Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tafiya.
Hadimanta kuma na zagaye da ita.
Suna shigowa ta tashi zaune daga kishingiɗar da tayi.
Cikin tsananin baiyana farin cikin ta, ta nunawa Jabeer kusa da ita.
a hankali suka iso suka zauna gabanta.
Umaymah kuwa gefenta ta zauna.
Ummi ko na bayansu hadiman kuma suna can falo.
Hannunta tasa ta kamo hannun Jabeer.
Cikin fara'a tace.
"Alhamdulillah Muhammad Jabeer, Allah ya sanya al'khairi ya baku zaman lfy".
To shifa suna ɗaure mishi kai, da tarin addu'o'insu na al'khairi, shi dai ba sonta yakeba ba kuma zama da ita zaiba,
to me zai wahal dashi da zaice Amin Amin.

Umaymah da Jakadiyarsu ne suka amsa da Amin Amin kamar dai yadda sukayi a sauran wuraren.

Batool ce ta kalli Shatu cikin isa tace.
"Amarya ki ɗago kanki mana kinga gaban uwar mijine kike".
Duk da taji mgnar Batool sai tayi kamar batajiba,
Abubuwan ci da sha dake gabansu ne,
Hajia Mama ta jawo wani ɗan ƙaramin tray da cups biyu ke kanshi.
Gyara zama tayi da kyau, tana murmushi ta kalli Shatu dake mgna a hankali.
"Ina kwana Mama".
Cikin kula tace.
"Lfy lau ɗiyata ya baƙun ta".
Alhamdulillah tace, tare da tsurawa madara da zumar da Hajia Mama ta zuba musu cikin kofu nan ido.
a hankali ta ɗan muskuta kaɗan tayi baya, tare da ƙara yin ƙasa da kanta.
ita kuwa Hajia Mama, kofin ta ɗauka ta miƙa mata.
Tare da cewa.
"Gashi ɗiyata amshi kisha."
Cikin sanyi murya can ƙasa ta girgiza kanta tare da cewa.
"Alhamdulillah".
cikin nuna kulawa da so Hajia Mama ta ƙara miƙo mata kofin tare da cewa.
"A a ɗiyata, amshi kisha, wannan al'adace ta masarautar Joɗa, dole in marabceki dashi."
Kai ta kuma girgiza alamun ya isheta.
da sauri Umaymah ta matso kusa da ita tare da cewa.
"A a Shatu amshi kisha kinji ko?".
Cike da mamaki ta ɗan kalli Umaymah ta gefen idonta.
jin Umaymah na ƙoƙarin matso da kofin kusa da itane yasa tayi mgna cikin ɗan ɗaga murya tace.
"Bana shan madarar".
wani irin kallo mai cike da damuwa Hajia Mama tayi mata tare da cewa.
"Subahanallahi, bakya sha, kuma, amai yake sakine? Ƙa'idane da dole kishi".
Ta ƙarishe mgnar cikin damuwa.
Ita dai Shatu shiru tayi idonta na bisa kofunan madarar.
Ummi ce ta matsota tare da cewa.
"Shatu amshi kisha koda kurɓa ɗaya ne".
Cikin rawan murya tace.
"Bana sha".
Jin alamun rawan murya irinta an takura mutum ne, yasa duk sukayi cirko-cirko suna kallon Madarar.
Zuwa can Hajja Mama ta sauƙe wani bahagon ajiyan zuciya, kana ta ɗauki ɗaya kofin ta miƙa Jabeer tare da cewa.
"To gashi kai kam kasha naka".
Zamanshi ya ɗan gyara tare dasa hannun damansa ya amshi kofin.
Wani irin zaro ido Shatu tayi.
Kallon kofin takeyi tamkar zata maida kwayar idanunta cikin kofin.
duk jikinta tsuma yakeyi, wani irin masifeffen bugawa ƙirjinta yakeyi da ƙarfi.
Shi kuwa Sheykh Jabeer zaune yake riƙe da kofin, ya fuskanci Hajia Mama da kyau.
Ita kuwa Hajia Mama hannunta tasa ta kamo ɗaya hannun Jabeer da baya riƙe da kofin.
Kana ta miƙowa Shatu hannun alamun ta miƙo mata hannunta.
Ƙara runsunar da kanta tayi tamkar bata gane me take nufiba.
Cikin murmushin Hajia Mama tace.
"Kawo hannunki ko ɗiyata".
A hankali ta ƙara maida hannunta baya,
dai-dai lokacin kuma Jabeer ya ɗago kofin ya kai saitin bakinshi da niyar zai sha.
cikin hikima ta muskuta ta ƙara matsowa jikinshi da sauri ta ɗago hannunta kamar zata miƙawa Hajia Mama hannun.
sai kuma ta ɗan kaikaice, ta buge c...!




