta. Wannan shi ne mutumin da ta ji ta tsana a cikin qanqanin lokaci a ranar da ta fara ganinsa a rayuwarta. Nan da nan kwakwalwarta ta tuno mata da kamannin Zahra, ta hada fuskokinsu ta tabbatar kamanninsu daya. Ta sake tuno kalmar da ya fada mata cewar yana da 'yarsa sa'arta Zahra, wacce yake kwatanta ta da ita ce kwaryarsa ta gari da ya saqale ta a ragaya. Lallai akwai wani tuggu da mutumin nan ya hado mata na ya raba ta da abun qaunarta don shi ya aure ta.
Sajida ta fada a ranta, "Sai dai a kai gawata ta zauna da wannan amma ba ni ba."
Bakura ne ya katse tunaninta ya ce, "Assalamu alaikum warahamatul lahi ta'ala wa barakatuh. Sajida mun hadu a kashi na biyu, sai dai wannan haduwar tamu ta sha bamban da ta farko. Sajida, da kin san irin girma da darajar wacce kike yi min kama da ita da baki shiga damuwa ba. Ba zan iya wulakanta ki ba, ba zan iya cutar da ke ba.."
Bai rufe bakinsa ba ta daka masa wata tsawa mai tsoratarwa, ta ce, "dakata Malam, rufe min baki, yi min shiru."
Dariya ce ta subuce masa, domin ya tuna
wasansu da Zuhuriyya, tabbas muryarsu da yanayin maganar Sajida da Zuhuriyya iri daya ce. Haka sak wannan kalmar Zuhuriyya take furtawa.
Dariyarsa ta sake hargitsawa Sajida fushinta, ta dada 6ata rai ta ce,
"Ka yi dariya mana tunda ka hada min tuggu, Zahra 'yarka ce ashe ka kawo ta ta shigo gidanmu ta ga abinda nake, don ku raba ni da Abdul dina, kai ka aure ni, to bari ka ji in fada maka da in aure ka gara in halaka kaina, kamar yadda Abdul majid ya rasa ni, kai ma ba za ka same ni ba Kada ka manta tun ranar da na fara haduwa da kai na ji na tsane ka, yanzu na qara tsanarka, kuma na tsani 'yar ka Zahra."
Kallonta kawai ya tsaya yana yi, tsiwa take yi tana murguda baki, ta gama cashe masa ta Juya ta shiga gida. Ya bi ta da kallo har da leqe. Ya fito jikin motarsa ya tsaya ya yi shiru, tamkar gunki. Ba baqaqen maganganun da ta fada masa ba ne suke yi masa reto a zuciya ba, a'a tsantsar kamar ta da Zuhuriyyarsa ce mamaki ya sake damqarsa.
Sajida na shiga tsakar gidansu ta yaye hijabi ta yi zaman 'yan bori 'dabas' ta rafsa wani uban ihu kamar wacce ake cirewa rai.
Ta ce, "Wallahi ba zan auri wannan mutumin ba gara in auri kuturu ko makahon da yake bara a titi."
Malam ya fito daga bandaki ya dire buta da sauri, yayin da matarsa ta fito daga daki a guje suka rintimo wajen Sajida suna tambayarta. "Lafiya? Me ya yi miki mutumin? Daman kin san shi?"
Cikin kuka ta ce,
"Shi ne Baban Zahrar nan da take hada min gulma. Ashe shi ne ya aiko ta, don a raba ni da Abdulmajid. To gara in auri kowa da in aure shi."
Umma Furera ta ce, "Ya aka yi ki ka san shi ne, wannan waçce irin magana ki ke yi?"
Malam ya ja dogon tsaki ya ce, "Ai kin aure shi kin gama da izinin Ubangiji, zancen banza. Har kin isa ma ki zabi abinda kike so? Ai mutunci da lallashi a tsakanina da ke ya wuce."
Ya fice ya bar Umma Furera riqe da Sajida. Da alama
Umma Furera ta shiga tabarbarewar tunani ta rasa kan zancen. Tana zanowa kanta tambayoyi. "A ina Sajida ta san wannan mutumin? Ya aka yi ta san mahaifin Zahra ne?"
Malam ya qaraso wajen motar Bakura, Bakura ya yi sauri ya saki ransa ya hau murmushin qarfin hali.
Ya ce da Malam, "Zan koma gida sai gobe idan Allah Ya kai mu."
Malam ya ce "Kun gaisa da Sajida ko? Bakura sai haquri fa, ka qara hakuri da Sajida."
Bakura ya katse Malam da cewa, "Kai haba, ai ba komai yarinta ke damun Sajida."
Malam ya ce, "Har ina tunanin in ce maka kar ka dauki fasagurbin kwai ka hada shi da kwayayenka masu kyau. Ma'ana kada ka dauki Sajida ka kai gidanka ta 6ata maka tsarin gida. Ni da Allah Ya bawa in ci gaba da hakurin zama da ita."
Bakura ya yi sauri ya ce da Malam "Ka daina fadar haka, haba Malam wadannan kalamai su daina fitowa daga bakinka a kan Sajida saboda karfin bakin iyaye a kan 'ya'yansu agar ka dinga furta alkhairi. Halin da Sajida ke ciki ba wani abu ba ne na daban, a kowanne gida yana faruwa. Bai kamata ka dauki Sajida kangararriya, ta gagari jama'a ba, har ana daure ta a sarka. Ka ci gaba da ba ta baki ku lallashe ta,a qarshe ku yi tayi mata addu'a."
A haka dai suka rabu da Malam, Bakura ya nufi gida. Gidan Bakura tamkar ana zaman makoki. Samira da 'ya'yan jugum-jugum, haka Bakura ya samu waje ya zauna ya yi jugum. Duk da ya na daurewa yana jan su da hira, amma shi ma hirar bata kai har zuciya ba, saboda tashin hankalin da yake ciki ta bangarori guda biyu, ko ina ba dadi. Sai ya ji a zuciyarsa kamar ya fasa auren kasancewar damuwar da iyalansa suke ciki, sai ya tuno kamannin Sajida da Zuhuriyya, sai ya ji ba zai iya fasa aurenta ba, komai runtsi.


*** *** ***
A cikin satin Bakura ya je gidan Hajjiya Farida ta dauko masa dogon list din abubuwan da ya kamata ya zuba a lefen amarya da uwargida iri daya, kamar
yadda Bakura ya umarce ta da ta yi komai iri daya kada ta bambanta. Hakika kayan suna da yawa, kuma tsadaddu ne, don haka miliyoyi za su sha kashi, akwatuna shida-shida har da kite din gwalagwalai. Ya ce ta lissafa akwatunan bibbiyu na Mahaifin samira da mahaifiyar Samira sannan Akwatuna bibbiyu na Mahaifin Sajida, biyu na Mahaifiyarta. Sai akwati guda ta Zahra, Akwati guda-guda ta Abubakar, Umar da na Usman. Cas ya caske mata kudin ya miqa mata cek, don haka a satin ta shigar da visa tafiya qasashe biyu don hado lefen, wato London da Dubai. Ta ba shi tabbacin a cikin sati biyu komai zai kammala.
A cikin satin Bakura ya yi wa kamfanin da suke yi masa gyaran gida da kawatawa waya ya ce su zo ga aiki, turawa ne, ofishinsu ya na Abuja. Ya sanar musu yana so su zo su sake masa fenti, labulaye da gaba daya furniture gidan, na zamani, sabon yayi. Sun san Bakura, sun san halinsa akwai naira, kuma baya tsoron kashewa. Abun ka da Nasara a sarar duniya a ranar suka hawo jirgin yamma daga Abuja zuwa Kano, su uku ne mace daya, maza biyu suka fara aune-aune, gwaje-gwaje, rubuce-rubuce da lissafe-lissafe. Babu irin lallashin da magiyar da Bakura bai yiwa Samira ba a kan ta zo su zauna da ma'aikatan nan ta fada musu yadda take son a tsara gidanta, ta qi fitowa. Ta ce duk yadda yake so ya je ya yi shi da amaryarsa Sajida.
Duk da aikinsu ne, amma hankalin Bakura bai kwanta ba sai da ya yi kiran Zahra ta zo ta zauna da su ta fada musu kaloli da irin yadda take ganin zai yi kyau.
Bakura ya yi ajiyar zuciya ya dubi Zahra ya ce,
"Wancan dakin da ku ke kira dakin baqi shi ne zai zama dakin Sajida, za a zuba mata kaya iri daya dana Mamarki, sai dai kalar ta bambanta. Haka bandakunan ma duk a ciccire tiles da kayan ciki a zuba masu tsada."
Zahra ta yi 'dumm' yayin da shi ma Bakura ya kula da hakan. Da alama ba ta ji dadin batunsa ba. Babu yadda ta iya haka ta kaikace ta zabarwa Sajida kalar fenti, labule, kujeru, gadaje, talibijin, C.D, hometharter, kayan toilet da dai sauransu, wadanda darajarsu daya da na Mamarta. Haka ta tsara dakin Bakura, haka na ta da na qannenta da kicin. Kacokan farfajiyar gidan aka canja yanayinta. Duk wannan abinda ake Samira ko uffan ba ta cewa, daki ta shige ta yi kwanciyarta.

*** *** ***
A cikin satin aka duqufa aka fara gyara, aka fitar da tsofaffin kayan gidan aka rabarwa 'yan uwa da abokan arziki, masu aiki ma suka kwashi rabonsu. Aka fente gida aka zuba komai sabo daga cikinnkwalayensu. Duk da ma'aikatan su na da kayan aiki na zamani sai da gyare-gyaren ya dauke su tsawon sati biyu, amma fa gida ya tsaru. Idan wanda bai sani ba ya shigo gidan sai ya rantse da Allah batan kai ya yi ba gidan ba ne qasar waje ne. Daidai sanda aka gama gyaran gidan daidai lokacin da Hajiya Farida ta gama hado lefe. Me ya yi saura?
Hajiya Farida da kawayenta guda biyu, sai matan abokansa uku da kannensa biyu daga Maiduguri ne suka hadu suka kai lefen Sajida. Umma Furera da 'yan uwanta da maqwabta sai suka bude baki kawai su na kallon wannan abin al'ajabi, sun ga lefen da duk tsurkukin unguwarsu ba a taba kawo irinsa ba. Naira ta yi kuka, lallai ko ba a fada ba kowa ya san Sajida ta yi tuntube da kasaitaccen miji mai arziki. Sal dai Hajiya Farida da tawagarta sun shiga wani hali na mamaki da ta yadda aka yi Bakura ya fada hannun wadannan talakawa liqis, sun yi bazata ba su dauka irin wannan gida da irin wadannan mutane za su kawowa wannan uwar dukiya ba. Bayan lefen har da damin kudin dinki da buhunhunan abinci. Kai hatta nama da juices da za a sha a ci ya aiko da su, domin dirkeken SA' aka turkewa Malam a qofar gida. Allah sarki yaku-bayi, zobo, kunun aya da lemon kwalba guda goma su Umma Furera suka tanadarwa baqi, sai dan cincin.
Hajja Farida suka shigowa Samira da albishirin cewar ta kwantar da hankalinta tamkar tsumma a randa. Yarinya dai ba kishiyarta ba ce mai aikinta ce, domin babu wayewa a tare da ita. Su ka yi wa Samira hudubar ta saki ranta ta dinka lefenta ta dinga caba ado, yadda ita kanta yarinyar da 'yan uwanta masu kawo amarya za su kidime. Haka shi ma mijin zai san ya yi kuskure wajen jajabo bakauyiya, 'yar talakawa likis.
Hakika Samira ta dauki shawararsu ta dan saki ranta, don haka ta shiga gyaran jiki ciki da waje.
Abu kamar wasa qaramar magana ta zama babba,in ji wani mawaqi. Auren Bakura da Sajida ya tabbata. Sai dai tun ranar da Bakura da Sajida suka hadu a zaure ba su sake ganin juna ba. Haka daidai da sakon daya Sajida ba ta ta6a saduda ta furta da bakinta ta ce yarda za ta auri Bakura ba. Ko da yaushe zillo take ana riqo ta kamar wata kifi. Duk da dinbin dukiyar da ta ga an kawo an jibge a gidansu kace-kace, bai sa Sajida ta ji digon son auren nan ba. Ta rame, ta Jejjeme, saboda tsananin kiyayyar auren. Sai kuka, sai tabara da tsiwar da take tafka musu a cikin gidan.
Dole ce tasa Umma Furera ta shiga cikin qawayen Sajida suka yi ta fita tare don aiwatar da abubuwan biki, kamar su kai dinkunan da amarya za ta saka ranar biki, da buga katin gayyatar biki. Haka Malam da almajiransa suma suka bazama suka shiga kasuwa don siyo fenti, tabarmin da zaa shimfidawa baqi su zauna 'yan daurin aure da katin gayyata. Domin daga dukkan alamu manyan baqi, jiga-jigan masu kudi, masu sarauta, 'yan kasuwa, da 'yan siyasa ne za zu halicci daurin auren nan. hakuri yake bayarwa baya gajiyawa. ta qona gidan, Allah ya kiyaye."

RANAR DAURIN AURE
Allah mai yadda Ya so, duk abinda ka ga ya faru da bawa to bawan ya kudira a ransa rubutacce ne daga Rabbul samawati. Babu wanda ya isa ya tsallake kaddarar da Allah ya rubuto masa. Matar wani ba ta auren mijin wata, haka Baban wani baya haifar dan wani.
Ranar Asabar da misalin qarfe goma na safe ne, daurin auren Alh. Bakura da Haj. Sajida. Haka kuwa aka yi, kafin goma ta cika kofar gidan Malam Yakubu ya cika maqil da bil-adama. Dangin Sajida na wajen uwa da uba sun hallara, yaransu da manyansu . Haka dangin Bakura daga Maiduguri na wajen uwa da na uba suma sun hallara kacokan dinsu. Ga uwa-uba abokan Bakura, abokan kasuwancinsa daga garuruwa daban-daban. Tsofaffin abokanansa tun na sakandire suma ba a bar su a baya ba. Don a cikinsu har da masu girma gwamnoni da mataimakansu na jihohi uku, Kano, Maiduguri, dana Yobe. Haka kusan gaba daya dangin Samira sun zo kama daga mahaifinta, yayansa, surukansa da 'yan uwansa suma ba a bar su a baya ba. Saboda su na son Bakura, suna ganin mutuncinsa, saboda ya san mutuncin kowa. Gashi su na jin dadin yadda ya riqe musu 'yarsu hannu bibiyu ita da 'ya'yanta asirinsu a rufe. Don haka da Bakura ya je ya sanarwa mahaifin Samira zai qara aure bai damu ba, sai ya yi masa addu'a gami da yi masa nasihu masu ratsa jiki.
Ya nunawa Bakura hatsarin rashin nuna adalci ga namijin da ya hada mata biyu. Daga karshe ya sa aka turo masa 'yarsa Samira ya yi mata fada sosai, ya ja mata kunne akan kada ta tayar da hankalinta, kuma ta bi mijinta sau da qafa, ta zauna da kishiryarta lafiya.
Ba gidan Malam Yakubu kadai ba, gaba daya layin ya cika. Kowacce kofar gida cunkoson jama'a ce makil. Babu abun da ka fi hangowa sai galla-gallan shaddoji a jikin jama'a dinkin Tazarce da manyan riguna malum-malum. Ga kamshin turararruka yana tashi. Maroka kuwa ba a iya kirga su, masu busa kuwa Suma yi suke saboda masu sarautar da suke wajen. Dakyar ake hango ango, saboda taron jama'ar da yake bi yana ta gaggaisawa da su. Hakika daga ka ga ango za ka gasgata shi ne ango ko ba ka taba ganinsa ba.Saboda ya fi kewa caba ado ya zankada kyau da wani tsadadden yadi fari tas, wanda ya sha surfani a rigar ciki da babbar rigar. Ya dora baqar hula da baqin takalmi tsadaddu.
Masu daukar hoto da bidiyo suka hau aikinsu, duk inda Bakura yasa kafarsa su na biye da shi. Saboda hayaniya da kyar suka tsagaita, misalin karfe goma sha daya da rabi aka daura auren. Waliyan ango suka miqawa waliyan amarya sadaki naira dubu hamsin lakadan. Aka yi sallati ga Shugabanmu Manzon Allah (S.A.W.) aka shafa, sannan kowa ya kama gabansa. Kowa ya shaida Sajida ta zama matar Alh. Bakura, kowa na yi musu fatan alhairi Allah Ya bada zaman lafiya.
Mata ma ba a barsu a baya ba wajen nado 'yan daurin kayansu su ka dungumo gidan biki. Don haka gidansu Sajida da makwabtansu a cike yake da 'yan yinin biki. Sai dahuwar abinci ake kace-kace komai a wadace. Uwar biki Umma Furera kuwa, sai shiga leshina da shaddoji take, kai ka ce ita ce amaryar. Danginta na kauye sai bin ta da kallo suke zuciyarsu cike da sha'awa, dama su ne suka sami irin wannan. Duk wadannan hidindimu da ake yi ina amarya?
Amarya na daka, a dakin ma a bayan qofa, ba wanka balle a cancada ado, duk da tulin leshina, atamfofi super, shaddoji masu tsada kala-kala, materials na zamani bayan gwala-gwalai 'yan kunnaye, sarkoki, zubbuna, da awarwaraye. Amma Sajida ta yi qiirmisisi ta toshe kunnuwanta ta qi sauraron kowa.Juyin duniyar nan da lallashi babu wanda Ummarta da danginta ba su yi mata ba, amma Sajimajid ta kekashe kasa ta ce sai dai a kashe ta, amma ba za ta yi wanka ba. Kawayenta ma ba su ji dadin wannan al'amari ba, sun so Sajida ta ware su karbi kudi a wajen ango su hada hadadden party a cashe, amma Sajida ta ki daukar shawararsu. Haka aka dinga kai kawo ana cashewa, amma biki ba amarya, har da masu kidan kwarya a tsakar gida mata suna ta shan rawa, amma Sajida ko tsakar gida ta qi leqowa. Tana bayan qofa a takure zuciyarta cike da tsantsar takaici, idanuwanta sun jejjeme. Duk ciye-ciyen nan da ake yi tun safe ko kwayar shinkafa Sajida ba ta jefa a bakinta ba, duk da tulin abincin da aka jere mata a gabanta.
La'asar sakaliya Sajida ta yi niyya da kanta ta fito tsakar gida, sanye da wata kodaddiyar doguwar rigarta ja da zurmikeken hijabinta ruwan toka. Fitowar ma ta dole ce, domin fitsari ne ya cika mata mara, ga salloli a kanta Azahar da La'asar. Nan da nan masu daukar hoto da masu daukar bidiyo suka yi ruddugu suna daukarta, ba tare da ta shirya ba. Da kyar Sajida ta samu ta shiga bandaki, saboda jama'ar da suka baibaye burtintinar amarya su na daukar hoto da ita. Shigarta bandaki ke da wuya, kafin ta rufo kofa Umma Furera ta danna kai dauke da ruwa bokiti guda da kwandon soso da sabulu na wanka. Mata uku ne suka shiga bandaki su na yi wa Sajida magiya ta daure ta yi wanka, idan ba ta yi da kanta ba zasu danne ta su yi mata.
Sajida ta cije, ta tubure ta ce ita fa ba za ta yi ba, amma da ta ga da gaske shirin tube ta suke da karfi za su wanke ta, sai ta saduda ta ce su fita za ta yi da kanta. Su ka fito suka bar ta a bisa sharadin idan ba ta yi wankan kirki ba sai sun sake yi mata wani.
Sajida ta fashe da kukan takaici, tana wanka

Please Login or Register in order to submit comment