Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

je in rakaka dakin wacce yau za ta ji dadin kalamanka, amma ba ni ba."
Ta mike tsaye zumbur ta rike kugu tana girgiza kamar mai shirin dambe, sai huci take tamkar kasa. Ba musu Bakura ya mike bakinsa cike da magana, haka dariya take son kufce masa, amma yana tsoron furtawa. Su na isa kofar dakin Sajida sai ya ji gabansa ya yanke ya fadi. Samira ta daga hannu za ta murda kofar ta bude, sai Bakura ya rike hannunta.
Ya ce, "Kar ki bude, mu je dakina ki taya ni kwana, ni ba sai na ganta ba."
Haushinsa ya sake rufe zuciyarta, ta fusge hannunta ta murda kofa ta tura kai cikin dakin, gamị da kwada sallama. Sun yi dayday a falo su duka kowacce ta lumtsuma cikin kujera mai laushi, sai lumshe ido suke yi. Ga A.C na ratsa sassan jikinsu, ga talabijin su na kallo.
Lokaci guda suka dago da idanuwansu suna kallon Samira, ta waiwaya bayanta ta tsuke fuska ta ce da Bakura. "Shigo mana."
Ya shigo cikin falon, yayin da idanuwansa suka dira akan Sajida kiri-kiri yana kallonta, kasancewar haske tar gashi ba ta bunjima hijabin nan na ta ba. Ba mayafi, ba dankwali tana zaune ta harde kafa tana saqe-saqen tuggu a zuciyarta. Kan ka ce kwabo Sajida ta murtuke fuska ta fara harbo masa kibiyoyin harara.
"Wai wannan yarinyar wacce irin kama su ka yi da Zuhurriyya haka kamar an tsaga kara ?" Bakura ya fada a zuciyarsa.
Ya yi karfin hali ya durkusa ya gaishe da tsohowar nan, yayin da su iyayye ma suka gaishe shi, ya amsa cike da fara'a, gami da cewa. "Me ku ke bukata a kawo muku?"
Su duka suka hada baki,
"Babu komai."
Samira ta yatsune fuska ta ce, "To amarya ga angonki na kawo miki, babu abinda zan ce sai addu'a, Allah ya bada zaman lafiya, ya kawo kazantar daki. Sai ku dunguma ki bishi dakinsa ni dai na tafi sai da safe."
Samira ta juya za ta fita Bakura ya yi zuruf ya bi ta a baya, suka fice.
Sajida ta ja wani dogon tsaki ta murguda baki ta ce,
"Wa ya ga amarya, amma kuwa kin yi batan kai da ki ka shigo min da wannan mutumin dakina."
Caraf Iyayye ta yi sauri ta toshewa Sajida baki, don kada su Samira su juyo ta.
Nan fa suka hau rokar Sajida akan ta tashi ta shirya ta je dakin ango. Saboda takaici ko kallonsu ba ta yi ba ta tashi ta shige uwar daki ta kwanta kan gado ko kayan jikinta ba ta cire ba.
A kofar dakin Samira suka tsaya suka dauki lokaci mai tsawo su na tataburza har da kokaye-kokaye. Bakura zai shiga dakinta, ita kuma ta ce ba zai shigar mata daki ba sai dai ya tafi dakinsa don ta san in anjima amaryarsa za ta je ta same shi.
Kalmar da ta fito daga bakin Bakura ita ta bawa Samira mamaki da ya ce "Ko Kur'ani ki ka ba ni zan dafa cewar Sajida ba za ta zo inda nake ba, saboda ba ta sona."
Wani kallo na takaici, gami da karka raina min hankali mana, haka Samira ta kalle shi ta tabe baki. Ta ce, "Ai kai kana sonta, tunda ka auro ta sai ku je can ku karata."
Ta yi wuf ta shige dakinta ta datse ta bar shi anan a tsaye. Ya yi shiru yana tunani, ya kalli kofar dakin Sajida, ya juya ya dubi dakin Samira sai ya girgiza kai ya yi murmushi, ya juya ya nufi dakinsa.
Yana shiga dakinsa ya tura qofa ya rufe yasa hannu a aljihunsa ya zaro wasu hotuna guda biyu ya ajiye a tsakiyar gadonsa. Hotunan Sajida ne, wanda aka dauke ta a tsakar gidansu dazu da yamma a wajen yinin bikinta.
Daya kafin ta yi wanka aka dauka, dayan kuma bayan ta yi wanka ta caba ado daidai lokacin da ta yi wannan murmushin nata aka dauka. Wato mai daukar hoton har ya wanko ya kawo masa shi ne ya bar sauran a mota ya zabo guda biyun nan wanda take ita kadai don ya tantance abinda ya ke so ya tantance.
Ya shiga bandaki, ya dade yana kwara ruwa a jikinsa, saboda duk jikinsa danko yake yi masa. Yana fitowa daure da tawul, sai ya zura doguwar riga 'yar yaloluwa marar nauyi. Ya taka gado ya kinkimo wata 'yar akwati akan wadurof ya zo ya zauna akan gado, ya baje wasu hotuna a tsakiyar gadonsa. Ma'ana hotunan Zuhuriyyarsa ne ya hada da hotunan Sajidarsa, don ya ga ta inda suka bambanta. Ai kuwa sak kamarsu daya, kirar jikin ma daya, ga dariya da murmushinsu iri daya. Sai mamakinsa ya sake daduwa. Surutai yake shi kadai cikin dare, kamar tababbe.
Hakika Bakura yana cikin wani hali domin akan ya san asalin wannan kama ya sa ya auro Sajida, amma har yanzu babu wata shaida da ta nuna masa alaka ko kadan tsakanin Sajida da Zuuriyya. Haka Bakura ya raba dare, sannan ya hakura ya kwanta.
Gajiya, gami da dogon daren da ya raba bai yi barci ba basu hana shi tashi da Asuba ya je masallaci ba. Ya na dawowa ya bi dakunan gidan gaba daya yana bugawa har da dakin Sajida.
Kowa ya tashi wuri-wuri ya shiga bandaki, don dauro alwala. Bakura kuwa da ya tabbatar kowa ya tashi sai ya shiga nasa dakin ya kwanta, saboda barcin da ya addabi idanuwansa ya sake kwanciya.
Samira kuwa tana farkawa bayan ta yi sallah, sai ta shiga kicin ita da kukunta suka shiga shiryawa yara 'yan makaranta abinci. Haka abincin mai gidanta da na Sajida da 'yan uwanta daban. Yau Samira ta sake zagewa wajen qara qawata abinci fiye da kullum, saboda tana so ta nunawa su Sajida bakin rijiya ba wajen wasan yara ba ne. Ta na so Bakura ya san ba irinta ake aurowa kishiya ba, saboda babu abin da amaryar za ta fi ta. Bayan komai ya dahu, ta dauko tsala-tsalan food fasks hade da plates da cokula da saving spoons hadaddu wadanda ta suyo su daga Saudiya na sarakai ne, domin an diga ruwan gwal da azurfa a jiki. Burinta ta burge qauyawan nan da suka zo gidanta da sunan amarya da qawayenta. Ta kira masu aikinta guda biyu Hajara da Grace suka dinga diba su na shigarwa dakin Sajida su na jerawa akan Dining table, yayin da farin ciki ya lullube zuciyar qawayen Sajida.
Sai kalmar "Sannu, mun gode." Suke fadi, daidai lokacin Sajida ta fito falo das da ita, ta yi wanka ta caba ado da wata atamfarta Super Holand kalar kore da ruwan dorawa (Green and ycllow) wacce ta sha dinkin riga da zani daidai jikinta. Ta kuwa nada dauri cas da ita kai ka ce ango ta yi wa wannan ado. Sai kamshi ne ke biye da ita a sanadiyar feshe jikinta da ta yi da turare (Designers).
Hakika yunwa ce taf a cike a cikin Sajida, kasancewar jiya ba ta ci abincin kirki ba. Dan yunwar dare ma ta so ta hana ta barci, bakin ciki ne ya hana ta tashi neman abinci cikin dare. Don haka ta yi farin cikin ganin wadannan galla-gallan warmers.
Kai tsaye Sajida ta haye kan tebur ta kalli kawayenta.
Ta ce, "Mai ci ta zo don ni ci zan yi, wanda ya ga bati ya kyale jahili ne. Wahalallun har sun gama abinci da sassafen nan, sai dai su dafa su ba ni dan ni babu wanda zan dafawa abinci a gidan nan, saboda ajiya aka kawo ni in ci in yi gaba."
Suka taso kowacce ta sami tata kujerar ta zauna.
Zainab ta dubi Sajida ta yi dariya.Ta ce "Sajida ba ki da mutunci."
Tsohuwa ta ce, "Ba zan hau tebur ba kar in fado saboda dadi ku zubo min nawa a kasa zan ci."
Tun kafin su Sajida su kai loma daya bakinsu suka fara santin kyawun cokulan da plates din nan. Ai da suka fara ci, sai suka ji cikin kunnuwansu ya dau kaikayi, saboda dadi. Tunda suke ba su taba cin abinci mai dadin irin wannan abincin ba. Wasu abubuwan cusawa suke ba tare da sun san sunansa ba. Kamar bangaren fruits irin su straw berry, inibi, duk sai dai su ganshi a talabijin ko a hoto ko kuwa su ga fukawar su.
Misalin karfe goma sha daya, Bakura ya farka daga barcin da yake yi, ya yi wanka ya fito a shirye tsaf sanye da wata shadda shudiya (blue), wacce aka yi masa gajeren dinki iya gwiwa, wato (boda), ya dora shudiyar hula. Kamar wadanda suka hada baki Samira ya iske a falo ta ca6a ado da wani shudin leshi, sai walkiya take.
Bayan ta gaishe shi sai ya shiga janta da wasa yana zolayarta, duk da ya san haushi yake bata shi kuwa dadin zolayar yake ji. Suka wuce kan tebur don karya kumallo, domin Samira ba ta iya cin abinci ita kadai, duk dadewar da Bakura zai yi a waje ko yana barci sai ta jira shi ya zo sun ci tare tun sanda suka yi aure.
Sun fara cin abincin kenan, sai Samira ta dube shi ta yi gatsine. Ta ce "Af, ya za a yi ka zo ka zauna kana cusawa cikinka abinci, ba ka damu da amaryarka ba, yaya ta kwana, ko me ta ci, ko me za ta ci?"
Bakura ya yi dariya ya ce,
"Ai bakuwarki ce, na san ba za ki bar ta da yunwa ba."
Takaici gami da daci ne ya dasu a zuciyar Samira. Ta tabe baki ta ce, ai gara aje a kira ta ta zo mu hadu mu karya tare ka ga sai ka fi jin dadin cin abinci kana yi kana kallonta, don na ga alamar har wata nutsuwa ka ke idan a gabanta ka ke."
Bakura ya kwashe da dariya Ya ce, "Kishi, kishi, Samira kishi sunanki daga yau. Yaushe aka kawo Sajidar da har ki ka lura ina nutsuwa idan a gabanta ne? Jiya-jiya ne fa."
Haka dai suka dinga fafatawa har suka gama cin abinci.
Bakura ya yi zunbur ya mike, gami da duba agogo. Ya ce, "Kaduna nake so in je akan maganar wadannan motocin da nace an turo min daga America sun zo, sai kin zaba kin darje kafin kowa ya zaba, saboda ke ce gimbiyar gidan."
Ta harare shi, ta ce, "Ka ce dai ka yi sauti a siyowa amaryarka mota ba ni ba."
Ya kwashe da dariya ya suri mukullin mota yana shirin ficewa.
Ta sa hannu ta kamo hannunsa, ta ce, "Ka fita ka je ina? Ai dole ka shiga kaga lafiyar abar qaunarka, kafin ka fice tunda ba ita ta kawo kanta ba, kai ka ajiye ta."
Bakura ya yi dariya ya ce, "Kai! Kai! Nima na jawowa kaina, na zama kamar waina sai juya ni ake ta ko'ina. To mu je ki raka ni dakin."
Samira na gaba yana biye da ita har falon Sajida. Sajida na ganin su ta daina fara'a ta dauke kai ta juya musu keya. Sai kawayen ne suka gaishe su. Su Kuma su Samira suka gaishe da tsohuwa.
Tsohuwa ta amsa, gami da cewa "mu yanzu za mu koma gida, ga Sajida nan amana, kuma ku yi hakuri da halinta, har Allah Ya sa ta gane."
Samira ta danne zuciyarta ta kalli Sajida ta ce, "Amarya ina kwana. Ko ba ki gaisa da ni ba kya gaisa da angonki ai ko."
Sajida ta yatsune fuska ta tabe baki ta amsa gaisuwa a ciki-ciki. Bakura kuwa ba a raba shi da qurawa Sajida ido. Ya tafi can wata duniyar tunani yana tuno kamannin Zuhuriyya, yana hadawa da abinda idanuwansa suke gane masa.
Kamar daga sama yaji muryar Samira ta katse masa tunaninsa da yake.
Ta ce "Sai ka sa direba ya kai su gida, kuma ka kawo kudin budar bakin amarya a bawa qawayenta su raba."
Nan da nan qawayen amarya suka warware kowacce fadi take, "A ba mu kudin siyan bakin amarya."
Bakura ya yi dariya ya ce, "To zan bawa Samira za ta sallame ku."
Ya juya ya fice, Samira na biyo da shi su na tafe Su na kallon dakwalkwalallen darning table din Sajida kaca-kaca da abinci da kwanukan da suka ci. Kowanne a watse ba tare da an kinkintsa wajen ba, balle a kwasa a kai kicin. Kowacce da ta gama ci sai ta koma Kan kujera ta nade. Don haka Samira na fita ta kira Grace ta ce ta shiga ta kwaso mata kwanukanta ta gyara musu kan tebur.
Bakura da Samida suka dinguma wajen motoci, ya zabi wacce yake so ya shiga, ta zo ta dafa murfin mota.
Ta ce, "Kawo kudin 'yan mata da ka yi alkawari."
Ya ce, 'Ke za ki sallame su ba ni ba, tunda baqinki ne."
Kafin ta ce wani abu ya jawo kofar motarsa ya rufe ya ja dogon ribas yana sheka mata dariya. Ta tsaya tana kallonsa kawai tana takaicin wannan al'amari, domin ita tafi jin haushin kanta da take shiga safgarsa da amaryarsa, ga shi ta zame masa abar tsokana tamkar wata kakarsa. Ta gyada kai ta yi qwafa, gami da cije baki alamar za ka dawo ka same ni.
Ta na shiga falo ta yi kicibus da qawayen amarya da tsohuwa sun fito za su tafi. Cikin fara'a take yi musu magana. "Ba dai har kun fito ba, ba za ku yinin mata ba har ta sake warwarewa ba?"
Su ka amsa cike da murmushi, "A'a daga gida aka yi waya aka ce mu dawo."
Samira ta ce, "To ku jira ni ina zuwa."
Ta shiga dakinta zuwa wani dan lokaci ta fito dauke da kudi, gami da wata leda a shaqe da sabulai kala-kala.
Ta miqa musu ta ce "Ga shi dubu ashirin ce yace a baku, wannan kuma sabulai ne kwa yi wanka ni na baku."
Suka ji wani tsagoron farin ciki ya rufę su, sai suka zube su na godiya.
iyayye ta lankwashe murya ta ce, "Hajiya Samira, gaskiya ba zan 6oye miki ba ko a bayan idonki za mu fada kina da kirki, kuma samun mace kamar ki sai an tona a cikin mata."
Samira ta yi dariya ta ce, "Ba komai ai mun zama daya. Ku je bakin get ku tambayi Lurwanu direba ku ce na ce ya kai ku gida da mukullin mota a hannunsa."
Haka tsohuwar nan ta dinga shi wa Samira albarka, har suka fice.
Samira ta dawo ta zauna a falo tana huci, tana fitar da zazzafar iskar da ta mamaye huhunta. Saboda ba karamin karfin hali ta yi ba wajen danne kishinta, duk wannan kissar da kisisinar ba ta kai zuci ba. Zuciyarta tafasa take tamkar ruwa akan wuta. Daman Sajida jira take kowa ya watse, Allah- Allah take duk su tafi su barta ta kunna sabuwar wayar da Abdulmajid ya aiko mata, don su yi magana. Fitar su iyayye ke da wuya ta dauko wayar ta saka a caji, ba tare da ta bari cajin ya cika ba ta kunna, gami da saka sabon layi da recharge card ta matso lambarsa wacce daman tuni ta haddace ta akai. Koda kuwa daga barci aka tashe ta za ta karanto lambar a Kwakwalwarta.
Bugu daya ya dauka, duk da bai gane kowace ce ba, domin bai haddace sabon layin ba. Daga yadda yake amsawa ka san baya cikin farin ciki, don da kyar
yake magana. Ko tashi daga kan shimfidarsa bai yi ba. ya sake kallonta.Kai ka fi cancanta

Balle karya kumallo, bashi da shirin yin wanka ya fita. Daga dukkan alamu zafin rabuwa da Sajida ya shige shi, don a da yana ganin wasa ne ba auren za ta yi ba yanzu kuwa ya tabbata. Har suka gaisa bai
fahimci ita ce ba, sai da ya ji kalamanta masu ratsa masa jiki, sannan ya farga. Kan ka ce kwabo ya ware murya.
Tambayar da ya fara jero mata ita ce, "Da fatan dai baki yarda wani abu ya hada ku ke da wannan banzan mutumin ba kö? Ina fatan ba kya sakar masa fuska, balle ya yi hira da ke ko?"
Ta amsa masa da, "Shi ya isa ma ya matso kusa da ni. Ai ko kallon inda yake ba na yi."
Ana badakala, haka Sajida da Abdulmajid suka dau lokaci mai tsawo su na waya, har sai da kudin wayarta ya qare, shi ma ya kira kudin wayarsa ya qare. Sai ya turo mata text massage cewar ta yi hakuri idan ya fita waje zai sa kati zai kira ta.
Yau farin ciki a zuciyar Sajida baya faduwa, ta sumbaci wayar ta rungume filo, gami dą lumshe ido tamkar tana tare da Abdul a kusa da ita. Yini guda Sajida na nade a daki, sallah ce ke tashinta daga kan gadonta.
Grace ce take kai kawo tsakanin kicin da dakin Sajida. Samira ba ta gaji ba ta aika aka kai mata abincin rana, da a ka kai na dare aka kwaso kwanukan rana. Ba kunya ba tsoro Allah Sajida take nadar abinci ta koma ta kwanta. Bakura bai shigo gida ba sai bayan sallar Isha'i.Bayan ya yi wanka ya ci abinci ya zauna a babban falo, tare da 'ya'yansa da uwar gidansa Samira. Ya taya yara Home work, suka yi 'yar hira, sannan ya sallami kowanne yaro ya je ya kwanta. Samira ma ta yi zumbur ta mike, gami da yi masa sallama ta nufi dakinta. Bakura ya yi kiran duniyar nan Samira ta qi dawowa, ta shige dakinta ta rufe. Yana qoqarin kiranta a waya ta murtsike wayar ta kashe. Ya dade a zaune, sannan ya miqe don tafiya dakinsa ya kwanta, domin ya gaji.Daidai qofar dakin Sajida ya jiyo muryar Sajida na hira har da kyalkyala dariya. Hakan ta ja hankalinsa ga tsayawa tsai yana sauraro. Da farko ya dauka talabijin ce, amma da ya kara kunnensa ya tabbatar muryar Sajida ce ya yi mamaki, sai ya shiga tunanin da wa Sajida take hira haka, to ko qawayen nata ba su tafi ba ne? Sai ya yanke hukuncin shiga dakin ya gani. Yana murda kofa, sai qofa ta bude ya ci sa'a a bude take ba an datse ba. Tsuru-tsuru ya ga Sajida ita kadai, ta yi daidai a kan doguwar kujera tana waya. Sanye take da atamfar dazu, amma kanta babu dankwali ta zubo gashinta har baya tana shafawa, Saboda dadin hira. Ya kalle ta, ta kalle shi kallon Kallon ake yi.
Sai yaji ta ce, "Ka gan shi ma ya shigo dakina ya tsaya yana ta muzu-muzu da ido, ka san kallo ne da shi kamar wani baqauye."
Da jin haka sai Bakura ya sami kújera a setinta ya zauna cike da mamaki.
Can ya yi qarfin hali ya tambaya. "Da wa kike waya, Sajida?"
Ta fada cikin gadara ta ce, "Abdulmajid."
Yadda ta ga Bakura ya tunkaro ta a fusace kamar mai shirin mauje ta, sai ta tsorata, ta wurgar da wayar ta qanqame akan kujera.
Bakura ya tsugunna ya dauki wayar a qasa, sai ya ga har yanzu wayar a kunne take Abdulmajid ne ke ta magana. Bakura ya kara wayar a kunnensa yana sauraronsa, kalmar da yaji yana cewa. "Baby, are you there?"
Bakura ya yi gyaran murya, gami da' cewa, Ba baby ba ce, wannan mai gidanta ne."
Abdui majid ya fada cike da gadara, "Alhamdulillahi, daman ina nemanka. Kai wawa ne, banza, jahili, ta yaya za ka auri yarinya bata sonka, saboda kana da kudi? To wallahi ka kuka da kanka.
idan ba ka saki Sajida ba sai na sa an farfarda min
cikinka."
Bakura ya yi murmushin haushi ya gyada kai. Ya ce "Yaro, idan ni da kai zaa hado mutane masu hankali mu zauna akan teburi daya kowa ya bada labarin abin da ya faru, to jama'a za su tantance waye wawa, banza, jahili. Ka san kai ne wawa, tunda ka bari na kwace maka Sajida a cikin dan qanqanin lokaci, alhali kun dade tare har kun shaqu, don da kana da wayo ba za ka bari in kwace ta daga hannunka ba. Idan jama'a suka ji haka zasu tabbatar maka kai banza ne, tunda aka baka dama ka fito ka aure ta ka kasa fitowa ka qi yin amfani da damar da aka ba ka, har sai da ta subuce maka. Sannan daga karshe ko jama'a ba su fada maka ba, kai da kanka ka san kai jahili ne, marar tarbiyyar

Please Login or Register in order to submit comment