Ƙaƙa tsara ƙaƙa




By
*GARKUWAR FULANI*
"Kamar tsoffin karnuka". Cikin fusata Gimbiya Saudatu ta miƙe tsaye tare da nufo inda yake.
Shi kuwa kanshi ya jinjina tare da cewa.
"Kinyiwa kanki Garkuwa da kika tashi daga kan kujerata".
A hatsale tace.
"Wai kai a zatonka tsoronka nake jine ko meye?".
Da sauri ya jujjuya mata kai tare da tsuke fuskarsa alamun baison sautin amon muryanta da take ɗaga mishi, a daƙile yace.
"A a, na isa inyi zaton tsorona kikeji. Ke da bakinji tsoron Allah'n daya halicce ki bama, ina zakiji tsoron wani bawa nashi, ai masu tattausan zuciya suke tsoro".
Hannu Baba Nasiru ya ɗago da alamun zai kifeshi da mari.
Ba zato yaji ya kama hannunshi, kana ya ɗan juyo fuskarshi gareshi, cikin sakekkiyar murya yace.
"Wai ku meyasa bakwa gane, yare da harshenmu na bani adam ne? Meyasa kukafi son Yaren dabobbin marasa hankali, a zatonka ka kai matsayin da zaka ɗago hannunka ka mari fuskanta?".
A hatsale ya fuzge hannunshi tare da cewa.
"Da uwarka kakeyi, kasan wacece dabbar ai!. Ɗan hegiya mai jajayen kunnuw..!".
Shiru yayi bai ƙarisa mgnarba ganin wani irin kallo da Jabeer ke mishi, ido cikin ido.
Kana ya ɗaga hannunshi na dama, yana ɗan buga bayan tafin hannun damanshi cikin tafin hannunshi na hagu.
Still idonshi na kan fuskar ƙanin Mahaifinshi, miƙar da tafin hannunshi yayi, tare da mishi alamun datsa a cikin tafin hannunshi, kana cikin danne fushinsa, dan baya son su gane abinda ke masifar ci mishi rai, sai dai duk danniyarsa ya rigada, sun gane babu abinda ya tsana a duniya sama da azagar mishi mahaifiyarshi bare a suffantata da ƙaddararta, da binta da kalaman bita da ƙulli.
Baba Basiru ne, yayi wani irin dariyar mugunta kana ya ɗan matsa baya kaɗan cikin izza yace.
"Datse mana wuya zakayi, dan a zagi waccar munafukar da Allah ya nuna mata ishara tun a duniya".
Murmushi mai rauni yayi kana yace.
"Mahaukaciyar tsohuwar ku ko! Eh na gane lallai kam, batunka haka yake".
Cikin fiffiƙewa suka fara kumfar baki ina dalilin zaicewa uwarsu mahaukaciyar tsohuwa".
Daga nesa za'a iya jiyosu.
Shi kuwa ko Aunty Juwairiyya dake Dinning area bata jiyo abinda yake faɗa.
Domin cikin nitsuwarsa yake zaro musu, duk amsar mgnar da sukayi mishi tunma kafin harshensu ya huta.
Gimbiya Saudatu kuwa, a masifance tace.
"Ai asirinku zai tonu nan bada dadewa ba, munafukar kakar takace, tayiwa mahaifiyarsu asiri ta haukatata dan baƙin kishi irin nata".
Murmushi yayi ganin yadda ƙannnen mahaifinshi keta ihu uwa karnuka.
Allah ya sani lamarinsu yana bashi mmki har yau ya rasa me yayi musu mai zafi a duniya da suke gaza danne tsanarshi a aransu.
Me Mahaifiyarshi tayi musu da suke masifar tsanarta?.
Kanshi ya juya ya kalli Umaymah daketa murmushi mai cike da jin daɗin yadda yake komai a nitse.
Juyawa yayi zai nufi gefen hanyan falonshi.
Sai kuma ya ɗan tsaya ganin Gimbiya Saudatu tasha gabanshi.
Cikin danne shakkarsa tace.
"A haka zaku ƙare. Komai na muna furci, anje anyi aure a muna furce a ɓoye, sannan an kawota yau kwana uku kenan an kasa fito da ita a nunawa mutane ita, dan masifar rashin gsky.
Ko dai cikin shegene da ita yasa kuke ɓoyeta."
Da sauri Umaymah ta ƙara so inda suke, cikin tsuke fuska tace.
"A kanki shege zai samu, in sha Allah bazai samu a tsatson yar uwata ba, kin kuma yi gaggawa, da yake dama aikin shaiɗan ne dole zakiyi ta aikatashi.
Ki koma ki wanke idonki zai kawo miki Amaryarshi matarshi kuma uwar ƴaƴan shi, har Side ɗin ki, cikin falonki, har gaban ki.
Kinaji zai gabatar mata ke da munanan ɗabi'unki dan tasan irin zaman da zatayi dake".
Laminu ne yace.
"Ke kuma waya kasa dake, ki bari ƴan gida suyi mg...!".
Wani irin tsalle yayi ya koma baya, jin marin da Jalal wanda yanzu ya shigo ya kifa mishi ta bayanshi.
Da sauri Baba Nasiru da Baba Basiru suka juyo kan Jalal, alamun wai zasu dakeshi.
Karkata kai yayi ya kallesu da gefen ido.
Kana a hankali yasa hannunshin ya ɗaga rigarshi, wata ƴar madai-daiciyar bindiga AK 47 ya zaro a ƙugunshi .
Wani irin wawan birki sukaja, tare da cewa.
"Eh lallai babu shakka masarautar Joɗa ta raini tantirin ɗan ta'adda bindiga, wato abin har yakai ka matakin riƙe bindiga".
Kanshi ya tankwashe tare dasa bakin bindigar yana sosai tattausan sajenshi irin na Hamma Jabeer ɗin shi.
Kana da bakin bindigar ya nuna musu hanyar fita.
Ai a jere suka juya suna fita.
Gimbiya Saudatu na cewa.
"Duk wanda yaci tuwo dani, tabbas miya zaisha.
Amaryar munafurcin a fito da ita mu ganta in an taki gsky".
Laminu ne ya amshi zancen da cewa.
"Menene ma abin gani a Bororiyar daji".
Da haka dai suka fita.
Shi kuwa Sheykh Jabeer wani irin kallo na tuhuma, da tarin mamaki yakeyiwa Jalal.
Bindiga a hannunshi, shi kuwa Jalal ganin yadda duk suka zubawa bindigar idone yasashi.
Meda ita cikin rigarsa.
Kana ya juya da sauri ya nufi hanyar fita.
Jabeer bai ce mishi komaiba.
Yana ganin ya fitane shi kuma ya juya, ya nufi falonshi.
Bedroom ya wuce, a hankali ya zauna bakin gado,
tare dasa hannunshi yana buɗa bakin al'kyabbar jikinshin sai kuma yasa hannu shi na dama ya dafe kanshi, kalmar amarya mata ya maimaita a fili.
Wani irin rumtse idanunshi yayi da ƙarfi Allah ya sani shi yama mance, batun wannan jagulellen auren da akayi kamar na wasan yara.
kanshi ya ɗago a hankali ya kalli Umaymah dake shigowa da sallama a bakinta.
Gefenshi tazo ta zauna bisa bedside drower'n tana fuskantarshi.
hannunshi yasa, ya fara cire hiramin kanshi.
ita kuwa Umaymah cikin hikima tace.
"Idan mutun yana yi maka fatan ci baya to kayi mishi nuni da nasarorin rayuwarka, ban cika son takura maka akan baka umarnin yin abubuwan da baka soba, to amman bani da zaɓi akan duk wata al'ada ta masarautar Joɗa, da cikin masarautarmu ne, tabbas inada damar hana wani abun da saka wani abun."
Cikin rauni ya kalleta da idonshi da sukayi jazir a hankali yace.
"Me Mahaifiyata tayi musu mai zafi da suka sata a gaba ita da ah'linta.
Duk abinda sukeyi Mata bata kulasu, bare ta kai ga ramawa, tana haƙuri akan komai, haka yasa suke zaton tsoronsu takeji.
Ita kullum yanayi musu uzuri.
su kuma kullum fatansu su cutar da ita har dai suka samu nasarar cutar da rayuwarta sannan muma basu barmu ba.
Ni na gaji da zama cikin masarautar Joɗa, zan bar musu garin gaba ɗaya".
Sauƙe numfashin tayi tare da cewa.
"Basu da nasara a rayuwarsu.
Nasara ɗaya ce garesu kuma sun yi ta.
Ta ƙare musu".
Sai kuma ta ɗan kalleshi cikin sanyi tace.
"Jazlaan!". A hankali ya amsa mata.
Fuska ta ɗan raunata kana a hankali tace.
"Yau kwanan matarka uku a gidan nan!".
Da sauri ya kauda fuskarshi a kanta wani irin haɗe fuska yayi tare da taune lip ɗin shi na ƙasa ta ciki.
Shi ya mance da wannan batun yana rayuwarshi hankali konce. Wannan kariyar matar Gimbiya Saudatu tazo ta tono zancen.
Ita kuwa Umaymah a hankali taci gaba da cewa.
"Baka gantaba! Baka nemeta ba! Baka san halin da take cikiba! Baka nunata wa ah'linku ta masarautar Joɗa, a matsayin ta, na matarka.
Lamiɗo yayi mgna har ya turo Umminka taxo ta sanar maka, sai tace bata so ɓacin ranka. Abbanka yace shi bazai ce maka komaiba, sabida babu abinda baka saniba kan al'adar masarauta.
Yace kada wanda yayi maka mgna akan matarka sabida.
kai ba jahili bane, duk ka fimu sanin haƙƙin mace akan mijinta. Yace kunya tashi kake son yi a idon mutane!".
Kanshi ya fara jujjuyawa a hankali yace.
"Me kukeso inyi! Umaymah ya kuke son inyi? Bazan iya juya kaina in dawo yadda kukeso bafa, daga yadda Allah ya halicce ni".
Cikin hikima da sanyi tace.
"Ka shirya gobe, ka gabatar da matarka ga ƴan uwanka da iyayenka".
Hannunshi biyu yasa ya dafe kanshi.
Tare da rufe idonshi, sabida sarawar da yaji kanshi nayi.
sai kuma ya ɗan kalli Umaymah jin tana shessheƙan kuka.
Cikin sanyi yace.
"To!".
Murmushi tayi tare da shafa kanshi kana ta juya ta fita da sauri.

Kai tsaye sashin Gimbiya Aminatu ta wuce, ta sanar mata yadda sukayi da ɗan nata.

Shi kuwa Sheykh Jabeer, a hankali ya miƙe al'kyabbar jikinshi ya zare, kana ya nufi bathroom da jallabiyar.

Yana shiga ya zare jallabiyar da snglet ɗin. Kana ya shiga wurin wonkan.
Ruwan sanyi ya sakarwa kanshi.
sabida sarawar da kanshi keyi,
tun ihun dasu Baba Basiru sukayi mishi a kanshi.
Ga kuma wani sabon zance na zagaye idanun mayu da kulullukan masu konciyar ɗaukan rai na masarautarsu.
A ƙalla yayi mituna biyar ruwan sanyin na zubo mishi a tsakiyar kai, kafin ya fara sauƙe ajiyan zuciya alamun kan ya fara lafawa.
Al'wala yayi kana ya fito.
A nan drower'n glass dake bathroom ɗin nashi ya kimtsa kanshi cikin wasu datsastsen yadi mai masifar kyau Super Nour, Noble blue mai ɗan karen kyau, tattausan yadine mara nauyi, kana yanada ɗan shara-shara kaɗan, riga da wonɗo ne dai-dai jikinshi rigar half jomfa ne wanda aka watsa mishi aiki da da baƙin surfani.
in ka tsura mishi ido sosai zaka iya hango shatin snglet and white boxes jikinshi.
Wani Oud mai daɗin gaske ya fesa.
Kana ya fito.

Baƙar fula ya kafa a kanshi wanda ya bawa tattausan gashin kanshi damar baiyana ta gefe da gefen kanshi da kuma ƙeyanshi.

Fararen kyawawan Ƙafafunshi, ya zura cikin. Wasu tattausan takalma baƙi.
Sai kuma yasa hannu ya ɗauki carbinshi.
Agogon dake liƙe saman mirror ya kalla,
Lokacin sallan la'asar yayi, dan haka dole babu baccin tsakanin azahar da la'asar ɗin da ya dawo yi.

A masallaci ya samu su Haroon da Jamil.

Bayan anyi sallan ne kowa ya kama sabgogin gabanshi.
Shi Jabeer komawa gida yayi.
Ya saka garen kayan jikinshin kana.
Ya fito, Ummi ya samu tsaye a tsakiyar falon, cikin kula tace.
"Zaka fitane?". Kai ya gyaɗa mata alamar eh.
ba tare da damuwar rashin bata amsarba tace.
"Da yan rakiya ko kai ɗaya?".
Yana gyara zaman hular kanshi yace.
"Ni kaɗai. Zanje gidan Malama Abubakar ne!".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Ka gaida minshi".
"In sha Allah zaiji. Umaymah fa?".
Gane abinda yake nufine yasata cewa.
"Tana can sashin Gimbiya Aminatu, wurin ɗiyarta Amarya Aysha".
Kanshi ya ɗan sunkuyar ba tare da yace mata komai ba,
ya fita.
Malam Abubakar shine, malamin da ya fara ɗiga mishi harafin Ba''un a allon shi, wato Be a fillance, Basinmi'arra a hausance ko?.
A wurin shi yayi sauƙan forko, sai dai zuwa yanzu, shi Jabeer shike ƙara wa Malam Abubakar sani, akan Nahawu da Tajwid sabida shi da karatun zaure yayi.

Umaymah kuwa, ita da kanta ta sanarwa Lamiɗo cewa, gobe Sheykh zai gabatar da amaryarshi.

Haka yasa, ta fara shirya Aysha, shiri na musamman.
Cikin Hadiman Juwairiyya ɗaya daga cikinsu.
Mai suna saratu, itace Umaymah tasa ta yarfawa Aysha zanen lalle mai ɗan karen kyau.
Kana Ummi da kanta ta wonke mata kai sabida ita keyiwa Juwairiyya ma.
Sosai ta fito ras.
Ita kuwa Shatu duk abinda sukeyi Mata.
Tunanin Hibba al'hinin da tun randa tazo bata kuma ganinta ba.
tana son ta tambayesu ta rasa ta ina zata fara, dole dai haka ta haƙura tai shiru.


Washe gari ranar talata. Da hantsi, ko ina na sashin Gimbiya Aminatu sai ƙashi yakeyi, sabida shiri da kimtsa amarya.
Umaymah da kanta take kimtsata, wani irin dakekken wagambarine mai matukar kyau Royal blue, tasaka doguwar rigace. Tayi cib-cib da jikinta.
wani irin ɗauri ɗan kwali Aunty Juwairiyya ta murza mata a kanta, irin mai stpes ɗin nan.
Kana sai wata farar al'kyabbar masarauta fara ƙal mai kolliyar zaren aiki da ulunta Royal blue.
da surkin Golding color mai sheƙi.
Wasu fararen takalma masu ratsin Sky blue ne a kekyawan kafarta da yasha jan lalle, takalman basu cika tsini da tuduba, sai dai kuma ba dab da ƙasa bane.
Tayi kyau iya kyau, sai ƙamshi da sheƙi take zubawa.
Umaymah ce ta kama hannunta har zuwa falon Lamiɗo, wanda bai rigaya ya fita fadaba.

Gefen Gimbiya Aminatu ta ajiyeta, kana tace.
"Bari inje inzo da Angon."
Murmushi Gimbiya Aminatu tayi tare da cewa.
"To kuyi sauri dai".
To tace kana ta fita.

A can sashin Sheykh Jabeer, kuwa.
Da alamun wonka ya fito, a nitse yake kimtsawa, cikin wani fitinenne yadi mai taushin gaske.
yadin Royal blue ne mai masifar kyau.
rigar half jomfa yar tsukekkiya,
tsaki ya ɗan ja lokacin daya gama dai-dai-ta zaman rigar a jikinshi sabida tayi kib-kib a jikinshi har kamar ta ɗan matseshi.
Wondon kuma irin mai iya kuibin sawune, irin sakun wondunan ahlul sunna.
a hankali ya iso gaban drower'n da hulunanshi da hirami da baƙin abun saman hiramin ke jere a ciki.
Har yasa hannunshi bisa wani farin hula, sai kuma ya sunkuya ya ɗan kalli. Kanshi.
Fuskarshi ya ɗan tsuke, sai kuma ya ɗan juyo jin muryar Haroon yana cewa.
"Wow masha Allah, gsky kayi kyau, Please ka fita haka mana, ka ganka ɗan saurayi mai jini a jika, amman in kasa al'kyabbar nan, sai kwarjininka yayi yawa yaseen.
Ni kaina sai inji ina shakkarka,".
Kai ya ɗan shafa kana yasa hannunshi ya zaro hiraminshi fari da baƙin zagayen.
ɗaya marfin drower'n ya buɗe tare da zaro wata dakekkiyar al'kyabbar fara mai ratsin blue na zaren aiki gaba da bayanshi.
Gaban gado ya dawo yana warware al'kyabbar tare da cewa Haroon.
"In na fita a haka ai ji zanyi kamar babu tufafi a jikina, sabida sunyi min kaɗan."
Ya ƙarishe mgnar yana zura al'kyabbar a jikinshi.
Masha Allah, Haroon yace.
Kana ya matsoshi yana tayashi gyara zaman al'kyabbar yana cewa.
"Duk shigar da kayi tana maka kyau, in na ganka ba al'kyabbar sai inga kamar kafi kyau.
In kuma kasa al'kyabbar sai inga kafi kyau".
Baice dashi komaiba yaci gaba da gyara sakun hiraminshi,
saida ya gama dai-dai-ta hiramin sai ya juya ya nufi, wannan drower'n da hulunanshi ke jere a steps biyu na sama.
Biyu na ƙasan kuma jerin takalmanshi ne.

Fararen takalma masu taushi ya saka ƙirar Gucci,
Zara-zaran yatsunshi sarari sabida ba sau ciki bane ba kuma half cover bane.
turare ya fesa, tare da sa hannunshin ya shafa sajenshi.
Kana ya kalli Haroon daketa ɗaukar shi hoto.
Cikin tura baki Haroon yace.
"Na bari, nasan yanzu zakayi ƙorafi, yanzu ina zakaje?".
Yana fita yace.
"Valli Hospital, akwai yaron da zan duba aikin da akayi mishi".
Bayanshi ya biyo tare da cewa.
"To sai ka dawo".
Ni zamuje wurin Budurwar Jamil taga babban yayanshi.
Wani kallo ya mushi tare da cewa.
"Allah ya shiryeka babban kobo".
Dariya Haroon yayi tare da cewa.
"Eh naji na yarda, zanje yaro ya samu matsala da ita tanata wahal dashi ba dole inje in dai-dai-ta musu matsalar ba".
Juyowa yayi jin abinda Haroon yace cikin sakin gajeren murmushi yace.
"Uhumm yaushe ka zama luwali, bani da lbri, to kai taka matsalarma yaushe ka warware ta, kun iya cikamu da zancen ku ƴan soyayya ne, kuma bakuma san yadda ake soyayya da magance matsalolin ta da tattalinta gudun ta lalaceba".
Wani irin dariya mai sauti Haroon yayi tare sara mishi.
Da sauri ya juya, da nufin tafiya,
sai kuma yaga Umaymah na tsaye a gabanshi.
Hannunta tasa ta kamo nashi tare da janshi suka fara tafiya.
Cikin sanyi yace.
"Oh Umaymah ina zamuje?".
Haroon kuwa baki ya taɓe tare da cewa.
"Wlh gobe zan koma in sha Allah, komai sai an nunawa mana ƴan ubanci".
Dariya Umaymah tayi tare da cewa.
"Allah kiyaye hanya".
Da sauri yace.
"To na fasa tafiya".
Suna gab da fitane yace.
"Umaymah sakeni karmu fita a haka".
Juyowa tayi ta kalleshi tare da cewa.
"To taho".
To yace mata kana yabi bayanta.

Suna tafiya cikin ƴar faffaɗan hanyar da bishiyoyin namijin gwanda yayi musu ƙawanya,
shiyasa wurin yayi sanyi.

A hankali ya kalleta lokacin da suka iso.
Bakin ƙofar Gimbiya Aminatu.
tare da cewa.
"Umaymah me zanyi a ciki?".
Hannunta tasa ta kamo nashi.
Kawai ta kutsa kai ciki. Dole ya bita a baya.
Yana saka ƙafarsa cikin falon yaji zuciyarshi ta buga,
da ƙarfi, lokaci ɗaya ta fara harbawa da sauri-sauri.
Cikin sanyi yace.
"Umaymah barni a nan".
Bata kulashi ba taci gaba da janshi tayi har bakin ƙofar falon Lamiɗo.
wani irin rumtse idanunshi yayi yin yadda zuciyarshi ke barazar fashewa.
Da sallama a bakinta, suka shiga.
Yayinda Lamiɗo da Abbanshi suka amsa mata.
Cikin wani irin azabebben bugun da zuciyarshi keyi, yasa ƙafarshi cikin falon.
yayinda Umaymah ke riƙe da hannunshi tana mishi jagora har zuwa gaban Lamiɗo da Galadima da Abbanshi da kuma Malaminshi Malam Abubakar.
Kana ta tsaya dashi kusa da Aysha tare da rusunawa.
Yayinda shi kuma cikin fargabar yadda ƙirjinshi keyi ya rusa a hankali ya zauna bisa tattausan carpet ɗin dake shimfiɗe a wurin.
Dib, dab, dib, dab, dib, dab. Haka zuciyarshi keyi.
yayinda itama Aysha da bai lura da ita Bama haka zuciyarta keyi,
sabida jin an mutun ya zauna kusa da ita.

A hankali ya lumshe idonshi, sabida bugawar da zuciyoyinsu keyi a tare yasa, ƙarfin nashi bugun ya ɗan ragu kaɗan.


Cikin nitsuwa ya kalli Abbanshi kanshi a sunkuye yace.
"Barka da safiya Abba".
Cikin kula yace.
"Barka dai".
Sai ya kuma kalli Malamin nashi cikin kamala yace.
"Allah hokke sabbugo, Malam Barka da zuwa ya gida?".
Cikin nitsuwa Dattijan yayi murmushi tare da cewa.
"Alhamdulillah Sheykh Jabeer ya hidima".
Alhamdulillah yace, kana ya kalli Lamiɗo da Galadima.
sai kuma ya kauda kanshi.
murmushi Galadima yayi tare da cewa.
"Mu bazaka gaishemu ba kenan?".
Ɗan tsuke fuskarsa yayi tare da cewa.
"Gaggawa dai aikin shaiɗan ne".
Murmushi Lamiɗo yayi sabida ya fahimci duk abinda zasuyi,
sai ya cisu gyara ta kuma fuskar gsky.
Galadima ne yace.
"To ni bari in gaisheka Ina kwana".
Kanshi ya jinina mishi tare da cewa.
"Kayiwa kanka tanadin lada ashirin, a madadin kaɗan da zaka samu in ni na ɗaga maka gaisuwar.
Lfyta lau Alhamdulillah."
Ya ƙarishe mgnar da amsa gaisuwar.
Dariya sukayi kana, ya kalli Lamiɗo a daƙile yace.
"Ina sauri dan inada aikin yi, menene kasa aka jawoni nan".
Ya ƙarishe mgnar a hankali yadda Abbanshi da Malaminshi bazasu jiba.
Kana ya ɗan muskuta ya matsa gefe yayi nesa da Aysha sabida wani tsalle da yakeji zuciyarshi nayi, a madadin bugun da takeyi kafin ya zauna kusa da ita.
Cikin zuba musu ido.
Lamiɗo yayi murmushi sabida sunyi masifar dacewa da juna, shigarsu da ta zamo iri ɗaya tayi matuƙar yi musu kyau.
Cikin wasa irin na kaka da jika yace.
"Ga amaryar taka baku gaisaba, ku gaisa sai ka kaita kuje ka gabatar da ita".
Fuskarshi a haɗe yace.
"Hakan addinine ko al'ada?".
Da sauri Galadima yace.
"Al'adace kuma sai kayi ta".
Ta gefen ido ya kalli Galadima tare da cewa.
"Da ba Galadima za'a bakaba, da sarkin raya al'adu za'a baka".
Shiru yayi jin Abbanshi na cewa.
"Allah ya bamu nisan kwana, kaima watan watarana a gabanka yaranka zasuyi min haka Muhammad".
Cikin yin ƙasa da kai cikin girmamawa da karrama mgnar mahaifin nashi yace.
"Sun isa! Suyi maka haka in barsu".
Murmushi Malam Abubakar yayi tare da cewa.
"Kamar yadda ka isaba".
Shiru yayi gane manufarsu.
Jin duk sunyi shiru ne, yasashi ɗago kai ya kallesu.
Suma shi suka zubawa ido, da sauri yayi ƙasa da kanshi.
Ita kuwa Aysha shiru tayi tamkar ruwa ya cinyeta, tanajin yadda suke musayan kalamai. Sai dai bata fahimtarsu domin, tuno nata ahlin.

Gyaran muryan da Abbansa yayine yasashi ɗago kai ya kalleshi.

Cikin bada umarni Abba ya nuna mishi Aysha tare da cewa.
"Kama hannunta kuje, ka gabatar da ita, ka fara daga sashin ƙannen Lamiɗo, sai na Mamanku, daga nan kuje wurin Gimbiya Saudatu,
dama sauran matansu Babanku Nasiru".
Bisa dole yace.
"To kana ya yunƙa ya miƙa,
da sauri Umaymah ta miƙe tazo ta miƙar da Aysha.
kana ta kamo hannunta ta miƙa mishi alamun ya riƙe hannunta.
Cikin tsuke fuskarsa da kwaɓeta tamkar zai ɗaura hannunshi a ka ya kurma ihu.
Ya zuba mata ido. Muryar Abbanshi ce ta katse tsayuwar da yayi kamar an dashi.
"Riƙe hannunta ku je". A hankali ya ware tafin hannunshi da Umaymah ta kamo
kana lokacin guda yaji zuciyarshi tana tsalle da harbawa, kamar dai tana mararin wani abu.
Hannun Aysha Umaymah tasa mishi cikin nashi tare da meda yatsunshi ta rumtsesu.
Dam-daradam-dam haka zuciyarshi tayi wani masifeffen bugun mai kama da na aradu kana tafara wani irin tsalle.
Ita kuwa Aysha, wani irin tsuma jikinta ya fara lokacin da taji tattausan yatsun hannunshi da fatar tafin hannunshi ya rumtse nata.
Hannun wani irin masifeffen tsoro da kunyane suka diro mata, a lokaci guda.
Shi kuwa Sheykh wani irin asirtace kuma ɓoyeyyen dogon ajiyan zuciya ya sauƙe mai sanyi, jin gaba ɗaya zuciyarshi ta koma ta nitsu tabar wannan tsinkewar da bugawar da tsalle tayi lib a cikin ƙirjinsa.
Jin muryar Jakadiya ne yasa, Sheykh Jabeer, yin ƙarfin halin ɗaga ƙafarshi ta dama.
Jin ya ɗan yi gabane yasa itama, ta ɗaga ƙafarta ta hagu, sai hakan ya bada wata dama ta musamman, ya zama suna ɗaga ƙafafuwan su, a tare kana suna taku a jere.
Sai dai shi ɗin ya ɗan kereta kaɗan.

"Masha Allah. Tabarakallah,". Sune kalaman da Umaymah ke Maimaitawa, lokacin da take biye dasu a baya.

Lamiɗo da kanshi da Galadima sunga wani irin dacewa na musamman a tsakin Muhammad Jabeer da Aysha.
Abba kuwa murmushi yakeyi mai baiyana jin daɗi.
Malam kuwa, Addu'o'in yaketa jero musu na fatan al'khairi da zaman lafiya da nitsuwa da samun zuriya ɗayyiba.

A hankali suke taku yayinda kowa zuciyarshi ke bin takun sawunsa,
A haka suka fito babban falon Gimbiya Aminatu nan suka samu Ummi. Tana ganinsu ta miƙe da tsauri tayi gabansu, hadimai hudu cikin na Gimbiya Aminatu kuwa, sukayi bayan Umaymah dake bayansu.

Shi kuwa Sheykh Jabeer suna fitowa yayi wani irin saurin sake hannunta tare da janye nashi,
Sabida shi ji yake tsikar jikinsa na tashi tamkar ya riƙe wutan lantarki ne sabida masifar tsuma da yaki naman jikinsa nayi.
Murmushi Umaymah tayi ganin still dai suna tafiya a jere a jere suna wani irin taku mai ƙayatarwa.

Suna fitowa, suka samu sallama a bakin mashigar wurin.
Nan ya shaida musu, duk sashukan gidajen anje anyi sallama dasu an kuma basu daman shiga.

Tafiya kaɗan sukayi daga sashin Gimbiya Aminatu,

2 Comments On GARKUWA
avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment