Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kujerar kana ya jawo marfin motar ya rufe da ƙarfi sabida jin da yayi yana baya alamun zai koma baya ya faɗi.
Cikin mamaki da ɗaga murya yace.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun, ke me hakan? Zaki kadamu fa!."
Ina gaba ɗaya jikinta rawa tsuma karkarwa yakeyi tamkar mazari, cikin fizgar numfashin ganin tsira tace.
"Ya Sheykh Jahan! Jahan!! Jahaaaaan!!!".
Ta ƙarashe mgnar tare da shigewa jikinshi da kyau ta cusa kanta cikin ƙirjinshi, wanda yake bugawa dib-dib yana harba sama da sau ɗari a cikin ko wacce daƙiƙa.
Yayinda nata ke harbawa samada sau ɗari da hamsin a cikin ko wanne daƙiƙa sabida tsananin tashin hankali da kiɗima da firgici.

Cikin wani irin yanayi ya rumtse idanunshi da ƙarfi kana ya buɗesu da sauri, yayinda tuni suke jazir kana shima jikin nashi tsuma yakeyi.
Hannunshi yasa ya ruggumeta gam-gam a jikinshi da kyau, al'kyabbar jikinshi ya ware da kyau ya buɗa ta kana ya rufeta dashi rib. Sabida yadda jikinta ke rawa abin ya zarta zaton mutun.
Cikin wata iriyar murya mai cike da diriricewa tausayi rauni murya a sarƙafewa yace.
"A'ich! A'ish!! Kiyi haƙuri I'm so sorry, in sha Allah bazan sakeba, ki yafe min kinji".
Ina babu amsa sai ƙara cusa kanta da takeyi jikinshi bata kuma haiyacinta har yanzu bare ta fahimci me yake faɗin.
Cikin taune lip ɗinsa na ƙasa yace.
"A'ich ki nitsu ki kwantar da hankalinki babu abinda zai sameki. Kinji ba gani ba.
Babu kowa da zai cutar dake da izinin Allah".
Ina ita dai sai ƙara ƙwaƙumarshi takeyi.

A hankali ya juyo ya kalli gefenshi jin ana ɗan ƙwanƙwas glass ɗin motar,
Ƙasa yayi da glass ɗin.

Ya Hashim ne da Affan da Jalal Imran da Sulaiman sai Kabir ƙanin su Haroon wanda suka haɗa uba, kuma a motarsa suke da kuma motar ɗaya Haroon dake hannun Jalal,
kasan cewar bai sauƙe gilashin sosaiba, basa iya ganin Aysha dake kwance a jikinsa.
Affan ne ya ɗan motse kana yace.
"Ya Sheykh mufa gobe sammako zamuyi, shiyasa muke son key ɗin motar ya kwana a hannunmu".
Kanshi ya jingina da jikin kujera kana ya kalli Ya Hashim da Sulaiman da Imran yace.
"Ku bari sai jibi ku tafi, mana kunzo jiya, gobe kuce zaku koma ku dai bari jibi".
Kai Sulaiman da Ya Hashim suka gyaɗa alamun yarda.
daga nan suka juya suka nufi motar Kabir tare da cewa.
"To sai da safe".
Allah ya bamu al'khairi yace kana ya ɗaga glass ɗin.
Su kuma suka shiga mota sukaja suka tafi.


A can gida kuwa bayan duk sun watsa ruwa kowa yayi shirin baccine, sai kuma duk suka firfito falo suka kafa hira irin ta ƴan uwa in an haɗu a biki.
Umaymah ce ta kalli Aunty Rahma dake kwance gefenta tayi pillow da cinyarta tace.
"Wai ina Safiyyah da Aysha ne, su ban gansuba".
Gyara konciyarta tayi tare da cewa.
"Safiyyah dai tabi mijinta, ita kuma surkar tawa inaga itama suna tare da ɗan naki".
Ummi ce ta ɗan kallesu tare da cewa.
"Ai kuwa ni tun ɗazuma naketa kiranta bata ɗaya wayar".
Mamma ce tace.
"Halan suna can tare".
Hajia Mama dake zaune gefen Umaymah ce ta ɗan kishiƙiɗa da tum-tum tace.
"Uhummm". Daga nan bata kuma cewa komaiba.
Ummi kuwa ci gaba da kiran Aysha tayi, wayar tana shiga amman ba'a ɗagawa.

