Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

meya hanasu zuwa wurinki na tabbar in suna raye cikin ƙishin lfy, dole zan samu ɗaya daga cikinsu a wurinki".
Mari matar Arɗo Bani ce wacce ta ɗan dawo haiyacinta ne, ta rumtse idanunta wasu zafafan hawaye ne suka silalo mata, cikin sanyi tace.
"Shatu sun tafi kiwo ne, zaki gansu".
Jajayen idanunta ta zura mata,
Alamun tana son tabbatar da abinda tace matan.
Fahimtar hakane yasa ta gyaɗa mata kai alamar eh hakane.
Cikin son kontar mata hanlali ne, Rafi'a, tace.
"Kinjiko Aysha, to kiyi haƙuri ki nitsu in sha Allah dukkan tsanani yana tare da sauƙi".
Kife kanta ta kumayi tana mai sake kuka mai ciwo a zuciya, gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi.
Haka dai sukaci gaba da bata baki, wai dan ta samu nitsuwa amman ina, fargabanta sai tsananta yakeyi.

Su Bappa kuwa, isarsu Rugar Kikan ya ƙara tada hankali matasansu da suka dawo kiwo da matansu da suka dawo tallan nono wanda sanadin basa nanne yasa suka tsira.
Gaba ɗaya Rugar ta birkice ta kiɗime.
Hankali dattawan nan yayi masifar tashi, ganin duk an karkashe musu, mafiya yawan matansu yaransu da jikokinsu.
Especially Alhaji Haro, da iya cikin gidansa kawai saida aka samu gawar mutun goma sha uku.
Koda aka jera masa gawakin suma yayi. Sai ga Tsoffin nan suna kuka cur-cur da hawayensu, gwanin ban tausayi.
Ganin yamma na rufawane yasa,
Dattawan maƙotansu, mazansu suka fara wonke gawakin maza kamar yadda addininmu ya koyar da mu.
Mata kuma sukayiwa mata wonka,
Kana suka sallaci Gawarwakin da a ƙalla sun kai mutun Settin da uku 63.
Kana suka rinƙa binnesu da taimakon Hausawa musulman cikin Numan da maƙotansu fulani.

Gaba ɗaya garin yayi tsit ya koma tamkar kufayi. Sauran rayayyun sunyi Kuka har muryoyinsu. Sun disashe.

A cikin Genaral Hospital Numan kuwa.
Musulmai Hausawa da Fulani, sune suka rinƙa kawai Fulanin Rugar Kikan taimakon abinci.
Hankalin Aysha ya ƙara tashi ganin, har dare babu wanda yazo.

Hakama da gari ya waye.

Su Bappa kuwa da Arɗo Bani, Alhaji Haro. Malam Manu, Alhaji Umaru, tashin hankali da kiɗima da firgici da ɓacin ransu ya tsananta, sabida ganin.
Duk Hukumar ma sun tafi,
Gashi babu wani babba da yazo ya duba halin da suke ciki, sabida ai su basu san da cewar su Waziri sun zo tun jiyan ba.
Ransu yayi matuƙar ɓaci, ganin Gwamnatin jihar,
da Masarautar jihar, babu wanda ya tako ƙafarsa, yazo ya dubasu ko ya turo wakilinshi.
Wato matsalarsu bata shafi kowaba.
Wannan abun shine mafarin Fara da baƙar Kaddarar Shatu a tarihin rayuwar ta, domin iyaye da yayun wannan Rugar sun tunzura sun hasala, iya hasala, sun cika fam da tarin baƙin cikin rayuwa, an rigada an taɓo zuciyar Fulani haka yasa zasu iya gayawa kowa mgna dai-dai da abinda yayi musu.

A can Saudia kuma, komai na dawowarsu Sheykh ya kammala, cikin kwana uku, domin hankalinshi yayi matuƙar tashi, jin irin kisan gillar da akeyiwa makiyaya, wanda Maimartaba ne, ya gaya mishi komai, ya ƙara da cewa.
Yayi maza ya dawofa, don yana jiranshi suje tare yaje ya danni fulanin ya basu hakuri ya kuma taushesu kada su ɗauki mataki da sunan ramuwa ko ɗaukar fansa.


Hakane yasa, Sheykh ya uzzurawa Haroon dole ya gama musu komai.
A kwanaki ukun.
Ranar Jumma'a da azahar jirginsu ya sauƙa, a birnin Shehu Sokoto.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi yaso. Jikan nashi ya kwana, sai dai ina ya tike dole a lokacin Haroon ya kuma saɓan mota suka fara kita hanyan kawoshi Adamawa.
Wanda sai ƙarfe uku da rabi suka isa.
Kasamcewar dama basu taso da wuriba.
Kasancewar isar dare sukayi babu wanda yasan Sheykh ya dawo.
Ƙasar sai Lamiɗo da kuma hadimanshi, uku kacal da sune suka tarbesu.

Sai washe gari da. Asuba, sautin muryarsa yana karatun limancin Sallah asuba ne ya shaidawa mutanen masarautar Joɗa dawowanshi.

Gaba ɗaya kowa ya cika da mamakin, kana da farin cikin dawowanshi.

Duk da kasancewar sa, mai larurar da wasu ke mishi kollo ko kiranshi majanuni, yasan kiyaye lokacin salla dama yinta cikin kushu'i.
Wannan shine ya hanashi sallame sallar, da akeyi yana cikin sahu na tara,
wanda jin muryar ɗan uwanshi ƙaninshi, ya sashi zubda hawaye masu ɗumi.
Ya Jafar kenan.
Jalal kuwa dake gefenshi wata irin sassanyan ajiyan zuciya ya sauƙe tare da lumshe kekyawan ƙwayar idanunsa da suke iri ɗaya dana Sheykh, ga kuma bacci daya cikasu, domin daren jiya, Ya Jafar ɗinsu ya hanashi bacci.
Jin muryar ɗan uwansu da shi kaɗai ke iya sarrafa babban yayan nasune ya sashi sauƙe, numfashin.
Jamil da Affan kuwa, wani irin yalwataccen murmushi ya sake jin muryar ɗan uwansun.

Abbansu kuwa, shi dai har yau yana rasa me yakeji a kan ƴaƴan nashi, Especially Sheykh, yana jin zuciyarshi na mishi nauyi duk sanda yaron baya kusa dashi, sai dai kuma in yana kusa dashi sai yaji tamkar bai taɓa wani farin cikiba a rayuwarsa.
Ya sani tabbas su abun tausayawa ne, suna buƙatar kulawarshi fiye data kowa a duniya, to amman ya rasa meyasa yake jin kamar baya son kusancisa dasu.

Maimartaba kuwa, suna cikin sahun na forko bayan liman,
Sai da sauran malaman fada.

A cikin gida kuwa, jin sautin zazzaƙar miryarshi yana rere karatun al'ƙur'ani, ya ida fatiha, kana ya ɗaura, Arrahama,
daga bisani ya rufe da lakadja'akum, kafin ya tafi zuwa ruku'uh.

Haka nan Juwairiyya ta tsinci kanta da zubda wasu zafafan hawaye, masu ƙuna a rai, tabbas ta sani.
Kasan cewar Sheykh a masarautar nanne kaɗai yasa, suke a ciki.
Ta sani in badon daraja da al'farmarsa ba, da tun tuni, an tabbatar da sunan mijinta mahaukaci.
Hannu tasa ta share hawayenta cikin sanyi ta miƙe dan gabatar da sallan asuba, a zahiri tace.
"Allah ne gatanmu, kaine GARKUWAR mu, Sheykh in baka nan gidan kanyi mana duhu, ƙasar tanayi mana zafi."
Daga nan ta tada kabbara.

Ummi Jakadiyarsu kuwa,
Tana bayan gida, tana al'wala ta jiyo muryarshi, wani irin murmushi tayi tare da yin mgna a baiyane.
"Dan Halak kaƙi ambato, ɗa ɗaya tamkar dubu, maƙiyanka fadawanka, sunyi sake ɗan zaki ya girma, in sha Allah zaka dawo da farin cikin masarautarnan, sunyi sake, sun bar kari tun ran tubani,
Muhammad Jabeer bawan Allah".

Haka ta fito tana wasu irin kalamai masu wuyar fahimta.
A can sashin Hajia Mama kuwa,
Wata kekyawar budurwa, ce.
Konce kan gado gefen Mama, datake zaune bisa sallaya.
jiyo muryashine ya sasu saurin juyowa, suka kalli juna,
Cikin tsananin farin ciki da tarin shauƙi budurwar ta diro daga kan gadon gaban Mama ta zauna cikin zaƙuwa tace.
"Lah Mama, yaushe ya dawo! Muryar Sheykh Jabeer nake jifa! Mama ko dai dama yana nanne?".
Wani irin kallo Mama tayi mata cikin sanyi da murmushi a fuskarta tace.
"Batul shine, ya dawo!."
Wani irin sassanyan numfashi ta sauƙe cikin tarin shauƙi tace.
"Yes Mama, farin cikina ya dawo, kamar yasan, nazo.
Alhamdulillah, Mama Allah yana sona, ki gani ina zuwa, na samu baya nan, naji baƙin ciki kamar in mutu jiya kafin inyi bacci, sai gashi Allah ya turo minshi cikin dare ɗaya."
Murmushi Mama tayi, tana mai jin mmkin yadda Batul ke masifar son Sheykh har take gaza ɓoyewa.
cikin haɗe fuska tace.
"To yanzu dai, sai ki tashi kiyi salla, tunda kinji muryar da kikafi so a duniya, kin sauƙo kan gadon, sau nawa ina tadake, sai kiyi miƙa ki kuma konciya".
Cikin jin dadi tace,
"Wayyo Mama baccinne bai isheniba Allah ko jiya kwana nai ina zulumi, sai 3:44 na asuba na samu bacci."
Murmushi Mama tayi kana ta miƙe ta kabbarta sallan.
Ita kuwa Batul, miƙewa tayi da sauri ta shige, bathroom tana cewa.
"Bari inyi wonka inyi salla, in shiga kitchin yau nida kaina zan mishi breakfast."
Tana faɗin haka ta shige ciki.

A masallaci kuwa, ana idar da salla kamar koda yaushe, da yawa basu fitaba saida sunata lazumi.
Yayinda Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero da kuma Sarki Nuruddeen Bubayero, da Habibullah Nuruddeen Bubayero, suka jero, suka fito a jere, domin su kullum ana idar da sallan asuba, suke fitowa su koma cikin masarautar, inda kowa zai wuce Side ɗinsa,
Yayi karatun qur'ani da kuma, Dua Azkar, inda har sai rana ta fito, kana suke ɗan maida bacci, to kuma sudayin breakfast sai 11.
Suna isowa tsakiyar masallaci, Sheykh yaji an ruggumeshi ta baya, yasan mutun ɗaya ne rak zai mishi haka a cikin masallacin,
Ya Jafar ɗinsu.
Yana juyowa kuwa yaga shiɗin ne.
Ruggumeshi yayi gam-gam Jalal, kuwa ido ya zuba musu,
shi kuwa Sheykh hannu yasa shima ya ruggume ɗan uwan nashi.
Yayinda ya zubawa Jalal kwayar idanunshi, ya rame sosai, hancinsa ya ƙara fitowa, sai sajenshi daya ƙara yin lib, da uban gashin daya tara, yayi wani kafurin aski.
Ramar da Jalal yayi ta daki zuciyarsa sosai baya son ganin ƙannen nashi cikin halin matsala,
a hankali ya janye kwayar idanunshi ya maidasu kan Jamil da Affan dake gefen damanshi,
Calikan ƙanenneshi kenan ba,
sheƙiyancinsu ɗaya, baki suka haɗa wurin cewa.
"Sabahul Noor Al'Sheykh".
A hankali ya ɗan motsa laɓɓansa, yana mai kallonsu yace.
"Sabahul khair ya Uktih".
murmushi sukayi, suna mai jin son ɗan uwan nasu,
Abbs da Maimartaba kuwa, kai suka ɗan jinjina kana sukayi gaba,
Ganin hakane suma suka bisu, a baya,
shi kuwa Sheykh hannu yasa ya shafa kan Imran da yanzu ya iso gabanshi cikin sanyi yace.
"Hamma Jabeer barka da safiya".
jin yana shafa kanshine ya sashi lumshe ido, inama ace yadda Hammanshi ke nuna mishi so haka zai shirya da Mom ɗin shi, yana masifar son ɗan uwanshi baya jin daɗin yadda yake ganin wata iriyar mu'amala tsakanin Mom da yayunshi.

Ganin Sheykh yaja hannun Ya Jafar sun tafine yasashi bin bayansu.

Ƙofar dake cikin masallacin wacce zata ɓulla cikin masarautarsu sukabi.

Suna shiga, kowa yayi sashinsa sabida sun sani ko sunbi Sheykh yanzu ba lokacin mgna bane, karatu zaije yayi.
Shi kuwa Sheykh yana riƙe da hannun Ya Jafar ɗinsa suka shiga side ɗinsa,
inda ya samu hadimai masu tsaron ƙofar, suna tsaye.

Suna shiga, tamtsetsen falon nashi kai tsaye ya nufi wannan babbar kusurwar da zata sadashi da.
Big part ɗin shi,
Suna shiga suka ɓulla cikin wani mashahurin, falo, wanda yaketa tashin ƙamshi mai masifar sanyi da daɗin shaƙa,
a hankali ya zauna bisa kujerar 3 str kana yaja hannun Ya Jafar ɗin suka zauna, tare.
A hankali ya juyo kanshi ya zuwa ɗan uwanshi idonu,
Karatu yakeyi kamar koda yaushe, yanayi cikin tsantsar lugga da tajwid, kana ga kushu'i,
Suratul yaseen yake karanta,
bisa alamu kenan ya kusa yayi sauƙa, domin step by step yake bin surorin, in yayi sauƙa sai ya sako daga sama, baya mancewa, kuma baya birkitashi,
Wannan rahamar da Allah yayi mishi, duk da anso a maidashi majanuni, sai Allah yayi mishi muwafaƙa da littafinsa maisarki, yazama sihirin yayi mishi tasiri tako ina, amman banda gefen addininshi.

Wasu irin hawa masu ƙunu yaji suna tsatstsafo mishi, cikin jijiyoyin kekyawan idanunshi,
sabida ganin yadda Ya Jafar ɗinshi ke karatu yana, kuka ya za'ayi ya sama mushi farin ciki a rayuwarsa ta ina, zai san me ke cin zuciyar ɗan uwan nashi.
Jin yadda ransa ke ƙuna da tafasa ne, yasashi. Komawa ya jingina bayanshi da jikin kujer, kamar yadda Jafar yake mahaddacin haka shima settin kab tana kanshi,
Ido ya lumshe tare da yin bisimilla kana ya fara karu inda ya ɗauko daga forkon suratul. Noor ya farayin ƙasa.

Saida sukayi awa ɗaya cur kana,
Suka fara Azkar, wanda sai da sukayi 23 minutes suna, jero addu'o'in cikin harshen dake nuni da cikekkiyar jimla ta larabci da lugga.
Koda suka shafa, sai ya ɗan kalli ɗan uwanshi dake riƙe da hannunshi gam.
Ya lura Ya Jafar na tsoron kada ya kuma tafiya ya barshine, yasan duk sanda yayi doguwar tafiya ya dawo, haka yake liƙe mishi.
Hannunshi yasa, ya share mishi hawayenshi kana,
ya miƙa tare da jawo hannunshi,
yasani yanzu lokacin yin baccinsa ne,
Side ɗinsu, ya nufa dashi, ta wata ƴar siririyar hanyar dake tsakanin sashukansu.

A babban falon suka samu Juwairiyya.
Tana ganinsu, ta miƙe da sauri, fuska ɗauke da murmushi kana ido na tsatsafo da hawaye tace.
"Barka da dawowa, Sheykh, Alhamdulillah zamu samu nitsuwar Ya Jafar".
Kanshi ya sunkuyar sabida bai son ganin hawayenta,
Hannunshi ɗaya yasa yana shafa, kam Mimi data ruggumeshi ta ƙafafunshi,
cikin murmushi ta nitsuwa yace.
"Mimina anyi sallako?".
Cikin sauri ta gyaɗa kanta alamar eh,
Shi kuwa kanta ya kuma shafawa tare da cewa.
"Kinyiwa Ya Jafar ɗina Addu'o'in Allah ya bashi lfy ko?".
Kanta ta kuma gyaɗawa tare da cewa.
"Eh nayi mishi".
A fakaice ya ɗan kalli Juwairiyya dake rugume da yarsu karamar, cikin sanyi yace.
"Kukan bashi da wani amfani, muyi ta mishi addu'a, in sha Allah dukkan tsanani yana tare da sauƙi.
Ina roƙon Ubangijina mahaliccina a cikin dukkan Ayyukana, daya aramin rai da lfy, kada ya ɗauki raina ko na ɗaya daga, cikinmu, har sai ya nuna mana lfyar ya Jafar, ya faɗa mana abinda ya maidashi haka a dare ɗaya, nasani shine ɗaya rak yasan meya faru, a dare mai duhu da muni na rayuwarmu".
Cikin sanyi tasa tafin hannunta ta share hawayenta.
Shi kuwa Sheykh, wucewa yayi da Ya Jafar ɗin har cikin ɗakinshi,
bisa gado ya zaunar dashi, kana yacewa Juwairiyya dake biye dasu a baya.
"Yasha mgninshi ne?".
Miƙo mishi gorar ruwa da magungunan tayi tare da cewa.
"Yaƙi sha, dan daren jiya kwana yayi, baiyi bacciba,
Jalal nan abin tausayi, ko nanda can bai isa ya fitaba,
sai ya bishi,
Kullum sai Jalal yayi kuka".
Wasu tafasassun hawaye ne suka cika masa ido,
A duniya shi baya son yaga ko yaji na miji na kuka, domin shi ya sani, duk abinda kaga yasa na miji kuka to abun ya tsananta musamman maza irin Jalal yasan ba ƙaramin raunine zaisa Jalal zubda hawayeba.
Shiyasa, shi kukan mace bai taɓa damunshi ba a zuciyarshi, domin mutane sunce in kaga mace na kuka to kayi dariya kafin ka tambayi meya sata kukan. In kuma kaga namiji na kuka to kaima ka fara kukan kafin ka tambayeshi meya sashi kuka.
Shiyasa shi kukan mace, bai shiga ranshi, sabida yanaga mata sun iya kukan munafurci da kukan gulma dana ha'inci da yaudara,
shiyasa in yaga mace na kuka haushinta yakeji a ransa.

Maganin ya bashi sannan ya kontar dashi kafin ya wuce, ya koma sashinsa.


Yana shiga, falon, ya samu, Haroon ma zaune, shida Jakadiyarsu,
tana ganinshi ta faɗaɗa fara'arta cikin kula da so mai zurfi tace.
"Farin gani, Garkuwa, Sheykh, Limamin Masallacin Moddibo Joɗa Jikan sarki mai hatimin sarauta."
Gefen Haroon ya zauna tare da rumtse idonshi cikin nitsuwarshi yace.
"Ummi ki bari mana, babu wani sarkifa sai Allah, Ummi nace ki dena min irin waɗannan zantukan masu sa kan ɗan adam girma".
Murmushi mai cike da tarin so, sabida ita dai jinshi take tamkar ɗan da raina a cikinta ta kuma haifeshi,
Koda yake hakan baya rasa nasaba, da cewar itace jakadiya gareshi tun randa aka haishi bacci kawai ke haɗashi da Mamanshi. Sai dai takanzo inda suke su sashi a tsakiya sunai mishi wasa da kallo mai cike daso."
Ganin tayi kasake tana kallonshi ne ya sashi ɗan gyara zama, cikin girmamawa yace.
"Ina kwana Ummi, ya su Jalal?".
Murmushi ta kumayi tare da cewa.
"Lfy lau Alhamdulillah, Jalal ya zama mazaunin gida, tunda ka tafi sabida, duk inda yaje , Jafar zai bishi,
sai dai kuma abokanshi masu shigar banza har gida suke biyoshi,
wani sa'in kwana kiɗe-kiɗe da rawa sukeyi a sashinsu, suna shan sigari.
Wasu lokutan dole, Jamil yake gudowa ya bar musu can yazo wurina yake kwana, ko ya shigo nan wurinka".
Kanshi ya ɗan maida baya, a hankali yace.
"Ummi Jamil da mata?".
Kai ta ɗan kauda kana a hankali tace.
"Tafiyar bata sauya zaniba, kwanaki uku da suka wuce wata tazo daga, Kano wai ita ƙawarshi ce, kwananta biyu, a sashin Juwairiyya, da Abbanku ya samu lbrine ya korata".
Cikin sanyi yace.
"Ummi waya gayawa Abba?".
Kai ta jujjuya tare da cewa.
"Allahu alamu, yadai ji har yace zai kori Jamil ya bar mishi gidanshi, to da yake Jafar yana wojen ne, sai ya riƙe hannun Jamil yayi ta kuka, hakane yasa ya barshi, Mamanku kuwa kuka tayi- tayi".
Wani irin zazzafan numfashi ya fesar kana, ya juyo ya kalli Haroon a hankali ya kuma kalli, Jakadiyarsu, cikin sanyi yace.
"Basaji Ummi suna samin tunani a raina, ga wannan kuma shima ƙato dashi, sai ya ruggumi waya yayi ta chatting ko waya Da waccar yar mitsitsiyar yarinya Jannart ɗin.
Da asuba nayi ta tadashi yafi sau uku baya tashi, sabida bai bacci da wuriba, gashi ko cikekken jam'i bai samuba".
Ido Haroon ya lumshe tare da cewa.
"Jiya dai ba chatting ko waya da Jannart bane, ya hanani baccin da yasani makara, Ummi ƙarshen darefa muka iso sabida ya sani dole sai mun taho nan."
Murmushi Ummi tayi kana tace.
"To Haroona ka kiyaye batun tsaida salla kan lokacin ta, kaji ko?."
Hararan Sheykh yayi tare da cewa.
"To Ummi".
Ita kuwa Jakadiyarsu cikin muryar kula tace.
"Haroona yaushene bikin naku kam?".
Kanshi ya ɗan shafa kana yace.
"Uhum Ummi saura watanni bakwai in Allah ya yarda, Ni dai zanyi aure in bar babban tuzurun".
Bai kulashiba saima tashi yayi ya nufi bedroom.
Ita kuwa Jakadiyarsu cikin yin ƙasa da murya tace.
"Yauwa ya dai-dai ta da Jazrah ko?".
Baki ya ɗan turo tare da cewa.
"Uhum Ummi gudowafa yayi, kuma wlh in ba dagewa kukayiba, wannan bauɗeɗɗen ɗan naku, ustazu bazaiyi aureba, mutun duk yadda akayi dashi sai ya kauce".
Kai ta ɗan juya ta kalli ƙofar ɗakin daya shigan,
cikin yin ƙasa da murya tace.
"Uhum ga zahiri ko mgnar aure akayi sai ya bar wurin."
Haka sukayi ta hira da yake akwai sabo tsakaninta dashi.

A sashin Hajia Mama kuwa, ita da kanta da kuma, Batul suka shiga kitchin sai kuma yardaddun hadimanta mutun biyu.
Breakfast mai kyau suka, haɗawa Sheykh.

Yayinda Aunty Juwairiyya ma ta shiga kitchin da kanta, ta haɗa mishi breakfast.

Jakadiyarsu kuwa da Jamil da Jalal da Affan Haroon suna falon sunata hirarsu.


A tare hadiman Mama dana Juwairiyya suka kawo, abin kari.
Suna fita ba da ɗewa, hadiman Gimbiya Aminatu kakarsu kenan.
Suka shigo suma da abun kari.

Suka jera komai kan babban dinning table dake dinning area'n dake falon.
Bayan sun fitane.

Suna cikin hira, sarƙin ƙofa, ya shigo, ya shaida musu, ga saƙo an kuma kawowa.
Jamil ne ya bada daman a shigo.
Nan ya juya ya fita,
jim kaɗan, aka turo ƙofar.

Cikin mamaki suka zuwa ƙofar ido.
Ganin M....!



*Wannan shafin nakine ke ɗaya MRS SARDAUNA, Sheykh yana godiya da soyayyarki gareshi. Domin duk masoyanshi bayanki sunka biyo*








By
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

🐄🕊️🌈🦚🐍🤴🏻💘

*GARKUWA*

PAGE 14

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

📝🍇🐄🌈🦚🤴🏻💘




*Daga gobe ne, FREE PAGE zai ƙare, in da zan saki page 15-16 daga su kuma in kin sake ganin littafin GARKUWA a woje ba cikin groups ɗin da na buɗe nasa wanda suka biya ba, To na satane, na waɗanda basu san darajar iyayenka da girman Allah da Manzonsa suka fitar ne, to ke kuwa in kin san darajan iyayenki da girman Allah da Manzonsa, kada ki karanta na sata, akwai group ɗin ɗari uku kacal ban tsauwala ba dan nasan halin TLC da muke ciki a ƙasar nan ga mai wadata wacce take da dama taga zata iya biyan na Special Group 1k ne rak. Zaki turo ta asusuna 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number dai 09097853276, kuma ƴan 300 zaku iya turowa ta ac na ɗin, in kuma baki da dama to turo katin mtn na ɗari uku kacal ta wannan number dai 09097853276. Dan Allah da Manzonsa in kin san zaki fitarmin da littafi biyoni PC ki gaya min wlh zan baki kuɗinki in fiddaki group salum-alum, ina kuma jin san saya zakiyi ki fidda na roƙeki da Allah da Manzonsa wanda bayansu babu wani kada ki saya ki riƙe kudinki ki barni in riƙe littafina🤗*


FREE PAGE, daga gobe dai zasu ƙare ki biya kuɗin ki in kinada niyan saya.



Ganin Mom ce, yasa fuskokinsu ya baiyana abinda ke cikin zuƙatansu.
Cikin ƙasaita, Mom ke tafiya, hadimanta biyu na biye da ita da manyan kuloli na al'farma.
Jakadiyarsu ce tayi murmushi mai kama da yaƙe, tare da rusunar da kai, cikin girmamawa tace.
"Barka da shigowa, Gimbiyar ahlin masarautar Joɗa.
Cikin isa da ƙasaita ta gyaɗa mata kai bayan ta zauna, gefen Jamil dake ruggume da waya kamar, abin masifa,
Kanta ta ɗan juyo ta kalli Jalal daya haɗe fuska,
Juwairiyya yace ta ɗan gyara zamanta tare da cewa.
"Barka da safiya Mom".
Murmushi mai wuyar fassarawa tayi, tare da taɓe baki, a gyatsine tace.
"Barka dai". Sai ta kuma juya ta kalli inda Jakadiyarsu ke zaune, cikin isa tace.
"GARKUWAN YA FITANE?".
A daƙile Jalal yace.
"Yana ciki kuma hutawa yakeyi".
Ko inda yake bata kallaba tace.
"Jakadiya ina buƙatar ganinshi, yanzu".
Cikin biyeyyarta tace.
"Ranki ya daɗe, in zaton bacci yakeyi".
A taƙaice tace.
"A tadoshi".
Haroon dai ido ya zuba musu yana ganin ikon Allah, kowa ji da kai da ƙasaita.
Juwairiyya ce ta ɗan kalli Haroon ɗin cikin sanyi tace.
"Ukhti, shiga ka sanar mishi".
To kawai yace, kana ya miƙe ya shiga bedroom ɗin, da Sheykh ya shiga mituna ashirin baya,
kasake yayi a bakin kofar ganin babu kowa a cikin bedroom ɗin.
A hankali ya tako ya shiga ciki, bakin ƙofar bathroom ya ɗan matso, kunnenshi ya kasa wai a lissafinshi ko zaiji mitsin ruwa.
Shiru babu kowa a ɗakin da kuma bathroom ɗin.
Ko ina yayi tsit sai wani fitinenne sanyi daya cika ɗakin, wanda sai sautin
A/C dake busawa shuuuuu a hankali.
Waige-waige yayi ganin babushi babu, motsinshi ne, ya sashi ɗan ɗaga murya yace.
"Jabeer! Jabeer!! Jabeer!!!".
Jin shirune yasashi sa hannunshin ya ɗan ƙonƙosa ƙofar bathroom, still shiru.
Hakane yasa ya ɗan tura ƙofar, wayam baya ciki.
Ganin hakane ya sashi juyawa,
shima ɗin cikin takun ƙasaitar ya fito gefen Jalal ya zauna tare da kallon Juwairiyya,kana yace.
"Baya cikifa".
Wani irin kallo Mom tayi mishi, wanda yake nuna abinda ke bakinta, cikin ɗan sakin fuska yace.
"Allah kuwa Mom baya ciki".
Kanta ta gyaɗa tare da yunƙura ta tashi tsaye.
Kana a hankali tace.
"Uhummm". Sai kuma ta juya ta kama hanyar fita, hadimanta na biye da ita a baya.
Har yaje bakin ƙofa ta juyo tare da cewa,
Ga breakfast ɗin Garkuwa".
Haroon ne yayi godiya kana ta juya ta fita.

Cikin mmki Haroon ya kalli Jamil tare da cewa.
"Jamil baya cikifa".
Murmushi Juwairiyya tayi tare da cewa.
"Kun dai haɗa baki, kunƙi ya fito, ya gaisa da Mamanshi".
Jalal ne ya ƙara tsuke fuskarsa tare da cewa.
"Mamarshi ko makirarshi".
Jakadiyarsu ta ɗan gyara zama tare da cewa.
"Uhummm, sanin halin mutum sai Allah".
Sai kuma ta kalli Haroon tace.
"Haroona kace mishi yazo yayi karin kumallo, kace mishi daga sashin Gimbiya Aminatu ce, ga kuma na Juwairiyya".
Cikin jaddawa yace.
"Allah kuwa Ummi baya cikifa".
Da mamaki a fuskokinsu suka ɗan kalleshi, Jamil ne yace.
"Bai fita bafa".
Juwairiyya ce, ta amshi zancen da cewa.
"To kuma dai bai biyo nanba, tunda ya shiga bai fitoba".
Shi dai Haroon Ido ya zuba musu, ganin kamar basu yarda Jabeer baya cikiba.
Kuwa hakanne, saida Jamil yaje ya duba babu shi a ciki babu alamarsa.

Cikin tarin mamaki ya sanar musu, baya nan ɗinfa.
Jalal ne ya ɗan kauda tunaninsu da cewa.
"To kunata surutu, ta ina zakuga sanda ya fita, kai Jamil hankalinka duk na kan waya ina zaka ganshi."
Cikin kula Jakadiyarsu tace.
"Kaga fitarsane?".
Baki ya ɗan taɓe tare da cewa.
"Ni ban ganiba, na dai san shi ba kuɗi bane bare ya ɓata, ku jira zaku ganshi".
Da haka sukayi amanna dan a zatonsu yaga fitarshi kawai bauɗewarshi ne yasa bazai sanar musuba.

A can cikin fadar Masarautar Joɗa kuwa, falon sashin mai martaba Lamiɗo, cike yake da ƴaƴanshi maza, ziryan, wanda kullum iwar hakan suke haɗuwa domin gaidashi kana su gaisa da juna, ya tambayi lfyar ko wanne ɗanshi da ahlinshin.
To yau ta kasance jumma'atu babbar rana, wanda kuma, duk safiyar jumma'a.
Cikin wani ɗakin gadon sarautarsu, yakan shiga shida kanshi, yake tsabtace wannan ɗakin duk ran jumma'ar duniya, a tarihi da tsarin masarautarsun babu wanda zai shiga ɗakin sai wanda yake, matsayin Sarki.
Babu wani wanda ya taɓa shiga wannan ɗakin, sai wanda yake sarki.

Suna cike a falon a ƙalla sun kai su bakwai dukansu. Manyan mutanene masu tarin wadatar duniya, jinin sarauta na yawo a jikinsu.
Suna zaune kamar yadda kullum suke zama, suna ɗan hira a tsakaninsu.

Habibullah ne, zaune a can tsakiyarsu a matsayinsa na shine babban ɗa ga Lamiɗo, hannunsa riƙe da.
Carɓi, sai gefen damansa, Alhaji Sani, sai kuma Barrister Kamal, kana sai. Dr Aliyu, kana sai,

2 Comments On GARKUWA
avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment