Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

quater su taso Lurwanu direba ya zo ya kai su asibiti wajen Bakura. Da gudu Zahra da qaninta suka nufi Boy's quater suka taso shi, a gigice ya dauko mukullin mota ya fito. Ba tare da bata lokaci ba Samira da 'ya'yanta suka duru a mota suka nufi asibiti, sai addu'a suke su na koke-koke a hanya.
Sajida na shiga falonta ta jawo wayarta ta bugawa Abdul majid, zuciyarta cike da 6acin rai, domin tana zargin da sa hannunsa a cikin wannan al'amari,
Ya na amsawa ta harbo masa wannan tambaya. "Abdul majid me kasa a yiwa Bakura?"
Ya tabe baki ýa ce "Me ki ka ga an yi masa, wannan wacce irin tambaya ce kike yi min? Kar ki raina min hankali mana."
Ta fada cikin tsawa da bacin rai, "An ce 'yan fashi sun tare shi sun dake shi, har sun fasa masa mota. Ina tunanin kai ne kasa a yi masa haka."
Ya ce, "Ki daina tunanin nasa an dake shi, nine da hannuna na tare shi ni da su Shehu abokaina muka farfasa masa kai dazu da magruba a Hotoro G.R.A. Kin fara sonsa ne, ina ruwanki ko mutuwa ya yi?"
Ta fada a fusace, "Ka ga Abdul majid ba na son haka, ya za ka nemi ka kashe mutum ba da hakkinsa ba. Me ya yi maka? Mutumin nan ya ba mu damar mu yi magana har ma katin waya yake siya ya ba ni in kira ka. Me ye laifinsa?" firgitarwa.
Kai ka fi cancanta

Paid book 300
0023843938
Unity bank
Jamila umar tanko

0803719670i

Ya fusata ya ce "To ki je police station ki yi qarana da kan ki kafin ya warke ya sa a nemo mu, don na fada masa ko mu su waye, kuma na haska masa fuskata tangararai ya ganni, kuma zai shaida ni. Tunda kina sonsa kada ki qara kirana a waya."
Ya yi tsaki ya kashe wayar, Sajida ta dade zaune tana ta tunani tana zullumin abinda zai je ya dawo.
Hakika har cikin ranta ba ta ji dadin abinda Abdulmajid da abokansa suka aikatawa Bakura ba. Don haka babu irin kiran da Abdul majid bai yi mata ba a cikin daren nan Sajida ta qi amşa wayarsa, daga qarshe ma ta kashe wayar gaba dạya ta yi kwanciyarta. Tana jiyo motsin dawowar su Samira har da Bakura, amma ko leqowa qofar dakinta ba ta yi ba, balle ta yi masa sannu. Haka washe gari Bakura ko falo bai fito ba, yana dakinsa a kwance ya hana Samira ta fadawa kowa cewar bashi da lafiya, don haka masu aiki ma ba dukkansu ba ne suka san Bakura na kwance ba lafiya ba.
Wannan al'amari na Sajida ya yi matukar batawa Samira da 'ya'yanta rai, sai shige da fice take tsakanin dakinta, falo zuwa kicin tana nuna halin ko in kula bai dame ni ba. Rashin lafiyarsa ku ta dama ba ni ba.
A fusace Samira ta zo shiga kicin yayin da a fusace Sajida ta zo fitowa daga kicin suka bangaji juna a bakin qofar kicin, Sajida dauke take da qatan kwalin juice da kofi a hannunta.
Samira ta ce, "Mutum ko dabba ne ai ya san mai ba shi abinci, don haka baya samun sukuni idan ya ga kwana biyu bai ga mutumin nan ba. Ma'ana shi mai ciyar da ke, mai tufatar da ke, mai siyo wannan juice din da ki ke yini kina sha, ba shi da lafiya a ce ko Sannu, yaya mai jiki baki iya ba. Duk rashin tarbiyyarki ai kya tausayawa rai, saboda idan mutumin nan ya fadi ya mutu, sai dai fa ki koma gargajiya zancen juice ya kare."
Sajida ta yi wurgi da kwalin juice din hannunta, gami da rada kofin tangaran a qasa ya ragargaje.
Samira ta ce "Dole ki fasa min kofi, saboda ba ku taba sanin yadda ake siyan kayan gado ba balle kayan kicin."
Sajida ta fusata ta cakumi kwalar Samira. Ta ce, "Ke dakata kada ki fada min magapar banza akan wani banzan mijinki. Bakura har mutum ne da zan yi kishi a kansa? Ko an ce miki na zo da niyyar aure har da-zan shigo da kayan daki, shi ya ce ya ji ya gani, shi ya maqale ya nace ya raba ni da wanda nake qauna, ya kawo ni gidansa ba dan ina qaunarsa daidai da kwayar zarra ba."
"Sakar min kwalar riga kafin in wanka miki mari." In ji Samira.
Zahra ta fito daga dakinta da gudu, don ta jiyo hayaniya, haka qannenta suka fito daga falo a guje, don su ganewa idanuwansu abinda ke faruwa. Cikin fushi Zahra ta zo ta fusge hannun Sajida daga wuyan mahaifiyarta ta daki kirjin Sajida da hannayenta biyu ta shiga tsakanin Samira da Sajida.
Ta ce, "Mama koma daki ki zauna ki bar ni da ita, ni ce sa'arta ba ke ba."
Mamaki ya hana Sajida magana, har murmushi take na hamdala daman tana neman irin wannan rana da za su gwabzu da Zahra, saboda haushinta da take ji tuntuni.
Zahra ta ce, "Sajida yau ne rana ta farko da zan yi fada a rayuwata, yau ce rana ta farko da zan tabbatarwa mahaifiyata ta iya haihuwa ba ta sha wuyar banza ba. Yau ita ce rana ta farko da zan nuna miki ba na tsoronki, shiru-shiru ba tsoro ba ne. Ke ba ajina ba ce, domin halinki irin na 'yan matan da ba su taba zuwa makaranta ba ne sai talla a titi. Ba ki da tarbiyya, ba ki sami tarbiyya ba a matsayinki na 'ya mace. Ba kya jin maganar iyayenki, hakan ne ya jawo miki yin aure da wuri maimakon karatu. Kin amsa sunanki na kwaryar tsakar gida mai gagari, ke ba kwarya ta gari ba ce, wacce aka saqale a ragaya don yin ado da ita ba."
Wannan kalamai na Zahra ya yi matukar burge Samira, Zahra ta ba ta mamakin yadda wadannan kalamai suka fito daga bakinta. Yayin da ita kuma Sajida ta qufula, ta fusata, ta sake tabbatarwa wannan kalmar mahaifinta ce, don haka bakinsu daya komai a shirye suka hada mata don su raba ta da Abdul majid .
A fusacc Sajida ta kaiwa Zahra mari, Zahra ta riki hannun Sajida, yayin da ita ta kai mata mari har sai Sajida ta ga hasken wuta.
Zahra ta ce, "A da kin fasa min kai, kin ji dadi, kar ki sake tunanin za ki iya cin galaba a kaina kuma.
Sai dambe ya hautsine tsakanin Zahra da Sajida, Abubakar, da Umar sai suka shiga fadan, qafar Sajida kawai suka kwaso sai ga ta a qasa, yayin da suka hau ciccibarta wai za su fitar da ita daga gidansu. Samira ta ga abin yana kokarin lalacewa sai ta shiga rabiya tana jan 'ya'yanta tana cewa, "Ku sake ta, ku kyale ta haka."
Duk wannan abu da ake Bakura na jiyo hayaniya
daga dakinsa, tun yana zaune yana kwalla kiran Samira, har ya daure ya sauko daga kan gado yana dingishi ya fito, ga tsananin ciwon da kansa yake yi masa saboda raunin da ke gefen idonsa ya kumbura ya aune.
Ya na fitowa ya ji hankalinsa ya tashi, ganin yadda 'ya'yansa ke cali-cali da Sajida a qasa. Ya rafsa ihu, kai ka ce bindiga aka burma masa ya danno da gudu yana kurma salati, har da tuntu6e saura kiris ya fadi qasa.
"Me zan gani? Samira me ki ke nufi da za ki sa 'ya'yanki su daki matata? ku sake ta kafin in kakkarya ku."
Su ka watse gaba dayansu suka gudu gefe sai huci suke.
Ya taho da sauri ya tashi Sajida tsaye yana karkade mata jiki, fadi yake, Yi hakuri Sajida, kwantar da hankalinki zan rama miki."
Ta rushe da kuka ta fizge jikinta daga gare shi ta ce, "Wallahi zamana ya qare a gidan nan yau, ko awa daya ba zan qara ba tafiya zan yi. Zahra sai na nuna nıiki ko ni wacece, sai kin gwammace baki dora hannunki a kaina ba."
Bakura ya juya ya dubi Samira da 'ya'yanta ya ce "Ki shirya ke da 'ya'yanki ku bar min gidana."
Gaba daya suka bude baki don mamaki ko a mafarki ba su zata akwai ranar da Bakura zai iya furta wannan kalma ba komai girman laifin da suka yi masa ba, balle a kan Sajida.
Sajida ta yi murmushi ta goge hawaye ta kalle su sama da kasa ta ce "A qara gaba ko, ni dai kun ga shiga ta daki, kada ku yi addu'ar inyi arangamata da ku a kashi na biyu dan haduwata da ku ba zatayi kyau ba."
Ta shige dakinta ta datse. Zahra cikin kuka ta ce "Abba, yanzu akan Sajida za ka kore mu? A kan matarka za ka rabu da uwar 'ya'yanka?"
Samira ta dakawa Zahra tsawa ta ce, "Ki rufe min baki, don me za ki dinga roqarsa? Ki bar shi ya zauna da Sajida. Kowannenku ya je ya dauko kayansa ku zo mu tafi ba za mu kwana a titi ba, Allah yasa ina da iyaye da gatana."
Yara har murna suke suka shiga dakunansu su na hada kaya. Haka Samira ta wuce zuwa dakinta da sauri har karkarwa take tana hado kayanta. Zahra ce ke shar6ar kuka tana tafiya tamkar babu laka a jikinta ta wuce zuwa dakinta, ta fara hada kayanta.
Bakura ya dora hannu aka kira yake, "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un."
Ya fice da sauri wajen masu gadi ya ce su daddatse kowacce qofa da mukulli, su ba shi 'yan mukullan, yau ba shiga ba fita duk wanda ya zo kar a bude masa, haka duk wanda zai fita kada a bude masa Ya zuba mukullai a aljihu ya shiga gida. Ya ci karo da su kowannensu yana jan akwatuna riki-riki.
Ya dakawa yara tsawa "Ku koma da kayan nan ciki kada in ga qafar wani a waje!"
Usman dan auta ya ce "Abba kai fa ka ce mu tafi mu mun fi so mu tafi."
Umar ya ce "Tunda Aunty Sajida ta zo gidan ba dadi, gara mu koma Yakasai mu zauna mu bar mata gidan."
Abubakar ya ce "Gaskiya Abba mu tafiya za mu yi, tunda ka ce mu tafi."
A fusace Bakura ya yo kansu kamar zai dake shi yana fadin, "Ku kwashi kayan nan ku koma da su daki."
Jikinsu na rawa suka dinga juyawa da akwatinansu ciki gida. Zahra ba ta ce uffan ba ta ja akwatinta ta nufi dakinta sai sharbar kuka take.
Samira ta ci gaba da jan tata akwatin ta nufi kofar fita fadi take, "Idan ka hana 'yaranka tafiya daman ba da su na zo ba. Ni kuwa babu abinda zai sa in qara sakon daya a cikin gidan nan. Na tafi na tafi kenan ba zan dawo ba."
Bakura ya rike akwatin gam yana ja tana ja.
Samira ta ce "Ka sakar min akwatina tafiya zan yi. Zamana da kai ya qare."
Ya durkusa gwiwoyinsa guda biyu a qasa yana mai tsananin nuna nadama da bada hakuri.
VYa amsa da bakinsa, "Na yi kuskure da na furta wannan kalma, na yi dana sani dana yanke hukunci cikin fushi. Ki rufa min asiri kada ki fita da kayanki, saboda masu aiki da masu gadi za su ganki. Ko da kin je get ba su da mukullan da za su bude miki get ga mukullan a aljihuna. Samira, ba zan iya rabuwa da ke ba, kin zama ni, na zama ke. Ranar rabuwarmu sai ranar da aka saka min likkafani aka kai ni kabarina aka binne, ko ranar da aka saka miki likkafani aka kai ki kabari aka binne. Babu yadda za a yi daya ya bi daya kabarinsa, saboda Allah bai halatta mana yin hakan ba da ba za mu rabu ba. Ki yafe min, na yi kuskure. "
Hawayen Bakura shi ya sa Samira rushewa da kuka ta taho da sauri ta rungume shi, su duka kuka suke yi.
"Kanka da zafi da alama ciwo yake. Mu je daki ka sha magani, ka kwanta." Samira ta ce da Balkura.
Allahu Akbar! Soyayya saboda Allah ba karya ba ce. Ina masoyan zamani?
Washe gari Sajida ta bude ido ta ga su Samira daram a zaune a gida suna ta hidindimunsu kamar kullum. Haushi ya rufe ta ta sake tsanar Bakura. Idan zai kwana yana yi mata magana ko kallonsa ba ta yi. Haka ta dinga takale-takalen masifa a cikin gidan nan babu mai kula ta, kasancewar Bakura ya ja musu kunne kar su kara sauraronta duk abinda za ta yi a zuba mata ido.
Ta bangaji wannan, ta harari wancan, ta yi tsaki ta tsartar da yawu, babu wanda ya damu da ita. Har tsawon sati biyu Bakura na jinya ko sannu ba ta hada shi da Sajida ba.
Ya warke ras ya ci gaba da harkokinsa bai taba cewa kowa ga abinda ya same shi ,ba, ko Sajida da Samira bai fada musu cewar ya san wadanda suka yi masa wannan ta'addancin ba. Haka Malam Yakubu ya yi ta bugowa Bakura waya yana tambayarsa lafiya kwana biyu bai ganshi ba, Bakura ya fake da cewa baya gari ya yi tafiya.Koda yaushe Malam na tambayar Bakura yanayin zamansa da Sajida, Bakura yana nunawa Malam ai yanzu Sajida ta yi laushi lafiya kalau suke zaune. Bai taba fadawa Malam halin da suke ciki ba, don haka hankalin Malam da matarsa a kwance. Ba su san Sajida na da waya ba, don haka har tsawon watannin nan uku ba su yi magana da Sajida ba, kuma ba su zo sun ganta ba. Malam ya hana kowacce qawa ta tako gidan Sajida ba, ko danginsu ma ya hana su zo. Ya ce abar ta sai ta shekara ta cire duk wani baqin rai, sannan a je a ganta sannan ita ma ta zo a gaisa.
Yamma sakaliya Bakura ya dira a kofar gidan Malam. Malam ya yi marhaba da ganin Bakura, domin sun dade ba su hadu ba. Bayan an dau karatu, an yi sallar Magriba jama'a sun watse sai Bakura da Malam ne suke hira.
Can Malam ya ce, "Af, na manta ban fada maka ba, Baquwa muka yi daga nesa kuwa take. Wata kakar Sajida ce, wacce ba su taba ganin juna ba tunda suke a duniya.Ta niko gari tun daga Gashuwa ta zo ganin Sajida ta sami labarin auren ta, duk da bata samu ta zo ba amma an kai mata kayan biki da atamfar da aka rarrabawa kakanni da iyaye, daga cikin atamfofin da ka ce a rabawa dangi sai yanzu ta sami damar zuwa."
Bakura ya gyara zama, gami da cewa, "Allah sarki, tun daga Gashuwa ta zo ba ta samu ta zo bikin ba kenan?"
Malam ya ce, "Ai ta tsufa ga ciwon qafa, shi yasa ba ta zo ba."
Bakura ya ce, "Amma na ji ka ce ba su taba ganin Juna ita da Sajida ba. Baku ta6a tunanin kai ta ba duk tsawon shekarun nan? Ko dangantakar da nisa ne?"
Malam ya ce "Wallahi dangantakar ta kusa ce, jini daya. Ka san kowa da halinsa, Furera wata irin mata ce ba ta da zumunci sosai, ba ta mayar da kai ta kaita Gashuwa ba."
Bakura ya ce "Kakarta ta wajen dangin uwa kenan?"
Malam ya ce "Kwarai, ta bangaren Furera suka hadu."
Bakura ya ce "Idan na je wa zance mata sunanta, ko yanzu zan tafi da ita can su kwana su na hira?"
Malam ya ce "Gobe da safe dai za su taho ita da Furera, don a yi mata bayani tunda ba ta san ta ba. Idan na fada mata sunanta ba za ta gane ba, amma ka ce mata kakarta Iya Azumi ta zo daga Gashuwa za ta zo gobe su gaisa."
Bakura ya ce "Insha Allah zan fada mata, Allah ya kai mu goben, ni ma za su same ni a gidan, don ba na fita da wuri har sai wajen sha biyun rana nake fita."
A haka Bakura suka yi sallama da Malam ya shiga motarsa ya tafi gida. A masallacin qofar gidansa ya jima yana tattaunawa da liman akan abinda masallaci yake buqata, sannan ya shiga gida. Bayan ya yi wanka ya ci abinci, sai ya tura qofar dakin Sajida ya shiga da yake yau ita ce da kwana, Samira tuni ta shige dakinta ta rufe. Kamar kullum, kamar yadda suka saba sai dai Bakura ya shiga dakinta, iyakacinsa kan kujera ya tsura mata ido yana kallonta, ita kuwa tana ganinsa sai ta danno lambar Abdulmajid dinta don ta ba shi haushi. Da alama ba ya jin haushin don har yau bai taba bata rai idan tana waya ba. Bai kuma daina kara mata recharg card ba, idan kudin wayarsu ya qare.
Sajida ce a kwance a kan gado, ba tare da ta ji motsin shigowa ba ta ga Bakura a tsaye a kanta.
Ta fada cikin tsiwa, "Malam ya aka yi ne ka shigo min har cikin daki ba izini, lafiya?"
Ya yi murmushi ya ce, "Lafiya ranki ya dade, sako na zo in isar miki."
Ta maimaita "Saqo, wanne iri?"
Ya ce "Baba ya ce in sanar miki gobe da safe Umma Furera da wata kakarki its Azumi daga Gashuwa ta zo za su zo su ganki."
Ta tabe baki ta ce "Duk danginmu babu Azumi, haka ba mu da dangi a Gashuwa, ka (tuno dai wajen wacçe aka ba ka sako, amma ba ni ba."
Bakura yana niyyar magana sai Sajida ta jawo wayarta ta matso sunan Abdulmajid ta kashe murya ta ce, "Hello darling, ka kwanta ne?"
Bakura ya juya ya fice ba tare da ya jira amsar da zai bata ba. Ya tabbatar korarsa take so ta yi, don ba ta Son ganinsa.
Ya wuce dakinsa ya kwanta yana juyi a gado ya rasa yadda aka yi rayuwa ta zame masa haka. Don haka yau bai ga ta zama ba, alwala ya dauro ya dauko jarbi mai dubu ya fara kiyamullaili yana tasbihi yana roqo, ya na hawaye a gaban Ubangiji da Ya yaye masa duk wata damuwa, hargitsi da sarkakiyar da take a tsakanin shi da Sajdia. Domin Sajida ta zame masa tamkar qadangaren bakin tulu, idan ya jefe shi ya fasa tulun, ko ya fada ruwa, ruwan ya lalace. Haka ya kai Asuba bai rintsa ba har sai da ya yi sallar Asuba ya je ya tashi iyalansa sallah, sannan ya dawo ya kwanta. Barci mai dadi ne ya sure shi mai hade da kyawawan mafarkai.
Abun mamaki sai ya yi mafarkin Sajida da Zuhuriyya su na tare. Wannan mafarki ya bawa Bakura mamaki matuka, tun daga cikin barci har ya bude ido yana mamaki. Samira ya gani a tsaye akansa,ya sake gwale ido don ya tabbatar ita din ce kuwa?
Kai ka fi cancanta

Paid book 300
0023843938
Unity bank
Jamila umar tanko

08037196708

Ta yi murmushi ta ce "Wanne irin barci ka ke yi yau tunda safe. ka san qarfe nawa ne yanzu? Qarfe daya saura har yara şun kusa tasowa daga makaranta kuma kun yi baqi ina jin mahaifiyar Sajida ce da kakarta. Sau biyu babar Sajida na leqowa kicin tana tambayata ba ka tashi ba ne. To kar su ga ko ni ce ba na so ku gaisa, gara ka je ka gaishe su sannan kai ma ka ci abinci."
Bakura ya murje ido ya ce "Ki je zan yi wanka yanzu zan fito."
Ta na fita ya miqe ya shiga bandaki ya yi wanka, gami da dauro alwalar Azahar. Tunda rana ta yi zafi ba shi da niyyar fita sai da yamma, amma jin surukansa sun zo sai ya saka manyan kaya. Rigar shadda ce koriya tazarce da wando ya dauko hula ya dora, sannan ya fito.
A nutse ya wuce falo, don cin abincin safe.
Samira ya iske a zaune a falon tana ganinsa ta tambaya. "Ka je kun gaisa da bakin?"
Ya ce "So na ke in ci abinci yunwa nake ji, ko so kike in je gaban surukai yunwa ta buge ni in kwanta?
Samria ta kwashe da dariya ta ce, "Allah ya kiyaye ma, ci abincin tukunna sai ka je ku gaisa. Ba na so dai su qara leqowa su tambaya."
Bayan

Please Login or Register in order to submit comment