A can kuwa wurin Sheykh da Aysha.
Gyara zamanshi yayi da kyau bayan, abokan Abbanshi duk sun tafi.
Gyara mata zamanta a jikinshi yayi da kyau yadda bazata takurashi yin tuƙiba gaba ɗaya zuciyarshi a hautsine take, ya rasa gano wake tura mishi wasu pictures ɗin Shatu da mishi zantukan ita yar iskace.
Allah ya sani baya zarginta ko wannan abun ya fara faruwa ne dan ta ganshi da kamanninsa na sirri, da fari tsiya yake mata, sai kuma yake jin dadin yanayin yakanyi ta murmushi in ya tuno tsoron da yake gani a kwayar idanunta, yana mmkin yadda take gaza gane muryarsa, to batun hotunanta fa da ake tura mishi da wani yanzu ya gama gamsuwa aiki magautansa ne.
Ajiyar zuciya ya sauƙe mai nauyi tare da tada motar, A/C'nta ya kunna, sabida wata iriyar fitinenneyar zufar dake tsastsafo musu su duka biyun.
Ƙafarshi ya murza ya kaita kan birki, lokacin da ya iso gab da bakin gate, ɗan tsayawa yayi aka buɗe musu gate ɗin, kana ya cilla hancin motarsa woje.
Da hannun ɗaya yake murza siterin motar, hannun damanshi.
Kana hannun hagunshi kuma na ruggume da ita.
Zuwa yanzu yaji rawanda jikinta keyi ya fara tsagaitawa.

Ita kuwa Aysha cib tayi a jikinshi tana jin yadda bugun zuciyarshin ke harbawa da sauri-sauri kana kuma da ƙarfi-ƙarfi.

Tafiya mai tsawo sosai, har ya fara fitowa wojen gari.
A hankali ya ratsa wani titin ya shiga, tafiya kaɗan yayi ya ratsa cikin wani tamfatsetsen hotel mai masifar kyau wanda yake killace a bayan gari, sabida manyan mutane ba kasafai suke son hotel ɗin dake sarari ba.

Bayan ya gyara parking ya kashe motar.
Ɗan sunkuyar da kanshi yayi kanta
sannan a hankali yasa tafin hannunshi ya tallabo kanta, cikin sanyi ta buɗe idonta.
Ta ɗan kalleshi kana ta medasu ta lumshe.
Manyan yatsunshi yasa yana ɗan shafa kuma tunta dasu.
Kana a hankali yace.
"A'ish kiyi haƙuri kinji bazan sake yin nesa da keba".
Sai kuma ya ɗanyi shiru kana ya kusanto da fuskarshi gareta sosai, a hankali ya hura mata iskar bakinshi kan idanunta tare da cewa.
"Buɗe idon Yah Sheykh ɗinki ne, ba Jahan ba".
A hankali ta buɗesu, ta kalleshi.
Wani dogon nannauyan ajiyan zuciya ta sauƙe tare meda kanta saman ƙirjinshi".
A hankali yace.
"Wayyo Mamy zata karya min cinya, sauƙa muje ciki."
Bata kulashi ba, ganin hakane yasa ya buɗe ƙofar kana ya ɗan mirginata gefe, sannan ya sauƙo.
Gyara tsayuwarshi yayi tare da gyara hiraminshi ya rufe fuskarsa da kyau sannan yace.
"Aish fito ko Boɗɗi".
Da sauri ta zuro ƙafafuwanta woje sabida gani take yana matsawa Jahan zai zo.

Marfin baya ya buɗe. Wasu ledodi masu kyau ya ɗauka kana ya rufe motar tako ina, sannan ya juya, ya nufi ciki da sauri ta bishi a baya.
Tafiya kaɗan sukayi suka haɗu da Jamil.
cikin sauri ya iso gabansu, key ya miƙa mishi tare da cewa.
"Room number 37 VIP Side".
Kai ya gyaɗa tare amsar key ɗin.
"Sai da safe". Yace yana mai wucewa.
"Allah ya bamu al'khairi yace kana.
Suka wuce shima ya wuce.

