Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Subhanallahi, sannu ka buge kai ko? Qofar ce irin tamu ta al'majirai." In ji Malam.
Bakura ya murza ido ya ce, "Ba komai, na manta ban durqusa ba, ka san tsawo gare ni kamar dare masha Allah."
Shigarsu cikin dakin ke da wuya Bakura ya yi ido hudu da wani gaftareren hoton Sajida (Lamination) a kafe a jikin bango. Ta kuwa tsala kyau, kai ka ce ba ita ba ce. Ta yi dariya a hoton, yayin da siririyar wushiryarta ta hadu da fararen hakoranta, suka hade da hasken kyamara suka bada wani haske. Duk wancan ganin da ya yi wa Sajida bai kare mata kallo ba ma ashe, a dalilin kukan da take yi, sai yanzu a hoto ya qare mata kallo.Tashin farko da ya dubi hoton, sai ya dafe kirji, saboda mummunar faduwar gaban daya riske shi, ya ce a ansa "Ianalillahi wa'inna ilaihir raju'un." Saboda tsantsar kamar da Sajida ta yi da Zuhuriyyarsa. Kamarsu ma har ta baci kamar an tsaga kara, in ji Bahaushe.
A ce har wushiryar cikin baki da jerin haqora iri daya, dariyarsu iri daya, har da lobawar kuncinsu iri daya (beautiful point) idan sun yi dariya. Kai wannan kama tasu ta yi yawa, in dai babu dangantaka. Kallon hoton Sajida kawai Bakura yake bai ma kula da Sajida ba, tana maqale kanta a cikin gwiwoyinta a lungu, ga sarka a daure a hannu da qafa, kamar wata 'yar fashi.
Malam ya kula Bakura fa bai ga Sajida ba, saboda dan akurkin dakin ya fara duhu, kasancewar yamma ta yi, sai ya ce da Bakura. "Ga ta can fa a takure a lungu."
Bakura ya juyo da sauri ya dubi lungun. Bai ci sa'a ba dan bata dago da kanta ta dube shi ba, kasancewar kukan da take shararawa, amma idonsa ya nuna masa kafafuwanta da hannayenta suma sak irin na Zuhuryya, don haka su ya tsaya yana duba kawai, ba tare da ya iya furta kalma daya ba, don kidimewa. Zuciyarsa ta shiga aikin tantance masa wannan abin al'ajabi, kwakwalwarsa ma wannan aikin ta shiga gaba daya jini da tsokar jikinsa suka canja, saboda rikcewa. Gumi take yi tun karfi, jayayya ake tsakanin huhunsa da numfashin da yake shiga da fitar iske saboda dimaucewa. Idanuwansa suka yi jawur, yayin da yawun bakinsa ya qafe, don haka ba shi da wata kalma da zai iya fadawa Sajida. Ya juya ya sake duban hoton Sajida, kamar ya kira sunan Zuhuriyýa ta amsa, sai ya ji kansa ya fara sarawa saboda tunani ya yi masa yawa. Ya yankewa kansa hukuncin ficewa daga dakin, kafin ya shide ya suma. Wannan al'amari ya fi qarfin ace sai ya nemo kwakwab gara ya barwa Allah ikonsa.
Malam ya yi tsaye yana jiran Bakura ya wanke masa Sajida tas, ya so Bakura ya turance masa ita, don ta san ba ita kadai ba ce 'yar boko. Malam ya so Bakura ya fito mata da dara-daran idanuwansa, kamar yadda yake ritsa 'yarsa Zahra, amma sai ya ga Bakura ya fice daga dakin da sauri ba tare da ya ce uffan ba.
Malam ma ya biyo shi suką fito tsakar gida Umma Furera ta fashe da kuka, ta durqusa gwiwoyinta guda biyu a qasa ta dubi Bakura.
Ta ce "Yaro, ka roqi Malam ya cirewa 'yar nan sarqa a qafa. Na dauka ma kwance ta za ku yi. Sajida ta qi ci, ta qi sha, tunda safe fa take daure."
Bakura ya ji hankalinsa ya dada tashi, ya yi sauri ya ce da Umma Furera.
"Tashi Iya, ki daina durkusa min, ni danki ne, za a kwance ta ki daina damuwa."
Ta koma ta zauna tana sharbe hawaye.
Bakura ya dubi Malam ya ce, "Baba, ka taimaka ka kwance ta, ba inda za je."
Malam ya bude baki zai yi magana Bakura ya dakatar da shi, ya ci gaba da cewa, "Ka bani wuqa, ka ba ni nama, a kan Sajida da Abdul majid."
Malam da matarsa suka yi sororo su na duban Bakura, duba na rashin fahimta. Bakura ya gyara tsayuwarsa, gami da duban qasa. Ya fada cikin wata murya mai dauke da tsananin kulawa, hade da tausayawa.
Ya ce, "Na yarda, na amince, zan aure ta, ni na fi cancanta in auri Sajida."
Malam ya ji tamkar an zuba masa wani ruwa mai sanyi a cikin zuciyarsa. Ya ji kamar an masa albishir da gidan Aljanna. Ya ji tamkar Allah Ya yi masa Albishir da aljanna, Ya gasgata Allah Ya amshi adduarsa Ya aiko masa da bawanSa dan da ya zo ya fitar da shi daga cikin wata gagarumar matsala da take so ta zama ajalinsa. Ya ji a jikinsa ya yi sallama da matsalar Sajida a duniya. Daga qarshe sai ya ji hawayen farin ciki ya fara kwarara.
Ya ce da Bakura, "Allah Ya yi maka albarka, Allah Ya tabbatar da wannan al'amari. Allah Ya sa an hada alhairi"
Umma Furera kuwa daga dukkan alamu ta shiga sarqaqiya, ta bude baki tana duban Bakura da Malam.
Can ta tambaya ta ce, "Malam wacce Sajidar ku ke magana?"
Malam ya tsuke fuska ya ce, "Sajida nawa gare mu? Ki na ganin Sama'ila zai iya da Sajida ko Abdul majid? Bakura sunansa wannan shine wanda ya kai mu Abuja muka yi masa aikin addu'a. Ya yarda ya amince zai auri Sajidą saboda ya taya mu kula da tarbiyarta."
Kafin Malam ya rufe baki, Umma Furera ta rusa kukan dadi, gami da jawo albarka iri-iri ga Bakura.
Bakura ya fice da sauri ba tare da ya ce komai ba. Malam ne ke biye da shi a baya har bakin motarsa suka yi sallama Bakura ya ja mota ya tafi.
Malam ya dawo cikin gida suka ci gaba da tattaunawa da Umma Furera, game da wannan abin farin ciki da ya same su. Malam da matarsa ne suka shiga dakin Sajida har yanzu ta qi dago da kanta, balle ta dubi masu shigowa. Malam ya tsugunna ya kwance sarkar da ya yi mata dabaibayi, ya ce da matarsa.
To ki yi mata bayani."
Ya fice ya bar su a dakin, kasancewar magruba ta qarato. Umma Furera ta matsa kusa da Sajida ta zauna gami da rungumo ta jikinta, ta dago kanta tana mai murmushi ta ce da Sajida.
"Albishirinki, aure ke da Sama'ila babu."
Wannan kalamai sun sa Sajida tattara hankalinta gaba daya ga sauraron mahaifiyarta. A wani bangare na zuciyarta kuwa, wani haske ne gami da farin ciki suka rufto mata.
Umma Furera ta ci gaba da cewa, "Bakon da ya shigo dazu ya ce shi zai tsaya miki mu ba shi wuqa, mu ba shi nama."
Sajida ta ji wani farin ciki ya lullube ta, ta zabura ta rungume mahaifyarta, ta fada cikin farin ciki.
"Mutumin ya roqi Baba ya bari in auri Abdul majid ne?"
Umma Furera ta yi 'dumm'! Can ta ce, "Ina wani sabon aminin Babanki, wanda kwanaki ya kai Babanku da su Abashe almajiri Abuja, mai arzikin nan da yake da kamfanoni, to shine ya shigo har cikin dakinki, shi ne yasa Malam ya kwance miki sarkar nan ya ce bai kamata a daure ki ba. Kuma na lure Malam ya na daukar shawararsa, duk da yaro ne ba sa'an Malam ba ne. Ga kudi, ga kyau, ga nutsuwa, mai ilimi dan boko."
Sajida ta yi ajiyar zuciya ta gyara zama ta ce, "To Umma me ya ce? Ya bawa Baba shawara ya kyale ni in auri Abdul majid ne?"
Umma Furera ta ce, "Sajida ki nutsu, kin san Abdul majid ba sonki yake ba, ba kuma aurarki zai yi ba. Amma wannan babba mutum ne ya san darajarki."
Sajida ta tsuke fuska ta ce "Ban fahimce ki ba, kamar yaya?"
Umma Furera ta yi murmushi ta shafa gefen fuskar Sajida da bayan hannunta ta ce. "Shi ya fi cancánta ya aure ki."
Sajida ta zabura ta miqe tsaye, kai ka ce cinnaka ne ya galla mata cizo, ko in ce kunama, don firgici. Ta daki wani tebur inda kayan kwalliyar da ke kan teburin suka watse kasa. Hawaye marar kakkautawa ya fara shatata daga idanuwanta.
Ta ce "WallahI ba zan aure shi ba, ko shi wanene. Haka ba zan auri Sama'ila ba, ko da kuwa za a kashe ni a gidan nan. Har a je a kirawo wani wanda ban sani ba, ban taba gani ba, a ce in aura, saboda an tsane ni."
Umma Furera ta ce, "Za ki gan shi zai zo, daga kin ganshi za ki so shi, har ya fi Abdul majid kyawun gani,"
Ho ho hoo! Tamkar Umma Furera ta zubawa zuciyar Sajida wuta, haka ta ji wani zazzafan baqin ciki. Ta kufula ta fice daga dakin ta fito tsakar gida tana huci, don takaici. Ji take tamkar ta hadiyi zuciya ta mutu, kar ta kai gobe.


*** *** ***
A bangaren Bakura kuwa, ya na isa gida sai ya tsaya a masallacin qofar gidansa ya yi sallar magruba da Isha'i, ya đaga hannu sama ya yi ta addu'a akan Allah Ubangiji Ya yi masa jagora, ya zaba masa abin da ya fi alkhairi akan wannan al'amari.
Da ya isa cikin gida, sai ya iske iyalansa kakaf a falo. Bayan ya rungume kowannansu, an yi sannu da zuwa. Sai suka wuce kai tsaye kan daning table, inda
Samira da masu dafa musu abinci suka sarrafa abincicika kala-kala. Suka ci, suka sha, kowa ya qoshi. Sannan suka raba dare suna hira, har wajen sha biyun dare. Bakura ya ce yara duk su je su kwanta.
"Good night mama. Good night Abba. Good night my lovely Daddy, good night Mum."
Sautin da kake ji yana fitowa daga bakin Zahra da qannenta kenan.
"Good night my babies." Amsar da Bakura da matarsa suka ba su kenan. Sannan suka dunguma suka wuce dakunansu.
Samira ta matso kusa da maigidanta ta dube shi cikin fara'a da murmushi ta karya murya ta ce, "My dear, ka dawo lafiya?"
Ya dube ta da gefen ido ya yi murmushi ya lankwashe murya ya ce, "Lafiya my love. "
Ta sake naniqarsa ta riqe yatsun hannunsa ta ce, "Alkawari kaya ne, ina alkawarina?"
Bakura ya ji 'rass-rass'!!! Gabansa ya yanke ya fadi. Babu yadda zai yi ya gocewa maganar a matsayinsa na babba, mai halin dattako. Amma duk da haka ya dauki lokaci mai tsawo kafin ya furta wata kalma. Can ya rufe ido, domin abin ya fi qarfin a fada ido a bude.
Ya ce, "Samira, za mu shiga wata sabuwar rayuwa, wacce ta sha bamban da irin wacce mu ke ciki a baya. Kin yi min biyayya, iya biyayya a zamanmu.Kin nuna min qauna, iyakar qauna. Amma sai yanzu da za mu shiga sabuwar rayuwar nan zan tabbatar da biyayyar da qaunar da kike yi min ta gaskiya ce.
"Sabuwar rayuwa?" Samira ta tambaya cike da mamaki.
Bakura ya bude ido ya dube ta ya yi murmushi ya gyara zama ya ce, "Sajida yarinya ce da take neman taimako, wacce rayuwarta take daf da rugurgujewa, domin ta rasa karatunta na boko da Islamiyya a sanadiyyar wani mayaudarin yaron da yake kade mata hankali. Don haka take buqatar a taimaka mata."
Samira ta sake jin wani mamaki mai kama da mafarki ya daure mata kai.
Ta ce, "Ban fahimce ka ba, Sajidar da ta fasawa 'yata kai, ka ke so mu dauko mu riqe ta a gidan nan ta ci gaba da karatu, har mu aurar da ita'? Ko kuma yaya kake nufin a yi? Abban Yagana, ka kula da irin mutanen da za ka jajibo. Duniya a yanzu ba gaskiya, ka daina la'akari da yadda zuciyarka take, ka dauka kowa haka yake. Rayuwa ta canja, ka yi wa mutum rana ne shi kuma yayi maka dare. Daga haduwa da Baban yarinya, yana koya maka karatu, shi kenan, kun zama 'yan uwa har za ka jajibo mana 'yarsa fitsararriya ta zo ta batawa namu 'ya'yan tarbiyya."
Bakura ya dakatar da ita ya ce, "Ba haka ba ne, mahaifinta ma baya so ta ci gaba da karatu, aure yake so ya yi mata."
Samira ta yi ajiyar zuciyar dadi ta ce, "Oho kayan daki yake so ka taimaka mu su da shi, ai ba komai zan dauki nauyin kayan kicin, ai sadaka ce."
Bakura ya yi shiru kansa a kasa. Can ya dago ya dubi Samira ya ce, "My wife, kin fi kowa sanin yadda Zuhuriyya take a wajena ko?"
Samria ta gyada kai ta ce "Na sani."
Ya sake cewa, "Kin fi kowa sanin irin tsananin quncin da nake ciki, tun daga ranar da Zuhuriya ta tafi ta bar ni, har zuwa yanzu ko? Kin fi kowa sanin yadda zan iya salwantar da rayuwata a wajen nemo inda Zuhuriyya take da a ce zan iya nemo ta don kawai in sake ganinta ko? Samira na san irin halaccin da ki ka yi min a rayuwata, wanda ba dan na hadu da so da qaunarki ba da ban kawo ga wannan matsayi ba. Ba ni da wacce ta fi ki, domin duk inda aka bata min rai Allah-Allah nake in dawo wajen ki, kece me kwantar min da hankali. Samira, ina so in taimaki rayuwar Sajida, saboda abu biyu."
Samira ta yi murmushin jin dadi, zuciyarta cike da annuri ta ji rabin ranta, abun qaunarta yana yabonta.
Ta gyara zama tana mai muradin ta ji abin da zai zano mata.
Bakura ya lumshe ido gami da kankame yanyatsun hannunta ya ce, "abu na farkon da yasa nake jin ba zan iya barin rayuwar Sajida ta wulakanta ba, shi ne ina da 'ya'ya, akwai mutuwa, akwai laurara, ba na fatan yau a ce babu ni 'yata Yagana ko qannenta su shiga irin rayuwar da Sajida take shirin fadawa. Ni Musulmi ne, Sajida Musulma ce, ya cancanci in taimaka mata."
Samira ta gyada kai ta ce, "Haka ne my dear. Allah zai taimaki duk wani mai taimakon jama'a. Bayanka zai yi kyau, da izinin Ubangiji."
Bakura ya ci gaba da cewa, "Sai abu na biyu kamar yadda na fada miki a baya, Sajida ta yi kama da Zuhuriyya, tamkar kafar hagu da dama, tamkar an baskara goro gida biyu. Tun da nake ganin tagwayen da ake haifa tare su yi kama daya, ban taba ganin irin wannan kamar ta Sajida da Zuhuriyya ba. Na rasa Zuhuriyya, na hadu da Sajida, bana jin zuciyata za ta iya barin Sajida ta kauracewa idanuwana, ma'ana in daina ganinta a doron qasa ba, ba na so ta yi nesa da ni."
Wannan karon Samira ta ji kirjinta ya buga,bamm'!! Kamar an buga ganga.
Ta zare ido ta ce,
"Kamar yaya, ban gane ba?"
Bakura ya sunkuyar da kai kasa ya ce,
"Ni ne kadai na cancanci in auri Sajida. Har na amsawa mahaifanta."
Kamar wani garwashin wuta, haka Samira ta warbar da hannun Bakura daga hannunta, ta zabura ta miqe tsaye. Yayin da gaba daya gidan ya fara jujjuya mata, ji take tamkar kanta ya koma kasa, qafafuwanta ne a sama. Ta rasa gabas, ta rasa kudu. Ta ji kwakwalwarta ta rude, ta kasa tuno duk wani abin da ya taba faruwa a rayuwarta, wato ta yi (loosing memory).
Bakura ya taso yana qoqarin ya riqe ta, sai ta daka tsalle gefe tana ja da baya.
Fadi take. "Kar ka taba ni, kar ka qaraso inda nake, ba na son ganinka."
Bakura cike da mamaki ya ce, "Samira, nine fa. Ni kike cewa ba kya son ganina?"
Daga yadda ya ga idanuwanta na wurwurgawa daga inda ya tabbatar Samira ba ta cikin hayyacinta.
Bin ta yake yana lallashi, ita kuwa sai ja da baya take, daga qarshe ma ta bude qofa ta fice waje da gudu.
Bakura ya bi ta a guje suka dinga tsere a farfajiyar gidan, ba tare da masu gadi sun san abin da yake faruwa ba. Bakura ya yi ta maza, ya damkota ta na fisgewa tana fadin ita ya bar ta ta fice ta tafi ko'ina ne ma a rasa ta da ta ci gaba da zama da shi.
Ya kankame ta tsam a kirjinsa babu kalmar da take fitowa daga bakinsa sai "I'm really sorry my dear, I love you my love."
Kalaman maigidanta sun zame mata tamkar zuma a zuciyarta, sun zame mata tamkar ana hura sarewa a kunnuwanta, don haka ta ji ta kasa fisgewa saga jikinsa. Sai ta fashe da kuka, mai tafe da hawayen kunar zuci.
Hankalin Bakura ya tashi matuqa, idan ya duba hawayen Samira sai ya tuno hawayen Sajida, sai ya tuno hawayen Zuhuriyya, sai ya ji zuciyarsa tamkar an diga darmar wuta, ma'ana hawayensu dafi ne a ransa.
Ya fada a bayyane "Hawayenku tamkar dafi ne a cikin zuciyata. Ku yi hakuri zan mayar da kukanku dariya, in Allah Ya yarda."
Da kyar da sudin goshi Bakura ya lallashi Samira ta yarda suka shiga dakinsa suka kwanta, yadda ta kwana bata runtsa ba, haka ya kwana bai runtsa ba.
Kuka take, shi kuwa

Kwanakin Bakura uku a cikin gida baya fita ko qofar gida, yana nan yana gadin Samira. Ta tubure, ita sai ta fita an neme ta an rasa. Bakura ya damu, ya rasa yadda zai yi ya shawo kan wannan matsalar, daga qarshe ya buga waya ya sanarwa da babbar yayar Samira, mai suna Hajja Farida, da ke zaune da maigidanta a unguwar Janbulo. Ko awa guda ba ta yi ba ta diro cikin gidan su Bakura. Aka zauna ga Samira, ga Bakura, ga Hajjiya Farida aka mayar da magana. A tunanin Samira yayarta za ta bi bayanta, sai ta ji yayar ta bi bayan Bakura, har take yi mata fada cewar shashanci ne wannan. Ta nuna mata qara aure ga namiji ba wani abu ba ne, domin ita ma kishiyoyinta biyu, ita ce ta uku, kuma ita ce uwargida. Da yake 'yar kasuwa ce qasashe take zuwa tana kawo kaya, sai ta ce da Bakura ya ba ta kwangila ma ta hado masa lefen amarya da uwargida.
Cikin farin ciki Bakura ya amsa mata cewa. "ki yi min lissafin duk abinda ya kamata a saya musu, zan zo har gida mu zauna."
Wani kullutun bakin ciki ne ya kakare a wuyan Samira a halin yanzu ta fi jin haushin yayarta Hajjiya Farida a kan Bakura ma. Bakura ya yi wa Farida sallama ya dauki mukullin motarsa ya fice don ya ba su waje, ya san Farida za ta taimaka masa wajen bawa matarsa shawara mai kyau, dadin dadawa kuma Samira na matuqar jin tsoron Hajja Farida, kasancewar ita ce babba a dakinsu, ga ta mafadaciya ce, kuma mai kudi ce.
Bakura ya bude mota ya shiga ya zauna kenan, kafin ya jawo qofa ya rufe sai ya ji muryar Zahra. Ya yi sauri ya waiga, sai ya ga Zahra a durqushe jikinta a sanyaye kamar marar lafiya.
Cikin harshen turanci take magana ta fara da tambaya. Ta ce, "Abba, me yake faruwa ne tsakaninka da Mamanmu kwana biyu take kuka?"
Bakura ya rasa amsar da zai ba ta. Kafin ya gama kame-kamensa Zahra ta qara da cewa.
"Yanzu kuma da Hajjiya Farida ta zo Abubakar ya ce min yaji ana cewa za ka qara aure. Haka ne?"
Bakura ya gyada kai cikin sanyin jiki ya ce, "Haka ne Mamana."
Hawaye ya cika mata ido, sai ta yunqura ta miqe ta ce "Allah ya sanya alkhairi,"
Bakura ya ce da ita, "Zo nan, kin san wacce zan aura ne?"
Zahra ta girgiza kai alamar a'a.
Ya ce, "Yagana, ki yi hakuri da abinda zan fada miki, na san ba zai yi miki dadi ba. Kada ki girgiza, kada ki ga laifina ina da dalilin yin haka, wanda ba za ki gane ba sai nan gaba."
Zahra ta sharbe hawaye ta girgiza kai ta ce, "Ba zan damu ba Abba kowace ce.
Ya yi

Please Login or Register in order to submit comment