Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana ratsa hudojin jikinta. Ba ta ankara ba sai ta ji wata muguwar girgiza a qarqashin filonta, a tunaninta garin ne gaba daya yake girgiza. Ta tashi zaune gami da daga filon da sauri ta son ta ga abin da ke ciki ashe wayarta ce ta manta ba ta kashe ba, ashe wayar a ta vibration take. Ta yi wata ajiyar zuciya domin tuni numfashinta ya qauracewa huhunta, saboda tsorata. Ta miqa hannu ta dauki wayar ta duba sunan Hassana Ummi Sulaiman ne ya fito dara-dara. Ta yi mumushi gami da farin cikin jin kira daga kawarta, aminiyarta, makarantarsu ta boko wato PRIME COLLAGE, haka Islamiyyarsu daya Hassan Gwarzo islamiyya dake Sulaimanu Cresent. Ta fada cikin tsokana. Ummi 'yar autar Mama ya kike? Ya gari? Ya aka yi kika kai goma da rabi baki kwanta ba, don na ji hayaniyar Nura, Sulaima da Faruk?"
Ummi ta yi dariya ta ce, "albishir na kira in miki. Ashe gobe mid-term break ne babu makaranta har muke damun kanmu da karatun test mun manta, sai yanzu Khadija Rabi'u Gumel ta kira ta tuna min."
Zahra ta kama kai ta tsuke fuska ta ce, "Oh God! na manta, amma ban ji dadi ba wallahi na karantu sosai. Don dazu bayan na dawo gida daga makaranta da yake babu Islamiyya, Na kira Abbana a waya ya zo ya kaini Kano State Library mu ka yi ta karatu da shi. Ya sake koya min Physics sosai sai qarfe shida muka dawo gida. Shi ma ya manta gobe ba makaranta yanzu ya gama cewa in zo in kwanta, saboda gobe in tashi da wuri. To bari in bar wayana a kunne idan Mama ta tashe ni da Asuba, in ce mata ta yi kwanciyarta gobe hutu ne. Thank you very much Hassana Ummi kin taimaka da kika tuna min. Ki gaida gaida su Mama dan Allah."
Hassana Ummi ta ce "Za su ji insha Allah. Good night partiner."
Su ka kashe waya a lokaci guda, Zahra ta mayar da waya qarqashin filo ta kwanta tana tunano hirar da suka yi da kawarta wacce koda yaushe Su na tare a wani 6angaren kuma rashi yin makarantar taimaka mata aka yi da aka fasa yin test din saboda yau ta karantu idanuwanta har ja suka yi saboda barci. Ai ko ba komai ta san za ta bar
kwakwalwarta ta huta, kafin ranar jarabawar.
Sai ta ji wayarta ta sake daukar qara wannan karon mamaki ne ya rufe Zahra. Sai ta ce a ranta, "Na san Sadiya Idris ce ko Bilkisu Hamisu za su fada min gobe ba makaranta, ba su san Hassana Ummi ta riga su ba."
Tana duba wayar, sai ta ga lamba ce ba suna, don haka ba su ba ne, amma zai yiwu su din ne ko wayarsu ba kudi suka yi amfani da ta 'yan gidansu. Kamar yadda a da kafin a hada mata waya take amfani da wayar Mamarta wajen kiransu. Ta danna wayar cikin farin ciki gami da cewa. To Hassana Ummi ta riga ku, na sani gobe mid-term break babu makaranta, don haka babu test."
Sai ta ji an yi wani lallausan murmushi an ce, "Hello, dan Allah Zahra ce akan layi?"
Gabanta ya yanke ya fadi ragagagasss!!!! Domin muryar namiji ce. Tunanin da ya fado mata shi ne, to tunda ba Babanta ba ne yake kira tabbas Baban daya daga cikin kawayenta ne. Abin da ta dauka wata kawarta ce marar waya ta roqi Babanta ya kira mata qawarta shi ne ta ji muryar namiji. Nan da nan Zahra , ta gyara zama ta duka ta gaishe shi cikin ladabi. Ta cigaba da sauraron abin da zai fada mata. Ya na magana cikin sanyayyar murya, nutsatstsiya. Ko wanene wannan mai maganar hakika ya san darajar bil'adama. Tunanin Zahra sai ya fara banbanta da manufar wannan mai wayar, ma'ana ba ta ji ya ce ma ta ga kawarta ba wance. Bayani kawai yake yi mata akan ya yi matukar farin ciki da jin muryarta.
Ta gigice yayin da hankalinta gaba daya ya tashi. Ta tambaya cikin wata hardaddiyar murya mai rawar disko, saboda gigicewa.
Ta ce, "Malam ko ka yi kuskure ne ka bugo ba ni Zahrar ka ke nema ba?"
Ya yi murmushi mai fitar da sigar muradi ya ce, "Ban yi kuskure ba, ke Zahra nake nema, domin lambarki ko daga barci aka tashe ni zan kawo ta."
Saboda tsabar firgicewa sai tasa hannu ta katse wayar jikinta ya dau karkarwa tamkar mai jin sanyi.Matukar mamaki ya rufe ta. Ta ina wannan mutumin ya sami lambarta? Me yasa ya kira ta'? Me yake nema a wajen ta'? Babu amsar wadannan tambayoyi na ta.Tana cikin wannan hali sai kuwa ta ji wayarta na girgiza ta sura da sauri ta duba lambar dazu ce, don haka sai ta ki dauka yayin da kuka ya fara rufto mata, tsoro ya addabi zuciyarta ta rasa abin da yake yi mata dadi. A zaune take akan gado ta yi quri, domin
kwanciya ta gagari hakarkarinta. Mutumin nan dai bai hakura ba, kira yake sake yi tsakaninsa da Allah. Ta miqa hannu ta danna kai ka ce kashi ne a jikin wayar yadda take kyamar wayar. Ba tare da ta bari ya yi magana ba ta fada cikin kuka da rawar murya.
"Malam waye kai? Me kake nema a wajena?"
Ya yi murmushi ya fada cikin lallausar murya ya ce "Zahra cool do down my dear, Za ki ji ko ni waye, kuma da kuma dalilin da yasa na bugo miki."
Ya yi ajiyar zuciya mai hade da murmushi ya ce "Na san baki sanni ba, kuma za ki yi mamaki da na kira ki, actullaly my name Is Abdulmajid El-Museh ina kira daga Bampai quaters."
Zahra ta maimaita sunan, "Abdulmajid El-Museh ban sanka ba, ban taba jin sunan nan ba."
Ya yi dariya, "Allah sarki daman na san ba za ki sanni ba. Sai dai ina fatan ki san ni nan gaba,"
Zahra ta fada cikin fushi, gami da daga murya, "Me yasa ka kira ni, me kake nema?"
Ya sake lanqwasa murya ya ce, "Haba baby me yasa kike tayar da hankalinki, ko ban ganki ba daga ji muryarki na san kina da kyau. Ba'a son mace me kyau ta dinga wahala cool down."
Zahra ta ji wani dacin takaici yana qokarin shaqe mata wuya, sai wani hawaye mai dumi ne ya ke zubo mata. Hankalinta gaba daya ya tashi, abin da take ji wai-wai-wai a gari ya iso gare ta.
Ya katse mata tunaninta ya ci gaba da cewa, Zahra gaskiya abin da ke tafe da ni alkhairi ne, babu komai a ciki sai tsananin so da qauna. Kin fahimce ni ko? I love u so much Zahra."
Yayin da Zahra ta dafe qirji, domin ta ji wani abu daga cikin kirjinta ya na zillo zai fado qasa, don a fargaba. Ba tare da ta iya cewa komai ba, ta katse wayar. Daga nan ta tabbata lallai wannan bawan Allah ya dauko hanyar da zai rugurguza Zaman lafiya a gidan nan. Ba ita kadai ba har mahaifiyarta kashinta ya bushe daga lokacin da mahaifinta ya san abin da yake faruwa. Kuma nan da nan Bakura Zai Iya ganewa saboda duk sanda za ta tafi makaranta ya kan karbi wayar ya riqe har sai ta dawo sannan zai ba ta. Haka
kuma duk bayan wata yana karbar wayarta data mahaifiyarta ya fita da ita ya sako musu credit. Ya na yawan bincike wayar har wani lokaci ya yi game. Bakura yana yawan ja mata kunne cewar ta kiyaye kada ta sake ta kira saurayi ko wani ya kirata. Ya hada mata waya don ya dinga tashinta da Asuba ko idan ta fita unguwa a kira aji in ta isa lafiya, sai kuma don ta dinga hira da kawayenta mata.
Kuka mai yawa ya karu. Ta fito falonta ta zauna
a kan kujera yayin da ta dora kafafunta biyu akan kujera tasa hannayenta biyu ta matse kafafuwanta tana mai karanto, "Inna illlahi wa'inna ilaihir raji'un."
Wayarta ce a gefenta ta sake daukar ruri, ma'ana waya na shigowa. Ta juya fuskarta a hankali tana duban wayar, saboda tsabar tashin hankali, lambar Abdul majid ce ke shigowa don haka sai ta qi amsawa.
Matukar mamaki ya rufe zuciyarta, ta na tunanowa a duniya a ina ma ta ta6a jin mai su Abdulmajid. Don ita ba ta taba hulda ko a danginta na wajen uwa da ba kacokan babu mai irin wannan suna Abdulmajid, sai kira yake tun karfi. Ya kira ta yi ringing har ta gama Zahra ta qi ta amsa. Sai ta ji massage ya shigo. Cikin rawar hannu ta dauki wayar ta bude sakon, ta ga dai har yanzu Abdul majid ne abin da ya rubuta kuwa shi ne kamar haka:
Hi sweety, answer my calls. I will explain pls. Ma'ana ya abar zazzaqar kauna ki amsa wayata žan yi miki bayani."
Firgita kan firgicewa yayin da ta kwatanto a zuciyarta ace mahaifinta ne ya bude sakon nan wayar na hannunsa, ya ya za ta yi ai na lahira sai ya fita jin dadi in ji Bahaushe. Abdulmajid ya cigaba da kira, Zahra ta yanke hukunci mafi sauki akanta gara ta dinga amsa wayarsa akan ta qi amsawa idan ya ci gaba da turo mata irin wadannan sakonnin matsala ne. Amma in waya ce a gaban iyayenta ta iya dauka ta ce wrong number ta katse, amma idan a rubuce ne babu mai fitar da ita sai Allah.
Zahra tasa hannu ta danna ma'ana wajen amsa waya, ta fada cikin dakakkiyar zuciya, domin tsananin tsoron da take ji ya fita yanzu, fatanta ta kwaci
kanta.
Ta ce, "What do you want from me?"
A wannan karon shi kuma tasa muryar ce take karkarwa.
Ya ce, "Zahra ki saurare ni mana ina sonki ne, na yi miki alkawari zan canja miki rayuwarki. I will do anything for you."
Ta fada cikin fushi, "Kamar ya ya?"
Ya ce, 'Waya mai tsada, in zuba miki kudi a ciki account babu adadi, English wears kala-kala. Ke zan iya siya miki mota saboda ina sonki, ki rabu da sauran samarinki..."
Ta daka tsawa ta katse shi ta ce, " enough is enough, ka sanni kuwa? Ka san yaya nake? I'am a small girl, I am just 15yrs ya za ka dinga kirawo min sunan samari? Ya za ka ce za ka siya min mota? Me ye Abbana ba shi da shi da kake so ka nuna min kudi? Abdulmajid please I beg you ka rabu da ni kana so ka jawo min matsala infact ka jawo abin da Abbana zai aikata kisan gilla a kaina ko a kanka. Akwai manyan 'yan mata a gari ka je ka tsara su ka rabu da ni please. Yaushe ka san ni? A ina ka sami number na for God sake, za ka jawo min problem."
Sai ta fashe da kuka. Abdul majid ya fada cikin nadama da tausayawa "Oh God baby don't cry. Ni mai sonki ne zan kawo miki farin ciki ba zan jawo miki problem ba. Na sami number a dalilin wata sister ta Sajida."
Zahra ta dakata da kukan ta maimaita sunan "Sajida, Sajida, Sajida."
Har sau uku a inda kwakwalwarta take kai kawo tana so ta tuna inda ta taba jin mai suna Sajida ta na ta kokarin tuna a duniyar da ta taba haduwa da mai suna Sajida a rayuwarta.
Abdul majid ya ci gaba da cewa, "Ba kawarki ba ce Sajida? Ai ta taba kiraną da wannan lambar anan na sami lambarki, ta fada min sunanki Zahra."
Zahra ta sake maimaitawa, "Kawata Sajida, a ina nake da qawa Sajida? Ni gidan wacce kawa ake barina in je?"
Abdul majid ya ce, "Common baby, ki tuna mana a cikin satin nan Sajida ta kira ni da wannan lambar da yamma. Baki tuno Sajida Yakub Kawo ba?"
Sai a lokacin computer kwakwalwarta ta fito mata da Sajida muraran ta gane wacce yake nufi, sai ta ji wani sanyi a ranta, ta fada cike da murna.
"Okay na gane Sajida a Kawo ka kira ne a bata waya, ai bama tare. Ko ba SajiAbdulmajid ba budurwarka. Ai Sajida aminiyata ce duk sanda mu ka hadu zan kira ka in ba ta waya saboda haka ba sai ka qara kira ba."
Abdulmajid ya yi dariya ya ce, "Kina da wayo da yawa Zahra. Tunda kin fahimci Sajida budurwata ce, no need in boye miki harma kin riqe sunan da ta hada Sajimajid. Abdulmajid so yake yanzu in zama na an
hada mana SAJI-ZAH-MAJID ma'ana Zahran Abdulmajid."
Zahra ta tsuke fuska yayin da wani mummunan sabon tashin hankali ya far mata. Ta mike tsaye a fusace.
Ta ce "Kai ba zai yiwu ba, ba zan iya ba, ba zai yuwuwa ba. Gara ka rabu da ni tunda wuri kafin mahaifina ya sani. Kar ka kara kirana. Ka zama mai bata tarbiyyar da iyaye suka yi wa ya'yansu.
Mace kwarya ce me kyau wacce iyayenta suka adana ta suka saqale ta a ragaya, don karta fito tsakar gida a yi amfani da ita ta yi datti. Amma kai ka zuga kwaryar an mai kyau take ballowa daga ragaya take fita titi tana tunbele kana garari da ita, har sai da ta baci, sannan ta zagayo ta haye ragaya kamar ba ta yi datti ba a tunanin Iyayenta, kwaryar nan ta su tana nan da kyawunta,"
Ta ci gaba da cewa "Abdulmajid, Abbana ya ce ni kwaryarsa ce mai kyau, ya saqale ni a ragaya don kada in yi datti ya ce min yana fatan wannan kwaryar tasa ba ta fakon idonsa tana ballowa tana fita ta yi yawan garari ta yi baki ta zo ta d'ane a ragaya, kamar wata kwarya ta gari kamar yadda Sajida ke yi."
Zahra ta na gama fada sai ta murtsike wayar gaba daya ta kashe. Yayin da take murza idanuwanta ta ji ko mafarki take a cikin barci. Ta ga daram ba mafarki ba ne, ido biyu ne. Babu abin da take hangowa a cikin idanuwanta sai lokacin da suke tafe da mahaifinta a mota bayan sun taho daga gidan su Sajida sanda ta yi masa zancen Sajida ta na lekawa katanga ta ari waya su yi magana da saurayi. Hankaiinsa ya yi matukar tashi kamar zai jawo ya dake ta ita mai ba shi labarin. Ina ga idan ya ji ita ce take zance da saurayi a waya?
Jikinta na karkarwa ta koma kan doguwar kujera ta takure yayin da wannan dare ya zame mata shine daren farkon da ta taba haduwa da irin wannan gagarumin tashin hankali a rayuwarta ta duniya, tun da Allah ya halicce ta. Dan haka yau ne dare na farko da barci ya kauacewa fatar idonta. Yadda ta ga rana, haka ta ga dare tana zaune tana tunani. Ba tare da tasan Asubah ta yi ba, Abbanta ya gwada kiran wayarta ya ji a kashe, don haka sai ya zo da kansa har kofar dakinta yana bugawa. Saboda tsabar ba'a cikin hayyacinta take ba, haka ta zurawa kofar ido tana kallo ta manta idan ka ji ana buga kofa budewa ake a ga ko wanene.
Muryar mahaifinta ta ji ya ce "Yagana, bude kofa mana. Wanne irin bacci kike yi haka ne?"
Sai ta yi firgigit ta tashi zaune daga kishingiden da take ta amsa cikin rawar murya. "Na'am."
Ta yi duru-duru ta fisgo wani 'dogon hijab ta maqala ta bude kofar falon da sauri. Nan, aka hau kallon-kallo tsakanin Zahra da mahaifinta. Shi ya na kallonta saboda yadda yaga tana kallonsa galala tana zare ido kamar wata sabuwar tababbiya da alama idanuwanta su na tattare da barci mai yawa don sun yi luhu-luhu. Ita kuma tana ganin mahaifinta sai tsoro ya kamata don ta kwatanto irin tashin hankalin da za a yi duk lokacin da ya kama ta Abdulmajid ya bugo mata waya ko ya turo mata sako ta waya.
Bakura ya fada cike da mamaki, "Mamana, lafiyarki kalau kuwa? Kin yi bacci yau ko karatun test din kike yi tun dare?"
Zahra ta ji dan sanyi a ranta da ta ji ya fadi haka, ta amsa da sauri. "Eh karatu na kwana ina yi."
Bakura ya yi shiru na wani dan lokaci, sai ya
girgiza kai. Ya ce "Ba kya jin magana, maimakon ki yi bacci yau ki tashi a nutse meye amfanin kin kwanciya ba ki yi barci ba, ki shiga dakin jarabawa kina gyangyadi? Ki shiga ki shirya ki je makaranta da wuri."
Tana rawar jiki ta rufe kofar falonta, ta shiga ciki da gudu ta lalubo wayarta a karkashin filon kujera, hannunta na karkarwa ta kunna wayar cikin 'yan dakikai sai ga waya radau ta kunnu, yayin da kunnuwanta suke jiyo mata wani sauti daamm, daamm sakon text message yana shigowa, har guda uku.Wannan karon ma firgita ta sake yi tun kafin ta bude ta ga me aka rubuta babu tantama ta ji a jikinta Abdulmajid ne mai wannan danyen aikin.
Ta bude sakon farko, sako ne daga Abdulmajid yana bayyana mata tsantsar kaunar da yake yi mata. Sai ta ji kwallar
takaici. Ta bude sako na biyu, sako ne daga Abdulmajid yana bayyana mata tsananin begen da yake yi mata. Sai ta ji hawayen qunar rai. Ta bude sako na uku, sako ne daga Abdulmajid ya na bayyana mata tsagwaron halin da ya shiga a sanadiyar kin ba shi hadin kan data yi, ya baza hajarsa bai siyar ba ma'ana bata karbi soyayyarsa ba. Sai ta ji wuyanta ya hau makakin tashin hankali. Wannan ne karo na farko da Zahra ta ji ta fara tsanar rayuwarta.
Bugun da ta ji ana yiwa kofar falonta ne ya zaburar da ita, ta cillar da wayar gefe ta mike tsaye tana muzurai, sai ta ji muryar mahaifinta yana kwalla kiran sunanta. Ta na karkarwa ta je ta bude sai ga mahaifinta da kaninta Abubakar a tsaye carko-carko sai zare ido take, ta kalli wannan ta juya ta kalli wancan.
Bakura ya ce "Da gaske ne yau babu makaranta kun fara mid-term break?"
Zahra ta fara gwagwarmaya da makoshinta. "Eh, eh, ashe haka ne na manta."
Bakura ya tsuke fuska ya ce "Me yasa kika kashe
wayarki? Na san kawayenki su Khadija Rabi'u za su kira su fada miki tunda ke kin manta. Ki na 'yar yarinyarki qarama kina matuwa, kamar wata tsohuwa? Ki je ki dauko wayar ki kunna ki kawo min in yi magana da principal. Ya za a yi a ce ana hutun mid-term ba'a ba ku a rubuce ba."
Zahra ta na karkarwar jiki ta koma cikin falonta da sauri yayin da fargaba da tashin hankali suka qaru akan na da.
Abubakar ya dubi mahaifinsa ya ce "Abba an bamu takarda a rubuce a cikin mota muka bar su, bari in je in duba."
Ya nufi wajen mota kafin Bakura ya bude baki Zahra ta fito cikin muzurai da rawar jiki ta mikawa mahaifinta waya. Ya karba ya juya ya nufi dakinsa da wayar. Juyawarsa ke da wuya sai wavar ta yi qara alamar sako aka turo (Test massage). Bakura ya yi sauri ya tsaya Cak ya duba wayar bai yi wata-wata ba sai ya bude sakon ya karanta ya juyo da sauri ya dubi Zahra. Tuni numfashin Zahra ya fara tafiya kamar mai shirin tafiya barzahu. Ya dube ta, ta dube shi, sai taga ya gyada kai ya juya ya tafi. Ta sulale ta tsugunna don tsananin tashin hankali, ta san tabbas Abdulmajid ne, sakonnin kuma soyayya duk da ta goge wadancan na jiya kafin ta mika masa wayar. Ta irin matakin da mahaifinta zai dauka akanta, yanzu ta sake tsanar kanta, takaicin da dana sanin dama bata nace ta ce mahaifinta ya kai ta ta ga Sajida mai kama da Zuhuriyya. Ba dan ta je gidan ba, da tsautsayi bai sa ta bada aron wayarta ba. Da a ina Abdul majid zai sami nummbar wayarta?
Hawaye ya dinga surnano mata babu tunanin da bai zo mata ba a rai ba, ta ji kamar ta hada kayanta ta gudu wajen dangin mahaifinta a Maiduguri a neme ta a rasa, saboda ta san yau hukuncin da zai dauka akanta ba kadan ba ne.
Muryar mahaifinta da mahaifiyarta ta ji su na fitowa daga dakinsa, Zahra ta zabura ta miqe tsaye gami da goge hawayen da ya yi mata faca-faca a Idanuwanta. Ta yi zuruf tana kokarin shigewa cikin daki da gudu sai ta ji muryar mahaifinta ya kwalla kiran sunanta. Ta waiwayo a firgice cikin rawar murya ta amsa. Ya qaraso kofar falonta a inda take tsaye ya mika mata wayarta. Ba tare da ya sake duban inda take ko ya yi wata magana ba, ya zarce zuwa babban falo.
Mahaifiyarta ce ke biye da shi ita ce ta tsaya tana kallon Zahra kallo irin na lafiyarki qalau kuwa? Zahra ta gaishe da mahaifiyarta cikin firgici. Samira ta amsa gami da jero mata tambayoyi har guda uku a jere.
"Lafiyarki kalau kuwa? Me ke damunki duk ki a susuce? Me yasa kika kashe wayarki?"
Amsar wadannan dogayen tambayoyi su ne, "Ba komai." In ji Zahra.


Please Login or Register in order to submit comment