Suna shiga, ɗakin.
A hankali ya miƙa mata ledodin.
Sannan ya juyo ya rufe ƙofar, duk da yasa Jamil ya bincika masa ɗakin saida ya ƙara duba jikin ƙofar da makunnin fanka da A/C da kyau. Kana ya dawo tsakiyar ɗakin ya ɗaga kanshi sama ya kalli sanan sosai hakama ya shiga bathroom ya duba komai saida ya tabbatar ba komai daga cikin ababen da ya kamata duk musulmi in larurar zuwa hotel ya kamashi ya tabbatar da ya bincikesu da kyau Especially in ku mata da miji ne.

Ita kuwa Aysha da Ido take binshi, ta rasa me yake nema a duk ɗakunan hotel da suka taɓa zuwa.

Bathroom ɗin ya koma, bai daɗe sosai ba, ya fito, bisa alamu ruwa ya watsa, kana dan al'kyabbar shi na hannunshi yanzu dagashi sai jallabiya.
ninke al'kyabbar yayi, kana, ya ajeshi gefe, inda ya ajiye hiraminshi da wayoyinshi.
Ledodin hannunta ya amsa tare da cewa.
"Je kiyi wonka kizo ki kwanta".
Cikin sanyi tace.
"Ni nayi wonka ɗazu".
Kanshi ya gyaɗa dan ya lura har yanzu a tsorace take.
Zama yayi bisa sallayar da yasan Jamil ne ya shimfiɗa misa kana yace.
"To zauna kici abinci".
Da sauri tace na ƙoshi".
Ido ya ɗan zuba mata, kana yace.
"Uhummm, to kwanta kinga gani nan kusa babu abinda zai sameki da izinin ubangiji".
Da sauru tace.
"Toh".
Ta ƙare mgnar tana nufar kan luntsumemen gadon.
Ledodin da Safiyyah ce ta ajiye musu cewa na abincin walimar ne kuma tace mishi Ummi da Umaymah da Mamma ce da kansy sukayi aikin ne yasa, ya gamsu da aikin kuma zaici.
Sosai yaci naman zabuwar da Arish ɗin.
Ɗan saura kaji akayi na zabbin na musamman ne shiyasa su Umaymah suka yishi da kansu.

Ruwa yasha, kana ya gyara zamanshi tare da tattare sauran bakin ledar ya ƙulle. Jingina bayanshi yayi da jikin gadon.
Kana ya fara rairai karatun al'ƙur'ani cikin zazzaƙar muryarsa haka yasa yaji sanyi zafin da zuciyarsa keyi na fahimtar sharrin magautanshi har baiwar Allahr da bataji bata ganiba, kawai dan ta kasance matarsa magautansa ke bita da sharri.

A hankali Aysha ta sauƙe ajiyan zuciya, tana mai jin daɗin sautin muryarsa da karatun da yakeyi a hankali.

Mirginowa tayi bakin gadon.
Kana ta kwanta tayi lib ta matso da kanta kusa da kafaɗunshi.

Lokacin ɗaya taji bacci na fizgarta.
Shi kuwa Sheykh a hankali ya juyo ya kalli wayarshi daketa haske alamun ana kiranshi.
kasan cewar yazo ƙarshen suratul Maeda sai yayi addu'a ya shafa.
Kana ya miƙa hannunshi ya ɗauki wayar, Ummi ya gani a saman screen ɗin ya kai yatsarsa kenan kiran ya katse.
Dama shima katse kiran zaiyi shi zai kuma kiranta.

A can gida kuwa Umaymah ce ta ɗan kalli Ummi tare da cewa.
"Sake kiranshi ni naji tsoro ita a kirata bata ɗagawa kuma shima a kirashi bai ɗagawa".
Cikin gyara zama Ummi tace.
"Zai kira, in yaga kiranmu inaga baya kusa da wayane sanda kika kirashin."
Shiru suka ɗan yi.
da sauri Ummi ta kalli wayarta.
"Yauwa gashi ma ya kira".
Ta faɗa tana amsa kiran.
"Assalamu alaikum, Ummi".
Cikin jin daɗi tace.
"Wa laikassalam Sheykh kana lfy".
"Alhamdulillah". yace
Yana gyara zamansa.
Da sauri tace.
"To Masha Allah. Aysha fa munyi ta kiran wayarta bata ɗagawa, hankalinmu ya tashi tana lfy ko?".
Juyowa yayi ya ɗan kalleta kana yace.
"Uhummm to ga dai ta nan Ummi, wannan tsoron nata ne yau kuma ya dawo a cikin mota kafin in fito tace, wai Jahan yazo, gaba ɗaya ta gigice shiyasa ma ban kawota nan wurinku ba". Ya ƙarashe mgnar a kunyace wai kada suyi zaton rashin kunyane da jarabar mace ya sashi ɗauketa.
Cikin tsoro Ummi tace.
"Subahanallahi Jahan kuma, Sheykh ya kamata kasa ido sosai fa a kan abun nan".
Juyowa yayi ya ɗan kalleta, tayi shiru ta zuba mishi ido.
A hankali yace.
"Ummi babu batun wani Jahan fa, Ni inaga Ja Ha N nefa Ummi suka bada Jahan.
Kawai dai magautanna ke mata barazana da sunan.
Dan suna da wata manufa akanta akayi katari kuma akwai mai suna Jahan sanane a gari aikinsa kuma sirrine, shi kuma an bani tabbacin ma baya ƙasar mafa tun watannin baya kawai mutanenta ne".
Da sauri ta tashi zaune cikin rauni tace.
"Wallahi mutum ne, ba iska bane, Ni bani da iska ka dena cewa iskokaina, wlh Ummi mutum ne".
Ummi da taji muryarta cikin kula tace.
"Sheykh ka ƙara kula kan iya linka".
"To Ummi". yace
Ita kuwa Umaymah ta miƙawa wayar.
Jin muryar Umaymah ne ya sashi cewa.
"Umaymah ba komai fa ku kwantar da hankalinku".
Cikin kula da so tace.
"To Jazlaan Allah ya kare mun ku, saida safe ko".
Amin Amin yace kana ya katse kira.
Miƙewa tsaye yayi, tare da wayar a hannunshi inbox ɗinsa ya ɗan shiga text ɗin da aka turo mishi ɗazu da pravate number, ya Kuma zuwa ido.
"Da kyau kayi tabsir mai zafi, sai ka kula da yar iskar bororiyar da aka auro maka, mai son maza.
kayi amfanin da wannan damar ko zaka gaskata abinda muke gaya maka, na son maza da binsu."
Idonshi ya rumtse da ƙarfi kana ya buɗe su a hankali.

Su kuwa can sashin magautan Sheykh sun dade da fara turo mishi irin waɗannan saƙonnin a saninsu dai sun san sun kashe mazakunta Sheykh bazai iya raɓar maceba.
Shiyasa suke nuna mishi ita Aysha yar iskace dan su samu su haddasa zargi a tsakaninsu, shiyasa suke cewa ya gwadata duk da su a zatonsu wani zai wakilta ya gwada masa ita.
Sabida basu san yanada wani sashi na sirrin aikinshiba. Wanda yake bibiyar komai wanda Shatu kuma ta taɓa yin karo dashi a lokacin da yake fita aikin nashi da dare.
So shiyasa yake amfani da wannan damar.

Numfashi mai zafi ya fesar.
A hankali ya kalleta ganin ta mirgina ta koma can tsakiyar gado tana mgna kaɗan-kaɗan.
"Ni bani da iska Allah ma ya sani, koma menene ai a gidanka ne ya fara min, komai sai kayi ta cewa inada iska, har kana gayawa mutane, zakasa ayita min kallon mai iska.
Na tambayi Bappa na yace min iya tsawon rayuwata basu sanni da iskaba, kuma ai da sun sani da zasu gayawa Lamiɗo".
A hankali yasa hannunshin ya kashe wutan ɗakin.
Da sauri ta taso zaune lokacin da duhu ya mamaye ɗakin.
"Dan Allah ka kunna wutan".
Da sauri ta matso kusa dashi jin yayi mgna kusa da ita yace.
"Ni bana iya bacci in haske na kunne. Kwanta gani nan babu wani al'jani Jahan da zaizo da yardar Allah".
A hankali ta zame ta kwanta kusa dashi.

