Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sun gama cin abinci, domin ita ma ruwan shayi kawai ta kurba tun safe kasancewar idan ba da Bakura ba, bata iya cin abincin kirki.
Bakura ya miqe ya ce da Samira "To zo ki raka ni in gaishe su."
Samira ta fada cike da mamaki, "Wai ni ce zan yi maka zaman auren ne Abban Yagana? Ka ji mutum, na san sanda ka je ka yi durqushe-durqushe da gaishe-gaishen dangi har aka baka 'ya? Babu inda zan je, ka je kai kadai kun fi kusa."
Bakura ya tafi fuskarsa cike da murmushi, ya qwanqwasa qofar falon Sajida cikin ladabi ya murda ya bude. A falo ya iske su, su dukka ukun su na zaune a qasa akan kafet. Sajida na ganinsa ta tsuke fuska ta kawar da kai gefe kamar ta ga maqiyinta har sai da Umma Furera ta lura da haka, ta shiga tunanin ashe daman har yanzu da matsala a zamansu? Ashe Sajida ba ta saduda an zauna da ita lafiya ba?"
Yayi sallama ya zo a nutse ya durkusa a gabansu yana mai sunkuyar da kai kasa, don kunya da girmamawa. Ya gaishe su suka amsa dukkansu a kunyace.
Umma Furera ta ce da shi, 'Wannan kakar Sajida ce ta zo jiya daga Gashuwa, don ba ta samu ta zo biki ba, sunanta lya Azumi."
Bakura ya ce "Ai jiya Malam ya fada min, Allah sarki ya yaya hanya?"
Daidai lokacin ne Bakura ya dago ido ya dubi Iya Azumi.
Ta ce, "Angona lafiya kalau."
Ita ma ta na dubansa, amma wannan karon duban da suke yiwa juna ya tashi daga surukai ya koma duban qeqe-da-qeqe mai dauke da alamar tambaya. Duba ne irin na ban mamaki da tsantsar gigita mai hade da tashin hankali tamkar su kurma ihu, haka yanayin kowannensu ya canja. Karkarwa Bakura yake yana nuna iya Azumi ita ko hannu ta dora a ka ta na hawaye da salati.
"Lafiya, me ya faru?" Haka Umma Furera da Sajida suke tambayarsu a gigice suma
. Babu wanda ya iya ba su amsa a ciknsu.
Bakura ya yi karfin hali ya ce "Innono"
Ta amsa masa "Na'am, Bakura kai ne?"
Sai su duka suka fashe da kuka mai tafe da zazzafan hawaye.
Babu kalmar da take fitowa daga bakin Innono sai "La'ilaha illallahu Muhammadul Rasulullahi sallallahu alaihi wasalam, Bakura kana raye ashe?"
Wannan dogayen salatai ne yasa Samira shigowa cikin dakin, don ta ganewa idanuwanta abinda ke faruwa.Ta iske Bakura tsaye ya kifa kai da bango yana wani kuka mai tsanani, har idanuwansa sun yi jawur.
Ta riklqe shi a gigice tana tambayarsa lafiya. Haka Sajida da mahaifiyarta suka shiga wannan rudanin suka riqe Iya Azumi su na tambayarta "lafiya".
Ta ce, "Labarin yana da tsawo, yana da ban mamaki."
Da jin baka sai Umma Furera ta dauko waya ta danno lambar maigidanta ta na sharbar kuka.
Ta ce "Malam, ka taho gidan Sajida yanzun nan akwai magana."
A gigice ya ke tambayarta "Lafiya, guduwa ta yi?"
Umma Furera ta ce "Ko daya babu abinda ya faru, illa Iya Azumi ce da Bakura suka shaida juna su na ta koke-koke. Na san lallai akwai wani 6oyayyen al'amari sun san juna. Ka san kuwa dole yau a fayyacewa Sajida komai."
Malam ya fada cikin sauri "To gani nan zuwa.
Hankalin Sajida ya tashi matuqa da jin bayanan Ummarta. Sai ta dora hannu a ka ta rusa kuka, ta ce, "Umma, ba dai tsintata ku ka yi ba, ba ke ce ki ka haife ni ba ne?"
Umma Furera ta girgiza kai ta ce, "Ni na haife ki Sajida ba tsintarki na yi ba."
Sajida ta koma gaban Iya Azumi ta durusa, ta ce "lya ki fada min gaskiya me ya faru da ni?
lya Azumi ta runtse ido hawaye ya surnano sai ta nuna Bakura. Ta ce "Bakura ne ya fi kowa sanin ko ke wacece, amma ni ban sani ba."
Sajida ta miqe da gudu ta nufi inda Bakura ke tsaye ta durqusa a gabansa cikin kuka.
Ta ce "Bakura ni wace ce? Me yake faruwa ne?"
Bakura ya matse hawaye yasa hannu ya tashi Sajida tsaye, Ya ce, "Je ki ki zauna bari Malam ya zo, bari su Zahra su dawo daga makaranta, sannan in zo in bayar da tarihin rayuwata. Zan sanar da ke ko ke wacece, amma kada ki damu kanki ki na da uwa, kina da uba ba 'yar tsuntuwa ba ce."
Sajida ta sulale ta zauna zuciyarta na dukan uku-uku, qwaqwalwarta ta kasa shiryo mata abinda zai iya kasancewa. Fatan ta dai kar ace ba Furera da Malam ba ne suka haife ta ba, kada dai ace Bakura ne Babanta..
Haka Samira ta shiga wannan hali na mamaki da tambayoyi iri-iri. Umma Furera ma kukan take da alama ta san komai.
Bakura ya fice, Samira ta bi shi da sauri zuwa qofar fita. Ta ce da shi "Ina za ka je ne?"
Ya tsaya cak ya ce da ita "Masallaci zan je yanzu zan dawo."
Samira ta tambaya
"Me yake faruwa ne Malam?" Ya ce "Yau zan ba ku tarihin rayuwata kacokan. Yau zan bayyana muku ko ni wanene, kuma daga ina na fito, mene ne asalina? Yau za ki ji ko wacece Zuhuriyya kuma ya ya take a wajena. Yau za ki tabbatar da maganata da na ce Sajida ta yi kama da Zuhuriyya. Yau za ki tabbatar da dalilina da na dage na auri Sajida dan ada ban yarda na fada muku komai ba."
Samira ta tsaya tana kallon Bakura jikinta a sanyaye. Ta fada cikin cikin siririyar murya mai tafe da rashin kuzari,
"A dawo lafiya."
Ya fice da sauri zuwa masallaci. Fitar Bakura ba Jimawa sai ga 'yan makaranta sun dawo, wato Zahra da qannenta suka yi sallama suka shigo. Da sauri Samira ta jawo su gefe ta ce da su "Ku yi sauri ku je ku cire kayan makarantarku, ku yi sallah, ku ci abinci akwai meeting a dakin Sajida in ji Abbanku."
Cike da mamaki suke tambayarta. "Wanne irin mecting?"
Ta ce, "Ku je ku yi abinda na fada mu ku kawai, ko mene ne ma za ku ji in an je can."
Har Zahra ta shiga daki ta ajiye jakarta sai ta ji zuciyarta ta kasa kwanciya ta yi wuf ta fito tana neman mahaifiyarta ta leka ko'ina ba ta ganta ba, sai ta leqa dakin mahaifinta a can ta ganta.
Samira na ganin Zahra ta tambaye ta. "Lafiya?"
Zahra ta ce "Mama qararmu ta sake kaiwa wajen Abba?"
Samira ta ce "A'a, wani boyayyen al'amari Allah Ya bayyana, wata kakar Sajida ce ta zo daga wani gari. Ashe Abbanku ya santa, don haka dole Sajida tana da dangantaka da Zuhuriyya."
Mamaki ya rufe Zahra ta ce, "To bari in je in yi sallah in zo mu ji labarin."
Bakura da Malam Yakubu ne suka shigo kai tsaye dakin Sajida suka wuce suka iske Umma Furera, Sajida da Iya Azumi kowanne zugum ya doka tagumi babu mai cewa komai. Su ka sami kujera suka zauna. Haka Samira da 'ya'yanta suka shigo a nutse suka sami waje suka zazzauna. Bayan an gaggaisa sai Bakura ya fara gabatarwa iya Azumi 'ya'yansa da matarsa Samira.
Ta jawo Zahra jikinta ta rungume ta shafa kayukan, mazan tana mai shi musu albarka tana hawaye.
Fargaba marar musaltuwa, haka dimbun tashin hankali ne ya cika zuciyar Sajida. Ba Sajida kadai ba kowa ya qagu ya ji labari.
Bakura ya matse hawaye zazzafa daga cikin idanuwansa ya fara magana cikin wata marainiyar murya, mai nuna tsananin damuwa da alhini.Kai ka fi cancanta


LABARIN BAKURA
Ya ce "Sunana Muhammad, sunan kakana ne wanda ya haifi Babana aka saka min don haka ake kirana da Bakura wato Babban Baba. Ni haifaffen garin Mangono ne a cikin kasar Maiduguri. Sunan mahaifiyata wacce ta haife ni sunanta Fatukamba, Mahaifina kuwa Usman ana kiransa da Bawa. Na taso cikin matsananciyar rayuwa marar gata, kasancewar iyayena talakawa ne liqis, talaucin da har ma ya kai mu da yin bara, don haka iyayena almajirai ne masu bara da roqo.
Dadin dadawa mahaifiyata tana da larurar tabin hankali , mahaifina kuma makaho ne, wanda bai taba ganin hasken rana ba. Dama a haka suka hadu suka yi aure, suka haife ni."
Malam ya gyada kai ya ce "Allahu Akbar, Allah mai girma, tsarki ya tabbata ga Ubangijin talikai."
Samiia da 'ya'yanta suka bude baki su na mamakin abinda Bakura yake zanowa. Saboda bai taba basu irin wannan tarihin ba. Haka Sajida ta tsura ido ta na kallonsa zuciyarta cike da zulumi.
Iya Azumi (Innono) sai gyada kai take ta na cewa "Haka ne, duk an yi haka."
Bakura ya matse hawaye ya ce "Saboda tsantsar talaucinmu har ba mu da takamaiman gidan zama, a bakin bola a cikin kasuwa muke yini ni da mahaifiyata, mahaifina kuma a bakin tasha yake zama yana bara. Idan dare ya yi sai mu je bakin shagon kasuwa ko bakin tasha mu shimfida kwalaye mu kwanta, saboda an kore mu daga gidan haya. Hayar gidan kara dakin bukka ma talauci ya hana iyayena su biya kudin haya.
A lokacin duka-dukka shekarana uku kacal a duniya. Rigata daya ta wani yadi fari, saboda datti ya zama baqiqirin ko wando ba ni da shi, haka nake rayuwa. Bayan busasshiyar majina da hawaye a idanuwana sanoda ba a yi min wanke. Bakina kuwa dambar yake da busasshen koko, kamar yadda aka ba ni tarihi.
Ina cikin wannan hali na wahala da talauci, Allah (S.W.A) ya Jeho min mai agaza min, wacce ta zame min haske a lokacin duhu a cikin rayuwata, wacce ta kula da ni har na girma, wacce ta wanke min dattin da ya addabe ni, wacce ta kwantar da ni a daki na daina barcin bakin titi, wacce ta sadaukar da rayuwarta a kan ta ga na rayu. Ta saka ni a makarantar allo da boko, har na zama yadda nake a yanzu."
Sai Iya Azumi tą rushe da kuka kamar yadda Bakura ya fara kuka ya kasa ci gaba da magana. Kan ka ce kwabo idanuwan duk wanda yake wajen ya cika da hawaye, manyansu da yaransu.
Zahra ta sharbe hawaye ta ce "Wacece wannan Abba?"
Bakura ya ce "Wannan ita ce wacce nake baku labari, wato Zuhuriyya."
Malam ya ce "Oho, ita ce Zuhuriyyar da duk kadarorinka sunanta ne ka saka?"
Bakura ya gyada kai ya ce "Ita ce Zuhuriyya, yanzu za ku san kowace ce Zuhuriyya? Kuma me yasa nake ji da ita a rayuwata na kasa mantawa da ita."

WACECE ZUHURIYA?
Bakura ya gyada kai ya sharce hawaye da bayan hannunsa ya sunkuyar da kai qasa kamar mai tunani, ya dago ya dubi jama'ar da ke zaune a falon.
Ya ce "Zuhuriya ita ce uwata, ita ce ubana, ita ce yayata, ita ce qawata. Ba ni da kowa a duniya sai Zuhuriya. Allah shi ne gatan bawanSa sannan Zuhuriyya ita ce gatana. Ban san kowa a rayuwata ba sai Zuhuriya, tun daga yarinta har izuwa girmana."
Daga dukkan alamu ba su fahimci abin da Bakura yake nufi da wadannan kalamai da ya fassara Zuhuriya da su ba. Akwai alamar daure kai da zuzurfan tunani a zuciyoyinsu.
Zahra ta ce "Abba, da farko ka ce kana da iyaye har kuna bara tare sannan ka ce Zuhuriya ce uwa ita ce uba? lyayenka sun rasu ne?"
Bakura ya yi murmushin qarfin hali ya girgiza kai ya ce "Alhamdulillah, da kika yi min wannan tambayar, Mahaifana ba su rasu ba. Na kira Zūhuriya da wannan Sunan na uwata kuma Ubana, saboda wasu dalilai masu yawa. Kamar yadda na fada muku a cikin kasuwar garinmu Mangono muke yini a cikin kasuwar ma a bakin bola muke zaune. Tun daga safe har dare, wata rana mu kwana a nan idan kuma an koro mu daga cikin kasuwar mu fito waje mu kwana a waje ko mu je bakin tasha mu kwana in da mahaifina yake bara."
Kuka ya kecewa Zahra don tausayi, yayin da idanuwan Samira ya cika taf da hawaye. Abubakar kuwa tuni ya shiga wani hali na daurewar kai, duban mahaifinsa yake ta yi, tamkar hoto, domin bai zaci mahaifinsa ya san wani abu mai su na talauci a rayuwarsa. Malam kuwa ya shiga rudani yana zuci-zuci ya ji qarashen labarin da yadda aka yi Bakura ya san lya Azumi.
Sajida kuwa gaba daya qwaqwalwarta ta rikice, domin ta ji labarin Bakura bai shafe ta ba, to me yasa Umma Furera ta ambaci sunanta a waya'? Me yasa Iya Azumi ta ce ta tambayi Bakura shi ya fi kowa sanin ta? Ta ina Bakura ya santa har ya fi kowa saninta? Wannan al'amari ya razana zuciyar Sajida. Babu yadda za ta iya katse shi, dole ta ci gaba da sauraron Bakura, amma ta qagu ta ji qarshen labarin.
Bakura ya ci gaba da cewa "Na hadu da Zuhuriyya a cikin kasuwar garinmu Mangono, a daidai inda nake kiransa da gidanmu wato bakin bola, ita kuma sun zo wani shago siyayya, shagon yana daf da bolarmu. A lokacin ina da shekaru uku, Zuhuriya na da shekaru goma sha hudu a duniya. Amma a lokacin an dade da yi mata aure har ta haifi da kafin a yi suna ya rasu. Sun zo Mangono ne ita da mahaifiyarta ganin danginsu. Domin mahaifin Ummata Zuhuriya Alh Umar dan asalin garin Mangono ne, kuma ma dan sarauta ne a lokacin ya rasu sai Yayansa shine hakimin garinmu haka aka ba ni tarihi."
Samira ta buga tagumi tana duban Bakura, duba cike da tausayi tana mamakin duk wannan shaquwar da suka yi amma bai taba zama ya faiyace mata irin wannan tarihin rayuwarsa ba sai yau da yake fada take ji.
Ta tambaye shi "daga nan ya aka yi?"
Bakura ya yi shiru, saboda tsananin zafin da zuciyarsa ke yi. can ya ci gaba da cewa."Ina qarami sosai, amma mahaifñyata tana dukana, dukan da ko wani qato ake yi wa sai ya kwanta jinya, amma ba laifinta ba ne kamar yadda na fada muku a baya tana da tabin hankali. A daidai lokacin da Ummata Zuhuriya da mahaifiyarta da kuma qanwar mahaifin Zuhuriya suke cikin shago su na siyayya ni kuma na tafi yawo cikin kasuwa. Mahaifiyata ta kamo ni ta kawo ni bakin bola ta jibge ni yayin da ta samo bulala ta yi ta duka kamar ta sami casar gero. Bulala ta kakkarye tasa hannu ta daka har ta gaji sannan ta saka haqoranta ta cije ni bakina ya fashe, goshina ya yi loti, yayin da bayana da duk ilahirin jikina ya daddare ya yi shatin duka. Tana dukana tana fada tana cewa, "Indara na'aduwa kozina famdime."
Malam ya ce "Me take cewa kenan?"
Zahra ce ta fassara musu domin ta fi sauran qannenta jin yaren.
Ta ce "Abin da take cewa shine ina kake da shi, inda ya fi nan bakin bola?"
Iya Azumi ta ce "Haka aka yi kuwa, hankalinmu ya tashi, musamman Zuhuriya har kuka take saboda tausayin yaron nan, abin ka da mai son yara domin Zuhuriya Allah Ya yi mata son yara."
Gaba daya suka juyo su na kallon Iya Azumi, duba na mamaki.
Sajida ta tambaya cike da mamaki "lya Azumi, ya aka yi ki ka sani kina wajen ne?"
Iya Azumi ta gyada kai ta ce "Ina wajen, ai muna tare da Zuhuriya a cikin kantin."
Bakura ya ce "lya Azumi ita ce mahaifiyar Zuhuriya, wacce ta haife ta."
Kamar an tsikara musu allura haka kowa ya zabura ya waiga yana duban Iya Azumi. Daidai lokacin kowa ya gyara zaman don jin labari, don labari ma yanzu aka fara.
Sajida ta ce a ranta "Kenan idan Iya Azumi kaka ce a wajena, ashe ina da dangantaka da Zuhuriya. Ashe Zuhuriya 'yar uwar Umma Furera ce kenan?"
Iya Azumi ta ci gaba da cewa "Zuhuriya ta tambayi mai shagon da muke siyayya a shagonsa. me yasa take dukan dan qaramin yaron nan da bai wuce shan nono ba?"
Mai shagon ya yi murmushi ya ce, "Ai tana da tabin hankali. Dukan yau ma kadan ne ai, wata ran tana yi masa wanda ya fi haka." Zuhuriya ta fashe da kuka tana. Ta ce masa "Me yasa bakwa kwatarsa idan tana dukansa?"
Ya ce, "Ai babu mai iya zuwa kusa da ita idan tana dukansa, zafin rai ne da ita idan ka je sai ta hada da kai."
Zuhuriya ta sake tambayarsa "Ina Baban yaron, ai da an kwace shi daga hannunta, don kar ta kashe shi."
Mai kanti ya ba ta amsa, "Baban yaron makaho ne, shi ma almajiri ne, bara yake."
Ta ce" ko a dangi ba za'a sami mai daukarsa ba?"
Ya ce, "Ina ji babu, amma wasu sun so su dauka ta hana su. Ai ba za ku tausayawa yaron nan ba sai idan uban ya kai shi wajen wanzami ya yi masa aski kwalkwal. Yini take tana dukan kan yaron nan, wai sai ta ci ladan aski. Duk juyin da ta yi sai ka ji raff-raff ta dalla masa duka a kai, sai ka ji ya dau kuka. Yini suke 'ana abu daya har sai gashi ya fito akan sannan yake hutawa."
Bakura ya kwashe da dariya, sannan kuma ya fashe da kuka ya girgiza kai alamar tausayawa kansa da kansa.
Iya Azumi ta ci gaba da cewa "Tun a lokacin Zuhuriya ta je wajen yaron ta goge masa hawaye ta ba shi alewa, ya yi shiru ya daina kuka. Ta bawa mahaifiyarsa sadaka, sannan ta dawo shagon da muke zaune.
Ta dube ni ta ce da ni, "Innono (sunan da suke kirana kenan) ina son yaron nan, ina so in dauke shi in riqe shi kamar dana tun da yaron da na haifa ya mutu."
Ni kuma na zazzage ta na ce kada ta sake cewa za ta dauki wani yaro don ta rike. Dalilina kuwa shi ne daga nesa muka zo baqunta tafiya za mu yi, idan muka tafi kuwa a shekara biyar ba za mu dawo ba don jifa-jifa muke zuwa, saboda nisa ga tsadar kudin mota bamu da hali da kyar muka hada wannan kudin motar da muka zo da dan abin tsaraba. Gashi mahaifin Zuhuriya ya dade da rasuwa na yi wani auren a Cinkilawa can qaramar hukumar Warawa dake kusa da lahadin makoli a hanyar Wudil cikin jihar Kano. Da Zuhuriya na je garin a matsayin agola, saboda ita kadai ce 'yata a duniya na wi yarda dangin mahaifinta su karbe ta a Mangono. Ita ma Allah cikin ikonsa ta sami miji a Cinkilawar na aurar da ita tana da shekaru goma sha daya a duniya. Ta samu ciki ta haihu kafin a yi suna yaron ya rasu. Bayan ta yi arba'in ne na ce to ta shirya in kawo ta Mangono ta gaishe da dangin Babanta saboda sun dade ba su hadu ba ko bikinta ma ban samu na fada musu ba, mijina ne ya wakilce su. Dan haka sai naga ta ina? Ta ya ya za mu dauki wata dawainiyar bayan muma muna ta kanmu a can, don haka na hana ta. Ta yi ta kuka tana yi min magiya har muka isa gida. Kowa ya fara tambaya me aka yi wa Yagana take kuka, domin su a can dangin uban Yagana suke kiranta. Ni da ita babu wanda ya fada musu abinda ya faru.
Kamar yadda Bakura ya shaida muku a baya yayan Babanta shi ne hakimin Mangono, don haka hakimi da kansa ya kira ta, don yana jiyo hayaniyar mata a tsakar gida su na yi da bakin su su na tambayarta dalilin kukan da take. Ya tambaye ta sannan ta fada masa abun da take so, da yake qaramin gari ne kowa ya san kowa sai ya yi dariya.
Ya

Please Login or Register in order to submit comment