Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baƙa ƙarin da ita, ga jajayen idanu, fuskarnan a haɗe ta kalli Junainah dake gaidata da fullanci cikin tsananin tsawa tace.
"Ke tafi daga nan ƴan iskan fulani masu jajayen kunnuwa, dan uwarki Ni ba fillatace da zaki gaidani da fullanci, hegu kwarkwasa fidda mai gida a gidanshi yan iska masu kama da al'janu, in sha Allah ƙarshen zamanku a wannan yanki yana nan tafe".
Da sauri Junainah ta koma bayan Junaidu, shi kuwa Junaidu wani irin tafasa zuciyarshi keyi akanme zata zagesu dan kawai sun gaidata da fullanci.
Bukar ne mijinta wanda yake babarbaree ya kalleta tare da cewa.
"Kuma dai al'barkacin fulanin kikeci".
Ba'ana ne ya ɗan harari mahaifin nashi tare da waskewa yace.
"Fulani kecin al'barkacin ta dai, tunda kowa ya sani wannan yankidai na Ɓachamawa ne, ba fulaninba".
Cikin ƙarfin hali Junaidu yace.
"Ato ai dai ba kyau aka bamuba da kuɗin mu aka bamu, kai kamma ya Ba'ana kaifa bawanmu ne tunda kai babarbarene".
Wani irin suka kalawan yaron suka mishi a ƙahon zuciyarshi amman sai ya dake,
ledan su ayaba da inabin ya bawa Junainah tare da cewa.
"Uhu Junaidu kenan aini ba bakanuri bane ni ba Bachamene, Dan da in zama bawan fulani gwara in zama bawan karnuka".
Haka nan kalamansu ke tafasa zuciyar Junainah da Junaidu, haka yasa fuska a hade suka juya suka tafi, har sunje bakin ƙofar fita Ba'ana yace musu.
"Yauwa kuce mata ina zuwa yanzu bari inyi wonka".
To sukace kawai suka fita suka tafi.


A ƙofar gidansu suka tsaya gaban Ya Salmanu da Aysha, ledan Junainah ta ajiye a tsakiyarsu cikin jin haushi tace.
"Addana gashi inji ya Ba'ana wai in kawo miki, yace kuma yanzu zaizo wai wonka kawai zaiyi".
Tana kaiwa nan tayi cikin gida shi ma Junaidu Binta yayi a baya, har gabansu Ummey ya tsuguna suka gaisa kana yace.
"To Ummey ga Ƙanwaliya na rakota Ya Ganin ne yace in rokata har cikin gida".
Murmushi Ummey tayi tare da cewa.
"Mun kuwa gode, ka gaida min Innonka kace mata, in Allah ya kaimu gobe ta turo min Hari tazo tamin kitso".
Kanshi ya gyaɗa tare da cewa.
"To saida Safe Bappa".
Allah ya bamu al'khairi sukace baki ɗayansu.

Daga nan ya fito, har ya wuce Ya Salmanu yace.
"A a Junaidu zoka amshi tsarabar mana".
Cikin girmamawa yace.
"A a Ya Salmanu ya isheni".
Cikin kula Salmanu yace.
"Ni kam yaushenene zaku koma school?".
Da sauri yace.
"Saura kwana biyar hutunmu zai ƙare".

"To Allah ya taimaka yanzu aji nawa kane".

Murmushi ya ɗanyi tare da cewa.
"Ina SS 3 ne fa, Ya Salmanu na kusa gamawa ai".

"Masha Allah, Allah ya taimaka".

Amin Amin yace kana ya juya ya tafi.


Ita kuwa Shatu cikin tsoro ta kalli Ya Salmanu a hankali tace.
"Ya Salmanu tashi ka tafi kada yazo ya sameka".
Cikin harshen fillanci yace.
"To shi mala'ikan ɗaukan raine? Ko dai so kike in guje masane Shatu, kina son ragon mijine?".
A hankali tace.
"A a Ya Salmanu zai cutar da kaine nake tsoro".
Da sauri ya katseta da cewa.
"Babu mai rayawa da kashewa sai Allah, ko yaya zaiyi bashi da ikon kasheni sai in kwana-nane ya ƙare. Ko ciwon kai bai isa ya samin ba".
Shiru tayi tana kallonshi.
Sai kuma tai maza ta miƙe tsaye ganin kamar daga sama aka jefo Ba'ana gabansu.

Kallon kallon sukeyiwa juna shida Ya Salmanu, cikin wani irin mugun kallo mai cike da mugunta yayi kwaffa tare da cewa.
"Uhummm Salmanu manyan gari, wato har an samu wani mai yar guntuwar jarumtar da zai iya haɗa so dani a kan Shatu, to bazan ce maka komaiba, amman ka shirya ranar litinin zamuyi shaɗi muddin ka cini na bar maka ita duniya da lahira, zan kuma bar garin Bani, da ƙasar nan gaba ɗaya zan koma ƙasar Cameroon, in kuwa na cika zaka bar duniya baki ɗayanta!".
Cikin tsananin tsoro da kaɗuwa Shatu tace.
"A a fa Ya Ba'ana wlh ba sona yakeyiba, karatu yake koya min".
Da sauri Salmanu ya katseta da cewa.
"Sonta nakeyi Ba'ana so kuma na aure, na kuma yarda zan shiga gasar Shaɗi da kai a ranar Litinin na amince".
Wata irin muguwar dariya yayi wacce har tasa Aysha kowa cikin gida da gudu, shi kuwa saida yayi dariyar mai isarshi kana yace.
"Lallai gidan Arɗo Yabani na gab da rasa motsin ɗana miji".
Yana faɗin haka ya murza layar zananshi, sai gashi ya ɓaci.

Cikin ƙarfin hali Salmanu ya nufi gida.

Shi kuwa Ba'ana yana ɓacewa a tsakiyar dottawan Fadan Arɗo Yabani ya baiyana,.
Wanda badon tsoffin makiyayene sun saba ganin abinda yafi haka ba tabbas watsawa zasuyi.

So amman suka dake, cikin kamala Bappa ya kalleshi tare da cewa.
"A a Ba'ana lfy kuwa?".
Sunkuyar da kanshi yayi kamar mutumin kirki, cikin danne fushinsa yace.
"Ku gafarceni Bappa nazone da batun neman al'farma fagen shaɗi, nida Salmanu ɗan Arɗo zamuyi gasa kan Shatu, na kuma yarda, muddin yayi nasara akaina na bar mishi Shatu zan kuma bar Rugar Bani baki ɗaya".
Da sauri Bappa yace.
"A a".
Da sauri Arɗo Yabani yace.
"A a Malam Liman ba komai, na amince na basu damar yin gasar Shaɗi mai nasara yaci gasar".
Jin haka yasa dattawan nan duk sukayi shiru.

Shi kuwa Ba'ana cikin tarin ƙeta jikinshi har tsuma yakeyi yana maganar zuci.
"Uhumm zan kashe Salmanu kuwa kisa mafi muni zaku gane kurenku hegun fulani kunzo garin daba nakuba kun fisu dukiya zan kashe Salmanu irin kisar da ban taɓa yiwa waniba kisan da zaisa har abadan babu wanda zai sake cewa yana son Shatu".
A zahiri kuwa, godiya yayi musu kana ya juya ya tafi.
Nan dattawan kuma sukaci gaba da tattaunawa yadda Shaɗin zai kasance.


Washe gari ranar asabar da sanyin safiya akayi shelar sanar da gasar Shaɗi da za'ayi jibi litinin, da kuma, waɗanda zasuyi gasar da sunan wacce za'ayi dan ita.

Gaba ɗaya magarna ta cika Rugar Banin da kewayenta, duk wanda yaji yana firgici,
Maman Salmanu kuwa tuni taketa kuka tana cewa ita kam so ake a ƙarar mata da yaranta an kashe mata Hashimu yanzu kuma ace da Salmanu za'ayi gasar Shaɗi da mutun da sun san ba'a taɓa nasara a kansa a.,
Mutanen sauran rugogin Fulani dake mutunci da Arɗo Yabani kab sai gudumowar magunguna suke kawo na dauri dan a tsuma jikin Salmanu.

Sosai kuwa babanshi da yayunshi mata da maza da abokanshi keta tsumashi.

Shi kuwa Ba'ana tun ranar ya ɗauki tunƙur ƙasar da yake tsuma bulalinshi, ya kaishi Ƙauyen Bonon, gaban dodon tsafinsu,
Anan tukunyar ta kwana bulali tamanin dake cikin tunkuyar nan aketa tsumawa da tsafi.
Kana an jikasu da ruwan gishiri sannan an juye kunamai sama da ɗari a ciki, irin baƙaƙen kunamun nanne masu mugun dafi, an sasu ciki sunata harbin bulalin nan suna sa dafinsu a jiki. ranar lahadi da yamma ya amso tukunyar,
Har zauren gidansu Shatu yaje yasa aka kira mishi ita bayan ta fitone yace ta leƙa cikin tukunyar, a hankali tace.
"Me zan gani a ciki?".
Kanshi ya jinjina mata tare da cewa.
"Nazo in nuna miki bulalin shaɗi nane, ki gansu da kyau, dan ki cewa wancan koɗeɗden ya shirya shan zabga".
Kai ta jujjuya tare da cewa.
"Ni ba sai na ganiba".
Murmushi yayi tare da buɗe tukunyar kana ya karkatar mata shi gabanta.
Da sauri taja da baya tare da cewa.
"In......




Littafina na kuɗine turo katin mtn na ɗari uku kacal ko karanta a nitse.





By
*GARKUWAR FULANI*📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘

*GARKUWA*

PAGE 10

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

📝🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘


LITTAFIN GARKUWA NA KUƊINE, TURO KATIN MTN NA ƊARI UKU KACAL ta number 09097853276 domin samun cikekken labarin, ko kiyi min transfer ɗin 1k ɗan samun SP GROUP ta asusuna 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number 09097853276


FREE PAGE

Cikin tashin hankali tace.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun. Ya Ba'ana me wannan, abu kamar macizai". Da sauri ya meda ya rufe kana ya miƙe cikin yin ƙasa da murya yace.
"Kinga ni kada ki tayarmin da hankali kinsan bana son ganinki cikin tashin hankali, in sha Allah nine da nasara ko dai bakya so nane".
Da sauri ta girgiza kanta tare dasa tafin hannunta ta rufe bakinta.
Ganin haka ya kwashi abinshi ya tafi.

Ita kuwa koda ta shiga gida, gefen Inna ta zauna tare da cewa.
"Inna ku cewa Bappa ya cewa Arɗo ya hana gasar nan, kada a cutar da Ya Salmanu".
Cikin sanyin jikin da duk kwanan haka inna ta zama, a hankali tace.
"Uhumm ba komai Shatu in sha Allah duk abinda zai faru da sanin Allah.
Yanzu ke yaushe nema zaki koma hutunmu?".
Kanta ta gyaɗa a hankali tace.
"Rana ita yau zan koma kimga saura mako ɗaya kenan".
Ummey ce dake gefe ta ɗanyi ajiyan zuciya gami da cewa.
"Alhamdulillah ni in kin komama hankalinmu zaifi konci, domin muddin kinanen sai Ba'ana yayi ta kalato fitina".

Shiru sukayi baki ɗayansu, jin an fara kiran sallane tasa, duk kowa yayi al'wala haraman salla.


A daren ranar kuwa Ya Salmanu da abokinshi Sale suka zo, wurinta, nan take ce musu ita kam bata son wannan gasar da za'ayi kuma tunda an kafe sai anyi sam ita bazata jeba.
Haka dai sukayi ta hira daga bisani suka tafi.

Washe gari ranar Monday kuwa, tun da sanyin asuba aketa gangamin.
Haɗuwa a filin da za'ayi shaɗi.
Mutanen sun cika maƙil dan anfi yawan yin gasar da safe, sabida da rana duk makiyaya sun tafi kiwo manoma sun tafi daji.
Tuni matasan Fulani na rugogin nesa da Bani ma sun zo.

Bukar kuwa tunda aka fito sallan asuba yaje. Gidan Arɗo Yabani, yaso ace an janye gasar tun randa aka shelanta amman Arɗo yaki,
still yanzuma da yazo, bayan sun gaisane ya ɗanyi gyaran murya tare da cewa.
"Haƙiƙa naso a janye wannan shaɗi, domin nasan abun bazaiyi daɗin ganiba ace Ba'ana na zane Salmanu ɗan Arɗo ga wannan rugar, amman kaƙi ka saurari zancena,
Dan haka ni ba kada wani abu ya faru ku kuskura kuyi kuka dani, duk abinda ɗana yayiwa ɗanku kune kuka saya mishi da yawun bakinku kun rigada kun san bazaku taɓa samun wanda zaifi ƙarfin ɗanaba".
Shiru Arɗo Yabani yayi yana nazartan kalaman Bukar,
ganin yayi shirune alamun ya gama magarsa cikin sanyi Arɗo Yabani yace.
"Duniya da faɗi take, Bukar Mai kanwa a kwana a tashi watan-wata-rana zakaji zaka gani da idanunka za'a samu wanda zaifi ƙarfin ɗan ka, Allah zai bijiro da wanda zai iya jure bulalin ɗan ka".
Cikin wani irin yanayi Bukar yace.
"Babu mamakin a samu mai iya, jure bulalin, tabbas babu mamaki. Sai daifa abun da bazai taɓa yiwuwa bane har illa masha ALLAH ace an samu wanda zai iya nasara a kanshi babushi babu namijin da zai iya sashi jin zafin bulala bare ya zubda hawayen da zaisa ya rasa Shatu".
Wani dogon numfashi Arɗo Yabani yaja tare da cewa.
"Uhummmmmm". Daga nan bai kuma cewa komaiba,
Shi kuwa Bukar tashi yayi ya kakkaɓe rigarsa ya juya ya tafi yana faɗin.
"In dai kunne yaji gangan jiki ya tsira".
Da ido Arɗo Yabani ya rakashi, yana maiji a cikin ransa inma ace yanada dama, inama ace zai samo wannan bulalin da Malam Chuɓaɗo ya gaya musu, da tabbas ya samu hanyar da zai cire mugun iri a garinshi.

A haka Salmanu da abokinshi, sukazo suka sameshi zaune. Bayan sun gaisane Sule ya ɗan matso kusa da Arɗo a hankali yace.
"Allah rene, duk wuri an taru mu ake jira, shi Ba'ana tun da asuba yana can, yanzu Iro yazo yake ce mana gacan fili ya cika, mu kaɗai ake jira, har wasu nata maganganun wai Salmanu ya ji tsoron Ba'ana ya gudu".
Murmushin da yafi kuka ciwo Arɗo Bani yayi dafa tsakiyar kan Salmanun yayi kana yace.
"Kuje Salmanu, Allah ya bada sa'a Ubangiji yaga niyarmu na son tseretar da wannan yarinyar daga fadawa auren wannan mushurkin, taƙadiri in Shatu matarkace Allah ya baka sa'a in kuwa ba matarka bace, Allah ya baiyono mata wanda zai zame mata GARKUWA daga faɗawa auren wannan azzalumin".
Amin Amin sukace baki ɗayansu kana su sukayi gaba.
Shi kuwa Arɗo, saida ya jira su Malam Liman Bappa kenan dasu Ahaji Horu, da Ahaji Umaru da Garbati.
Koda sukazo ba ɓata lokaci suka nufi, farfajiyar wurin da aka tanada dan shaɗi.

Filin ya cika ya batse tako ina mutane zuwa sukeyi arna da musulmai fulani da hausawa da ƙabulun, Ɓachamawa, domin duk yankin nahiyarsu an san babu taƙadiri sama da Ba'ana sabida tunda ake gasar Shaɗi da kuma gasar kokuwa yayin nunan sabon gero ba'a taɓa cin nasara kanshiba, muddin ya shiga gasa tofa shine da nasara.
Har ta kai da in dai ya ɗaga hannun to babu mai ɗagawa.
To sanadinshi aka hana Shaɗi a Rugar Bani, tsawon shekaru biyu sai gashi yau an dawo dashi.

Wannan dalilin ne yasa gaba ɗaya Rugar Bani ta cika maƙil da mutane maza da mata manya da yara,
Ga mai busar sarewa kuma yana tsakiyar taro inda akabar filin da za'a gobza yanata rere kirari wa Ba'ana.

Isowar su Arɗo yasa aka basu hanya har suka iso gaba inda aka tanada musu, kujerun zama. Na bencin katako.
Daga nan manyan Dattawan duk suka Zazzauna.
Bisa ƙa'idar gasar Shaɗi wanda ya fara cewa yana son yarinya shi zai fara duka, in wanda yace yana sonta daga baya ya ƙetare bai zubda hawayeba baiyi kukaba, to sai asa kwanaki sai yaje yayi jinya ya worke daga zabgar da yasha, sai ya dawo ya ɗauki fansa, to in ya zana wannan yayi kuka shike nan yayi nasara in kuma wannan ma baiyi kukaba za'a sakeyi har sau uku to nan in babu wanda yayi kuka cikinsu sai yarinya ta zaɓi wanda takeso, don anada yaƙinin duk wanda ta zaɓa, zai iya kare kanshi tunda ƙarfinsu yazo ɗaya.

Bayan an gama dai-dai-ta komai, Salmanu ya cire rigarsa kamar yadda ƙa'idar gasar take, ya rage dagashi sai gajeren wondon.
Shi ma Ba'ana ya cire rigarshi ya zama dagashi sai gajeren modo, irin masu zuwa har guiwa ɗinnne.

To dole a ƙa'ida Ba'ana ne zai fara duka, amman da yake ya shiryawa abun sai yace, shi ya amince a fara dashi, kuma shima yau zai rama Ba sai an ware kwanakin zuwa jinya ba.


Nan kuwa take al'kalin gasa Barmuji yace an amince.
Daga nan aka zaro bulalin shaɗi na cikin tanɗun masarautar Arɗo Yabani wanda an ƙara tsumasu suma.

A hankali Barmuji ya miƙa wa Salmanu, bulalin,
kana ya ɗaga hannunshi ya dawo dashi ta bayan Ba'ana.
Shi kuwa Ba'ana tsayuwa yayi ƙam tare da ɗan ware sawunshi,
Busar sarewar da mai busan yayine alamun a fara,
Ai kuwa cikin kuzari da jaruma Salmanu ya ɗan ja da baya,
kana ya tattaro ƙarfin shi ga ba daya, ya ɗaga kitsetsten bulalan nan, ya taƙarƙara ya zabgawa Ba'ana shi a tsikar bayanshi,
Wanda a take taron matasan dake wurin suka kurma ihu mai karaji,
Yayinda shi kuwa Ba'ana, ƙim ya tsaya kamar ba shiba, domin ko idonshi bai ƙebtaba.
Sake taƙarƙarewa Salmanun yayi ya kuma zabga mishi bulalar a inda ya kima mishi na farin.
Still ihu, taron matasa sukasa, tarin ƙabilar ɓachama kuma dake wurin sai rurrufe idanunsu sukayi da ƙarfi sabida wai bazasu iya jurar ganin ana zabgar jakadan suba.
Mai irge kuwa da iya ƙarfinshi yake kware baki yana cewa.
"Ɗaya! Biyu! Uku! Huɗu! Biyar! Shida! Bakwai!!!".
Haka yaketa irga duk bulalar da aka kaiwa Ba'ana amman wannan tagadirin mutumin ko a jikinshi kamar dutse ake zanawa ba shiba.

Ƙa'idar bulalin shaɗi Hamtsine akeyi.
Haka Salmanu yake ware iya ƙarfinsa yana zabgar Ba'ana, yana tsaye ƙiƙama. In wannan bulalan ya lauye, sai a bashi wani bulalan.
Har akaje arba'in da takwas ko gezau.
Gaba ɗaya hankalin mutanen kirki ya gama tashi, domin sun sadakar da nasara ta kubcewa, Salmanu.
Shi kuwa Salmanu tattaro sauran ƙarfinshi kab yayi,
ya narka mishi bulala ta 49-50".
Amman shirunshi.
Ihun da kafuran ƙabilar ɓachama suka sakine ya tabbar an gama, nan take suka shigo filin da gudu ruggumeshi suketayi suna shafa bayanshi, da yayi shati-shati.

Shi kuwa Salmanu gaban Arɗo yaje ya zauna, nan aka basu ruwa sukasha gaba ɗayansu.
Hutun 30 minutes sukayi aka koma fagen fama.

Da ƙarfi mai busan sarewa ya busa alamun a fara,
wani irin kafurin murmushi Ba'ana yayi tare da gyara riƙon da yayiwa bulalar tashi.
Cikin tsananin mugunta ya ɗan koma da baya, kana ya ɗago bubalar da masifan karfi ya zabgawa Salmanu ita a tsakiyar fatan bayanshi.

Wani irin gan tsarewa Salmanu yayi, sabida wani irin masifeffen azaba mai girgiza zuciya da yaki yana ratsa dukkan sasasan jikinshi.
Bai gama dawowa daga gigi da azabar bulalar forkoba, yaji ta biyu,
Rumtse idanunshi yayi da azaban ƙarfi, gaba ɗaya inda bulalar ya taɓashe, harbin kunama yakeji yana ratsashi.
Wani irin numfarfashi yaka lokacin da aka zabga mishi bulala ta goma.

Gaba ɗaya hankalin mutane ya tashi domin kowa yaganshi yasan yana jin azaba.
Bulala ta ashirin da biyar da akayi mishine ya sashi buɗe idanunshi da suka koma jajazir dan azaban da yakeji.
Su kuwa kafuran nan sai ihun farin ciki sukeyi.
Shi kuwa Barmuji zagayawa yayi gaban Salmanu wai yaga ko idonshi ya kawo ruwa,
babu ruwa kam sai azabar da yakeyi tamkar idanun zasu faɗo ƙasa, ci gaba da irgens yayi.
"Ashirin da uku! Ashirin da huɗu!!".
Wani irin tsalle Ba'ana ya buga da iya ƙarfinshi ya tsulawa Salmanu bulala ta ashirin da biyar.
Wani irin duhune ya rufe ganin Salmanu, saiga wasu zafafan hawayen azaba sun kwaranyo masa, ihu ya kuma zurma jin zafin bulalar ta isa kan mazantakanshi.

Gaba ɗaya su Bappa dama matasan kowa rufe ido yayi sabisa dukan da akewa Salmanu dukane na son ɗaukan rai.

Aysha kuwa tana gidansu kamar kullum tajiyo ihun Ya Salmanu kamar yadda kullum ihun wanda ake gasar dasu ke shaida mata sun faɗi.

Cikin kuka konta bisa cinyar Ummey tare da cewa.
"Shike nan Ummey zai kashe ya Salmanu".
Tuni itama Ummey da Inna hawayen suke zubdawa.

A can gidan Arɗo Yabani kuwa inna laure Maman Salmanu, kuka takeyi tamkar zata shiɗe domin yaranta mata sun zo sun gaya mata halin da yake ciki.


A can wurin gasar Shaɗi kuwa, ganin tuƙuru Ba'ana so yake ya kashe Salmanu ne yasa,
matasan Fulani sukayi kanshi dan dukanshi yake harda tattakashi kuma tuni ya wuce balali hamsin ɗin ƙa'idar gasar.

Koda matasan Fulani suka shiga dan crton ran Salmanu kawai sai ga ƙabilar ɓachamawan nan, sun fara zaro makamai sun rufa duk wani ba fulatani da duka da saran wuƙa.

Lokaci ɗaya wurin ya hargitse gaba ɗaya.
Aka kaure da faɗa saida.

Ganin wurin ya hargitse ne yasa,
Gaini yayi saurin kiran hukuma mafi kusa ya sanar musu.
Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa suka iso.
Hakane yasa duk ƙabilun Ɓachamawa suka gudu.
Allah ya takaita faɗan baiyi nisa ba, a take ɗaya daga cikin police ɗin wanda yake abokin Salmanu ne ya kwashesu suka tafi asibi.

Bayan garin ya lafa, kowa ya dawo haiyacinsa ne.
Isa ƙanin Salmanu ya tafi asibiti dan jinyar ɗan uwanshi kuma Alhamdulillah da yake ya samu taimakon gaggawa komai yazo da sauƙi.

Shi kuwa Ba'ana daga nan izayarsa ta ƙaru manufarsa shida ƙabilar ɓachamawa shine. Su tarwatsa al'ummar fulanin Rugar Bani baki ɗayansu.

Zuwa yanzu kuma ko ƙudane in dai na mijine to bazai sauƙa kan jikin Aysha ba,
sabida asirce, asircen da yakeyi da kuma tsoronshi da akeji.

Aysha kuwa ko zuwa dubo Salmanu ya hanata domin yace muddin taje a bakin ransa.

Yau kwana huɗu da faruwar abun, ya da faruwar abun kuma yau ta kasance jumma'a ne.

Kasan cewar jummace yasa gaba ɗaya makiyayan suka taso kiwo da wuri, sabida son samun jam'in sallan jumma'a.

Iro ɗaya daga cikin yaran Ahaji Horo, wanda yake yayan Binto da kuma Junaidu.
Kusan shine karshen dawowa kiwo.
ya taso ya taso tarin dabobbin sa a gaba kenan ya haɗu da gungun matasan Ɓachamawa, har sun wuceshi, sai kuma suka bishi a baya, cikin izaya babban cikinsu yace.
"Kai ɗan fullo nan garin ubankane ko garin ubanmu?".
Cikin jarumtar jinin fulani yace.
"Gari dai da daji namune tunda iyaye da kakannimu sun saya, in kuma kuna maganar tushen nasabane, to Adanawa Yola dama kewayenta duk namune fulani".
Cikin mugunta ɗaya daga cikinsu ya kai mishi mari da addan dake hannunshi".
Murmushi Isa yayi cikin hausar fulani yace.
"Kada ka sake dukana".
Kusan a tare suka haɗa bakin wajen cewa.
"In mun dakeka sai me?".
A kufule yace.
"Wallahi sai in rama, yawanku ba shine abin tsoro ba".
Ai kafinma ya rufe baki suka haushi da duka,
da sauri ya fara kare kanshi tare da kai musu duka,.
Kamar da wasa su rai shida sun gaza ji da ɗan lenge-lengen saurayi matashi ɗan Fulani.
Ganin kamar zaici galaba a kansune, yasa, ɗaya daga cikinsu ya dawo baya-baya ya zaro wukar dake ƙugunshi, da ƙarfi ya dawo kan Isa, ya luma mishi wuƙan a cikinsa wani irin ƙara isa ya sake, sai dai babu mai jinsa bare ya kawo masa agaji domin.
Dai-dai wannan lokacin duk wani musulmin wannan yankin yana masallacin jumma'a,
Da wannan damar suka samu suka kashe isa,
wanda suka daddatseshi da wuƙa.
Daga nan suka kira Ba'ana a waya, nan take ya kaɗa shanayen yace. "Yauwa aikinku yayi kyau, yanzu kuyi maza kuyi gaba da shanayen kasar Cameroon, zaku nufa birnin Yahunde kuna isa bakin boda yarana na kasar zasu amshi shanayen ku kuma sai ku dawo, kafin nan ma komai ya lafa baza'a zargekuba".
Haka kuwa sukayi, suka kaɗa kan shanu suka fasa daji, suka nufi hanya, shi kuma ya dawo cikin gari ya wuce ɗakinsa bayan ya bawa uwarsa lbri.


Koda aka taso sallan jumma'a, anyi mmkin ganin isa bai dawoba, shiru-shiru dai har akayi sallan la'asar babushi, tofa daga nanne hankali ya ƙara tashi.
Cikin kiɗima suka fara shiga daji a duba ko lfy bai dawoba.

Ai kuwa nan maza matasan Fulani suka watse cikin daji,
Bayan sun gama bulayin nemane babushi babu shanunshi, suna cikin zagayawan ne Sale yayi arba da gawar Isa dake malale cikin jini.
Nan suka ɗauki gawa suka koma cikin gari dashin.

Wannan rana hankali Fulanin Rugar Bani yayi masifar tashi, gaba ɗaya ma sai ba'amaida hankali kam ɓatan shanunba,
Hankali ya tashi, ɗauki ɗai-ɗai da akeyi musu ya fara hautsuna musu tunanin,
Gashi kisane da babu wanda za'a iya kamawa, koda aka sanarwa hukar cikin Numan sai suka korasu da case ɗin, sabida a lokacin da suka zo shigar da report babu musulmi a police cikin officers ɗin shiyasa suka korasu da batun.
Salmanu wanda shine ɗan bokon da kan iya jagorantan lamarinsu, yana gadon asibiti, bisa ƙarƙashin kulawar abokinshi badon hakaba da tuni Ba'ana ya kasheshi.

Koda fulani suka hatsala kamar kullum haka Arɗo Yabani ya tarasu ya taushi zuciyarsu, da kuma shawarar, su kai kukanmu ga sarkin Numan ɗin, tunda ya hanasu samun damar ganin sarkin Nuruddeen Bubayero.

Koda sukaje masarautar Numan ɗinma abin da akayi musu a police station, fiye dashi akayi musu.

Dole suka dawo suka nade hannun suka kai kukansu ga, Allah, sai dai sun ɗauki mataken kare kai da kai, bisa shawarar daddatawa cewa kada makiyayan ko manoma su yarda su rinƙa rabuwa a daji ya zama suje tare su dawo tare da hakane zasu gane mai ke musu ɗauki ɗai-ɗai ɗin.

Yau la'hadi tunda safe, Aysha keta shirin komawa makaranta. Sabida hutunsu ya ƙare.

Tafiyan safe takeso tayi shiyasa ta gama shirinta da wuri.

gaba ɗaya suna tsakiyar gida Yayunta maza sune zasu rakata bakin hanya.

Haka nan taji bata son tafiya ta barsu, tsoro mai yawa ya rufeta Especially in tayi tunani da yadda ake kashe makiyayan.

Durƙushe take gaban Bappa yana yi mata masiha mai ratsa jiki da zuciya ya kare nasihar tashi da cewa.
"Allah ya miki al'barka Shatu, Allah ya kaiki lfy."
cikin sanyin murya tace.
"Amin Amin Bappa ngd matuƙa".
Sai kuma ta kalli Ya Giɗinta da ya zuba mata ido tamkar bai taɓa ganintaba, cikin sanyin murya yace.
"Yanzu shike nan zaki tafi ki barmu, ki tafi can ke ɗaya ki zama baki da kowa naki a kusa".
Haka nan kalamanshi ya karyar mata zuciya, sai kuma taji hawaye nason zubo mata.
A hankali tace.
"Ya Giɗi bazan daɗe ba zanzo".
Cikin sanyi Seyo yace.
"Allah yasa ki samemu in kinzo ɗin".
Da karfi ƙrjinta ya bada wani sauti mai karfi, ta buɗi baki zatayi mgna kenan Ya Lado ya ɗanyi murmushi cikin sanyi yace.
"To Shatu Ni zan tafi inje in kunce dabobbin, bazan samu daman rakakiba, Allah ya kaiki lfy, ya ƙaddara saduwarmu kan al'khairi, ki yafe".
Kawai sai taji hawaye na zubo mata, cikin dariya ya

2 Comments On GARKUWA
avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment