Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taron ziyara za su jewa Jamilu idan zan zo wajenka in shirya. Tunda Asuba suka fara soye-soyen kaji, cincin, naman rago da dai sauransu."
Zuhuriya ta fashe da kuka ta ci gaba da cewa
"Ba ni da kudi, bare in sayi kaji, ba ni da kudin da zan yi cincin, na aika ko'ina a samo min bashi ba a samo ba. Da kyar na ranto shinkafa gwangwani biyu da kaza daya na dafa maka. Kudin motata bai cika ba na qaraso da qafa."
Bakura ya fashe da kuka ya ci gaba da cewa "Na sa hannu a kwanan abincin ina ci ba don ina so na ci ba sai don ta yarda ta ci itama. Sannan tasa hannu muka ci shinkafar nan a karkashin bishiya, cusawa nake yayin da zuciya ke cike da tausayinta kwalla ce ke cikowa daga idanuwana ina damben mayar da ita don kada Zuhuriya ta gane. Na dube ta na ce Zuhuriya ciki gare ki ne na ga cikinki babba kafarki a kunbure? Ta langwabar da kai tasa gefen gyalenta ta share hawaye ta ce shi yasa ka ji ni shiru, tun sanda na sami cikin ba ni da lafiya. Ban taba lafiya ba tunda na sami cikin nan ga mugayen mafarkai Allah dai yasa in haifi cikin nan lafiya."
Na goge mata hawaye yayin da na fara farin ciki ina murmushi na ce da ita za ki haihu lafiya da izinin Ubangiji, amma na fi son ki haifi mace in dinga siya mata ribon."
Ta yi dariya ta ce "namiji dai ka sami abokin shawara ko bana raye idan na haifi mace kuwa mata na haifa maka."
Na tambaya cike da mamaki na ce "mata kin manta ni yayanta ne wa yana auren qanwarsa ne?"
Ta yi dariya ta dafa kafadata ta ce "idan ba su sha nono daya ba zai iya aurenta tunda ba uwarsu daya ba."
Na girgiza kai na ce na fi son ki haifi mace in dinga yi mata wasa ina goya ta a bayan keke."
Zuhuriya ta saki jikinta muka dinga hira cikin farin ciki har rana ta fadi, sannan na tuna ashe ba ta da kudin mota, kuma ba za ta taba fada min cewar bata da kudi ba tafiya zata yi tayi da qafa har ta isa garinmu, don haka na shiga zulumi ina tunanin yadda zan samo mata kudin mota ko rance ne. Don haka na shiga hostel wajen abokaina da kyar na samo rance na kawo mata, ta qi karba da farko sai da ta ga raina ya 6aci sannan ta karba. Na rakata har get tana daga min hannu, ina daga mata hannu, ashe mun yi sallamar qarshe kenan har abada."
Bakura ya rushe da kuka mai tsanani, yayin da Innono ta dau kuka mai ruri har da dora hannu aka.
Gaba daya suka dafe kirji suka tambaya "mutuwa ta yi a hanya?"
Bakura ya girgiza kai ya ce "ta isa gida lafiya. Bayan zuwanta da kwana biyu ta haihu."
Samira ta tambaya cikin damuwa hade da qaguwa, "Da ta haihu me ya faru?"
Bakura ya ce "Allah shi Ya barwa kan Sa sani har yau ban sami wanda ya fada min gaskiyar al'amarin ba."
Sai ya sake rushewa da kuka.
"Kamar yaya ba ka san gaskiyar abun da ya faru ba?" Malam ne ya tambaya.
Bakura ya dago da luhu-luhun idanuwansa jajaye ya kalli Malam ya qyada kai ya ce "Babu wanda ya fada min gaskiya har yanzu. Mun rabu da Zuhuriya a lokacin da ya rage min saura sati biyu in gama makaranta. Da sati biyu ta cika muka na zana jarrabawar qarshe sai na yiwa Malam Abbas da iyalansa sallama har da koke-koken rabuwa Aunty
Asiya da 'yayanta muka yi,saboda mun shaqu. Mu ka yi hotuna da koke-koke ni da abokaina, sannan kowa ya kama hanyar garinsu. Da jakar kayana kacokan na nufo gida. Ina tafe ina zulumi, ina tunanin da Magarubar nan ina zan nufa gidan Innono ko gidan Zuhuriya? Na yanke shawarar gara in je wajen Zuhuriyata, don na damu na ga lafiyarta in ya so ko a zauren gidan sai in kwana kafin mu yi shawarar inda zan zauna. Ina isa kofar gidan na iske Malam Yahuza mai gidanta da sauran mutane. Na gaishe su, amma sai kowa yake yi min duba irin na tausayawa na lura da haka, amma ban kawo komai a raina ba na wuce zuwa cikin gida. Na iske sauran matan biyu su na zaune bisa tabarma daya sun hada kai su na qus-qus su na ganina sai na ga sun zabura sun miqe tsaye yayin da daya take qoqarin zurawa da gudu su na tambayata, Lafiya? Me na zo yi a gidansu?
Sai na yi mamakin wannan tambaya ta su, amma ba su da wata amsar da zan iya ba su, domin bai kamata su tambaye ni abun da na zo yi ba a wajen Zuhuriya ba. Na kada kai na nufi dakinta. Abun da na gani shi ya firgita ni na tsaya cak yayin da na juyo da sauri na dube su.
Yayin da bakina yake karkarwa na tambaye su "Ina dakin Zuhuriya, ina Zuhuriya?"
Sai Bakura ya riqe kai ya barke da wani zazzafan kuka mai zubo da hawaye ba kakkautawa. Hankalin kowa ya tashi, yayin da gaban kowa ke faduwa. Yara da manya hawaye ne fal a idonsu.
Sajida ta tambaya cikin damuwa "Me ya faru da dakin Zuhuriya?"
Bakura ya dago da kyar ya dube ta ya fada ciki wata nakasasshiyar murya, "Dakin Zuhuriya ya kone kurmus sai toka."
Zahra ta ce "Ina Umma Zuhuriyar? Ina bebin da ta haifa?"
Bakura ya, girgiza kai saboda tsabar jimami ya ce "Zuhuriya na ciki ita da baby lokacin da wutar ta kama don haka suma sun qone."
Su ka hada baki su duka "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un."
Kowa ya yi shiru babu wanda ya iya cewa komai, fuskar Bakura na tsugunne a qasa sai hawaye ne ke zuba a kan tiles fat-fat-fat daga nan ya kasa ci gaba da labarin.
Innono ce ta ci gaba ita ma cikin rurin kuka, hawaye ke zubowa kamar ruwan famfo ta ce, "Daga sanda Bakura ya ji Zuhuriya ta qone qurmus ko gawarta ba a fitar ba, sai toka, a take ya suma har bayan Isha'i bai farfado ba ana zuba masa ruwa.
Washe gari da safe ya nufo Cinkilawa wajena. Bakura ka yafe min abun da na yi maka a rayuwa. Iyalan Bakura kuma ku yafe min shiyasa ake son mutum ya shuka abun alkhairi a rayuwarsa, ina ganinsa zai shiga Cikin gidan sai na zo na tare qofa da hannuna na tambaye shi ina zai je? Ya kalle ni galala kamar Zautacce sai na nuna masa hanyar waje na ce yau babu Zuhuriya a duniya, don haka babu kai babu zama a Cinkilawa ka hada kayanka ka koma Mangono. Ya Juya a sanyaye yana tafiya sai na ga idan ya tafi aka rasa shi ni za a kama a Mangono a ce ina dan da muka dauko sai na kira shi ya dawo na ba shi tabarma a zaure na ce ya zauna nan da kwana biyu zan hada kudin mota in mayar da shi Mangono da kaina. Bakura baya kuka sai dai ajiyar zuciya ko ba a fada maka ba ka san turniqin qunar da yake ji ba zai fasaltu ba. Kuma baya magana sai kallo da ido. Da Magaruba ya tashi ya fice ban sake ganin Bakura ba sai yau, neman duniya nasa a yi ba a ganshi ba. Baya Cinkilawa, baya Balle batai, baya Yan lanya, baya Jarawa, baya Warawa, baya Lahadin makoli baya kadara, baya Rimi,baya Token, haka baya Larabar gadon sarki sannan baya makarantarsu Wudil, don haka na ja bakina na yi shiru, duk wanda ya tambaye ni Bakura sai in ce ai tun bayan mutuwar Zuhuriya iyayensa suka zo suka dauke shi sun tafi da shi Mangono."
Har wani lokaci mai tsawo Bakura ya dauka kansa a sunkuye bai dago ba. Can ya dago ya dubi kowa daya bayan daya ya sharbe hawaye.
Ya ce "Kun ji yadda mutuwa ta raba ni da Zuhuriyar da nake matukar kauna take matukar sona a duniya. Na yi rashin uwa, na yi rashin uba, na yi rashin yayata, na yi rashin aminiya, na yi rashin mai sona. Daga sanda na ji Zuhuriya ta rasu daga lokacin na ji wani qaton abu mai kama da dutse ya zo ya tokare min a tsakiyar kirjina har yau bai sauka ba. Ban fara kukan mutuwar Zuhuriya ba da hawaye sai da na shekara biyar zuwa shida bayan mutuwarta, saboda abun da nake ji ya fi kuka ciwo. Kukan da na fara shi ne sauqin ciwon mutuwar har yau ban taba kwana biyu ba cur ban zubar da hawayen dacin mutuwar Zuhuriya ba a zuciya ba. Ban taba samun naira daya, ban yi hawayen daman Zuhuriya na nan in ba ta ba. Ban taba miqawa wani kudi ko kaya ban tuna dama Zuhuriya nake bawa ba. Alhamdulillah Alakulli halin, Allah ne mai yadda ya so da bayinsa. Tsakanina da ita sai addu'a marar adadi, sai na dinga sadaukar mata da sadakatul jariya. Ina addu'a, Allah ya kai mata rahama cikin kabarinta."
Su duka suka amsa masa da, "Amin."
Zahra ta sharbe hawaye ta ce "Abba, a lokacin shekarunka ba su wuce goma sha shida zuwa sha bakwai ba kana yaro, ina ka tafi da ba'a ganka ba, ko Mangono ka koma?"
Bakura ya girgiza kai ya ce "Ban yi tunanin Mangono ba, ban yi tunan komawa Wudil ba. Ban yi tunanin a duniyar da na ke ba, ni dai na sa gabana gadi ina ta tafiya a dawa cikin dare. Ban damu da duhu ba, ban damu da maciji ba, ban damu da 6arayi ba ko 'yan fashi, ba ko gajiya, tafiya nake ni kaina ban san matsayina ba a raye nake ko a mace? Ban san ina na nufa ba ko ina na dosa. Ashe cikin Kano na nufa a cikin kasuwar Singa Asuba ta yi min na fadi a bakin hanya sumamme."
Ya dubi Zahra ya ce "Daga nan Allah ya hada ni da kakanki, mahaifin Mamanki Samira. Allah ya yi wa Alhaji albarka shi yasa aka dauke ni aka kai ni asibiti aka yi ta qaramin ruwa har kwana uku, sannan aka sallamo ni ya fara tambaya ta garinmu. Ban fada masa komai ba na dai ce masa ban san kowa ba anan kuma ba ni da inda zan je sai dai ya dauke ni aiki. Ya saka ni a cikin yaransa muka fara aiki, sai ya yaba da hankalina gashi kuma ni kadai ne na iya rubutu shi ma bai iya ba. Don haka ya ja ni a jiki. Ya na aikena har cikin gida in kai sakon cefane, ko kuma kafin ya fito kasuwa ya kira ni in shigo har falonsa in yi masa lissafi da cike-ciken takardu. Anan sai Allah Ya jarrabi Samira 'yarsa da tsananin sona, nima ina sonta, amma abun da kamar wuya a ganina ba zai yiwu ba.
Babu abin da ya gagari Ubangiji, Alhaji ya amince min na aui Samira, amma sai da ya tisa ni a gaba na kai shi Mangono ya ga mahaifana. Sai da Samira ta qare sakandire aka yi aurenmu lokacin tana da shekaru goma sha shida, ni kuma ina da shekaru ashirin. Ya ba mu aron gida muka zauna ina zuwa kasuwa na ci sa'a na sami mace ta gari mai tsananin sona, mai lallaba ni, mai ba ni hakuri, idan ta ga ina cikin damuwa. Amma duk da haka ba na jin dadin rayuwata.
Wata rana na hadu da wani babban ma'aikaci ya yaba da hankalina ya samar min tallafí daga gwamnatin tarayya. wato (Scholarship) zuwa qasar England don yin degree. Gwamnati ta dau nauyina da matata muka tafi England har tsawon shekaru uku a can muka haifi 'yar mu ta fari na saka mata sunan Zuhuriya, muke kiranta da Zahra, ko in kira ta da Yagana. Tun daga lokacin Allah Ya fara buda min hanyoyin samu. Na dawo Nigeria na fara aiki ina kasuwanci ina zuwa England ina saro kaya ina shigowa da su. Har rana irin ta yau kullum ci gaba nake samu a rayuwata.
Na shiga cikin matsananciyar fargaba a lokacin da na fara ganin Sajida a rayuwata, saboda tsananin kamar da ta yi da Zuhuriya sak kamar an tsaya kara"
Sajida ta dago da sauri ta dubi Bakura ta dafe kirji ta ce "Ni, ta yaya zan yi kama da Zuhuriya?"
Bakura ya gyada kai ya ce "Haqiqa duk wanda ya san Zuhuriya, yaga Sajida sai ya fadi haka. Wannan dalili yasa na bi Sajida gidansu, dan ganin su waye iyayenta, kuma ta ina ta samo kamannin Zuhuriyata. Na ga mahaifinta, na ga mahaifiyarta, na ji tarihinsu babu ta inda suka hadu da Zuhuriya.
Hankalina ya qi kwanciya, tun ranar da na baro Cinkilawa ban sake komawa ba sai sanda na hadu da Sajida, anan na fara zuwa Yan lanya na tambayi wani tsohon makwabcin gidan malam Yahuza ya shaida min malam Yahuza ya rasu tuntuni matansa ma daya ta sami tabin hankali. Na tambaye shi game da abun da ya faru da Zuhuriya, sai ya ce Zuhuriya da 'yar da ta haifa suka qone a cikin dakin. Na fito daga Yan lanya na shiga Cinkilawa na tarar Innono ba ta garin, mijinta ya dade da mutuwa. Na tambaya ko Zuhuriya ta bar 'yar da ta haifa? Sai aka ce min ai namiji ta haifa, shi ma daga baya yaron ya mutu. Na rasa gaskiyar magana, hankalina ya kasa kwanciya."
Umma Furera ta gyara zama ta goge hawaye ta ce
"Malam Yahuza yayana ne uwa daya uba daya, amma ni a garin Shanono na girma shi kuma a Yan Lanya ya girma kasancewar yawon almajiranci ya je yi. Ya yi aure-aure da dama, amma Allah bai bashi haihuwa ba, na ji labari ya auri Zuhuriya, amma ban taba zuwa lokacin da suke tare ba, ta samu ciki ta haifi 'ya mace. To kamar yadda aka ba ni labari da muka je zaman makokin Zuhuriyya. An ce ta haihu da kwana biyu sai ba ta da lafiya, saboda haka tana kwance a daki akwai wani Malami da ya zo daga Balle bantai ya ce a kawo yarinyar zai yi mata addu'a, sai Malam Yahuza ya shiga ya dauko 'yar a kwance a gaban Zuhuriya ya ce min har Zuhuriyar ta yi masa magana ta ce masa kada a yi wa jaririyarta zane, dan Allah a bar mata fuskarta haka, kasancewar mu Fulani ne ta ga duk 'yan uwanmu da zane irin nawa nan, ya ce ai ba wanzami ba ne, malami ne ya zo zai yi mata addu'a.
Ya ce min ya fito ya bar ta da garwashin wuta a gabanta cikin kasco saboda sanyin da ake yi sai dai idanuwanta lumshe kamar mai magagin barci. Ita kadai ce a dakin kasancewar babu wata wacce ta zo ta zauna da ita daga Cinkilawa, amma mahaifiyarta na zuwa ta yini, sannan ta koma. To bayan ya fito da 'yar jaririyar zaure aka mata addu'a ya karbe ta zai mayar da ita wajan mahaifiyarta sai ya iske wuta ta gauraye dekin har rufin dakin babu ta inda mutum zai fito. Babu kowa a tsakar gidan sauran matan su na dakunansu. Sai da Malam Yahuza ya yi ruri yana kiran "Jama'a ku taimake ni wuta!"
Sannan kowacce ta fito daga dakinta da gudu, maza daga qofar gida suka shigo ana ta zuba ruwa da qasa, amma ina abu ya ci tura, sai da daki ya qone kurmus Zuhuriya na ciki ko ihunta ma ba a jiyo ba, sai toka babu alamar bil adama."
Bakura ya gyara zama yayin da Sajida ta qurawa mahaifiyarta ido tana dubanta zuciyarta cike da mamaki hade da tunani mai firgitarwa ta qagu ta ji qarshen labarin, kwakwalwarta ta kasa tantance mata abun da yake shirin faruwa.
Umma Furera ta ci gaba da cewa, "Labarin rasuwarta ya iske mu muka dungumno daga Shanono muka iso Yan lanya don yin gaisuwa. Ba tare da doguwar magiya ba na roqi yayana Yahuza cewar ya ba ni 'yar in rike tunda ban taba haihuwa ba a lokacin. Nan da nan ya ce in dauka ya ba ni ita tunda ba mu da iyaye ni da shi ne kawai mu ka rage"
Sajida ta ji wani jiri ya fara tasowa daga cikin kwakwalwarta, ta dubi Umma Furera yayin da hawaye ya cika idonta ta fada cikin wata murya mai karkarwa "Umma, baki taba fada min kin taba rike wata 'ya ba, rasuwa ta yi ne daga baya?"
Umma Furera ta girgiza kai yayin da wata fargaba ta rufto mata.
Ta dubi maigidanta Malam Yakubu ta rushe da kuka ta ce "Malam ka fadawa Sajida gaskiya, yau ne ranar farko da ya kamata ta san gaskiya."
Sajida ta waiga da sauri ta dubi Malam ta fada cikin tashin hankali ta ce "Baba me yake faruwa ne? Ka fada min gaskiya."
Ta tashi da gudu ta tafi wajen lya Azumi (Innono) ta rike ta tana kuka. "Ki fada min abun da ban sani ba, mene ne yake faruwa ko ba ni da iyaye tsinta ta aka yi?"
Samira, Zahra da kannenta suka shiga rikitaccen tunani, sun kasa gane abun da zai faru.
Innono ta sharbe hawaye ta ce, "Ke ce yarinyar da Zuhuriya ta mutu ta bari. Ma'ana ke 'yar Zuhuriya ce da malam Yahuza ba Furera da Yakubu ne suka haife ki ba."
Ba ta rufe bakinta ba Sajida ta cukuikuye ta kame a gefe ta rusa kuka, saboda tashin hankali.
Bakura ya yi kabbara hade da hamdala ya dubi Sama ya ce "Allah Kai ne mai hikima, Kai ka san abun da yake boye. Ni ban san gaibu ba, amma na san tabbas akwai wani sirri na boye game da kamar da suka yi."
Umma Furera ta je wajen da Sajida ta qame ta dafa kanta gami da murza bayanta ta na kuka itama ta ce, "Sajida ki yi hakuri ki yafe mana, na san ba za ki ji dadi ba, ya kamata ki sani tuntuni musamman lokacin aurenki. Ban san yadda zan fada miki ba, kasancewar mun shaqu ko Malam baya so ki san babu wata alaqa a tsakaninku.'
Umma Furere ta zauna a gefen Sajida tana rungume da ita, ta ci gaba da cewa "Na karbi Sajida daga hannun dan uwana a bisa amana zan rike ta har aurenta. Bayan da aka yi sadakar bakwan mahaifiyarta Zuhuriya ko da yake Fatsima na ji mijin yana fada mata, don haka ya ce a mayarwa 'yar sunan mahaifiyarta Fatima, shi ne muke kiranta da Sajida tunda duk Fatima ce. Mun hadu da Iya Azumi a zaman makokin sau daya, amma ta yi fushi ta fice daga gidan mutuwar da ta ji labarin ni a ka bawa jaririya ba ita ba. Ta so a ba ta jikarta ta rike mahaifin Sajida ya qi amincewa, don haka da ta tafi ba ta sake waiwayar yarinyar ba, amma qanwarta ta taba zuwa ta nemo mu kuma ta zo bikin ita ce ta tafiwa da iya Azumi kayan biki , sai jiya da muka ganta kwatsam.
Na dawo gidana goye da jaririya, sannan na yi wa Malam bayani sosai ya yi farin ciki, kasancewar ni da shi dukka muna tsananin son haihuwa, Allah bai ba mu ba. Muka dinga qulla-qulla, muna tanade-tanaden kudin madarar da muka shayar da 'yar jaririya har Allah ya raya ta, ta fara cin abinci sosai. Na shaqu da Sajida, haka Malam ma, sajida ta kasance yarinya ce mai wayo da yawan suruu, don haka ne ma ko da wasa ba na fadawa kowa wannan sirrin cewa Sajida ba 'yata ba ce, haka shi ma Malam yake cewa 'yarsa ce ta cikinsa. Da ta isa sawa a makaranta ma Nursey School mai kyau muka saka ta.Akan keke yake kai ta, ya dauko ta, har ta shiga primary tana amfani da sunan Malam wato Sajida Yakub.
Allah mai amsa addu'ar bayinsa, kwatsam sai na ganni da ciki Allah ya ba ni ciki a lokacin da ya so in haihu na haifi da namiji muka sa masa suna Yahuza, sunan mahaifin Sajida kenan da Allah ya yi masa rasuwa tun tana da shekaru biyu kacal a duniya. Don haka Sajida da Yahuza suka taso a matsayin uwa daya, uba daya, ba tare da sun ga wani bambanci daga wajen Malam ko daga wajena ba."
Umma Furera ta yi shiru tana sharce hawaye da gefen gyalenta, yayin da kowa ya yi tsuru kamar masu zaman makoki.
Sautin kukan Sajida ne kawai yake tashi, yayin da ta miqe qafa a qasa ta kifa kai a kan kujera. Tana rusa kuka mai tsanani, gami da cewa, "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, ba ni da uwa, ba ni da uba ashe, ban san uwata ba, ban san ubana ba, babu wanda ya taba fada min gaskiya. Kakata wacce ta haifi uwata ce ta rage min amma ba ta taba neman in da nake ba. Sai yanzu? Ashe ba ni da kowa, ba ni da wa ba ni da qanwa, ko qani, ban san asalin garina ba, balle in san dangin uwata da ubana ba. Wannan baqin ciki ya ishe ni har gara a ce Allah Ya đauki raina in mutu in je in sadu da mahaifaina, zamana a duniya ba shi da amfani. Wayyo Allah Zuhuriyya, ban sanki ba, ban taba sanin kamanninki ba, ko a mafarki ban taba kwatanto ki a raina ba. Allah yayi miki gafara."


Please Login or Register in order to submit comment