Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidanka. Ka yi tunani ka samo måna mafita, nima zan je in yi tunani."
Malam ya kashe waya ya bar Bakura nanike da waya a kunne, tamkar gunki. Ya kasa ajiye hannunsa qasa, don kidimewa da tsananin tashin hankali. Babu abin da yake masa yawo a cikin kwakwalwarsa da zuciyarsa, sai kalmar Malam KAI KA FI CANCANTA ka aurar da Sajida! KAI KA FI CANCANTA ka samo mata miji!"
"Cafdi jam! Abun da kamar wuya." In ji Bakura.
Bakura ya ji a ransa shi ya fi CANCANTA ya auri Sajida amma rana quna, inuwa quna, shi da wanne ido zai kalli Samira ya ce zai auro Sajida? Irin wannan falli da ta fara tayarwa tun kafin ta gano gaskiyar magana? Ko kuwa da wanne ido zai dubi 'yarsa Zahra ya ce zai auro yarinyar da ta so ta nakasta ta? Da wanne ido zai dubi Sajida ya ce ya zo
neman aurenta, shi da ta furta masa da bakinta ta tsane shi? A wacce hujja yana ji yana gani zai je ya jajobo fitsarartiyar yarinyar da ba ta jin maganar kowa, sai ta saurayinta? Ko da wanne ido zai dube ta ya ce ta rabu da rabin ranta ta zo su zauna? Sannan da wanne ido zai dubi Malam ya qi share masa hawayen da yake zuba saboda ya rasa yadda zai yi da 'yarsa a matsayinsa na Malaminsa tamkar mahaifinsa ya dauke shi? Daga qarshe kuma Bakura yake tambayar zuciyarsa wanne tsautsayin ne zai sa yana ji yana gani ya rabu da mai kama da Zuhuriyyarsa sak bayan duk sanda yake son farin ciki a rayuwarsa to sai ya hasko rayuwarsa da Zuhuriyya. Sai ya hasko kamanninta zuciyarsa, sannan yake jin sanyi a ransa. A yanzu haka fuskar Sajida, muryarta da siffar jikinta ce ta maye kamannin Zuhuriyyarsa.
"Ya ya zan yi?" Bakura ya tambayi zuciyarsa.

*** **** ***
Kwanaki biyu Bakura ya yi a cikin gida, a cikin wannan hali mai tsananin dabarbarcewar tunani. Daga wanka, sai sallah ce take tashinsa daga kan gado. Abinci har kan gado Samira take kawo masa, amma sai ya ji ya kasa ci, idan ya ci kadan sai ya bari sai dai ya na yawan shan ruwa da juices din da ke shaqe a cikin firij din da ke gefen gadonsa.Yanayin Bakura yasa Samira ta bar fushin da take yi, ta shiga ba shi hakuri, ta na lallashinsa tana yi masa nasiha, duk da ba ta san me yake damunsa ba kuma bai fada mata ba.
A bangaren Zahra kuwa, ita ma hankalinta a tashe yake koda yaushe cikin fargaba take, tana gudun kada Sajida ta fadawa babanta dangantakar da ke tsakaninta da Abdul majid wayar da yake yi mata , duk da dai ba ta san dalilin da ya sa Sajida ta kira ta da munafuka ba. Zancen dai bai wuce Sajida ta gane Abdul Majid yana yi mata waya ba, abun ka da munafukin namiji zai iya ce mata Zahrar ce take yi masa waya ita kuma ta kullace ta. Don haka ganin yanayin da Abbanta ya shiga, na rashin walwala, sai hankalin Zahra ya tashi matuqa suka shiga wasan 'yar buya da shi. Daga sun idar da sallar Asubah, idan ta gaishe shi to sai tayi wuf ta fada daki ta shirya su tafi makaranta. Zahra ta yi zuguf ta rame, sabo da fargaba, tunani, kuka da uwa-uba tsayuwar dare tana addu'a akan Allah Ya rufa mata asiri, kada a fadawa mahaifinta cewar Abdul-Majid yana sonta. Allah yasa dai shirun da ya yi bai ce mata komai ba, ba wani tsatstsauran mataki yake shirin dauka a kanta ba.
Kaico!!! Rashin sani yana damun Zahra, ba ta san abin da yake damun Bakura daban ba ne, shi har ya manta da rigimarta da Sajida. Abun da yake damunsa ba zai fadu ba, sai shi sai Rabbul Alamin, sai Malam wanda ya hada abun.
A rana ta uku Bakura ya yanke hukuncin zuwa gidan Malam Yakubu, don su zauna su yi magana qeqe-da-qeqe, babu zancen nuqu-nuqu ko 6oye boye ko kara, kunya, da jin nauyi. Gara a yi fito-na-fito kowa ya fadi rá'ayinsa, ba tare da wani ya cutu ba.
Yamma na yi, Bakura ya yi qarfin hali ya miqe ya shiga bandaki ya fesa wanka, gami da caba ado da wata galleliyar shaddarsa fara sol sai walkiya take tana santsi kamar tarwada. Ya dora farar hula, gami da farin takalmi, hade da farin gilashi a fuskarsa. Rangadi! Wa ya ga baqar fata a cikin fararen kaya, ya yi 'karr' da shi, son kowacce 'ya mace. Mai ya yi saura? Sai ya feshe duk illahirin jikinsa da zabga-zabgan turarurruka (designers), wanda babu na qasa da dubu ashirin da biyar. Kan ka ce kwabo qamshi ya karade ciki da wajen gidan.
Samira ce dauke da farantin yankakkun kayan marmari ta shigo dakin Bakura. Daga ganin irin duban da take yi masa ka san duba ne irin na mamaki, hade da farin ciki. Ta ajiye farantin akan durowar gefen gado, ta mayar masa da lallausan murmushin da yake yi mata, irin na ma'aurata masu farantawa juna,ta qarasa inda yake tsaye gaban madubi.
Ta ce "Ran maigidana ya dade, ina za'a je ne? Ko kai fa? ka ga yadda na ji dadin ganinka kuwa? Ka yi kyau yau fiye da kullum, na dade ban ga ka yi kyawun kwalliya irin ta yau ba."
Bakura ya yi dariya, sai ga fararen haquransa tarr a fili masu dauke da wushiryoyinsa sama da qasa sun bayyana, sai kwalliyar ta qara qawata.
Ya ce "Ke kin cika zuga, kullum ki yi ta zuga ni ina fasa kai, ina daukar kaina kyakkyawa, alhali ke kadai kike ganin kyawun."
Su duka suka bushe da dariya. Samira tasa hannu tana balle masa maballin gaban rigarsa.
Ta lankwashe murya ta ce, "My dear, ka qi ka fada min halin da kake ciki, ka saka ni cikin zullumi da kokonto. A ce yanzu tsakanin miji da matarsa akwai boye-boye? My love ka kawo agaji wajen fitar da ni daga wannan damuwa da zuciyata take ciki. Ka daina boye min gaskiyar al'amari, na sanka, na san halinka. Kai jarumi ne, ba ka tsoro, na san za ka ce bai shafe ni ba, amma ya kamata in sani. Wace ce Sajida? Mene ne dangantakarka da ita?"
Bakura ya ji zuciyarsa ta harba '6amm'!!! Don fargaba da tsananin firgici. Ga idanuwan Samira tsai a kansa, tana kallonsa tana jiran jin amsar tambayarta.
Ya ji yawun bakinsa na qoqarin qafewa, yayin da sautin maganarsa ke qoqarin kifewa cikin cikinsa. Ya yi ta maza, musamman irin wannan kirari da kodawar da ta yi masa.
Ya ce, "My heart kenan, tambayar da ki ka yi wacece Sajida. Amsa ita ce Sajida wata yarinya ce qarama, 'yar kimanin shekaru goma sha shida. Sunan mahaifinta Yakubu, mahaifiyarta kuwa Furera. Su na zaune ne a unguwar Kawo, da ke kusa da Giginyu a qaramar hukumar Nassarawa, da ke cikin garin Kano. Kamannin Sajida da Zuhuriya shi ya ja hankalina na sanin wacece Sajida? Su waye iyayenta? A wacce unguwar suke?"
Samira ta yi murmushi ta ce "Na ji amsar tambayata ta farko, sai tambayata ta biyu. Bayan ka gano wacece Sajida ka tantance ba su da alaqa da wacce kake tunani, mene ne dangantakar ka da ita?"
Bakura ya yi ajiyar zuciya, gami da murmushi ya lumshe ido. Ya ce, "Wannan amsar ta ki ba za ta fadu ba a yanzu, amma ki ba ni awa hudu zan fita in dawo, za ki ji cikakkiyar amsa marar gargada."
Samira ta yi masa duba irin na rashin fahimta, ta bude baki za ta yi magana kenan, Bakura yasa hannu ya rufe bakinta.
Ya ce, "Kada ki ce komai, ki yi addu'ar Allah ya kai mu, shi ne za ki ci ribar zama da ni da samun labarin da kike nema daga gare ni. Mace ta gari ba ta jayayya da mijinta, na yi alkawari zan fada miki komai."
Ya sumbaci kumatunta, ya juya zai fita, yayin da ya barta a tsaye tamkar bishiyar da aka dasa, ta bishi da kallon kawai. Ta ambaci sunansa, nan da nan ya juyo.
Ta ce "Na dauki fiye da awa guda ina yanka maka fruits din nan na ga ko kallon inda suke baka yi ba, balle ke sha."
Ya dafe kai alamar mantuwa ya dawo da sauri ya ce, "i am sorry my dear, bari in sha yanka biyu, kada in yi laifi in yaso sai a ajiye min sauran sai na dawo da daddare, ina baki labari muna sha zai fi dadi."
Samira ta yi dariya ta ce, "Ko kai fa, shi yasa ka ke burge ni akwai ka da gudun bacin raina."
Ta sa cokali mai yatsu (folk) ta dauko yankan abarba ta saka masa a baki, ya cinye. Ta cako yankan gwanda ta saka masa a baki, ya cinye.
Ya juya zai tafi ta sake cewa, "Saura guda daya ga kankana ba ka sha ba."
Ya dawo ya bude baki ta saka masa yanka daya.
Ya yi murmushi ya ce, "Kina shagwaba ni kamar wani yaro qarami dan goye."
Ya rungume ta tsam a kirjinsa, har zuwa wani lokaci mai dan tsawo, sannan ya sake ta.
Ta fada cikin wata 'yar siririyar murya mai kama da rada, "Allah ya bada sa'a."
Ya amsa cikin murmushi ya ce "Amin my Wife."
Ya juya ya fita da sauri yana yi yana duban agogo. Ta biyo shi a baya tana fadin, "Yau dai sauri ake har ba a jiran rakiya ta."
Su ka dunguma zuwa farfajiyar gidan, a inda ake ajiye motoci.
Ta dube shi ta ce, "Ina fatan dai mukullin farar motar nan ka dauko ko? Domin ita ce ta dace da fararen kayanka, na sanka mutumina akwai hada to march."
Ya yi dariya ya ce, "Ita zan hau, sai dai idan kin ce in hau baqar mota, kada fararen kalar su yi yawa."
Ta ce "A'a, ka hau farar, za ka fi yin kyau."
Ya shiga ya ja ya tafi, tana daga masa hannu, yana daga mata, har ya fice daga cikin gidan. Samira kuwa sai ta tsinci kanta yau cike da farin ciki, kai ka ce an mata albishir da gidan Aljanna. Ita kanta ba ta san dalilin wannan farin ciki ba, duk da dai kowa ya san farin cikinta yana da nasaba da farantawar da maigidanta ya yi mata a yau. Domin farin cikin 'ya mace bai wuce idan mijinta yana dadada mata ba, haka musgunawa daga namiji ya kan susuta 'ya mace ta shiga damuwa, har ya kaita ga samun tabun hankali, hawan jini, ko bugun zuciya. Don haka farin cikin Bakura shi ne farin cikin Samira, farin cikin Samira shi ne farin cikin yaranta.
Da yake Alhamis ce, babu Islamiyya, Samira ta hado kan 'ya'yanta gaba daya zuwa cikin lambu su na hira, su na wasa da dariya, kai har da tatsuniya da waqe-waqen gargajiya suke rerawa ita da su.
Hakika Zahra ma ta saki jikinta, hankalinta ya kwanta, ta gasgata cewar mahaifinta bai ji maganar Abdul majid ba, ta dora da addu'a kada Allah Ya sa ya ji wata magana nan gaba.
Da Bakura ya fita bai tsaya a ko ina ba sai a qofar gidan Malam Yakubu. Su ka zauna a qofar gidan su na hira, duk da a cikinsu babu wanda ya tabo zancen Sajida.
Can Bakura ya dubi zauren gidan Malam ya ce, " Sama'ila ya kawo min gero da masarar ne, na ga buhunhuna a jibge?"
Malam ya yi dariya ya ce, "Af ka ga shaf na manta, ai tun jiya ya kawo har ma na ba shi kudin."
Bakura ya ce "Me yasa ba ka yi min waya ba tun a jiyan ai da na bar abin da nake yi na zo na biya shi, da ba ka biya ba."
Malam ya ce "Gero duk buhu daya naira 5,000, masara kuma duk buhu naira 6,500."
Bakura yasa hannu a aljihu ya dauko kudin ya miqawa Malam, sai Malam ya dakatar da shi. Ya ce "Ka bar shi kawai zansa ya kawo maka naka har gida. Wannan ni na saya, saboda sai a ci a bikinSajida."
Bakura ya bude baki ya na duban Malam, duba irin na mamaki, ya tambayi Malam cike da tangardar sauti, "Bikin Sajida da wa, yaushe ne bikin?"
Malam ya gyara zama, gami da tsuke fuska ya girgiza kai don takaici. Ya ce "Al'amarin Sajida da yaron nan Abdul majid sai Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un. Wato bayan mun yi wayar nan da kai, na je na sallami Sama'ila ban fada masa abin da nake so in fada masa ba, na hakura har sai mun yi tunanı ni da kai, kamar yadda ka shawarce ni. Sai rana tsaka ba aka nemi Sajida aka rasa, ta katanga ta haura da qullin kayanta wai za ta gudu wajen Abdul majid."
Wata mummunar faduwar gaba ce ta tabbata a zuciyar Bakura, ya dafe kirji ya fada a bayyane, "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un. Yanzu ina Sajidar?"
Malam ya girgiza kai ya tabe baki ya ce "tana cikin gida a daure, a mari na saka ta har yanzu bakinta bai daina ambaton za ta fita ta gudu ba. Ai tana kama hanyar gidan su Abdul majid ba ta kai ga qarasawa ba, wasu almajiraina suka ganta da gudu akan babur suka zo suka sanar da ni, muka runtuma akan babura muka damko ta, ni kuwa na sa mata mari na daure hannuwa da kafafuwan na jefa ta a akurkin dakinta."
Bakura ya yi wata doguwar ajiyar zuciya a bayyane ya sunkuyar da kansa qasa yana mai tsananin tunani da daurewar kai.
Malam ya katse masa tunani ya ci gaba da cewa "Kai har ta kai ta kawo na kira kawarta Iyayye na ritsa ta na karbi lambar wayar Abdulmajid, na zo gida. Ga ni, ga Sajida, ga mahaifiyarta na bugawa Abdul Majid waya, kuma na bude wayar (hand's free) yadda kowa zai ji."
Bakura ya dago da sauri ya dubi Malam ya ce "Ka kira Abdul majid saboda me?"
Malam ya ce saboda ina so in ga karshen soyayyarsu, ina so Sajida ta san wannan yaro ba sa'an auranta ba ne, ba tsarin su daya ba, ba martaba da tarbiyyar gidansu daya ba ce. Ina so ta san ba kaunarta yake ba, ba kuma aurenta zai yi ba."
Bakura ya ajiye kudin da yake rike da shi tun dazu ya hada gwiwoyinsa biyu ya rike da hannayensa ya ci gaba da sauraron Malam.
Malam ya ci gaba da cewa, "Bugu daya waya ta yi ringing, dan iskan ya dauka, abunka da lalatacce maimakon ya yi sallama, sai ya yi fito. Ya ce, "Ya ya aka yi ne babyna?"
Ashe ma ya san lambata, har wayata take sata ta buga masa, idan na ajiye a caji na tafi masallaci."
Bakura ya tsuke baki, sai kada kai yake kamar wani kadangare. Ya rasa ta cewa, sai tsananin bugun da zuciyarsa take yi, tamkar 'yarsa ce ta fada hannun mayaudari. Hakika ya tausayawa Malam, ya kudiri niyyar taimakawa Malam da 'yarsa Sajida wajen yaqi da Abdul majid, mayaudaran samarin da suke yaudarar 'yan mata. A kan me?"
Malam ya ci gaba da cewa, "Sai na yi masa sallama, amma yaron nan bai razana ba ma da ya ji muryar tsoho. Har wani turanci ya juya yake yi min.
Na ce masa ba na jin wannan yaren mu yi Hausa. Na tsufa, ga rashin isasshiyar lafiya."
Sai hawaye ya surnano daga idon Malam. Bakura sai ajiyar zuciya yake yi, har yanzu gyada kai yake, yana huci kamar wani kumurcin miciji. Ga wata zufa da yake yi kai ka ce a gaban wuta yake.
Malam ya ci gaba da cewa, "Dan haka auren Sajida da Sama'ila ya tabbata, don har na fadawa Sajida kuma yau din nan na kira Sama'ila na shaida masa."
Bakura ya dago da sauri ya dubi Malam ya ce, "Ka fadawa Sama'ila?"
Malam ya ce "Kwarai, kuma ya amince duk da shi ma ya yi tantamar iya zama da Sajida, amma ya amince har ya yi murna, gami da godiya. Ya ce zai je ya hado dan abun da Allah ya hore masa ya zo a daura aure. Don haka ne ma na ce ni na sayi gero da masarar, sai ya kawo maka wasu."
Bakura ya buga kansa da hannu, ya ja dogon numfashi mai ribas, ya girgiza kai.
Ya ce, "Malam ba ka nemo mafita ba, wannan abu bai yi ba, wannan qofar ba mai 6ullewa ba ce."
Malam ya yi tsuru yana duban Bakura. Can ya ce "Me yasa ka ce haka?" Bakura ya ce, "Sajida za ta dauwama a daure a mari ne? Za'a yi zaman aure ne a haka a daure? To idan ba haka ba Sajida ba za ta yadda ta zauna a gidan Sama'ila ba guduwa za ta yi. Auren dole yana iya jawowa mace ta falle ta gudu, ta shiga yawon bariki. Auren dole kan iya sawa mace ta nemi ta kashe kanta, ko ta kashe mijin, koKai kafi cancanta paid book #300




Malam ya yi zugum, can ya ce, "Bakura ina mafita? Ya ya zan yi da rayuwata? Yaya zan yi da Sajida? Muddin Sajida na zaune a gidana duk dabarata sai ta yi yadda zata hadu da Abdul majid, so yake ya cuci yarinyar nan ya bata mata rayuwa, Bakura babu amfanin zama da Sajida a gidana, tunda Sajida ba makaranta take yi ba. Ba na barcin kirki, saboda gadinta."
Bakura ya miqawa Malam kudin nan, gami da cewa, "Ka yi min izinin ganin Sajida zan yi mata magana."
Malam ya zabura ya miqe da sauri ya ce da Bakura, "Bismillah mu shiga ciki."
Malam na gaba Bakura na biye da shi, har tsakar gida. Bakura na tafe yana waiwaye, yana duban kowacce kusurwa ta cikin gidan. Babu abinda idanuwansa suke nuna masa, illa ragargajejjen bango da dakwalkwallallan fenti baqiqirin.
Su ka iske Umma Furera a zaune akan kujera a tsakar gida ta buga tagumi tana tunani, kallo daya za ka yi wa jemammun idanuwanta ka tabbatar ta narki kuka son ranta, har ta gaji.
Cikin nutsuwa da sanyin jiki Bakura ya yi mata sallama, gami da rusunawa don girmamawa. A tsorace ta dago ta dube shi, duba na ban mamaki. Ta sake wurga idonta gefe ta dubi maigidanta. Sai ta sadda kai qasa ta gyara lullubinta, gami da amsawa Bakura sallamar da ya yi mata.
Malam ya ce da ita. "Ki bawa baqo kujera mana ya zauna."
Ta yi sauri ta sauka daga kan kujerar da take zaune ta tura a gaban Bakura.
Ya ce, "A'a, babu komai yi zamanki ba zama zan yi ba."
Bakura ya durkusa a gaban Umma Furera ya gaishe ta, ta amsa cike da fara'a mai hade da mamaki, tana yi masa duba inin na ban gane ka ba.
Babu abin da Bakura yake nanatawa a ransa sai "Allahu Akbar, na ga mahaifin Sajida, na ga mahaifiyarta, ammá babu hadin ta da Zuhuriyyarta."
Bai ma taba cin karo da mai kama da siffar Umma Furera ba, balle su hada dangantaka da Zuhuriyya.
Kalmar da ta fara fitowa daga bakin Bakura ita ce "Ina Sajida?"
Wannan tambaya tasa ita tasa Umma Furera dago da jajayen idanuwanta, ta dube shi. Ta tambayi zuciyarta."Wanene wannan? Daga ina yake? Mene ne dalilin zuwansa? A ina ya san Sajida? Menene dalilinsa da yake neman Sajida?"
Furta wadannan tambayoyi ba za su yiwu ba dan haka ta hada tambayoyinta ta kunshe a cikin zuciyarta.
Malam ya nuna dakin Sajida ya ce "Ta na ciki, tana baqin ranta da ta saba. Mu shiga ka ganta."
Malam a gaba, Bakura na biye da shi, har qofar dakin Sajida. Abin ka da dogo, ga 'yar gajeriyar qofa a rashin sani bai durqusa ba ya doke kai a jikin qofa, yayin da burbushin jar qasa suka kado a jikin fararen kayansa, har da idanuwansa.


Please Login or Register in order to submit comment