Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewar su ji tsoron Allah su san duk inda suka shiga suka labe Allah na ganinsu, idan ni bana ganinsu."
Baba ya dubi Bakura ya ce "yaro na ji abinda ka ce, kuma na gode."
Ya juya ya shiga gida da sauri, Bakura ya shiga motarsa ya tafi gida.

*** *** ***
Ya na isa gida Auwalu mai gadinsa ne ya taso a guje ya wangale tafkeken get din shiga farfajivar gidan. Sanyin ni'ima da qamshin fulawoyi ne za su daki hancinka. Yayin da korayen fulawoyi da jajaye da ruwan dorawa da fararen furanni ne zasu dinga haskake kwayar idonka. A tsakiyar farfajiyar gidan wani round about aká yi shi da tiles amma an dankara fulawoyi a tsakiyarsa don haka akwai wani ruwa da yake bululowa ta ciki ya na tashi sama yana ban ruwa. Ga filin ajiyar motoci nan fiye da mota goma za su iya tsayawa a lokaci guda, gefe kuwa liluka ne a jejjere na wasan yara kai ka ce a 'Wander land Abuja' kake ( wajen wasan yara).
Tsuntsaye ne masu kyawun gaske suke kai kawo a farfajiyar gidan, kamar dawisu, talo-talo, jimina, aku, da 'yan qananun tsuntsaye masu launuka daban-daban, gefe kuwa qaton fili ne aka kewaye da birirruka da maguna da burguza-burguzan Karnuka irin na turawa masu gashi buzu- buzu gidan kowananansu akwai bangarensu akwai masu kula da su. Masu kula da filawowi dabam masu wanki da guga daban, direbobi daban-daban. A cikin gida kuwa mata masu aiki kala-kala, akwai makekiyar boy's quarter a bayan gidan akwai dakunan masu aiki burjik. sauke kunun da zafinsa."Kai ka fi cancanta 1


JUT


Paid book



0️⃣5️⃣

Ya na shigowa farfajiyar gidan dan girmamawa sai dukka ma'aikatan kowa ya durqusa ya na kwasar gaisuwa. Dakyar Bakura ya ke daga hannu yana amsawa saboda d'imuwar da ya ke ciki. kai tsaye ya zarce da motar runfunan da aka yi su don ajiye motoci ya tsaya ba tare daya kashe motar ba ya dora kai akan sitiyari ya yi shiru ya na tunani mai zurfi. Bayan 6acin ran halin da Abdulmajid yake kokarin saka Sajida, sai tunanin yaya aka yi Sajida ta yi kama da Zuhuriyyarsa? Lallai kuwa kamar ta baci, dömin idan ya rufe ido ya hango fuskar Zuhuriyya ada, sai ya hango fuskar Sajida, da maganar da yanayin jikinsu sai ya ga sak iri daya ce babu abinda ya raba su.
" Ina cikin wani hali. Yaya zan yi na gano bakin zaren ne? Qarshe magana dai na je na ga iyayen Sajida kuma babu hadinsu da qauyen Cinkilawa. Kuma na san dangin Zuhuriyya gaba dayansu babu had'insu da unguwár Kawo amma Allah cikin ikonsa ya halicesu kamarşu daya sak." Bakura ne ya fada a bayyane.
Fiye da mintuna talatin Bakura na zaune a mota ya kifa kai ya na tunani. Ma'aikata su na ta kai kawo su na tambayar kansu da kansu shin yau maigida lafiya, ya zauna a mota ya kasa fitowa? Tsananin girmamawa da shayinsa ya hana kowannansu qarasowa su tambaye shi. Da kansa ya duba agogo, ya ga magaruba ta yi, sai ya kashe mota ya fito.
Idanuwansa sun kada sun yi jawur da alamar tashin hankali a tattare da shi. Kallo daya ya yiwa ma'aikatan da su ka yi layi a bayan motarsa sai su duk suka watse domin sun tattaru a waje daya sun yi jugum, hankalinsu ya tashi saboda ganin sabon al'amarin da ba su taba gani ba.
Ya kwallawa Magaji direban yara kira, Magaji ya amsa cikin ladabi ya zo ya duqa ya gaishe shi. Bakura ya ce da shi ya miqe tsaye kuma ya d'ago da kansa ya dubi kwayar idonsa zai yi masa wata tambaya. Kuma ya tabbatar amsar da zai bashi gaskiya ce kada ya sake ya yi masa karya.
Jin haka sai hankalin Magaji yayi mummunan tashi, kan ka ce kwabo ya fara gumi, muryarsa ta hau karkarwa ya tambaya "maigida me ya faru?"
Bakura ya yi ajiyar zuciya ya qurawa Magaji ido,
Magaji ma ya qurawa Bakura ido zuwa wani dan lokaci.
Bakura ya ce "daga makarantar boko da ta islamiyya ina da ina Zahra take cewa ka kaita?"
Magaji ya sake zazzare ido ya fad'a cikin rawar murya "daga makaranta ba inda na taba kaita wallahi."
Bakura ya gyada kai ya yi shiru can ya ce "wallahi, Allah kenan fa. Na yarda amma ka tabbatar abinda ka fad'a min gaskiya ne, zanci gaba da bincike, daga lokacin da na gane ka yi min qarya daga sanda na lahira zai fi ka jin dadi. Domin ka fi kowa sanin halina a duk cikin ma' aikatan nan. Shekararmu goma sha daya kenan tare."
Bakura ya wuce cikin gida ya bar Magaji a nan ya na muzurai gami da mamakin wannan tambaya.
Kofar wani katafaran falo ya nufa wanda aka yi shi a cikin wata kayatacciyar baranda mai dauke da tukwanen fulawoyi a jejjere kana shiga dosar kofar falon za ka ji sanyin na' urar sanyaya daki (AC) ta daki hancinka gami da qamshi mai dadi. Ka na shafa labulen da ke zagaye da falon za ka tabbatar bada gujari-gujarin auduga gama gari aka halicci yadin labulen ba, saboda laushinsa. Zanen fulawar jikin labulen zai tabbatar mu ku da cewa ba daqiqan mutane ne suka qera labulen ba. Haka yanayin dinkin da yadda aka liqa labulen kansa sai wanda ya yi masters akan dinki, wanda ya karanci design and decoration ne. Labule ma kenan ina ga kayan alatun dake cikin falon nan? kallo daya za ka yiwa kujerun, center table, flower bases din falon ka gasgata cewa an qera su ne da ruwan gwal, anyi musu design da azurfa. Komai na falon anyi masa kalar kore da ruwan goro (green and orange) kama daga fentin jikin bango har centre kafet dake tsakiyar kujcrun har su kan su kujerun da dining table da yake dining area a falon. Hatta fitulun falon abun kallo ne domin su ma hasken da suke bayarwa kore ne da ruwan goro.
Qatuwar talabijin woto LCD ce a maqale a jikin bangon falon kai ka ce mutum ne a jikin bangon ba hoto ba. Akwai qofa wacce za ta kai ka cikin gida, ka na fita tsakar gida za ka gani. Wanda aka qawata shi da tiles tsakiyar kuma anyi masa dan zagayyen tudu an dora flower veses da wata qatuwar bishiyar (unbrellar) wacce take hana rana shigowa. Wasu qawatattun kujeru na kaba aka jejjera domin shan iska. Qofofi ne guda shida a zagaye da tsakar gidan, idan ka bude na farko wani qaton kicin ne mai girman gaske wanda babu abunda za ka hango illa kayatattun kitchen cabinet kalar ruwan dorawa (yellow) sai Gas cooker da electronics kala-kala. Hakika kallo daya za ka yiwa kitchen din nan ka tabbatar wadanda su ka hada kicin din karanta su ka yi ba kai tsaye suka tari aradu da ka ba. A takaice dai duk abunda ya ke cikin kicin din nan fari da ruwan dorawa ne. Sauran qofofin kuwa guda biyar kowannensu qaton falo ne, da kuna bibbiyu da kayataccen bandakai guda biyu.
D'aya na Zahra ne, d'aya na 'ya'ya maza ne, daya na matar gidan ne, d'aya na mai gidan, d'aya kuma a rufe ya ke ba kowa na saukar baqi ne.
Sai dai dakin Bakura (master bed room) ya fi sauran girma sosai da qawatuwa domin girman falonsa ya kai girman wani qaramin gidan kacokan.
Falon hade yake da dining area, da kicin sai ka shiga bed room maimakon dakuna bibbiyu irin na sauran d'akunan shi guda d'aya ne aka yi shi makeke, ya yi dukka biyun girma in abun a fashe su ne.
Biro na da takarda baza su iya zaiyana haduwar bangaren maigida ba sai dai na kan iya fadar kalar da aka hada a ciki. komai na ciki kalar uwan madara ne aka dan sirka da fari. Kama daga fenti, kujeru, dining table, kayan kicin, set din gadon da kayan toilet shima ko ba'a fada maka ba ka san turawa ne su ka zo Nigeria su ka baje fasahar da Allah ya ba su, suk a shiryawa Bakura gidan nan.
Haka ma dakin matarsa aka qawata mata falonta, dakuna biyu da bandakanta, ita kuma kalar jan duhu (maroun) ne komai.
Dakin Zahra babbar 'yarsu kuma ita ce 'yar su mace kadai itama na ta bangaren falo da dakuna biyu da bandaki a kowanne daki. Itama an zuba mata funiture da su ka dace da budurwa, duk ko ina tayi like-liken hotunanta dana iyayenta, qannenta da qawayenta. Komai kalar pink ce a dakin.
Dakin 'yaya maza kuwa su uku ne, na biyun sunansa Abubakar shekararsa goma sha uku, shi ya dauki daki daya. Mai bin sa Umar shekarunsa bakwai da d'an autansu Usman shekarunsa hudu su biyu a dayan d'akin. Kowannensu da d'an qaramin gadonsa da lokar kayansa da mudubi da kujera da teburin karatu da rabutu. Falo kuwa durowar litattafai ce iri-iri da set din kujeru, sai Talabijin da settelite game da tashoshin cartoons da karatun qur'ani kadai aka jona musu. Duk abinda ke cikin dakin kama daga fenti har furniture da bandaki kalar Blue ne aka sirka da pupple.
Dakin dake rufe ma ba'a bar shi a baya ba wajen kyau da tsari duk da ba kowa a ciki amma akan yi baqi mata daga wani gari su ake saukewa, shi ma duk abunda ya ke ciki kalar brown ne.
Bakura na shiga katafaren falon nan ya iske matarsa abar qaunarsa Samira, ta caba ado ta na jiran mai gidanta ya dawo. Ya na shigowa ta daga ido ta dube shi, sai ta yi masa fari da fararen idanuwan nan na ta dara-dara. Irin farfarin da ta gane yana kwantar masa da hankali. Ya yi murmushin qarfin hali gami da yi mata sallama. Samira ta amsa cikin jin dadi tare da miqewa da sauri ta na rangwada ta nufo shi sanye da wata atamfa koriya super Holland wacce ta yi mata hadadden dinki na matsatstsiyar riga da siket mai daukar hankalin maigida.
Ta na qarasowa inda ya ke sai hancinsa ya daki qamshin turaren jikinta designers, hade da na hadaddiyar humra da turaran wuta.
Ta fada cikin sanyayyiyar murya mai kama da rada "sannu da zuwa Sweety."
Kafin ya bude baki ya amsa ta sumbaci gefen kumatunsa, ya sa hannu ya dakatar da ita gami da zare jikinsa daga gare ta ya wuce abinsa. Ya shiga cikin gida Samira ta tabbatar yau hankalin Sweety ba'a kwance ya ke ba, sai ta fara jerowa kanta tambayoyi ta na tuhumar kanta da kanta ko ta yi ma sa laifi ne kafin ya fita. Ta tuno ai lafiya kalau su ka rabu har ta raka shi mota su na wasa da dariya da yamman nan ya fita ya na nishadi.
Samira ta fada a bayyane "waye ya tsokano min maigidana? Ya b'ata ma sa rai mutumin da idan ransa ya b'aci ya kan yi fushin kwana uku bai huce ba."
Fushin Bakura shi ne babban tashin hankalin Samira domin ba zai kula ta ba, ba zai ci abincinta ba, babu wasa balle hira, ga mummunar harara da daka tsawa. Dan haka yadda take lallaba jaririn da ta haifa sabowar haihuwa haka take lallaba maigidanta don kada ya yi fushi.
Allah ya jarrabi Samira da tsananin qaunar Bakura, ta na ji a jikinta da a raba ta da Bakura gara a rabata da rayuwarta.Kai ka fi cancanta 1

JUT

Paid book


0️⃣6️⃣

A sanqare a tsaye Bakura ya bar Samira ta na tunani hade da fargaba da karanto addu'o'i a zuci. Addu'ar Allah Ya yayyafawa zuciyarsa ruwan sanyi koma me aka yi masa a waje.
Shigarsa dakinsa ba dadewa ya fito jikinsa da ruwa da alama dai alwala ya dauro.
Ta yi sauri ta saki fuskarta ta dube shi ta yi murmushi ta ce "alwala kayi, za ka je masallaci?"
Ya amsa a ciki-ciki "eh:" Har ya kai qofar fita ya juyo ya dubeta ya ce "ina Yagana?"
Ta amsa cikin jin dadin maganar da ta samu ya yi mata.
Ta ce "ta na daki ta na karatu, saboda sun kusa fara jarabawa."
Ya sake cewa "ina Abubakar, Umar da Usman? Ta ce "su na nan a masallacin qofar gida tunda yamma, Malam Hashim ya zo su na daukar karatu."
Ya juya ya fice ba tare daya ce komai ba.
Mamaki ya sake lullu6e zuciyar Samira ta kasa gane halin da yake ciki yau, kamar ya na farin ciki kamar ya na baqin ciki. Ta shiga dakinta ta yi alwala ta yi sallar magrib. Tayi ta lazumi tana addu'a kamar yadda ta saba kullum akan Allah ya sassauta zuciyar
Bakura, ya so ta d'ari bisa d'ari kamar yadda take son sa, ya dinga sakar mata fuska, ya rage wannan muzuran da kwarjinin da ya ke yi mata don haka kawai ta ji ta na tsoransa. Kada Allah ya hada shi da wacce zai ji ya na so a rayuwarsa balle ya yi mata kishiya, duk da ta san tsautsauran ra'ayinsa ba shi da niyyar yin mata biyu a rayuwarsa. Mata basu cika burge shi ba amma ta san lallai idan ya hadu da yarinya mai tarbiyya wacce take da ladabi da biyayya za ta iya burge shi ya aure ta, ita kuma tsantsar sonsa ne ya dasa mata tsananin kishinsa. Addu'ar Samira kenan, dan duk wanda ya santa ya san ta ya san ra'ayinta.
Aka kira sallar sha'i a masallacin qofar gida, su Bakura suka bi jam'i aka tayar da sallah. Samira ma daga dakinta ta aiwatar da ta ta sallar, bayan ta idar ta yi shafa'i da wutiri da laziminta sannan ta miqe ta qarasa wajen kayan kwalliya ta sake caba ado. Aka sake saka huda, jagira, jan baki, ta sake yin daurin dankwali ta feshe jiki da turararruka designers sannan ta fito.
Ta na fitowa ta nufi dakin Zahra, ta iske Zahra ma ta idar da sallah. Cikin ladabi Zahra ta dubi mahaifiyarta tayi murmushi,
Ta ce "Mama sannu da gida. Kin yi kyau."
Samira tayi murmushi ta ce "Zahra sannu da karatu, ki fito mu ci abinci, Abbanki ya dawo ki yi masa sannu da zuwa don ya tambayeki kafin ya tafi masallaci."
Zahra ta amsa da "to Mama."
Su ka d'unguma suka fito, Zahra sanye doguwar riga baqa (abaya) kanta a lullu6e da qaramin hijab baki mai hula iyaka Rirji. A babban falon gidan suka ci karo da Bakura tare da yaransa Abubakar, Umar da Usman sun dawo daga masallaci.
Samira ta ce "yauwa sai mu wuce kan dining table mu ci abinci ko Abban Zahra? Yau da kaina na shiga kicin na dafa maka burabusko irin na ku na barebari."
Ta ga ya yi turus bai juya ya kalli dining table din ba ma balle ya bude ya ga abinda aka dafa masa balle ya burge shi.
Zahra ta ce "Abba sannu da zuwa, shugabar makarantarmu ta ce in gaisheka."
Sai su ka ga ya tsuke fuska ya kada kai zai nufi dakinsa, har ya kai qofar fita sai ya juyo ya dubi Zahra.
Ya ce " Zahra ki kula da rayuwa, ki tabbatar kin saka tsoran Allah a cikin zuciyarki a duk inda kike. Ba ruwanki da lalatattun qawaye da samari bata gari. Na sakale Kwaryata ta gari a ragaya ba na fatan kwaryar nan ta tsinke ta fado daga ragaya ta dinga garari a tsakar gida."
Yajuya ya tafi abinsa ya tafi.
Cafdijam!!! Wannan Hausa ta yiwa Uwar Zahra tsauri balle ita Zahrar kanta. Daman idan aka dunkule Hausa, ko karin magana Zahra ba ta ganewa, ta fi gane yaren kanuri sai kuma turanci. Tabbas tana jin Hausa amma ta ina za ta fahimci wannan maganar ta da?
Samira bahaushiya ce gaba da baya amma ya aka yi wannan Babarbaren ya yi ma ta Hausa cikin Hausa ba ta fahimce shi ba? Dadin dadawa ba su san kan maganar da ya ke yi ba balle su gano bakin maganar.
Hanakalin Zahra ya tashi, ta kalli mahaifiyarta ta dafe kirji. Ta ce "Mama me na yiwa Abba, wacce kwarya ya ke magana?"
Samira ta fita da sauri ta bi shi dakinsa, ta iske zai shiga wanka, ta dube shi.
Ta ce "Sweety Zahra ta damu ta na tambayar ko wanni laifi ta yi maka."
Ya girgiza kai ya ce "ba laifin komai ta yi min ba dama ba lallai ne ku gane abinda na ke nufi ba yanzu sai a nan gaba."
Ya juya zai shiga bandaki Samira ta qara dakatar da shi. Ta ce "sai kayi wanka za ka fito mu ci abinci ko na kawo maka na ka kan daning table din nan dakinka?"
Ya girgiza kai ya ce "ba zan ci ba na qoshi."
Hankalin Samira ya tashi ta fara magana kamar mai shirin fashewa da kukan kissa da nuna damuwa.
Ta ce "haba Yayana, maigidana, abin qaunata. Ya zan dage in yi maka abincin daka fi so a rayuwarka wato burabuskon gero, kuma ka ce ba za ka ci ba. Mu yaya za' ayi mu iya ci...?"
Kafin ta rufe bakinta ya dakatar da ita ya ce "ki je ke da yaranki ku ci, ni na qoshi. zan yi wanka in kwanta idan kin shigo kada ki kunna min fitila, jada ki tashe ni ba zanyi hira ba yau. Ka da ki kuskure abinda na fada miki wannan doka ce."
Samira ta juya sadan-sadan ta fice daga dakin ba tare da ta sake cewa komai ba kuma bata san me hakan yake nufi ba.
Sai ta ji ya yi magana ya ce "ka da ku damu ke da yaranki babu wanda ya yi min wani laifi a cikinku."
Ta juyo da murna ta dube shi ta ce "kawai yanayi ne ya canja?"
Ya ce "yanayi ne kawai, yau na ga mai kama da Zuhuriyya sak kamar an tsaga kara shine hankalina ya tashi."
"Mai kama da Zuhuriyya fa ka ce? A ina? Bakura ka san abinda kake fada kuwa?" Samira ta tambaya cike da mamaki.
Ya daga mata hannu ya dakatar da ita. Ya ce " tambayoyin sun isa haka. Sai da safe."
Samira ta fito zuciyarta cike da mamaki da kokonton anya kuwa Bakura ba shi da wata aljana a jikinsa? Ko dai aljanun ne su ka tashi yau?"
Samira mace ce dirarriya mai tsawo da 'yar qiba. Fara ce sosai, sai dai ba ta da dogon hanci , bakinta madaidaici ta na da dara-daran idanuwa farare qal ma su kyau. Ba ta da gashi mai tsawo amma kuma ba gwaguyyaye ba ne. Mace ce mai tsafta gami da taushin murya, mai tsananin haquri domin idan ba ita ba ba mai iya zama da Bakura. Ta iya lallashi ta iya tausar ran mijinta, ta na da tausayi da kyautatawa masu aikinta. Ta na da son wasa da dariya da yaranta har da ma sauran jama'a. Ta na da ilimin addini daidai gwargwado da na boko duk da iyakacinta daga sakandire ta tsaya ba ta ci gaba ba haka kuma bayan ta auri Bakura bai bar ta ta ci gaba ba.
Samira ta fito ne daga babban gida ma'ana gidan arziki da mutunci. Mahaifin Samira mutumin Kano a unguwar yakasai yake. Ta na da qanne da yayye ba adadi kasanceyar mahaifinta mata hudu gare shi. Dukkansu su na nan da ransu reras. Amaryar gidan ma har yanzu ta na haihuwa.
Ta auri Bakura saboda ta na sonsa Zahra ce babbar 'yarsu ta fari kasancewar sunan mahaifiyarsa ne yake kiranta da Yagana. Zahra tayi matukar yin kama da Babanta ko ba'a fada maka ba idan ka kalli Bakura ka kalli Zahra ka san irin su daya.Banbancin shi namiji ita kuma mace. Da wuya ka kira shi Babanta sai dai ka dauka Yayanta ne kasancewar auren wuri yayi da haihuwar quruciya. Zahra tafi mahaifinta haske kasancewar ta dauko hasken fatar mahaifiyarta amma ba dukka ta dauko farin ba ta hada da baqar fatar mahaifinta sai ta bada kala mai kyau wato hasken duhu (chocolate colour).
Wannan kalar ta Zahra ta sake fitar mata da kyawunta, dogon hancinta siriri har baka irin na barebarin asali, bakinta dan qarami har ya fi na mahaifinta kyau, haka fararen haqoransu da wushiryar sama da qasa duk iri daya. Ga wani Iallausan gashi har qasan qeyarta bakikiirin mai tsawo. Jikinta abin sha' awa, doguwa ce siririya. Kirar kamar Bakura ba su da kiba.
Mazan kuwa Abubakar, Umar da Usman ga farin har gajeran hancin sak irin na mahaifiyarsu sak, daba

Please Login or Register in order to submit comment