Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata dadi, tunda take a rayuwarta bata taba shiga irin wannan tashin hankali ba. Tayi nadamar zuwa gidan su Sajida da ta yi.
Sautin kukanta ne ya ke tayarwa da Samira hankali ta kasa zaune ta kasa tsaye sai safa da Marwa take a tsakanin qofar falo zuwa cikin gida. Ta san Zahra da zurfin ciki, Bakura kuma da zuciya. Idan ya hasala zai iya mangare ta a sake yin rauni na biyu. Ta ji kawai ba zata iya ba gara kawai ta matso daga kusa tana ganin abinda zai faru. Ta yi sallama ta shigo falon bata damu da hararar da Bakura ke yi mata ba .Ta sami kujera ta zauna a kusa da Zahra , magana take yi mata cikin rada, shawara take bata kawai ta fadi sunan yarinyar da adireahinta babu abinda zai faru hakkinta zaa kwato mata.
Su Bakura su ka gama cin abinci tas, Zahra ta san kanta zai dawo. Zahra ta dubi malam Yakubu ta juya ta dubi mahaifinta sai ta ji gabanta ya sake faduwa.
Tsawa mai firgitarwa Bakura ya dakawa mata daga ita har Mahaifiyarta sosai da suka razana ya ce "wannan shine tambayar da zan yi miki ta karshe ki fada min wacece yarinyar? Kuma waye ubanta a Kano? Kuma da wa take taqama a kasar nan?"
Bakin Zahra yana karkarwa, haka hannunta yana rawa sai ta nuna malam Yakubu cikin rikikitacciyar murya ta ce "Malam ne mahaifinta, Sajida ce."
Malam ya kalli Bakura, Bakura ya dubi Malam gaba daya suka juyo suka dubi Zahra. Su ka hada baki a tare su ka tambaya
"Sajida? "
Samira ma ta tambaya
"Wacece Sajida?"
Wannan amsar ta gagari bakin Zahra, ba ta san amsar da za ta bata ba.

TAMBAYA???

*Shin wacece Zuhuriyar nan da Bakura yake mutukar kauna fiye da iyalansa, fiye da kan kansa?

*Meye dangartakar Zuhuriya da Bakura da yake tsananin begenta?

*Shin ina Zuhuriyar take ne, ko ina ta tafi?

*Shin Bakura zai yarda ya auri Sajida? musamman yadda tsantsar rashin tarbiyyarta ya bayyan a fili?.

*Shin yaya za'ayi a raba soyayyar Abdulmajid da Sajida? yadda Sajida take tsananin kaunarsa haka?

*Shin yaya soyayyar Zahra da Abdulmajid zata kasance? Musamman daya ganta a zahiri kuma tayi masa?

*Shin wanne mataki Bakura zai dauka akan
mahaifin Sajida da ita Sajidar kanta? Tunda yayi rantsuwa sai ya dau fansa ba zai qyale wacce ta aikatawa 'yarsa Jalli daya kwal wannan ta'asar ba?

*Shin wanne mataki malam Yakubu zai dauka akan Sajida da mahaiiyarta musamman idan ya ji ance da Abdulmajid suka fita?

Amsoshin wadannan tambayoyin suna nan tafe ku ci gaba da saurarona
Kai ka fi cancanta paid book #300



Bakura ya ji gabansa ya yanke ya fadi, kamar yadda irin wannan fargaba ta ruftowa Malam. Bakura ya juya ya dubi Malam, yayin da shi ma Malam ya juyo ya dube shi, duba mai cike da dimaucewa, gami da gigicewa, lokaci guda suka juyo suka dubi Zahra. Bakura ya ji gabbansa sun yi sanyi, har ba shi da kuzarin da zai iya ci gaba da rike qaton faskaren itacen da yake hannunsa. Cikin sanyin jiki ya tsugunna ya ajiye faskaren itacen a qasa, yayin da Malam ya sulale ya durkushe a qasa yana karkarwa.
Yana fadin."Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Sajida, Sajida kin cuce ni,ba zan barki ba har sai an fitarwa da Zahra hakkinta kamar yadda muka kudira, saboda kada mu yi kaffara ni da kai gaba daya. Sajida ta cancanci a hukunta ta, saboda yarinya ce marar jin magana, mai tsiwa. Ka haifi mutum ba ka haifi halinsa ba. Ya ya zan yi da rayuwata? Ina zan saka raina? A ce ni a rayuwata ba zan matsa nan da nan ba, sai dai in zauna in yi gadin Sajida da Abdul Majid. Yanzu Sajidar da na hana zuwa makaranta, ita ce aka hadu da ita har a Super market....."
Kafin Malam ya rufe bakinsa, kuka ya kece masa saboda takaici.
Hankalin Bakura ya tashi, tausayin Malam ya lullube shi, yayin da ya ji kwalla ta cika masa ido. Ya yi sauri ya mayar da ita. Tsananin fushin da tafasar da zuciyar ke ciki sai ya ji zuciyaryarsa ta yi sanyi qalau, hade da sanyin jiki.
Ya girgiza kai ya ce da Malam "Na yafe, na bar zancen nan duniya da lahira, tunda Sajida ce. Sai dai na yi mamakin abin da zai hada ta da Zahra har ya kai su ga haka. A iya sanina, sanda Zahra ta ziyarce ta sun rabu lafiya, ba tare da sun yi fada ba. To me yake faruwa?'"
Malam ya rike kai yana jujjuyawa, don takaici yana magana cikin zubar da hawaye. Ya ce, "Mugunta ce kawai tsagoranta, amma me Zahra za ta yi mata har ya kai su ga yin fada. Ai ko baka sa an kulle Sajida ba, yanzun nan zan biyo ta police station, in tafi da 'yan sanda su kulle ta."
Bakura ya zabura, gami da daga hannu biyu yana yi wa Malam magiya akan ya yi wa Allah ya bar zancen nan. Yasa hannu ya tashi Malam tsaye, gami da ci gaba da lallashinsa, yana mai ba shi baki ya kwantar da hanakalinsa ya bi abin a hankali, kada ya biyewa sharrin zuciya ya lahanta 'yarsa. Ita ma Zahrar ba kyalle ba ce, watakila wani abu ta yi wa Sajidar har ta kai su ga haka. Da kyar Malam ya jefa qafafuwansa ya qarasa wajen mota, Zahra da Samira su ma suka dungumo dan su yi musu rakiya. Bakura na gefensa ya yi sauri ya bude masa kofa ya shiga gidan gaba ya zauna, yayin da sauran almajiran suka shiga baya. Har Bakura zai rufe masa qofa, Malam ya rike qofar, gami da juyowa ya dubi Zahra ya kwalla kiran sunanta. Ta yi firgigit ta karaso gabansa ta durkusa, yayin da bugun zuciyarta ya sake qaruwa. Malam ya dube ta cike da tausayi da nadama.
Ya ce, "Zahra ki yi wa Allah ki fada min duk abin da ya faru tsakaninki da Sajida?"
Zahra ta dago da sauri ta dubi mahaifinta, yayin da ta ci karo da galleliyar hararar da yake gallo mata, ta durkusar da kai kasa, yayin da muryarta ta hau rawar disco tana sama tana kasa don fargaba.
Babban tashin hankalinta kada zancen saurayi ya fito a cikin maganar, saboda yadda mahaifinta yake kyamar abun. Ita kuma ta san saboda Abdul Majid yana yi mata waya, Sajida ta kullace ta.
Zahra ta yi narai-narai da ido. Ta ce "Babu abin da na yi mata ta jawo gwangwani ta fasa min kai."
Tsawa mai firgitarwa Bakuřa ya daka ma ta, ta ji har tsakar kanta á karkarwa, Ya ce, "Ki fada mana gaskiya, ko mahaukaci ka ga ya bi yara tsokanarsa suka yi."
Cikin kuka Zahra ta ce, "Abba, wallahi na rantse da wanda numfashina yake hannunsa, tun ranar da muka je da kai ban sake ganin Sajida ba, kuma babu abin da ya hada ni da ita sai ranar da muka hadu a Super market dinmu. Kalmar da na ji ta ambata itace ta cewa kawarta Iyayye ga munafukar da take hada min tuggu. Kafin in tambaye ta munafuncin da na yi ma ta ta wawuro gwangwani ta kwada min."
Kuka ya sake kece mata, Malam ya gyada kai ya ce, "Ita da Iyayye suka fita Super market sayayya kenan?Ina suka sami kudi? Wannan ma abun tuhuma ne, tabbas kwarya ta gari tana ragaya, Sajida ba ta yi sa'ar uwa mai tarbiyya ba. Zahra goge hawayenki zan bi miki hakkinki. Tashi ki tafi ki yi hakuri, ki yafe mana, ki yi mana afuwa ba za a sake ba."
Zahra ta ce, "Na yafe mata Malam."
Ta yunkura ta tashi ta nufi inda mahaifiyarta da kannenta ke tsaye carko-carko, suna kallo suna sauraron wannan al'amari mai kama da al'mara.
Bakura ya ce da Malam, "kamar yadda kake ba ni shawara nake dauka, ka yi min alfarmá guda daya nima a yau. Dan Allah idan ka je gida kada ka daki Sajida, balle ka ce za ka dauki itace ko wani makami ka fasa mata kai, ko ka ce za ka hada ta da 'yan sanda da dai sauransu. Ka lallaba ta ka tambaye ta dalla-dalla abun da ya faru tsakaninta da Zahra, kamar yadda ka tambayi Zahra cikin sanyin rai. Ka mata nasiha, kada takurar ta yi mata yawa har ta falle fiye da yadda take a yanzu."
Malam ya gyada kai ya ce, "Na yi maka alkawari ba zan dake ta ba. Sai dai ina gudun kada wannan abu ya jawo silar tabarbarewar zumuncin da ke tsakanina da kai."
Bakura ya zabura ya ce, "Haba, haba Malam me zai sa ka yi wannan tunanin, babu abin da zai sa in canja. Jibi ma zan zo daukar karatu insha Allah. Sajida 'yata ce, ko in ce kanwata ce. Ita da Zahra duk daya ne."
Malam ya ji dadin kalaman Bakura, ya yi murmushi ya ja kofar motar ya rufe. Ya ce "Allah ya saka da alkhairi, na gode ina sauraron zuwanka jibin."
Direba ya ja mota suka tafi, kallo daya Bakura ya yi wa dandazon 'yan aikin da suka taru don bada hakuri, sai kowa ya warwatse sum-sum-sum, ya kama gabansa. Yayin da ya sake wurga idonsa ya dubi iyalinsa suma suka dibi 'yan kafafuwansu zuwa cikin gida. Bakura ya sami kujera a gindin wata bishiya mai sanyi dake farfajiyar gidan ya zauna yana mai tsananin tunani, yana jujjuya kalmar da Sajida ta fadawa Zahra. "Ga munafukar da take hada min tiggu." Wanne munafunci Zahra ta yi mata a karon farko da ta fara saninta? Wannan al'amari ya dimauta zuciyar Bakura matuqa.
A cikin gida kuwa, Zahra ce da Mamarta ake fafatawa, domin ran Samira ya baci matuqa. Ta saka Zahra a lungu ta ritsa ta, ta ce sai ta fada mata.
Wacece Sajida? A ina take? Yaya aka yi har suka je gidansu, amma ba su taba fada mata ba? Zahra ta zayyaanawa mahaifiyarta duk yadda aka yi da dalilin da yasa suka je ta ganta. Samira ta ji hankalinta ya tashi, duk da ta san labarin yarinya mai kama da Zuhuriyya, amma ba ta ga dalilin da Bakura zai dauki Zahra ya kai ta gidansu ba.
Lallai akwai wani boyayyen al'amari, akwai wata hujja mai karfi a cikin wannan magana,.musamman ga wanda ya san tsatstsauran ra'ayin Bakura." Samira ce take tattaunawa a zuciyarta, yayin da take kai-kawo a tsakiyar falo.
Zahra ta takure akan kujera ita da kannenta gaba daya sun rasa abin da yake yiwa rayuwarsu dadi a yau, domin su ba su saba haduwa da irin wannan tashin hankalin a gidansu ba. A koda yaushe iyayensu a cikin nishadi suke, amma yau komai ya hautsine.
Samira ta juyo a fusace ta dubi Zahra, ta ce "Mahaifinki ne abokin shawararki, mahaifinki ne abokin hirarki, shi ne ki ke fadawa damuwarki, ban da ni."
Zahra ta bude baki za ta yi magana, Samira ta dakatar da ita da hannu, gami da daka mata tsawa mai qara. Samira sai bambamin fada take har da kumfar baki, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, domin ranta ya baci matuqa. Zahra ta yi shiru, yayin da kuka ya addabi idanuwanta ta yi nadama tayi dana-sanin zuwa gidan su Sajida a rayuwarta.
Ana jiyo Muryar Samira har farfajiyar gidan, inda Bakura ke zaune, hakan yasa ya shigo gidan don ya ji me yake faruwa. Shigowarsa ba ta sa Samira ta daina fadar maganganun da take fada ba akan Sajida. Yau ba ta tsoro, daga dukkan alamu ta zama 'yar ta kife, ko a samu ko a rasa. Yau ba ta tsoron a yi duk wacce za a yi, in ji beran da ya zubar da garin mage. Bakura ya fahimci zancenta bai wuce akan kishi ba, wai kumallon mata in ji masu iya magana. Sai ya wuce zuwa dakinsa abinsa ba tare da ya ce da kowa uffan ba.
Ya na shiga ta bishi a baya, kalmar da ta fito daga bakinta ita ce, "Wacece Sajida? Kuma meye dangantakarka da ita, har za ta fasawa 'yarka kai amma ka ce ka yafe ba tare da bincike ba? Shin Baban nata asirce ka ya yi da har kai ka ke ba shi hakuri? Ko ya zo ne ya samarwa 'yarsa dan mutsugunni a gidana, saboda ta yi kwantai, ko kuma in ce talauci ya yi musu kanta?"
Saboda takaici bai iya ba ta amsa ba, ko kallon inda take bai yi ba. Ya cire rigar da take jikinsa ya hau gado ya kwanta, gami da matsa remote din A.C, don sanyaya gumin da ya addabi jikinsa.
Samira ta sake cewa "Ka yi zumucinka da Sajida da mahaifinta, amma ban da ni da 'ya'yana."
Wannan karon nuni ya yi mata da hannu, alamar ta fita ta ba shi waje. Ta fice a fusace ba tare da ta sake cewa komai ba. Fitarta ke da wuya Bakura ya yi zumbur ya tashi zaune, ya rike kai yana Jujjuyawa saboda al'amura sun tsananta a gare shi. Ya rasa abun da yake yi masa dadi. Wayarsa ce ta dau ruri yana dubawa sai ya ga sunan Malam Yakubu, wato mahaifin Sajida. Ya ji gabansa ya yanke ya fadi, ya danna wayar da sauri gami da rada sallama. Sai ya ji muryar Malam na karkarwa, alamar yana cikin tashin hankali.
Bakura ya tambaya cikin kidiméwa. "Malam lafiya?" Malam ya nisa ya ce, "Kamar yadda ka ba ni shawara in bi abun a hankali, na bi shawararka, na kira Sajida da Iyayye na tambaye su na ji duk yadda aka yi. Ka ji ashe da Abdul Majid suka fita, shi ne ya kai su Super Market siyayya. Uwarta na gida, ta amince musu suka fita dan haka na yanke hukunci akan Sajida. Ba duka, ba zagi, amma ba za ta wuce sati biyu a gidana ba zan daura mata aure ga duk wanda na ga dama, mahaifiyarta kuma dole ta fice ta bar min gidana."
Bakura ya miqe tsaye, gami da dafe kirji ya ce,"Baba kada ka yi min haka. Ina fatan dai yanzu baka furta saki ba?"
Malam ya matse hawaye ya ce"Ban sake ta ba, amma gara ta tafi gidansu can rigarsu ta huta, nima in huta, ta ga ko ina da amfani.
Bakura ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ka yi hakuri ka bar ta, kada ta tafi, kai namiji ne kada ka hada tunanin ka da na mace, ba ka ganin ko da ta hana Sajida fita sai ta fice din tunda bata tsoron kowa, yara ba su cika jin tsoron iyayensu mata ba.
Musamman Sajida yadda take son Abdul Majid ba ta jin maganar kowa sai tasa, tana shakkarka shi yasa ba ta fita idan kana nan. Babu yadda Umma Furera za ta yi da ita ne shi yasa ta bar su suka fita, amma ka yi hakuri Malam. Zancen aure kuma nan da sati biyu ba zai yiwu ace Sajida ta yarda ta auri wanda ba ta sanı ba, wanda ba ta so, kuma ka ce a zauna lafiya. Ka bari a tsanake ka na addu'a sai ta dawo kan hanya ko Allah Ya shiryi Abdul majid din su yi aure, ko Allah ya yaye mata sonsa, ta sami wani nagari ta aura."
Malam ya ji tamkar Bakura ya watsa masa wuta a zuciya, ya yi farat ya ce, "Wallahi idan kaga Sajida ta auri Abdul majid a duniya, sai dai in ba na numfashi, amma idan ka ga na ci gaba da zama da Sajida a cikin gidana fiye da sati biyun nan to duk mazajen duniya sun guje ta, amma idan da namijin da zan bawa ya karba, to na aurar da Sajida na gama duk talaucinsa, duk naqasarsa, kuturu ko makaho. A yanzu haka na aika almajirina Usman ya je kasuwar Dawanau ya kira min Sama'ila, wani almajirana da yake can yana kasuwanci, na ce ya zo ya aure ta na tabbatar ba zai qi ba. Domin Sama'ila yana da hankali, ya na yi min biyayya, duk da matansa biyu, ita sai ta zama ta uku. Kuma in kafe ta da addu'a sai ta zauna a gidan ba za ta iya fitowa ba, balle ta gudu."
Hankalin Bakura ya tashi matuqa, duk da sanyin A.C da ke dakin amma zufa yake.
Ya ce, "Baba kada ka yi haka amma kashe wayar zan kira ka, saboda kada in cinye maka kati maganar tamu ta na da tsawo."
Malam ya kashe waya, Bakura ya koma ya kwanta yana mai tsunani akan wannan matsala. Hakika ya tausayawa Malam, haka yana tausayawa rayuwar Sajida, Ya tuno irin matsananciyar rayuwar da yara matan da ake yiwa auren dole suke shiga, haka duk akasarin karuwai daga auren dole suke fallewa. Ya tuno irin tsananin son da Sajida take yi wa Abdul majid, ya hasko irin barnar da za ta iya afkuwa idan Sajida ta samu ta fice daga gidan mijinta ta gudu wajen dan iskan nan Abdulmajid. Sai ya tuno 'yarsa Zahra, ya kwatanto a ce bayan ransa komai zai iya faruwa da ita. Ya shiga tunanin hanyar da zai bi ya warwarewa Malam da 'yarsa wannan matsalar, ba tare da kowa hankalinsa ya tashi ba. Da ya rintse ido babu abin da ya hango sai fuskar Sajida da tsananin kamar da suka yi da Zuhuriyyarsa, ya ji a ransa ya kamata ya taimakawa rayuwar Sajida ko don albarkacin kamar da ta yi da Zuhuriyya a matsayinsa na mai ilimi, mai dukiya, kuma cikakken Musulmi.
"Ina mafita? Ina mafita?" Haka Bakura ya fada a bayyane yana ta nanatawa, tamkar karatu, ko kuma in ce tamkar wani tababbe, sabon kamu. Abdul majid, zai iya yiwuwa ma gama lalata rayuwar yarinyar nan."
Ya jawo waya ya bugawa Malam, bugu daya Malam ya amsa ya ce da Bakura. "Ka kira ni anjima, ina tare da Sama'ila an kirawo min shi, zan isar masa da buqata ta, duk yadda muka yi zan sanarmaka."
Bakura ya dakatar da Malam da sauri ya ce, "Kada ka yi haka Malam, ka bari mu yi shawara, yin haka zai iya cutar da rayuwar Sajida, ya wargazawa Sama'ila lissafi, ta rugurguza masa tsarin gidansa, ta wargaza kan iyalansa. Malam ka yi min wata alfarma yanzu ka taso daga gabansu Sama'ila ka fito qofar gida mu yi magana."
Malam ya ce, "Yanzu haka na bar su a zaure na fito qofar gida."
Bakura ya nisa ya ce, "Da za ka bi shawarata kada ka yanke wannan hukuncin, ka kirkiro wani dalili daban ka fadawa Sama'ila na dalilin kiransa, amma ba wannan ba. Tun da a kasuwar Dawanau yake na san awo yake, ka ce masa ina son buhun gero biyu, buhun masara biyu, ya kawo min zan saya, ka sallame shi ya tafi ba tare da ka fada masa ba."
Malam ya ce "toh na ji shwararka, amma idan na sallame shi, ya tafi ya bar ni da Sajida ya ya zan yi da ita?"
Bakura ya numfasa ya ce, "Sajida ka barta kamar yadda na fada a baya, har Allah Ya sa ta gane Abdul majid ba mai qaunarta ba ne sai kaga ta canja shawara, Allah zai kawo mata wani."
Malam ya dakatar da Bakura ya ce "Na rantse Sajida ba za ta wuce sati biyu a gidana ba insha Allah, Bakura ka kasa gane halin tashin hankalin da hatsari da illar da ke tattare da zaman Sajida ba aure.Takai-ta-kawo Sajida ta fara daukar hure kunnen da Abdul majid yake yi mata akan ta daina jin maganar iyayenta ta bi shi su watse daga nan sai ya koya mata shaye-shaye. Ba ka ganin daga tafiyata ta fice, uwarta ma ta ce ba ta san da Abdul majid suka fita ba. Da ta fita kuma ta je ta debo min magana, har da fasawa yarinya kai, ba dan 'yarka ba ce da yanzu ina kulle. Ta jawo mutuncina ya zube a unguwa, ana ganin mota na zuwa ta na daukar 'yata ana fita da ita."Kai kafi cancanta

Bakura ya yi ajiyar zuciya, ya ce "ta fadi gulmar da Zahra ta yi mata, har ta kai su ga batawa?"
Malam ya ce, "Abin da na fahimta, zancen nan ne dai da Sajida ke aron waya a makwabta ta buga masa, wanda Zahra ta fada maka, kai kuma ka fada min, ni kuma na dake ta.shine take ganin babu wanda ya san ta ari waya sai Zahra ta zargin ta yi mata gulma."
Bakura ya ji tausayin Zahra ya kama shi, ya jawo an fasa mata kai a banza, ba tare da hakkinta ba.
Malam ne ya katse dogon tunanin da Bakura ya tsunduma ya ce, "Bakura, zan je in sallami Sama'ila kamar yadda ka shawarce ni, kuma zan yi tunani zuwa kwana biyu idan na rasa mafita, zan sake kirawo Sama'ila in fada masa bukatata. Amma duk shawarwarin da zan je in yi, da wacce za ka yi akan wannan magana ba zai kai wacce nake kwatantowa a raina ba. Bakura KAI KA FI CANCANTA ka samarwa Sajida miji."
Wata hanta ce ta yi girgiza daga cikin cikin Bakura, ya fada cikin wata gigitácciyar murya mai kama da rawar nanaye, dan dimauta ya ce, "Na'am, na'am."
Malam ya nanata ya ce, "Babu abin da hankalina ya fi kwantawa illa in aurar da ita, kuma KAI KA FI CANCANTA ka taya ni zabar mata miji saboda illiminka, na yarda da tarbiyar gidanka, da tsananin tsaron

Please Login or Register in order to submit comment