Yayinda shi kuma yake zaune.
"Tashi ki zauna kiyi addu'a kafin ki kwanta". Yace mata lokacin da yaji ta kwanta.
Cikin bacci tace.
"Na gaji kayi min mana".
Kanshi ya jinjina jin wai ai ta gaji.
Tafukan hannunsa ya hada ya buɗa, kana ya karanta ƙulhuwa 3 falaƙi 3 nasi 3 Ayatulkursi'u 1 ya tofa, kana ya shafawa jikinsa.
Sannan ya kumayi kamar yadda yayi ya tofa kana ya juyo kanta, daga kan fuskarta ya kife tafin hannunshi ya shafa mata har zuwa kan yatsun ƙafarta kana ya shafa kanta, sannan ya kwanta kan gefen damanshi.
A hankali yasa hannunshin ya juyata yace.
"Kwanta ta gefen dama".
To tace ya zama baya ta bashi.
Shiru tayi tanajin alamun kamar karatu yakeyi.
tsawon lokaci sukayi a haka batayi bacciba shima baiyi baccinba.
A hankali ta juyo sabida gajiya da gefen daman yayi mata.
Lumshe ido tayi.

Shi kuwa Sheykh a hankali ya yunƙuro ya matsota sosai, cikin sanyi tace.
"Ka matseni fa".
"To ki koma can baya mana."
Yace mata. Yana lumshe idonsa.

A hankali ta mirgina zata matsa, sai kuma ta ɗan tsaya jin tama isa bakin gado, daga ita sai katanga, juyowa tayi ta fuskanci katangar ta kwanta tayi shiru.

Shi kuwa Sheykh shima shirun yayi, yana dogon nazari kan al'amarin Jahan da yake girmama kullum a wurinta, ya lura yau saura kiris ta suma.

Numfashi ya ɗan fesar a sanyaye kana ya juyo da kyau ya fuskanceta, sannan ya matsota ya manna bayanta da ƙorjinsa.
Da sauri ta buɗe idonta tare da buɗe baki zatayi mgna sai kuma tayi shiru jin ya sunkuyo kanta kanta sosai daga koncen, kanta ya ɗaga kana ya ture pillow'n da kanta yake kai, sannan miƙar da hannunshi a wurin,
kanta ya kwantar bisa damtsen hannunshi da ya miƙar, kana ya juyota rigingine, ƙafarshi ya ɗan ɗaura gefen cinyarta kaɗan,
kana yaja cinyarta yasa tsakankanin cinyoyinshi.
a hankali ya fesar da numfashi kana murya can ƙasa yace.
"Shike nan baki da iska.
Kiyi haƙuri, Umaymah kawai na gayawa fa."
Cikin wani irin masifeffen sanyi da jin daɗin kulawarshi gareta a hankali tace.
"Toh, amman Yah Sheykh da gaske inada iska ne wai".
Kanta ya shafa kana yasa bakinshi ya sumbaci goshinta cikin son kawar da tambayar tata yace.
"Me Jahan ɗinkin yake miki in yazo wurinki? Yana mgna ne? In yanayi me yake ce miki?".
Baki ta tura tare da cewa.
"Ni dai ba Jahan ɗina bane".
hannunshi yasa a hankali ya fara janye dogowar rigar jikinta yanayi sama dashi kana yace.
"To na ji, me yake miki?".
Cikin takaici tace.
"Ba kanaga kamar wai al'januna bane sai kake ɗaukar abin wasa to wata rana sai yamin ciki ai da ƙarfi".
Cikin sauri ya rumtse idonshi da ƙarfi tare da yin sama da rigar sosai kana a hankali yace.
"Na yarda ai baki da al'janani.
To amman ta yaya zai miki ciki".
Juyowa tayi ta fuskanceshi da kyau kanta na damtsen hannunshi, tattausan gemunshi na taɓa goshinta, cikin muryar da tafi kama data tsoro da raɗa tace.
"Duk fa lokacin da ya zo na ganshi sai yayi kissing lips ɗina.
Ɗazu kuma harfa kwance min igiyoyin wuyan rigata yayi, gasuba har yanzu ban ɗauresu ba".
Cikin hikima ya zare hannunta ɗaya cikin rigar kana ya zare ɗayanma sannan yace.
"To sai kuma yayi me daya kunce igiyoyin?".
ya ƙareshe mgnar yana ajiye rigar tata bisa inda ya ajiye al'kyabbar shi.
Kana ya zare jallabiyar jikinshi, ya ajeta, sannan ya matso gareta tare da jawo musu blanket yace.
"Uhumm".
Cikin tsurawa inda yake ido tace.
"Harda sa hannunshi cikin rigata, kuma yana mammatse min ƙirj.."
Da sauri ya lumshe idanunshi tare da jawota jikinshi ya matseta gam har saida tayi ƙara sabida matsar tayi ƙarfi, shi kuwa Sheykh gaba ɗaya jikinshi tsuma yakeyi ya gama gamsuwa Shatu Mar'atussaliha ce.
Ya yarda ita bata da wanda ta yarda dashi a Masarautar Joɗa sama dashi bata ɓoye mishi komai, ya kuma gamsu da son kiyaye lfyarsa da takeyi.
Cikin wata iriyar fitinenneyar murya mafi daburcewa yace.
"Bana son ji, kuma kodama al'janin nakine, zanyi mgninshi da izinin Allah, bashi da hurimi da mallakin Muhammad, shi kaɗai yake mallakar abunsa, kuma ko gani nai wani bazai yiba in sha Allah a mutum dai babu mahaluƙin da zai min kutse a gidana ma bare a kan iyalina."
Ita dai ba jinshi sosai takeyi ba, sabida wasu abubuwan da yakeyi mata sun zarta abinda Jahan ya aikata mata.

Dib, dib, dib, haka zuciyarta keyi lokacin da taji ya haɗe lips ɗinshi da nata, kana tattausan tafin hannunshi na yawo a cikin dukkanin sasan jikinta.
Gaba ɗaya sai tsoro ya rufeta, a hankali taketa jujjuya kai alamun a a.
A hankali ya rabe lips nasu, cikin sanyi tace.
"Ya Sheykh bacci nakeji".
Uhummm yace kana ya gyara musu kwanciyar.


A can ƙasar Cameroon kuwa.
Ba'ana ne zaune gaban wani ƙasurƙumin bokanshi mai ƙara buɗa mishi ido, da koya mishi siddabaru iri-iri.

Wani ƙaton kaskone a gabansu.
Cikin muryar da babu daɗin amo boka Dumba ya cewa Ba'ana.
"Leƙa ka gani, gacan ajiyarka tana kwance tana bacci lfy lau babu wani mahluƙin namiji da zai iya taɓa koda farcenta ne bai mutuba, bare har ya shafeta ko ya kai ga taɓa wani sashin sirri na jikinta bare a kai ga ya kusanceta".
Tuni Ba'ana ya leƙa kanshi yana ƙarewa fuskar Aysha kallo, cikin jan dogon numfashi yace.
"Boka Dumba to shi wannan haskenfa da yake kwance kusa da ita menene shi kuma wane haskene ya zagaye ɗakin da fuskarta?".
Cikin yin cacuɓe-cacuɓenshi yace.
"Wannan haskene dake wanzu da izinin ubangiji haskene dake kare wanda ke kusa da ita sam bamu da tsumi ko dabarar ganin komai a kanshi, sabida shi mutum ne da bakinshi baya bushewa da ambaton Allah kana baya rabuwa da al'wala a jikinshi.
Ita kanta in dai tana kusa dashi ainun jikinta ya taɓa nashi to bazamu ga komai a kanta ba, batun kusanta ne dai tabbas babu mahaluƙin da zai kusanceta ya rayu, domin madadin ɗanɗanon ni'imomin da ko wacce mace take dashi, in namiji ya sadu da ita, to ita dafin kuna da macijiya ne ni'imarta zata shigeshi a sashi mai tsada a jikinshi kan gari ya waye zai mace ya bar duniya".
Wata iriyar muguwar dariya suka kece da ita kamar zasu fasa kogon da suke ciki, boka Dumba ne yaci gaba da cewa.
"Kai dai ka gama aiyu kan ka hankalinka kwance, shi wannan da yayi sanadin faɗinka gasar Shaɗi har yasa kabar ƙasarku, tuni munsa ajalinshi a jikin matar da yakega matarsa ce, kaga koda baka tare da Shatu zata tayaka yaƙi ba tare da ta sani bama".
Cikin jin daɗi da baƙar mugunta Ba'ana yace.
"Dole ma ya mutu, sai dai babarsa ta haifi wani hegen bafullatani mai jajayen kunnuwa".

Daga nan sukaci gaba da hirarsu da tanadin hana fulanin ƙasar Nigeria da Cameroon zaman lfy.


A nan Ɓadamaya kuwa, cikin Masarautar Joɗa, a wannan lokaci na tsakiyar dare.
Suka fito cikin masarautar suka nufi gidan boka Tsitaka, garin yayi duhu yayi dim sai azabar zafi da ake tsulawa zafi irin na tsakiyar damuna irin wanda in an kwana biyu ba'ayi ruwan samaba, bisa alamu hadari ke diddigowa daga ƙasa shiyasa garin yayi dim babu alamun iska.

Suna shiga Boka Tsitaka ya kwashe da dariya tare da cewa.
"Lbri mara daɗin gashi can konce da matarsa bisa gado ɗaya, sai dai kun san ɗan naku ba'a iya ganin sirrinshi, ko matar tashi bana gani sai wani haske daya rufesu.
Kuma yana gab da ɗirkawa ƴar fulani ciki hegen yaro dan yanada ƙoyayen haihuwa da ƙenƙesa".
Cikin tashin hankali ɗayan yace.
"Kusantar mata harda haihuwa, anya kuwa bazan sa a dandatse min wannan yaron ba, shin wai shi wanne irin mutum ne da baya jin sihiri da tuggu da makirci".
Ɗayan ne yace.
"Ai kuwa koda ya haihu yarane dai bazasu rayuba".
Dariyar mugunta Boka Tsitaka yayi tare da cewa.
"Ku dai kun iya kawo aiki kun kuma iya faɗin mugunta sai dai tabbas akwai wani wanda yake gefenku, da yake aikata musu fiye da shirinku, kullum in kun tuna yimasa wani abun kafinma kuyi abun zakuga fiye da hakan ya faru tun shekarun baya.
To bare kuma yanzu an sake samun wani taƙadirin ma yasa mishi ido".
Dariyar jin daɗi sukayi kana sukaci gaba da muhawarar mugunta.

Washe gari azahar Gimbiya Aminatu ce zaune gefen Lamiɗo da ya kira Sheykh suna gaisawa, tare da cewa.
"Muhammadu Akwai babban uzurin dake buƙatar ka dawo gobe".
Gyara zamanshi yayi tare da kallon Aysha dake gefenshi ita da Hibba da Jalal da sune suka kawo musu abinci a hotel ɗin da suke. Maida kanshi yayi ya jingina da kujera kana ya lumshe idonshi tare da cewa.
"Eh dama gobe zamu taho, amman sai dare jirginmu zai tashi.
Su Ya Hisham da Affan kuwa sunce sammako zasuyi wai tafiyar mota zasuyi".
Cikin sauƙe numfashin Lamiɗo yace.
"To Allah ya kaimu ya kuma dawo daku lfy, itafa Juwairiyya sai yaushe zata dawo".
Kanshi ya ɗan mirgina kana yace.
"Zan dai taho da Ya Jafar da Jalal, in bata gama uzurorinta ba, sai ta koma masarautar Jadda ta dawo daga baya."
Cikin gamsuwa da hakan Lamiɗo yace.
"To hakan yayi Allah ya kawoku lfy".
Amin Amin yace kana ya katse kiran.

Jalal ne da Hibba suka miƙa tare da cewa.
"Mu zamu tafi."
Bai kulasu ba, Jalal ne ya ɗan matsoshi tare da cewa.
"Umaymah tace ka kai mata Ɗiyarta taga ya ta kwana da jikin".
Kai ya gyaɗa alamar to.
kana Hibba ta kalleta tare da cewa.
"Aunty Aysha sai kin dawo, Allah ya ƙara sauƙin".
Amin tace tana gyara zamanta tare da jawo ƴar jakar kayan da Hibba ta kawo mata. Wai na anko ɗin fansan idon da za'ayi.

Su kuma nan suka fita.

Suna fita, ya miƙe ya rufe ƙofar, kana ya dawo ya hau kan gado ya kwanta.
Da ido ta bishi tare da cewa.
"Yah Sheykh gado kuma to yaushe zamu tafi ko inbi su Hibba kawai ne?".
Lumshe idonshi yayi alamun bacci zaiyi, a hankali tace.
"Dole ne kullum sai kayi baccin tsakanin azahar da la'asar ɗin nan". Kanshi ya gyaɗa mata alamar eh.
kana ya juya mata baya.

Dole itama ɗin ta hau ta kwanta, tana konciya ya jawota jikinshi nan take sukayi bacci.


Ƙarfe uku da minti arba'in da biyar ya farka, da sauri ya zareta daga jikinshi kana ya shiga bathroom, wonka yayi fes kana yayi al'wala ya fito.
zaune ya sameta bakin gado.
"Tashi kiyi wonka mu tafi tunda ke bakya cikin masuyin salla".
Cikin sanyi tace.
"Ah ina cikin masuyin salla mana".
Kai ya gyaɗa yana zura tattausan al'kyabbar shi. Yace.
"Eh amman ni dai tun jiya banga kinyi salla ba".
Cikin rashin fahimtar wayon da yake mata tace.
"In Sha Allah gobe dai da safe ai zan fara".
Murmushi yayi tare da cewa.
"To tashi kiyi wonka kafin inyi sallan".
To tace kana ta miƙe ta shiga Bathroom da ƴar jakar kayanta.
Shi kuwa ya kabbarta sallan la'asar.

A cikin bathroom ɗin ta canza kayanta bayan ta kimtsa jikinta.
Kana ta ninke wanda ta cire ta saka a ciki ta feshe jikinta da turarenta mai sanyin ƙamshi, sannan ta fito.

Zaune ta sameshi bisa sallayar yasa System ɗinshi a gaba ya maida hankalinshi kab kanta. Bisa alamun wani abu mai tarin mahimmanci yakeyi.
Dan gaba ɗaya yatsun hannunshi aiki sukeyi sai kwayar idanunshi da yake jujjuyawa kan screen ɗin na'ura. Yanayi kuma yana motsa lips ɗinshi alamun still kuma tasbihi yakeyi bincikar number da ake tura masa text a rufe yakeyi yadda zai samu ya buɗe layin yabi diddiginshi.
A hankali ta kalleshi da kyau, kana ta kalli kayanshi da ya cire ɗauka tayi ta ninninkesu ninkewa mai kyau, tasa a ƴar jakar ta zuge zip ta rufe.
Sannan ta koma gefenshi can ta zauna bayanshi.
Cikin sanyi tace.
"Ni dai banga wayata ba".
Bai kulata ba, domin aikin da yakeyi ya tunzura mishi nitsuwa.
Cikin sanyi tace.
"Ayyah to dan Allah. Sammin wayarka in yi kira".
Tura mata wayarshi dake gefenshi yayi sabida ya samu ta rabu dashi dan tana raba mishi hankali".
Ɗaukar wayar tayi sai kuma taga akwai security code a jiki.
Matsoshi tayi da mamaki dan tasan akwai woyoyin shi biyu data taɓa riƙewa basa da security, jujjuya yar wayar tayi ganin yar micilace kuma harda liƙa mata matakan tsaro, taɓe baki tayi tare da cewa.
"Me code ɗin buɗe shi".
"Mamey". Yace mata ba tare da ya kalleta ba.
jujjuya yar mitsitsiyar wayar tayi a tafin hannunta, contacts ta danna da nufin ta ɗan duba ko da number sai ta samu nanma a garƙame yake.
Ikon Allah tace a hankali kana ta danna. Phone na ma kirib yake, cike da mamaki tace.
"Wayarfa tako ina ansa mata

2 Comments On GARKUWA
avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment