Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana kuka babu abun da take tunawa sai Abdul Majid' dinta. Ta yi wanka mai kyau, ta yi brush, ta dauro alwala ta fito ta wuce daki fuskarta a murtike haushin kowa take ji. Bayan ta idar da sallolin da ke kanta, nan ma iyaye da qawayenta suka baibaye ta kowa đauke da kayan kwalliya. Masu taje kai na yi ana mulka mai, masu yanke farce na yi, masu shafa mata mai na yi, masu shafa hoda da jagira na yi. Ta yi ta fizge-fizge tana fadar baqaqen maganganunta da fitsara iri-iri babu wanda ya damu da abin da take fada kowa burinsa amarya ta yi kyau, domin yau da daddare za a kai ta gidan angonta Bakura.
Wani tsalelen leshi ne baqi, wanda aka yi masa ado da fulawa ruwan goro, wanda ya sha dinkin riga da siket matsattse, shi ne aka sakawa Sajida. Yayin da aka dandan bara mata gwal-gwalai a kunne, wuya, yatsu, da awarwarye a hannunta kan ka ce kwabo Sajida ta fito sak amaryarta. Abarka da Kai ka fi cancanta..

Gashinta kuwa mai laushi ne aka gyara aka zubo mata da shi har bayan qeyarta, aka nade mata daurin dankwalin leshin a samansa, sannan aka yafa ma ta mayafin da ya dace da leshin wato mai ruwan goro, takalmi ma kalarsa ne, yayin da aka feshe duk illahirin jikinta da turarurruka masu qamshi na cikin lefe.
Aka ruqo ta zuwa tsakargida aka zaunar da ita akan wata doguwar kujera aka fara daukar hotuna. Babu yadda Sajida za ta yi, domin an ce sarkin yawa ya fi sarkin karfi, amma zuciyarta cike take da baqin ciki da damuwa. A zaune take tamkar gunki, sai kallon mutane take sasarai kai ka ce ba ta da laka a jikinta. Duk sanda ta tuna ita da Abdul majid shi kenan sun rabu sai ta ji zuciyarta ta harba kamar ana harba bindiga. Idan ta tuno mutumin da aka daura mata aure sai ta ji ta qara tsanarsa.
Ta ce a ranta "Lallai kuwa mutumin nan ya yi kuskuren aurena. Iyayena sun yi kuskuren ba shi aurena, sun yi kuskuren karbar dukiyarsa saboda asara ce. Sai na zame masa tamkar kunama mai cizo a shimfidarsa. Zan zame masa duhu alhali da hasken rana. Sai na disashe farin cikin zuciyarsa, ya koma tsananin baqin ciki da damuwa kamar yadda ya sakani ni da Abdul Majid dina. Sai na fardo wannan kyakkyawar kwaryar tasa da yake ji da ita wacce ya saqale a ragaya, idan ta fado qasa ko ba ta fashe ba, zata yi gagari a tsakar gida. Sai na yaqi uwar gidansa na hana ta sukuni a gidanta. Sai na takurawa duk wani mai rai a gidan in ya so idan ya gaji zai sake ni, ko ya kore ni, sai ya ji ya tsani zama da ni."
Sajida ta yi murmushin mugunta, wanda har wushiryarta ta fito ta girgiza qafa, 'yan biki suka dau shewa hadi da guda a tunaninsu amarya ta saki ranta ta amince da auren.

*** *** ***
A daidai wannan lokacin Samira da tawagarta na can su na ta su walimar. Samira ta dage ta cije ta danne tsananin kishinta ta shiga cikin 'yan uwa da qawayenta su na taya Bakura farin cikin aurensa. Don haka an zuba kujeru a farfajiyar gidan, an yi dafe-dafe, an hado kayan maqulashe, mata ne zalla suka taru. Wata Malama ce mai suna Malama Jamila take wa'azi, tana tunasar da mata darajar miji a wajen matarsa. Ta na fadakar da mata su cire zafin kishi a ransu su zauna da kishiyoyinsu lafiya. Daga qarshe ta fadakar da mata da su kula da tarbiyyar 'ya'yansu, musamman 'ya'ya mata.
Daga dukkan alamu wa'azin yana ratsa zuciyar Samira, ta yi shiru tana sauraro. Cancandi! Amma fa Samira ta zuba kyau, kai ka ce ita ce amaryar idan ka duba tsadaddiyar material da ke jikinta, sai walkiya take gata da iya kwalliya. Sai dai duba daya za ka yiwa Samira ka tabbatar ta rame, tana cikin damuwa. Haka 'yarta Zahra ta yi tsuru ita da qawayenta a gefe da alamar damuwa a tare da ita.
Tun qarfe takwas na dare Alh. Bakura ya tura motocinsa kakaf dana abokansa gidansu Sajida don dauko amarya da masu rakiyarta. Amma ba a samu an fito da amarya ba sai qarfe goma na dare, saboda gwagwarmayar da ake ta yi da amarya, ta bujere ta ce ba za a kai ta ba. Ihu take tana bori, tana faduwa tana burgima a qasa. Hankalin kowa ya tashi, babu wanda bai zo ya tsaya akan Sajimajid ya yi mata nasiha ba.
Malam da kansa ya shigo ya tashi Sajida tsaye, ya goge mata hawaye, ya dau lokaci mai tsawo yana ba ta haquri, sannan ya shiga yi mata nasihohi masu ratsa jiki, gami da jawo mata manya-manyan ayoyin Kur'ani mai girma, wadanda suka yi magana akan bin iyaye da bin miji. Daga qarshe ya yi mata magiya da roqo akan ta rufa masa asiri ta shiga mota a kai ta gidan mijinta, kada ta ba shi kunya idan ta je kuma ta zauna lafiya da kowa. Ya yi mata addu'a, gami da fatan alkhairi ya dora da godiya. Domin ya ga jikinta ya yi sanyi, tana hawaye kanta a sunkuye a qasa.
Ta dauko gyalenta ta yafa, ta dauko dankwalinta ta karkade ta daura ta sharbe wani zazzafan hawaye ta fara tafiya a hankali kai ka ce kwai ne ya fashe mata a ciki, ta nufi qofar fita ba tare da ta cewa kowa komai ba. Duuuuu'!! Haka mata suke biye da ita har qofar gida inda motoci suke.
Galla-gallen motoci ne duma-duma masu sanyin A.C da sautin kida reras a qofar gidansu Sajida. Wacce ta fi kyau da tsada ita ce aka Kawowa amarya gabanta aka yi mata tayi ta zo ta shiga gidan baya, amma ta qi shiga. Daga qarshe aka ba ta zabi ta shiga duk wacce take so, Sajida tsaye take qiqam ta qi motsawa.
Ijiyayye awartaq ce ta zo ta rada mata wata magana a kunne ko sakon daya Sajida ba ta qara ba aka ga ita Ijiyayyen sun nufi wata jifgegiyar mota qatuwa a cikin jerin motocin da suke laye. Sajida ta bude gidan gaba ta zauna, yayin da Ijiyayye ta shiga baya.
Umma Furare ta yi sauri ta ce da wasu tsofaffi biyu yayyanta su je su shiga motar da Sajida ta shiga, don ba ta yarda da wannan radar da aka yi ba. Haka kuwa aka yi, zuruf su Sajida suka ga tsofaffi biyu sun fado cikin motar sun zauna. Babu wanda ya ce da kowa komai. Sai diddika ake cikin motoci, duk motar da ka leqa mata ne jingim da 'ya'yansu wasu kan wasu. Haka suma 'yan mata sun cika motoci da yawa ana ta falli ko Allah zai sa daga cikin abokan ango daya zai dasa. Duk yawan motocin nan sai da aka bar wasu a qasa, saboda yawan mata, wasu ma 'yan gayyar sodi ne sun zo su ga qwakwab.
Umma Furera na küka tana dagawa Sajida hannu, haka shi ma Malam kwalla yake yana tsaye a gcfe, har motocin suka ja suka tafi a laye.
Motar da amarya ke ciki tana tsakiya, suka hau titi dodar aka nufi gidan Bakura. Sajida ta juya gefenta ta dubi direban da yake tukawa sanye yake da rawani ya rufe fuskarsa Idanuwansa kadai ne a waje, shi ma ya dube ta ya yi murmushi. Cikin harshen turanci Sajida ta yi magana, saboda tana gudun kada tsofaffin nan su ji abinda a suke cewa.
Ta ce "Who are you?"
Ya lankwashe murya ya ce, "Sajimajid."
Haqiqa wannan muryar tayi kama da muryar abin qaunarta Abdul majid. Kan ka ce kwabo Sajida ta saki ranta farin ciki ya gauraye zuciyarta. Ta waiwayo da sauri ta dubi Iyayye wacce its ce umul aba'isin da ta hada wannan tuggun tayi yadda ta yi ta hado Sajida da Abdul majid har sai da suka hadu suka ga juna. Su na hada ido suka yi wa juna dariayar farin ciki.
Ya saka hannu ya zame rawanin da ya nada don yin badda kama ya dubi Sajida duba na so da qauna cikin harshen Turanci.
Ya ce, "Kin rame, kin kode, kin lalace, iyayenki su na cutarki baby."
Ta yi naira-nairai da ido hawaye ya kwararo ta sunkuyar da kai qasa ta ce, "Yaya zan yi? Yaya ka ke tunanin rayuwata zata kasance idan ka bar ni a cikin wannan halin? Don haka yanzu ba zan bari ka tafi ka barni ba sai dai ka Juya kan motar nan mu gudu a neme mu a rasa."
Saboda dimaucewa bai san sanda ya taka burki gaba daya suka kusa buga baki da gaban mota, sannan ya ci gaba dà tafiya.
Ya ce Baby, ya ya zan yi da tsofaffin nan da suke kallona tsuru-tsuru?"
Sajida ta juya ta dube su cike da takaici ta galla musu wata uwar harara mai firgitarwa.mai kyau, kowa ya kalle ta sKai ka fi cancanta


Ta ce, "Sai mu zubar da a daji kawai. Ijiyayye ma kwakwalwar irin ta tsofaftin ce ba turanci, don haka su dukka sun yi turus suna kallon su Sajida, ba su san abinda ake shirin aikata musu ba.
Abdulmajid ya girgiza kai. ya ce, "Ba zai yiwu ba baby, ki tafi kawai gidan mijinki, amma ki dinga bin duk wani abu da zan gindaya miki. Daddy na yana gari ya kira ni ya yi min fada cewar ya sami labarinki, don haka kada in sake in hana ki zaman aure. Idan ya ji mun gudu zai hukunta ni, koma ya kore ni daga gidansa. Mutum ne mai zafi, ga shi dan ka'ida , zai iya bi na da bindiga ya ce zai harbe ni."
Sajida ta rushe da kuka ta ce, "ni fa ba zan sauka daga motar nan ba, bin ka zan yi, daman mutane suna cewa ba ka sona, ba ka damu da ni ba."
Abdul majid ya yi ajiyar zuciya a bayyane ya tsuke fuska, yayin da ya fara magana cikin wata kakkausar murya mai nuni da bayar da umarni. Ya ce "Ki kula da abun da nake fada miki, kuma ki bi duk abun da nake fada miki. Ba zan gudu da ke ba, kuma ba za ki qi zuwa gidan mijinki ba, sai dai kada ki yarda wani abu ya shiga tsakaninku. Nan da wani dan lokaci idan na gama shirya abinda nake shiryawa zan san yadda zan fito da ke mu gudu a rasa mu. Kinaji na ko?"
Sajida ta amsa cike da ladabi da tsananin tsoro.
Ya ce, "Ki goge hawayenki ki daina kuka, ki dauka tamkar na kai ki ajiya ne nan da wani loakci zan zo in dau ajiyata."
Su duka suka yi murmushi, Sajida ta goge hawayenta ta ci gaba da kallon abin kaunarta Sajimajid tana sauraron dadadan kalamansa.
Daya daga cikin tsofaffin nan ce ta zuro da kanta tsakiyar Sajida da Abdul majid ta ce "Daman kin san dircban nan ne ku ke hira? Na ga alamar ma Buzu ne, don na ji kuna yaren Buzaye, daman kin iya yaren? Wacce irin hira ku ke yi idan kika yi kuka sai ki yi dariya kuma?"
Haushi ya rufe Sajida da Abdul majid, har suka rasa abun da za su ce mata.
iyayye ce ta ba ta amsa. Ta ce, "Iya, dan Allah ki gyara zamanki, ina ruwanki da hirarsu."
Tsohuwa ta koma ta zauna. Ta ce "A'a, 'yar nan kar ki ga laifina, dole in tambaya, don in sani. Na sani ko wannan dan iskan ne Abdul majid da take so ya aiko Buzu ya sace ta."
Daya tsohuwar ta ce, "Ai kuwa da mun cî ubansu, don idona idon Abdul majid sai na sharara masa mari, saboda wahalar damu da yake yi. Gaba daya ya hargitsawa yarinya lissafi, ya hanata zama lafiya, ga gidan arziki da wadata ta samu, amma ta qi kwantar da hankalinta. Ai shi ma Abdul majid din ko hauka yake ba zai fara tako qafarsa qofar gidanmu ba, ko ya turo a saçe ta ba."
Sajida ta juyo ta dube su, duba na takaici da bacin rai sai ta ja dogon tsaki ta juyar da kanta gefe.
Abdul majid kuwa mudubi ya seta baya yana kallon tsohuwar da take niyyar kwashe shi da mari, sai ya yi murmushi kawai.
iyayye kuwa kunshe baki ta yi da gyalenta tana ta dariya a ciki-ciki. Daidai lokacin ne motocin da suke gaban su Abdul majid suka saka siginal din shiga wani katafaren gida. Nan da nan masu gadi suka wangale get a jere a layi motocin daukar amarya suka dinga kutsa kai su na shiga.
Abdul majid ya ja rawaninsa ya rufe fuskarsa, sai idanuwansa ne kawai a fili, ya wangale idanuwan nan nasa kwala-kwala yana duban farfajiyar gidan. Ya gasgata, ya tabbatar Bakura ba sa'an yinsa ba ne ya cara masa wajen naira, sai dai su goga da babansa, koma Bakura ya fi Babansa kudi.
Kalmar da yake ta fada kenan. "Wonderfiul, fantastic, beatiful. "
Wata tsoka ce daga cikin qirjin Sajida ta yanke ta yi wani qarai, yayin da kuka ya tunkarowa kwayar idanuwanta.
Ta dubi Abdulmajid ta fada cikin harshen turanci.
"Ka kawo ni gidan wanda ba na kauna a rayuwata ka ajiye ni za ka tafi ka bar ni ko?"
Ya cije baki ba tare da ya ba ta amsa ba.
Ta sake cewa "in har kana sona ba za ka so in zauna da wani kato a gida daya ba da sunan mijina. Mai zai hana ka tunkari hatsari, wuya da duk wani wulakancin da za a yi mana kamar yadda na yarda zan gudu koda za a kashe ni."
Ya sami waje ya tsaya ya zare mata jajayen idanuwansa da suka cika da hawaye ya ce, "Fita ki shiga gidan nan kafin wadanda suka sanni su zo su gane ni. Zan bawa iyayye sabon layi da wayar da na siya miki zata kawo miki, za mu dinga magana. Na fada miki ki daina kuka, kuma ina tare da ke a duk inda ki ke."
Kaico! Soyayya gamon jini, sai Abdulmajid ya fashe da kuka .
Cikin shashshekar kuka Sajida ta bude kofa da sauri ta fice tamkar ranta zai fice.
iyayye da tsofaffi suka fita suma suka bi bayan Sajida. Duk wanda yake qoqarin ya riqe ta sai ta fusge. Babu yadda ba a yi ba akan ta sa mayafi ta rufe fuskarta amma ta qi, haka ta shiga gidan mayafinta a kafada, dauri a gaban goshi wato ture ka ga tsiya, ga wani kodadden idon da ya sha koke-koke.
A babban falo suka iske Samira da 'yan uwanta da makwabta jingim suna jiran isowar amarya. Bayan 'yan uwan Sajida sun yi sallama, su Samira suka amsa musu, sai tsofaffi biyu 'yan uwan Sajida suka shiga tsakiyar Sajida suka kaita gaban Samira suka durkusar, sannan kowa ya sami waje ya zauna.
Bayan an gaggaisa aka fara bayani, dangin Sajida ne su ka ce. "To uwargida, ga Sajida mun kawo miki ku zauna lafiya qanwarki ce, koma mu ce 'yarki ce ki gyara mata, idan ta yi kuskure. Ke kuma Sajida yi na yi, bari na bari, ke ce qarama."
Samira na murmushin qarfin hali, dan ba qaramin yaqi ta yi ba da ta danne kishinta ta zauna tana sauraron wadannan bayanai.
Sajida kuwa idonta tsai akan Samira da tawagarta bayan kallon banza ma har da harara take harba musu daya bayan daya. Can idonta ya hasko mata Zahra a zaune a lungu, nan fa ta kafa mata ido tana harara sama da qasa har da girgiza kai wato 'ada kai kawai na fasa miki, yanzu kuma sai na ragargaza kan dukka'.
Zahra ta yi sauri ta sunkuyar da kai qasa, yayin da jikinta ya dau rawa, a halin yanzu tafi tsoron Sajida a kan mutuwarta.
Haka Hajja Farida ta riqe baki tana kallon Sajida tana gyada kai, tana jinjina fitsarar Sajida. Ta tabbatar yarinyar nan ba ta shigo da niyyar zaman lafiya ba. Haka suka dinga kallon-kallo tsakanin Samira da tawagarta da 'yan uwan Sajida.
Tun kafin a gama bayani Sajida ta yi zumbur ta mike tsaye ta yi kiri-kiri da ido tana duban jama'ar, ma'ana idan za ku daina bata yawun bakin ku gara ku daina, don ni babu zaman lafiya a tare da ni. Manufarta kenan duk da ba ta furta ba.
Ba shiri 'yan kawo amarya suka miqe suka saka ta a tsakiya aka ja ta zuwa dakinta, tun kafin ta bude baki ta fadi wata magana da za ta kunyata su. Sajida na tafiya ta na girgiza tana tabe baki.
"Lallai wannan falalliyar 'yar za a yi da ita." ln ji Hajiya Zuwaira. Daya daga cikin yayyun Samira.
Samira ta koma ta jingina da jikin kujera jikinta a sanyaye, sai gyada kai take tana al'ajabin yadda Bakura yana ji yana gani ya dauko wannan halittar ya kawo musu gida.
Hajja Farida ta dau dogon salati ta salallame ta ce, "Tun da nake a doron kasa shekaruna arba'in har da doriya, ban taba ganin fitsararriyar amarya irin Sajida ba."
Nan dai kowacce mace ta fara tofa albarkacin bakinta, tana zayyano abun al'ajabin da idanuwansu suka hango game da Sajida.
Daga karshe suka bawa Samira hakuri da nasihar ta ci gaba da hakuri komai nisan jifa qasa zai fado. Ta ci gaba da yi wa mijinta biyayya ta zuba musu ido ta yi kallon yadda za ta qarqe musu, wato tsakanin ango da amarya. Daga karshe dangin Samira suka kaiwa dangin amarya abinci kala-kala, abun sha da snacks da aka yi musu, sannan kowacce ta kama gabanta.
Sajida ta yi mamaki matuqa yadda Bakura ya kashe kudi ya gyara mata daki, ba tare da sisin yayenta ba. Ta yi matukar mamakin inda Bakura ya santa har ya kamu da sonta haka. Wasu abubuwan ma daga ita har yan uwanta ba su san shi ba, na turai ne, Musamman da suka shiga cikin bandakuna sun hadu an zuba kayan Kamshi da na decoration. Aka yi shawara a bar qawayen amarya guda hudu da tsohuwa daya su kwana da ita ko Allah zai sa hankalinta zai dan kwanta.
Haka kuwa aka yi kafin sha biyun dare gaba daya 'yan rakiyar amarya da masu karbar amarya sun watse. Kawayen amarya ne guda hudu da tsohuwa daya suka rage a dakin Sajida.
Samira da 'ya'yanta ne jugum a zaune a falo har Bakura ya shigo gidan ba su iya tashi sun je sun kwanta ba, abun duniya ya ishe su kasancewar Bakura ya san abinda zai tarar don haka bai bari ko da daya daga abokansa ya rako shi ba.
Haka ya shigo hannunsa ziqai bai siyo kazar amarci ba irin ta al'ada. To duk abinda zai suyo na marmari akwai shi jingim a gidansa, masu aiki ma ya ishe su, balle iyalansa. Kaza ce, juices, fruits, duk su na nan a shaqe a firij. Ya yi sallama ya shigo falon, gami da murda mukulli ya kulle kofar. Su duka suka amsa masa a sanyaye.
Ya dube su ya yi murmushi ya ce, "Yara ba ku yi barci ba, har yanzu? Gobe fa Monday. Yau ba a cewa Abba oyoyo ne?"
Abubakar ya taso ya miqawa mahaifinsa hannu suka tafa, haka Umar da Usman ma a layi suka zo suka tafa.
Zahra ta taso ta dubi mahaifinta a sanyaye ta ce, "Congratulations Abba, ina muku fatan alkhairi."
Sai qannenta duka suka hada baki, "Congratulations Abba."
Mamaki ya kama Bakura ya tabbatar Zahra tana taya mahaifiyarta kishi ba kuma kishin kadai take taya ta ba, wacce ya auro ita ce damuwarta. Da a ce wata ya auro ba Sajida ba, ya san Zahra za ta bi bayansa ba za ta bi bayan mahaifiyarta ba, saboda Zahra tafi son abun da mahaifinta ke so.
Yaran ne suka katse masa tunaninsa suka hada baki, "Good night Abba, Good night Mama."
"Good night children. " Samira da maigidanta suka fada cike da fara'a.
Yara suka nufi dakunansu ba tare da su na jin dadin zuciyoyinsu ba.
Bakura ya matso kusa da Samira ya zauna ya dube ta ya yi murmushi ya fada cikin wata 'yar siririyar murya. Ya ce, "Samira, kin yi kyau, kamar ke ce amaryar, har kin fi amaryar."
Hohoho! Idan ka tona zuciyar Samira za ka yi mamakin irin baqin da ta yi, don takaici.
Ta bata rai, gami da daga hannu ta dakatar da shi.
Ta ce, "Ba na so, kar ma ka fara wannan zancen. Ni a suwa? Ka tashi mu

Please Login or Register in order to submit comment